An kashe wani attajiri da matarsa Canada


Mamatan sun bar 'ya'ya hudu.

Image caption

Mamatan sun bar ‘ya’ya hudu

An samu gawar wasu attajirai miji da mata ‘yan kasar Canada a cikin gidansu da ke birnin Toronto, a cikin wani yanayi da ‘yan sanda suka bayyana a matsayin “ba mutuwar Allah da Annabi ba ce.”

Mista Sherman shi ne wanda ya samar da kamfanin hada magunguna na Apotex kuma shi ne shugaban kamfanin.

Yana daya daga cikin manyan masu kudin Canada kuma wanda ya shahara a taimakawa mutane.

A wani bayani da aka fitar a yammacin Juma’a ‘yan sanda sun ce ba a samu wata alama da take nuna da karfi aka shiga cikin gidan ba.

Kafar sadarwa ta kasar sun bayar da rahoton cewa masu bincike ba su gudanar da bincike a kan neman wanda ake zargi a lokacin ba.

Detective Brandon Price ya shaida wa kafar watsa labarai ta kasar (CBC ) cewa, har yanzu masu bincike na kokarin gano ko akwai wanda yake da hannu a cikin lamarin.

‘Yan sanda sun bayar da bayani kadan kuma ba su tabbatar da shaidun matattun ba.

Kodayake, abokai da jami’ai sun ambato sunan wasu da suka nuna razana da tashin hankali da suka ji labarin.

Ministan lafiyar kasar Eric Hoskins ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, “Ba ni da wani abu da zan iya fada a wannna lokacin”.

Ya kuma kara da cewa, “An samu abokaina Barry da Honey Sherman a mace. Mutane masu kirki, masu taimakawa jama’a, manyan jagorori a fagen magani”.

Mai magana da yawun ‘yan sanda ya ce, an kira masu taimakon gaggawa gidan ranar Juma’a.

Constable David Hopkinson ya ce,”yanayin mutuwarsu ya nuna cewa akwai lauje cikin nadi kuma muna bin al’amarin”.

Toronto Globe and Mail ya bayar da rahoton cewa, kwanan nan ne ma’auratan suka saka katafaren gidansu a kasawa, sai kuma dillalen gidaje ya tarar da gawarsu lokacin da ya zo ganin gidan,

Mamatan sun bar ‘ya’ya hudu.

Mista Sherman ya kama kamfaninsa ne a shekarar 1974, kuma yanzu shi ne na bakwai wajen hada magani a duniya.

An yanke wa tsohon minista hukuncin daurin shekara 8 a gidan yari


An yanke wa tsohon minista hukuncin daurin shekara 8

Image caption

An yanke wa tsohon minista hukuncin daurin shekara 8

Kotin Moscow ta yanke wa tsohon ministan tattalin arzikin Rasha Alexei Ulyukayev hukuncin daurin shekara takwas a gidan yari bisa laifin cin hanci.

Har ila yau an ci tarar shi fiye da fam miliyan daya. Shi ne minista na farko da aka taba yankewa hukunci tarihin Rasha na baya-bayan nan.

An kama Ulyukayev mai shekara 61 a shekarar 2016, inda aka tuhumeshi da kokarin yin almundahana na dala miliyan biyu daga kamfanin mai mallakin gwamnati.

boss ne ya tuhumeshi, na hannun daman shugaba Vladimir Putin.

Rosneft boss Igor Sechin ya bukaci ya gabatar shaida amma ya gaza hakan.

Allkali ne ya karanto hukunci inda yake cewa”Ulyukayev ya yi amfani da mukaminsa don ya bukaci cin hanci daga Rosneft chief Sechin, ta hanyar musayar bayar da amincewa, a kan sayar da kamfanin mai da gas na Bashneft mallakin gwamnati.

Mr Feoktistov ya ce, Mr Sechin ya shaida masa cewa “Amfani da yatsu biyu da ya yi ya nuna cewa kudin da ya bukaci ya karba sun kai dala miliyan biyu.

Zawarci: ‘Rashin miji babban tashin hankali ne’

Adikon Zamani filin ya duba batun zawarcin ne a tsakanin mata. Wadanne matsaloli zawarawa ke fuskanta a kasar Hausa?

Latsa alamar lasifikar da ke sama don jin ganawar da aka yi da wadansu zawara kan batun.

Adikon Zamani tare da Fatima Zahra Umar

Ana iya cewa abu mafi muni da ka iya faruwa a wajen mace a yankin arewacin Najeriya shi ne ta zama bazawara.

Ana kallon mata zawarawa a yankin matsayin wadanda ba su da daraja.

Ko kuma wadanda ba su da kima muddin suna amsa sunan zawarawa.

Irin wadannan matan sau da yawa ana takura musu da tsangwama da kuma gulmace-gulmace.

Bazawara a kasar Hausa ba ta da wani aji da ake saka ta a cikin al’umma, tun da ta wuce a kirata budurwa kuma ita ba matar aure ba ce.

Bazawara na tsakankanin wani gurbi mai hadari a tsakanin ‘yan matanci da kuma zaman aure, wanda aka fi sani da “zawarci”.

Kasancewar mace bazawara ba wai wulakanci kawai yake jawo wa mace a cikin al’umma ba a arewacin Najeriya, har da haifar da matsala a bangaren abin batarwa na yau da kullum.

Domin kuwa hakan ba karamar barazana ba ce, domin kuwa ba kowacce mace ba ce take da halin daukar dawainiyar kanta.

A wannan makon filin Adikon Zamani ya tattauna da wasu zawarawa da suka fada irin wannan hali.

Wadannan zawarawa na fuskantar wulakanci da muzgunawa a cikin al’umma, kuma suna yin iya kokarinsu don ganin sun fita daga cikin wanann halin.

Mun tambaye su wane irin hali da nuna wariya zawarawa suke fuskanta a cikin al’umma, da kuma yadda maza suke ci gaba da yin saki ba tare da kwakkwaran dalili ba.

 

http://www.bbc.com/hausa/labarai-42377850

'Ancelotti zai koma Chelsea'


Carlo AncelottiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bayern Munich ta kori Ancelotti a watan Satumba

Tsohon Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti zai koma Chelsea a matsayin sabon kocinta a kakar wasa ta badi, a cewar jaridar Daily Record.

Dan wasan Chelsea Batshuayi zai bar kungiyar a watan gobe amma zai tafi aro ne, kamar yadda jaridar London Evening Standard ta bayyana.

Kocin Manchester United Jose Mourinho zai sayi sabbin ‘yan wasa a watan gobe duk da cewa shi ba mai kaunar yin hakan ba ne a kasuwar saye da ‘yan wasa ta watan Janairu, in ji jaridar Daily Mail.

Kocin tawagar Masar Hector Cuper ya ce kungiyar Real Madrid tana zawarcin dan wasan Liverpool Mohamed Salah, yayin da Kocin Madrid Zinedine Zidane ya ce yana jinjina wa kwarewar dan kwallon, kamar yadda jaridar Daily Sun ta bayyana.

Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona ya ce ya ba Madrid shawarar ta sayi Kylian Mbappe gabanin kungiyar PSG ta riga ta, in ji kafar yada labarai ta Goal.com

Mu za mu sa Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 – Malami


Nigeria Justice Minister Abubakar Malami

Image caption

Shugaba Buhari bai bayyana matsayinsa ba game da zaben 2019

Ministan Shari’ar Najeriya Barista Abubakar Malami ya ce za su roki Shugaban Kasar Muhammadu Buhari don ya sake tsayawa takara a babban zaben kasar wanda za a yi a shekarar 2019.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kawo mana a ofishinmu na Landan kwanakin baya.

Sai dai babban lauyan gwamatin kasar ya ce shugaban bai sanar da su matsayinsa a kan hakan ba tukuna, amma ya ce su a shirye suke su “roke shi da ya sake tsayawa takarar saboda ganin abubuwa na alkairi da shugaban ya faro a kasar sun wanzu.”

Yayin da aka tambayi ministan ko zai amsa kiran nasu, ganin cewa su mukarrabansa ne.

Sai ya kada baki ya ce “za su tsananta roko.”

Game da batun talauci da al’ummar ke fama shi kuwa, ministan ya ce abubuwa suna “kyautatuwa” ganin yadda kasar ta fara yin karfi a bangaren noma.

Har ila yau ya bayyana cewa an samu ci gaba ta fuskar tsaro, inda ya ce “a baya ma ai ba batun talauci ake yi, batun rayuwa ake yi.”

 • Latsa alamar lasifika a hoton da ke kasa don sauraron hirar

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Za mu tsananta rokon Buhari kan tazarce’

Yadda hijabi ya hana wata zama lauya a Nigeria


A halin yanzu dai Firdaua ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta "kira ta"

Image caption

A halin yanzu dai Firdaus ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta “kira ta”

An hana wata ‘yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama lauya – mai iya aiki a kotu – saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.

Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.

Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet na Nigerianlawyer.com.

Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A jihar Legas ma dai sai da aka kai maganar saka hijabi a makarantin sakandare kotu

Wata mata dai ta wallafa wani sako a shafin sa da zumunta na Instagram inda ta yi korafin cewa masu kula da lamuran dokar Najeria sun yi wa wata “‘yar uwa” wariya tana mai amfani da maudu’in #justiceforFirdaus.

Tuni dai ‘yan Najeriya suka yi ta tafka muhawara a kotu kan hana mai saka hijabin zama lauya.

Wannan batu dai shi ne ya mamaye kafofin sada zumunta a Nigeria tun daga ranar da wannan abun ya faru.

Misali wasu ma’abota shafukan twitter sun yi ta yada hotunan ita wannan daliba da aka hanata zama cikakkiyar lauya.

Wasu kuma sun yi ta yada hotunan daya daga cikin ‘ya’yan shugaban Najeriya wacce a bara ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin lauya.

Shima shugaban Kungiyar lauyoyin wato A B Mahmoud ya wallafa wani hoto na ‘yarsa a shafinsa na twitter inda a hoton ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin lauya a birnin New York na kasar Amurka.

Ya kara da cewa kungiyar lauyoyi ta Najeriya za ta yi kokarin ganin an kawo karshen wannan batu na hana lauyoyi masu son sanya hijabi.

Nigeria: Ana ci gaba da muhawara kan 'hana' Musulma zama lauya saboda sanya hijabi


A halin yanzu dai Firdaua ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta "kira ta"

Image caption

A halin yanzu dai Firdaus ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta “kira ta”

An hana wata ‘yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama lauya – mai iya aiki a kotu – saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.

Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.

Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet na Nigerianlawyer.com.

Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A jihar Legas ma dai sai da aka kai maganar saka hijabi a makarantin sakandare kotu

Wata mata dai ta wallafa wani sako a shafin sa da zumunta na Instagram inda ta yi korafin cewa masu kula da lamuran dokar Najeria sun yi wa wata “‘yar uwa” wariya tana mai amfani da maudu’in #justiceforFirdaus.

Tuni dai ‘yan Najeriya suka yi ta tafka muhawara a kotu kan hana mai saka hijabin zama lauya.

Wannan batu dai shi ne ya mamaye kafofin sada zumunta a Nigeria tun daga ranar da wannan abun ya faru.

Misali wasu ma’abota shafukan twitter sun yi ta yada hotunan ita wannan daliba da aka hanata zama cikakkiyar lauya.

Wasu kuma sun yi ta yada hotunan daya daga cikin ‘ya’yan shugaban Najeriya wacce a bara ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin lauya.

Shima shugaban Kungiyar lauyoyin wato A B Mahmoud ya wallafa wani hoto na ‘yarsa a shafinsa na twitter inda a hoton ta halarci taron tabbatar da ita a matsayin lauya a birnin New York na kasar Amurka.

Ya kara da cewa kungiyar lauyoyi ta Najeriya za ta yi kokarin ganin an kawo karshen wannan batu na hana lauyoyi masu son sanya hijabi.

Russia 2018: FIFA ta yi gargadi ga Spain


World CupHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Spain na cikin manyan kasashen da za su iya lashe kofin duniya a Rasha

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi gargadi ga hukumar kwallon Spain kan yadda gwamnatin kasar ke katsalandan ga sha’anin zaben shugabancin hukumar.

Rahotanni sun ce gwamnatin Spain ta tuntubi hukumar kwallon kafar kasar kan batun wanda ta ke son ya maye gurbin tsohon shugaban hukumar Angel Maria Villar wanda ya yi murabus a watan Yuli saboda zargin rashawa.

A tsarin FIFA, ana na iya dakatar da wakilcin kasar da gwamnati ta yi katsalandan a sha’anin zaben shugabannin hukumar kwallon kafa.

FIFA ta aike da wasikar gargadi ga hukumar kwallon Spain, tana mai yin kashedi ga duk wani mataki na tsoma bakin gwamnati.

Idan har hakan ta tabbata, FIFA na iya korar Spain daga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a 2018.

FIFA ta fadi a cikin wata sanarwa cewa za ta tura tawagar jami’anta da na hukumar kwallon kafar Turai UEFA zuwa Madrid domin gudanar da bincike tare da sa ido ga sha’anin hukumar kwallon kafar Spain.

Shugaban hukumar kwallon Spain na rikon kwarya Juan Luis Larrea ya tabbatar da cewa sun karbi takardar gargadin daga FIFA, kuma ya ce sun gabatar da sakon ga ministan wasannin kasar.

Kaftin din Spain Sergio Ramos ya ce ba zai taba yadda ace Spain ta rasa abin da suka yi fafutika ba.

Spain dai ta taba lashe kofin duniya da aka gudanar a Afirka ta kudu a 2010, kuma ko yanzu kasar na cikin kasashen da ake ganin za su iya lashe kofin gasar da za a gudanar a Rasha a badi.

A 2015 FIFA ta taba haramtawa Indonesia buga wasannin neman zuwa gasar cin kofin duniya saboda tsoma bakin gwamnati a harakokin hukumar kwallon kafar kasar.

Kanu da Diouf sun jagoranci wasan tallafi ga 'yan gudun hijira a Kano


KanuHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kanu Nwakwo na Najeriya da Elhaji Diouf na Senegal ne suka jagoranci wasan a Kano

Tsoffin gwarzayen Afirka da suka kunshi Elhaji Diouf da Kanu Nwakwo da Garba Lawal da Tijjani Babangida sun kara da kungiyar Kano Pillars a wasan neman tara tallafin kudi ga ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram.

‘Yan wasan sun amsa kira ne daga bangarori daban-daban na nahiyar Afirka, inda suka hada tawaga guda don yin wasa mai manufa daya. Duk da cewa shekaru sun fara kama galibinsu.

Tsoffin zaratan ‘Yan kwallon da suka yi fice a Afrika sun nuna wa duniya cewa har yanzu tauraruwarsu na haskawa.

Sai dai masu iya magana na cewa “Mai laya ya kiyayi mai zamani”, inda ‘yan wasan Kano Pillars, suka nuna tsoffin zakarun gasar Firimiyar Najeriya ne, ta hanyar nuna wa mazan-jiyan cewa lokacinsu ne.

Kano Pillars dai ta samu nasara a wasan da ci 2-1. Amma, rashin samun nasarar tsoffin ‘yan wasan na Afrika ba shi ne sakon da wasan ke son isarwa ba, illa manufar shirya wasan. Kuma ko ba komai dama ce ta sada zumunci tsakanin tsoffin ‘yan wasan da kuma takwarorinsu na yanzu.

Wasan dai ya ba daruruwan masoya kwallon kafa yin cudanya da tsoffin gwanayen wadanda tarihin kwallon kafa a Najeriya da ma Afrika ba zai taba mantawa da su ba musamman mafi yawancinsu suna cikin tawagar Najeriya da suka lashe zinari a wasannin Olympics a 1996.

Mutane sama da miliyan daya ne rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu. Kuma galibi tsoffin ‘yan wasa a duniya kan gudanar da wasa na musamman domin tara kudin tallafi ga wadanda wani bala’i ya shafa.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli kanu da Elhaji Diouf da Garba Lawal da Tijjani Babagngida a fili

A Najeriyar dai an kfa gidauniya iri-iri, duka da nufin tallafa wa masu gudun-hijira, amma za a iya cewa wannan ne karon farko da gwarzayen kwallon kafa daga sassan nahiyar Afirka suka yi gangami don agazawa ta hanyar taka-leda, tare da nuna irin tasirin da kwallon kafa ke yi wajen hada kan duniya.

Nigeria: An nada sabon Sarkin Katagum


Alhaji Baba Umar FarukHakkin mallakar hoto
TWITTER

Image caption

Ya taba rike babban sakatare a ma’aikatun gwamnatin tarayya da dama

Gwamnatin jihar Bauchi da ke Najeriya ta nada Alhaji Baba Umar Faruk a matsayin sabon Sarkin Katagum.

Sabon sarkin shi ne babban dan marigayi Sarkin Katagum Kabir Umar, wanda ya rasu a makon jiya bayan ya sha fama da jinya.

Lifindin Katagum, Alhaji Magaji abdulkadir Dahuwa ya shaida wa BBC cewa mutum biyar ne suka nemi sarautar ta Katagum, amma gwamnatin jihar ta zabi Alhaji Baba Umar Faruk.

An haifi sabonSarkin ne a shekarar 1957 a garin Azare.

Yana da digiri na farko a fannin Tarihi, sannan ya kammala digiri na biyu a fannin Kasuwanci.

Ya taba rike babban sakatare a ma’aikatun gwamnatin tarayya da dama kuma kafin nadin nasa shi ne Hakimin Shira da ke gundumar Katagum.

Image caption

Sarkin Katagum Kabir Umar ya rasu a makon jiya

Nigeria: An yanke hukuncin kisa kan sojan da ya kashe fararen hula


Nigerian armyHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun dade suna zargin sojojin Najeriya da kashewa da kuma cin zarafin fararen hula

Wata kotun soji a Najeriya ta yanke hukuncin kisa a kan wani jami’in sojin kasar bayan kama shi da laifin kisan wasu fararen hula a yankin arewa maso gabashi da ake yaki da Boko Haram.

Kotun sojin ta musamman a Maiduguri ta zartar da hukuncin ne kan koforal John Godwin da ta samu da laifin kisan fararen hula biyar da sojoji suka kubutar a garin Yamteke.

Jami’in wanda yana cikin rundunar Lafiya Dole da ke fada da Boko Haram, ya harbe mutanen ne a garin Maiduguri, a yayin da ake tsare da su domin amsa tambayoyi.

A cikin sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta ce kotun ta kuma daure wani jami’in soja rai da rai mai suna Innocent Ototo wanda kotun ta samu da laifin azabtarwa da kisan wani yaro dan shekaru 13 bayan jami’in ya zarge shi da sace wayarsa ta salula a Maiduguri.

Sannan kotun ta kuma zartar da hukuncin daurin shekaru 20 a kan wasu jami’an soja guda biyu kan laifin kisa da mallakar makamai ta hanyar da ba ta dace ba.

Rundunar sojin Najeriya ta ce laifukan da jami’an suka aikata sun saba dokokin kasa da na duniya.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na gida da na waje dai sun dade suna zargin sojojin Najeriya da kashewa da kuma cin zarafin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, zargin da rundunar sojin kasar ta sha musantawa.

Rwanda ta haramta sha da shigo da tabar Shisha


Rwanda ShishaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rwanda yanzu ta bi sahun Tanzania da Saudiya da wasu kasashen duniya da suka haramta shan Shisha

Matakin Gwamnatin Rwanda na haramta zukar tabar Shisha ya janyo cece-kuce tsakanin ‘yan kasar da ma kasashen da ke makwabtanka da ita.

Wasu ‘yan kasar na shakku kan cewa gwamnatin ta dauki matakin haramta tabar ne domin kare kudaden shiga da ta ke samu daga kasuwar taba sigari.

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya ta fitar a kwanan baya ya bayyana cewa hayakin da ake zuka daga tabar Shisha na tsawon sa’a daya, kamar kwatankwacin zukar hayakin taba sigari guda 100 ne.

Rwanda yanzu ta bi sahun makwabciyarta Tanzania da wasu kasashe kamar Saudiya da Pakistan da Jordan da Singapore da suka haramta shan tabar Shisha.

Wasu ‘yan Rwanda dai na ganin idan har za a haramta shan shisha to ya dace a haramta shan taba sigari.

Shan tabar Shisha dai yanzu ya kasance ado musamman ga matasa a kasashen Afirka.

Rwanda kuma ta haramta shigo da tabar da tallarta da kuma sha saboda dalilai na kare lafiya musamman barazanar cutar kansa da huhu.

Me Tottenham za ta yi wa Man City ranar Asabar?


MeTottenham za ta yi wa Man City ranar Asabar?

Image caption

Me Tottenham za ta yi wa Man City ranar Asabar?

Tottenham na fatan kare kambunta, kuma koma dai me zai faru a karawarsu da Manchester City ranar Asabar, su dai suna fafatukar yadda za su kare a cikin manyan kungiyoyi hudu na teburin firimiya.

Sai dai kungiyar har yanzu za ta iya jajircewa a wasan nasu don samun nasara a gaba, inda suka fara yadda zasu tunkari wasan.

A kungiyar da take magana game da kansu a matsayin zakarun gasar Firimiya na nan gaba, tarihin da suka kafa a karkashin jagorancin Pochettino a wasansu a waje da sauran karawarsu a kakar bara sun kare ne a cikin manyan kungiyoyi shida a teburin firimiya.

Ba wai kawai rashin nasarar da suke samu a sakamakon wasansu ba. Ba zan iya tuna wani kokari da kungiyar ta yi a kowanne wasa da ta buga a waje ba, daga White Hart Lane ko Wembley.me.

Saboda haka ya kamata a wannan karon su sauya salo, su kuma jajirce a manyan wasan da zasu tunkara.

Hakan zai iya faruwa idan suka nuna kwazo, musamman a lokacin da zasu fara, fiye da idan suka dogara da tunanin da suke na cewa, “Mun iya buga tamaula, mun zo ne don mu taka leda mai kyau”, sai ta zo musu da sanmatsi, kamar yadda suka yi da Arsenal a watan November.

A wurina, Kungiyar tana gani zata iya samun dukkan nasara a wasan da zai zo a nasu tunanin. Ko suna da yakinin cewa kungiyar zata iya samun gurbin zama ta hudu a teburin Firimiya?

Suna son su nuna hakan yauzu, saboda duk abin da na gani a wurinsu a Anfield ko Old Trafford sama da shekaru da dama da suka shude, musamman kuma a filin wasa na Emirates a kakar bana, abu ne da basu da yakini.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Harry Kane ya buga wasa 16 cikin 17 da Tottenham ta fafata a cikinsu zuwa yanzu kuma ya ci kwallo 12 a kakar wasa ta 2016-17

Victor Wanyama bai taka leda ba tun watan Agusta sakamakon raunin da ya ji, kuma Pochettino bai samu mai tsaron tsakiya da zai maye gurbinsa ba.

Harry Wink yana kokari wajen taka leda, kuma akwai lokutan da ya taka rawa sosai amma salon wasan da ya buga ya ba wa wasu ‘yan wasan dama.

Ba zan ce Spurs sun samu matsala a kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ba, saboda sun sayo Davinson Sanchez wanda kuma yana cikin manyan ‘yan wasa.

Sai dai sun rasa fitaccen mai tsaron baya a Firimiya lokacin da Kyle Walker joined ya koma City.

Idan ka kalli City da kuma yadda take taka leda a bana, ta sha gaan kungiyoyi.

Babban fatan da Spurs take yi shi ne ta mamayesu, ba wai su koma tsren baya ba. Idan kuka yi haka kuwa daga karshe City zata kai ku kasa.

Na ga yadda kungiyar Shakhtar Donetsk da Napoli suka yi da City a wasansu na zakarun Turai, dukkansu sun taka rawar gani kodayake ba suyi nasara.

Idan suka jajirce, ina ganin Spurs zata iya cin kwallo ranar Asabar.

Nigeria: An 'hana' Musulma zama lauya saboda ta sanya hijabi


A halin yanzu dai Firdaua ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta "kira ta"

Image caption

A halin yanzu dai Firdaua ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta “kira ta”

An hana wata ‘yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama lauya – mai iya aiki a kotu – bayan saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.

Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.

Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet Nigerianlawyer.com.

Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin karan keta hakkinta na bil Adama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A jihar Legas ma dai sai da aka kai maganar saka hijabi a makarantin sakandare kotu

Wata mata dai ta wallafa wani sako a shafin sa da zumunta na Instagram inda ta yi korafin cewa masu kula da lamuran dokar Najeria sun yi wa wata “‘yar uwa” wariya tana mai amfani da maudu’in #justiceforFirdaus.

Tuni dai ‘yan Najeriya suka yi ta tafka muhawara a kotu kan hana mai saka hijabin zama lauya.

An hana wasan tartsatsin wuta a Ghana lokacin Kirsimeti


Sayan wuta mai tartsatsi na karuwa a nahiyar Afirka a lokacin KiristimetiHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sayan wuta mai tartsatsi na karuwa a nahiyar Afirka a lokacin Kiristimeti

‘Yan sandan Ghana sun yi barzanar gurfanar da duk wanda ya yi amfani da tartsatsin wuta mai hatsari a lokacin bukukuwan Kiristimeti domin kare rayukan jama’a.

An haramta amfani da tartsatsin wutan ne bisa la’akari da wata dokar shekarar 1999, kuma an bai wa jami’an tsaro umarnin kama “duk wani mutum ko kuma mutane” da suka ki bin umarnin hana amfani da tartsatsin, in ji wata sanarwar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda David Eklu ya fitar.

A wata hira da wakilin BBC, ya kara da cewa “mutane da dama suna tunanin cewa wannan dokar ta daina aiki, amma muna amfani da wannan damar domin tabbatar wa mutane cewa za mu kaddamar da dokar yadda ya kamata.

“Wannan ba zai dauke farin cikin bikin Kiristimeti ba domin tartsatsin wuta mai hatsari kawai aka haramta amfani da shi. Ya fi dacewa ka kare kanka da makwabtanka, a kan ka samu kanka a asibiti a lokacin Kiristimeti.”

An dakatar da zirga zirgar jiragen sama a sabon filin saukar jiragen sama na Dakar babban birnin Senegal


Na'urar kulla da tashi da saukar jiragen sama

Image caption

Na’urar kulla da tashi da saukar jiragen sama

An dakatar da tashi da saukar jiragen sama a sabon filin jirgin sama na Dakar babban birnin kasar Senegal.

Ma’aikatan filin jirgin saman dai sun shiga yajin aiki ne mako guda bayan da aka bude filin jirgin saman.

Ma’aikatan na korafi kan batun albashi da sauran hakkokin su lamarin daya haifar da tsaiko a zirga zirgar jiragen sama a baki daya.

Daruruwan matafiya ne lamarin ya rutsa da su sakamakon yajin aikin.

Paul Francois Gomis shugaban kungiyar kwadon ya shaidawa BBC cewa ”masu kula da harkar zirga-zirgar jiragen sun nuna rashin gamsuwar da yadda yanayin aikin ke gudana.

Kamfanonin jiragen kasar Portuguese ko kuma Portugal sun sanar da cewa an dage tashi da kuma saukar wasu jiragen su.

A halin yanzu kamfanonin jirage da dama na karkata akalar su zuwa Banjul babban birnin Gambia.

Shi dai wannan sabon filin saukar jirage na Blaise Diagne an kashe dala miliyan 600 wajen gina shi.

Yajin aikin dai zai kasance na kwana guda ne to sai dai duk da haka matafiya da dama sun shiga wani mawuyacin hali .

Kotu ta dakatar da El- Rufai daga korar malaman Firamare


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana goyi bayan sallamar malamai kimanin 22,000 wadanda suka fadi jarrabawarHakkin mallakar hoto
NASIR EL-RUFA’I TWITTER

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana goyi bayan sallamar malamai kimanin 22,000 wadanda suka fadi jarrabawar

Kotun Ma’aikata ta kasa wato National Industrial Court a Kaduna ta yanke hukuncin dakatar da korar malaman makarantun Firamare sama da dubu ashirin da gwamnatin jahar Kaduna ta dauri aniyar yi.

Gwamnatin dai ta ce zata yi hakan bayan da malaman suka fadi jarrabawar ‘yan aji hudu na Firamare wacce aka yi musu a watan Oktoba.

Alkalin kotun Justice Lawal Mani ne dai ya bada umarnin dakatar da korar har sai lokacin da kotun ta duba tare da yanke tabbatacce hukunci a bisa wannan kara.

Kotun dai dage sauraren karar har zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun 2018.

Daya daga cikin dubban malaman Firamaren da gwamnatin El- Rufa’i ta sallama daga aiki ta ce gwamnatin Kaduna ta yi “diban karan mahaukaciya ne kawai” wajen tantance malaman da ta sallama.

Malamar wadda ta ce ta shafe tsawon kimanin shekara tana koyarwa inda ta kai har matakin shugabar makaranta ta ce sun yi mamaki da jerin sunayen da aka fitar a matsayin wadanda gwamnati ta tantance.

Ta yi ikirarin cewa sunayen wadanda ba su cancanci su fito ba ma, “sun fito, kamar wadanda suka rasu da wadanda suka yi ritaya da masu gadi. Sunayensu sun fito a matsayin wadanda suka cancanci su ci gaba da koyarwa.”

Malamar wadda ba ta yarda a kama sunanta ba ta ce akwai mamaki a ce kamar ita, da ke da takardar shaidar malanta ta Grade II da NCE da kuma shaidar karatun digiri amma a ce ba ta cancanci koyarwa ba.

Harkar ilimi a Najeriya al’amari ne da aka dade ana kokawa kan tabarbarewarsa, musamman ma a arewacin kasar.

Kotu ta dakatar da El- Rufai daga korar malaman Firamare


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana goyi bayan sallamar malamai kimanin 22,000 wadanda suka fadi jarrabawarHakkin mallakar hoto
NASIR EL-RUFA’I TWITTER

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana goyi bayan sallamar malamai kimanin 22,000 wadanda suka fadi jarrabawar

Kotun Ma’aikata ta kasa wato National Industrial Court a Kaduna ta yanke hukuncin dakatar da korar malaman makarantun Firamare sama da dubu ashirin da gwamnatin jahar Kaduna ta dauri aniyar yi.

Gwamnatin dai ta ce zata yi hakan bayan da malaman suka fadi jarrabawar ‘yan aji hudu na Firamare wacce aka yi musu a watan Oktoba.

Alkalin kotun Justice Lawal Mani ne dai ya bada umarnin dakatar da korar har sai lokacin da kotun ta duba tare da yanke tabbatacce hukunci a bisa wannan kara.

Kotun dai dage sauraren karar har zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun 2018.

Daya daga cikin dubban malaman Firamaren da gwamnatin El- Rufa’i ta sallama daga aiki ta ce gwamnatin Kaduna ta yi “diban karan mahaukaciya ne kawai” wajen tantance malaman da ta sallama.

Malamar wadda ta ce ta shafe tsawon kimanin shekara tana koyarwa inda ta kai har matakin shugabar makaranta ta ce sun yi mamaki da jerin sunayen da aka fitar a matsayin wadanda gwamnati ta tantance.

Ta yi ikirarin cewa sunayen wadanda ba su cancanci su fito ba ma, “sun fito, kamar wadanda suka rasu da wadanda suka yi ritaya da masu gadi. Sunayensu sun fito a matsayin wadanda suka cancanci su ci gaba da koyarwa.”

Malamar wadda ba ta yarda a kama sunanta ba ta ce akwai mamaki a ce kamar ita, da ke da takardar shaidar malanta ta Grade II da NCE da kuma shaidar karatun digiri amma a ce ba ta cancanci koyarwa ba.

Harkar ilimi a Najeriya al’amari ne da aka dade ana kokawa kan tabarbarewarsa, musamman ma a arewacin kasar.

Mallika Sherawat ta ‘kasa’ biyan kudin hayar gida a Paris


Bollywood star Mallika SherawatHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Malika Sherawat ‘yar fim da ta kasa biyan kudin haya a Paris

Fitacciyar ‘yar fim din Bollywwod Malika Sherawat na fuskantar barazanar kora daga gidan da ta take haya tare da mijinta a Paris.

Ana bin Ma’auratan bashin kudin haya da suka kai 80,000 na yuro, kuma an tsayar da ranar da kotu za ta yanke hukunci game da batun a Paris.

Lauyan da ke kare ma’auratan ya ce da gangan suka ki biyan kudin hayar saboda harin da aka kai wa ‘yar fim din a cikin gidan a bara.

Amma yanzu haka wanda ke da mallakin gidan ya bukaci a kwace kayayyakin da suka mallaka a cikin gidan hadi da agogo mai tsada.

Gidan da Malika Sherawat ke haya yana cikin gidajen unguwar masu hannu da shuni da ake kira “16 Arrondissment” a Paris inda mafi yawanci ofisoshin jekadan kasashen waje suke.

Lauyan da ke kare mai Mai gidan ya ce babu wata tattaunawar da suke tsakaninsu game da sabunta hayar, duk da cewa Malika da mijinta suna da halin biyan hayar.

Ko da yake lauyan ma’aurantan ya amsa cewa suna cikin yanayi na rashin kudi.

Malika Sherawat ta fito a finafinan Bollywood sama da 40.

Damisa ta tarwatsa taron biki


Damisa ta tarwatsa mutane suna tsaka da shagalin bikiHakkin mallakar hoto
CHRISTIAN CHARISIUS

Image caption

Damisa ta tarwatsa mutane suna tsaka da shagalin biki

Wasu mutane saun tsalleke rijiya da baya a wurin taron biki a Indiya, bayan da wata damisa ta yi musu dirar mikiya daga dajin da ke makwabtaka da su.

Bidiyon da abun ya faru ya nuna yadda mutane suke gudun ya- da kanin wani da kuma haura katanga don tserewa daga wurin taron.

Ba wanda ya ji rauni kuma ba dadewa damisar ta shige cikin surkukin bishiyoyi aka neme ta aka rasa.

Sai dai jim kadan kuma ta afka wa wata mata tayi mata rauni a kauyen da ke kusa da su.

Yanzu dai hukumar da ke kula da daji ta jihar Madhya Pradesh na lura da shige da ficen dabbobi, inda damisar ta taratsa yankin.

Kun san kasar da beraye ke aikin likitoci?


Tanzania za ta yi amfani da berayen a wasu kananan asibitoci 60 a fadin kasar.Hakkin mallakar hoto
LIFE ON WHITE ALAMY

Image caption

Tanzania za ta yi amfani da berayen a wasu kananan asibitoci 60 a fadin kasar.

Kasar Tanzania tana kokarin rubanya yawan berayen da take horas da su wajen sansano kwayar cutar tarin fuka wato TB saboda yadda suke da saurin gano ta.

Su dai berayen an horas da su ta yadda za su gano cututtuka masu halaka jama’a ta hanyar sunsuna majinar mutane.

Haka kuma cikin minti 20 kacal, berayen za su iya sunsuno majinar mutane 100, wanda sai jami’an kiwon lafiya masu aiki a dakunan binciken cututtuka sun kwashe kwanaki hudu kafin su iya yin haka.

A yanzu dai Tanzania za ta yi amfani da berayen a wasu kananan asibitoci 60 a fadin kasar.

Kusan shekara goma da ta wuce ne wata gidauniya da ke kasar Belgium ta fara amfani da berayen saboda saukin kudi da kuma sauri da suke da shi wurin aikin idan aka kwatanta da ainahin hanyoyin da aka saba bi wajen gwaji don gano kwayar cutar ta tarin fuka.

Kasar Tanzania dai na cikin kasashe 30 da ake ganin sun fi fama tare da yada cutar ta tarin fuka, wadda tana daya daga cikin cutukan da suka fi hadari a duniya, kodayake ana maganinta da rigakafinta.

Klitschko ya sayar da rigar da ke dauke da hasashen dambensa da Joshua naira miliyan 78


Wladimir KlitschkoHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wladimir Klitschko ya sha kashi a karo na biyar a tarihinsa na damben a karonsa da Anthony Joshua a Wembley

A watan Afrilu, Wladimir Klitschko ya sayar da rigar da ya shiga fage da ita wadda ke dauke da ‘yar ma’adanar bayanan kwamfuta ta tafi da gidanka (USB stick), mai kunshe da hasashen yadda dambensa zai kasance da Anthony Joshua, wanda ya doke shi, a kan fam dubu 160.

Klitschko tsohon zakaran damben boksin na mafiya nauyi na duniya mai shekara 41, ya sanya doguwar rigar ne ya zo dandalin, kafin damben nasa na karshe a Wembley, da zakaran na duniya na yanzu Anthony Joshua.

An dinke ‘yar na’urar ne a jikin rigar wadda ke dauke da hasashensa na yadda yake ganin damben zai kaya, wanda ya ce mutumin kawai da zai ji wannan hasashe shi ne wanda ya sayi rigar.

A turmi na goma sha daya Joshua ya doke Klitschko dan Ukraine, wanda tuni ya yi ritaya daga damben boksin din.

Kudin da aka samu na sayar da rigar a wurin wani taron samar da tallafi a Landan ranar Laraba, za a yi amfani da shi ne a ayyukan da Gidauniyar Klitschko ke taimaka wa.

Kofin Cecafa: Kenya ta kai wasan karshe bayan doke Burundi 1-0


'Yan wasan KenyaHakkin mallakar hoto
OTHERS

Image caption

Kenya ta tsira ne bayan da a cikin lokacin fitar da gwani dan wasanta Whyvonne Isuza ya ci mata kwallon

Kenya ta kai wasan karshe na gasar cin kofin majalisar hukumomin kwallon kafa ta Afirka ta tsakiya da ta gabashin Afirka Cecafa, bayan da ta doke Burundi da ci 1-0 a ranar Alhamis.

Bayan kammala minti 90 na wasan ne ba ci aka shiga lokacin fitar da gwani, har mai masaukin baki Kenya, karkashin jagorancin sabon kociyanta Paul Put, wanda a watan da ya wuce ne ya kama aiki ta samu damar jefa kwallon daya.

Dan wasan Kenya Whyvonne Isuza, shi ne ya jefa kwallon bayan minti hudu da fara wa’adin raba gardamar tsakanin ‘yan wasan kasashen biyu.

Yanzu tawagar ta Harambee Stars tana jiran wadda za ta yi nasara a daya wasan kusa da karshen a ranar Juma’a tsakanin mai rike da kofi Uganda da kuma Zanzibar.

An tuhumi Jose Mourinho a kan Manchester City


Jose Mourinho da Pep GUardiolaHakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Dangantaka ta kara tsami tsakanin Jose Mourinho da Pep Guardiola bayan wasansu na hamayya

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta umarci kociyan Manchester United Jose Mourinho da ya fayyace mata wasu kalamai da ya yi kafin wasansu na hamayya na ranar Lahadi wanda Manchester City ta doke su 2-1.

Hukumar ta bukaci hakan ne kan maganganun da ya yi a lokacin taron manema labarai na shirye-shiryen tunkarar wasan, a ranar Juma’a.

A lokacin Mourinho, wanda aka ba wa wa’adin zuwa karfe 6:00 na yamma agogon GMT, ranar Litinin ya bayar da bayani, ya ce ‘yan wasan City suna da saurin faduwa, ta yadda ko da iska ce ‘yar kadan ta taba su sai su je kasa.

Mourinho, mai shekara 54, ya kuma ce ba ya jin za a bar shi ya yi wasu kalamai na siyasa a filin wasa kamar Guardiola, wanda a kwanan nan aka gan shi ya sanya wata roba mai ruwan dorawa a hannunsa, ta alamar nuna rashin goyon baya kan tsare masu rajin neman ‘yancin yankin Catalonia na Spaniya.

United ta yi rashin nasara a wasan da City da ci 2-1 a Old Trafford, ya zamanto abokan hamayyar sun ba ta tazarar maki 11 a teburin na Premier.

A yayin bureden murnar cin United din aka je fi Mourinho da ruwa da madara a kofar dakin sauya tufafi na ‘yan City lokacin sa-in-sa tsakaninsa da golan bakin Ederson, dan Brazil, game da korafin da kociyan yake yi kan wuce makadi da rawa da yake ganin sun yi a lokacin murnar.

Kociyan dan Portugal daga baya ya bayyana wannan abu da ‘yan City suka yi da cewa matsala ce ta bambancin dabi’a da kuma bambancin ilimi.

Gwamnoni sun amince a kashe dala biliyan daya don yaki da Boko Haram


Nigeria Boko HaramHakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Gwamnonin Jihohi 36 sun tattauna matsalar tsaro da karancin Fetur

Gwamnonin jihohin Najeriya sun goyi bayan a kashe kudi dala biliyan daya domin yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari shugaban gwamnonin jihohin kasar 36 ne ya sanar da matakin a taron majalisar zartarwa da aka gudanar, wanda Farfesa Yemi Osibanjo ya jagoranta a fadar shugaban kasa a Abuja.

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya shaidawa manema labarai cewa gwamnonin sun amince gwamnatin Tarayya ta kashe kudi dala biliyan daya domin yakar Boko Haram.

Za a dai kashe kudaden ne daga asusun rarar kudin mai na kasar.

Gwamnonin sun ce sun amince a kashe kudaden ne saboda ci gaban da aka samu a yaki da Boko Haram.

Boko Haram dai na ci gaba da zama barazana a arewa maso gabashin kasar, inda mayakan kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake tare da kashe fararen hula.

Gwamnonin kuma sun tattauna matsalar karancin fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya, inda karamin ministan albarkatun mai ya yi alkawalin cewa za a kawo karshen matsalar nan da sa’o’i 48.

Har yanzu ana fama da dogayen layi a gidajen mai a manyan biranen Najeriya, kasar da ta fi arzikin mai a nahiyar Afirka.

Sojin Nigeria sun fatattaki 'yan Boko Haram a Minok


Boko HaramHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Boko Haram na ci gaba da zama barazana a Najeriya

An kashe ‘yan Boko Haram 14 a wata musayar wuta da suka yi da sojojin Najeriya, a yayin da mayakan suka yi kokarin kwace wani sansani a jihar Borno.

Kamfanin dillacin labaran AFP ya ce mayakan na Boko Haram sun abka sansanin sojin cikin manyan motoci takwas a ranar laraba, amma sojoji sun yi nasarar fatattakarsu a sansaninsu da ke kauyen Mainok a jihar Borno.

Musayar wutar ta tilastawa matafiya tsakanin Maiduguri zuwa Damaturu fakewa a kauyen Jakana na tsawon lokaci.

Amma rahotanni sun ce an sace wasu motocin yaki na sojin Najeriya bayan arangamar da suka yi mayakan na Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya da ke fada Boko Haram a Borno ta tabbatar da harin tare da cewa dakarunta sun murkushe maharan.

A watan Satumban 2013 mayakan Boko Haram sun taba rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a daidai Benisheik da ke kusa da Minok inda suka kashe mutane 167.

Mafi yawanci dai mayakan Boko Haram na kai hare-hare ne da motocin sojin Najeriya da suka sace.

Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk da ana ikirarin an karya lagonsu.

Eric Bailly ya ji rauni sosai – mourinho


Eric BaillyHakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Eric Bailly ne dan wasa na farko da Jose Mourinho ya saya lokacin da ya koma Manchester United

Kila a yi wa dan wasan baya na Manchester United Eric Bailly aiki a kafarsa sakamakon tsananin raunin da ya ji in ji kociyansu Jose Mourinho.

Dan wasan mai shekara 23 wanda Mourinho ya ce ya ji rauni a idon sawu lokacin da ya je buga wa kasarsa Ivory Coast wasa, bai taka wa United leda ba tun lokacin da Chelsea ta ci su a gidanta a ranar biyar ga watan Nuwamba.

Ba dai a jin jinyar za ta kai shi ga rasa sauran wasannin da kungiyar za ta yi a kakar nan.

Mourinho ya ce a yanzu suna jarraba wasu hanyoyi na maganin raunin kamar yadda aka saba amma idan ya ci tura to dole sai an yi masa aiki.

A rashin dan wasan yanzu kociyan ya ce yana amfani da Chris Smalling da Phil Jones kamar yadda ya sa su a wasan jiya Laraba da suka ci Bournemouth 1-0, kuma ya ce yana jin dadin hadin.

Bailly shi ne dan wasan farko da United ta sayo daga Villareal a bazarar 2016 a kan fam miliyan 30, bayan da Mourinho ya zama kociyanta.

Wales ta fasa ladabtar da shugaban hukumar kwallonta da ya yi bambarma


Jonathan FordHakkin mallakar hoto
OTHERS

Image caption

Jonathan Ford ya bayar da hakuri ne kan bambarmar da ya yi cewa ba za su dauki dan Ingila kociya ba

Hukumar kwallon kafa ta Wales ta fasa daukar matakin ladabtarwa a kan shugabanta Jonathan Ford a game da furucin da ya yi a kwanakin nan cewa kocin tawagar yankin na gaba zai iya kasancewa dan kasar waje amma dai ba dan Ingila ba.

Hukumar ta kafa kwamitin mutane uku ne da zai yi bincike a kan wata hira da BBC ta yi da shugaban, wadda a ciki ya yi wannan kalami, har ma yake cewa a ko da yaushe kusan suna bayar da fifiko a kan ‘yan Wales saboda su suna nuna sha’awa a kan aikin.

A yanzu dai an kawo karshen wannan magana, bayan da Jonathan Ford din ya bayar da hakuri kan maganar da ya yi wadda ake gani wata bambarma ce.

A da an shirya kwamitin ladabtarwar zai gana domin ya titsiye Ford a kan maganar, ko da yake zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba yayin da Wales din ke kokarin maye gurbin Chris Coleman, wanda ya bar aiki saboda kasa sama wa tawagar yankin gurbin gasar kofin duniya ta 2018, da za a yi a Rasha.

Mataimakin Coleman Osian Roberts da tsohon dan wasan Wales na gaba Craig Bellamy da John Hartson da kuma Ryan Giggs dukkaninsu sun nuna sha’awarsu ta samun aikin kociyan.

Kuma tun da dadewa hukumar kwallon ta Wales tana sha’awar ba wa tsohon dan wasansu na gaba da kuma Manchester United.

Sannan shi ma Tony Pulis, dan Wales din wanda a watan da ya wuce aka kore shi daga aikin kociyan West Bromwich Albion na daga cikin wadanda ake duba yuwuwar ba su aikin na horar da tawagar kwallon ta Wales.

Da gaske Facebook na raba kan jama'a?


Chamath Palihapitiya ya yi aiki a Facebook lokacin da kamfanin ke bunkasa sosaiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chamath Palihapitiya ya yi aiki a Facebook lokacin da kamfanin ke bunkasa sosai

Facebook ta mayar da martani ga wani tsohon ma’aikacinta wanda ya ce shafin sada zumuntar da makamantansa na raba kan jama’a.

Chamath Palihapitiya ya yi bayanin ne a watan jiya amma a ranar Litinin ne aka yada labarin a shafukan intanet.

Facebook ya fitar da wata sanarwa domin kare kansa.

Wani mai magana da bakin kamfanin ya ce Mr Palihapitiya bai wuce shekara shida ba ya na aiki da Facebook.

“Lokacin da Chamath ya ke aiki a Facebook, mun mayar da hankali wajen kirkiro sabbin hanyoyin inganta shafukan sada zumunta da kuma bunkasa Facebook a fadin duniya. Facebook ya bambamta da sauran kamfanoni a lokacin kuma da muka kara bunkasa sai muka gane cewa nauyin da ke kanmu shi maya karu.”

Mr Palihapitiya, wanda a da shi ne mataimakin shugaban Facebook ne na fannin bunkasa masu amfani da shafin, yanzu wani fitaccen dan kasuwa ne.

Shi ne sabon jami’in wata kungiya wacce ta ke nuna damuwarta game da illar al’adar tambarin “Like”- wani yanayi mai nuna cewa jama’a da dama sun dogara ga shafukan sada zumunta wajen samun nutsuwa da farin ciki.

“Mun kirkiro abubuwan da ke wargaza ginshikin yadda zamantakewa ta ke,” in ji Mr Palihapitiya.

Ba shi kadai ke da wannan ra’ayi ba. Sean Parker, Shugaban Facebook na farko kuma wanda ya tsara da yawa daga cikin shirye-shiryen kasuwancin kamfanin, ya nuna nadamarsa dangane da rawar da ya taka a tarihin Facebook.

“Allah kadai ya san abunda Facebook ke yi wa kwakwalwar yaranmu,” ya gaya wa Mike Allen daga shafin labarai na Axios.

“Mu na daukar aikinmu da muhimmanci kuma mu na iya kokarinmu wajen ganin mun ci gaba,” sanarwar ta Facebook ta ci gaba da cewa.

“Mun yi aiki gami da bincike mai yawa tare da wasu masana daga waje da kuma malamai domin fahimtar irin tasirin da ayyukanmu ke yi a kan lafiya, sannan mu na amfani da shi wajen ci gaban kamfaninmu.”

“Kuma mu na samun masu zuba hannun jari da kuma kimiyya- kamar yadda Mark Zuckerber ya ce a taronmu na karshe, mu na fatan mu rage ribarmu domin ganin mun zuba hannun jari a inda ya kamata.”

Duk da wadannan manyan jami’an kamfanonin sun bayyana ra’ayoyinsu, fannin kasuwancin kamfanin Facebook din ya jajirce wajen isar da nufin kamfanin.

A makon jiya ne su ka fitar da sabon shafinsu na yara, wanda shi ne shafinsu na farko domin yara ‘yan kasa da shekara 13.

Kalli yadda aka gurfanar da Maryam Sanda da 'yan uwanta


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda aka gurfanar da Maryam Sanda da ‘yan uwanta

A wannan karon dai an gyara tuhumar da ake yi wa Maryam Sandan inda aka tuhume ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru, ta hanyar daba masa wuka da sauran makamai masu hatsari.

Sai dai Maryam ta musanta tuhumar.

Har ila yau an tuhumi mahafiyarta, Maimuna Aliyu da ‘yan uwanta Aliyu Sanda da Sadiya Aminu da laifin goge hujjar kisan kai domin kubutar da Maryam Sanda daga fuskantar da shari’a kan laifin kisan kai.

‘Yan uwan Maryam din dai sun musanta tuhumar da aka yi masu.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kotu ta ba da umarnin tsare Maryam a gidan yarin Suleja

Da aka fara gurfanar da Maryam dai, lauyan rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, James Idachaba, ya nemi kotun ta ba shi lokacin domin ya gyara tuhumar da ake yi wa wadda ake zargin bisa sabbin bayanai da rundunar ‘yan sandan birnin ta samu.

Yayin zaman kotun na ranar 7 ga watan Disamba domin jin sabuwar tuhumar, sai lauya James ya ce bai samu ya bai wa sauran wadanda ake tuhuma da aikata laifi kan lamarin sammaci ba.

Image caption

‘yar Uwar Maryam Sanda, Sadiya Aminu tare da Maryam Sanda a kotu

Saboda haka sai kotun ta ba shi mako daya domin ya gabatar da sauran wadanda ake zargi da aikata laifi a lamarin.

Dan kunar bakin wake ya kashe 'yan sanda suna fareti


A kalla jami'an 'yan sanda 13 ne suka mutu a lokacin harin

Image caption

A kalla jami’an ‘yan sanda 13 ne suka mutu a lokacin harin

Wani dan kunar bakin wake ya kashe a kalla jami’an ‘yan sanda 13 a lokacin da suke fareti a cibiyar horar da ‘yan sanda da ke Mogadishu, babban birnin Somaliya.

An kuma samu rahoton akalla wasu mutum 15 ne suka jikkata.

Dan kunar bakin waken ya yi shigar burtu ne a matsayin dan sanda, inda ya tayar da bam din a kwalejin horor da ‘yan sanda ta General Kaahiye.

Kungiyar al-Shabab ta ce ita ce da alhakin kai harin. Kungiyar dai ta sha kai harin bama-bamai a birnin Mogadishu da kuma sauran biranan kasar.

Wani ganau ya ce jami’an ‘yan sandan na cikin yin fareti da safe lokacin da dan kunar bakin waken ya tayar da bam din.

“Wasu daga cikin ‘yan sandan sun jeru a layi, wasu kuma sun taru, a lokacin da dan kunar bakin waken da ya yi shigar ‘yan sanda ya tayar da bam din,” in ji Hussein Ali.

Mai magana da yawun kungiyar ta al-Shabab Abdiasis Abu Musab ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa yana kusa da gurin da aka kai harin.

A watan Oktoba ma, mayakan al-Shabab sun kai hari wani otel a babban birnin kasar inda suka kashe kimanin mutum 20.

Ko da yake kungiyar ta musanta wani harin bam da aka kai na babbar mota a birnin kasar a farkon watan Oktoba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 358.

Dakarun kungiyar tsaron Afirka kimanin 22,000 ne a kasar ke kokarin taimaka wa gwamnatin don kwato babban birnin kasar daga hannun mayakan.

Nigeria: An kori 'yan sanda masu fataucin wiwi


Ibrahim IdrisHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan sanda sun ce ba za su bari ana bata musu suna ba

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi da ke Najeriya ta ce ta kori jami’anta uku da take zargi da laifin fatauncin wiwi.

Kakakin rundunar ASP William Aya ya tabbatar wa BBC cewa jami’an hukumar hana sha da fataucin kwayoyi, NDLEA ne suka kama ‘yan sandan a watan Nuwamba lokacin da suke yin rakiya ga wata mota dauke da buhu 30 na wiwi a Lokoja, babban birnin jihar.

Ya kara da cewa hukumar NDLEA ce za ta gurfanar da su a gaban kotu.

A cewar ASP Aya, rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci duk wani jami’inta da zai bata mata suna ba.

Ana zargin ‘yan sandan kasar da yin kaurin suna wajen aikata laifukan da suka kamata su hana aikatawa, ko da yake sun sha musanta zargin.

Ministan Farin Ciki ya 'kashe' wata mata a India


Lal Singh AryaHakkin mallakar hoto
Twitter/ @LalSinghArya

Image caption

Ana zargin Lal Singh Arya, ministan Farin Ciki na India, da laifin kisa a shekarar 2009

‘Yan sanda a jihar Madhya Pradesh da ke Indiya na neman ministan ma’aikatar sanya farin ciki ruwa a jallo saboda zargin yin kisa.

‘Yan sandan sun ce suna farautar Lal Singh Arya, mai shekara 53, wanda ba a gani ba tun ranar Talata bayan kotu ta bayar da umarnin tsare shi.

Ana zarginsa da kashe wata ‘yar siyasa a shekarar 2009 ko da yake a baya ya sha musanta zargi.

Madhya Pradesh ita ce jihar da kawai take da ministan farin ciki da zummar kula da walwalar jama’a.

Gwamnatin da jam’iyyar Bharatiya Janatake jagoranta ce ta kirkiro da ma’aikatar a shekarar 2016 sannan ta dora mata alhakin “tabbatar da farin ciki da walwalar ‘yan kasar”.

Madhya Pradesh, ita ce jiha ta biyu mafi girma a Indiya, inda take da kimanin mutum miliyan 70.

Hakkin mallakar hoto
Prakash Hatvalne

Image caption

Ma’aikatar ta bayar da takardar shaida ga mutanen da suka taba shiga shirye-shiryenta

Mr Arya, wanda shi ne mutumin da ke shugabancin ma’aikatar tun da aka bude ta, yana kuma jagorantar ma’aikatu biyu, ciki har da na safarar jiragen sama da gudanarwa da walwalar kabilu.

Ana sa ran zai gurfana a gaban kotu ranar 19 ga watan Disamba.

“‘Yan sanda suna nemansa. Muna da kwarin gwiwar cewa za mu kama shi,” in ji wani dan sanda a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Za a fara shari'ar magajin Dakar kan almundahana


Ana zargin Khalifa Sall da almundahana da kuma wadaka da kudaden gwamnatiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana zargin Khalifa Sall da almundahana da kuma wadaka da kudaden gwamnati

Idan an jima a yau ne za a fara shari’ar magajin garin Dakar Khalifa Sall, na kasar Senegal.

Tun a ranar bakwai ga watan Maris din daya gabata ne ake tsare da magajin garin Dakar din, lokacin da alkalin da ke gudanar da bincike kan dala biliyan uku da suka yi batan dabo inda aka tuhume shi da almundahana da hada baki da kuma aikata laifin hallata kudin haram.

Sai dai ya musanta zargin da ake yi masa.

An dai kama shi ne tare da wasu mukarabansa su bakwai.

Lauyoyinsa sun dinga kokarin ganin cewa an bada belinsu, amma hakarsu bata cimma ruwa ba saboda alkalin ya ki ya amincewa da bukatar da suka shigar a gaban kotu.

Magajin jarin wanda dan jamiyyar Socalisat ne, ya gudanar da yakin neman zabensa a gidan yari a zaben majalisar dokokin da aka yi watan Yulin da ya gabata

Sai dai a watan Nuwamban daya gabata ne ya zama mamba a majalisar dokokin amma kuma gwamatin Senegal ta cire masa rigar kariyar da yake da ita a matsayinsa na mamba a majalisar dokoki.

Mr Sall, wanda shi ne magajin garin Dakar tun daga shekarar 2009, an rika masa kallon wanda zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za’a yi a shekarar 2019.

Sai dai magoya bayansa sun ce zargin da ake yi masa kan almundahana ba komai bane illa wani shirin da aka shirya domin ya kawo cikas ga anniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

Idan kotu ta same shi da laifi, to watakila a yanke masa da kuma mukaranbansa hukuncin daurin shekara goma a gidan kaso.

MSF: An kashe musulmi dubu 6 a Myanmar


Wannan shi ne karon farko ake samun rahoton da ya bada cikakken bayani kan yawan musulmii yan Rohingya da aka kashe a MyanmarHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan shi ne karon farko ake samun rahoton da ya bada cikakken bayani kan yawan musulmii yan Rohingya da aka kashe a Myanmar

Kungiyoyin kare hakkin bil’dama da ‘yan jarida da kuma jami’an MDD sun riga sun tattara bayyanai daga ‘yan gudun hijira da suke samun mafaka a kasar Bangladesh akan cin zarafi mai tayar da hankali, da suke zargin jami’an tsaron Myanmar sun yi a jihar Rakhine.

Sai dai wannan shi ne karon farko da ake samun binciken da ya samar da cikakken bayyani kan yawan musulmi ‘yan Rohingya da aka kashe a tashin hankalin da ya barke sakamakon jerin hare haren da mayakan sa kai yan Rohinja suka kai a watan Augustan daya gabata

Lamarin ya sa sojoji suka kai mummunan farmakin da MDD ta bayyana a matsayin kawarda wata kabila daga doron kasa.

Kungiyar agaji ta likitoci ta Medicine san frontiers ta gudanar da bincike guda shida a watan daya gabata a sansanonin ‘yan gudun hijira , inda ta yi magana da mutane dubu biyu da dari biyar .

Ta gano cewa mace macen da aka yi musaman tsakanin yara a mafi yawan lokuta ya zarta yadda ake tunani kuma kashi sabain cikin dari na mace macen sun faru ne a tashin hankalin, da ya faru.

MSF ta kuma ce akasarin su sun rasa rayukansu ne daga raunukan da suka ji daga harbin bindiga, adadin da ya zarta kiyasin da aka fitar tun farko.

Sai dai wannan rahoton zai karfafa kiraye kirayen da wasu suke yi akan cewa ya kamata a binciki hukumomin Myanmar game da zargin cin zarfin bil’adama.

Rundunar sojin Myanmar din dai ta riga ta gudunar da bincike kan zargin da ake yi ma sojojin kasar kuma ta ce sojojinta basu aikata laifi ba.

Har yanzu masu bincike daga MDD da kuma kungiyoyi agaji basu sami damar zuwa jihar Rakhine ba.

Afrika ta tsakiya: Kasar da Malamai suka gudu


Image caption

Apollinaire Zaoro wani magidanci kuma manomi da ya rungumi aikin koyarwa

Iyaye sun koma koyar da ‘ya’yansu a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya bayan malamai sun kauracewa makarantu saboda rikicin da ake yi a kasar.

Tun a 2013 ake rikici mai nasaba da addini da kabilanci a Afrika ta tsakiya, matakin da ya sa malamai kauracewa makarantu.

Apollinaire Zaoro, manomi ne kuma magidanci, yanzu ya sadaukar da lokacinsa domin koyar da dalibai a kauyensa da babu malamai.

Mista Zaoro ya shafe watanni uku yana bada darasi a aji mai kunshe da yara dalibai 105 a wata Makarantar da ke kauyensu kusa da Bangui babban birnin Afrika ta tsakiya.

Bangaren Ilimi ya fuskanci koma-baya shekaru da dama a Afrika ta tsakiya sannan abubuwa sun kara tabarbarewa a shekaru hudu da aka kwashe ana yaki.

Matsalolin dai sun shafi kusan dukkanin bangarorin ci gaban al’umma musamman asibitocin kananan hukumomi da wuraren shan magani.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce kusan rabin alummar kasar na dogaro ne da tallafin da kasar ke samu.

Fadan da ake gwabzawa tsakanin mayaka masu dauke da makamai ya shafi kusan kashi 80 na yankunan kasar.

Mayakan na amfani da makarantu a matsayin sansanonin yaki, inda suka mayar da tebur da kujerun dalibai a matsayin itacen abinci.

Yawancin kwararrun Malaman sun kauracewa makarantu ne saboda rashin albashi sakamakon bankuna da babu a wajen Bangui.

Barci tare da Maciji

A tsawon shekaru uku har zuwa 2016, rikicin Mayakan Seleka ya tursasawa Mista Zaoro da wasu daruruwan mazauna Yamboro kauracewa gidajensu.

Image caption

Makarantu na bukatar gyra a Afrika ta tsakiya

“Muna tserewa mu shiga jeji mu buya a itace, tare da macizzai. Abincin da zamu ci ma yana gagararmu. Ko da yake mun samu sauki a lokacin da abokan adawarsu Anti-Balaka suka fatattake su. Amma har yanzu muna cike da fargaba,”

Mista Zaoro ya ce yana jin dadin aikin koyarwar, inda yake iya kokarinsa wajen koyar da yara ilimin kidaya daga 1 zuwa 100.

Yana amfani da dabarar rubuta lambobi a babbar takarda wacce ya manna a bango. Sannan zai kira lamba ya bukaci daya daga cikin daliban ya nuna a bango.

Yaran na rige-rigen nuna lambar, wanda hakan ya nuna cewa suna gane karatun da Mista Zaoro ke koyarwa.

Darasin koyon harshen Faransanci ya fi kayatarwa, inda Mista Zaoro ya kira yara biyu a gaban allo, ya umurci su yi wasan damben boxing.

Image caption

Apollinaire Zaoro ya yi watsi da aikinsa na noma domin koyarwa

A 2013 ne yaki ya barke a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya bayan da mayakan Seleka musulmi suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize kirista.

Dakarun Faransa ne kuma suka kifar da gwamnatin Seleka, matakain da ya haifar da rikici tsakaninsu da Anti-Balaka.

Yanzu dakarun Majalisar Dinkin Duniya Minusca, ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui, fadar gwamnatin shugaban kasar na yanzu da aka zaba Faustin-Archange Touadera.

Image caption

Dakarun Minusca ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui

Mayakan Seleka da Anti-Balaka ke rike da sauran sassan kasar, inda suke ci gaba da fada da juna domin karbe ikon hanyoyi da albarkatun kasa musamman zinari da lu’u’lu’u.

Yara Manyan gobe

Mista Zaoro na daga cikin iyaye 500 da suke koyarwa wadanda suka samu horo daga wata kungiyar agaji ta kasar Finland.

Yanzu haka akwai iyaye kimanin 8,000, da aka dauka domin ba su horo na musamman kan ilimin koyar da ‘ya’yansu a makarantu.

Mista Zaoro wanda manomi ne ya ce yana alfahari da aikin ilmantar da yara wadanda sune manyan gobe a Afrika ta tsakiya. A cewarsa yana fatar ganin yaran sun samu ci gaba a rayuwa kamarsa.

Image caption

Yaran da suka samu damar karatu

Zaoro da wasu sauran iyayen da ke aikin koyarwa na samun tallafin kudi dala 65 a wata daga hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ilimin yara kanana.

Amma ya ce ba suna yi ba ne saboda kudi.

“Tun da babu bankuna kuma hanyoyi ba tsaro, mun bukaci a biya mu bayan wata uku a Bangui. kuma a karshen watan Disemba ne zan fara karbar albashi” a cewar Mista Zaoro.

Rungumar aikin koyarwa da iyaye suka yi ya taimaka yara sun koma makaranta, duk da cewa tsarin bai kai nasabar tsarin ilimin kasa ba.

Yaran kauyen Yamboro ne dai ke amfana da tallafin.

A Sangala 1, wani kauye da ke nisan kilomita 70km da Bangui, duk Yanar gizo ta lullube ajujuwan, sannan da alamun albarussai da suka fasa rufin ginin makarantun.

Yara sun kauracewa makarantu saboda babu malamai, a cewar Hakimin garin Mongombe.

Hukumar UNICEF dai ta ce ba za ta iya kiyasta adadin yaran da ba su zuwa makaranta ba saboda rashin malamai.

Rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mayakan Anti-Balaka sun rungumi makamai bayan mayakan Seleka sun kifar da gwamnatin Bozize a 2013.

 • A 2013, Mayakan Seleka Musulmi suka kwace ikon gwamnati
 • Mayakan Anti-Balaka sun rungumi makamai domin yakar Seleka
 • Sama da mutane miliyan daya rikicin ya raba da gidajensu, sannan daruruwa ne aka kashe
 • Kimanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya 13,000 ke aikin wanzar da zaman lafiya da ake kira Minusca.

Bankin Duniya zai daina bayar da rancen hakar mai


Bankin Duniya zai daina bayar da rance domin aikin hakar man fetur da iskar gasHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bankin Duniya zai daina bayar da rance domin aikin hakar man fetur da iskar gas

A wannan makon ne Babban bankin duniya, ya sanar da cewa zai daina samar da kudi rance don aikin hakar man fetur da iskar gas.

Babban bankin, ya sanar da hakan ne a wajen taron da ake yi kan sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa.

To sai dai kuma masana sun bayyana cewa zai yi wuya matakin da Babban bankin duniyar ya ce zai dauka ya yi wani muhimmin tasiri nan take.

Dr Ahmad Adamu, malami ne a Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua dake Katsina, kuma masani a kan tattalin arzikin man fetur ya shaida wa BBC cewa, wannan mataki na bankin duniyar hannun ka mai sanda ne, domin ana so ne a dakile amfani da danyen mai da iskar gas.

Masanin ya ce, yawancin kasashen da suka ci gaba a duniya baki daya basu da albarkatun man fetur da iskar gas sai kasashe masu tasowa kamar Najeriya ne ke da albarkatun danyen man.

Dr Ahmad Adamu, ya ce baya ga dakile amfani da danyen man da iskar gasa, ana kuma ganin cewa danyen man fetur din da iskar gas na gurba muhalli wanda shi ke kawo dumamar yanayi.

Masanin ya ce, idan har akwai bukatar danyen man fetur da iskar gas, to duk wani yunkuri na dakile hako shi zai matukar wuya.

Dr Adamu, ya ce ” Mafi yawancin hako man da ake yi kamfanoni ne na kasashen waje da kuma ‘yan kasashen da ake hako man wadanda ke da hali ne ke bayar da kudin hakowa, sannan kuma bayan babban bankin na duniya da ke bayar da rancen kudin, akwai sauran bankuna da suke bayar da rancen kudi a hako man fetur din da iskar gas”.

Don haka dan babban bankin shi kadai ya ce ya daina bayar da rancen kudi, to sauran kamfanoni wannan mataki ba zai yi tasiri a kan su ba inji masanin.

Arsenal da Liverpool sun yi kasa, Tottenham da Everton sun yi sama


Wayne Rooney ya ci NewcastleHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wayne Rooney ya ci kwallo ta tara ke nan a kakar nan

A sauran wasannin da aka yi guda shida na Premier, Wayne Rooney ya ci wa Everton bal din da ta ba ta nasarar farko a Premier, a waje tun watan Janairu a karawar da ta doke Swansea 1-0.

Yanzu Everton tana daidai da ta tara a tebur Watford da maki 22, Newcastle kuma ta zama ta 16 da maki 15.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Lokacin da Arsenal ta kasa zura kwallo a Premier tun wasanta da Chelsea ranar 17 ga watan Satumba

Leicester kuwa ta lika wa Southampton mai masaukinta 4-1, nasarar da ta sa yanzu ta zama ta takwas da maki 26, yayin sa Southampton take ta 11 da maki 18.

Liverpool ta ci gaba da zama a wajen hudun farko bayan da a gidanta ta kasa cin West Brom, suka ta shi canjaras 0-0, lamarin da ya sa Liverpool din take ta biyar da maki 31, ita kuwa West Brom ta zama ta 17 da maki 14.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Roberto Firmino da sauran ‘yan wasan gaba na Liverpool sun kasa ratsa bayan West Brom

Kociyan Mancester United Jose Mourinho ya ce zai tafi hutu a Brazil ko birnin Los Angeles na Amurka, idan har ya ga ba su da sauran dama ta fafutukar daukar kofin Premier a bana, bayan da kungiyarsa ta ci Bournemouth 1-0, wadda Lukaku ya lika ta.

United ta ci gaba da bin City a matsayi na biyu da tsiran maki 11, ita kuwa Bournemouth tana mataki na 14 da maki 16.

Tottenham kuwa ta sake komawa cikin hudun farko sakamakon kwallo biyu da Serge Aurier da Son Heun-min suka ci mata, a karawarsu da Brighton.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tottenham ta kankane wasan, ko da yake ta fuskanci matsala daga bakin kafin Aurier ya daga raga

Yanu ta dare matsayi na hudu da maki 31, yayin da Brighton ke matsayi na 13 da maki 17.

Sai kuma Arsenal wadda wasa uku kenan ta yi na Premier ba tare da ta ci ko daya ba, lamarin da ya sa ta koma kasa ta bakwai da maki 30, bayan da ta kasa daga ragar ta 19 a tebur West ham wadda ke gida mai maki 14.

Manchester City ta kara zama daram bayan doke Swansea 4-0


David Silva lokacin da ya ci SwanseaHakkin mallakar hoto
PA

Image caption

David Silva ya ci wa Manchester City kwallo a wasa uku a jere

Jagorar Premier Manchester City ta ci gaba da bajintarta ta cin manyan wasanninta a jere zuwa 15, inda ta caskara ta karshe a tebur Swansea da ci 4-0.

David Silva ne ya fara daga ragar masu masaukin a minti na 27 da shiga fili kafin kuma Kevin de Bruyne ya ci ta biyu a minti na 34.

Daga nan kuma sai bayan hutun rabin lokaci aka ci gaba da daga ragar ta Swansea inda Silvan ya jefa ta uku, wadda ita ce ta biyunsa a minti na 52, sai kuma Aguero ya kammala da ta hudu a minti na 85.

Da wannan nasara Manchester City ta kara tabbatar da ratar maki goma sha daya da ke tsakaninta da abokiyar hammaya Manchester United ta biyu a tebur.

Ita kuwa Swansea rashin nasara na shida a gida a wasa tara na gasar ta Premier a bana ya kara tabbatar da su a kasan tebur da maki biyu tsakaninsu da tsira daga faduwa a gasar.

Zakarun Afirka: Plateau United da MFM na Najeriya za su yi fama


Wydad Casablanca ta Morocco lokacin da ta doke Al Ahly ta Masar ta ci kofin zakarun Afirka na 2017Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wydad Casablanca ta Morocco lokacin da ta doke Al Ahly ta Masar ta ci kofin zakarun Afirka na 2017

An fitar da jadawalin gasar cin kofin zakarun Afirka a birnin Alkahira a ranar Larabar nan, inda masu rike da kofi Wydad Casablanca na Morocco za su fara kare kofin da Stade Malien ta Mali ko Williamsville AC ta Ivory Coast.

Wydad na daya daga cikin kungiyoyi biyar da za a ba wa damar shiga zagaye na biyu na gasar kai tsaye, wadda za a fara a watan Maris na shekara ta 2018 mai kamawa.

Su kuwa kungiyoyin Najeriya biyu da suke cikin gasar, Plateau United da Moutain of Fire and Miracles dole ne su tsallake wasu shingaye masu wuya kafin su kai matakin wasan rukuni na gasar.

A jadawalin gasar na wasan share fage da kuma na zagaye na farko da aka fitar an hada kungiyoyin biyu da abokan karawa masu karfi fiye da yadda za su so.

A wasan sharar fage an hada Plateau United da wata sabuwar zuwa gasar ita ma Eding Sport ta Kamaru, inda za su yi wasansu karo biyu a karshen mako biyu a jere a watan Fabrairu.

Idan United din ta yi nasara za ta hadu da Etoile Sahel ta Tunisia a watan Maris, wadda tana daya daga cikin kungiyoyi 10 a gasar ta 2018, da suka taba cin kofin na zakarun Afirka.

Etoile ta bayar da mamaki lokacin da ta yi galaba kan wadda ake ganin za ta dauki kofin shekara ta 2007 Al Ahly ta Masar, inda ta doke su a wasansu na biyu a Alkahira 3-1, bayan canjaras ba ci da suka yi a wasan farko.

Ba kamar Plateau United ba kungiyar ta Tunisia suna da kwarewa sosai a gasar ta Afirka, domin su kadai ne zakarun gasar hukumar kwallon kafa ta Afirka biyar na da da kuma na yanzu.

Sannan sun kai wasan kusa da karshe na gasar ta zakarun Turai a wannan shekarar, kafin su bayar da kai a wasansu na biyu a gidan Ahly, wadda ta casa su da ci 6-1 a birnin Askandariya.

Etoile na daga tsoffin zakarun gasar gfuda biyar da aka ba wa damar wucewa zuwa zagayen kungiyoyi 32 na gasar kuma da kyar idan ba su fitar da Plateau ko Eding ba.

Ita kuwa kungiyar Mountain of Fiore and Miracles, sunanta ya fi daukar hankali daga cikin na kungiyoyi 59 daga cikin gasar, za ta hadu da Real Bamako ta Mali.

Idan kungiyar ta coci ta Najeriya ta yi nasara to kila za ta hadu da zakarun gasar ta 1976 Mouloudia Alger na Algeria, wadda ta kai wasan dab da na kusa da karshe na kofin Confedreation na Afirka a kakar nan.

Ahly wadda ta kafa tarihin daukar kofin sau takwas, ba za ta gamu da matsala kila daga Kadiogo ta Burkina Faso ko Mounana Gabon.

Zakarun gasar sau biyar TP Mazembe na Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo bayan da suka kasa zuwa matakin rukuni na gasar sau biyu a baya kila su yi awon gaba da Ngaya ta Comoros ko kuma Songo ta Mozambique.

Kofin Duniya: Real Madrid ta doke Al Jazira 2-1


Cristiano Ronaldo a lokacin da yake rama wa Real MadridHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Cristiano Ronaldo ne ya farke kwallon da aka fara cin Real Madrid

Zakarun Duniya Real Madrid za su yi wasan karshe da kungiyar Gremio ta Brazil a gasar kofin duniya na kungiyoyi bayan da ta doke Al Jazira 2-1 a ranar Larabar nan.

A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta kara da kungiyar ta Brazil wadda ita ma a Larabar ta fitar da Pachuca ta Mexico a daya wasan na kusa da karshe.

Real Madrid aka fara ci a wasan da ake yi a Abu Dhabi, bayan da dan wasan kungiyar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, da Silva ya ci daga musu raga a minti na 41.

Cristiano Ronaldo ne ya rama cin bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 53, kafin kuma Gareth Bale ya kara ta biyu a minti na 81.

Real Madrid za ta kafa tarihin daukar kofin na duniya a jere, wanda zai zamar mata na uku, kuma kofi na biyar da ta dauka kafin a wannan shekara mai karewa ta 2017.

Zakarun na duniya sun dauki kofin a shekara ta 2014 da kuma 2016.

Abokiyar hamayyarta ta La Liga Barcelona ita ce ta taba cin kofin na duniya sau uku tun lokacin da aka kirkiro da gasar a shekara ta 2000.

Damben Boksin: Kila a dawo wa da Tyson Fury lasisinsa na dambe


Tyson FuryHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rabon da Tyson Fury ya yi dambe tun lokacin da ya yi nasara a kan Wladimir Klitschko a watan Nuwamba na 2015

Hukumar kula da harkokin damben boksin ta Birtaniya za ta waiwayi batun dakatar da lasisin damben Tyson Fury dan kasar ta Birtaniya a watan Janairu.

Hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta Birtaniya ce ta haramta wa Tyson mai shekara 29 dambe saboda samunsa da laifin amfani da wata kwayar da ta hana amfani da ita a shekara ta 2015.

An matsar da wa’adin hukuncin baya, wanda hakan ke nufin tsohon dan damben na ajin babban nauyi yana da damar sake yin damben.

Ita kuwa hukumar kula da harkokin damben boksin ta Birtaniya ta soke lasisinsa ne a watan Oktoba saboda matsalar rashin lafiya da ta shafi damuwa.

Haka shi ma dan uwan Tyson Fury din, Hughie Fury, an wanke shi ya sake komawa fagen damben, bayan da aka same shi da laifin amfani da abubuwan kara kuzari a wasa a watan Fabrairu na 2015.

Ba a tuhumi dukkaninsu ba har sai a watan Yuni na 2016, kuma dukkaninsu sun kafe cewa ba da saninsu ko kuma da niyya suka yi amfani da abubuwan kara kuzarin ba.

Shi dai Tyson Fury ya dora alhakin samunsa da alamar amfani da abin kara kuzarin ne a kan cin naman aladen dawa wanda ba a fidiye ba.

A wata sanarwa da shi da dan uwan nasa suka fitar sun ce suna farin ciki an sasanta batun, kuma yanzu za su ci gaba da shiga dambe ba tare da ana kallonsu a matsayin masu zamba ta amfani da abubuwan kara kuzari ba.

An soke damben da suka yi a watan Fabrairu na 2015, ciki har da wanda Tyson Fury ya doke Christian Hammer, amma an bar sakamakon duk boksin din da suka yi bayan wannan lokacin, har da wanda Tyson din ya doke Wladimir Klitschko.

An kama wata mata da laifin sayar da tagwayenta a Katsina


Nigerian police forceHakkin mallakar hoto
Getty Images

An kama wata mata ‘yar Najeriya bisa zargin sayar da tagwayen jariranta ‘yan wata guda.

Lamarin ya faru ne a jihar Katsina da ke arewacin kasar.

Ana tuhumarta ne da laifin safarar yara, amma ‘yan sanda sun ce za a iya kara tuhumarta da wasu laifukan na daban.

Rahotanni sun ce matar ta yi yunkurin sayar da ‘ya’yan nata mata tagwaye a kan naira 350,000 ga wani mutum, wanda shi ne ya gaya wa ‘yan sanda.

Matsalolin sayar da jarirai da safarar yara sun jima a Najeriya.

Matar, ‘yar shekara 30, ba ta yi wani bayani ba da aka gurfanar da ita a gaban kotu a birnin Katsina, amma wani shafin intanet na Gistmania ya bayyana cewa ta ce aikin shaidan ne.

Hukumar hana safarar mutane a Najeriya (NAPTIP) ta bayyana cewa binciken da ta gudanar a shekarar 2011 ya nuna cewa a kan sayar da jarirai a kan $6,400.

A shekarar 2013, ‘yan mata 17 masu juna biyu da jarirai 11 aka kubuto daga wani gida da ake haifar jarirai domin a sayar da su a jihar Imo.

Duk da nuna tsananin rashin jin dadi da jama’a su ka yi da kuma alkawarin gwamnati na cewa za ta dauki manyan matakai domin magance matsalar, iyaye mata a Najeriya sun ci gaba da siyar da ‘ya’yansu.

Shekara biyu bayan an bankado gidan haihuwar jariran a Imo, an kama wata mata yayin da ta ke kokarin siyar da jaririnta a kan dala 90 ko kuma fan 67 a Jihar Cross River a kudu maso gabashin Najeriya.

Za a fara bai wa 'yan gudun hijirar Nigeria katin shaida


NigeriaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Miliyoyan ‘Yan gudun hijira ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR da hukumomin Najeriya sun kaddamar da aikin bai wa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu katin shaidar dan kasa.

Ana gudanar da aikin ne a sansanonin ‘yan gudun hijira a Maiduguri babban birnin jihar Borno yankin arewa maso gabashin Najeriya

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ce mutanen da rikcin na Boko Haram ya raba da gidajensu dubu dari daya ne zasu amfana da shirin bayar da katin shaidar a tashin farko.

Amma kawo yanzu ba a san ko zuwa karshen aikin, jimillar ‘yan gudun hijira nawa ne za a bai wa katin ba.

Hukumar ta UNHCR da kuma hukumar bayar da katin zama dan kasa ta Najeriya ne ke gudanar da aikin a Maiduguri inda aka soma da sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram na fuskantar matsaloli da dama a Najeriya

Hukumomin sun ce wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu da suka kai shekara goma sha shida zuwa sama ne suka cancanci a ba su katin na shaida.

Ana ganin hakan zai taimaka wajen kare su daga cin zarafi kodai daga jama’a ko daga hukumomi, tare da damar samun ilmi da harkokin kiwon lafiya ba tare da shakku ba.

Malam Ibrahin Dangana, jami’i a hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, a Maiduguri, ya shaida wa BBC cewa sun lura rashin wata shaida da ke tabbatar da mutanen ‘yan gudun hijira ne kan jefa su cikin matsala.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce mutane fiye da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da suka kunshi Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

An taya Newcastle fam miliyan 300


Rafael BenitezHakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Kociya Rafael Benitez na fatan samun kyakkyawan labarin sayar da kungiyar bayan wasansu da Everton

Mai kungiyar Newcastle Mike Ashley da ‘yar kasuwar Birtaniyan nan Amanda Staveley sun gana a karon farko domin tattaunawa a kan yadda za a sayar da kungiyar ta gasar Premier.

BBC ta fahimci cewa mutanen biyu sun gana ne a wani gidan cin abinci na Indiyawa a Landan a makon da ya wuce, bayan da kamfanin da matar take tafiyarwa – PCP Capital Partners, ya yi sabon tayi na kusan fam miliyan 300 a kan kungiyar.

Ya zuwa lokacin hada wannan labari kungiyar ta Newcastle ba ta ce komai ba a kai, amma kuma ba ta musanta ganawar mutanen ba.

A watan Oktoba Ashley ya ce yana son sayar da kungiyar bayan da ya mallake ta tsawon shekara goma.

Dan kasuwar da ya tafi Amurka amma yanzu ya dawo Ingila yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

In dai har cinikin ya kaya to sai dole ya samu amincewar hukumar gasar Premier, wanda kuma zai dauki kwana talatin.

‘Yar kasuwa Staveley, ita ce ta shiga tsakani wajen cinikin sayar wa Sheikh Mansour Manchester City a 2009, kuma rahotanni sun ce ita ce ta jagoranci tayin fam miliyan 400 da kamfanin Dubai International Capital ya yi a kan Liverpool a 2008.

Shi dai Ashley, mai shekara 53 ya jawo rabuwar kai a kungiyar Newcastle, inda wasu magoya baya a kai a kai suke nuna rashin amincewarsu da yadda dan kasuwar yake tafiyar da kungiyar.

Attajirin ya sayi Newcastle ne a kan fam miliyan 134.4 a shekara ta 2007.

Sau biyu kungiyar na faduwa daga Premier a tsawon shekara goma da ta yi a hannun attajirin, kuma yanzu tana matsayi na 16 a gasar bayan wasa 16, bayan haurowa da ta sake yi gasar a karkashin kociya Rafael Benitez.

Ba na nadamar bata wa Mourinho rai – Guardiola


Pep Guardiola da Jose MourinhoHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Guardiola ya ce indai ran Mourinho ne ya baci kan murnarsu ta cin Man United to shi ba ya nadama

Pep Guardiola ya ba wa Manchester United hakuri da cewa idan har yadda suka cashe lokacin da suka doke abokan hamayyar tasu ‘yan United din ba su ji dadi ba, amma kuma ya ce ba ya nadama idan ran Mourinho ne ya baci a kan lamarin.

Kociyan dan kasar Spaniya ya ce, indai har yadda suka yi wannan murna da farin ciki ta cin Manchester United 2-1 a Old Trafford sun bata wa kungiyar rai, amma ba wani dan wasa daya ba ko Jose Mourinho, to yana bayar da hakuri a kai.

Sai dai Guardiolan ya jaddada dama da ‘yancin ‘yan wasansa na nuna farin cikinsu a kan nasarar da ta sa suka ba wa abokan hamayyar tasu tazarar maki 11 a teburin Premier.

Ya ce dole ne su yi farin ciki a wannan lokaci, amma idan mutane sun kasa fahimtar hakan to sai dai ya ce wannan su ta shafa, domin wasa ne na hamayya suka yi nasara, nasara kuma ta 14 a jere.

A lokacin bureden da kuma sa-in-sar da aka samu bayan da Mourinho ya nuna damuwa kan abin da ya dauka zakewar ‘yan City din a murnar, an watsa wa kociyan na United madara da ruwa ko da yake ba su bata shi ba, amma sun samu wani jami’inshi.

Mourinho ya yi gugar zana kan abin da ya faru a lokacin da cewa matsala ce ta bambancin dabi’a da kuma bambancin ilimi.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ba wa kungiyoyin biyu wa’adin zuwa Larabar nan su ba ta bahasi kan lamarin.

Wales za ta ladabtar da shugaban hukumar kwallon kafarta


Jonathan FordHakkin mallakar hoto
OTHERS

Image caption

Maganar da Jonathan Ford ya yi cewa ba za su dauki dan Ingila kociya ba, ita ce ta jefa shi cikin matsala

Hukumar kwallon kafa ta Wales ta fara shirin daukar matakin ladabtar da shugabanta Jonathan Ford saboda ya ce kociyan tawagar yankin na gaba zai iya kasance dan kasar waje amma dai ba dan Ingila ba.

Hukumar ta kafa kwamitin mutane uku da zai yi bincike a kan wata hira da BBC ta yi da shugaban, wadda a ciki ya yi wannan kalami, har ma yake cewa a ko da yaushe kusan suna bayar da fifiko a kan ‘yan Wales saboda su suna nuna sha’awa a kan aikin.

A yayin taron majalisar zartarwa ta hukumar kwallon kafar ta Wales ne aka taso da maganar hirar ta BBC da Ford, inda aka neme shi da ya fita daga dakin taron.

Kwamitin ladabtarwar zai gana domin ya titsiye Ford a kan lamarin, ko da yake zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba yayin da Wales din ke kokarin maye gurgin Chris Coleman, wanda ya bar aiki saboda kasa sama wa tawagar yankin gurbin gasar kofin duniya ta 2018, da za a yi a Rasha.

Mataimakin Coleman Osian Roberts da tsohon dan wasan Wales na gaba Craig Bellamy da John Hartson da kuma Ryan Giggs dukkaninsu sun nuna sha’awarsu ta samun aikin kociyan.

Kuma tun da dadewa hukumar kwallon ta Wales tana sha’awar ba wa tsohon dan wasansu na gaba da kuma Manchester United.

Sannan shi ma Tony Pulis, dan Wales din wanda a watan da ya wuce aka kore shi daga aikin kociyan West Bromwich Albion na daga cikin wadanda ake duba yuwuwar ba su aikin na horar da tawagar kwallon ta Wales.

Yadda wani mutum ya mutu bayan ya fado daga bene hawa 62


Wu Yongning uses a selfie stick to photograph himself reclining on top of a structure far above the surrounding buildingsHakkin mallakar hoto
Weibo

Wani fitaccen dan China mai kasadar hawa dogayen gine-gine ya mutu a lokacin da ya rikito daga bene mai hawa 62.

Wu Yongning ya samu dubban mabiya a shafin sada zumunta na Weibo domin kananan bidiyon da ke nuna shi kan saman dogayen gine-gine ba tare da amfani da abubuwan kare kansa ba.

Masu sha’awar bidiyonsa sun damu a cikin watan Nuwamba da suka daina ganin sakonninsa.

Yanzu haka ta bayyana cewa ya mutu bayan ya fado daga wani dogon gini mai hawa 62 a birnin Changsha.

Kafofin watsa labarai na China sun ba da rahoton cewa ya shiga wata gasa ce wadda za ta iya samar masa kyautar makudan kudi.

Dan shekara 26 din ya mutu ne ranar 8 ga watan Nuwamba, amma budurwarsa ce ta tabbatar da mutuwarsa a wani sakon da ta wallafa a shafukan sa da zumuntan China wata daya da mutuwarsa.

Abin da ake ce wa “kasancewa a saman gida” – hawa gine-gine masu tsawo sosai ba tare da kayayyakin kariya ba- yana kara samun karbuwa a duniya cikin ‘yan shekaraunnan.

Sakonnin Mista Wu a shafin sa da zumunta na Weibo sun gargadi masu kallo kada su kwaikwayi irin abubuwan da yake yi. Ya samu horaswa ta fadan hannu, kuma a baya ya shiga shirye-shiryen fina-finai da na talabijin.

Amma hotunansa a saman dogayen gine-gine ne suka fi jan hankalin mutane a shafukan sa da zumunta- kuma rahotanni sun ce sun fi riba.

Hakkin mallakar hoto
Weibo

Image caption

Wu Yongning ya wallafa hotunan bidiyon dukkan hawan da ya yi kan shafin sa da zumuntan China Weibo

An ambaci wani dan uwansa yana cewa ya shiga wata gasa ta hawa saman bene kan kudi yuan 100,000 (daidai da fam 11,300), duk da cewa ba a bayyana nau’in gasar ba.

Jaridar South China Morning Post ta ambato wani dan uwansa yana cewa: “Ya yi shirin neman budurwarsa ta aure shi (washe garin faduwarsa).”

“Ya bukaci kudin ne domin aure, da kuma jinyar mahaifiyarsa da ke fama da rashin lafiya.”

A shafin Weibo, ‘yan uwa da magoya baya suna da ra’ayi mabambanta game da labarin mutuwarsa.

Amurkawa sun nuna wa Trump iyakarsa


AlabamaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Doug Jones ya ci zaben da kashi 49.9%

Doug Jones ya zama dan jam’iyyar Democrat na farko a cikin shekaru 25 da ya ci zaben kujerar majalisar dattawa a jihar Alabama, bayan da ya tsaya takarar neman zaben tare da dan jam’iyyar Republican Roy Moore.

Nasarar Mr Jones ta bayar da mamaki kuma ta jaddada rashin amincewar Amurkawa da akidar Shugaba Donald Trump wanda ya nuna tsananin goyon bayansa ga Mr Moore ko da wasu jiga-jigan jam’iyyarsu ka ki bayar da na su goyon bayan.

Har yanzu Mr Moore bai mika wuya ba, kuma ya ce akwai sauran rina a kaba.

A lokacin gangamin neman zaben, an yi zargin Mr Moore da cin zarafin wasu ‘yanmata amma ya karyata hakan.

Jihar Alabama za ta samu wakilcin Demokrat a majalisar dattawan Amurka, wanda hakan zai iya bai wa ‘yan Demokrat dama wajen mamaye majalisar a zaben rabin zango a shekarar 2018.

Duk da Mr Moore bai mika wuya ba, Shugaba Trump ya yi wa Mr Jones murna a shafinsa na twitter bayan kafofin sadarwar Amurkar sun bayyana shi a matsayin wanda yayi nasarar zaben.

'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban EFCC Ibrahim Magu


Ibrahim MaguHakkin mallakar hoto
Efcc

Image caption

Ibrahim Magu ya bukaci a rika kai masu cin hanci da rashawa dajin Sambisa

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan gonar shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Talata da misalin karfe goma na dare.

Gidan gonar yana yankin karamar hukumar Karshi ne da ke wajen babban birnin tarayya.

Kakikin hukumar EFCC, Wilson Uwajuren da takwaransa na rundunar ‘yan sandan Abuja, Anjuguri Jesse Manza sun ki tabbatar ko musanta aukuwar lamarin, a lokacin da BBC ta tuntube su.

Majoyoyinmu sun shaida mana cewa ‘yan bindigar sun sace shanu da tumaki.

Sun kara da cewa shugaban na EFCC ya gina gidan da zai zauna a harabar gidan gonar, ko da yake bai kai ga tarewa a cikinsa ba har lokacin da aka ba shi shugabancin EFCC.

Wannan lamarin ya faru ne watanni da dama bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin EFCC da ke unguwar Wuse Zone 7 da ke birnin na Abuja.

A wancan harin da aka kai a watan Agusta, ‘yan bindigar sun yi ta harbe-harbe a cikin ofishin kafin su ajiye wata wasika da ke yin gargadin kashe wani babban jami’in bincike na EFCC, Ishaku Sharu.

Ibrahim Magu dai ya sha fama da mutanen da ake zargi da wawure kudaden Najeriya, a yunkurin da yake yi na ganin sun fuskanci hukunci.

Ya taba yin kira da a kafa kurkuku a dajin Sambisa domin a rika tsare wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa a kasar.

'Yan Boko Haram 'yan kwaya ne'


Mutane sun taru a gaban motoccin da suka kone lokacin da bam ya tashi a kasuwar Monday da ke birnin Maiduguri na jihar Borno a shekarar 2014.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Boko Haram ta kai hare hare da dama a Nigeriya

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadi akan yawan kwayar tramadol da ake safarasu a yammacin Afrika, ya yinda wani jami’i ya bayyanna cewa ana ganin kwayar a cikin aljihun wadanda za su kai harin kurnar bakin wake.

Hukumar yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi ta Majalisar dinkin duniya ta ce yawan kwayar da aka kwace tun daga shekarar 2013 ya karu matuka daga kilo 300 zuwa tan fiye da 3 a kowce shekara.

An gano kwayoyi miliyan uku a wasu akwatuna masu tambarin Majalisar dinkin duniya a jamhuriyar Nijer a watan Satumba daya gabata.

Mayakan kungiyar Boko Haram na amfani da kwayar ta tramadol.

Kwayar da ake amfani da ita domin rage zafin ciwo, ana tsamanin cewa ana amfani da ita wajan kwantar da hankali wadanda zasu kai hari. kuma jaridar Gaurdian a baya baya nan ta wallafa rahoton da ya ce mayakan ‘yan ta’ada kan zuba kwayar cikin dabino wanda suke ba yara kafin su turasu su kai hari.

Gidan tsohon shugaban Boko Haram zai zama gidan kayan tarihi

Nigeria: Sojoji sun fatattaki ‘yan Boko Haram daga Magumeri

An ki daukar matasa aikin asibiti saboda shan kwaya a Kano

A watan Augustan daya gabata ne aka kwace kwayar tramadol 600,000 wanda zaa kai ma kungiyar Boko Haram a kan iyakar da ke tsakanin Nigeria da Kamaru.

Wakilin UNODC a yamacin Afrika Pierre Lapaque, ya yi gargadin cewa be kamata a bar yanayin da ake ciki ya cigaba da gudana ba, saboda hakan zai yi kafar ungulu ga tsarin tsaron duniya.

“Ana ganin kwayar tramadol a cikin aljihun mutanen da aka kama, wadanda ake zargin yan ta’ada ne a yankin Sahel ko kuma wadanda suka kai harin kurnar bakin wake”. a cewar Mr Lapaque

” Wannan ya sa alamar tambaya dangane da wadanda suke samar da wadannan kwayoyi ga mayakan Boko Haram da kuma al-Qaeda, ciki har da yara maza da mata wadanda suke shirin kai harin kurnar bakin wake.”

Hukumar ta UNODC ta ce kwayar wadda miyagun kungiyoyi suke safarata daga Asiya da kasashen Larabawa ta koma wata babbar matsala a tsarin kiwon lafiyar yankin Sahel, musaman a arewacin Mali da Niger, inda yawan matasan da ke kasashen da ke kudu da sahara ya sa ma su safarar miyagun kwayoyi na samun kasuwa.

Wata mata a Mali ta fadawa hukumar cewa ta kan ga yara masu shekara 10 suna tafiya bayan an basu kwayar a cikin shayi domin su daina jin yunwa.

Hukumar ta UNODC ta ce mutanen da ke shan kwayar ta haramtaciyyar hanya na shan maganin fiye da kima , abin da ya zarta adadin da likitoci suke bada har sau biyar.

PDP na rarrashin 'ya yanta da suka fusata


Wasu 'ya yan jamiyar sun rika tada jijiyar wuya bayan da aka bayana sakamakon zabenHakkin mallakar hoto
PDP FACEBOOK

Image caption

Wasu ‘ya yan jamiyar sun rika tada jijiyar wuya bayan da aka bayana sakamakon zabenWasu ‘yayan jamiyar sun rika tada jijiyar wuya bayan da aka bayana sakamakon zaben

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta tura wata tawaga wadda zata zagaya sassan Nigeria domin ta bai wa ‘ya yanta da suka yi fushi hakuri dangane da zaben shugabanninta da aka yi ranar Asabar.

Ta dauki wannan matakin ne bayan da wasu ‘ya yanta suka nuna rashin jin dadinsu dangane da zaben.

Tun kafin a kammala zaben dai ‘yan takara shugabancin jami’yyar da dama ne suke janye takararsu don nuna adawa da yadda zaben ya gudana kuma har yanzu ake ci gaba da kace-nace a kansa.

Wasu ‘ya yan jamiyar sun rika tada jijiyar wuya bayan da aka bayana sakamakon zaben.

 1. PDP ta zabi Uche Secondus sabon shugabanta
 2. PDP na gudanar da babban taronta na kasa
 3. Atiku Abubakar ya koma PDP

Wasu daga cikinsu sun nemi jam’iyyar ta mayar musu da kudin fom dinsu saboda a cewarsu ba a yi adalci a zaben ba.

Yan takarar dai sun nuna rashin jin dadinsu game da wata takarda mai dauke da jerin sunnayen wasu da aka ce sune sabbin shugabannin jam’iyyar da aka kira Unity list, da aka rika rarabawa tun kafin a kamala zaben.

Sai dai kwamitin da aka dorawa alhakin shirya zaben ya musanta cewa an yi magudi a zaben.

Sakataren watsa labarai na kwamitin, John Odey ya ce jam’iyyar ta dauki wasu matakan rage ‘yan takara ne saboda yawansu ya wuce kima

Wasu masana harkokin siyasar Nigeria ,sun ce har yanzu jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta koyi darasi ba, tun zaben da ta sha kaye a shekarar 2015.

Ana zubar da ciki miliyan 15 a India a duk shekara


Matan India kan yi amfani da kwayoyi wajen zubar da cikiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matan India kan yi amfani da kwayoyi wajen zubar da ciki

Wani sabon bincike da aka gudanar ya gano cewa ana zubar da ciki fiye da miliyan 15 a India a kowacce shekara.

Wannan kididdiga dai ta dara wadda aka bayar a hukumance a kasar.

Wata cibiyar bincike mai suna Guttmacher Institute’s research da ke New York, ta gano cewa mafi yawan matan Indian da suke zubar da cikin, suna amfani ne da kwayoyi ba bu ka’ida a gida ba tare da tuntubar yadda za a yi amfani da su ba.

Gwamnatin kasar ta India, ta ce ana zubar da ciki kasa da dubu 700 ne a kowacce shekara a kasar ne.

Gwamnatin ta samo adadin ne bayan ta hada bayanai daga asibitocin jihohi da kuma dakunan sha ka tafi.

Masu binciken sun ce matan kan sha wuya a yayin zubar da cikin.

Real Madrid na harin Kofin Duniya na uku


'Yan wasan Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid na fatan kammala wannan shekara da kofinta na biyar a birnin Abu Dhabi a wannan makon

Zakarun Turai Real Madrid za su fara kokarin daukar kofin duniya na kungiyoyi a karo na uku, inda za su yi wasan kusa da karshe da kungiyar Al Jazira a birnin Abu Dhabi a ranar Laraba.

Kungiyar ta Zinedine Zidane na harin zama ta farko a tsakanin sauran takwarorinta zakaru da za ta ci kofin haka a jere.

Abokiyar hamayyarta ta Spaniya, Barcelona ita ce kadai ta ci kofin na duniya na kungiyoyi sau uku, tun lokacin da aka bullo da gasar a shekara 2000.

Gasar tana kunsar zakarun nahiyoyi ne shida na Fifa, tare da kungiyar da ta dauki kofin lig na kasar da za a gudanar da ita.

An daga wa Real Madrid kafa a gasar zuwa matakin wasan na kusa da karshe, kuma kungiyar da za su yi da ita, Al Jazira, ta samu tikitin gasar ne saboda ita ce ta dauki kofin zakarun gasar kasashen yankin tekun Persia.

Kungiyar ta kai wannan mataki ne na karawa da Madrid bayan da ta doke takwararta ta Auckland City ta New Zealand a wasan raba-gardama.

Bayan wannan kuma ta yi galaba a kan Urawa Red Diamonds ta Japan a wasan dab da na kusa da karshe na gasar.

Real Madrid ta dauki kofin a shekara ta 2014 da 2016, kuma wannan shi ne zai kasance kofi na biyar da zakarun za su dauka a wannan shekara mai karewa ta 2017.

A daya wasan na kusa da karshe kungiyar Gremio ta kasar Brazil za ta hadu da Pachuca daga Mexico.

Tottenham:Toby Alderweireld ya tafi jinya sai Fabrairu


Toby Alderweireld lokacin da ya ji rauniHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Toby Alderweireld ya rasa wasa takwas tun lokacin ya ji raunin a karawarsu da Real Madrid

Dan wasan baya na Tottenham Toby Alderweireld ba zai sake taka leda ba daga yanzu har zuwa watan Fabrairu na shekara mai kamawa saboda raunin da ya ji a cinyarsa kamar yadda kociyansu Mauricio Pochettino ya tabbatar.

Dan bayan na Belgium mai shekara 28, bai yi wasa ba tun lokacin da ya samu matsalar a karawar da suka ci Real Madrid 3-1 ta gasar zakarun Turai ranar 1 ga watan Nuwamba.

A tsawon wannan lokacin Tottenham din ta yi nasara sau biyu ne kawai a wasa shida da ta yi na gasar Premier.

An ruwaito kociyansu Pochettino yana cewa ba abin da za su iya yi da kaddara, abin da ya faru ya riga ya faru, dan wasan ya ji rauni kuma ba zai sake wasa ba sai a watan Fabrairu.

Kungiyar ta Spurs tana wasa 10 a gasa daban-daban tsakanin yanzu da watan na Fabrairu, wasannin da suka hada da na Premier, da za ta yi da Manchester City da kuma Manchester United.

Sannan kuma za ta yi wasan hamayya na arewacin Landan, wato karawarta da Arsenal ta gaba ranar 10 ga watan na Fabrairu a Wembley.

Sannan kuma bayan kwana uku za ta yi wasanta na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin zakarun Turai da Juventus.

A ranar Laraba ne Tottenham din da ke matsayi na shida a teburin Premier za ta fafata da ta 13, Brighton.

Fifa ta hukunta Najeriya saboda sa dan wasan da bai cancanta ba


Alkalin wasa lokacin da ya ba wa Abdullahi Shehu katin gargadi a wasan Najeriya da ZambiaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An ba wa Abdullahi Shehu na Najeriya katin gargadi na biyu a wasan neman tikitin gasar kofin duniya ta 2018 a karawarsu da Zambia

An hukunta hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) saboda sanya dan wasan da bai cancanta ba a karawar kasar da Algeria ranar 10 ga watan Nuwamba na 2017.

A hukuncin an ayyana Najeriya ta saryar da wasan tare da ba wa Algeria nasara da ci 3-0, da kuma cin tarar hukumar kwallon ta Najeriya sama da naira miliyan biyu.

Hukunci ya danganci dan wasan kasar ne Abdullahi Shehu, wanda Najeriya ta sa a haduwarata da Algeria duk da cewa ya kamata ya tsallake wasa daya sakamakon katin gargadi da aka ba shi a wasa biyu daban-daban na gasa daya.

Sai dai kuma hukuncin ba shi da wani tasiri ga sakamakon karshe na gasar ta neman gurbin gasar cin kofin duniya, saboda daman Najeriya tuni ta cancanci zuwa gasar kafin wasan, kuma ita Algeriya, an rigaya an fitar da ita.

Marvin Zeegelaar: An yi watsi da bukatar janye jan katin dan wasan na Watford


Lokacin da Marvin Zeegelaar ya yi ketarHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Marvin Zeegelaar ya koma Watford ne daga Sporting Lisbon a kan fam miliyan 2.75

An yi watsi da bukatar janye jan katin da aka ba wa dan wasan baya na Watford Marvin Zeegelaar a karawarsu da Burnley ta ranar Asabar.

Alkalin wasa ya kori dan wasan mai shekara 27 saboda keta kafa bibbiyu da lafirin yake ganin ya yi wa Steven Defour a wasan da Watford ta yi nasara 1-0 a gidan Burnley, Turf Moor.

Dan wasan na Holland yanzu ba zai buga wasan da za su yi na lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara ba, inda za su kara da Crystal Palace da Huddersfield da kuma Brighton.

An jiyo kociyan Watford Marco Silva a ranar Asabar yana cewa hukuncin da aka yi wa dan wasan ya yi tsanani.

Bayan wasan Silva ya kara da cewa, ba laifi ne na bayar da jan kati ba, katin ya sauya komai a wasan, domin bayan minti biyu ko uku da bayar da shi suka ci, in ji kociyan yana korafi.

Watford za ta yi fatan ganin ta yi nasara a wasanta na farko a cikin hudu, idan suka hadu da tawagar Roy Hodgson, Crystal Palace a ranar Talatar nan.

An ji wa Oscar Pistorius rauni a gidan yari


Oscar Pistorius tare da jami'an tsaroHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An samu Oscar Pistorius (na hagu a 2016) da laifin kashe budurwarsa a shekarar 2015

An raunata tsohon dan tseren Afrika ta Kudu Oscar Pistorius a wani fada da suka yi a gidan yarin da yake, kasa da mako biyu da lillinka hukuncinsa na kisan budurwarsa Reeva Steenkamp.

Wani kakakin hukumar gidan yarin ya sheda wa BBC cewa an ji wa dan tseren gasar Olympic ta nakasassun ne raunin a yayin sa-in-sa kan amfani da wayar tarho ta gidan kason.

Kakakin ya ce Pistorius wanda aka daure shekara 13 da wata biyar ya dan kurje ne a lokacin rigimar, amma ba wani ciwo mai tsanani da ya ji.

Mai magana da yawun hukumar gidan yarin a Attridgeville Correctional Centre, Singabakho Nxumalo, ya ce Pistorious ya yi rigima da wani dan gidan kason ne a kan amfani da wayar tarhon ne.

Rigimar ta faru ne a ranar shida ga watan nan na Disamba, kwana 10 bayan da masu gabatar da kara na kasar ta Afirka ta Kudu suka yi nasarar gamsar da kotu cewa akwai bukatar kara wa’adin shekara shida da aka yanke wa tsohon dan tseren na Olympic.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Pistorius ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp a ranar masoya ta shekarar 2013

A watan Nuwamba kotun kolin kasar ta daukaka kara ta yanke wa Pistorious hukuncin zaman gidan maza na shekara 15, mafi karancin da dokar Afrika ta Kudu ta tanada a kan laifin kisan kai, wanad tuni ya yi rabin wa’adin.

A da dai kotu ta samu Pistorious da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp ba da niyya ba, a ranar masoya ta 2013 amma kuma daga baya kotun kolin ta daukaka kara ta sauya hukuncin inda ta same shi da laifin kisan da gangan.

Za a sake yi wa Saraki shari'a


Kotun daukaka karar dai ta wanke Saraki a cikin shekarar 2017Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Kotun daukaka karar dai ta wanke Saraki a cikin shekarar 2017

Kotun daukaka kara ta yankin Abuja ta tasa keyar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, zuwa kotun da’ar ma’aikata domin a sake masa sharia kan zargin rashin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa.

Gwamnatin Najeriya dai ta daukaka kara ne bayan kotun da’ar ma’aikata ta wanke shugaban majalisar dattawan Najeriyar da farkon wannan shekarar.

Kotun da’ar ma’aikatar ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume 18 na rashin fadin gaskiya wajen bayyana kadarori da aka yi wa Saraki.

A zamanta a yau, kotun ta yanke hukuncin cewa Mista Saraki bai bayar da gamsasshiyar amsa kan uku daga cikin tuhume-tuhume 18 da aka masa ba.

Masu shari’ar uku da suka jagorancin zaman kotun karkashin alkali Tinuade Akomolafe-Wilson, sun yi watsi da sauran tuhume-tuhume 15 din da gwamantin Najeriyar ta yi wa Saraki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana Tuhumar Bukola Saraki da rashin yin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara

Sai dai kuma wata sanarwa daga ofishin watsa labaran Bukola Saraki ta ce shugaban majalisar dattawan Najeriyar zai daukaka kara kan hukuncin.

Tsananin sanyi a Ingila ya sa an dage wasan kofin FA


Kankara ta mamaye fili har ma da jikin kwallonHakkin mallakar hoto
OTHERS

Image caption

Ana iya ganin kankara a filin wasan nan da ma jikin kwallon

An dage biyu daga cikin wasannin ranar Talata na zagaye na biyu na gasar cin kofin FA da kuma gasara tseren doki ta Ayr saboda tsananin sanyi.

Sanadiyyar kankara a filayen wasan ne aka dage karawar ta gasar ta FA tsakanin Crewe da Blackburn Rovers da kuma ta Carlisle da Gillingham.

Yayin da aka dage wasan na Crewe zuwa ranar Laraba 13 ga watan nan na Disamba da karfe 7:45 agogon GMT, ba a tsayar da ranar da za a yi daya wasan ba.

Haka ita ma gasar tseren dokin ta Ayr an dage ta ne saboda filin tseren ya daskare da kankara.

Man City ba ta wuce makadi da rawa ba a murnar doke Man Utd – Pep Guardiola


Guardiola da MourinhoHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Tawagar Guardiola, Manchester City ta bayar da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester United bayan ta doke ta a ranar Lahadi

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya musanta cewa ‘yan wasansa sun wuce makadi da rawa a yayin murnar cin abokan hamayyarasu Manchester United da suka yi ranar Lahadi, 2-1.

Kociyan dan kasar Spaniya ya ma kara da cewa shi da kansa ne ya karfafa wa ‘yan wasan nasa da su yi bureden.

A yayin murnar ne shi kuma kociyan United Jose Mourinho aka watsa masa ruwa da madara a kofar dakin sauya tufafi na Man City a filin na Old Trafford, lokacin da yake musayar kalamai da mai tsaron ragar City, dan Brazil, Ederson.

Guardiola ya ce ko alama abin da tawagar tasa ta yi daidai ne da wanda ta yi lokacin da suka doke Southampton.

Harry Kane ya kusa ya kai Alan Shearer yawan kwallaye


Harry Kane heads in his first goal for Tottenham against Stoke on SaturdayHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Harry Kane ya ci kwallaon shi na farko a karawar Tottenham da Stoke ranar Lahadi

Ya fi Cristiano Ronaldo da Neymar da kuma West Brom da Crystal Palace – yawan kwallaye a shekarar 2017.

Iya zura kwallo a raga na dan wasan gaban Tottenham din ya ci gaba ranar Asabar inda ya ci kwallo biyu a wasan da Spurs ta lallasa Stoke da 5-1 a filin wasa na Wembley.

Kane ya ci kwallo 33 cikin wasannin gasar Firimiya 32, wadanda suke cikin kwallaye 50 da ya ci cikin wasanni 48 a dukkan gasa da ya buga wa kulob dinsa da kasarsa.

Dan shekara 24 din ya yi kusa da tarihin da mutumin da ake ganin Kane zai gada ya kafa- tsohon dan wasan gaban Blackburn da Newcastle da kuma Ingila, Alan Shearer.

Wadanda suka fi cin kwallaye a gasar Firimiya a shekara cikin tarihi

Dan wasa Kulob Kwallaye Shekara
Alan Shearer Blackburn 36 1995
Robin van Persie Arsenal 35 2011
Thierry Henry Arsenal 34 2004
Harry Kane Tottenham 33 2017
Alan Shearer Blackburn 30 1994
Les Ferdinand Newcastle 30 1995
Ruud van Nistlerooy Manchester United 30 2003

Kwallayen Kane 33 suna daidai da ko kuma sun fi na kungiyoyin kwallon kafar gasar Firimiya a wannan shekarar – na Swansea da Burnley (jumulla sun da 33), Crystal Palace (tana da 31) kuma West Brom (tana da 30).

Kwallaye biyun da Kane ya ci Stoke sun sa jumullar kwallayen da ya ci a gasar Firimiya sun kai 90, matakin da ya cimma cikin wasanni 131.

Shearer kadai ne kawai fi saurin kai wannan matakin a tarihin gasar Frimiya , inda ya kai matakin cikin wasanni 113 kafin ya kai ga kafa tarihin cin kwallaye 260 a wasanni 441 .

Shearer ya cigaba da taka leda har ya kai shekara 35. Idan Kane ya cigaba da murza leda har ya kai wadannan shekaraun, zai samu damar shekara 11 inda zai nemi cin kwallaye 170 da yake bukata domin kamo iya kwallayen Shearer, abin da zai kai ga in yana cin kwallaye 15 a ko wace kaka har zuwa karshen kakar 2028-29 .

Kane da Shearer – tarihin cin kwallo a kakarsu takwas ta farko
Kane Shearer
kaka Kulob Wasanni Kwallaye Kaka Kulob Wasanni Kwallaye
2010-11 Leyton Orient (loan) 18 5 1987-88 Southampton 5 3
2011-12 Millwall (loan) 22 7 1988-89 Southampton 10 0
2012-13 Leicester, Norwich (both loan), Tottenham 19 2 1989-90 Southampton 26 3
2013-14 Tottenham 10 3 1990-91 Southampton 36 4
2014-15 Tottenham 34 21 1991-92 Southampton 41 13
2015-16 Tottenham 38 25 1992-93 Blackburn 21 16
2016-17 Tottenham 30 29 1993-94 Blackburn 40 31
2017-18 (kawo yanzu) Tottenham 15 12 1994-95 Blackburn 42 34

'Turai na da hannu a cin zarafin 'yan ci-rani a Libya'


A picture taken on June 27, 2017 shows Libyan coast guardsmen standing in a dinghy carrying illegal immigrants during a rescue operation of 147 people who were attempting to reach EuropeHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Jami’an tsaron da ke gadin gabar tekun Libiya suna yawan kama kwale-kwalen ‘yan cirani

Gwamnatocin Turai suna da hannu a cin zarafin ‘yan cirani da ‘yan gudun hijira a Libiya, in ji kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International .

Kungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wani rahoto inda ta kara da cewa a kokarinta na dakile kwararar bakin haure, kungiyar tarayyar Turai tana taimaka wa “wani shirin cin zarafin” bakaken fata a gabar tekun Libiya.

Kudaden kungiyar tarayyar Turai suna zuwa ga hukumomin da ke aiki da mayaka da kuma masu safarar mutane, in ji rahoton.

Kungiyar tarayyar Turai ta bayar da jiragen ruwa da horaswa da kuma kudi ga jami’an tsaron gabar tekun Libiya.

Libiya ita ce hanyar da ‘yan ci-rani masu son zuwa Turai suka fi bi wurin isa Italiya.

Amma Amnesty ta ce jam’ian tsaron suna aiki da ‘yan daba masu laifi da kuma masu safarar mutane wadanda aka samu da laifin nau’o’i na cin zarafi, da sanin jami’an kungiyar tarayyar Turai.

Kungiyar Amnesty ta yi zargin cewa kokarin dakile kwarar bakin haure ya janyo “kama mutane da yawa da kuma daure su ba gaira ba dalili”.

Me ya sa ba a daina wahalar fetur a Nigeria ba?


'Yan Najeriya da dama na kokawa kan matsalar karancin man feturHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan Najeriya da dama na kokawa kan matsalar karancin man fetur

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da fuskantar karancin man fetur duk da umarnin da gwamnati bai wa ministan man fetur na ya tabbatar an kawo karshen matsalar.

A ranar Larabar makon jiya ne ministan watsa labarai Lai Mohammed ya yi wa ‘yan jarida bayani bayan taron Majalisar Ministoci cewa an umarci takwaransa na harkokin mai, Ibe Kachikwu ya gaggauta kawo karshen matsalar ta man fetur kafin karshen makon jiya.

A wancan lokacin, kakakin babban kamfanin mai na kasa, NNPC, Ndu Ughamadu, ya bayyana kwarin gwiwarsa ta kawo karshen matsalar.

Sai dai mutanen da muka yi magana da su a jihodi da dama na Najeriya ranar Talata sun ce suna ci gaba da fuskantar wannan matsala.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan bumburutu na ci gaba da cin karensu babu babbaka

Mallam Ibrahim Adamu wani direban motar haya a jihar Kano ya ce “babu wata alama da ke nuna cewa za a kawo karshen wannan matsala nan kusa”.

“Hasalima tun daga ranar da aka ce za a shawo kan wannan matsala, mu a Kano kamari take dada yi”, in ji shi.

Wannan kalami na Mallam Ibrahim shi ne kusan abin da dukkan mutanen da BBC ta tuntuba ke cewa.

Hakan ya sa masu sayar da fetur a kasuwar fage ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin kamfanin mai na NNPC kan abin da ya sa ake ci gaba da fama da karancin fetur duk da umarnin da gwamnati ta bayar kan magance shi amma ba mu yi nasara ba.

Kuna da labarin da kuke so BBC ta bibiya? Ku karanta labarin nan


Idan ka/kina son yin tambaya kan wani abu domin BBC ta bincika, sai ka/ki cike wannan fom din.

Kada ku manta ku rubuta suna da imel dinku ta yadda za mu iya tuntubarku idan za mu amsa tambayar da kuka aiko.

Ba za mu sanar da kowa adireshinku na imel ba.

Za mu wallafa labaran da muka yi game da tambayar da kuka aiko a shafinmu na intanet da ke nan BBC da talabijin da rediyo da kuma shafukan sada zumunta.

Kazalika za mu nemi masu mu’amala da mu su auna tambayoyin da kuka turo kan mizani domin mu ga wadanda suka fi dacewa mu yi bincike a kansu.

Za mu wallafa yadda aka auna tambayoyin da mizanin da aka yi amfani da shi a shafin da muka buga labarin.

Sannan za a tambaye ka/ki ko kuna so a wallafa sunanku tare da tambayoyinku.

Idan kuna da tambaya kan bayananku za ku iya tuntubarmu a [http://www.bbc.co.uk/news/20039682]

BBC za ta ajiye bayananku na tsawon wata 12.

Sannan za ta kare sirrin bayananku, za kuma ta fitar da shi ne kawai idan bai sabawa ka’idojin manufar kare sirrin mutane da BBC ta tanada ba <http://www.bbc.co.uk/privacy>, inda za ta shigo da wani bangare na uku wanda shi ma ba zai bayyana sirrinku ba [<http://www.bbc.co.uk/privacy>]

Bikin cikar Kaduna shekara 100 da kafuwa


Za a nuna al'adun gargajiya da raye raye da hawan daba domin murnar cikar Kaduna shekara 100 da kafuwaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a nuna al’adun gargajiya da raye raye da hawan daba domin murnar cikar Kaduna shekara 100 da kafuwa

An soma shirye shiryen gudanar da bikin cikar binin Kaduna na arewacin Nigeria shekara 100 da kafuwa.

A makon da mu ke ciki ne zaa gudanar da wannan biki, inda za a nuna al’a’dun gargajiya da raye raye da kade da kuma hawan daba .

Sai dai wasu a jihar Kaduna sun nuna rashin jin dadinsu kan bikin da za a yi musaman idan aka yi la’akari da ma’aikatan da aka kora da yanayi kuncin rayuwa da mutane suke ciki a jihar.

Sun ce kamata ya yi a yi zaman makoki a jahar, ba biki ba.

A shekara 1917 aka kafa Kaduna kuma Lord Lugard shi ne gwamnan farko na jihar wanda ya dauko shelkwatar arewa daga Zungeru ya kawota Kaduna.

Bisa la’akari da wannan ne gwamnatin jihar Kaduna ta ce ya kamata ta gudanar da bukukuwa domin murnar cikar jihar shekara 100.

'Rashin bin doka ne ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma'


An jima ana samun rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma a Najeriya

Image caption

An jima ana samun rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma a Najeriya

Gwamnatin Najeriya, ta bullo da wani tsari domin magance tashe-tashen hankulan da ake fama da su tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma a wasu yankuna na kasar.

A ranar litinin din data gabata ne mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya tattauna da wasu masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin magance matsalar.

Mai martaba sarki Kano, Muhammadu Sanusi na II da kuma Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu, na daga cikin wadanda suka halarci taron, baya ga wasu shugabannin fulani.

Dr Aliyu Tilde na daga cikin wadanda suka halarci taron, ya kuma shaida wa BBC cewa, an tattauna matsalolin da suka kunno kai a baya-bayan nan wadanda suka shafi tashen-tashen hankulan da ake samu tsakanin fulani makiyaya da manoma.

Dr Tilde, ya ce an tattaunawar an fito baro-baro an shaida wa mataimakin shugaban kasa irin matsalollin da makiyaya ke ciki.

Ya ce, matsaloli na kin bin doka da kuma barin abubuwa su lalace ba tare da daukar matakin da ya da ce a kai ba suke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Dr Tilde, ya ce yakamata yanzu makiyaya su sani cewa ana kokari ayi nazari a kan matsalolinsu da kuma lalubo hanyar magance su.

A makon da ya gabata ne mataimakin shugaban Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci garin Numan na jihar Adamawa bayan hare-hare da aka kai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Kazalika ko a watan Nuwamban 2017 ma, rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a yankin tsakanin kabilun Bacama da Fulani inda aka kashe mutane akalla 20.

Ba za mu rusa rundunar SARS ba — 'Yan sanda


Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don jin hirar da SP Almustafa Sani ya yi da BBC:

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce babu wani abu da zai sa ta rusa rundunar nan ta musamman mai yaki da fashi da makami da ake kira SARS duk da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na soke ta.

Rundunar na mayar da martani ne ga zanga-zangar da ake yi a wasu biranen kasar ta neman a soke rundunar, bayan gangamin da aka rika yi a shafukan zumunta na neman a rushe ta bisa zargin taka hakkin bil’adama.

Mamadou Sakho na Crystal Palace ya tafi jinyar tsawon lokaci


Mamadou Sakho (a dama)Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mamadou Sakho (a dama) ya yi wa Faransa wasa sau 28

Dan wasan baya na kungiyar Crystal Palace a Premier, Mamadou Sakho ya ji raunin da zai yi jinya ta tsawon lokaci a sharabarsa.

Sakho ya ji raunin ne a wasan da suka yi canjaras 2-2 ranar Asabar da Bournemouth, kociyan Palace Roy Hodgson yana ganin dan wasan zau dauki makwanni kafin ya warke.

Kungiyar za ta kuma duba yanayin Yohan Cabaye, wanda aka sauya shi a wasan da suka yi da Bournemouth, saboda dan rauni da ya ji.

Ita kuwa kungiyar Watford ta daukaka kara a kan jan katin da aka ba wa Marvin Zeegelaar a lokacin wasansu da Burnley a karshen mako.

Sannan Kiko Femenia ya samu ‘yar matsalar cirar nama a cinyarsa, wadda kungiyar ke dubawa, yayin da shi kuwa Miguel Britos ke dab da warwarewa ya dawo taka wa kungiyar leda nan ba da jimawa ba.

Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Africa ta BBC


"MO" Salah ya ce yana son ya sake cin kyautar a badi

Image caption

“MO” Salah ya ce yana son ya sake cin kyautar a badi

Dan wasan kasar Masar da kuma Liverpool, Mohamed Salah, ya ci kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta BBC ta shekarar 2017.

Bayan ya samu kuri’u masu tarin yawa, Muhamed Salah ya doke dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da dan kasar Guinea Naby Keita da dan Senegal Sadio Mane da kuma dan Najeriya, Victor Moses.

Dan wasan mai shekara 25 ya shaida wa BBC cewar: “Na yi murnar cin wannan kyautar.”

“Mutum zai ji dadi na musamman idan ya ci wata kyauta. Za ka ji ka taka rawar gani a shekara, na yi murna matuka. Zan so in sake cin kyautar a shekara mai zuwa!”

Salah, wanda ya fi kowa cin kwallo a gasar Firimiya da kwallayensa 13, ya taka rawar gani a wannan shekarar a kulob dinsa da kuma kasarsa.

A farkon shekarar 2017, shi ne ya jagoranci kasar Masar a lokacin da ‘yan wasanta suka zo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Daga baya a cikin wannan shekarar, dan wasan gaban mai yawan gudu, ya taka rawa a wajen cin dukkan kwallaye bakwai din da suka sa tawagar kasarsa, Pharaohs, ta samu zuwa gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a karon farko tun shekarar 1990 – ya tallafa wajen cin kwallo biyu kuma ya ci kwallo biyar, ciki har da fenareti na karshen da ya yi amfani da shi ya ci Kongo, lamarin ya sa kasarsa ta samu zuwa gasar ta Rasha.

“Ina so na kasance dan Masar da ya fi fice saboda haka ina aiki tukuru,” in ji mutumin da ya zama dan Masar na uku da ya ci kyautar kuma na farko tun shekarar 2008.

“Ina bin hanyata kuma ina son kowa a Masar ya bi hanyata.”

Iya taka ledar Salah a kungiyar kwallon kafarsa ta yi kyawun yadda yake taka leda wa kasarsa.

A Italiya, ya ci kwallaye 15 kuma ya taimaka a ci wasu 11 a lokacin da ya tallafa wa Roma ta zo ta biyu a gasar Serie A, mataki mafi girma da kungiyar ta kai cikin shekara bakwai, kafin ya koma Liverpool ya kuma ci mata kwallaye 13 cikin wasannin gasar Firimiya 16.

“Zan so in gode wa takwarorina na Liverpool kuma na ji dadin kakar da na yi da Roma. Saboda haka ya zama dole in gode wa abokan taka leda na a can da kuma tawagar kwallaon kafar kasata,” in ji Salah.

“Tun da na zo nan, na so in yi aiki tukuru domin nuna wa kowa salon kwallo na. Na so in dawo gasar Firimiya tun da na bar ta, saboda haka ina matukar murna.”

Salah ya dauki hankalin masu kallon gasar Firimiya cikin gaggawa a wannan kakar, maimakon irin rawar da ya taka a kakar 2014-15 da ba ta kai haka ba.

“Ya cancanci kyautar,” in ji kocin Liverpool Jurgen Klopp, wanda ya bai wa dan wasan kyautar a makarantar kulob din ta horaswa da ke unguwar Melwood.

“Ni wani mutum ne mai sa’a. Na samu damar aiki da wasu ‘yan wasa kwararru kadan kuma ina murnar cewa a yanzu da “Mo” nake aiki.

“Ta inda maganar ta yi da di ita ce kasancewarsa matashi har yanzu, yana da damar kara kwarewa, yana da baiwa mai yawa da zai iya kara kwarewa a kai, amman haka ya kamata, da gaske, in yi aiki da shi.”

A yanzu haka sunan Salah ya shiga cikin jerin sunayen ‘yan wasan Afirka da suka fi fice irin su Abedi Pele da George Weah da Jay-Jay Okocha da kuma Didier Drogba, ta hanyar cin kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta shekara.

“Ina matukar murnar kasancewa kaman su wajen cin wannan kyautar,” in ji dan Masar din, wanda ya bi sahun ‘yan kasarsa Mohamed Barakat (a shekarar 2005) da kuma madugu Aboutreika (a shekarar 2008) wajen cin kyautar .

Image caption

Mohamed Salah ya zama dan Masar na uku da ya ci kyautar bayan Mohamed Barakat da Mohamed Aboutreika

Wadanada su ka ci kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na shekara a baya :

2016: Riyad Mahrez (Leicester City da Algeriya)

2015: Yaya Toure (Manchester City da Kot Dibuwa)

2014: Yacine Brahimi (Porto & Algeriya)

2013: Yaya Toure (Manchester City da Kot Dibuwa)

2012: Chris Katongo (Henan Construction da Zambiya)

2011: Andre Ayew (Marseille da Ghana)

2010: Asamoah Gyan (Sunderland da Ghana)

2009: Didier Drogba (Chelsea da Kot Dibuwa)

2008: Mohamed Aboutrika (Al Ahly da Masar)

2007: Emmanuel Adebayor (Arsenal da Togo)

2006: Michael Essien (Chelsea da Ghana)

2005: Mohamed Barakat (Al Ahly da Masar)

2004: Jay-Jay Okocha (Bolton da Najeriya)

2003: Jay-Jay Okocha (Bolton da Najeriya)

2002: El Hadji Diouf (Liverpool da Senegal)

2001: Sammy Kuffour (Bayern Munich da Ghana)

2000: Patrick Mboma (Parma da Cameroon)

An jefi Jose Mourinho sannan an fasa wa Mikel Arteta na Man City kai


Pep Guardiola da Jose MourinhoHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An jefi Mourinho da madara da ruwa a lokacin da yake cacar-baki da golan Manchester City, Ederson a kofar dakin sa kaya na ‘yan City

An jefi kociyan Manchester United Jose Mourinho da ruwa da madara shi kuma mai koyar da ‘yan wasan Manchester City motsa jiki Mikel Arteta ya ji rauni a ka yayin wata sa-in-sa bayan wasan kungiyoyin biyu ranar Lahadi.

‘Yan United sun harzuka ne kan abin da suke gani ya wuce-makadi-darawa a lokacin murnar da ‘yan wasan City suke yi bayan sun bi abokan hamayyar tasu har gida Old Trafford sun casa su 2-1, suka yi musu fintinkau da maki 11 a teburin Premier.

‘Yan wasan City sun rika burede a gaban magoya bayansu bayan an tashi daga wasan, kuma ‘yan tawagar horar da ‘yan wasan sun nemi kociyansu Pep Guardiola shi ma ya bi sahu a cashe da shi amma ya ki.

Bayan ‘yan wasan gaba daya sun kama hanyarsu zuwa dakunanunsu na sauya tufafi, a nan ne ake ganin Mourinho ya nuna bacin ransa a kofar dakin tawagar Man City, a kan hanyarsa ta zuwa wajen hira da ‘yan jarida.

‘Yan Manchester City sun mayar da martani inda mai tsaron ragarsu dan Brazil Ederson da Mourinho suka yi cacar-baki da harshen Portugal.

Daga nan ne kuma aka jefi Mourinhon da wani kwalin madara da aka bari a dakin na bakin, ko da yake ba ta bata shi ba amma ta bata wani daga cikin ma’aikatansa.

Kuma an ga kociyan ya shiga dakin alkalin wasa a lokacin daga bisani ya fito ya tafi wajen hira da ‘yan jarida, amma dai bai yi maganar abin da ya faru ba a yayin ganawar.

Hakkin mallakar hoto
CAVENDISH PRESS

Image caption

Mikel Arteta ya rufe goshinsa lokacin da ya je filin atisaye na Manchester City ranar Litinin da safe

An ga mai horar da ‘yan wasan City motsa jiki Mikel Arteta ya ji rauni a ka amma ba a san yadda ya ji ciwon ba, kuma dukkanin bangarorin kungiyoyin biyu sun ce ba a ba wa hammata iska ba.

Kofin Europa: Arsenal za ta hadu da FK Ostersunds, Celtic da Zenit


Theo Walcott na murnar cin kwallo a karawarsu da Bate Borisov a gasar EuropaHakkin mallakar hoto
APf

Image caption

Theo Walcott da Welbeck a lokacin wasan da suka casa Bate Borisov a gasar Europa

Arsenal za ta hadu da FK Ostersunds ta Sweden yayin da aka hada Celtic da Zenit St Petersburg ta Rasha a matakin wasan kungiyoyi 32 na gasar kofin Turai na Europa.

Arsenal wadda ta zama ta daya a rukuninta na gasar ta Europa za ta fara ziyartar kungiyar ta Sweden ne a matakin wasan na sili-daya-kwale.

Celtic kuwa ta gama a matsayi na uku ne a rukuninsu na gasar zakarun Turai ta Uefa, saboda haka ta fado kasa zuwa gasar ta Europa, inda dukkanin kungiyoyi 32 da suka kai matakin za su yi fafatawar farko a ranar 15 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa, da karfe shida na yamma agogon Najeriya.

Sannan kuma sai a ranar 22 ga watan na Fabrairu na shekarar ta 2018 da karfe 9.05 na yamma agogon Najeriya, duka kungiyoyi 32 za su yi wasa na biyu, wanda daga nan ne za a tankade rabi wato 16, zuwa mataki na gaba.

Ga yadda jadawalin da aka fitar ranar Litinin din nan a hedikwatar hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, a birnin Nyon na Switzerland na gasar ta kofin Europa yake:

Borussia Dortmund v Atalanta

Nice v Lokomotiv Moscow

FC Copenhagen v Atletico Madrid

Spartak Moscow v Athletic Bilbao

AEK Athens v Dynamo Kiev

Celtic v Zenit St Petersburg

Napoli v RB Leipzig

Red Star Belgrade v CSKA Moscow

Lyon v Villarreal

Real Sociedad v Red Bull Salzburg

Partizan Belgrade v Viktoria Plzen

Steaua Bucharest v Lazio

Ludogorets v AC Milan

Astana v Sporting Lisbon

FK Ostersunds v Arsenal

Marseille v Braga

An kai harin bama-bamai a Amurka


Police at Port AuthorityHakkin mallakar hoto
AFP

‘Yan sanda a birnin New York City na Amurka sun ce an tsare wani mutum sakamakon tashin wasu abubuwan fashewa a tashar jirgin kasa da ke yankin Manhattan mai cike da hada-hada.

Abubuwan sun fashe ne a kusa da Times Square.

Ma’aikatan kwana-kwana sun ce mutum hudu sun ji rauni, ko da yake ba masu muni ba ne.

‘Yan sanda sun ce mutumin da ake zaergi da tayar da abubuwan ma ya ji rauni.

Wasu kafofin watsa labaran Amurka sun ambato jami’an da ba su bayyana sunayensu ba na cewa mutumin ya tayar da bam din da ke jikinsa a lokacin da ake tururuwar zuwa aiki.

Mai magana da yawun fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta ce an shaida wa Shugaba Donald Trump hfaruwar lamarin.

Za a kyale 'yan Saudiyya zuwa kallo a sinima


A Saudi woman takes a selfie with person dressed as the Beast from Disney's 2017 Beauty And The Beast film at a Comic Con Arabia event Riyadh on 25 November 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta dage haramcin da ta sanya kan zuwa sinima fiye da shekara 30 da suka wuce.

Ma’aikatar al’adu da watsa labaran kasar ta ce za ta soma bayar da lasisi nan take ga masu gidan sinima domin su fara budewa a watan Maris na shekarar 2018.

Matakin na cikin sauye-sayen da mai jiran gadon sarautar Saudiyya Yarima Mohammed bin Salman yake gudanarwa zuwa shekarar 2030.

Kasar ta Saudiyya, wacce ke bin tafarkin Musulinci sau da kafa, tana da gidajen sinima a shekarun 1970 amma Malaman addini sun sanya hukumomi rufe su.

A watan Janairun da ya gabata, an ambato Babban Limamin Masallatan Harami, Sheikh Abdul Aziz a–Sheikh yana yin gargadi kan illolin sinima, yana mai cewa za su bata tarbiyyar ‘yan kasar.

‘Ya’yan gidan sarautar Saudiyya da kuma Malaman addini na bin mazahabin Sunnah.

Wata sanarwa da ma’aikatar al’adu ta fitar ranar Litinin ta ce an dauki mataki bai wa masu gidan sinima lasisi ne saboda yana da muhimmanci wurin “saye-sauyen da gwamnati ke yi domin karfafa gwiwar samar da budaddiya kuma cikakkiyar al’ada ga ‘yan kasar”.

“Hakan wata hanya ce ta bunkasa al’ada a fannin tattalin arziki a wannan kasar,” in ji ministan Al’adu Awwad Alawwad.

“Bude sinima zai zama wata hanyar bunkasa tattalin arziki da; idan aka fadada al’adu za a samar da sabbin ayyuka da horaswa, da kuma bunkasa hanyoyin samar da nishadi a wannan Daula.”

Wasu mawakan hip hop irin su Nelly da Ceb Khaled za su yi waka a birnin Jedda ranar Alhamis, ko da yake maza ne kawai za su halarci wurin.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hiba Tawaji ce mawakiya ta farko da ta rera waka a kasar Saudiyya a makon jiya

Hazo ya hana jirage tashi a Nigeria


Hazo ya hana daruruwar mutane tafiyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hazo ya hana daruruwar mutane tafiya

Hazo ya sa an soke tashin gomman jirage a Najeriya, lamarin da ya sa matafiya da dama suka kasa samun jirage.

An soke akalla tashin jirage 20 a manyan filayen tashin jiragen sama a fadin Najeriya lamarin da ya sa daruruwan matafiya suka shiga wani hali na rashin tabbas.

Hazon dai ya sa ba a iya gani fiye da mita 400 a wurare da dama a Najeriya, yayin da ake bukatar iya gani na mita 800 kafin jirgi ya tashi ko kuma ya sauka.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi gargadin cewa za a yi hazo a sararin samaniyar jihohin da ke tsakiyar Najeriya, ranar Litinin.

Amfani da jiragen sama dai wata hanya ce wadda wasu ‘yan Najeriya ke bi wajen zirga-zirgar yau da kullum.

Borrussia Dortmund ta raba gari da kocinta


Peter Bosz, bayan da ya shafe wata bakwai yana jan ragamar kungiyar,

Image caption

Peter Bosz, bayan da ya shafe wata bakwai yana jan ragamar kungiyar,

Borrussia Dortmund ta kori kocinta Peter Bosz, bayan da ya shafe wata bakwai yana jan ragamar kungiyar.

Kungiyar ta kuma nada tsohon kocin Cologne, Peter Stoger, a matsayin kocin rikon kwarya har zuwa karshen kakar bana.

A makon da ya gabata ne Cologne ta kori kocinta Stoger.

Kungiyar ta Dortmund ta gaza samun nasara tun watan Satumba, ko a wasanta na ranar Asabar ma Werder Bremen ce ta doketa da ci 2-1 a gida.

Chelsea za ta hadu da Barcelona a Gasar Zakarun Turai


UEFAHakkin mallakar hoto
Getty Images

Chelsea za ta kara da Barcelona a sabon jadawalin da aka fitar na kungiyoyi 16 da za su fafata a Gasar Zakarun Turai.

 • Juventus da Tottenham
 • FC Basel da Manchester City
 • Porto da Liverpool
 • Sevilla da Manchester United
 • Real Madrid da PSG
 • Shakhtar Donetsk da Roma
 • Bayern Munich da Beskitas.

Karanta wadansu karin labarai

Wanene zai lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar BBC na bana?


Victor Moses (Nigeria), Sadio Mane daga Senegal, Mohamed Salah (Masar), Pierre-Emerick Aubameyang daga Gabon da kuma Naby Keita dan kasar Guinea su ne ke takarar lashe gasar dan kwallon Afirka na BBC na bana. Mun tambayi wasu ‘yan Afirka kan wanda suke so ya lashe gasar. Idan anjima ne da misalin karfe 6:30 na yamma a agogon Najeriya da Nijar za a sanar da wanda ya lashe ta.

Yadda fyade da kisan 'yar shekara 6 ya harzuka India


Locals carry the body of the six-year-old who was brutally raped and murderedHakkin mallakar hoto
Manoj Dhaka

Image caption

An yi wa ‘yar shekara shidan fyade tare da kashe ta

‘Yan sanda a Indiya suna yi wa mutane da dama tambayoyi dangane da fyade na rashin imani da kuma kisan gillan da aka yi wa wata yarinya ‘yar shekara shida a jihar Haryana da ke arewacin kasar.

An tsinci gawarta ranar Lahadi kusa da gidansu inda aka yi zargin cewa an sace ta cikin dare ranar 8 ga watan Disamba.

Irin mummunan ciwon da aka yi wa yarinyar lokacin fyaden ya bata wa Indiyawa rai matuka inda mafi yawa daga cikinsu suke alakanta batun da fyaden cikin bas da aka yi a birnin Delhi a shekarar 2012 wanda ya harzuka mutane matuka.

Mahaifiyar yarinyar ta shaida wa BBC cewa suna bukatar a hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

“Yanzu an samu sa’o’i 24 bayan aikata wanna aikin, kuma kawo yanzu ‘yan sanda ba su kama kowa ba,” in ji ta.

‘Yan sanda sun kama ‘yan uwan mijinta uku domin yi musu tambayoyi, amma har yanzu ba a tsare kowa ba. Sai dai kuma da haka ba a bayar da karin bayanai ba.

Gwamnatin kasar ta nada wani kwamitin masu bincike yayin da mutane suke kara matsa mata lamba domin ta kama wadanada suka aikata danyen aikin. Mutane ciki har da masu fafatuka da shugabannin siyasa daga gundumar sun hallara a kauyen domin su kaddamar da zanga-zanga.

Iyayen yarinyar suna bukatar cewa ‘yan sandan gwamnatin tarayyar kasar su gudanar da bincike kan lamarin, suna masu cewa ba su amince da ‘yan sandan jihar ba.

Mahaifin yarinyar, wani mai sana’ar sayar da tsumokara, ya ce ya fita aiki ne a daren da aka saci ‘yarsa.

A lokacin da matarsa ta tashi washe gari, ya ce , ta fahimci cewa ‘yarsu ta bata. Iyayen yarinyar suna da wasu ‘ya’ya uku – yara biyu da ‘ya mace daya.

Hakkin mallakar hoto
Manoj Dhaka

Image caption

Daga farko dai iyayen yarinyar sun ki su kona gawarta har sai an yi kame

Iyayen suna zama ne a wani fili tare da wasu iyalai hudu a garin Haryana. ‘Yan sanda suna zargin cewa wadanda suka yi wa yarinyar fyade tare da kashe ta za su iya kasancewa sun zo ne daga unguwar marasa galihu da ke kusa da inda iyayen suke.

Daga farko iyayen yarinyar sun ki su kona gawarta har sai an kama wadanda suka kashe ta. An ci gaba da jana’izarta ne kawai bayan ‘yan sanda sun tabbatar musu da cewa za su yi kame nan ba da jimawa ba.

Sun bai wa ‘yan sanda wa’adi – karfe 11 na safiyar Laraba – na su yi kame. Idan hakan bai faru ba, sun yi barazanar zuzuta zanga-zangar.

'Yan Kannywood sun yi jimamin shekara uku da mutuwar Dan Ibro


Ibro ya fito a fim din Babban Direba na Ilyas Tantiri dab da rasuwarsaHakkin mallakar hoto
Instagram/Abdul Ilyas Tantiri

Image caption

Ibro ya fito a fim din Babban Direba na Ilyas Tantiri dab da rasuwarsa

Masu ruwa da tsaki a fina-finan Kannywood sun tuna da mutuwar fitaccen dan wasan barkwancin nan Rabilu Musa (Dan Ibro), shekara uku bayan rasuwarsa.

Dan Ibro ya rasu ne ranar goma ga watan Disambar shekarar 2014 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya bayan ya yi fama da ciwon koda.

Wasu daga cikin masu harkokin fim sun bayyana irin kusancin da ke tsakaninsu da kuma kyawawan halayensa.

Darakta kuma jarumin fina-finai Falalu Dorayi ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa: “Shekara uku kenan, 10th December 2014 da rasa abokin neman halak. Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.

“Allah ya yi maka Rahma Alhaji Rabilu Musa Ibro. Allah ya sanya haske da ni’ima a kabarinka. Allah yai mana rahma baki daya. Allahu akbar. Rashin da babu madadinsa.”

Shi ma Abdulmumini Tantiri, wanda fim dinsa shi ne na karshe da Dan Ibro ya fito a ciki kafin ya rasu, ya ce “Alhaji Rabilu Musa (Ibro) mutum ne sak, mai kishin sana’arsa da abokan sana’a.Bai fiye magana ba a inda babu ruwansa, mai fadar gaskiya ne ba tare da tsoro ba. Kuma yana da halacci ga wanda ya yi masa halacci. Allah ka jikan Rabilu, ka yafe masa kura kuransa.Amin”.

Hakkin mallakar hoto
InSTAGRAM/ALI NUHU

Image caption

Ali Nuhu da Dan Ibro sun fito tare a fina-finai da dama

Hakkin mallakar hoto
InSTAGRAM/Falalu Dora

Image caption

Dan Ibro ya sha yin kalamai irin na siyasa a fina-finansa

Shi kuwa jarumi Ali Nuhu wallafa wani sashe na fim din da ya fito tare da Dan Ibro ya yi a shafinsa na Instagram, kana ya yi sharhi a karkashinsa inda ya ce: ” Sarki, sarki ne har abada. Muna kewarka, Chairman”.

Yara dubu 170 na hawa intanet a kullum


UNICEF ya ce dole a rinka sakaya sunan yara masu hawa intanetHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

UNICEF ya ce dole a rinka sakaya sunan yara masu hawa intanet

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya yi kira ga kwararru a fannin sadarwa ta zamani da su dauki kwararan matakan kare kananan yaran da ke amfani da kafar sadarwa ta internet.

UNICEF, ya ce a kowacce rana ana samun sama da yara dubu dari da saba’in da suka fara amfani da internet a duniya.

Asusun ya ce, a dai-dai lokacin da ake kara samun karuwar yaran da ke amfani da intanet din, akwai bukatar fito da sabbin matakan kare masu amfani da ita.

A karshe UNICEF, ya bada shawarar a duk lokacin da yara su ka hau yanar gizo, ya na da kyau a rinka sakaya sunayensu.

An ci zarafin jarumar fim din Dangal Zaira Wasim a cikin Jirgi


Zaira Wasim ta fito a cikin fina-finan India, kamar Dangal da Secret SuperstarHakkin mallakar hoto
ZAIRA WASIM INSTAGRAM

Image caption

Zaira Wasim ta fito a cikin fina-finan India, kamar Dangal da Secret Superstar

‘Yan sanda a Mumbai na kasar India, sun kama wani mutum da ake zargi da cin zarafin wata jaruma ‘yar kimanin shekara 17 da haihuwa a lokacin da suke cikin jirgin sama.

Zaira Wasim, ta wallafa a shafinta na Instagram wanda ta ke da masu binta kusan dubu 400 cewa, wani mutum mai matsaikacin shekaru da ke zaune a bayan kujerarta a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Mumbai daga Delhi, ya rinka shafa mata wuyanta har zuwa bayanta da kafarsa a lokacin da ta ke gyangyadi.

Zaira Wasim, wadda ta fito a cikin fina-finai biyu da suka yi fice a kasar india, wato Dangal da kuma Secret Superstar, ta ce ” Ina cikin gyangyadina mai dadi sai na rinka jin kamar abu yana bin bayana, da farko sai na yi watsi, to amma sai na ji har an taho ta bayana, anan ne na farga cewa lallai shafa ni ake yi ba zato nake ba”.

Jarumar a shafin nata na Instagram, ta ce ta so ta dauki hoton bidiyon mutumin a lokacin da ya ke shafa mata jikin da kafarsa, amma saboda ba haske a cikin jirgin ba ta yi nasara ba.

Zaira Wasim ta ce, ta so yin hakan ne saboda shaida, to amma duk da haka ta tona masa asiri kuma yanzu haka yana hannun hukuma.

Ta ce “Idan irin haka ta samu wata, to dole ta tona asirin wanda ya aikata, saboda sai mun taimaka wa kanmu kafin wani ya taimake mu”.

Yanzu haka dai kamfanin jirgin mai suna Air Vistara, ya nemi afuwar jarumar ya na mai cewa bai san hakan ya faru ba sai bayan sun isa Mumbai, kuma ba zai taba lamuntar irin wannan halayya a cikin jirginsa ba.

Cutar murar tsuntsaye ta hallaka dalibai 4 a Ghana


Hukumomi na cigaba da bayar da alurar rigakafi ga dalibai da kuma sauran ma'aikatan makarantarHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hukumomi na cigaba da bayar da alurar rigakafi ga dalibai da kuma sauran ma’aikatan makarantar

Hukumomin lafiya a Ghana sun tabbatar da cewar cutar murar tsuntsaye itace ta yi sanadiyyar mutuwar wasu dalibai hudu a babbar makarantar sakandire ta Kumasi Academy.

Sun kuma ce ana jinyar wasu daliban a wasu asibitoci da ke Kumasi.

A gwaje -gwajen farko da aka yi, an kasa gano cewa cutar ce tayi sanadiyyar mutuwar daliban amma daga bisani an tabbatar da bullar cutar.

Wakilin BBC da kai ziyara yankin ya ce dalibai kalilan ne suka rage a makarantar saboda iyaye sun kwashe ‘yayansu daga makaratar.

An kuma dage taron iyayen yara da aka aka shirya yi a ranar Asabar zuwa ranar Litinin.

Sai dai kawo yanzu dai hukumomi na cigaba da bayar da rigakafi ga daliabai da sauran ma`aikatan makarantar.

Matan da suka saka wando a Sudan basu aikata laifi ba


Matan da suka shigar bata dace ba a Sudan na cikin hadarin fadawa hannun 'yan sandaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matan da suka shigar bata dace ba a Sudan na cikin hadarin fadawa hannun ‘yan sanda

An janye tuhumar da ake yi wa wasu mata 24 wadanda aka kama saboda sun saka wando a wani taron liyafa da aka yi kusa da Khartoum babban birnin kasar.

‘Yan sanda sun cafke su ne bayan wani sameme da suka kai yayin taron liyafar a ranar Laraba.

Matan da ake tuhuma za su iya fuskantar hukuncin bulala 40 da kuma tara saboda sun yi shigar da bata dace ba.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce dubban mata ne ake wa bulala duk shekara a kasar bayan an same su da laifin rashin kamun kai.

Har ila yau sun ce dokar hana mata sanya wando da kuma guntun siket tana shafar Kiristocin kasar wadanda su ne tsiraru.

Galibin al’ummar Sudan Musulmi ne kuma mata a kasar suna sanya dogayen tufafi ne bisa al’ada.

Man City ta doke Man Utd


Man City ta doke Man United 1-2Hakkin mallakar hoto
Michael Regan

Image caption

City ta kara yi wa United nisa a teburin gasar firimiya

Manchester City ta yi nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United a wasan da suka yi gumurzu ranar Lahadi inda suka tashi wasan 2-1.

David Silva ne ya fara zura kwallo a ragar Manchester United a minti na 43 da fara fafatawar, yayin da Marcus Rashford ya farke wa kungiyarsa a minta na 45.

Bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ne Nicolas Otamendi ya kara zabga kwallo ta biyu a ragar Manchester United a minta na 54.

City ta ci gaba da zama ta daya a teburin firimiya da tazarar maki 11 tsakaninta da mai bi mata baya Machester United.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar a ranar Lahadi su ne:

 • Southamton 1-1 Arsenal
 • Liverpool 1-1 Everton

Karanta wadansu karin labarai

'Ana cin zarafin' matan Afirka da ke aikin gida a kasashen Larabawa


Rothna BegumHakkin mallakar hoto
Rothna Begum

Wani rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta fitar ya ce, matan kasar Tanzaniya da ke aiki a kasashen Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa na fuskantar fyade da azabtarwa da cin zarafi daga iyayen dakinsu.

Fiye da mata 50 da aka yi hira da su a yayin gudanar da binciken ya ce, iyayen dakinsu kan kwace musu fasfo kuma ana tursasa musu yin aiki na tsawon sa’o’i 15 zuwa 21 a ko wacce rana.

Sai dai ma’aikatar kwadago ta Oman ta karyata hakan.

Kusan rahotanni biyu daga cikin biyar na nuna ana samun cin zarafi da kuma yi musu fyade.

Gwamnatin Tanzaniya dai ba ta ce komai ba kan binciken, wanda ya yi zargin cewa ofisoshin jakadancin kasar ba sa wani abun a zo a gani don taimakawa matan.

Ga dai abin da uku daga cikin matan ke cewa, inda suka bayar da labaran da suka hada da na yadda ake cin zarafinsu. Amma suna iya daga muku hankali:

An min barazana da ruwan asid

Hakkin mallakar hoto
Rothna Begum

Dotto ta shaida wa Human Rights Watch cewa ta sayar da gonarta da ta gada daga iyayenta don ta biya wani kamfanin shirya tafiye-tafiye da ke Dar es Salaam, kudi kimanin dala 76, daidai da naira 27360, don tafiya zuwa Oman a shekarar 2015.

Matar mai shekara 32 ta ce iyayen dakinta kan lakada mata duka, su tursasa ta yin aiki tsawon sa’a 20 a duk rana, babu hutu, kuma suna biyan ta dala 130 (N46800) maimakon dala 210 (N75600) da aka yi yarjejeniyar bata.

“Na fara samun matsalar tabin hankali saboda rashin abokan mu’amala na kwarai. Na kuma yi ta fama da ciwon kai, don har na zaci ma ko haukacewa zan yi,” in ji ta.

A haka dai kuma sai aka fara cin zarafina.

“Ina cikin goge wata doguwar rigara abaya, sai ta kone. Uwar dakina ta yi fushi sosai, na yi koakrin nuna mata cewa ni ‘yar adam ce mai kuskure. Amma sai ta ki saurara ta, sai ta fara dukana ta kuma watsa min ruwa a fuska.

“Ta cewa danta ya samo ruwan asid. Na gudu cikin daki na buya na rufe don kar su shiga cikik.

A lokacin da ta je ofisihin jakadancin Tanzaniya don neman taimako, sai aka kulle ta na tsawon wata shida.

Ta ce tana iya tuna wa a wancan lokacin a watan Mayun 2016, akwai kusan mutum 60 a wajen.

“Ba a barin mu mu fita waje. An kulle mu cikin daki da kuma kicin.”

Ta ce bayan ta tsere ofishin jakadancin ne uwar dakinta ta bukaci sai an biya ta dala 1,560 a madadin asarar da aka ja mata.

Dotto ta ce jami’an ofishin jakadancin sun yi ta kokarin shawo kaita ta koma gidan da take aikin.

Sun ce min: “Idan ba ki ba da hadin kai ba fa za su kai ki gidan yari. Don haka ya rage naki.”

“Na ce, “Ta ya ya zan iya biya? Aikin wata biyu kawai na yi inda ake biyana dala 130, to ya ya zan yi biya?”

Ta je kotu kamar sau shida don sauraron batun warware matsalar, inda ofishin jakadancin suka hada ta da wani tafinta don ta bayar da labarin irin bakar wahalar da ta sha.

“Ina da hujja. An yanke ni a bayana da madubi, kuma na zo da wata yagaggiyar riga da aka dake ni lokacin da nake sanye da ita.”

A karshe dai uwar dakin nata ta yarda ta yi watsi da karar, amma fa sai da Dotto ta biya dala 260 kudin jirginta na komawa gida.

Maigidan ne ya yi min fyade

Atiya, wadda ta tafi Oman a watan Yunin 2015, ta ce iyayen dakinta sun kwace mata fasfo dinta da wayarta, suna kuma tilasata mata yin aiki na tsawon sa’o’i 21 ba hutu.

Ta shaida wa Human Rights Watch cewa ko abinci ba ta iya ci sai an ba ta izini kuma kullum sai an dake ta.

Bayan mako uku ne ta yi kokarin guduwa, amma uwar dakinta ta dawo da ita ta kuma ce mata: “Idan kina son komawa dole sai kin biya mu kudin da muka kashe wajen daukoki, kusan dala 890, (N320400).

Kamfanin da ya yi jigilarta tafiyarta a Oman ya ce ba zai iya taimakawa ba.

A watan Afrilun 2016 sai da aka kai ta asibiti bayan da ta suma saboda yadda ba ta iya cin abinci sakamakon ciwon makogoro.

Bayan ta koma gidan kuwa, ta ce sai da iyayen dakinta suka dauki fansa.

“Matar ta fara dukana tana cewa: ‘Ba wai kin dawo nan ba ne don ki sake rashin lafiya.’

“Ta kira kanwar mijinta don ta taimaka mata, suka yi min tsirara suka min duka da abun sakale kaya na roba.

“Masu aikin gini daga waje na jiyo ni ina ihu amma ba za su iya kawo min dauki ba.

“A lokacin da mijin ya dawo sai ya dauke ni ya kai ni daki ya min fyade, kuma ta baya ya neme ni. Bayan ya gama, sai washe gari suka sa ni a jirgi don komawa Tanzaniya.

“Suka kwace duk kudin da na samu, fasfo dina kawai suka bai. Suka kuma watsar da ni a filin jirgi kawai.”

Ta kai rahoton duka da fyaden da aka yi mata ga ‘yan sandan Tanzaniya da kuma sakatariyar masu hana fasa-kwabrin mutane da ma’aikatar cikin gida – na kai musu har da hotunan tabon dukan da aka yi min a baya.

Sai jami’an suka ce mata ai da tun a Oman din ta kai kara.

‘Yan sanda dai sun kama wanda ya yi silar tafiyarta a Tanzaniya, amma ba ta gasmu da wannan hukunci ba kadai.

“Har yanzu ina jin takaici idan na tuna abun da ya faru dani. Kawai ina son a biya ni diyyar abun da aka yi min ne kuma a dawo min da hakkokin, albashina da kayana da wayata.”

An mayar da ni wajen masu cin zarafina

Hakkin mallakar hoto
Rothna Begum

Mwajuma ta ce ta tsere zuwa ofishin jakadancin Tanzaniya da ke Oman a shekarar 2015, bayan da iyayen gidanta suka ci zarafinta kuma suka hana ta albashin wata shida.

Ofishin jakadancin ya gaya mata cewa ba abun da za su iya yi sai dai wanda ya yi mata hanyar aikin ya karbe ta.

Mwajuma mai shekara 27 ta ce ba ta son komawa hukumar don kuwa ta ga yadda wanda ya kawo su aikin ke dukan mata a zuwan da ta yi a baya.

Don haka sai ofishin jakadancin ya samu tabbaci daga hukumar cewa za su mayar da ita gida. Amma maimakon haka sai aka tursasa ta ta yi aiki a wani sabon wajen da ta biya kudaden da aka yi wahalarta.

“A yayin da na ga wasu matan ana dukansu a can, sai na tsorata, sai matan suka ba ni shawarar cewa gara na yarda ko ni ma a dake ni. Sai tsoro ya sa na ce, to.

An dauki tsawon wata biyu ba a biyanta albashi, a wasu gidaje biyu da ta yi aiki.

Sun ce wai suna bai w wanda ya akwo ta ne.

Ta kai kukanta ga ma’aikatar cikin gida ta Oman, amma sai wanda ya kai su kasar ya ki halartar sauraron koarfin, amma daga baya ya mayar mata fasfo dinta.

Ta kai korafin cin zarafin da aka yi mata bayan ta koma Tanzaniya, amma kuma tana ganin ba a bi mata hakkinta yadda ya kamata ba.

“Ina jin takaici idan na ga mutane na tafiya Oman. Har sai da na je hukumar hana fasa-kwabrin mutane na kai karar abu da aka yi min.

“Sun ce, matsalar daga wajenku take, da ku ke nacewa sai kun je.”

Kun san birnin da mazaunansa ba sa fushi?


Daga Megan Frye

Zai yi wuya ka ga dan Mexico City ya bata rai a bainar jama'aHakkin mallakar hoto
John Mitchell/Alamy)

Image caption

Zai yi wuya ka ga dan Mexico City ya bata rai a bainar jama’a

Na zauna a birnin Mexico City har kimanin wata shida kafin na ga wanda ya yi fushi a bainar jama’a.

Kuma mutumin ba dan kasar Mexico ba ne.

Lamarin ya faru ne bayan an kammala aikin ranar, kuma kantin shan shayi mai cike da mutane da nake ciki a wancan lokacin jerin mutane ya mamaye teburinsa.

Nan da nan sai wani mutum ya fara daga muryarsa ga mai karbar kudi: “kana son ka yi mini fashi!” ya yi ihu cikin harshen Spaniyanci, mara karin harshen Mexico.

Ya kalli kantin shan shayin, sannan ya yi shelar cewa ya bai wa mai karbar kudin kudin Peso 500, amman canjin Peso 200 kawai ya karba.

Da alama hankalin matashi mai karbar kudin ya tashi, kuma mutanen da ke layi sun mayar da hankalinsu kan kafafunsu ko kuma akwatin nuna kayan mako-lashe dangin fulawa da ke gabansu.

“Wannan abin mamaki ne!” mutumin ya ci gaba da ihu, yana mai juya akalar fushi da takaicinsa ga dukkan mutanen da ke cikin kantin shan shayin. “wannan laifi ne.”

Babu wanda ya kawo masa dauki. Kowa dai ya yi matukar mamakin cewa zai iya daga muryarsa da karfi haka.

Daga karshe, mai karbar kudin ya juya kuma ya shiga dakin baya. Mutmin ya yi huci na wani minti kafin ya bar gidan shan shayin cikin fushi.

Hakkin mallakar hoto
Lucas Vallecillos/Getty Images

Image caption

Ana yi wa Mexico City kallon daya daga cikin biranen kasashen Latin da suka fi kasancewa na zamani da masu yawan mutane daban-daban

Da zaran ya fice, mai karbar kudin ya dawo ya yi murmushi ga abokin hulda na gaba kuma ya ci gaba da sayar wa mutane abubuwa kamar yadda ya saba.

Ban san daga ina wannan mutumin ya fito ba, amman a karara take cewa ba daga Mexico yake ba, ko kuma wani wuri da ke kusa da Mexico.

Zai yi wuya ka ga dan Mexico ya fice daga hayyacinsa ta hanyar fushi sai dai in ya sha barasar mai yawa.

Wannan ya kasance ne saboda abu biyu ne ba in da za su kai ka a Mexico: nuna fushi a bainar jama’a da kuma fito-na-fito.

Tun suna yara, ake koyawa ‘yan Mexico kada su rinka nuna fushi.

Wata karin maganar Mexico na cewa ‘El que se enoja pierde’ ma;ana tana nufin: ‘wanda ya ba ta rai, zai yi asara.’

Hakkin mallakar hoto
Tony Anderson/Getty Images

Image caption

Wata karin maganar Mexico na cewa ‘El que se enoja pierde’ ma;ana tana nufin ‘wanda ya bata rai, zai yi asara.’

“An koya mana cewa muna bukatar kasancewa cikin nitsuwa a ko wane hali,” in ji Eleazar Silvestre.

Kuma an fi daukar wannan shawarar da muhimmanci a tsakiyar kasar ciki har da Mexico City wadda ake yi wa kallon daya daga cikin biranen kasashen Latin da ya fi kasancewa na zamani da kuma hada mutane daga wurare daban-daban.

Al’adar mutane a birnin Mexico City na kunshe da girmamawa a bainar jama’a wanda ban taba ganin irinta ba a sauran biranen da suka kai shi.

Tabbas, ya kamata tashin hankali ya yi yawa duba yadda kimanin mutum miliyan 25 ke yawo a birnin a ko wace ranar.

Amman a nan wani irin hatsaniya mai tsari da ya dogara ga gaisuwa da kuma tsabar hakuri.

Abin da ya faru a Afirka makon jiya

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

_99111861_nigeria_reuters
A ranar Talata ne wata mata ta dauki hoton kanta lokacin da mata suka yi zanga-zanga kan bukatar a karfafa musu gwiwa ta hanyar sana’o’i a birnin Abuja da ke Najeriya

_99111867_02_congo_afp


A ranar Laraba ne Fifi Loukoula na Congo-Brazzaville ya samu kai wa zagaye na gaba a gasar daga karfe ta duniya da ake yi a Mexico
_99132020_70c493e4-6839-463e-9dd9-e5fcd44e838e


A ranar Talata ne ‘yar kwallon hannu ta Kamaru Vanessa Djiepmou ta yi nasara a Leipzig da ke kasar Jamus
_99111865_senegal_afp


A ranar Alhamis ne wata ‘yar Senegal take rawa lokacin bikin bude sabon filin jirgin sama a babban birnin kasar Dakar
_99113142_05_sierraleone_afp


A ranar Laraba ne aka daukin hoton mawaki dan kasar Saliyo Janka Nabay a dakin wake-wake na Le Libert a birnin Rennes da ke Faransa
_99113625_06_algeriaafp5976


A ranar Alhamis ne mutane suka leko kallon shugaban Faransa Emmanuel Macron
_99113626_07_algeriaafp7976


Emmanuel Macron ya kai ziyara karon farko yankin da suke neman ‘yancin kai daga Faransa
_99113312_08_tunisia_reuters


A ranar Alhamis ne wadansu masu zanga-zanga suka kona tutar Amurka a Tunisiya
_99113314_09_athens_epa


A ranar Asabar ne ‘yan ci rani suka yi zanga-zanga a kan rahoton da aka samu na sayar da su a matsatin bayi a kasar Libya
_99113628_10_nigerai_af-2976


A ranar Talata ne aka dauki hoton wata ‘yar Najeriya bayan an dawo da ita gida a kokari da take na tsallakawa kasar Turai ta tsallakawa ta Libya
_99113317_11_southsudan_afp2


A ranar Talata ne wadansu yara suke zana hoton Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir a babban birnin kasar Juba
_99113491_12_zim_afp


A ranar Litinin ne aka saka hoton Emmerson Mnangagwa a gidan gwamnatin Zimbabwe, bayan kwana 10 da rantsar da shi a matsayin shugaban kasa
_99113493_13_congoafp2


A ranar Lahadi ne wani yaro yake kewayawa a cikin babban dakin fadar Mobutu Sese Seko tsohon Shugaban Zaire., inda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo
_99113495_14_supermoon_epa


A ranar Lahadi ne farin wata ya haskaka wani tsauni a Afirka ta Kudu
_99113497_15_tanzania_afp


A ranar Asabar ne wata take duba wayarta a makon tallan kayan kawa na Swahili da aka yi a Dar es Salaam babban birnin Tanzaniya
_99113881_16_tanzania5afp


A ranar Asabar ne aka yi makon tallan kayan kawa na shekara-shekara da ake yi Dar es Salaam, babban birnin Tanzaniya
_99113623_17_tanzania4afp


Wasu maza masu tallan kayan kawa lokacin a lokacin makon kayan ado na Swahili a birnin Dar es Salaam
_99113880_afpqueen


Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba

Ronaldo ya ce babu dan kwallon da ya fi shi a tarihi


Ronaldo ya lashe gasar Ballon d'Or karo na biyarHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ronaldo ya lashe gasar Ballon d’Or karo na biyar a bana

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce shi ne “fitaccen dan kwallo a tarihi”, bayan da ya lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya, wato Ballon d’Or karo na biyar.

Ronaldo ya lashe kyautar karo na biyar jere, inda ya yi kankankan da dan kwallon Barcelona Lionel Messi, ya kuma ce bai yi amannar cewa akwai wani dan wasa da ya fi shi ba.

“Babu dan wasa sama da ni. Ina buga tamaula sosai, ina da sauri, ina da karfi, ina buga kwallo da kai, na ci kwallaye, na taimaka an ci, akwai mutanen da suka fi son Neymar ko Messi, amma na fada babu wanda yake da irin wadannan abubuwan fiye da ni,” in ji dan kwallon.

Ya kara da cewa,” Babu wanda ya lashe kyautuka iri daban-daban kamar ni. Ba ina magana a kan kyautar Ballon d’Or kawai ba ne.”

Karanta wadansu karin labarai:

Ana tuhumar mata 24 da laifin sanya wando a Sudan


Sudanese women in KhartoumHakkin mallakar hoto
Getty Images

An gurfanar da mata 24 bisa tuhumarsu da nuna rashin da’a bayan sun sanya wanduna a wani taron fati a kusa da birnin Khartoum na kasar Sudan.

‘Yan sanda sun kai sameme ne yayin taron fatin a ranar Laraba.

Matan da ake tuhuma za su iya fuskantar hukuncin bulala 40 da kuma tara.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce dubban mata ne ake wa bulala duk shekara a kasar bayan an same su da laifin rashin kamun kai.

Har ila yau sun ce dokar hana mata sanya wando da kuma guntun siket tana shafar Kiristocin kasar wadanda su ne tsiraru.

Galibin al’ummar Sudan Musulmi ne kuma mata a kasar suna sanya dogayen tufafi ne bisa al’ada.

Karanta wadansu karin labarai:

Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassan Najeriya daban-daban a makon jiya.

 

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yayin da ya gana da shugabannin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yayin da ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP a Abuja ranar Talata
Wani dan Najeriya, wanda yake cikin mutum 400 da aka dawo da su daga kasar Libya a kokarinsu na zuwa nahiyar Turai yin ci rani, ya koma wurin iyalansa a jihar Edo ranar Alhamis
Wani dan Najeriya, wanda yake cikin mutum 400 da aka dawo da su daga kasar Libya a kokarinsu na zuwa nahiyar Turai yin ci rani, ya koma wurin iyalansa a jihar Edo ranar Alhamis
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da ya kai ziyara fadar Sarkin Biu bayan wani harin kunar bakin waken da aka kai kasuwar Biu a makon jiya
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da ya kai ziyara fadar Sarkin Biu bayan wani harin kunar bakin waken da aka kai kasuwar Biu a makon jiya
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da ya halarci addu'o'in musamman da aka yi don fatan Allah Ya kawo Shugaba Muhammadu Buhari lafiya, shugaban ya kai ziyarar kwana biyu jihar ne a ranar Laraba
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da ya halarci addu’o’in musamman da aka yi don fatan Allah Ya kawo Shugaba Muhammadu Buhari lafiya, shugaban ya kai ziyarar kwana biyu jihar ne a ranar Laraba
Shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jami'an gwamnatin jihar da kuma al'ummar jihar
Shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jami’an gwamnatin jihar da kuma al’ummar jihar
Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba
Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba
Shugaban Riko na jam'iyyar PDP Ahmad Mohammed Makarfi yayin babban taron jam'iyyar wanda a yi a Abuja ranar Asabar
Shugaban Riko na jam’iyyar PDP Ahmad Mohammed Makarfi yayin babban taron jam’iyyar wanda a yi a Abuja ranar Asabar
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yayin da ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda jam'iyyar take gudanar da babban taronta na kasa a ranar Asabar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yayin da ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda jam’iyyar take gudanar da babban taronta na kasa a ranar Asabar.
Matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, bayan ta halarci zaman wata babbar kotu da ke Abuja ranar Alhamis
Matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, bayan ta halarci zaman wata babbar kotu da ke Abuja ranar Alhamis

Yadda za a kauce wa rubuta mummunan sakon i-mail


emailHakkin mallakar hoto
Getty Images

Daga Alina Dizik

5 ga Satumbar 2017

A makonni kadan da suka gabata, ya haifar da rudani a lokacin da ta aike da sakon Twitter, ta zabi yin amfani da cin zarafin wani cikin ruwan sanyi don kaskantar da shi a wajen aiki ta hanyar -i-mail: ta hanyar amfani da jimla sassauka “dangane da sakon i-mail dina da ya gabata.”

Tattare da dukunkunannen sakon cin mutunci, marubuciya , kuma mai talllata haja da ke birnin Washington DC ta umarci wadanda ke tare da ita ( a shafin sadarwa) da su baza sakonninsu.

Sakamakon dai ya zama mabudi, inda sakon ya bazu a tsakanin daruruwan mutane, wadan suka yi ta yada wannnan sako marasa cutarwa a sakonnin i-mail din in an kwata furta shi da ce-ce-ku-cen baka a dukunkune.

Sai dai, muna tura munanan kalamai a sakonnin i-mail dinmu cikin rashin sani.

Sakon i-mail wajen dasa bama-bamai (tayar da hankali) ne, saboda ba ka san yadda mutane za su mayar da martani ba.

Idan ka aike da sakon i-mail da kyajkkyawar manufa har ya haifar da mummunan martini, kana iya zama abin zargi kan kuskuren da kee bayyane karara.

Tun daga kan “kamar yadda ka sani” zuwa “a taimake ni da shawara, dimbin martini shafin twitter na nuni da cewa musayar sakonnin i-mail sun zama takaddamar ce-ce-ku-cen zamantakewa, inda amfani da munnunar kalma bisa kuskure a lokacin da bai dace ba, cikin suaki zai iya harzukawa ko fusata mutane.

Bibiyar rubutu na wani lokaci

Daukacinmu muna isar da ma’ana ta kai tsaye, sabanin kimar kalmomi da yanayin furucinsu tare da manufar sakon i-mail dinmu.

Hatta tsawon rubutun i-mail da nahamunmu (ko rashin kimanta matsayin kalmomi) na nuni da wani abu kan tsarin tunaninmu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sai dai lamarrin na da wahala a gano yadda yadda muka tarkato su zuwa ga wasu.

A kai-a kai mukan latsa maballin aikewar sako (send) ba tare da dan dakatawa mun yi has ashen yadda za fasssara sakon a wajen wanda ya isa gare shi/ita.

Ba mu cika tambayar kanmu ba: na yi bayani karara, ko ba za a fahimce ni ba?

“Mun natsu da cewa a irin wannan kafar (aikewa da sako) ba ma bnukatar tuhumar kanmu: shin na yi bayani karara?

Ko za a yi mini mummunar fahimta?” a cewar Naomi Baron, Farfesar nazarin harsuna a Jami’ar Amurka ta Washington DC , kuma mrubuciyar kalmomin allon kallo (Words on the Screen): makomar karatu a duniyar kwamfuta.

Bayan an aike da sako, ta kara da cewa, “mutane da dama za su yi maka hukunci (kan manufa ko ma’ana).”

Tabbatar da gaskiyar lamari

A ‘yan shekarun nan, i-mail na kara zama hanyar sadarwa mafgi inganci, musamman saboda kafar isar da sako a kan kari kamar ‘Slack.’

Matasan ma’aikata yanzu suna da tabbacin cewa “i-mail ta tsofaffin mutane ce,” a cewar Baron. “Irin wannan dabi’a tna sauya kasurar nagartar yadda i-mail ta zama,” in ji ta.

Sai dai kauce wa tsarin al’ada na rubuta jimlolin sakon i-mail da aka saba da shi zai nuna cewa kana da karancin ilimi, a cewar Madhumita Lahiri, Farfesan Ingilishi sa Jami’ar Michigan da ke Ann Arbor, wanda ya yi aiki a Indiya da Afirka ta Kudu da Birtaniya kafin ya koma Amurka da zama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Don kauce wa zama mutumin da koma-bya, kalmomin irin su “zuwa ga” ko “ina fatan kana/kina cikin koshin lafiya” na da kyau a fara sakon i-mail da sulkdon taimaka wa mai karu ya samu saukin fahimtar abin da kake rubuto masa, a cewar Lahiri.

“Akwai hanya mafi dacewa wajen farawa da karkarewa da ke nuni da cewa ka san abin da kake yi.”

Kauce wa nuna rauni

Ko da yake kana son nuna kwarewa wajeen amfani da i-mail, al’amarin d ake nuna kimar mutuntakarka da haskaka kyakkyawar manufarka, a cewar Alex Moore, abokin hadin gwiwar turakar inganta ayyukan i-mail na Bloomerang a San Francisco.

Matasan ma’aikata suna da tabbacin cewa sakon i-mail na tsofaffin mutane ne.’

Kamar yaddda yake kunshe a binciken Booomerang na shekarar 2016 dangane da kamala i-mail, inda aka tattara bayanai kan sakonni 350,00, daukacin wadanda suka kasance managartan sakonni da munana, an gano cewa an samu martini da ya hauhawa kan sakonnin i-mail din da kashi 10 zuwa 15 cikin 100 wadanda suka fi zama tsakatsaki (‘yan ba ruwanmu).

“Ba ka son tsananta zama mai kyakkayawan sako ko mafi munin sako, amma dai mutane za su mayar da martani da abin da cikin zukatansu a rubuce,” inji Moore

A yi cikin sauki

A cewar binciken Boomerang, sakon i-mail da aka yi cikin sassaukan kalamai yana samun kyakkyawar amsa.

Binciken da kamfanin ya gudanar ya bayyana cewa i-mail din da aka rubuta a daga mai karatu a matakin aji na uku yana samun martini da kashi 53 cikin 100 in an kwatanta da kashi 39 cikin 100 na mai rubutun da yake a matakin karatun jami’a, da kashi 46 cikin 100 na matakin share fagen koyon karatu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ci gaba da amfani da sassaukan kalamai zai taimaka wajen kauce wa mummunar fahimta da aka dora a ma’aunin al’ada.

Za ka dauka cewa kana kyautatawa da sarkakiyyar kalamanta, amma a hakikanin gaskiya ka karke da nuna wasu kalamai da ba ssu dace ba, a wajen wani sashe na wannan duniya, kamar yadda Lahiri ya yi gargadi.

A Birtaniya, ta ce, rubuta cewa “abin takaicin shi ne…” ko “na yi nadamar..” an daukesu kalaman mutuntawa da kyautatawa, amma za su iya harzuka masu karatu a wani wurrin daban.

Alal misali a Amurka, “Lamari ne mafi sauki a yi dimbin godiya,” inji ta. “kalamai irin su ‘ina tsoron’ za su iya zama manuniyar mummunan tunani sabanin kyautatawar a Amurka kawai.”

A lura da kyau kan sarkakiyar alamomin rubutu

Ra’ayoyi sun bambanta in an yi la’akari wajen sanya alamar motsin rai da digge-dige da manyan bakake, da kuma abin da amfani da su ke nuni da shi ga wanda aka aika wa a sakon i-mail.

Yayin d amatasa ke zafafga kalaman sakonnin i-mail dinsu da alamomin motsin rai don nuna nagartar abota, tsofaffin ma’aikata kuwa suna amfani da su ne a matsayin takatsantsan da takaita kalamai.

A wajen masu shekar ashirin da doriya “alamar motsin rain a nufin kai aboki ne nagari, yayin da kwanan wata ke nuni da cewa da gaske kake yi,” inji Lahiri.

Dige-dige na da rudarwa, inda suke nuni da karshen jimla ga tsofaffin mutane, amma suna nuni da mummunar manufa ga matasa.

Daukacin kalmomin da aka fara da manyan baki a sakon i-mail na nuni da fushi a wajen wasu, sai dai bah aka lamarin yake ba , a wajen tsofaffin mutane, a cewar Lahiri.

Duk mukan yi ishara da mabambanciyar fahimta da salo-salon harshe a rubutunmu.

Kuma fassara sakon i-mail kan bambanta a tsakanin jinsi. A binciken da ta gudanar, ta nan ne ta gano cewa matan da ba sa amfani da alamar motsin rai, suna maimaita haruffa (bakake- tooo ko zooo) ko sauran alamun da ke nunin muhimmanci sosuwar rai a i-mail dinsu wadanda akan fassara a amtsayin bacin rai a wajen wwasu da sakon ya isa gare su..

Sai dai mazan da ke aikewa da sakonnin i-mail kai tsaye ba tare da nuna sosuwar rai ba ko kadan ba haka suke kasan cewa ba, kamar yadda ta gano.

Sannan maza sukan aike da takaitaccen sakon i-mail, wanda a mafi yawan lokuta yake kunshe da barkwanci, wanda idan ya isa ga masu karanta sakon i-mail din ba su cika fahimtarsa ba, kamar yadda yadda Tannen ta ankarar.

“A yi takatsantsan kana bin da irin wadannan sakonni ke n8uni a kanka da yaddda za a fassara shi,” in ji ta.

Juyin furuci

Duk da cewa yana da matukar alfanu a fara rubbuta ssakon i-mail da nuna kyautatawa cikin kwarewa, za ka iya bin kyakkyawan tsarin da aka sani yayin da kake kulla alaka, har ka saba da wani.

Wata dabarar da Tannanen ta bijirro da ita ita ce kwaikwayon kalaman mutumin da akek aike wa sakon i-mail din.

Idan har yanzu kana cikin damuwa kan yadda ake fassara sakonnni i-mail dinka na hada-hadar kasuwanci, to kirrkirarriyar fasaha za ta taimaka a nan.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Amfani da maballan shafukan sadarwar intanet da suka hada da martanin Booomerang da bibiyar kalamai na Watson da ke IBM za ssu tiamaka wajen warware boyayyar ma’anar d ake kudundunee a sakonka ko na wani daban.

“Daukacinmu muna nuni da ambambantan tsarin tunani da sarrafa harshe a rubutunmu,” a cewar Rama Akkiraju, wani Injiniya a IBM, a bangaren Watson da ke reshensu na San Jose a California.

Irin wannan kirkirariyar basira kan bibiyi komai tun daga kan zabar kalma da tsawo da ka’idojin rubutun nakala don nuna maka cewa kai mai kambama kai ne ko mai kyakkyawar mu’amala ko kwarin gwiwa.

Yi tunanin kammalawarka

Hanyar da ta fi dacewa a kammala rubuttun i-mail ita ce nuna kyakkyawan zato da godiya, a cewar Boomerang Moore.

Hanya mafi kyawu ta kammala rubutun sakon i-mail, ita ce ta nuna karamci, a cewar Boomerang’s Moore.

Kammalawa na iya kasancewa da “godiya har a gaba” nkamar yadda yake kunshe a sakamakon binciken da Boomerang ya gudanar da ya tabbatar da amincewa kasha 65 cikin 100.

Sai dai tsanantawa gme da amrtani, alal misali “kada a yi sako-sako wajen kira” zai zo a matsayin kaskantarwa fiye da taimakawa, a cewar Lahiri.

“Tabbas zazzafan kalami ne aka jero a dukunkune,” saboda zai sa mai karatu ya zurfafa tunani kan tasirin martanin su, a cewarta.

Duk wani abin da aka rubuta yana tattare da hadarin yi masa mummunar fasssara, don haka da zarar ka aike da martini cikin hanzari, sai ka sake bibiyarsa, ta yadda ba za ka fada tarkon wadanda ake ganin a matsayin masu harzuka cikin fushi.

Sai dai idan kawai abin da kake bukata ke nan.

Birnin Kudus: An tarwatsa masu zanga-zanga a Lebanon


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar a birnin Beirut

An yi arangama yayin wata zanga-zangar adawa da matakin Trump kan birnin Kudus a gaban ofishin jakadan Amurka da ke birnin Beirut na kasar Lebanon.

A makon jiya ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila da kuma mayar da ofishin jakadancin kasar zuwa can.

Yayin zanga-zangar jami’an tsaron Lebanon sun rika watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi a arewacin birnin Beirut.

A daren ranar Asabar ne Kungiyar Kasashen Larabawa ta yi Allah-wadai da matakin Shugaba Trump.

Kungiyar ta ce daga yanzu bai kamata a dogara ga Amurka wajen samar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ba.

Masu zanga-zangar sun rika jefa da duwatsu da cinna wuta a kan tituna a kusa da ofishin jakadancin da ke unguwar Awkar.

Wadansu kafafen yada labarai sun ce masu zanga-zangar sun yi kokarin kutsa kai cikin ofishin jakadancin.

Masu zangar-zangar wadanda suke sanye da bakaken kaya sun rika rera wakokin Allah-wadai da Shugaba Trump.

Akwai dubban Falasdinawa ‘yan gudun hijira da ke zaune a kasar Lebanon.

Tun bayan da Shugaba Trump ya sanar da daukar matakin ne aka rika samun zanga-zangar adawa da matakin a birnin Kudus da kuma sauran biranen duniya.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugabannin duniya sun yi wa Trump kashedi kan Kudus

An bukaci duniya ta amince da kafa kasar Falasdin


Middle EastHakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Rikici ya barke a garin Nablus da ke Gabar Yamma da Jordan ranar Asabar

Ministocin harkokin waje ashirin da biyu da ke wakiltar kasashen Larabawa sun nemi Amurka ta janye matakin da ta dauka na daukar Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawan ta ce shawarar amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, tana cike da hatsari.

Matakin dai ya kawo karshen kasancewar Amurka ‘yar ba-ruwanmu a daya daga cikin batutuwa mafi zafi a Gabas ta Tsakiya.

Ministocin wajen kasashen Larabawa a yanzu sun ce hakan na nufin ba a iya dogaro da Amurka a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya a yankin ba.

Sanarwar kasashen 22, wadda ta kunshi manyan kawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya, ta zo ne bayan hargitsi a kwana na uku da jerin zanga-zanga a Gabar Yamma da kuma Zirin Gaza.

A wata sanarwa bayan wani taron gaggawa a birnin Alkahira, ministocin sun ce matakini, keta dokar kasashen duniya ce kuma yana barazanar tsunduma Gabas ta Tsakiya cikin rikici.

Sun kuma yi kira ga kasashen duniya su amince da kasar Falasdin da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta.

Ministan wajen Lebanon, Gebran Bassil ya ma yi kira ga kasashen Larabawa su yi tunanin kakaba wa Amurka takunkuman karya tattalin arziki don hana ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Kudus daga Tel Aviv.

Gasar Hikayata: Saurari labarin 'Zawarcina'


A wannan makon Sashen Hausa na BBC zai ci gaba da kawo maku karatun labaran da suka lashe gasar Hikayata ta 2017.

An karrama matan da suka ciri tuta a gasar yayin wani biki a Abuja, babban birnin Najeriya a cikin watan jiya.

Tafe muke da labarin da ya zo na biyu, wato “Zawarcina”, kamar yadda za ku ji daga bakin wadda ta rubuta shi, Balkisu Sani Makaranta, idan kuka latsa alamar lasifikar da ke jikin hotonta da ke sama.

Karanta wadansu karin labarai

Kasar UAE na shirin fara noma abinci a duniyar Mars


Artist's impression of UAE's Mars domesHakkin mallakar hoto
Dubai Media Office

Image caption

Yanzu kasar tana da wani babban buri – wato burin shuka bishiyoyin kwakwa da kuma ganyen latas a duniyar Mars

Wani abu da za a iya zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da shi shi ne rashin kyakkyawan tsarin tunkarar gaba.

Da farko sun bayyana wani shirin da za su yi a duniyar Mars. Sannan kuma hakan ya yi arashi da burin karbe iko da duniyar.

Yanzu kasar tana da wani babban buri – wato burin shuka bishiyoyin kwakwa da kuma ganyen latas a duniyar Mars.

Bangaren binciken sararin samaniya ya kasance babban bangare ne a kasar, inda ake shirya manyan taruka kuma ake gayyatar manyan masana kimiyya kamar Al Worden, wanda ya taba zuwa duniyar wata a cikin kumbo Apollo 15.

Amma gabanin na’urar bincike ta UAE ta tashi zuwa duniyar Mars daga Japan a shekarar 2020, UAE din na aikin hadin gwiwa da babbar masana’anta ta Mitsubishi, inda a yanzu ta sanar da shirinta na fara aikin noma a can.

Wani babban jami’i na hukumar kula da sararin samaniyar kasar Rashid Al Zaabi, ya ce: “Akwai kamanceceniya sosai tsakanin duniyar Mars da hamada. Yanayin filin duniyar da kasar wajen iri daya ne.”

Don haka UAE ta yanke shawarar zuba kudi a wasu ayyukan bincike biyu, noma bishiyoyin kwakwa da tumatur a duniyar Mars.

Mr Al Zaabi ya ce: “Ai idan muka je can dole muna bukatar cin abinci.”

Hakkin mallakar hoto
Dubai Media Office

Image caption

A yanzu kuwa UAE na aiki ne wajen bunkasa fannonin kimiyya da fasahar zamani

An zabi shuka bishiyar kwakwa ne saboda yadda alamarta ke da alaka da yankin, sauran itatuwan kuma saboda masana kimiyya sun yarda cewa za su iya girma a duniyar Mars.

Duk da cewa wannan abun zai zama kamar tatsuniya, to akwai muhimman dalilan tattalin arziki da suka sa za mu yi.

Kasar UAE, musamman ma Dubai da Abu Dhabi, suna kokarin habaka tattalin arziki a shirye-shiryensu na kawo karshen zamanin amfani da kasa.

Kasar ta fara ne da gagarumin fadada bangaren yawon bude ido da harkokin jiragen sama, da kuma ayyukan fasaha da ke tattare da su.

A yanzu kuwa UAE na aiki ne wajen bunkasa fannonin kimiyya da fasahar zamani.

Shugaban aikin nomar da za a yi a duniyar Mars Omran Sharaf, ya ce: “Akwai matasa miliyan 100 da ke yankin kasashen Larabwa.

Hakkin mallakar hoto
MBRSC

Image caption

Kasar UAE dai ta sanya jarin fiye da dala biliyan 5.4 a bangaren hukumar sararin samaniyarta

“Muna so su taka rawa nan gaba wajen kai yankin matakin ci gaba.

(Yawan al’ummar UAE dai ya kai miliyan tara, wadanda daga cikinsu miliyan 1.4 ne kawai ‘yan asalin kasar.)

Ya kara da cewa: “Ana magana ne a kan kirkirar wani yanayi bayan an daina dogaro, yanayi na dogaro da ilimi da kuma yanayin kirkirar wasu hanyoyin inganta tattalin arziki. Don haka yana da muhimmanci a samar da cibiyar kimiyya.

“Mun kirkiri injiniyoyi, amma ba masana kimiyya sosai. Wannan harka ta duniyar Mars kuwa aikin kimiyya ne zalla.”

Kasar UAE dai ta sanya jarin fiye da dala biliyan 5.4 a bangaren hukumar sararin samaniyarta da suka hada da tauraron dan adam.

An kaddamar da wani gwaji na karshe da aka yi na bincike kan aikin da za a yi a duniyar Mars.

An samar da tauraron dan adam din binciken ta hanyar amfani da wata tawaga wadda ta hada zallar ‘yan kasar Daular Larabawa, kuma za ta nemo inda ruwa yake da kuma yanayin sararin samaniya, in ji hukumar binciken sararin samaniyar.

Hakkin mallakar hoto
Dubai Media Office

Image caption

The plan is that scientists and researchers will live in the sealed facilities for a year

Kasar UAE ta kuma fara aiki kan birnnin kimiyya a duniyar Mars, wata cibiya da za a sadaukar da ita don koyar da yadda za a mallaki duniyar ta Mars.

Jerin ayyukan da za a yi a wajen, ya kai murabba’i miliyan biyu da za a iya rayuwa da kuma wuraren bincike, zai taimaka wajen binciken abinci da ruwa da sauran abubuwan bukatu.

Wannan aiki na duniyar Mars da UAE ke yi ya sa ta zama daya daga cikin kasashe tara da ke kokarin gano yada za su shiga duniyar.

Mista Sharaf ya ce: “Hakan na nufin zuba jarinmu a fannin ilimi da kimiyya da dakunan gwaje-gwaje da jami’o’i, zai zama gagarumi.

Kuma a cewar matukin jirgin da ya taba zuwa duniyar wata a cikin Kumbo Apollo 15, Al Worden, abun yana kuma bukatar hadin kan kasashen duniya.

Ya ji dadin wannan buri na UAE, da kuma nasarar da aka samu zuwa yanzu.

Amma ya kara da cewa: “Sai dai kalubalen fasaha da za a samu zai yi wa kasa daya yawa.”

Hakkin mallakar hoto
Dubai Airshow

Image caption

Matukin jirgin da ya taba zuwa duniyar wata a cikin Kumbo Apollo 15, Al Worden, ya ce abun yana bukatar hadin kan kasashen duniya

Babban darakta janar na hukumar kula da sararin samaniya ta Mohammed Bin Rashid, Yousuf Hamad Al Shaibani, ya ce babban dalilin da ya sa za a yi amfani da sararin samaniya wajen yin wannan aiki, shi ne don a jawo hankalin kwararru na kasashen duniya don su zo su taka tasu rawar.

Ya ce: “Yin amfani da sararin samaniya don yin bikin da aka saba duk shekarar na taron sararin samaniya a wannan mako, babbar dama ce ta haduwa da manyan kamfanoni da cibiyoyin sararin samaniya na duniya, a kuma gina dangantaka mai inganci.”

Ko masu mulkin kasar UAE ma sun bayyana wannan abu da ake kokarin yi a matsayin wani abu gagarumin abu da ba kowa ke iya yi ba.

A dauka cewa komai ya tafi yada ake so, mataki na karshe shi ne wata tawagar mutane cikin jirgi za ta sauka a duniyar Mars nan da shekara 100.

Ba zai taba yiwuwa ba. Amma dai a kalla kasar ta samar da wata al’umma ta masana kimiyya a yankin kasashen Larabawa – wadda ta koyi yada za a shuka kayan marmari da kayan itatuwa da yawa a duniyar Mars.

PDP ta zabi Uche Secondus sabon shugabanta


PDP ConventionHakkin mallakar hoto
FACEBOOK/PDP

Image caption

‘Yan takara guda hudu ne aka bayyana cewa sun shiga zaben

An bayyana Uche Secondus a matsayin sabon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, a babban taron da aka tsawon daren Asabar ana kidaya kuri’u.

Da yake sanar da sakamakon zaben, shugaban kwamitin zabe, Mista Gabriel Suswam, ya ce Uche Secondus ya kayar da abokan takararsa uku bayan ya samu kuri’a 2000.

Duka-duka, mahalarta babban taron sun zabi sabbin mukamai guda 21 don jagorantar jam’iyyar PDP.

Kashi 70 na daliban arewa a jahilai suke gama makaranta – Masani


StudentsHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masanin ya bukaci kawar da cin hanci da rashawa a harkar ba da ilmi a Najeriya

Wani masani daga Jami’ar Alkalam a Najeriya ya bayyana fargaba kan karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar, a cewarsa kusan duk ‘yan arewa sun kwanta sun zuba ido “ilmi ya gyara kansa”.

Gogaggen malamin jami’ar wanda ya gudanar da bincike na kashin kansa a makarantu daban-daban cikin yankin ya ce ya yi matukar kaduwa da abin da idonsa ya gani.

A cewar Dr. Aliyu Muri: “to kuma abin kusan kullum sai kara ci gaba yake yi. Kamar ciwo ne, kullum ba a magance shi ba, yana kara hauhawa ne”.

“Ta kai (matsayin) yanzu yaranmu hakan nan suke gama karatu, wadanda suke gama firamare, su gama hakan nan, wadanda suke gama sakandare, su gama haka nan (ba tare da wani ilmi ba),” in ji shi.

Ya ce binciken da wata kungiya ta gudanar inda ta gano cewa kashi 70% na yaran da suke gama makarantu a arewa, suna gamawa jahilai, shi ne dugunzuma shi kuma ya yi masa kaimin gudanar da nasa bincike.

Dr. Muri ya ce ya ziyarci makarantu da dama a yankunan karkara da maraya, kuma akasari makarantun karkara da ya halarta ya gano matsanancin karanci na malaman da ke koyarwa.

“A karkara za ka iske akwai sakandaren da ke da malamai guda biyar kawai kuma ana koyar da kimiyya da fasaha. Babu malamin turanci ballantana a yi maganar lissafi.”

Ya ce ya ziyarci wata makaranta da ya shiga ajin karshe na sakandare, wadda da kyar aka iya samun wani yaro da ya tashi ya iya karanta kalmar “Allahu” da ke rubuce a kan allo.

“Kuma wadannan yaran, idan sun gama za a ce maka duk sun yi WAEC. Sun ci jarrabawarsu ta gama makaranta, sannan kuma irinsu ake kwasa a shigar da cikin manyan makarantunmu. Ina za mu sa kanmu?” Ya tambaya.

Dr. Aliyu Muri ya alakanta rashin kulawar da ake bai wa bangaren ilmi, da zama ummul aba’isin wannan matsala.

A cewarsa: “Za ka iske makaranta mai (dalibi) dubu biyar, dubu shida. Akwai wadda aka fada min tana da yaro dubu goma sha uku.

Ya yi tambayar ko yaya arewa za ta yi da kanta idan wadannan yara suka taso daga nan zuwa shekara, musammam idan ka yi la’akari da irin yawansu a kan tituna idan sun dawo bayan an tashe su?