Wariyar launin fata: An ba wa Sulley Muntari katin gargadi kan korafi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sulley Muntari ya fice daga fili yana nuna wa magoya bayan Cagliari: ”Ku duba launina kenan”

Dan wasan kungiyar Pescara ta Italiya Sulley Muntari ya fice daga fili domin nuna bacin ransa kan katin gargadi da alkalin wasa ya ba shi bayan da ya yi korafin cewa ana masa cin mutuncin wariyar launin fata.

Tsohon dan wasan tsakiya na Ghana mai shekara 32 ya bukaci alkalin wasa Daniele Minelli ya dakatar da wasan na ranar Lahadi na gasar Serie A wanda suke yi a gidan Cagliari.

Amma sai alkalin wasan ya ba shi katin gargadi a minti na 89 bisa laifin kawo rudu a wasan, lamarin da ya harzuka tsohon dan wasan na Portsmouth da Sunderland ya fice daga fili cikin fushi, yana nuna wa magoya bayan Cagliari hannunsa yana cewa: ”Wannan ne launi na.”

Kociyan Pescara Zdenek Zeman, wanda aka ci kungiyarsa 1-0, ya ce, dan wasan ya bukaci alkalin wasan da ya dau mataki a kai, amma sai ya ce shi bai gani ba bai kuma ji komai na cin mutuncin da danwasan ya yi korafi ba.

Kociyan ya ce Muntari ya yi dai dai amma da bai fice daga fili ba, domin za mu iya yin korafi amma ba mu da ikon yin hukuncin.

Muntari yana AC Milan lokacin da abokin wasansa a kungiyar Kevin-Prince Boateng ya fice daga fili saboda wakar warinyar launin fata da magoya bayan Pro Patria suka rika yi masa a watan Janairu na 2013.

Lamarin ya jawo korafi da nuna goyan bayan ga Boateng a shafukan sada zumunta a lokacin, har Fifa ma ta mara masa baya, amma ta ce bai dace ba da ya fice daga wasan.

Kungiyar Pescara ita ce ta karshen teburin Serie A kuma tuni ta riga ta fadi zuwa gasar rukuni na biyu na Italiya.

Boksin: Fury ya amince da kalubalantarsa da Joshua ya yi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tyson Fury ya ce yana son su dambata da Anthony Joshua, domin ‘yan kallon da ba a taba samun yawansu ba, su kashe kwarkwatar idanunsu

Tyson Fury ya amsa kalubalantarsa da zakaran damben boksin na ajin masu nauyi na duniya Anthony Joshua na Birtaniya, dan asalin Najeriya, ya yi na su gwabza bayan doke Wladimir Klitschko da zakaran ya yi ranar Asabar.

Joshua, wanda ya gama da tsohon zakaran, dan Ukrania a turmi na 11 a filin wasa na Wembley, nan take ya kalubalanci Fury wanda shi ma dan Birtaniya, wanda shi ma ya doke Klitschko da yawan maki a karawar da suka yi a watan Nuwamba na 2015.

Bayan nasarar ta ranar Asabar ne, Joshua ya tambaya, ”Fury ina kake ne?” Ya ce: ”Na san yana ta magana, to ina son in ba wa ‘yan kallo dubu 90 damar ganinmu.”

Fury, wanda bai kara wani dambe ba tun lokacin da ya doke Klitschko, ya amsa kalubalantar da Joshua ya yi masa inda ya ce : “Ba ri mu taka rawa.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan shi ne karo na biyar da ake doke Wladimir Klitschko a sana’arsa ta damben boksin

Yanzu dai ba a taba doke Joshua a damben da ya yi 19 ba. Kuma nasarar da dan damben dan asalin Najeriya mai shekara 27 a gaban yawan ‘yan kallo 90,000 da ba a taba samu ba a Birtaniya tun bayan yakin duniya a babban filin wasa na Wembley, ya kara hada kambin WBA a kan na IBF da yake rike da shi.

Shi ma Fury, mai shekara 28, ba a taba doke shi ba tun da ya fara damben boksin na kwararru, inda ya doke abokan karawarsa 18 a dambe 25.

Amma kuma ya saryar da kambinsa biyu na duniya, domin ya samu dama ya mayar da hankalinsa wajen maganin larurar kwakwalwa da ke damunsa, sannan a yanzu ba shi da lasisin yin dambe.

Tottenham ta ci gaba da bin Chelsea bayan doke Arsenal 2-0


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

A duk haduwarsu da Arsenal biyar a jere a Premier Harry Kane sai ya ci Arsenal, wadda ya taso daga kungiyar matasan ‘yan wasanta

Tottenham ta ci gaba da bin jagorar Premier Chelsea bayan da Dele Alli da Harry Kane suka zura kwallo biyu a ragar abokan hamayyarsu na arewacin Landan, Arsenal bayan hutun rabin lokaci.

Tottenham na bayan Chelsea da maki hudu yayin da ya rage wasa hudu a gama gasar, bayan da tun da farko Chelsean ta bi Everton gida ta doke ta 3-0.

Nasarar ta wasan na hamayya ta sa a karon farko tun kakar 1994-95 Tottenham za ta gama Premier a saman Arsenal.

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci masu masaukin bakin suka barar da damar kasancewa a gaba a wasan, inda Christian Eriksen da Dele Alli kowannensu ya barar da damar da ake ganin ruwa-ruwa za su ci.

Sai bayan da aka dawo daga hutun rabin lokacin ne a minti na 55 Alli ya ci kwallon wadda ita ce ta 21 da ya ciwa Tottenham a bana.

Dakika 146 tsakanin sai kuma Kane ya ci ta biyu da fanareti, bayan da Gabriel ya yi masa keta ya fadi a cikin da’irar Arsenal.

Kwallon da ta sa Kane ya zama kan gaba a ‘yan wasan Tottenham da suka ci Arsenal, inda yake da shida, yayin da Gareth Bale, da ya koma Real Madrid, yake da biyar.

Arsenal mai kwantan wasa daya ta ci gaba da zama ta shida a tebur, maki shida tsakaninta da ta hudu Manchester City wadda take da maki 66.

'Yan sanda sun kama Sule Lamido


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alhaji Sule Lamido ya na daya daga cikin jigajigan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya

‘Yan sanda a jihar Kano dake arewacin Najeriya sun kama tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.

Rahotanni sun ce an kama tsohon gwamnan ne bisa zargin ingiza magoya bayansa don su kawo tarnaki ga zaben kananan hukumomi a Jihar Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru ce ta shirya zaben kananan hukumomin da za a gudanar ranar daya ga watan Yuli.

An kama Sule Lamido ne a gidan shi dake Sharada, Kano da safiyar Lahadin nan.

Har yanzu dau hukumomin ‘yan sandan ba su fitar da sanarwa a hukumace ba game da dalilan da suka ka a ka kama tsohon gwamnan.

Alhaji Sule Lamido, yana daya daga cikin jigajigan ‘ya’yan babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, kuma a ‘yan kwanakin nan, ya yi ta sukar irin kamun ludayin gwamnatin kasar ta jam’iyyar APC.

Chelsea ta fara jin kanshin kofi bayan ta doke Everton 3-0


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Conte na murna da Cesar Azpilicueta bayan wasan, da ya kawo karshen karawarsu 11 ba tare da an ci su ba

Jagorar Premier Chelsea ta kara matsawa kusa da kofin sakamakon kwallo uku na bayan hutun rabin lokaci da ta zazzaga wa Everton a gidanta Goodison Park.

Chelsea ta yi jinkiri da kuma hakuri wajen neman kwallayen wadanda har sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 66 Pedro ya daga ragar masu gidan.

Bayan minti 11 da fara cin sai Cahill shi ma ya zura tasa kafin Willian shi ma ya ci tasa a minti na 86, bayan wata kwallo da Fabregas ya sanya masa.

Nasarar ta sa Chelsea ta kara tazarar da ke tsakaninta da ta biyu Tottenham wadda za ta kara da Arsenal, ita ma a ranar Lahadin, da maki bakwai, inda yanzu take da maki 81 a wasa 34.

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Pedro yana da hannu a kwallo hudu cikin takwas da Chelsea ta ci Everton a Premier bana

Hakan na nufin ko da Chelsea ta yi asarar maki uku a ragowar wasanninta hudu, za ta iya daukar kofin nata na biyu a shekara uku, ko da kuwa Tottenham ta ci dukkanin wasanninta.

Canjasar din da Manchester City ta yi a gidan Middlesbrough na nufin kungiyar ta Ronald Koeman (Everton), a matsayi na 7, tazarar maki 8 ne tsakaninta da rukunin hudun farko, yayin da ya rage wasa uku a gama gasar.

Wasan shi ne babban fatan Tottenham na ganin an ci Chelsea, domin Everton ce ake ganin tafi dukkanin sauran abokan karawarta hudu karfi, yayin da Chelsean za ta yi wasanni uku a gida.

Lissafin mai sauki ne ga Chelsea, domin yadda yake shi ne, idan ta ci karin wasa uku to shikenan za ta dauki kofin a karo na shida.

Kuma daga yadda kociyanta Conte da ‘yan wasansa suka rika murna bayan wasan na Everton, kai ka ce sun ma riga sun dauki kofin, kamar sun gama da Middlesbrough da West Brom da Watford da kuma Sunderland.

Idan kuma har Chelsean ta yi nasara doke Arsenal a wasan karshe na Kofin FA, ranar 27 ga watan Mayu, za a ce Conte ya yi gagarumar nasara kenan a kakarsa ta farko a Ingila.

Masu sana'o'i a birnin Kumasi


A ranar 6, ga watan Mayun shekarar 1957, kasar Ghana wacce a baya aka santa da cinikin zinare, ta samu ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya.

A bikin cika shekara 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, wani mai daukar hoto, Ricky Darko ya yi duba da garin da aka haife shi wato Kumasi, a kudancin kasar, don nuna ire-iren ayyukan da matasa suke da damar samu a lokacinsa.

Hakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Birnin kumasi da ke Ghana

A lokacin da Darko ke bikin cika shekaru 30 da haihuwarsa, ya kira samari sa’anninsa da su fito su dauki hotuna a wuraren da suke aiki.

Ya hadu da abokan nasa a ranakun da suke gudanar da aikinsu, inda ya tarar da kowanne yana da fannin da ya kware a sana’arsa, wanda yawanci sun gada ne daga wurin iyaye da kakanni.

Daga cikin kanikawan da suke aikin kere-kere, yawancin mazan suna aiki tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta, cikin zafin rana da ya kai maki 35 na ma’aunin Selsiyos.

Darko ya ce, yadda suke gudanar da rayuwarsu sai san barka.

ya ce, suna yin aikinsu da kwazo na tsawon sa’o’i a cikin yanayin zafi amma ba tare da yin korafi ba.

David yana daya daga cikin samarin da ya ci karo da su.

Ya zagaya cikin Kumasi yana yin ayyuka daban-daban tun daga kwashe bola zuwa kai ruwa gidaje.

David,mai kaya a KumasiHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

DavidYa zagaya cikin Kumasi yana yin ayyuka daban-daban

Kwame ya leko waje ta tagar motar da yake ciki mai launin azurfa, wacce ake aikin da ita a gidan attajiran da yake yi wa aiki.

A wannan ranar ne, zai dauki iyalansa don ziyartar abokai, sannan su wuce kasuwa su sayi kayan masarufi don amfanin yau-da-kullum.

Kwame na zaune a motarsaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Kwame ya leko waje ta tagar motar da yake ciki mai launin azurfa

Kumasi, GhanaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Ghana wacce a baya aka santa da cinikin zinare,

Nana Kwasi da ke zaune a kan Bonnet din motarsa, ya shaida wa Darko cewa yana biyan kudin balas na hayar motarsa a kan cedi 40 na kudin Ghana a kowacce rana.

Sannan ya zagaya cikin garin Kumasi, dan ya yi kokarin samun isasshen kudin da zai tallafa wa iyalansa.

Wani na tsaye kusa da motarsaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Nana Kwasi da ke zaune a kan Bonnet din motarsa,

Akwasi na tsugune a kusa da kofofin karfe da ya kera.

Garejinsa na kusa da gidaje, kuma yana aikin waldan kayayyaki daban-daban da ‘yan kasar Ghana ke amfani da su.

AkwasiHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Akwasi na tsugune a kusa da kofofin karfe da ya kera.

wani mai aikin waldaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Wani mai aikin walda

Francis na waldar kofaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Francis na aikin waldar karafuna

Francis yana aikin ne a matsayin mai sayar da kayayyakin cimaka, galibi ya fi sayar da alewa a kan titinan cikin gari da motoci suke yawan wucewa.

Ya ce, Suna gudanar da cikakkiyar rayuwarsu kuma duk lokacin da suka ganni suna min dariya, a matsayi na na wanda nake kokarin yin magana da harshen Twi (wani yare ne a harshen Aka, wanda yawancin ake magana da shi a kudancin Ghana).

Darko ya ce, ina jin harshen ba dadi, idan na cakuda shi da kalmomina.

FrancisHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Wani saurayi

Wadannan samarin ‘yan uwan juna ne ke zaune a kofar shagonsu, inda suke sayar da kayayyakin amfanin gida.

Yaw daga hagu, Poku a dama, suna gudanar da harkokin cinikinsu na tsawon sa’o’i 16 a rana.

Two men sit outside a stallHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Yaw (daga hagu), tare da Poku, suna zaune a shagonsu

A roadside hut in Kumasi, GhanaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Wasu kayayyaki a Kumasi.

Emmanuel na aiki dare da rana a matsayin mai gadin wasu kayayyaki a Kumasi.

A karshen mako ne kawai, yake samun sa’o’i uku, don ya zauna tare da iyalansa.

Emmanuel, mai gadiHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Emmanuel na aiki dare da rana a matsayin mai gadi

Michael na sayar da katin waya, a cikin wani dan akwati da aka kera da katako, da ruwan leda a cikin kula.

Michael, mai sai da katin wayaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Michael na sayar da katin waya

Dukkan wadannan hotunan mallakar Ricky Darko ne.

Harin Madina: Saudiya ta kama mutane 46


Image caption

A karshen azumin watan Ramadanan bara ne aka kai harin a Madina

Saudiya ta ce ta kama mutane arba’in da shida, bayan harin kunar bakin wake da a ka kai a birnin Madina bara.

Akasarin mutanen ‘yan kasar ta Saudiya ne, amma an ce akwai goma sha hudu ‘yan wasu kasashe da suma a ke tsare da su.

Saudiya ta ce mutanen, mambobin wata kungiyar ‘yan bindiga ce da ta kai harin, a inda a ka kashe jami’an tsaro hudu.

A lokacin da a ka kai harin, an dora alhakin shi ne a kan kungiyar IS.

Harin ya auku ne a watan Yulin bara, a karshen azumin watan Ramadana.

Ba dai a san lokacin da a ka yi kamen mutanen ba.

Swansea ta yi wa Man United fancale


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gylfi Sigurdsson ya ci wa Swansea kwallonsa ta farko tun watan Fabrairu

Swansea ta samu maki a fafutukar da take yi ta tsira a gasar Premier ba, yayin da kuma ta yi wa mai masaukinta Manchester United cikas kan neman shiga hudun farko da take yi, inda suka tashi 1-1.

Gylfi Sigurdsson ne da bugun tazara ya ci wa bakin kwallonsu a minti na 79, ya rama fanaretin da Wayne Rooney ya ci ana dab tafiya hutun rabin lokaci, wadda ‘yan Swansea suka yi korafi da cewa Marcus Rashford faduwa ya yi da gangan, ba keta aka yi masa ba.

Sakamakon ya sa yanzu maki biyu ne tsakanin Hull City ta 17 mai maki 34, da Swansea ta 18.

Man United ta cigaba da zama ta biyar, da maki 65 maki tsaya tsakaninta da abokiyar hamayyarta Man City ta shida da maki 66, wadda da ta yi canjaras 2-2 da Middlesbrough yau Lahadi.

Bayan makin da United ta yi asara a gidan nata ta kuma gamu da matsalar rasa karin ‘yan wasanta da suka ji rauni, inda a wannan karon ta rasa Eric Bailly da Luke Shaw, bayan daman ‘yan bayanta Phil Jones da Chris Smalling da Marcos Rojo suna jinya.

Na gargaɗi Jonathan kan makircin 'yan Arewa – David Mark


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mr Mark [daga dama] ya ce ya yi mamakin yadda Jonathan ya kasa gane makircin da ake shiryawa

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark ya ce ya gargadi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan irin makircin da ‘yan arewacin kasar ke shiryawa domin kayar da shi a zaben 2015.

Mr Mark, wanda ya bayyana hakan a littafin Against the Run of Play, wanda fitaccen mai sharhin nan na jaridar ThisDay Olusegun Adeniyi ya wallafa, ya ce da gangan jam’iyyar PDP, a karkashin Ahmad Adamu Mu’azu ta gaya wa Mr Jonathan cewa zai lashe zaben bisa dogaro da hasashe kan tsarin kada kuri’ar da ‘yan arewacin kasar za su yi.

A cewarsa, “Na tsinkayi faɗuwar sa [Jonathan] zaben kuma na nuna masa hakan, sannan na bayyana masa cewa hasashen da wasu mutane da ke kusa da shi suka yi kan tsarin kada kuri’ar da za a yi a Arewa ba daidai ba ne.”

“Na gane makircin da aka kitsa da kuma taron dangin da aka yi a Arewa domin ganin Jonathan bai cimma burinsa ba amma ba sarkin yawan ya fi sarkin karfi, domin wadanda ke kusa da shi na ganin babu yadda shugaban kasa da ke kan mulki, kuma a jam’iyyar PDP ya fadi a zabe,” in ji Mr Mark.

Tsohon shugaban majalisar ta dattawan Najeriya ya ce wasu mutane sun rika yaudarar Mr Jonathan suna gaya masa cewa ba zai sha kaye a zabe ba kuma mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo ya gane cewa yaudarar tsohon shugaban kasar ake yi “amma ban san irin tasirin da yake da shi a yakin neman zaben ba. Kuma har yanzu ian matukar mamakin yadda Jonathan ya kasa gane cewa ana yaudararsa har sai da lokaci ya kure”.

Mr Mark ya ce Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience ne suka sa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal bijire musu saboda wulakacin da suka rika yi masa.

A cewarsa, sun yi zaton shi da Tambuwal na son yin takarar shugabancin kasar a shekarar 2015, amma “na gaya wa Jonathan ni da shi cewa duk wadanda ke ba shi irin wadannan labaran karya suke yi.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau hudu Mr Mark ya zama dan majalisar dattawa

Zan faɗi gaskiya abin da ya faru

Shi dai tsohon shugaban na Najeriya ya ce tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ne suka sa ya sha kaye a zaben 2015.

Mawallafin littafin ya ambato Mr Jonathan na cewa Shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama da jami’an gwamnatinsa sun bayyana masa ƙarara cewa suna son sauyin gwamnati a Najeriya kuma za su iya yin komai domin cimma hakan.

A cikin gida kuma, tsohon shugaban ya ce shugaban hukumar zabe na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya yi masa abin da bai yi tsammani ba, saboda har yanzu nan ya kasa fahimtar abin da ya sa Jegan ya nace cewar ya shirya wa yin zabe lokacin da kashi 40% bisa dari na masu zabe ba su karbi katinsu na zabe ba.

Ya ce ya gana da shugaban hukumar zabe ya bayyana masa damuwarsa kan yi zaben a watan Fabrairun 2015, amma ya kafe cewar ya shirya wa zaben domin Amurkawa sun ingiza shi abin da ba za taba yi a kasarsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Goodluck Jonathan ne shugaba mai ci na farko da ya fadi zabe a Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya musanta wannan zargi, yana mai cewa zaben da aka yi shugaba Muhammadu Buhari zabi ne da nuna abin da ‘yan Najeriya ke so.

Shi ma tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya ya musanta hakan, inda ya ce na’urar tantance zaben da aka yi amfani da ita a 2015 ta hana kowanne irin magudi.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya ce zai buga littafin da zai fayyace gaskiyar abin da ya sanya shi faduwa zaben shekarar 2015.

Bayan ƙara kyau, ko dashen mama na da wata illa?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akan yi amfani da roba ko balan-balan ɗin silicon don mayar da tsohuwa yarinya

Dashen mama, nau’in kwalliyar mata ce ta cikin jiki da ya fara samun wajen zama a ƙasashe kamar Nijeriya, don kuwa su ma ba sa so a ga tsufansu.

Mata kan yi wannan kwalliya ce ta yadda za a riƙa ganinsu gwaɗas da ƙuruciya, bayan ƙara burgewa da jan hankali.

Tun tale-tale, mata sun shahara wajen son gyaran jiki, a cancanɗa gayu don kyaun gani da kuma fita kunya.

A baya Turawa aka sani da kwalliyar dashen mama, kafin yanzu da take ƙara bazuwa a duniya.

Matan Nijeriya, ‘yan ƙwalisa ne masu son su jera da zamani, ga kuma son tsere sa’a, kuma ba sa son a ga tsufansu.

Shin yaya ake dashen mama?

Wani ƙwararren likitan fida, Dr. Sa’ad Idris ya ce fiɗa ake yi nono, a tsarga shi don yi masa ƙari ko ciko.

Ana amfani da wani abu mai kama da balan-balan, inda ake sanya ta daidai da surar maman.

Shi wannan abin mai kama da balan-balan ana kiransa Silicon da kuma wani sinadari mai alaƙa da gishiri da ake zuba shi a cikin balan-balan ɗin silicon.

Akan yanka ƙoramu ko jijiyoyin da suka haɗa kan nono da sauran gangar jiki.

Ko mai dashen mama na iya shayarwa?

Dr. Sa’ad Idris ya ce binciken da aka yi, ya nuna cewa likitoci ba su cika ba wa wadda ta yi dashen mama shawarar ta shayar da jariri ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mata kan kashe maƙudan kuɗi don ganin sun yi wannan kwalliya ta burgewa

“Yanka ƙoramun nono da aka yi, kan sa ruwan nono zai janye.”

Haka zalika, sinadaran da aka zuba a cikin balan-balan ɗin silicon a wasu lokuta ka iya tsiyaya, kuma idan jariri ya sha, suna iya illata shi.

Ko dashen mama na da wata illa?

Dr. Sa’ad Idris ya ce dashen mama kamar kowacce irin tiyata, ta jiɓanci yanka jikin mutum da kuma ba da maganin kashe kaifi.

A cewar likita hakan na da matsaloli, don kuwa wasu idan suka kwanta, ba lallai ne su sake tashi ba, idan an gamu da matsala.

Haka kuma “akan iya samun jini ya tattaru a wurin da aka yanka, ballantana inda aka sanya balan-balan ɗin silicon.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu irin wannan dashen mama ya bazu a duniya

Ko yaushe mace za tai ta jin ciwo ga mamanta bayan an yi dashe.

“Maimakon ma a gyara…(ƙirjin mace ya zama cas a tsaye) ƙila ɗaya ya fashe,” in ji likita.

A cewarsa (fatar) nonon ka iya canza launi, ko kuma girmansa ya ragu.

Sai dai a iya sanina da kuma binciken da muka yi, “ban ga inda aka alaƙanta dashen mama da cutar sankara ba, in Dr. Sa’ad Idris.”

Barca na ci gaba da jan zarenta a La Liga


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lius Suarez ya ci kwallayensa ne saboda kuskuren da ‘yan wasan Espanyol suka yi

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta rike matsayinta na kasance a gaba a gasar La Liga inda Lius Suarez ya ci kwallo biyun da suka sa ta yi nasara kan Espanyol.

Burin Barcelona na daukar kofi ya fuskanci koma-baya a zagayen farko, bayan Real Madrid ta samu maki uku lokacin da ta doke Valencia ranar Asabar inda ta matsa gaba.

Jose Manuel Jurado ya yi kuskuren buga wata kwallo, wacce Suarez ya samu, sannan ya doka ta cikin raga.

Image caption

Barca na ci gaba da jan zarenta

Ivan Rakitic ya zura kwallo ta biyu sannan Suarez ya kara samun damar wurga kwallo a raga bayan Espanyol sun sake yin kuskure.

Yanzu Real da Barca na da maki daidai wadaida sai dai Barca na gaba da yawan kwallaye.

Amma Real za ta dauki kofi idan ta ci dukkan wasanni hudu da suka rage mata.

Sakamakon wasannin bana ya girgiza 'yan wasan Arsenal – Wenger


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wenger ya ce ‘yan wasansa sun kaɗu

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce wasu daga cikin sakamakon wasannin da aka yi a kakar wasa ta bana sun “girgiza” ‘yan ƙwallonsa, sai dai ya dage cewa a shirye ƙungiyar take ta fafata da Tottenham ranar Lahadi.

Arsenal su ne na shida a teburin gasar Premier kuma suna bayan Manchester City, wacce ke mataki na huɗu, da maki shida ko da yake suna da sauran wasa shida da za su gwabza.

Wenger ya bayyana kashin da suka sha a hannun Bayern Munich da ci 5-1 a watan Fabrairu da kuma dokewar da Chelsea ta yi musu da ci 3-1 a matsayin “babban koma-baya.”

Ya ce “Mun zama kawar wani ɗan dambe wanda aka kayar amma ya tashi sau biyu. Mun sha kashi amma mutane sun fassara hakan a matsayin abin da ba su damu da shi ba.”

Kocin, mai shekara 67, ya kara da cewa “Watakila saboda sun damu sosai ne shi ya sa muka kaɗu sosai. Mun yi matukar kaɗuwa.”

“Ina ganin ‘yan wasan sun damu. Suna da kwazo. Ina son yadda suke nuna halayensu. Muna cikin yanayi mai kyau idan ka kwatanta da wata daya zuwa biyu da suka wuce,” in ji Wenger.

A cikin wasanni 49 da Wenger, Arsenal ta yi nasara a 22, ta yi kunnen-doki a 20 sannan ta sha kaye a bakwai, amma ba ta doke Tottenham ko da sau daya ba a wasannin lig guda biyar da suka fafata.

Mauricio Pochettino shi ne kocin Tottenham na farko da ba a doke ba a gasa biyar da ya buga.

Costa ne gwarzon ɗan wasan gaba na duniya – Conte


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Diego Costa ya zura kwallo 19 a gasar Premier ta bana. Da ce bai zura su ba, da Chelsea ta rasa maki 15

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce Diego Costa shi ne ɗan wasan gaban da ya fi kowanne iya murza leda a duniya.

Chelsea, wacce ke kan gaba a gasar Premier za ta je gidan Everton ranar Lahadi, inda za su yi karon-batta da Romelu Lukaku, dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar Premier ta bana.

Dan kasar ta Belgium, Lukaku, mai shekara 23, ya zura kwallo 24, yayin da shi kuma Costa, dan kasar Spain mai shekara 28, ya ci kwallo 19.

Conte ya ce, “Lukaku yaro ne mai gwaninta amma a wurinmu Diego yana da matukar muhimmanci, kuma shi ne ke share mana hawaye a bana.”

“Muna magana a kan ‘yan wasan gaba biyu mafiya iya taka leda. Amma, a wuria, Diego shi ne gwarzon dan wasan gaba a duniya,” in ji Costa.

Kocin na Chelsea ya kara da cewa “Ina ganin yana da matukar basira. Amma abin da na fi ƙauna shi ne yadda dan wasan zai nuna shi gwarzo a lokacin da yake murza leda, fiye da haka kuma, idan ‘yan wasa haziƙai suka nuna basirarsu ta yin aiki tuƙuru lokacin wasa.”

Hotunan Afirka a makon da ya gabata


Wasu daga cikin kyawawan hotunan Afirka da kuma wasu ‘yan Afirka a ko ina a duniya.

Hakkin mallakar hoto
Tamasin Ford

Image caption

Wasu matasa ‘yan gayu daga DR Congo da Ivory Coast sun taru ranar Talata domin tunawa da mawaki Papa Wemba wanda ya mutu a bikin wakokin Femua a Abidjan shekarar da ta gabata

SapeursHakkin mallakar hoto
Tamasin Ford

Image caption

Shi ne sarkin masu gayu, kuma shi ne ya samar da hadaddiyar kungiyar masu gayu.

Dan gayuHakkin mallakar hoto
Tamasin Ford

Image caption

Dole dan gaye ya yi kwalliya da kyau, ya sanya kaya masu daukar hankali, su kuma sanya turare, su kuma gyara gashinsu.

Wata mata ke jiran masu saen kaya a titi streetside boutique a tsakiyan birnin cibiyar kasuwancin kasar wato LagosHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wata mata kenan take sayar da gwanjon singileti, ke jiran masu saya a wata kasuwa da ke birnin Lagos ranar Laraba

Wani matashi kenan, ke tura Wul baro a kan titin OkepopoHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani matashi kenan, ke tura Wul baro a kan titin Okepopo da ke birnin na Lagos.

Wata a tsaye cikin shagon ajiye kayan tarihin KiristociHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wata mata ke zaune a wani shagon sayar da kayan tarihin Kiristoci lokacin ziyarar Fafaroma Francis zuwa birnin Alkahira, ranar Asabar.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (Hagu)Tare da Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ke wuce wani Abun girmamawaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (Hagu)Tare da Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ke wuce wani abun girmamawa lokacin wata tarbar ziyara a birnin Ankara, da ke Turkiyya.

Wani mai tura Wul baro ke dakon wasu mayan robobi zuwa shagon mai sayar da suHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani mai tura Wul baro ke dakon wasu mayan robobi zuwa shagon mai sayar da su a wajen birinin Nairobi da ke kasar Kenya.

Mai goyon bayan jam'iyyar adawa aHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani mai goyon bayan Jam’iyyar ‘Orange Democratic Party’ a Kenya lokacin da aka kaddadamar da Raila Odinga a matsayin dan takarar hadin gwiwar Jam’iyyun adawa

Hotunan na kamfanonin dillancin labaran AFP, EPA, Getty Images and Reuters ne.

Mene ne ke damun jam'iyyar APC?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kakakin APC ya ce kan ‘yan jam’iyyar a haɗe yake

Tun bayan da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta lashe zaɓen shekarar 2015, masana harkokin siyasa ke cewa ta yi abin da hausawa ke cewa samun duniyar ɗan tsako: ba samun ba, inda za a zauna a ci.

Sun kuwa bayyana haka ne ganin cewa, ba kamar jam’iyyar PDP ba wacce aka kafa da zummar bin turbar dimokraɗiyya ba, akasarin ‘yan jam’iyyar APC haɗin gambiza ne: ‘yan tsohuwar jam’iyyar CPC irin su Shugaba Muhammadu Buhari, da na tsohuwar jam’iyyar AC, kamar su Bola Tinubu da kuma waɗanda zama a jam’iyyar PDP ya yi wa zafi, irinsu tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

A cewar Dr Abubakar Kari, na Sashen koyar da kimiyyar siyasa a Jami’ar Abuja, babban ƙalubalen da APC ke fuskanta shi ne na rashin haɗin kan ɓangarori daban-dana da suka kafa ta.

Ya shaida min cewa “Babbar matsalar jam’iyyar APC ita ce har yanzu ba ta zama jam’iyya ta dunƙule wuri ɗaya ba; har yanzu gungu-gungu na ‘yan jam’iyyu daban-daban ne irinsu tsohuwar jam’iyyar ACN da CPC da kuma tsohuwar PDP. Babu wanda yake kallon APC a matsayin jam’iyya, kuma hakan ne ya sa ake fuskantar manyan matsaloli a jam’iyyar.”

Shi ma Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma ƙusa a jam’iyyar PDP mai hamayya, ya gaya wa BBC cewa APC jam’iyya ce ta mutanen da suka yi fushi, waɗanda ba su da wata kyakkyawar manufa sai dai “cin mutuncin jama’a.”

Sai dai kakakin jam’iyyar ta APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya shaida min cewa: “APC jam’iyya ɗaya ce da ke da manufa guda: kawo ci gaba a Najeriya. Haka kuma kan ‘yan jam’iyyar a haɗe yake, ko da yake ba za a rasa ‘yar rashin jituwa tsakanin wasu ba, amma haka mulkin dimokraɗiyya ya gada.”

Wani babban batu da ya nuna cewa zama ake irin na gidan haya a APC shi ne yadda tun da aka zo zaɓen shugabannin majalisar dokokin tarayya ‘yan jam’iyyar ta APC suka ƙi zaɓar mutanen da jam’iyyar ta tsayar, abin da Dr Kari ya ce ya dasa dambar rashin jituwa tsakanin manyan ‘yan jam’iyyar.

Wasu dai na ganin hakan ba ya rasa nasaba da alwashin da Shugaba Buhari ya sha ba na barin kowanne bangare ya ci gashin kansa ba tare da katsalandan ba.

Sai dai wasu masu sharhin na ganin karan dimokraɗiyyar Najeriya bai kai tsaikon da shugaban ƙasa zai ƙi sanya hannu a sha’anin wasu ɓangarorin ba, musamman ganin cewa duk abin da ya faru a wani ɓangaren, kai-tsaye zai shafi wasu ɓangarorin.

Da alama masu wannan ra’ayi na da hujja domin kuwa shurun da Shugaba Buhari ya yi kan al’amuran da ke faruwa a majalisar dokoki da kuma jam’iyyarsa ta APC har sai da lokaci ya kusa ƙurewa ya sa al’amura sun riƙa rincaɓewa a ƙasar.

An yi ta samun rigingimu tsakanin shugaban jam’iyyar Cif John Odigie-Oyegun da wasu jiga-jiganta irinsu Bola Ahmed Tinubu a kan zaɓukan jihohin Kogi da Ondo, lamarin da ya har ya kai su yin fito-na-fito a kafafen watsa labaran ƙasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Buhari ya kayar da Atiku a zaben fitar da gwani na APC

Shi kansa tsohon mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar sai da ya tsoma baki a cikin rigimar inda ya nuna goyon bayansa ga Mr Tinubu.

Bayan faruwar wannan lamari ne, wanda har yanzu wasu ke ganin tsugune ba ta ƙare a kansa ba, wasu rahotanni suka nuna cewa manyan jami’an na APC cikinsu har da shi Ahmed Tinubun da Atiku Abubakar na shirin kafa sabuwar babbar jam’iyya, zargin da suka musanta.

Babban taro ya gagara

A can jihar Adamawa ma, mahaifar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, an ambato wasu shugabannin jam’iyyar APC na cewa babu wanda za su mara wa baya a zaben 2019 idan ba Atiku Abubakar ba.

Kazalika wasu ‘yan kasar na ganin hatsaniyar da ke faruwa tsakanin ‘yan majalisar dattawa da ɓangaren zartarwa kan wasu batutuwa na da nasaba da hanƙoron da shugaban majalisar Bukola Saraki ke yi na tsayawa takara a 2019, ko da yake ya shaida wa BBC cewa “yanzu ba lokacin siyasa ba ne.”

Sau da dama APC na shirya gudanar da babban taro amma hakan ya ci tura.

Ko da a baya bayan nan, an shirya yin taron ranar 24 zuwa 25 ga watan nan na Afrilu amma shuru kake ji tamkar an aiki bawa garinsu.

Sai dai Malam Bolaji Abdullahi ya shada min cewa an riƙa ɗage taron ne “saboda wasu dalilai na tsare-tsare.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bola Tinubu ( na dama) ya taka muhimmiyar rawa wajen yin nasarar APC

“Tun da muka kafa jam’iyyar nan muka amince cewa ba za mu riƙa yin amfani da kuɗin gwamnati wajen gudanar da ita ba; sai dai mu riƙa samun gudunmawa daga ‘yan jam’iyya shi ya sa ake samun matsala wurin kiran taron. Na biyu kuma akwai matuƙar wahala bakin kowanne ɗan jam’iyya ya zo ɗaya a kan lokacin da za a gudanar da taron. Don haka wanna ba batu ne na samun matsala a jam’iyya ba,” in ji Mallam Bolaji Abdullahi.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin rashin gudanar da babban taron jam’iyyar na da alaka da barakar da ke tsakanin wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Dr Kari ya ce, “Rashin gudanar da tarukan jam’iyya ya sa ana samun rauni a cikinta; kuma saboda halin ko in kula da ake nuna wa jam’iyyar shi ya sa ba a tuntubarta a al’amuran da suka shafi gudanar da gwamnati, hakan ne ma ya sa kake ganin dukkan naɗe-naɗen da shugaban ƙasa ke yi wasu ‘yan tsiraru ne ke yi, ba a la’akari da irin rawar da wasu suka taka wajen cin zaben wannan gwamnatin.”

Sai dai fadar shugaban ta sha musanta cewa ba ya tuntuɓar jam’iyyar, suna masu cewa babu wata matsala tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar.

A cewarsa, matakin farko da APC za ta ɗauka domin shawo kan matsalolin da ke addabarta shi ne: ta dauki kwararan matakai na hadan kan ‘ya’yanta da kuma sakin mara ga ɓangarorin jam’iyyar irinsu kwamitin amintattu, babban kwamitin zartarwa na kasa, kwamitin gudanarwa da kuma rassanta na jihohi.

Masanin kimiyyar siyasar ya ƙara da cewa dole Shugaba Buhari ya fahimci akwai buƙatar ya tsaya tsayin daka wajen ci gaban jam’iyyar, ko da ba zai sake yin takara ba “domin kuwa ko ba komai ita ce dokin da ya hau ya zama shugaban ƙasa, bai kamata ya sa ido ya ga darewarta ba.”

‘Yan ƙasar da dama za su zuba ido su ga yadda al’amuran jam’iyyar za su ci gaba da gudana musamman a lokutan da zabukan shekara ta 2019 ke ƙara ƙaratowa.

'Halin da Nigeria ta shiga ya ƙara mana matsin rayuwa'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nijar na bukatar agajin tunkarar matsalar karancin abinci

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun gudanar da wani taro da cibiyoyin ba da agaji don shawo kan matsalar ƙarancin abinci da mutane kimanin miliyan ɗaya da rabi ke fuskanta a kasar.

Ba kawai mutane ne, suka samu kansu cikin halin yunwa ba, dabbobin ƙasar ma suna cikin tasku sakamakon rashin ciyawa a Nijar.

Gwamnati ta ce faɗuwar darajar Naira da ta shafi kasuwar dabbobin ƙasar a Nijeriya da kuma rashin kasuwa a ƙasashen Libya da Aljeriya duk yi tasiri wajen sanya Nijar a wannan hali.

Ta ce tana buƙatar saifa biliyan sittin da biyu don cike giɓin abincin da mutane da dabbobi ke buƙata a faɗin ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida Malam Bazoum Mouhammed ya ce Nijar ba ta taɓa fuskantar ƙarancin ciyawa musammam a wurare kamar jihar Tawa irin na bana.

“Babbar matsalar ita ce busashenmu mu…naira ta faɗi. Nairar da a da ake canzar da jaka guda (ta saifa) naira 300, (yanzu) ta kai jaka ɗaya, naira 800.

Ya bayyana damuwa game da karayar arziƙin da makiyaya da manoman ƙasar suka samu saboda dabbobi ba sa daraja.

“Abin da muka shaida a watannin da suka gabata, shi ne ake kawo busashe daga Nijeriya a sai da su a Nijar.”

Gwamnatin Nijar dai ta ce a bana ne wannan matsala ta fi ƙamari, don kuwa a baya ko an samu ƙarancin abinci, mutane ba sa shiga mawuyacin hali saboda dabbobi suna kuɗi.

Haka zalika, ana fuskantar hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar, lamarin da ya ƙara tsananta halin takura ga jama’a.

Bazoum ya ce: “Da hasashen da muka yi, har mu kai azumi kuɗin hatsi buhu guda, bai zarce jaka 20 ba, sai ga shi nan yau ya kai jaka 30.”

Ya ce ƙasar tana buƙatar tan dubu arba’in da uku na hatsi don cikawa a kan abin da take buƙata tan dubu saba’in da biyar, da za a sayar cikin farashi mai rangwame.

Haka zalika, jamhuriyar Nijar na buƙatar gudunmawar abincin dabbobi har tan dubu sittin da takwas baya ga iri tan dubu goma sha biyu don raba wa manoma a cewar Bazoum.

Mahukuntan dai na danganta wannan matsala da sauyin yanayi inda a wasu yankunan ƙasar aka fuskanci fari, yayin da a wasu kuma aka gamu da ambaliyar ruwa da ta lalata albarkatun gona da kashe dubban dabbobi.

Joshua ya tamfatse Klitscko a zagaye na 11


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bugun da Joshua ɗan asalin Nijeriya ya yi wa Klischko ya sanya tsohon zakaran boksin ɗin ganin faɗuwarsa ta biyar

Anthony Joshua ya yi wani gagarumin ƙwazo ta hanyar ƙara wa kambunsa, lambar zakaran boksin ajin masu nauyi ta duniya saboda bajintar buge Wladimir Klitschko a filin wasa na Wembley.

‘Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar tsallen-baɗake, inda Joshua ya buge tsohon gwarzon duniyan a zagaye na biyar, kafin a kai shi ƙasa a zagaye na shida – karon farko a fafatawa 19 da ya yi.

Duka ‘yan damben boksin ɗin sun fuskanci shan kaye a wannan karawa da za ta daɗe a zukatan mutane, kafin Joshua ya yi wa abokin karonsa dukan zauna-ka-ci-doya a zagaye na 11.

Joshua, wanda iyayensa ‘yan Nijeriya ne, ya sauke wa Klitschko wani wawan naushi da ya ba shi damar kai shi ƙasa cikin laulayi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Klitschko aka fara kai wa ƙasa a zagaye na biyar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sai dai irin wannan ƙaddara ta faɗa wa Joshua a zagaye na shida

Klitschko ya yi ta maza ya sake jan zare, bayan an sa shi a maƙatar hagu daga bisani.

Sai da lafari David Fields ya karɓe shi lokaci da aka takure shi a jikin igiya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau biyu ana kai Klischko ƙasa a zagaye na 11 kafin lafari ya karɓe shi

Joshua ya cira hannuwansa sama lokacin da ihu da sowa suka ɓarke a filin Wembley.

Ya tsallake karawarsa mafi zafi a yau, yayin da Klitschko ya gane irin wayon da yake da shi.

Ko da yake, ya nuna har yanzu duk da shekarunsa 41, za a ci gaba da kai ruwa-rana da shi a fagen karawa ta duniya.

Klitschko zai ciji yatsa a kan rashin gama wa Joshua aiki, lokacin da ya shimfiɗe shi ƙasa, har ma aka riƙa ganin ba wata makawa ya kusa sake karɓar biyu daga cikin kambun da ya rasa a hannun Tyson Fury a shekara ta 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ingila Rio Ferdinand na daga cikin mutanen da suka taya Joshua murna

“Me zan ce? Karawa 19, ba a buge ni ba, a shekara uku da rabi,” in ji Joshua. “Ban cika bakin na fi kowa ba, amma dai ludayina ne ke kan dawo. Ka san kuma ba a ƙwace wa yaro garma.

“Kamar yadda ‘yan boksin ke cewa, ajiye girman kanka a waje kuma ka mutunta abokin karawarka. Don haka ina yi wa Wladimir Klitschko jinjinar ban girma.”

Wata uwar 'boge' ta mayar da 'yar da ta saya


Hakkin mallakar hoto
CHRISTOPHER FURLONG/GETTY IMAGES

Image caption

An ba wa wani gidan marayu jaririyar (ba ita ce a wannan hoto ba) don samun kulawa

An zargi wata mace ‘yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mai da jaririyar da ta saya, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne.

An zargi matar ‘yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800, kwatankwacin naira miliyan bakwai.

An kama matar tare da mahaifiyar jaririyar ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin.

Ba da goyon ciki a ƙasar Italiya, haramtaccen abu ne kuma akan ɗaure mutum a gidan yari a ci shi tara mai tsanani.

An ce uwar ‘bogen’ ta faɗa wa ‘yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta.

Rahotannin kafofin yaɗa labarai a Italiya sun ce abokin zamanta yana ɗaure a gidan yari kan laifin safarar ƙwaya, kuma a baya-bayan nan ta yi ɓari har sau biyu.

‘Jaririyar ruwa biyu ce’

Mahaifiyar jaririyar, ‘yar ƙasar Romaniya mai shekara 25, bayanai sun ce ta yi ciki ne bayan alaƙarsu da wani mutumin ƙasar Mali.

Lokacin da gano asalin jaririyar, sai uwar bogen ta ce lallai zai yi mata wahala ta iya yin bayani game da launin fatar yarinyar.

Don haka, bayan kwana uku, rahotanni sun ce, sai ta mayar da jaririyar.

An fara nuna wasu-wasi ne farko a ofishin rijistar haihuwa na birnin Latina a kudancin Rome cikin watan Fabrairu, lokacin da wata mata ta nemi sanin yadda ake yi wa jaririn da aka haifa a gida rijista.

Bayan shafe lokaci, amma ba a je an yi rijistar ba, sai jami’ai suka sake tuntuɓa – sai dai an ce sai mai amsawar ta riƙa kwana-kwana.

Hakan ya sanya fargaba lallai da walakin, don haka sai suka ankarar da ‘yan sanda.

Masu bincike sun gano jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma mahaifinta na asali yana aiki ne a Rome.

A yanzu dai ba ta fi tsawon wata guda a duniya ba, kuma an damƙa ta gidan marayu don kula da ita.

An zargi wata mace ‘yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mayar da jaririyar da ta sayo, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne.

An zargi matar ‘yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800 kwatankwacin naira miliyan bakwai.

An kama matar tare da mahaifiyar jarirai ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin.

Al’adar ba da goyon ciki haramun ne a ƙasar Italiya, inda akan yi mutum ɗauri a gidan yari da cin tara mai tsanani.

An ce uwar bogen ta faɗa wa ‘yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta.

Rahotannin kafofin yaɗa labarai a Italiya sun ce abokin zamanta yana ɗaure a gidan yari kan laifin safarar ƙwaya, kuma a baya-bayan nan ta yi ɓari har sau biyu.

Mahaifiyar jaririyar, ‘yar ƙasar Romaniya mai shekara 25, bayanai sun ce ta yi ciki ne bayan alaƙarsu da wani mutumin ƙasar Mali.

Lokacin da gano asalin jaririyar, sai uwar bogen ta ce lallai zai yi mata wahala ta iya yin bayani game da launin fatar yarinyar.

Don haka, bayan kwana uku, rahotanni sun ce, sai ta mayar da jaririyar.

An fara nuna wasu-wasi ne farko a ofishin rijistar haihuwa na birnin Latina a kudancin Rome cikin watan Fabrairu, lokacin da wata mata ta nemi sanin yadda ake yi wa jaririn da aka haifa a gida rijista.

Bayan shafe lokaci, amma ba a je an yi rijistar ba, sai jami’ai suka sake tuntuɓa – sai dai an ce sai mai amsawar ta riƙa kwana-kwana.

Hakan ya sanya fargaba lallai da walakin, don haka sai suka ankarar da ‘yan sanda.

Masu bincike sun gano jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma mahaifinta na asali yana aiki ne a Rome.

A yanzu dai ba ta fi tsawon wata guda a duniya ba, kuma an damƙa ta gidan marayu don kula da ita.

Nigeria: An kama mutanen da suka so kashe Dino Melaye


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jami’an ‘yan sandan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi holin wasu mutane da makaman da a ka samu a wurinsu, wadanda ta zarga da yunkurin kashe wani dan majalisar dattijan kasar, Sanata Dino Melaye a watan Afrilu.

Cikin wata sanarwa da kakakinta, CSP Jimoh O. Moshood ya fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce daga cikin mutanen da a ke zargi, akwai shugaban karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Taofiq Isah, wanda ta ce shi ne ya shirya harin.

Rundunar ‘yan sandan ta ce bincike ya nuna shugaban karamar hukumar ne ya bai wa wani Abdulmumini da a ka fi sani da “iron” ko karfe, izinin kai wa Sanata Dino Melaye hari.

“Daga nan ne shi kuma Abdulmumini ya dauki hayar wasu mutane da suka kware wajen kisa domin aiwatar da nufinsu,” Inji sanarwar.

Har yanzu dai ba a kama Abdulmuminin ba, amma sauran mutanen da ya dauka hayar sun shiga hannun hukuma.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Senate

Image caption

Sanata Dino Melaye

Sanarwar ta bayar da sunan mutanen da aka kama kamar haka: Ade Obage, da Abdullahi Isah da Ahmed Ajayi da Michael Bamidele da Ede James.

Acewar sanarwar, makaman da a ka samu a wajen mutanen sun hada da bindigogin AK 47 guda biyar, da pistol daya, da bindigogi kirar gida biyu da harsasai masu yawa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce Ade Obage mai shekara 29 ne ya kai rahoto don kashin kan shi ga ‘yan sanda bayan sun yi yunkurin halaka dan majalisar.

Rundunar ta ce ta zafafa bincike domin kamo sauran mutanen da ke da hannu a cikin harin, sannan za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

A tsakiyar watan Afrilu ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan Sanata Dino Melaye a Aiyetoro-Gbede a karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, lokacin da yake cikin gidan da dare.

‘Yan bindigar ba su samu kai wa gare shi ba, amma sun lalata katangar gidan da harsasai.

Tattaunawa da mai safarar sassan jikin 'yan gudun hijira


Idanuwan Abu Jaafar na cike da gadara lokacin da yake bayyana hanyarsa ta samun kuɗin shiga a rayuwa.

Yana aiki ne a matsayin mai gadin mashaya lokacin da ya hadu da gungun wasu mutane da ke safarar sassan jikin bil’adama.

Aikinsa shi ne ya nemo mutane da ke cikin halin ni-‘ya-su domin su sayar da wani sashe na jikinsu, kuma kwararar ‘yan gudun hijira daga Siriya zuwa Lebanon ta sa harkarsa ta buɗe.

Ya ce “Ina ci da gumin mutane, ko da yake ya nuna cewa da yawansu ka iya mutuwa cikin sauƙi a Siriya, don haka cire wani sashe na jiki ba komai ba ne, idan an kwatanta da munanan haɗurran da suka fuskanta.

“Ina ci da guminsu, amma su ma suna ƙaruwa.” in ji shi.

Yana zaune ne a wani ɗan karamin shagon sayar da gahawa, a ɗaya daga cikin unguwannin mafi cunkoson da ke kudancin birnin Beirut, wani gini ne duk ya ji jiki da aka lulluɓe shi da tamfol.

A bayan ginin, wani daki ne da ke jikin wata iyaka da aka raba gidan cunkushe da tsoffin kujeru, tsuntsaye na ta kuka a cikin keji a kowacce kusurwa.

Ya ce daga nan ne ya tsara cinikin sassan jikin ‘yan gudun hijira kimanin 30 a cikin shekara uku da ta wuce.

“Sun fi tambayar ƙoda, amma kuma ina iya nemowa na shirya cinikin sauran sassan jiki”. in ji shi.

“An taɓa neman idon mutum, kuma na yi ƙoƙari na samo wani buƙatar sayar da idonsa.”

“Na ɗauki hoton idon mutumin, kuma na aika wa masu sayen ta shafin Whatsapp don su gani ko ya yi. Daga nan, sai na kai mai sayarwar.”

Ƙananan titunan da yake gudanar da harkarsa na cike da ‘yan gudun hijira. Mutum ɗaya cikin huɗu na ‘yan Lebanon a yanzu ya gudo ne daga tsallaken iyakar Siriya saboda rikici.

Mafi yawansu ba za a bari su yi aiki a karkashin dokar Lebanon ba, da ƙyar iyalai da yawa ke maleji.

Daga cikin waɗanda suka fi tagayyara, akwai Falasɗinawa wadanda ake ɗauka a matsayin ‘yan gudun hijira a Siriya, don haka ba su cancanci sake yin rijista da hukumar kula da ‘yan hgudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ba idan suka iso Lebanon.

Suna rayuwa a sansanoni masu cunkoso kuma tallafin da suke iya samu kaɗan ne.

Waɗanda suka yi kusan kamo su wajen tagayyara su ne mutanen da suka zo daga Siriya bayan watan Mayun shekara ta 2015, lokacin da gwamnatin Labenon ta ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta daina yi wa sabbin ‘yan gudun hijira rijista.

“Duk wanda ba a yi wa rijista a matsayin ɗan gudun hijira ba ya shiga wahala,” in ji Abu Jaafar. “To ya za su yi? Sun shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, ba su da wata hanyar rayuwa face su sayar da sassan jikinsu”

Wasu ‘yan gudun hijirar kan yi bara a tituna, musammam ƙananan yara.

Samari kuma kan yi sana’ar goge takalmi, wasu na kurɗa-kurɗa a tsakanin motoci suna sayar da cingam ko hankici, ko kuma su kare a matsayin yaran da ake bautar da su wasu su dinga ci da guminsu.

Wasu kuma kan zama karuwai. Amma sayar da wani sashen jiki hanya ce ta samun kudi na da nan.

Da zarar Abu Jaafar ya samu masu son sayarwa, sai ya ɗauke su a mota, ya rufe musu ido, zuwa wani boyayyen waje a ranar da za a cire.

Wasu lokuta likitoci kan yi tiyatar ne a gidajen haya, waɗanda aka mayar da su ƙananan asibitocin wucin-gadi, a nan ake yi wa mutum gwaje-gwajen jini kafin aikin tiyatar.

Ya ce “Da an gama tiyatar sai na mayar da mutum inda na ɗauko shi”

“Zan kula da shi har kusan mako guda, lokacin da za a cire zaren ɗinkin da aka yi. Da zarar an cire, ba ruwanmu da abin da zai faru da su”.

“Ba ruwana, idan mutumin ya mutu, na samu abin da nake bukata. Ba matsalata ba ce, abin da zai faru da shi gaba matukar an biya mutum haƙƙinsa”.

Abokin cinikin Abu Jaafar na baya-bayan nan, wani matashi ne ɗan shekara 17, wanda ya baro Siriya bayan kashe mahaifinsa da ‘yan’uwansa a can.

Tsawon shekara uku yana zaune a Lebanon ba shi da aikin yi, ga shi ya ci bashi iya wuya, yana fama ya tallafa wa mahaifiyarsa da ‘yan’uwansa mata biyar.

So, through Abu Jaafar, he agreed to sell his right kidney for $8,000 (£6,250).

To, ta hanyar Abu Jaafar, ya yarda ya sai da ƙodarsa ta dama dala dubu takwas, kimanin naira miliyan uku.

Bayan kwana biyu, ga alama yana fama da ciwo duk da magungunan da yake sha, ya kasa kwance ya kasa zaune a kan wata yagalgalalliyar katifa.

Fuskarsa ta yi sharkaf da gumi, ga kuma jini yana jiƙe bandejin da aka yi masa.

Abu Jaafar bai faɗi ko nawa ya samu a wannan harka ba. Ya ce bai san abin da ake yi da sassan jikin ba, idan an saya, amma yana jin fitar da su wasu kasashen ake yi.

Ana fama da ƙarancin sassan jikin mutum da ake buƙata don yin dashe a yankin Gabas Ta Tsakiya, saboda tasirin al’ada da addinan waɗanda za su iya ba da gudunmawar sashen jiki.

Akasarin dangi sun fi son nan da nan a binne mamaci.

Abu Jaafar ya yi iƙirarin cewa akwai aƙalla dillali bakwai irinsa da ke aiki a kasar Lebanon.

“Harka tana tafiya,” a cewarsa “Harkoki gaba suke yi ba baya ba. Tabbas an samu bunƙasa bayan ƙaurar ‘yan Siriya zuwa Lebanon.”

Ya san abin da yake yi ya saɓa wa doka, amma ba ya tsoron hukumomi. a maimakon haka ma alfahari yake da sana’arsa. Yakan rubuta lambar wayarsa a jikin bangwayen da ke kusa.

A unguwarsu ana ganin girmansa kuma ana jin tsoronsa. Mutane kan shiga taitayinsu da zarar ya tunkari waje.

Ya cusa ƙaramar bindiga a kafarsa lokacin da muke zantawa.

Ya ce “Na san abin da nake yi ya saɓa doka, amma kuma taimako nake yi”

“Ni haka nake gani. mutumin da zai sayar da sashen jikinsa, yakan yi amfani da kudin, don neman rayuwa ingantacciya a gare shi da danginsa.

“Ya samu damar sayen mota inda yake aikin taksi, ko ma ya yi tafiya zuwa wata ƙasar.

“Ina taimakon mutane ne, ba ruwana da dwata oka”

A gaskiya ma ya ce ai dokar ce ta hana ‘yan gudun hijira da yawa samun ayyukan yi da tallafi.

“I am not forcing anyone to undertake the operation,” he says. “I am only facilitating based on someone’s request.”

“Ba na tilasta wa kowa yin haka, a cewarsa. “Ni kawai ina shiga tsakani ne idan mutum ya bukaci hakan.”

Ya kunna sigari yana zare ido.

“How much for your eye?” he asks.

“Nawa za ka sayar da idonka?” ya tambaya.

Abu Jaafarba sunansa ne na ainihi bakawai ya yarda zai yi magana da BBC ne bisa sharaɗi za a sakaya sunsan

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Trump ya ce Koriya ta Arewa ba ta kyauta ba

Kasar Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makami mai linzami, a cewar jami’an Koriya Ta kudu da Amurka.

Sun ce makamin ya tarwatse jim kadan da harba shi – karo na biyu kenan a mako biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Koriya ta Arewa da nuna “rashin da’a” ga China da shugabanta.

An harba makamin ne ranar Asabar daga kudancin Pyeongan, a cewar Koriya ta Kudu.

Mr Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Koriya ta Arewa ta nuna rashin da’a ga bukatun China da shugabanta da ke da kima inda ta harba makami mai linzami a yau, ko da yake bai yi nasara ba. Hakan babu dadi.”

A kwanan baya ne Mr Trump ya barki bakuncin shugaban China Xi Jinping inda ya yabe shi kan abin da ya kira “kokarin da kake yi matuka” kan Koriya ta Arewa.

An harba makami mai linzamin da bai yi nasara ba ne sa’o’i kadan bayan kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya tattauna kan shirin Koriya ta Arewa na kera makamai masu linzami.

Zan iya zuwa kotu a kan ɓata-suna – Shekarau


Image caption

A zamanin mulkin Ibrahim Shekarau ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin Sheikh Ja’afar Adam a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yana bin kadin ɓata-suna da ‘yan sandan ƙasar suka yi masa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata takarda da ke alaƙanta Shekarau da kashe Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.

A cewarta jami’anta ne suka gano takardar bayan wani samame da suka kai gidan sanata Danjuma Goje a Abuja.

Mai magana da yawun Shekarau, Malam Sule Ya’u Sule ya ce ba shakka suna bin bahasin wannan batu a wajen ‘yan sanda.

Ya ce sun tuntuɓi ‘yan sanda a kan su fito su binciko gaskiyar wannan al’amari kuma su yi wa jama’a bayani.

Sule Ya’u Sule ya ce suna iya zuwa kotu a kan wannan ɓata-suna da ya ce an yi wa Ibrahim Shekarau.

Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN SENATE

Image caption

Sanata Danjuma Goje ya nisanta kansa da takardar kuma ya nemi ‘yan sanda su fayyace gaskiya

A cewarsa, takardar da ‘yan sanda suka yi iƙirarin sun gano a gidan Sanata Danjuma Goje tsohuwar takarda ce da wasu abokan hamayya suka rubuta don shafa wa Shekarau kashin kaji.

Ya ce “Ni ma ina da wannan takarda. Al’umma da yawa a Kano sun samu wannan takarda…Na tabbata wannan takarda ce wannan tsohon gwamna (sanata Danjuma Goje) ya samu. Idan kuma wata ce daban, ya kamata ‘yan sanda su fito su yi wa mutane bayani.”

Shi da kansa Malam Ibrahim Shekarau ne a wancan lokaci ya nemi ‘yan sanda su yi bincike a kan wannan takarda.

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam yayin sallar asubah a Kano.

‘A yi wa jama’a bayani’

Mai magana da yawun Shekarau ya ce ‘yan sandan sun yi bincike a kai kuma sun san abin da suka gano game da batun, don haka ya kamata su fito su yi wa al’umma bayani.

Da aka tambaye shi ko Shekarau zai ɗauki matakin shari’ah a kan wannan al’amari, ya ce suna jiran bayanin ‘yan sanda kafin su san mataki na gaba da za su ɗauka.

Sule Ya’u ya ce sun ji Sanata Danjuma Goje yana bayani ta kafofin yaɗa labarai inda ya tsame kansa, don haka Shekarau ya miƙa komai ga ‘yan sanda.

A cewarsa waɗanda suka fito suka yi wannan batu, a wajensu suke neman bahasi amma ba Sanata Goje ba.

Ya yi shaguɓe kan yadda wasu mutane da bai bayyana ko su wane ne ba, da ya ce burinsu a kullum su ƙulla wa tsohon gwaman sharri, “su je su ci gaba da yi.”

Ko wayar salula na iya warkar da ciwon suga?


Hakkin mallakar hoto
JSHAO

Image caption

Ta hanyar shafa fuskar wayar salular ana iya gane yawan sukarin da ke cikin jini

Masana kimiyya sun yi amfani da wayar salula ta smartphone don sarrafa aikin ƙwayoyin halitta a jikin wata dabba.

An haɗa kimiyyar rayuwar halittu ce da fasaha don sarrafa yawan sukari a cikin jinin wani ɓera mai fama da ciwon suga.

Ana iya amfani da wannan dabara wadda aka bayyana a mujallar kimiyya ta Translational Medicine wajen duba lafiyar masu fama da cutuka iri daban-daban.

Masu binciken na ƙasar China sun ce dabarar ka iya buɗe wani sabon babi a fannin ba da magani.

Mataki na farko ana sauya ƙwayoyin halittun jiki zuwa wasu masana’antu.

An sarrafa sigar ƙwayoyin gadon halittun don samar da magungunan da za su iya taƙaita ƙaruwar suga a cikin jini – amma ta hanyar karɓar saƙwanni daga haske.

Ana kiran wannan fasaha a kimiyyance da optogenetics kuma ƙwayoyin halittu kan faɗa aiki wurjanjan da zarar an dallare su da wani jan haske.

Fasahar dai tana amfani da wani ɗan ƙanƙanin ƙwan lantarki da kuma wata manhajar wayar salula da ke sarrafa shi.

Masu binciken a jami’ar East China Normal da ke Shanghai kan dasa wannan fasaha ce a jikin ɓera, ta yadda za su iya daƙile ciwon suga ta hanyar ɗan taɓa fuskar wayar.

Hakkin mallakar hoto
JSHAO

Image caption

Ana iya maƙala ‘yar na’ura a ƙarƙashin fata don sadarwa a tsakani

Ayarin masu binciken ya ce nazarin “ka iya share fagen wani sabon babi na ba da magani gwargwadon buƙatar mutum ta hanyar fasahar dijital da za ta karaɗe duniya.”.

Masana kimiyyar na buƙatar ɗiban wani ɗan ɗigon jini don sanin yawan sugan da ke cikinsa ta yadda za su iya ƙididdige adadin maganin da jiki yake buƙata.

Babban burinsu shi ne ɓullo da wani cikakken tsarin amfani da na’ura don gano yawan sugan da ke cikin jini da kuma daidai kimar sinadarin laƙani da za a bayar.

A bayyane take cewa fasahar tana wani matakin farko ne, amma dai ba za ta taƙaita ga magance ciwon suga ba. Ana iya sarrafa ƙwayoyin halittu ta yadda za su iya haɗa magunguna iri daban-daban.

Wani masanin kimiyyar rayuwar halittar curin sinadari, Farfesa Mark Gomelsky a Jami’ar Wyoming, ya ce nazarin wani “cikar buri ne mai sa shauƙi”.

Ya ƙara da cewa: “Nan da yaushe ne za mu sa ran ganin mutane na tafiya a kan titi sun ɗaura ‘yar wata fitila a hannunsu da za ta riƙa dallare ƙwayoyin halittun jiki da za su samar da wani magani da ƙwayoyin halittun gado suka sarrafa, ta hanyar amfani da wayar salula?

An ɗaure angon da ya yi wa baƙuwa fyaɗe


Hakkin mallakar hoto
MET POLICE

Image caption

Derry Flynn McCann ya amsa laifi kan tuhuma uku ta aikata fyaɗe da kuma yin fashi

An yanke wa wani ango hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda yi wa wata baƙuwa fyaɗe sa’o’i kafin ɗaura masa aure da abokiyar zamansa mai juna biyu.

A ranar 13 ga watan Janairu ne, Derry Flynn McCann ɗan shekara 28, ya auka wa wadda ya yi wa fyaɗe na tsawon sa’a biyu a yankin Hackney da ke gabashin London.

Kwanan nan aka sako shi daga gidan yari saboda aikata irin wannan laifi.

Wani alƙali a kotun Snaresbrook ya bayyana Derry McCann a matsayin “wani ibilishi” kuma ya ce sai ya yi zaman gidan yari na aƙalla shekara 9.

Yayin wannan fyaɗe na tsawon lokaci, McCann ya yi duka kuma ya muzanta wannan mata sannan ya ɗauki hotunanta ya sace mata waya.

A zaman da kotun ta yi cikin watan Maris a baya, Derry McCann na unguwar Hackney ya amsa laifinsa kan tuhuma uku ta aikata fyaɗe da kuma wata tuhumar kan cin zarafin ‘ya mace gami da tuhuma ɗaya kan aikata fashi.

Masu bincike sun yi imani cewa Derry ya biyo wata mata ce amma sai ta ɓace masa don haka sai ya auka wa wadda abin ya faru a kanta.

An fahimta cewa ko a shekara ta 2006 ma an ɗaure McCann kan aikata wani dogon fyaɗe da ya yi.

Bibiyar Trump : Me da me Shugaban ya cimma ya zuwa yanzu?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Donald Trump ya cika kwana 100 a kan mulkin Amurka

Donald Trump ya hau karagar mulki ne da alkawarin kawo sauyi ta fuskar siyasa a Amurka da kuma mayar da iko hannun mutane .

Don haka me shugaban ya cim ma zuwa yanzu? Muna bibiyar ci gaban shugaba Trump kan manufofinsa da kuma yadda Amurkawa suka karbe su.


Waɗanne matakan zartarwa Trump ya ɗauka?

Wata hanya da Shugaba Trump zai iya aiwatar da iko a siyasance ita ce bayar da umarnin zartarwa, abin da ya ba shi damar tsallake majalisar dokokin kasar wajen fitar da wasu manufofi.

Bai ɓata lokaci wajen amfani da wannan iko ba, ta hanyar janyewa daga yarjejeniyar cinikayyar Pacific da rusa dokokin kasuwanci da kuma yin gaban kansa wajen shimfiɗa bututan mai guda biyu.

Duk da yake, ana ganin ya yi amfani da umarnin zartarwa ta hanyar da ba a taɓa gani ba, shi ma shugaba Obama da ya yi mulki gabaninsa ya yi amfani da irin wannan umarni a makonninsa na farko a kan mulki amma dai Mista Trump ya zarce shi.

Shugaba Trump ya bayar da umarninsa ne da niyyar cika alkawuran yaƙin neman zaɓen da ya yi, amma tasirinsu na da iyaka.

Yayin da umarni irin na zartarwa zai iya sauya yadda hukumomin gwamnati ke amfani da kudadensu, amma ba zai iya bai wa waɗannan hukumomin kudaden gudanar da harkokinsu ba, ko ma damar gabatar da sabbin dokoki – wannan iko yana hannun majalisar dokokin Amurka.

Alal misali, umarnin Trump kan shirin kula da lafiya na ObamaCare ya yi shi ne domin rage tasirin tsarin, amma alkawarinsa na soke tsarin da kuma maye gurbinsa, zai iya tabbata ne kawai da taimakon majalisar dokokin Amurka domin yana bukatar sabuwar doka.


Yaya karbuwarsa take awajen Amurkawa?

A lokacin da Mista Trump ya karɓi rantsauwar mulki ranar 20 ga watan Janairu, ya yi haka ne da mafi ƙarancin karɓuwa a ƙuri’un jin ra’ayin jama’a da aka taɓa samu game da wani shugaban Amurka mai jiran gado.

Ya yi watsi da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar a matsayin wadda aka yi murɗiya, kuma ƙarfin adawar da ya fuskanta, ya fito fili a lokacin da dubban mutane suka fita zanga-zangar nuna ƙin jininsa bayan an rantsar da shi.

Yawancin shugabanni na fara wa’adinsu ne da gagarumar karɓuwa, amma Shugaba Trump ya sauya wannan tarihi a Amurka. Yayin da Shugaba George W Bush da Shugaba Obama suka samu amincewar fiye da kashi 60 cikin 100 na Amurkawa a lokacin da suka cika kwana 100 a kan karagar mulki, Mista Trump ya samu karɓuwar sama da kashi 40 ne kawai.

Mista Trump ya lashe zaɓe ne da amincewar mutane kaɗan a ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a. Saboda haka ba abin mamamki ba ne cewa waɗanda suka amince da shi tsiraru ne har yanzu. Amma ce-ce-ku-cen da alaƙarsa da Rasha ta janyo da kuma matakinsa na haramta wa ‘yan wasu ƙasashe shiga Amurka sun sa waɗanda suka amince da shi na ƙara raguwa.

Duk da haka, yunƙurin Mista Trump na soke wasu dokokin kasuwanci da kuma tsattsauran ra’ayinsa kan harkokin shige da fice sun burge da yawa daga cikin magoya bayansa. Baya ga haka an tabbatar da wanda ya zaɓa a matsayin ɗaya daga cikin alƙalan kotun ƙolin Amurka, abin da ya dawo da rinjayen masu ra’ayin riƙau. Karɓuwarsa a tsakanin masu ra’ayin riƙau ta kai sama da kashi 80 cikin 100 kamar yadda a baya.

Shin karburwar wata abar damuwace? Ta yiwu ba wata abar damuwa ba ce, a halin yanzu.

‘Yan jam’iyyar Republicans suna jagorantar majalisar wakilai da ta dattawan kasar, saboda haka ya kamata a ce zai iya neman cim ma manufofinsa na dokoki, ba tare da damuwa game da karɓuwarsa ba- muddin ya samu goyon bayan ‘yan jam’iyyarsa ta Republican.

Amma idan har karɓuwarsa ta tsaya ƙasa-ƙasa, ana tsammanin wasu muryoyi masu ƙin amincewa da shi, za su bayyana a cikin jam’iyyarsa, a daidai lokacin da ‘yan Republican ɗin ke fara nuna damuwa game da zaɓen tsakiyar wa’adi da za a yi a shekarar 2018.


Shin Trump ya dauki matakin daƙile shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba?

Harkar shige da fice ita ce Trump ya fi mayar da hankali kanta a lokacin yaƙin neman zaɓe kuma ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa domin cika wanna alkwari.

Ɗaya daga cikin umarnin da ya fara rattaba hannu a kai, shi ne ayyana cewar Amurka za ta gina katanga ko kuma wani shamaki wanda zai hana tsallako iyakar ƙasar daga Mexico. Nisan iyakar ya kai mil 650.

Amma Mista Trump yana buƙatar amincewar majalisar dokokin Amurka kafin ya iya fara wannan gini, kuma har yanzu bai samu amincewar ba. Ya haƙiƙance cewa Mexico za ta biya kuɗin daga baya, duk da yake, hukumomin ƙasar sun ce ko kusa ba za ta saɓu ba.

Ko da yake, Shugaba Trump bai sauya dokar shige da ficen Amurka ba tukunna, amma dai ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa guda biyu waɗanda suka nemi jami’an shige da ficen kasar su ɗauki tsauraran matakai wajen aiwatar da dokokin da kasar ke da su.

Akwai wasu alamu da ke nuna cewar sauyin yin aiki da dokar shige da fice – da kuma kausasan kalaman Shugaba Trump – za su iya rage yawan mutanen da ke son shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.

A watan Maris, yawan mutanen da aka kama a lokacin da suke ƙoƙarin shiga Amurka ya ragu zuwa adadi mafi ƙaranci a cikin shekara 17, in ji Sakataren ma’aikatar tsaron cikin gida.

Mista Kelly ya ce raguwar mutanen ba abin mamaki ba ne, kuma hukumar kula da shige da ficen Amurka ta ce umarnin shugaban ya sauya salon yadda lamari ke tafiya.

Batun sabon shugaban na dakile kwararar baƙin haure ya sa ana tunanin baƙin haure sun samu yadda suke so a ƙarƙashin Shugaba Obama, amma akwai dalilai da dama da ke nuna akasin haka.

Tsakanin shekara ta 2009 – 2015, gwamnatin Obama ta kori fiye da mutum miliyan 2.5 – yawancinsu wadanda aka samu ne da aikata wasu manyan laifuka ko kuma waɗanda ba su daɗe da shiga Amurka ba, abin da ya sa wasu suka riƙa yi wa Mista Obama laƙabi da “shugaba mai korar baƙi.”

Kimanin baƙin haure miliyan 11 ne ke zaune a Amurka, yawancinsu kuma daga Mexico.

Hukumar da ke aiwatar da dokar shige da fice da hana fasa-ƙwauri ta ƙaddamar da wasu jerin samame a fadin kasar tun da aka zaɓi Mista Trump, amma lokaci bai yi ba, da za a iya yanke hukunci a kan ko korar baƙin haure ya ƙaru ko bai ƙaru ba.


Yaya tattalin arziki ke gudana a karkashin Trump?

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasa a shekara 2009, Amurka na cikin karayar arziki mafi muni wadda ba ta taɓa samun irinta ba tun shekarun 1930, inda tattalin arzikin ya janyo rasa ayyuka 800,000 a watansa na farko.

Amma bayan ɗan koma-bayan da ya samu a shekarar, tattalin arzikin Amurka ya samu lokacin mafi tsawo yana bunƙasa, inda ya janyo samar da ayyukan yi masu ɗumbin yawa. An samar da jimillar aikin yi miliyan 11.3 a karkashin Shugaba Obama.

A baya Mista Trump ya yi watsi da waɗannan alkaluman a matsayin na boge, kuma bayan ƙaddamar da shi ya siffanta tattalin arzikin ƙasar a matsayin abin da ke cikin rikici.

Sai dai, wani sabon rahoton wata-wata da aka fitar a watan Maris da ke nuna cewa an samu karin ayyuka 235,000 a watan Fabrairu, ya sa Sakataren yada labaran fadar White House Sean Spicer cewa matakin, babban labari ne ga ma’aikatan Amurka.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 25 a cikin shekara 10 da kuma “zama shugaba mai samar da aikin yi mafi yawa da aka taba samu a tarihi.”

Ya yi zargin cewar Mexico da China suna sace miliyoyin ayyuka don haka ya sha alwashin “kawo ayyukanmu gida.” Amma wani bincike ya nuna cewa yawancin ayyukan ma’aikatun ƙere-ƙere da suka salwanta a shekarun baya -bayan nan, an yi asararsu ne saboda ƙwarewar da na’urorin masana’antu ke kara samu wajen iya aiki da kansu, sabanin iƙirarin cewa hakan ta faru ne saboda ana kai ayyuka ƙasashen waje.

Kasuwannin hannayen jari na Dow da S&P 500 da kuma Nasdaq sun kai matakan habakar da ba a taba samu ba a makonnin farko na mulkin Shugaba Trump, wata alamar da ke nuna cewar masu zuba jari sun samu ƙwarin gwiwa a kan ayyukan ababen more rayuwa da Mista Trump ke son yi tare da zame hannun gwamnati daga tallafi da kuma rage harajin da yake son yi.

Amma haɓakar kasuwannin uku ta ragu a watan Maris lokacin da aka fara tunanin garambawul ɗin harajin ba zai samu da wuri ba kamar yadda gwamnatin Trump ta fada.


Me gwamnatinsa ta yi kan kiwon lafiya?

Dole ne kiwon lafiya ya kasance wani fannin da za a fara gwada Shugaba Trump bayan ya yakin neman zabensa ya mayar da hankali kan batun.

Tsarin kiwon lafiya na Shugaba Obama ya taimaka wa fiye da Amurkawa miliyan 20 wadanda ba su da inshora a da domin samun inshorar lafiya- amman Trump ya sha alwashin cewar zai gaggauta soke dokar ya kuma maye ta da wata.

Daga baya ‘yan Republican sun gabatar da kudirin dokar samar da kiwon lafiyarsu a farkon watan Maris inda kakakin majalisar Wakilan kasar, Paul Ryan, ya siffanta shi a matsayin wani gagarumin garambawul na masu ra’ayin rikau.

Shugaba Trump ya goyi bayan kudirin, amman kudirin ya sami kakkausar suka daga hukumar kasafin kudin majalisar wadda ta ce zai kara Amurkawa miliyan 24 wadanda ba su da inshora zuwa shekarar 2026.

Gwanatin Trump ta ce ita ba ta yarda da bayanan hukumar kasafin kudin ta majalisar dokokin kasar ba, amman an yi fatali da kudirin ranar 24 ga wata Maris bayan ta kasa samun isasshen goyon baya daga ‘yan jam’iyyar Reuplican.

Wani yanayi ne na cin fuska ga Shugaba Trump da kuma jam’iyyar Republican, wadda ke shugabancin kasar da kuma jagorancin majalisun dokokin kasar a karo na farko cikin shekara 11.

Mista Trump ya yi iya kokrinsa na mantawa da kayen da kudirin ya sha, yana mai cewar gwamnatinsa za ta koma ta sake hada tsarin kiwon lafiyar bayan tsarin kiwon lafiyar ObamaCrea ta “fashe.”

Yayin da tsarin samar da lafiya na Obamacare ya fuskanci kalubale tun da aka kaddamar da shi a shekara 2010, bai nuna alamu masu yawa na faduwa nan gaba ba kuma bayanin hukumar kasasfin kudin majalisar dokokin kasar ya ce kasuwannin tsarin na kiwon lafiyar sun daidaita.

Wanna zai canza in Shugaba Trump da ‘yan jam’iyyarsa ta Republican suka dau matakin rage kudin tallafin tsarin, amma wanna zai kasance wani dabara mai hatsari gabannin zaben rabin wa’adi a shekara mai zuwa, musamman a lokacin da kuri’ar jin ra’ayin jama’a na baya-bayannan ke nuna cewar shirin Obamacare na kara samun karbuwa.

‘Yan Jami’yyar Republican sun dauki alkawarin samar da sabon tsarin kiwon lafiya bayan hutun Easter, amman babu tabbacin me nene ke cikin tsarin da kuma ko jam’iyyar za ta mara masa baya ko kuma tsarin zai samu isassun kuri’u damin ya zama doka.

Bibiyar Trump : Da-me-da-me Shugaban ya cimma ya zuwa yanzu?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Donald Trump ya cika kwana 100 yana mulkin Amurka

Donald Trump ya hau karagar mulki ne da alkawarin kawo sauyi ta fuskar siyasar Amurka da kuma mayar da iko ga mutane .

Saboda haka menene ya cimma ya zuwa yanzu? Muna bibiyar cigaban shugaban kan manufofinsa da kuma yadda Amurkawa suka karbe su.


Wanne matakan zartarwa Trump ya dauka?

Wata hanyar da Shugaba Trump zai iya aiwatar da ikon zartarwa a siyasa ita ce ta bayar da umarnin zartarwa wanda ya ba shi damar tsallake matakin doka a majalisar dokokin kasar kan wasu monufofi.

Bai bata lokaci ba wajen amfani da wannan ikon wanda ya yi amfani da shi wajen janyewa daga yarjejeniyar cinikayyar Pacific da rusa dokokin kasuwanci da kuma yin kan gabansa da gina layukan bututun mai biyu.

Duk da cewar ana ganin ya yi amfani da umarni irin ta yadda ba a taba gani ba, Shugaba Obama da ya yi mulki gabaninsa ya yi amfani da umarni kusan irin hakan a makonninsa na farko a kan mulki duk da cewar Mista Trump ya zarce mishi.

Shugaba Trump ya bayar da umarninsa ne da niyyar cika alkawuran yakin neman zaben da ya yi, amman tasirin su na da iyaka.

Yayin da umarnin irin na zartarwa zai iya sauya yadda hukumomin gwamnati ke amfani da kudadensu, ba zai iya bai wa wadannan hukumomin sabbin kudade ba ko kuma damar gabatar da sabbin dokoki- ikon yin hakan na hannun majalisar dokokin Amurka.

Alal misali, umarnin Trump kan tsarin kiwon lafiya na ObamaCare ya yi shi nr domin ya rage tasirin tsarin, amman alkawarinsa na soke tsarin da kuma maye gurbinsa zai iya kasancewa ne kawai da taimakon majalisar dokokin kasar domin yana bukatan sabuwar doka.


Yaya karbuwarsa ta ke ga Amurkawa?

A lokacin da Mista Trump ya sha rantsauwar hawa karagar mulki ranar 20 ga watan Janairu, ya yi hakan ne da mafi raunin karbuwa a kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka taba samu game da wani shugaban Amurka mai jiran gado.

Ya yi watsi da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar a matsayin wata kuri’a wadda aka murda, kuma karfin adawar da ya fuskanta ya fito fili a lokacin dubban mutane suka fita zanga-zangar kinsa bayan an rantsar da shi.

Yawancin shugabanni na fara wa’adinsu ne da gagarumar karbuwa, amman Shugaba Trump ya sauya wannan yanayin. Yayin da Shugaba George W Bush da Shugaba Obama suka samu amincewar fiye da kashi 60 cikin 100 na Amurkawa alokacin da suka cika kwanaki 100 kan karagar mulki, Mista Trump ya samu karbuwar mutum sama da kashi 40 ne kawai.

Mista Trump ya lashe zaben ne da amincewar mutane kadan a kuri’ar jin ra’ayin jama’a. Saboda haka ba abun mamamki bane cewar wadanda suka amince da shi kadan ne har yanzu. Amman ce-ce-ku-cen da alakarsa da Rasha ta janyo da kuma matakinsa na haramta wa ‘yan wasu kasashe shiga kasar sun sa wadanda suka amince da shi na kara raguwa.

Duk da haka, yunkurin Mista Trump na soke wasu dokokin kasuwanci da kuma tsatsaurar ra’ayinsa kan shige da fice sun burge da yawa daga cikin magoya bayansa. Baya ga haka an tabbatar da wanda ya zaba a matsayin daya daga cikin alkalan kotun kolin kasar, abin da ya dawo da rinjayen masu ra’ayin rikau. Karbuwarsa a bangaren masu ra’ayin rikau tana sama da kashi 80 cikin 100 kamar yadda ta ke da.

Shin karburwar wata abar damuwace? Ta yiwu ba wata abar damuwa ba ce, a halin yanzu.

‘Yan jam’iyyar Republicans suna jagorantar majalisun wakilai da ta dattawan kasar, saboda haka ya kamata ace zai iya nemi cimma manufofinsa na dokoki ba tare da damuwa game da karbuwarsa ba- muddin ya samu goyon bayan ‘yan jam’iyyarsa ta Republican.

Amman in har karbuwarsa ta tsaya kasa-kasa, sai a tsammanci wasu muryoyi masu kin amincewa da shi su bayyana a cikin jam’iyyar a daiden lokacin da ‘yan jam’iyyar Republican ke fara nuna damuwa game da zaben tsakiyar wa’adi na shekarar 2018.


Shin Trump ya dauki matakin dakile shiga kasar ba bisa ka’ida ba?

Harkar shige da fice ita ce Trump ya fi mayar da hankali akai a lokacin yakin neman zabe kuma ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa domin cika wanna alkwarin.

Daya daga cikin umarnin da ya fara rattaba hannu akai ya ayyana cewar Amurka za ta gina katanga kokuma wani shamaki wanda ba za a iya wucewa ba a kan bakin iyakan kasar da Mexico, wurin da ya ke da mil 650 na katanga.

Amman Mista Trump yana bukatar amincewar majalisar dokokin kasar kafin a fara ginin, kuma har yanzu bai samu amincewar ba. Ya hakikance cewar Mexico za ta biya kudin daga baya, duk da cewar shuwagabanninta sun fadi akasin hakan.

Duk da cewar Shugaba Trump bai sauya dokar shige da ficen Amurka ba tukunna, ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa biyu wadanda suka umarci jami’an shige da ficen kasar su dau tsatsaurar matakai kan aiwatar da dokokin da kasar ke da su.

Akwai wasu alamun da ke nuna cewar wannan sauyin yin aiki da dokar shige da fice -da kuma kakausar kalaman Shugaba Trump- za su iya rage yawan mutanen da ke son shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.

A watan Maris, yawan mutane da aka kama a lokacin da suke neman ketarawa zuwa Amurka ya fadi zuwa mataki mafi karanci cikin shekara 17, in ji Sakataren ma’aikatar tsaron cikin gidan kasar.

Mista Kelly ya ce faduwar yawan mutanen ba abin mamaki ba ne, kuma hukumar kula da shige da ficen kasar ta ce umarnin shugaban ya sauya salon yadda lamari ke tafiya.

Maganar sabon shugaban na dakile kwararar bakin haure ya sa ana tunanin bakin haure sun samu yadda suke so a karkashin Shugaba Obama, amman akwai dalilai da dama da ke nuna akasin hakan.

Tsakanin shekara 2009-2015 gwamnatin Obama ta kori fiye da mutum miliyan 2.5- yanwacinsu wadanda aka samu da nau’o’i na manyan laifuka ko kuma basu dade da zuwa kasar ba abin da ya sa wasu suka yi wa shugaba Obama lakabi da “shugaba mai korar baki.”

Amman kimanin bakin haure miliyama 11 ke zama a Amurka, yawancinsu daga Mexico.

Hukumar da ke aiwatar da dokar shige da fice da ta hana fasa kauri ta kaddamar da wasu jerin samame a fadin kasar tun da aka zabi Mista Trump, amman lokaci bai yi ba da za a iya yanke hukunci kan ko korar bakin haure ya karu ko bai karu ba.


Yaya tattalin arziki ke gudana a karkashin gwamnatin Trump?

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasa a shekara 2009, Amurka na cikin kariyar arziki mafi muni wanda ba taba samun irin sa ba tun shekarun 1930, inda tattalin arzikin ta rasa ayyuka 800,000 a watansa na farko.

Amman bayan faduwa kadan a shekarar, tattalin arzikin Amurka ta samu lokacin mafi tsawo na ci gaba inda ta fi samar da ayyukan yi. An samar da jumullar aikin yi miliyan 11.3 a karkashin Shugaba Obama.

A baya Mista Trump ya yi watsi da wadannan alkaluman a matsayin na boge, kuma bayan kaddamar da shi ya siffanta tattalin arzikin a matsayin abin da cikin rikici.

Amman a lokacin da aka fitar da wani rahoton wata-wata a watan Maris wanda ya nuna cewar an samu karin ayyuka 235,000 a watan Fabrairu, Sakataren yada labaran fadar White House Sean Spicer ya ce babban labari ne ga ma’aikatan Amurka.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 25 a cikin shekara 10 da kuma “zama shugaba mai samar da aiki mafi yawa da aka taba yi.”

Ya yi zargin cewar Mexico da China suna satan miliyoyin ayyuaka kuma ya sha alwashin “kawo ayyukan mu gida.” Amman abincike ya nuna cewar yawancin ayyukan kere-kere da suka salwanta a shekarun baya-bayannan an yi asararsu ne sabili da mashunan masana’antu kara samu kwarewar iya aiki da kansu, sabanin cewar hakan ya faru ne domin ayyuka sun fita waje ne.

Kasuwannin hannayen jari na Dow da S&P 500 da kuma Nasdaq sun kai matakan habaka irin wadanda ba a taba samu ba a makonnin farkon Shugaba Trump, wata alamar da ke nuna cewar masu zuba jari sun samu kwarin guiwa kan ayyukan ababen more rayuwar da Mista Trump ke son yi tare da zame hannun gwamnati daga tallafi da kuma rage harajin da ya ke son yi.

Amman habakar kasuwannin uku ta ragu a watan Maris a lokacin da aka fara tunanin garambawul din harajin ba zai faru da wuri ba yadda gwamnatin Trump ta fada.


Me gwamnatinsa ta yi kan kiwon lafiya?

Dole ne kiwon lafiya ya kasance wani fannin da za a fara gwada Shugaba Trump bayan ya yakin neman zabensa ya mayar da hankali kan batun.

Tsarin kiwon lafiya na Shugaba Obama ya taimaka wa fiye da Amurkawa miliyan 20 wadanda ba su da inshora a da domin samun inshorar lafiya- amman Trump ya sha alwashin cewar zai gaggauta soke dokar ya kuma maye ta da wata.

Daga baya ‘yan Republican sun gabatar da kudirin dokar samar da kiwon lafiyarsu a farkon watan Maris inda kakakin majalisar Wakilan kasar, Paul Ryan, ya siffanta shi a matsayin wani gagarumin garambawul na masu ra’ayin rikau.

Shugaba Trump ya goyi bayan kudirin, amman kudirin ya sami kakkausar suka daga hukumar kasafin kudin majalisar wadda ta ce zai kara Amurkawa miliyan 24 wadanda ba su da inshora zuwa shekarar 2026.

Gwanatin Trump ta ce ita ba ta yarda da bayanan hukumar kasafin kudin ta majalisar dokokin kasar ba, amman an yi fatali da kudirin ranar 24 ga wata Maris bayan ta kasa samun isasshen goyon baya daga ‘yan jam’iyyar Reuplican.

Wani yanayi ne na cin fuska ga Shugaba Trump da kuma jam’iyyar Republican, wadda ke shugabancin kasar da kuma jagorancin majalisun dokokin kasar a karo na farko cikin shekara 11.

Mista Trump ya yi iya kokrinsa na mantawa da kayen da kudirin ya sha, yana mai cewar gwamnatinsa za ta koma ta sake hada tsarin kiwon lafiyar bayan tsarin kiwon lafiyar ObamaCrea ta “fashe.”

Yayin da tsarin samar da lafiya na Obamacare ya fuskanci kalubale tun da aka kaddamar da shi a shekara 2010, bai nuna alamu masu yawa na faduwa nan gaba ba kuma bayanin hukumar kasasfin kudin majalisar dokokin kasar ya ce kasuwannin tsarin na kiwon lafiyar sun daidaita.

Wanna zai canza in Shugaba Trump da ‘yan jam’iyyarsa ta Republican suka dau matakin rage kudin tallafin tsarin, amma wanna zai kasance wani dabara mai hatsari gabannin zaben rabin wa’adi a shekara mai zuwa, musamman a lokacin da kuri’ar jin ra’ayin jama’a na baya-bayannan ke nuna cewar shirin Obamacare na kara samun karbuwa.

‘Yan Jami’yyar Republican sun dauki alkawarin samar da sabon tsarin kiwon lafiya bayan hutun Easter, amman babu tabbacin me nene ke cikin tsarin da kuma ko jam’iyyar za ta mara masa baya ko kuma tsarin zai samu isassun kuri’u damin ya zama doka.

Ba zan yi takarar shugaban Amurka ba – Michelle Obama


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Michelle Obama ta kira Trump da cewa “sabon shugaban kasa”

Mai dakin tsohon shugaban kasar Amurka Michelle Obama ta nuna yiwuwar ba za ta tsaya takarar shugabancin kasar ba a karon farko da ta fito bainar jama’a tun bayan fita daga fadar White House.

Mrs Obama, wacce ta fice daga ofis a lokacin da farin jinta a idon ‘yan kasar ya kai kashi 68 cikin (fiye da kashi goma kan mijinta) ta ce “siyasa na da matukar wuya.”

Ta bayyana haka ne a Orlando kwana kadan bayan Obama ya fito bainar jama’a a Jami’ar birnin Chicago karon farko tun bayan saukarsa.

“Komai zai rika tafiya daidai amma da ka soma takara za a yi ta sukarka.”

Ta ce hakan zai bai wa iyalinta wahala, tana mai cewa: “Ba zan bari ‘ya’yana su sake fuskantar matsala ba, saboda idan mutum yana takara ba shi kadai lamarin ke shafa ba har da iyalinka .”

Sai dai Michelle Obama ta ce bautawa al’uma shi ne kan gaba a rayuwarta.

An sallami jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu daga kurkuku


Hakkin mallakar hoto
Nnamdi Twitter

Image caption

Daya daga cikin sharudan ba da balin Nnamdi Kanu shi kar ya yi zanga-zanga

An saki jagororin masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga gidan yari bayan ya cika sharudan da wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta sanya masa.

A ranar Talata ne dai kotun, karkashin mai shari’a Binta Nyako, ta bayar da belin Mr Kanu saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sai dai ta sanya masa sharuda, wadanda suka hada da cewa ya gabatar da mutum uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

Mai shari’ar ta ce ba a yarda a gan shi a cikin taron jama’ar da suka wuce mutum 10 ba.

Ta kara da cewa “kar ya yi hira da ‘yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga”.

Wannan ne karon farko da aka bayar da belinsa tunda aka fara sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Mista Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, tare da wasu mutum uku, wadanda duka suka musanta zargin da ake yi musu.

Mista Kanu ya shafe sama da shekara guda a tsare.

Canjaras ya ishe mu zuwa gasar Zakarun Turai – Antonio Conte


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ya ce daukar kofin Premier ne babban burinsa a yanzu.

Kocin Chelsea ya ce samun nasara ko yin canjaras a wasansu da Everton ranar Lahadi zai tabbatar musu da samun gurbi a wasan Zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Ya kara da cewa “lokacin da muka fara wannan kakar wasa, burinmu shi ne samun gurbi a gasar Zakarun Turai mai zuwa.”

“Wannan shi ne burin kungiyar, da magoya bayanta, da kuma ‘yan wasan. Amma a yanzu muna matakin da muke fatan daukar kofin,” in ji Antonio Conte.

Ya ce hakan “kyakkyawan ci gaba ne amma kuma daukar kofin Premier ne babban burinsa a yanzu.”

Kocin na Chelsea ya kara da cewa a fili take cewa biyu daga cikin kungiyoyi shida tsakanin Chelsea, da Tottenham, da City, da Arsenal, da United, da kuma Liverpool, ba za su samu gurbi ba a gasar Zakarun Turai mai zuwa ba.

Yana wannan maganar ne, lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi kan wasansu na ranar Lahadi da Everton inda ya tabbatar da cewa duk ‘yan wasansa sun shirya wa wasan.

Ya ce Everton kyakkyawar kungiya ce, kuma mai karfi, tana da manyan ‘yan wasa a tawagarsu, kuma kungiya ce mai karfi.

An kama shinkafar waje ta miliyan hudu


Image caption

Manoman shinkafa suna kokawa da irin tasirin da fasa kaurin shinkafa ke yi kan harkarsu.

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya da ke kula da yankin jihar Kano da Jigawa ta ce ta kama wata tirela makare da shinka `yar waje da aka yi yunkurin fasa-kwaurinta zuwa Najeriya.

Kwanturolan yankin, Matias Abutu Onoja yace shinkafar kudinta ya kai fiye da naira miliyon hudu. A cewarsa an kama motar ne a kusa da Dutse hedikwatar jihar Jigawa.

Hukumar ta yi wannan kamun ne kwana biyu bayan zargin da kungiyar masu sarrafa shinkafa ta yi cewa ana fasa-kwaaurin shinkafa ta wasu iyakokin Najeriya da ke tudu.

Ko da wakilin BBC ya tambayi Konturolan kan me ya sa kamun na su na zuwa kwana biyu bayan masu noman shinkafa suka fara korafi kan fasa kaurin, sai ya ce su na kamun ne in har sun gano an shigo da kayan waje ba bisa ka’ida ba.

Ya ce hukumar tana neman masu shinkafar domin ta hukunta su.

Wannan na zuwa ne a lokacin da manoma ke kukan cewar fasa kaurin shinkafa na yi wa harkar su lahani.

Na dawo wa da Man Utd martaba da farin jininta – Mourinho


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mourinho ya zo Manchester United a watan Mayun 2016

Mourinho ya ce ya dawo wa da kungiyar farin jini, da martaba, da armashin da ta rasa a hannun tsohon kocinta Louis van Gaal.

Kocin ya ce sababbin ‘yan wasa da za su zo kungiyar a kakar wasa mai zuwa “za su taimaka wajen samun manyan nasarori.”

An kori Van Gaal ne a watan Mayun shekarar da ta gabata, bayan ya lashe kofin FA, amma kuma ya kasa kai kungiyar gasar Zakarun Turai.

A kakarsa ta farko a Old Trafford, Mourinho ya ci kofin kalubale, kuma ana sa ran zai kammala gasar Premier a matakin kungiyoyin hudun farko.

Ya kuma taimaka wa kungiyar kai wa wasan kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ta Europa, inda za ta kara da Celta Vigo.

Ya ce “Ina tunanin Mista Van Gaal ya bar kyakkyawar kungiya, wadda ‘yan wasanta ke da alaka mai kyau a tsakaninsu”.

Sai dai sun rasa farin ciki, sun rasa karsashi, da martaba, amma wannan abin da suka samu yanzu zai taimaka wa kungiyar.

“Idan muka kara hada kungiyar ranar 19 ga watan Yuli kungiyar za ta zama mai karfi. idan sababbin ‘yan wasan suka zo, kungiyar za ta shirya wa samun manyan nasarori”, in ji Mourinho.

Wasan da kungiyar ta tashi canjaras ranar Alhamis tsakaninta da City, ya kara wa kungiyar yawan wasannin da ba a doke ta ba zuwa wasa 24.

Manchester United wacce yanzu ita ce ta biyar a kan tebur, da ratar maki daya tsakaninta da City, wacce ke mataki na hudu, wadda ita kuma ke bayan Liverpool da maki biyu tare da kwantan wasa daya. Za ta kara da Swansea ranar Lahadi mai zuwa.

Shugabancin Amurka na ba ni wahala —Trump


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mista Trump ya yi alkawura da yawa a lokacin yakin neman zabe

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana kewar rayuwarsa ta baya kuma yana mamakin yadda sabon aikinsa a fadar White House ke ba shi wahala.

Mista Trump ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “yana kewar rayuwarsa ta baya soboda yana da abubuwa da dama da zai yi a wannan lokaci.”

Ya kara da cewa “wannan aiki na bani wahala fiye da rayuwata ta baya. Na yi tsammani aikin na da sauki”.

Kusan babu wani lokaci da ya fi dacewa Mista Trump ya bayyana halin da yake ciki sama da yanzu.

Ya ce ”Ina kewar rayuwata ta baya”.

Wani ya rubuta a shafin sada zumunta na Twitter cewa ”Na san yadda Mista Trump ke ji. Ni ma ina kewar rayuwata kafin a zabe ni.”

Jama’a da dama sun ta yi wa shugaban ba’a kan kalaman nasa.

Wasu kuma suka ce Mista Trump, wanda tsohon mai gabatar da shirin ne a Talbijin, na da abubuwa da yawa da zai koya.

A don haka suna ganin ya fadi gaskiya, kuma halayyarsa ta yin hakan abin koyi ne.

Akwai kuma wadanda suka yi tambayar cewa abu da zai zamo mai zafi ga Mista Trump shi ne idan wata rana majalisa ta yanke shawarar tsige shi saboda bukatunsa na kansa sun shiga harkokin gwamnati.

Nigeria: An 'ceto jarirai sama da 200 da aka zubar' a Lagos


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rahotanni sun ce ana yawan zubar da jarirai a Najeriya

Gwamnatin jihar Lagos a Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto jarirai 237 da aka zubar a sassa daban-daban na jihar.

Jarirn 106 maza ne, yayin da 131 kuma suka kasance mata, kuma an jefar da su ne a bara.

Jaridar Punch da Guardian, sun rawaito cewa, kwamishinan matasan jihar, Uzamat Akinbile-Yussuf, yana ganin cewa an kara samun yawaitar adadin jariran da aka tsinta a watannin baya-bayan nan.

Yara na baya-bayan nan da aka tsunta su ne guda 53 da aka zubar a kusa da wata bola a jihar.

Wani wakilin BBC a Najeriya ya ce akan jefar da jarirai ne saboda iyayensu talakawa ne ko kuma an haife su ne ba ta hanyar aure ba.

Lovren zai ci gaba da zama a Liverpool


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dejan Lovren ya buga wasa 28 a kakar wasa ta bana

Dan wasan Liverpool Dejan Lovren ya sanya hannu akan sabuwar kwantiragi wacce za ta bashi damar cigaba da zama a kulob din har zuwa shekara ta 2021.

Dan wasan mai shekara 27 ya koma Anfield ne daga Southampton a kan kudi fam miliyan 20 a shekarar 2014.

Lovren bai taka rawar gani a kakarsa ta farko ba, amma duk da haka ya buga wasa 105 inda ya zura kwallo hudu.

Dan kwallon na Crotia ya ce ”Ina ganin a yau ni ne mafi murna a duniya.”

Ya kara da cewa burina shi ne in dade a kulob daya da nake so kuma shi ne Liverpool.

Lovren ya buga wasa 28 a kakar bana.

Yana haskaka wa sosai a karkashin koci Jurgen Klopp kuma yana cikin ‘yan wasan da ake ji da su, inda ake hada shi da Joel Matip domin tsare baya.

A lokacin da yake hira da shafin intanet na ya ce ”Bayan duk abin da ya faru a kaka biyu da ta gabata, ina ganin na fi kokari a kakar farko. Kulob din ya amince da ni, haka kuma magoya bayanmu.”

Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gidajen kallo na da farin jini sosai a Najeriya

Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta ce za ta girmama magoya bayanta da suka mutu bayan turken wutar lantarki ya fada kansu a lokacin da suke kallon wasa a birnin Calabar na jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, United ta ce ‘yan wasanta za su daura wani bakin kyalle a hannayensu a wasan da za su yi ranar Lahadi “domin tunawa da magoya bayanmu bakwai da suka mutu a kwanakin baya a Calabar da ke Nigeria.”

A lokacin da lamarin ya faru, wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya kirga gawar mutum 16, yayin da wasu rahotanni ke cewa wadanda suka mutu sun haura 30.

Amma mai magana da yawun ‘yan sandan Cross River, Irene Ugbo, ta shaida wa BBC cewa mutum bakwai ne suka mutu yayin da mutum 10 suka jikkata.

Lamarin ya faru lokacin da jama’a suka taru suna kallon wasan Europa tsakanin Manchester United da Anderletch.

A sakon da ya aike na ta’aziyya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kadu kwarai da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka.

Hakkin mallakar hoto
Manchester United

Image caption

United ta ce tana alhinin rasuwar magoya bayanta na Najeriya

Rahotanni sun ce gidan kallon ya cika makil da mutane a lokacin da babban layin wutar ya katse, inda ya fado kan jama’a.

Anthony Sunday ya ce “Ni da kaina na kirga gawarwaki sun kai 16, kuma jama’ar da ke wurin sun gaya min cewa adadin zai haura 31”.

Mista Sunday ya kara da cewa jim kadan bayan lamarin sai wurin ya rikide inda jama’a suka rinka gudu domin neman mafita.

An rinka zuba gawarwaki da wadanda suka samu raunuka a motar ‘yan sanda, in ji shi.

A karon farko malamai mata sun yi fatawa kan auren wuri a Indonesia


Hakkin mallakar hoto
BBC Indonesia

Image caption

Taron ya hada jagororin mata Musulmai daga kasashe da dama

Manyan malaman addinin Musulunci mata sun gabatar da wata fatawa a kasar Indunisiya a kan aurar da kananan yara.

An gabatar da fatawar ne a karshen taron kwana uku da malamai mata a kasar suka gudanar, sai dai dokar ba ta zama wajibi a yi amfani da ita ba.

Malaman sun bukaci gwamnati da ta mayar da mafi karancin shekarun da za a yi wa mace aure su zama 18, ba shekara 16 ba kamar yadda suke a yanzu.

Mafi yawancin ‘yan kasar Indunisiya Musulmai ne, kuma tana daya daga cikin kasashen da suke yawan aurar da kananan yara a duniya.

A cewar ofishin kula da kananan yara na Majalisar dinkin duniya, kashi daya ckin hudu na matan kasar ana aurar da su ne kafin su kai shekara 18.

An gabatar da taron ne a birnin Cirebon a kan tsibirin Java, wannan ne karo na farko da malaman addinin Musulunci mata suka shirya taro.

Mafiya yawan wadanda suka halarci taron ‘yan kasar ne, sai dai an samu halartar wasu daga kasar Pakistan, da Saudiyya da ma sauran wasu kasashe.

Ana gabatar da Fatwa a kasar akai-kai, sai dai galibi majalisar malaman kasar ce suke gabatarwa, wacce ita ce hukuma ta koli a harkokin addinin Musuluncin kasar kuma dukkansu maza ne.

Fatawar ta kira aurar da kananan yara a matsayin “cutarwa” kuma ya zama dole a hana yin hakan.

Ninik Rahayu, wacce ita ce ta shirya taron, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Malamai mata sun san al’amuran da suka shafi mata da kuma abubuwan da suke kawo wa mata cikas, ba za mu jira har sai gwamnati ta zo ta kula da wadannan yara ba, muma za mu iya daukar mataki.

Malaman sun yi nazari inda suka gano cewa, yawancin kananan yaran da ake musu aure ba a barinsu su cigaba da karatunsu da sun fara sai ayi musu aure, daga karshe kuma a sake su.

Batun aurar da kananan yara na daya daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron, sauran sun hada da yi wa mata fyade da kuma lalata muhalli.

Gwamnatin Afghanistan za ta dandana kudarta – Taliban


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Sojojin Afghan na fama da masu tada kayar baya na Taliban

Kungiyar Taliban ta bayar da sanarwar shiga lokacin kakar yake-yake, kwanaki kadan bayan mummun harin da suka kai wa dakarun Afghanistan.

Kungiyar ta ce za ta mai da hankali ne akan ”sojojin kasashen waje” kuma za’a kai hare-haren ne ta hanyoyi daban-daban da suka hada da yakin sunkuru da kunar bakin wake da kuma amfani da sojoji.

Har yanzu kasar ba ta gama murmure wa daga harin da aka kai wa barikin rundunar sojoji a makon jiya ba.

Ga bayanai da jami’ai suka fitar, masu tada da kayar bayan su 10 ne suka shiga sansanin horar da sojoji a Mazar-e Sharif inda suka kashe akalla sojoji 135.

Wasu rahotanin sun nuna cewa yawan wadanda suka mutu ya haura hakan.

Ministan tsaron da shugaban rudunar sojoji ta kasar sun yi murabus bayan da aka kai harin.

Taliban ta yi barazanar cewa sojojin kasashen waje da ma na gwamnatin Afghanistan za su dandana kudarsu.

‘Yan taliban sun ce kakar yake-yake ta wannan shekara za a sa mata suna Operation Mansouri domin tuna wa da shugabansu da Amurka ta kashe a wani hari ta sama.

Bahubali 2: Fim ɗin da aka jima ba a yi kamarsa ba


Image caption

An jima ba a kashe wa fim din India kudi kamar Bahubali 2 ba

A ranar Juma’a ce aka fitar da wani shahararren fim ɗin Bollywood a kasar Indiya mai suna Bahubali kashi na biyu.

Fim ɗin Bahubali na 2 tun kafin fitarsa, ya ja hankalin mutane ciki har da wadanda ba su damu da kallon fina-finan Indiya ba.

Tun a ranar Alhamis, aka fara nuna wannan fim a Amurka.

Shi ne irinsa na farko da aka kashe makudan kuɗaɗe wajen shirya shi, saboda haka ne a kusan ko’ina duniya ake maganarsa.

A Indiya kadai, za a nuna shi a Silimu sama da 6,500 cikin manyan yaruka daban-daban na kasar, babu wani fim da ya taɓa samun irin wannan tagomashi a tarihin Bollywood.

Fim ɗin, ci gaba ne daga Bahubali kashi na ɗaya, wanda ya fita a shekarar 2015, kuma ya samu karɓuwa sosai a duniyar fina-finai.

Sharhi, Aisha Shariff Baffa

Babban dalilin da ya sa Bahubali na biyu ya samu karɓuwa a wajen mutane shi ne yadda ya yi tsokaci cikin sha’anin masarauta.

Ya fito da irin kutungwila da maƙarƙashiyar da ke da alaƙa da neman mulki a wajen wasu. Bayan kashe wani sarki a fim ɗin na Bahubali, sai kuma ake yunƙurin kashe ɗansa.

Abin da mutane ke son gani a kashi na biyu shi ne, dalilin da ya sa babban na hannu daman sarkin, ya ci amanar sarki ta hanyar kisan gilla.

A Nijeriya, masu sha’awar fina-finan Indiya ba a bar su a baya ba, inda suka shiga sahun masu alla-alla su ga fitowar Bahubali na biyu da ke faɗin duniya don kashe kwarkwatar idanunsu a wannan fim.

Me ya sa 'yan Nigeria ke azarɓaɓin zuwa Turai ci-rani?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Yan ci-rani kan shafe kwanaki suna tafiya a cikin Sahara da teku don tsallakawa zuwa Turai

‘Yan Nijeriya na daga cikin ƙasashen da hukumar kula da masu ƙaura ta ce na kan gaba-gaba cikin mutanen ƙasashen duniya da ke rawar jikin zuwa Turai don ci-rani.

Wakilin BBC Martin Patience ya gano cewa akasarin masu tafiya ci-rani daga Nijeriya na sanya ɗan-ba ne a jihar Edo.

Kelvin Emeson ɗan Nijeriya ne da aka izo ƙeyarsa daga Libya bayan jirginsu ya nutse a cikin teku, inda ruwa ya ci ‘yar’uwarsa Augustina.

Ya ce jazaman ne na tari aradu da ka don cim ma burina na shiga Turai.

A cewarsa Augustina ma’aikaciyar jinya ce da ta yi aiki a wani ƙaramin asibiti don haka kuɗin da take ɗauka bai taka kara ya karya ba.

Mahaifiyarsu Charity wadda ta ce ba ta san lokacin da ‘ya’yanta suka yanke shawarar yin wannan tafiya mai hatsari ba.

Mace mai ƙaramin ƙarfi don haka su Kelvin ke fafutukar neman hanyar samun kuɗin shiga don tallafa wa kansu da mahaifiyarsu.

A bana kadai, ‘yan ci-rani masu yunƙurin zuwa ƙasashen Turai sama da dubu 40 ne suka tsallaka tekun Baharrum – kuma da yawa cikinsu ‘yan Nijeriya ne.

Alkaluman da hukumar kula da ƙaura ta duniya ta fitar sun ce baya ga ‘yan ƙasar Syria da Afghanistan, ‘yan Nijeriya a yanzu sun dauki wani kaso mai yawa da ke ƙoƙarin yin bulaguro zuwa Turai.

Da yawa daga cikinsu sukan je Turai ne don neman aiki da rayuwa mai inganci – duk da yake, kasarsu ba ta fuskantar wani rikici.

Wani mai fataucin masu zuwa Turai a Edo, Friday Egwadoro ya ce ƙarancin karatu ne ya sanya shi shiga wannan harka.

Ya ce karon ƙarshe da ya yi fataucin wasu zuwa Libya ya ci karo da wasu ɗalibai da suka kammala digiri su uku a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani Turai.

Sheikh Ja'afar: 'Ku fayyace gaskiya 'yan sanda'


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN SENATE

Image caption

Batun dai ya taso ne bayan shekara goma da kashe Sheikh Ja’afar Adam a Kano

Sanata Danjuma Goje ya buƙaci rundunar ‘yan sandan ƙasar, ta fito ta bayyana gaskiya kan mutanen da suka kashe malamin addinin musulunci Sheikh Ja’afar Muhd Adam.

Shugaban kwamitin kasafin kuɗi a majalisar dattijan Nijeriya, sanata Danjuma Goje ya ce ya yi wannan kira ne saboda yadda ake ƙoƙarin goga masa kashin kaji.

Ya ce “amma na haƙiƙance ba ni da wani alaƙa da takardar da ta shafi wai yadda Shekarau ya tsara halaka marigayi Sheikh Ja’afar…”

A cewarsa “‘Yan sanda, kamata ya yi su fi kowa shinin wa ya kashe Sheikh Ja’afar. Wa ya tsara.”

Sanata Goje na mayar da martani ne a kan bayanin da rundunar ‘yan sandan ta yi game da kuɗi da takardun da ta gano yayin samamen da ta kai gidansa.

‘Yan sanda sun ce a cikin takardun akwai wani fayel mai ɗauke da rubutu a kan kashe Sheikh Ja’afar Adam a Kano, har ma sun ambaci sunan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tuni dai wannan bayani ya janyo gagarumin ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta a tsakanin ‘yan Nijeriya.

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci yayin sallar asubah a Kano.

Danjuma Goje dai ya ce bayanin ‘yan sanda wani yunƙuri ne kawai na shafa masa kashin kaji “don a cuce ni.”

Ya ce yana wannan magana ce don ya lura da yadda ake son ɓata masa suna. “A manna mini abin da ba gaskiya ne a jikina ba.”

Ya zuwa yanzu dai ba a ji martanin da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya mayar game da batun ba.

Al'ummar Kano na fama da ƙamfar ruwan sha


Hakkin mallakar hoto
TOMMY TRENCHARD / IFRC

Image caption

Al’ummar birnin Kano na kokawa da matsalar karamcin ruwan sha da ta addabesu shekara da shekaru

Al’ummar birnin Kano sun auka cikin matsalar ƙarancin ruwan sha, inda unguwanni da dama suka koma amfani da ruwan rijiya da na famfon tuƙa-tuƙa.

A lokuta da dama waɗannan kafofi ba su da ingantaccin tsafta don haka akwai kasadar yaɗuwar cutukan da ake bazuwa ta hanyar ruwa.

Wani magidanci Malam Hamisu a unguwar Agadasawa ya ce suna matsalar ruwan sha sosai duk da yake akwai kawunan famfo.

Ya ce “sai mu shekara ruwa(n famfo) bai zo mana unguwar nan ba. Ya ce muna sayen ruwa ne daga masu kurar ruwa kuma suna sayar da jarka ɗaya kimanin Naira 30.”

A cewarsa, ɗawainiyar ta yi yawa. “Ina da mata ɗaya da yaro shida.”

Shi ma wani Rabi’u ya ce matsalar ƙarancin ruwan ta yi tsanani don kuwa sukan niƙi-gari zuwa wasu unguwanni don taro ‘yan ga-ruwa.

Kasuwar ‘yan ga-ruwa ta buɗe

Wani mai gidan sayar da ruwa mai suna Buhari a yankin Ƙofar Nassarawa ya ce suna matuƙar ciniki, ya ce a rana yakan sayar da ruwa na kimanin naira dubu uku zuwa sama.

Shi ma wani ɗan ga-ruwa, Malam Abdu Ƙyaure ya ce yana kai ruwa unguwannin da suka haɗar da Sabuwar Ƙofa da Sharaɗa da ƙofar Nassarawa da kuma Sokoto road.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, Alhaji Sule Riruwai ya ce na’urorin tura ruwa da ake da su zuwa birnin Kano na buƙatar gyara.

Ya ce a cikin na’ura takwas da ake ita a Kano, guda uku ne kacal ke aiki wurjanjan. Ko da yake, nan da mako uku za su kammala gyare-gyare.

Kwamishinan ya kuma zargi masu aikin kwasar yashi a koguna da karkatar da akalar ruwa saboda aikace-aikacensu.

Barcelona za ta kai karar shugaban Malaga kan kalaman batanci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona da Real Madrid suna da maki daidai a saman teburin La Liga

Barcelona za ta kai karar shugaban kungiyar Malaga Abdullah Al-Thani ga hukumomin wasan Spaniya kan kalaman batanci da tace ya yi mata a Twitter.

Ce-ce-ku-cen ya fara ne lokacin da wani mai goyon bayan Barca ya bukaci Al- Thani a shafin Twitter, kan Malaga ta doke abokan hamayyarsu Real Madrid a wasansu na ranar 21 ga watan Mayu.

Daga nan ne sai shugaban na Malaga ya mayar da amsa inda ya rubuta cikin Larabci ; “Da taimakon Allah za mu doke su a fili, amma dattin kumfar Catalonia (ma’ana Barcelona) ba za ta ji kanshin kofin ba, bayan karyar da ta yi a kan koci Michel,”.

Shi dai kociyan Malaga Michel ya harzuka magoya bayan Barcelona ne inda ya nuna cewa yana son Real Madrid ta dauki La Liga.

A wata sanarwa da Barcelonan ta fitar ta ce ta nuna rashin yardarta da bacin rai a kan kalaman da shugaban Malaga, Abdullah Al-Thani, ya rubuta a Tweeter, wadanda sun saba wa manufar wasan cikin lumana da kuma dokokin wasanni.

Barca ta kara da cewa: “A bisa wannan dalili ne kungiyar za ta gabatar lamarin kwamitin yaki rikici na hukumar wasanni, sanna kuma ta mika batun zuwa ga hukumar kwallon kafa da ta gasar La Liga.”

Zakarun na Spaniya, Barcelona da Real Madrid suna kankankan a maki a La Liga, amma Barcan na gaba saboda nasarar da ta fi samu a kan Real din wadda take da kwantan wasa daya.

A ranar karshe ta La Liga, 21 ga watan Mayu, yayin da Real za ta je gidan ta 14 a tebur Malaga, Barcelona za ta kasance a gidanta da Eibar wadda yanzu take ta takwas.

Kocin Malaga Michel ya taimaka wa Real Madrid ta dauki kofin La Liga sau shida a shekara 14 da ya yi a Bernabeu.

An tashi wasan Man City da Man United ba armashi


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Marouane Fellaini ya samu jan katinsa na uku a Premier kuma na biyu a Manchester United

Manchester United ta ci gaba da zama a matsayinta na biyar a teburin Premier bayan wasanta da abokiyar hamayyarta Manchester City, wanda suka tashi ba ci a Etihad, amma an kori Fellaini.

United tana da maki 64 a wasa 33 yayin da Manchester City ta hudu a tebur take da maki 65, ita ma a wasa 33.

Saura minti shida a tashi daga wasan alkalin wasa ya kori Marouane Fellaini, wanda bai dade da samun katin gargadi ba saboda keta da ya yi wa Aguero, bayan da ya sake yi wa Sergio Aguero karo.

United wadda take maki biyu a bayan Liverpool ta uku da kwantan wasa daya, ta yi wasa 24 kenan na Premier ba tare da an doke ta ba.

Wasanta biyu daga cikin biyar da suka rage za ta yi su ne a waje, a gidan Arsenal ranar 7 ga watan Mayu da kuma gidan Tottenham ranar 14 ga watan Mayu.

Manchester City wadda za ta gama kakar farko da Pep Guardiola ba tare da kofi ba tana maki daya tsakaninta da Liverpool, amma tana da kwantan wasa daya

Fifa ta ci tarar Brazil da Argentina da Mexico kan kyamar 'yan luwadi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fifa ta ci tarar kasashe da dama a kan amfani da tartsatsin wuta da wakokin kyamar masu neman jinsi daya a filin wasa

Fifa, ta ci tarar hukumomin kwallon kafa na Brazil da Argentina da Mexico a kan samun magoya bayansu da laifin wakokin kyamar masu neman jinsi daya a lokacin wasannin neman zuwa gasar Kofin Duniya na 2018.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta ci tarar Brazil fan 27,248 yayin da ta ci tarar Argentina 15,565, sannan ta ci tarar Mexico fan 7,781.

Fifa ta ce tarar ta wanna laifi ne na rera wakokin tsanar masu neman jinsi daya da kuma sauran abubuwa na rashin da’a da ‘yan kallonsu suka yi.

A sanarwar da ta fitar Fifa din ta ce, sun aikata laifin ne a lokacin wasannin baya-bayan nan na neman tikitin zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2018, amma ba ta fayyace wadanna wasanni ba ne.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Albania Fifa ta ci tararta fan 77,945 bisa laifuka da dama da magoya bayan kungiyar wasan kasar suka yi a lokacin wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya da Italiya ta doke su a gidanta ranar 24 ga watan Maris.

Laifukan sun hada da jefa abubuwan tartsatsin wuta cikin fili, lamarin da ya kai ga tsayar da wasan na wasu mintina.

Ita ma Iran an ci ta tararta fan 39,015, saboda magoya bayanta sun yi amfani da abubuwan tartsatsin wutar a filin wasan da ke makare da ‘yan kallo lokacin wasansu da China.

Su ma kasashen Bosnia da Herzegovina da Poland da kuma Montenegro Fifa ta ci tararsu saboda ‘yan kallonsu sun irin wannan laifi na amfani da abubuwan tartsatsin wuta a filin wasa.

Tsohon dan wasan Gabon Moise Brou Apanga ya mutu a fili


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Moise Brou Apanga ya yi wa Gabon wasa 33 da suka hada da na gasar cin Kofin Afirka karo biyu

Hukumar kwallon kafa ta Gabon ta bayar da sanarwar mutuwar da wasan baya na kasar Moise Brou Apanga sakamakon bugun zuciya.

A sanarwar da hukumar ta bayar ta rasuwar Apanga, mai shekara 35, ta ce ya rasu ne a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta yanzu Canon de Libreville, ranar Alhamis.

Dan wasan bayan haifaffen kasar Ivory Coast ya yi wasa a Turai a kungiyar Brest ta Faransa da kungiyoyin Perugia da Brescia na Italiya, bayan ya fara wasansa na kwararru a Romania.

Ko da yake an haifi Brou Apanga a Ivory Coast amma lokacin da ya fara zuwa kungiyar tasa ta yanzu Canon de Libreville ko FC 105, kociyansu na lokacin Alain Giresse ya shawo kansa ya koma dan kasar Gabon.

Daga nan ne kociyan da Faransa ya fara sa shi a wasan kungiyar kasar ta gabon a shekarar 2007, kuma ya taimaka masa ya tafi kungiyar Brest.

Apanga ya yi wa Gabon wasa a gasar cin Kofin Kasashen Afrika a shekarar 2010 da 2012.

Kyaftin din Gabon Pierre Emerick Aubameyang ya bayyana ta’aziyyarsa ta rashin dan wasan a shafinsa na Twitter, inda ya ce ”mun yi wasa tare, mun kuma kara a wasa a kungiyoyinmu daban-daban, amma abin farin ciki ne kasancewa tare da kai a ko da yaushe, Allah Ya jikanka dan uwana.

El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin Buhari -Tinubu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bola Tinubu na cikin wadanda suka mara wa Buhari baya a zaben 2015

Daya daga cikin shugabannin jam’iyya mai mulki a Najeriya kuma tsohon gwamnan Lagos, Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki, da kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ne suka hana shi zama mataimakin Shugaban buhari.

Jaridar Punch ta ambato littafin da babban editan Jaridar This Day, Olusegun Adeniyi, ya rubuta mai suna ‘Against The Run of Play’ yana cewa Tinubu ya ce ‘yan siyasan biyu suka hana shi zama abokin takaran Shugaba Buhari a zaben 2015.

A cewar Tinubu, El-Rufai da Saraki sun yi ta nanata wa Buhari da kuma ‘yan jam’iyyar cewar idan aka hada ‘yan takara Musulmai biyu, jam’iyyar ba za ta kai labari a zaben ba.

Tsohon gwamnan na Legas ya ce sun kaddamar da kamfae din hana shi zama abkoin takaran Buhari ne a boye duk da cewar duk abubuwan da jam’iyyar ke yi ana yin su ne a idon kowa.

Ya ce Nasir El-Rufai ya so Buhari ya dauko Pasto Tunde Bakare wanda ya yi abokin takaran Shugaba Buhari a zaben 2011 a karkashin jam’iyyar CPC.

Tinubu ya ce shi janye daga zama abokin takaran ne domin ya mika sunan farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ya taba ambata wa shugaban a shekara 2011.

Wannan labarin ya kara haske kan irin abubuwan da suka wakana a lokacin da ake neman wanda zai zama abokin takaran Muhammadu Buhari gabanin zaben 2015.

Duk da haka Bukola Saraki ya ambato ‘hana wasu zama abokin takaran Buhari’ a matsayin daya daga cikin laifukan da suka aka gurfanar da shi a gaban kotun da’ar ma’aikata a shekarar 2016.

Kawo yanzu gwamnan Jihar Kadun abai ce komai ba game da labarin.

An yi gasar ɓaunar da ta fi kyau a Pakistan


Hakkin mallakar hoto
WIKIMEDIA/JUGNI

Image caption

Hausawa na yi wa bauna kirari na saniyar sake

Akalla ɓauna 200 aka tara domin gudanar da gasar wacce ta fi kowacce kyau a kasar Pakistan.

Jaridar Dawn newspaper ta kawo rahoton cewa manoma da makiyaya ne suka hallara a birnin Mingora, babban birnin gundumar Swat da ke arewacin Pakistan, a wani taro da aka gudanar na kwana uku domin bunkasa harkar kiwo.

Taron, wanda hukumar raya kasashe ta Amurka USAID ta shirya, kuma hukumar bayar da agaji ta farar hula ta kasar ta sanya tsabar kudi naira 75,000 ga wacce ta zo ta daya.

Laiq Badar ne ya samu nasarar samun kudin, wanda ya nuna farin cikinsa da samun nasarar da baunarsa ta yi inda ya shaida wa jaridar Dawn da cewa, “Ina da bakane goma da nake kiwonsu a wuri daya wadanda su ne hanyar da nake samun abin biyan bukatuna na yau da kullum.

Wani jami’in hukumar kula da dabbobi Muhibullah Khan, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Pakistan APP cewa, kiwon bauna na da fuskoki nau’i-nau’i, kuma babbar manufar wannan taron shi ne, “wayar da kan jama’a da kuma nunawa mutane muhimmancin kiwon wannan kyakkyawar dabba.”

Wannan ne karo na farko da aka taba gabatar da gasar baunar da tafi kowacce kyau a Pakistan.

A yankin Swat kawai ake samun baunar, kuma an ce a yankin ne kawai ake samun sanyi da za a iya kiwonsu a wurin, saboda haka ne masu dabbobin ba sa sayar da su ko yankawa idan lokacin sanyi ya karato.

A cewar jaridar, wadanda suka kware a gasar ta garin Mingora sun ce ba ya ga kyau da dabbobin suke da shi, suna samar da madara da kuma wadataccen nama.

Gerrad zai yi kociyan matasan Liverpool


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Steven Gerrard (a hagu) ya koma Anfield a matsayin kociyan matasa a farkon 2017

Tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya ce lokaci ya yi da zai matsa gaba ya yi kocin kungiyarsa, bayan an tabbatar masa cewa zai horad da yi kociyan ‘yan wasan kungiyar ‘yan kasa da shekara 18.

Tsohon kyaftin din na Ingila, wanda ya yi wa Liverpool wasa sau 710 a cikin shekara 17 da ya yi zai maye gurbin Neil Critchley, kociyan ‘yan kasa da shekara 18 din, wanda shi kuma zai kula da kungiyar ‘yan kasa da shekara 23.

Gerrard, mai shekara 36, ya koma Liverpool ne a matsayin kociyan matsa a watan Fabrairu bayan da ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa a shekarar da ta wuce.

A lokacin da yake wasa a Anfield, Gerrard ya ci kwallo 186 kuma ya taimaka wa kungiyar ta dauki manyan kofuna takwas, da suka hada da Kofin Zakarun Turai na 2005, lokacin da kwallon da ya ci a wasan karshe ta ba wa kungiyarsa kwarin guiwa ta farfado ta doke AC Milan.

Bayan ya bar Liverpool a karshen kakar 2014-15 , ya koma LA Galaxy ta Amurka, inda ya ci kwallo biyar a wasa 34 a kaka biyu da ya yi kafin ya yi ritaya.

Haka kuma ya yi wa Ingila wasa 114, inda ya yi 38 a matsayin kyaftin, abin da ya sa ya zama na hudu a wadanda suka buga wa Ingila wasa.

FA ta ce karamin hukunci ta yi wa Barton


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barton ya soki hukumar kwallon kafa ta Ingila kan abin da ya ce dogaro da take yi da kamfanonin caca

Hukumar kwallon kafa ta ingila ta ce dakatarwar wata 18 da ta yi wa dan wasan Burnley Joey Barton, daga shiga duk wasu harkokin kwallon kafa, shi ne mafi karancin hukuncin da za ta yi masa, bayan da aka same shi da laifin caca.

A bayanan da hukumar ta gabatar a rubuce na dalilin da ta yi masa hukuncin a ranar Laraba, hukumar ta ce Barton ya yi caca sau 1,260 da ta kai ta fan 205,172, inda ya rasa fan 16,708.

Dan wasan na tsakiya na Burnley mai shekara 34 ya amince da saba dokokin hukumar wasan na shigar ‘yan wasa caca, yana mai cewa caca ta zama jiki ne a wurinsa.

Hukumar ta FA ta lamunta da mawuyacin halin da dan wasan ya samu kansa ciki, musamman ganin cewa caca ta ratsa ko ina a wasanni.

Kuma ta ce ta yarda cewa Barton ba wai yana shiga cacar ba ne domin ya samu kudi, abin ta ce wannan shi ya rage girman laifin nasa.

Obama da Jega ne suka kayar da ni a zaben 2015 – Jonathan


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jonathan ya ce Obama ba ya son ya ci gaba da mulkin Najeriya

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ne suka sa ya sha kaye a zaben 2015.

Mista Jonathan ya bayyana haka ne a cikin wani littafi mai suna Against The Run of Play wanda fitaccen mai sharhi a jaridar This Day Olusegun Adeniyi ya wallafa.

Ya ambato tsohon shugaban na Najeriya na cewa Shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama da jami’an gwamnatinsa sun bayyana masa karara cewa suna son sauyin gwamnati a Najeriya kuma za su iya yin komai domin cimma hakan.

Ya kara da cewa hakan ne ya sa ma suka turo jirgin ruwa yaki a gabar tekun Guinea domin nuna masa da gaske suke yi.

Mista Jonathan ya ce ba anan kadai Amurka ta tsaya ba wajen yunkurin kifar da gwamnatinsa, har ta kai Shugaba Obama ya shawo kan firaministan Burtaniya David Cameron ya mara masa baya duk da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Jonathan da Cameron.

Tsohon shugaban ya ce bai fahimci irin yadda Amurka ta himmatu wajen tumbuke shi daga kan mulki ba sai da ta sa shugaban kasar Faransa Faransuwa Hollande shi ma ya bi sawunsu ana makonni kafin a yi zabe.

A cikin gida kuma, tsohon shugaban ya ce shugaban hukumar zabe na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya yi masa abin da bai yi tsammani ba, saboda har yanzu nan ya kasa fahimtar abin da ya sa Jegan ya nace cewar ya shirya wa yin zabe lokacin da kashi 40% bisa dari na masu zabe ba su karbi katinsu na zabe ba.

Ya ce ya gana da shugaban hukumar zabe ya bayyana masa damuwarsa kan yi zaben a watan Fabrairun 2015, amma ya kafe cewar ya shirya wa zaben domin Amurkawa sun ingiza shi abin da ba za taba yi a kasarsu.

Mr Jonathan ya ce hatta shugaban jam’iyyarsa ta PDP a wancan lokacin Ahmad Adamu Mu’azu ya bi sahun masu kulla masa makirci, domin saboda dalilai wadanda Mu’azun kadai ya sani, ya yi masa zagon kasa domin ‘yan adawa su samu nasara kansa.

Ya kara da cewar lalle ya ji an yi masa zamba cikin aminci lokacin da ya ga irinsa sakamakon da ke fitowa daga jihohin arewa inda watakila saboda dalilai na kabilanci har jami’an tsaro suka hada baki da ‘yan adawa aka fitar wani sakamakon zabe na karya kansa.

Da marubucin ya tabo masa maganar almundahana da ake zargin ta yi katutu a lokacin mulkinsa sai Mista Jonathan ya yi watsi da zargin a zaman jita-jita kawai wadda ‘yan adawa, da kungiyoyin farar hula suka kururuta ta kafafen watsa labaran kasar.

Ya ce ya kafa kwamitoci hudu domin bincikar zargin da ake yi wa ministarsa ta mai Diezani Alison-Madueke, inda aka samu sabani tsakanin wasu shugabannin kwamitocin, wato Nuhu Ribado da Steve Aronsanye.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Goodluck Jonathan ne shugaba mai ci na farko da ya fadi zabe a Najeriya

Mista Jonathan ya ce ta ya ya za a yi ya yi aiki da rahoton wadanda suka kawo shi ke jayayya da juna.

Tsohon shugaban ya ce yana bakin cikin yadda ake yi wa mai dakinsa bita-da-kulli kuma shi ba zai je wata kasar waje ya ce ‘yan Najeriya sun fi kowa tafka cin hanci ba domin hakan ba zai yi wata rana ba, kuma idan ya ce haka kenan har da shi.

‘Yan Boko Haram sun daga wa Buhari kafa

Dangane da yaki da Boko Haram kuma ya ce ya yi iya kokarinsa da sojoji wajen murkushe ta.

A cewarsa a lokacinsa, mayakan Boko Haram na fada ne da gwamnatin kafiri, amma yanzu dole suka kwance damara domin ba za su iya kiran Buhari kafiri ba, kuma suna jin yanzu nasu ne a wajen.

Tuni dai fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa domin mayar da martani ga wasu daga cikin kalaman Mr. Jonathan a cikin wannan littafin inda ta ce Shugaba Buhari bai yi wa kowa bi-ta-da-kulli a yakin da rashawa illa dai kawai ya kan bar doka ta yi aiki kan kowa.

Shi ma ofishin jakadancin Amurka a Najeriya cewa ya yi zaben da aka yi shugaba Muhammadu Buhari zabi ne da nuna abin da ‘yan Najeriya ke so.

Shi kuwa tsohon shugaban jam’iyyar PDP Ahmad Adamu Mu’azu ya shaida wa marubucin littafin cewa ya kasa yarda cewa Mr Jonathan zai yi masa irin wannan zargin wanda ya kira maras tushe balle makama.

Adamu Mu’azu ya ce amma yana ganin laifinsa shi ne wasu sun bukace shi da ya zagi Buhari lokacin yakin neman zabe ya ki don inji shi ba a yi masa tarbiyyar zagin mutane ba musamman manya.

Man City za ta gane kurenta kan Pellegrini


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pep Guardiola (a hagu) ya dauki kofi uku-uku na gasar lig da Barcelona da kuma Bayern Munich

Halin da Manchester City ta samu kanta a ciki karkashin kociyanta Pep Guardiola ya nuna cewa kungiyar ba ta darraja tsohon kociyanta Manuel Pellegrini ba, in ji tsohon dan bayanta Martin Demichelis.

Tsohon dan wasan na Manchester City ya ce, idan aka duba halin da City take ciki a yanzu za a ga cewa ba wai kawai don kana da kwararren kociya sai ka samu komai cikin sauki ba.

Demichelis ya kara da cewa sannu a hankali kowa zai mutunta aikin da Manuel Pellegrini ya yi Manchester City.

A shekararsa ta farko a Manchester City bayan da ya dawo daga Malaga a watan Yuni na 2013, Pellegrini ya dauki kofin Premier da na Lig.

Ya kuma jagoranci City ta kammala a matsayin ta biyu a tebur, a bayan Chelsea a kaka ta gaba, ya kuma jagoranci kungiyar zuwa wasan kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai kafin kwantiraginsa ya kare a bazarar 2016.

Demichelis ya ce a matsayin Pellegrini na kociya dan kasar waje, a ce ya je Ingila ya dauki kofin Premier a shekarar farko, wannan ya nuna muhimmancinsa.

Bayan Manchester City Demichelis, ya kuma yi wasa karkashin jagorancin Pellegrini a kungiyar River Plate da Malaga.

Yayin da ya rage wasa shida a kammala Premier bana City ke maki 11 a bayan Chelsea ta daya a tebur, abu ne mai wuya Guardiola ya kwatanta nasarar da Pellegrini ya cimma.

Yanzu dai ta tabbata a karon farko a aikinsa na kociya Guardiola zai kare wata shekara ba tare da ya dauki wani kofi ba

China na amfani da fatar jaki a magunguna


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana fargabar raguwar jakuna a duniya

Wata sabuwar kasuwar bayan fage ta fatar jaki ta fara bunkasa a daidai lokacin da kasuwancin hauren Giwa da aka haramta ke ci gaba da addabar wasu yankunan kasashen Afrika.

Bukatar fatar Jaki na karuwa musamman a kasar China, inda ake amfani da ita wajen hada magungunan gargajiya.

Wani kiyasi ya nuna cewa Jakunan da ke doron kasa sun ragu cikin shekaru 20, wanda hakan ke kawo cikas a al’amura a karkara, yankunan da suka dogara da Jakuna wajen aikin gona, da sufuri da sauransu.

Wakiliyar BBC Nomsa Maseko ta ziyarci wata kasuwar bayan fage ta fatar jaki a yammacin birnin Johannesburg da ke Afrika ta Kudu.

Warin fatun jakunan da aka jeme ya lullube wurin kuma akwai akalla fatu sama da dari da aka baza.

Ana dai safarar fatun a asirtace a wata gona kusa da wani kogi kuma kasar China za a kai su.

Mutanen da suke zaune a kewayen wurin sun shaida wa wakiliyar BBC cewa kusan shekaru biyu kenan da aka fara haramtaccen kasuwancin, sannan kuma wari da hamamin yana matukar damunsu sai dai babu yadda za su yi.

Victoria Mkhize ta ce “Ba zan iya kwatanta yadda warin ya ke ba, tun da aka fara harkar nan nake sinitirin asibiti dan karbo maganin ciwon kirji, kuma sanadiyyar shakar warin na same shi. Gaskiya ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba.”

Wani kitse mai danko da ake samu a cikin fatar ta jaki ta zamo tamkar zinariya a China saboda yadda ake bukatarsa dan hada magunguna.

Kobe Montsho mazaunin wani kauye ne mai suna Hebron da ke kudancin kasar Afrika ta Kudu kuma ya dogara da jakinsa wajen dibar kasa da tarkacen kayan da aka daina amfani da su dan saida wa masana’antu su sake sarrafa su.

Ta hakan ne kuma yake samun abin da zai kula da iyalinsa “Yan China ne ke biyan bata-gari don su sace jakunanmu, an sace min jakuna guda biyar, idan na rasa sauran biyar din da nake da su, ban san ta yadda zan ciyar da iyalina ba. Jakunan kadai na dogara da su.”

Ana ci gaba da samun yawaitar kasuwancin fatar jaki a wasu kasashen Afrika, inda kasuwar ta bayan fage ke habaka.

Ashley Ness wata mai bincike ce a hukumar kula da dabbobi “Kasuwancin yanka jakuna ba bisa ka’ida ba ya zama wani gagarumin abu da ke kawo kudi, ba wai a Afrika ta kudu ba har da kasashen Kenya da Tanzania da Habasha da sauransu.”

Ta kara da cewa “Amma a yanzu sauran kasashen Afrika sun fara nuna damuwa kan yadda Jakunansu ke raguwa. Kuma tuni kasashen Nijar da Burkina Faso suka haramta safarar jakunan ko fatarsu, muna fatan sauran kasashe zasu shiga gangamin da ake yi dan magance matsalar baki daya.”

Hissene Habre zai fuskanci daurin rai da rai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hissene Habre shi ne tsohon shugaban kasa a Afrika na farko da aka taba yankewa hukunci a wata kotun da AU ke goyawa baya

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Senegal ta tabbatar da hukunci daurin rai da rai da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre.

A bara ne dai wata kotu ta musamman da kungiyar tarayyar Afrika ta kafa ta samu Habre da laifukan da suka hada da keta haddin bila’ama da laifukan yaki da azaftarwa da fyade tare da ba da umarni ayi kisa.

Lamarin dai ya faru ne a umarni a yi kisa a lokacin da ya ke kan mulki a Chadi a shekarun 1982 zuwa 1990.

Haka kuma kotun ta bukaci ya biya diyyar miliyoyin daloli ga wadanda abin ya shafa.

Tsohon shugaban Chadin mai shekaru 70 a duniya ya ki amincewa da kotun kuma bai yi magana ba a yayin zaman kotun ta musamman.

Habre dai yana zaman gudun hijira ne a Senegal a lokacin da aka damke shi bayan gwamnatin kasar ta fuskanci matsin lamba daga kasashen yamma da kuma iyalai da ‘yan wadanda lamarin ya shafa.

Ana binciken wani malami a Malaysia kan mutuwar Almajirinsa


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Yaron na zuwa makarantar mai zaman kanta, wacce daya ce daga cikin irinta masu yawa a kasar

‘Yan sanda a Malaysia na binciken mataimakin shugaban wata makarantar Islamiyya kan laifin kisan kai bayan mutuwar wani dalibi da ya zane.

Ana zargin malamin da laifin dukan Mohamed Thaqif Amin mai shekara 11, da robar ruwa.

Daga baya yaron ya kamu da ciwo mai tsananin, inda likitoci suka yanke kafafunsa.

A ranar laraba ne, ya mutu sakamakon fama da matsanancin ciwo.

Lamarin dai, ya janyo kiraye-kirayen akan gudanar da bincike kan makarantun addini.

Me ya faru da yaron?

A karshen watan Janairu ne, yaron ya shiga makarantar Islamiya mai zaman kanta dake garin Kota Tinggi, a jihar Johor.

‘Yan sanda sun ce yaron daya ne daga cikin yara 15 da malamin ya yiwa duka a ranar 24 ga watan Maris saboda laifin surutu.

Rahotonni sun nuna cewa mahaifiyarsa ta fitar da shi daga makarantar bayan da ta kai ziyara a makarantar kwanakin bayan haka ya faru, kuma ta same shi baya jin dadi sosai.

Hakkin mallakar hoto
Image copyrightAFP/GETTY IMAGES

Image caption

Akwai dubban makarantun Islamiya a kasar

An kai shi asibiti bayan makonni uku da kafafuwansa suka fara kumbura saboda taruwar jini da ya hana jini zagayawa cikin jikinsa.

Da likitocin suka lura cewa wurin kamu da cututtuka masu tsanani, sai suka yanke kafafuwansa.

Suna shirin yanke hannusa na dama ne a ranar Laraba da ya rasu.

Da farko dai, ‘yan sanda sun cafke mataimakin shugaban makarantar, wanda bai bayyana sunansa ba,da laifin cin zarafin yara amma sun ce zasu sake binicikensa akan kisan kai bayan mutuwar Mohamed Thaqif.

‘Yan sanda sun kara da cewa an taba tsare shi a kurkuku saboda laifin sata.

Makarantar dai, taki bada nata jawabi da cewa ‘yan sanda na gudanar da bincike akan lamarin.

Hukumar makarantar Johor ta gudanar da nata bincike inda ta ce makarantar bata yi laifi ba.

Amma shugaban makarantun addini a kasar ya ce hotuna daga CCTV, sun nuna cewa “ana dukan daliban akan kafa daya kadai” don haka akwai yiwuwar hakan ya haifar da wannan matsala ga yaron.

Wannan lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan kasar, inda suke tambayar dalilin da ya sa makarantar ta dauki mutumnin da aka taba samu da laifi ya kula da yaransu kuma ya aka yi ba a lura yana cin zarafin yaran ba?

Firayin ministan kasar, Najib Razak, ya yi kira da a gudanar da bincike na gaggawa akan lamarin

Me kuke son sani game da jam'iyyar APC?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

APC ta karbi mulki daga PDP a 2015

A watan gobe ne jam’iyyar APC da ke mulkin Najeriya ke cika shekara biyu da soma mulki bayan ta kayar da jam’iyyar PDP, wacce ta shekara 16 tana mulki, a zaben 2015.

Wasu na ganin jam’iyyar ta APC ta taka rawa sosai wajen kawo sauyi a shekaru biyun da ta yi a kan mulki, yayin da wasu ke cewa gara jiya da yau.

Bangarori daban-daban, wadanda suka hada da jam’iyyar CPC da jam’iyyar ACN da kuma gyauron ‘yan jam’iyyar PDP, ne suka dunkule wuri daya suka kafa APC, lamarin da ya sa masana siyasa ke ganin har yanzu zaman ‘yan marina ake yi a jam’iyyar shi ya sa ma ta kasa gudanar da babban taronta.

Sai dai manyan jami’an jam’iyyar sun ce bakinsu daya, kuma suna aiki ne domin ci gaban kasar.

Me kuke son sani game da wannan jam’iyya ta APC, musamman kan shugabancinta?

Ku aiko mana sako a cikin wannan akwatun da ke ƙasa.

Fitaccen jarumin Bollywood Vinod Khanna ya rasu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Vinod Khanna ya fito a fim din Bollywood fiye da 100

Jami’an lafiya a Indiya sun tabbatar ta mutuwar daya daga cikin fitattun jaruman fim din Bollywood, Vinod Khanna, wanda ya rasu yana da shekara 70.

Mista Khanna wanda ke harkar siyasa ya yi fama da ciwon daji, inda aka kai shi asibiti a farkon wannan watan bayan da rashin lafiyarsa ta yi tsanani.

Ya bayyana a fim fiye da 100 na Bollywood a tsawon rayuwarsa.

An zabe shi zuwa majalisar dokokin kasar sau hudu kuma ya taba zama mataimakin ministan harkokin waje.

Mista Khanna ya fara harkar fim a shekarar 1968 kuma sanan ne ne a Indiya musamman ma a shekarun 1970 da 1980 lokacin da ya yi wasu shahararrun fina-finai.

Mutane da dama na alhinin rasuwar Mista Khanna wanda ya mutu bayan rashin lafiya mai tsanani.

Masu jimami na amfai da maudu’in #VinodKhanna a shafin sada zumunta na Tweeter a kasar.

Shugaban Indiya, Pranab Mukherjee ya jagoranci ‘yan siyasa da suka nuna jinjina kan rawar da Mista Khanna ya taka a fanin siyasa.

Yayin da wasu fitattun ‘yan wasan Bollywood kuma ke nuna alhininsu ga mamacin.

'Ba mu kwashi takardun kasafin kuɗi a gidan Goje ba'


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN SENATE

Image caption

Wasu na ganin al’amarin dai ka iya ƙara janyo jinkiri wajen zartar da kasafin kuɗin shekara ta 2017

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke cewa jami’anta sun kwashe wasu takardun kasafin kuɗin 2017 yayin samamen da suka kai gidan Sanata Danjuma Goje.

A wata sanarwa da suka fitar, ‘yan sandan sun ce sun kai samame ne gidan Sanatan bayan sun samu bayanan sirri da ke cewa ana shirin fitar wasu maƙudan kuɗi da ake zargin na sata ne.

Ta ce kuma ba ta yi hakan ba, sai da ta samu izinin gudanar da bincike daga kotu.

Shi dai Danjuma Goje wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Nijeriya, ya ce kasafin kudin kasar na bana zai samu jinkiri don kuwa ‘yan sanda sun kwashe wasu muhimman takardu a gidansa.

Ya bayyana haka ne a zauren majalisar inda ya faɗa wa takwarorinsa batun samamen da ‘yan sanda suka kai gidansa da ke Abuja a makon jiya.

A cewarsa kasafin kudin da kwamitinsa ke aiki a kai na cikin kwamfutocin da ‘yan sanda suka dauke a lokacin da suka kai samamen.

Batun dai ka iya kara kawo cikas ga kasafin kudin na bana, wanda tuni aka samu jinkiri wajen amincewa da shi.

Hakkin mallakar hoto
Other

Image caption

‘Yan sandan sun ce babu gaskiya a kalaman Sanata Goje

Rundunar ‘yan sanda ta zayyana abubuwan da ta gano da suka haɗar da kuɗi da takardu da kuma kwamfiyutar tafi-da-gidanka.

Ta ce a ciki babu wani abu da ya shafi takardun kasafin kuɗin shekara ta 2017, kuma duk mai sha’awa yana iya zuwa ya duba.

Sanarwar ta ce a binciken da ta gudanar ta gano kuɗi Naira miliyan 18 da oriya. Sai kuma Dalar Amurka kusan 20,000.

Haka kuma akwai Riyal na Saudiyya 9,400 da kuma wasu takardun ambulan da ke ƙunshe da fayel-fayel.

A cewarta fayel-fayel ɗin sun haɗar da bayanan ayyukan Sanata Danjuma Goje lokacin da yake gwamna da kuma na harkokin kasuwancinsa.

Sun nanata cewa babu wasu takardu da suka danganci kasafin kuɗin shekara ta 2017 kuma tana da bidiyo da ta ɗauka yayin binciken.

Wasu na ganin wannan batu ba zai tsaya a nan ba domin majalisar dattawan ta mika shi gaban wani kwamitinta domin ya yi bincike.

Mutuwa ta ɗau ma'auratan da suka shekara 69 tare


Hakkin mallakar hoto
FAMILY HANDOUT

Image caption

Mutu ka raba….ma’auratan sun haɗu da juna ne tun a Argentina

Wasu ma’aurata a jihar Illinois ta Amurka da suka shafe shekara 69 a tare sun mutu sa’a ɗaya a tsakanin juna.

Jaridar Daily Herald ta ruwaito cewa Isaac Vatkin, mai shekara 91, yana riƙe da hannun matarsa Teresa mai shekara 89, a lokacin da ta ce ga-garinku-nan sakamakon cutar susucewa ta Alzheimer a ranar Asabar.

Isaac kuma ya bi ta bayan minti 40. Dangin mamatan sun ce zuciyarsu ta yi fari da suka samu labarin cewa ma’auratan sun mutu suna tare da juna.

Wani jika a wajen ma’auratan, William Vatkin ya ce “Rasuwarsu abin takaici ce, amma wanne fata za ka yi musu da ya wuce wannan?”

Hakkin mallakar hoto
FAMILY PHOTO

Image caption

Vatkins a ranar aurensu

‘Yarsu, Clara Gesklin ta faɗa yayin jana’izar haɗin gwiwa da aka yi wa mamatan cewa “Suna matuƙar son juna, ɗaya ba zai iya rayuwa ba tare da ɗayan ba.”

Limamin da ya jagoranci jana’izarsu a tsaunukan Arlington da ke wajen birnin Chicago, Barry Schechter ya ce “Suna ƙaunar juna ko da yaushe, to ga shi ma har ƙarshen rayuwarsu.”

Ma’aikatan asibitin Highland Park sun fahimci jikkunan ma’auratan sun yi tsanani kuma da ƙyar suke numfashi a ranar Asabar don haka suka ba su gado a kusa da juna.

Danginsu sun ɗora hannuwansu a kan na juna kafin mutuwarsu.

‘Ya’yansu sun ce ma’auratan na da ɗa uku kuma sun shaƙu da jikokinsu.

Ministan labaran Nigeria ya yi amai ya lashe


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN GOVERNMENT

Image caption

Tun bayan dawowarsa daga jinya a Ingila ne, shugaba Buhari ya rage fitowa bainar jama’a

Ministan yaɗa labaran Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya ce shugaban ƙasar zai yi aiki a gida ranar Laraba, amma ba daga yanzu zai riƙa aiki daga gida ba.

Wata sanarwa da ministan ya fitar ta ambato shi yana cewa wasu kafofin yaɗa labarai sun yi wa bayanin da ya yi, kuskuren fahimta.

A cewar sanarwar ministan bai taɓa cewa nan gaba shugaban Nijeriya zai riƙa aiki ne daga gida ba.

Ta ce kanun da wasu kafofin yaɗa labarai suka buga cewa “Daga yanzu Buhari zai riƙa aiki daga gida” bahaguwar fahimta ce aka yi wa kalamansa a wata tattaunawa da ‘yan jarida.

Jawabin dai ya tayar da hankulan ‘yan Nijeriya inda wasu ke bayyana fargaba game da halin da lafiyar Muhammadu Buhari take ciki.

Sai dai a wani sautin kalaman ministan da aka naɗa lokacin da yake jawabi ga manema labarai, an jiyo shi yana cewa shugaban ƙasa zai riƙa aiki ne daga gida.

“A kai masa duk fayel-fayel ɗinsa gida

Yayin taron ‘yan jaridar, Alhaji Lai Mohammed ya ce na tabbata kun lura cewa shugaban ƙasa ba ya nan.

Ba ya nan ne saboda ya ce a bar shi ya huta, don haka ya buƙaci mataimakinsa ya jagoranci taron (Majalisar Zartarwa), in ji shi.

“Kuma zai riƙa aiki ne daga gida. Ya ce ma a kai masa duk fayel-fayel ɗinsa zuwa gida.”

A cewarsa, mai yiwuwa ne mataimakin shugaban ƙasa zai gana da shugaban ƙasa nan gaba a yau don tuntuɓa.

Tun bayan dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga jinyar kwana 50 ne, aka daina ganinsa a bainar jama’a.

Karo uku kenan a jere, shugaban na Nijeriya bai halarci taron Majalisar Zartarwar ƙasar na mako-mako da ya saba jagoranta ba.

'Fasa-ƙwaurin shinkafa ya durkusar da kasuwancinmu'


Image caption

Masu sarrafa shinkafa a Najeriya sun koka da shigo da shinkafa daga waje

Masana’antun shinkafa a Nijeriya sun koka a kan koma-bayan kasuwa da shinkafar da suke sarrafawa a cikin gida take fuskanta saboda fasa-ƙwaurin ta ƙasashen waje da ake yi.

Sun bayyana fargabar cewa burin gwamnatin ƙasar na wadata Nijeriya da shinkafa a nan kusa ka iya zama mafarki, inda suka yi zargin cewa masu fasa-kwauri da hada baki da jami`an kwastam wajen satar shiga da ita ƙasar.

Wannan lamari dai a cewarsu, ya sa kasuwar shinkafar gida ta faɗi, abin kuma da ke tilasta rufe masana`antun.

Gwamnatin Nijeriya a baya-bayan nan ta ɓullo da matakai iri daban-daban don bunƙasa noman shinkafa a cikin gida.

Daga ciki har da bai wa manoma da masu masana’antun sarrafa shinkafa kariya ta hanyar taƙaita shigar da ita daga ƙasashen waje.

Sai dai, a baya bayan nan masu sarrafa shinkafar da kasuwancinta sun ce suna fuskantar barazanar da ka iya gurgunta musu sana’a.

Injiniya Nazifi Ilyasu shi ne kakakin kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nijeriya kuma ya shaida wa BBC cewa yanzu kasuwancin shinkafa ta cikin gida, ba ya tafiya.

Ya kuma yi zargin cewa: ” Ana shigo shinkafar kasashen waje sosai ta wasu kan iyakokin Nijeriyar, tana neman ta taɓa harkar masana’antunmu”

Image caption

Shiga da shinakafar waje na kashe wa ta gida kasuwa a cewar masu masana’antu

Masu shinkafar dai sun koka kuma da cewa rashin cinikin ya sa farashin shinkafar na faɗuwa.

Binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa akwai masana’antun sarrafa shinkafa da dama da suka rufe aiki a yankin jihar Kano.

Amma kuma a ɓangaren ‘yan kasuwa sun ce rangwamen farashi ne ke sa shinakafar waje kashewa ta gida kasuwa.

Alhaji Uba Zubairu Yakasai shugaban kasuwar kwanar Singer ta Kano, ya ce shinkafar gida ta fi ta waje tsada shi ya sa ake sayen ta fiye da ta gida.

Ya kuma ce ta gidan idan farashinta ya yi ƙasa babu abin da zai sa mutane su sayi ta waje.

Hukumar Kwastan ta Najeriya a nata bangaren ta ce tana da labarin fasa-ƙwaurin shinkafar amma bai yi munin da zai sa shinkafar waje ta mamaye kasuwannin kasar ba.

Ta kuma musanta cewa ana haɗa baki da wasu jami’anta wajen shigar da shinkafar daga waje.

An saye wani ƙauye da aka yi wa kuɗi fam miliyan 20


Hakkin mallakar hoto
CUNDALLS

Image caption

Ƙauyen West Heslerton na da nisan kilomita 9 daga Malton a Yorkshire ta Arewa

An sayar da wani ƙauye sukutum, da aka sa shi a kasuwa cikin shekara ta 2016 a kan kuɗi fam miliyan 20 a Ingila.

Ƙauyen West Heslerton, da ke kusa da yankin Malton, na da wani danƙareren gida mai ɗaki 21, da mashaya da gidan mai da gida 43 a kan fili mai faɗin eka 2,116.

Dangi guda ne suka mallaki ƙauyen tsawon sama da shekara 150, kuma an sa shi a kasuwa bayan mutuwar wanda ya mallake shi na baya-bayan nan.

Kamfanin hada-hadar gine-gine na Cundalls ya ce wani kamfani mai harkokin noma da zuba jari a Norfolk Albanwise ne ya saye ƙauyen West Heslerton.

Hakkin mallakar hoto
CUNDALLS

Image caption

Ƙauyen na da wani tamfatsetsen gida mai ɗaki sama da 20 a cikinsa.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya ce Albanwise na daf da kammala ciniki a ranar Juma’a kuma tuni ya fara ganawa da ‘yan ƙauyen

Ba a dai bayyana ko nawa kamfanin ya biya don saye ƙauyen ba.

A shekarar 1960 ce Eve Dawnay ta gaji rukunin gidajen ƙauye, amma sai makusantanta suka yanke shawarar sayar da shi bayan ta rasu a shekara ta 2010.

A lokacin da aka sa ƙauyen a kasuwa, mutanen ƙauyen sun bayyana lamarin da cewa “ƙarshen zamani”.

Ita dai Eve Dawnay ta yi suna a kan rashin tsawwala kuɗin haya, abin da kamfanin Cundalls ya ce ya taimaka wajen bunƙasa harkoki a ƙauyen.

Tottenham ta ci gaba da matsa wa Chelsea, bayan ta ci Palace 1-0


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Christian Eriksen ya ci kwallo biyar a wasa 12 da ya yi da suka gabata

Tottenham ta ci gaba da matsar jagorar Premier Chelsea mai maki 78, da tazarar maki hudu, bayan da ta je har gidan Crystal Palace ta doke ta da ci 1-0.

Bakin sun yi ta fama kan su samu damar keta masu masaukin nasu, amma abin ya gagara, sai a minti na 78 Eriksen ya samu ya daga ragar.

Palace wadda ta yi rashin jajircaccen dan wasanta na baya Mamadou Sakho saboda raunin da ya ji bayan an dawo hutun rabin lokaci, ba kasafai ‘yan wasanta suke kai hari ba, sai dai hana bakin.

Yanzu Palace, ta ci gaba da zama ta 12 a teburin na Premier, da maki bakwai tsakaninta da rukunin masu faduwa daga gasar.

Barcelona ta ci gaba da jagoranci, ta fitar da Osasuna daga La Liga da ci 7-1


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallo biyu da Messi ya ci ya sa suka zama kwallo 49 a bana a wasa 48

Lionel Messi ya zura kwallo biyu a raga a wasan da Barcelona ta ci gaba da jan ragamar La Liga, inda ta sa Osasuna ta fadi daga gasar da ci 7-1, yayin da Real Madrid ta ci Deportivo La Coruna 6-2.

Masu rike da kofin yanzu suna da maki 78 daidai da abokan hamayyarsu Real Madrid, wadda ita ma ta bi Deportivo La Coruna gida ta doke ta 6-2, amma kuma Madrid din tana da kwantan wasa daya.

Messi ne ya fara daga raga da kwallonsa ta 501 da ya ci wa Barca kafin Andre Gomes shi ma ya ci tasa.

Messi ne ya fara daga raga a minti na 12, da kuma na 61, sai André Gomes wanda shi ma ya zura biyu a ragar bakin a minti na 30 da na 57.

Alcácer shi ma ya zura biyu ne a minti na 64 da kuma minti na 86, yayin da Mascherano ya ci tasa da fanareti a minti na 67.

Roberto Torres ya karfafa wa bakin guiwa da kwallo daya a minti na 48.

Sakamakon ya sa Osasuna ta fadi kenan daga La Liga kasancewar Leganes ta doke Las Palmas har 3-0.

Ita ma Real Madrid ta casa Deportivo La Coruna ne da ci 4-1, abin da ya sa ta ci gaba da kasanncewa ta biyu a tebur da maki 78 daidai da Barcelonan amma da bambancin kwallo

Morata ne ya fara ci wa Madrid kwallo a minti daya da shiga fili , sai Rodríguez ya biyo baya a minti na 14 da kuma minti na 66.

Vázquez ya zura tasa ana shirin tafiya hutun rabin lokaci a minti na 44. Amma kuma masu masaukin bakin sun samu damar zura kwallonsu ta hannun Andone a minti na 35.

A nata wasan na La Liga Valencia ta sha kashi da ci 3-2 a hannun bakinta Real Sociedad.

Premier: Arsenal ta doke Leicester 1-0


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Monreal na murnar cin da Arsenal ta yi bayan da ya sheka kwallon da ta doki kirjin Robert Huth ta shiga raga

Arsenal ta ci gaba da fafutukar komawa cikin kungiyoyi hudu na farko a teburin Premier bayan da doke Leicester 1-0, bayan da Robert Huth ya ci kansu a minti na 84.

Magoya bayan Arsenal din sun kusa yanke kauna da samun nasarara a wasan na Emirates kafin Nacho Monreal ya sheko wata kwallo wadda ta bugi kirjin dan bayan na Leicester, dan Jamus ta shiga raga, ana dab da tashi.

Yanzu dai maki uku ne tsakanin Arsenal ta shida a tebur wadda ke bayan Manchester United ta biyar, sannan kuma hudu tsakaninta da ta hudu a tebur Manchester City tun da sun yi yawan wasanni daya.

Amma akalla daya daga cikin kungiyoyin na Manchester za ta rasa maki idan sun hadu a wasansu na hamayya na ranar Alhamis.

Liverpool tana matsayi na uku da maki shida a gaban Arsenal, amma kuma ta fi Gunners din da yawan wasa biyu.

Kun san tasirin wasan hamayyar Manchester na Alhamis?


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Wasan na neman kasancewa cikin kungiyoyin hudun farko ne a Premier

An yi tsammanin kakar wasan Premier ta bana za ta zama gogayya ce tsakanin Guardiola da Mourinho,wajen daukar kofin Premier, sai dai hakan ba tabbata ba.

A ranar Alhamis ne za su kara karawa a filin wasa na Etihad, yayin da Guardiola ke fatan maimaita nasarar da ya yi, kan Mourinho a watan Satumba.

Waccan nasarar ta sanya City a saman teburin Premier, kuma tun daga wancan lokacin har yanzu babu wata kungiya ta Manchester da ta kara samun wannan damar.

Rabon da Manchester United dai, ta zama a saman teburin Premier, tun ranar 19 ga watan Agusta. Yayin da rabonta da zama cikin kungiyoyi hudun farko tun ranar 15 ga watan Satumba.

Yanzu dai yakin na neman kasancewa cikin kungiyoyi hudun farko ne, ba daukar kofi ba. Saboda samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

A rashin uwa akan yi uwar daki, ko kuma a ce da babu gara ba dadi, domin rashin daukar kofi ba shi ne abin damuwa a wajen Guardiola, kamar yadda ya ce, amma samun karewa cikin hudun farko shi ne burinsa a yanzu.

Samun nasarar zuwa gasar Zakarun Turai dai, shi ne zai fayyace matsayin Guardiola da Mourinho, a kakarsu ta farko a kungiyoyin nasu.

Idan dai United ta yi nasara a wasan na ranar Alhamis, za ta dawo cikin kungiyoyi hudun farko, a karo na farko tun 15 ga watan Satumba, kuma City za ta fice daga hudun farko, a karon farko tun ranar 12 ga watan Fabrairu.

Wasan na ranar Alhamis ba shi ne siradin karshe na samun gurbi a wasan Zakarun Turai ba, saboda duk kungiyoyin biyu na da sauran wasa biyar.

Kuma akwai sauran kungiyoyi biyu cikin wannan fafatawar, watau Liverpool da Arsenal wacce yanzu ta farfado.

Ana binciken jirgin sama a kan mutuwar zomo


Hakkin mallakar hoto
CATERS NEWS

Image caption

Ana zaton Simon zai zama zomon da ya fi kowanne girma a duniya.

Kamfanin jiragen saman United Airlines na kasar Amurka na gudanar da bincike kan mutuwar wani babban zomo, wanda aka dauka a cikin daya daga cikin jiragensu.

Zomon mai tsawon santimita 90, da ake kira da Simon, an same shi a mace a cikin kayan jirgi a lokacin da jirgin ya sauka a filin saukar jiragen sama na O’Hare Chicago wanda ya taso daga filin jirgin saman Heathrow da ke Landan.

Rahotanni daga kafofin watsa labaran Amurka sun ce, babban zomon mai wata goma wanda aka tafi kaiwa wata sabuwar uwargijiyarsa.

Amurka – wacce ta kasance cikin matsanancin halin munanan tallace-tallace na wasu ‘yan makonni – ta ce ta yi matukar bakin-ciki da mutuwar Simon.

Ba a fiya samun mutuwar dabbobi a jirgi ba.

Sashen kula da harkokin sufuri na kasar Amurka, ya nuna cewa bayanan da aka samu na baya-baya nan a shekarar 2015, Kamfanin jiragen saman Amurka sun ba da rahoton mutuwar dabbobi.

Hakkin mallakar hoto
CATERS NEWS

Image caption

Annette Edwards ta rike zomonta mai suna Darius

A wata sanarwa da aka turawa BBC, inda Amurka ta ce, “Mun yi matukar bakin-ciki da jin wannan labari”. Samun cikakkiyar kulawa da tsaro na dukkan dabbobin da za su yi tafiya da mu abu ne mai matukar muhimmanci ga Kamfanin jiragen saman kasar Amurka.

“Muna da kyakkywar alaka da abokan huldarmu,kuma muna basu taimako. muna bibiyar wannan al’amari.

Jaridar Sun ta kawo rahoton cewa, Simon mai wata 10 dan zomon da ya fi kowanne zomo girma a duniya, wanda tsawonsa ya kai 1.3m babban zomon da ake kira Darius, kuma ana tsammanin zai yi girma fiye da babansa.

Annette Edwards, wacce ita ce mai zomon, ta shaida wa jaridar cewa, “Sa’o’i uku kafin su shiga jirgin likitoci sun duba lafiyar Simon kuma an tabbatar da lafiyarsa inda suka ce zai iya tafiya da shi a matsayin abin wasa.”

“Wani bakon al’amari ya faru kuma ina so na san menene. Na sha tura zomaye a fadin duniya amma irin haka bai taba faruwa ba a baya,” in ji ta.

Kim Jong-un zai dandana kudarsa a hannun Amurka


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Amurka ta aike da jiragen yaki na ruwa da jiragen karkashin ruwa zuwa zirin koriya

Babban kwamandan rundunar sojin Amurka da ke Pacific ya ce na’urorin kare kai daga makami mai linzami da ke Korea ta kudu za su sanya shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un ya shiga hayyacinsa ba wai a durkusar da shi ba.

Adm Harry ya shaida wa majalisar dokokin Amurka cewa Amurka za ta kasance a shirye da “fasahar zamani” domin ta murkushe duk wata barazanar makami mai linzami daga Koriya ta arewa.

Adm ya shaida wa kwamitin soji da ma’aikatar tsaron Amurka cewa Mista Kim na ci gaba da matsayawa kusa da manufarsa ta amfani da makaman Nukuliya a biranen Amurka.

Ya kara da cewa “kamar yadda shugaban Amurkan, Donald Trump da sakataren tsaron kasar James Mattis suka fada, duk hanyoyin da za mu tunkari kasar a bude suke”.

Amurka ta aike da jiragen yaki na ruwa da jiragen karkashin ruwa zuwa zirin koriya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Amurka zata kasance a shirye da ” fasahar zamani” domin su murkushe duk wani barazanar makami mai linzami daga Koriya ta arewa.

China na ganin cewa tsarin makami mai linzami na Thaad na Amurka zai hargitsa yanayin tsaro.

Ana ci gaba da samun tashin hankali a dai dai lokacin da ake zaman dar dar kan cewa ta yiwu Koriya ta Arewa na shirin gwajin wasu makamai masu linzami da makaman Nukuliya.

A lokacin da yake wani bayani gabanin wata tattaunawa ta sanatoci a fadar White House, Adm Harris ya ce ya yi amannar cewa Koriya ta arewa za ta yi kokarin kai wa Amurka hari da zarar ta samu karfin sojin da take bukata.

An dakatar da Neil Taylor sabodo jikkata Coleman


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alkalin wasa Nicola Rizzoli ya ba wa Neil Taylor jan kati bayan ketar da ya yi wa Seamus Coleman

An dakatar da dan wasan baya na Wales Neil Taylor, wasa biyu kan muguwar ketar da ya yi wa kyaftin din Ireland ta Arewa Seamus Coleman.

Alkalin wasa ya kori Taylor, mai shekara 28, saboda wannan keta da ya yi a lokacin wasan na neman gurbin gasar Kofin Duniya tsakanin Wales da Ireland ta Arewa a Dublin a watan Maris.

Yanzu dai dan wasan ba zai buga wasan da Wales za ta yin a neman damar zuwa gasar ta Kofin Duniya, guda biyu ba, da Serbia a watan Yuni da kuma Austria a watan Satumba.

Sakamakon raunin da dan wasan bayan na Everton, Coleman, ya ji ana ganin zai dade bai dawo tamola ba saboda tiyatar da aka yi masa a kauri.

Kociyan Everton Ronald Koeman, mai shekara 28, da kuma kyaftin dinsu, Phil Jagielka sun ziyrci dan wasan a gidansa a Ireland ta Arewa.

Ireland din it ace ta biyu a rukuninsu na hudu ( Group D), da maki daidai da Serbia wadda ke jagorantar rukunin, kuma tana da maki hudu a gaban Wales ta uku.

'Yan sanda sun kwace takardun kasafin kudin Nigeria – Goje


Hakkin mallakar hoto
Nigerian Senate

Image caption

Kawo yanzu dai ‘yan sanda ba su fito sun ce uffan ba kan samamen na gidan Sanata Goje

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawan Najeriya, Danjuma Goje, ya ce za a jinkirta kasafin kudin kasar na bana domin ‘yan sanda sun kwace wasu muhimman takardu a gidansa.

Sanata Goje ya fadi haka ne a zauren majalisar inda ya ba wa takwarorinsa labarin samamen da ‘yan sanda suka kai gidansa da ke Abuja a makon jiya.

Sanatan mai wakiltar Gombe ta tsakiya ya ce kasafin kudin da kwamitinsa ke aiki a kai na cikin kwamfutocin da ‘yan sanda suka dauke a lokacin da suka kai samamen.

Bayan ya saurari koken Goje, Shugaban majalisar Bukola Saraki ya mika batun ga kwamitin wucin gadin da majalisa ta nada don bin bahasi kan zargin yunkurin kashe Sanata Dino Melaye.

Wannan batu ka iya kara kawo cikas ga kasafin kudin na bana, wanda tuni aka samu jinkiri wurin amince wa da shi.

Kasasfin kundin na shekarar 2017 dai sai ya samu amicewar bangaren majalisar biyu kasar kafin ya zama doka.

A makon jiya ne ‘yan sanda suka kai samame gidan Sanata Goje da ke unguwar Asokoro a Abuja.

Rahotanni sun ce sun awangaba da kudade da kuma wasu kayayyaki daga gidan.

Kawo yanzu dai ‘yan sandan Najeriya ba su fito sun ce wani abu ba game da samamen.

Caca: An dakatar da Joey Barton na Burnley


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An taba dakatar da Joey Barton wasa daya a watan Nuwamba a kan caca

An dakatar da dan wasan tsakiya na Burnley, Joey Barton, daga wasa na tsawon wata 18 bayan da ya amsa tuhumar da aka yi masa ta laifin da yake da alaka da caca.

An ci tarar dan wasan mai shekara 34, kudi fam 30,000, an kuma gargade shi da kada ya aikata irin wannan laifi a gaba, bayan da aka tuhume shi da laifin karya dokar FA na yin caca har sau 1,260 a wasanni tsakanin 26 ga watan Maris na 2006 da 13 ga watan Maris din 2016.

Barton na shirin daukaka kara kan tsawon lokacin da aka dakatar da shi, yana mai cewa ; “wannan mataki zai tilastamin yin ritaya da wuri”.

Dan wasan ya yi caca a kan wasu wasannin da ya buga, sai dai ya fada a wata sanarwa a shafinsa na intanet cewa, “wannan ba cogen wasa ba ne, kuma ba wani lokaci da aka ga wani abu na rashin gaskiya a game da ni yayin wasannin”.

Ya kara da cewa: “Na yadda na karya dokar kwararrun ‘yan wasa, amma ina jin hukuncin ya yi tsauri, fiye da yadda za a yi wa ‘yan wasan da suka yi abin da bai kai wannan ba”.

Ana binciken Newcastle da West Ham kan zamba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana zargin jami’an kungiyoyin biyu da kin biyan harajin kusan fan miliyan biyar

Jami’an haraji sun yi wa filayen wasan Newcastle United da West Ham United dirar mikiya kan zargin zamba ta kin biyan haraji.

Ana ganin babban daraktan kungiyar Newcastle Lee Charnley na daga cikin tarin mutanen da aka kama wadanda ke cikin harkar kwallon kafar kwararru.

Hukumar da ke kamen (HMRC) ta ce ta baza jami’ai 180 a fadin Birtaniya da Faransa don gudanar da aikin sumamen.

BBC ta fahimci cewa yawan kudin harajin da ya kamata kungiyoyin biyu su biya amma suka ki biya ya kai fan miliyan biyar.

Jami’an sun binciki ofisoshin kungiyoyin da ke filayensu a yankin arewa maso gabas da kudu maso gabashin Ingila, inda suka kwace muhimman takardun bayanan kudi da kwamfutoci da wayoyin salula.

Jami’an sun fadada binciken nasu har zuwa ofisoshin kungiyar Chelsea, kamar yadda mai Magana da yawun kungiyar ya tabbatar.

Sai dai ana ganin ba sumame aka kai ofisoshin ba kuma ba a kama kowa ba a can, illa dai jami’an sun bukaci wasu bayanai ne game da kungiyar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lee Charnley ( daga dama tare da mai kungiyar Newcastle Mike Ashley), na daga wadanda aka kama

Wasu majiyoyi sun sheda wa BBC cewa tun da farko sai da aka kama manajan daraktan Newcastle Mr Charnley, mai shekara 39.

Shekara uku da ta wuce ne manajan ya kama aikin, kuma ana ganin shi ne ya shawo kan kociyan kungiyar Rafael Benitez ya tsaya byan da ta fadi daga gasar Premier a bara.

A ranar Litinin ne kungiyar ta yi nasarar dawowa gasar ta Premier kwanaki 348 bayan da ta fadi.

Abin da ya hana Buhari halartar taron majalisar zartarwa


Hakkin mallakar hoto
Kaduna state government

Image caption

Buhari ya ce bai taba yin jinya irin wacce ya yi a London ba

A karo na biyu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai halarci taron majalisar zartarwa da ake yi duk ranar Laraba ba, abin da ya kara jefa fargaba kan halin da yake ciki.

‘Yan kasar da dama na ganin shugaban bai halarci taron ba ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma wasu na nuna damuwa kan halin da yake ciki.

Sai dai ministan watsa labarai na kasar Lai Mohammed, ya ce shugaban na ci gaba da hutawa ne a gidansa.

Tun bayan da shugaban na Najeriya ya koma kasar daga jinyar da ya kwashe kusan kwana 50 yana yi a birnin London, ya ce ba zai rika yin aiki sosai ba saboda yanayin jikinsa.

Tun bayan da shugaban ya dawo kasar dai, ba kasafai yake bayyana a bainar jama’a ba.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al’amuran gwamnati, kuma wasu na ganin hakan yana kawo tsaiko wurin tafiyar da al’amura.

Sai dai mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa babu wani abu da ya tsaya a harkar gwamnati saboda matakin da shugaban ya dauka.

“Ya fada da bakinsa cewa bai taba yin jinya wacce ta ba shi wahala kamar wacce ya yi a birnin London ba,” kuma ya fada cewa zai ci gaba da huta wa, in ji Garba Shehu.

A lokacin jinyar da ya yi dai, sai da likitoci suka kara masa jini, ko da yake bai fadi larurar da ke damunsa ba.

A lokacin, shugaban na Najeriya ya ce yana samun sauki sosai, “amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti”.

Shugaban dai yakan fito masallaci da ke fadarsa duk ranar Juma’a domin halartar salla.

Matar da ke so 'yan China su rika cin kwari


Hakkin mallakar hoto
RYAN LASH/TED

Image caption

Matilda tana so ta yi amfani da fasaha wajen inganta yadda mutanen China ke cin abinci

Wata ‘yar kasuwa a China ta fara amfani da hanyoyin kasuwanci na intanet domin tallata na tallata wa mutanen kasar wasu kwari a wani kamfe na inganta yadda ‘yan kasar ke cin abinci.

Matilda Ho ta yi jawabi a wurin wani taron fasaha da tsare-tsare na Ted a kan bukatar yada manufarta a kan cin abinci mai gina jiki.

Mutane da dama a China na fama da matsalar matsananciyar kiba da ciwon siga.

Misis Ho ta shaidawa BBC cewa “yawan mutanen China sun kai kashi 20 cikin 100 na yawan mutanen da ke duniya amma kuma kashi 7 cikin 100 na gonakinsu ne kawai ake iya nomawa”.

Ta kara da cewa daya daga cikin mutum hudu masu ciwon siga dan China ne, haka zalika daya daga cikin mutum biyar na masu kiba sosai daga kasar ne.

Misis Ho ta fara magance matsalar ne ta hanyar samar da kasuwar manoma ta intanet wadda ke samar da sabbin kayayyakin abinci daga manoma 57.

Mutum 40,000 na bibiyar kasuwar intanet din tun da aka kaddamar da ita watanni 18 da suka gabata.

“Ina so na yi amfani da fasaha wajen takaita gibin da ke tsakanin masu samar da abincin da masu saye,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

“‘Yanci ne kasan daga ina ake samar da abincin da kake ci kuma hakan yana karfafawa mai saye gwiwa.”

Ana aike wa masu sayan kayan abincin na su ta motocin lantarki a cikin kwalayen da za su hana su lalacewa.

Misis Ho ta ankara cewa ba a da isassun kananan sanao’i na intanet don haka yanzu ta kaddamar da abin da zai bunkasa cigaban wasu kamfanonin da ke kirkirar fasahar abinci.

“A China, masana’antun da ke yin tufafi na amfani da tsutsar silkworm don haka suna da arha kuma suna da saukin samu kamar yadda Ho ta bayyana.

Ta kara da cewa “ba a cika kyankyaminsu kamar yadda ake yi wa kwari ba. Da muna yara mun yi kiwon tsutsar Silkworm a makaranta.”

Akwai tarihin cin tsutsa a China amma a yanzu tsutsotsin silkworm kawai aka halasta amfani da su a matsayin wani sinadarin hada abinci.

Hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutane a Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Boko Haram ta kara kaimi wajen kai hare-haren kunar bakin wake ne bayan sojojin Najeriya sun fatattake ta daga dajin Sambisa

Wasu jerin hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutum biyar a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wadanda suka mutu a hare-haren sun hada da ‘yan kunar bakin wake hudu da kuma wani dan kato da gora, wato Civilina JTF.

Jami’ai sun ce an kai wadanda suka ji rauni a harin asibiti yayin da hukumar ba da agajin gaggawar a jihar ta ce za ta ci gaba da tallafawa wadanda abin ya rutsa da su.

Rahotanni sun ce an ci gaba da harkoki a birnin kamar yadda aka saba.

Kungiyar Boko Haram ta koma amfani da mata da yara wajen kai hare-haren ta’addanci kan cibiyoyin farar hula tun bayan dakarun Najeriya suka fatattake su daga dajin Sambisa.

Nigeria: Yadda Oba na Legas ya 'wulakanta' Ooni na Ife


Hakkin mallakar hoto
OONI FACEBOOK GROUP

Image caption

Ooni na Ife shi ne gaba da Oba na Legas a tsarin sarautar kabilar Yarbawa

‘Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani a kafafen sada zumunta bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda Oba na Legas ya ki gaisawa da Ooni na Ife a bainar jama’a.

Oba Rilwan Aremu Akiolu, mai shekara 73, ya ki mika hannu domin gaisa wa da Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi, mai shekara 42 a lokacin wani taro a birnin Legas.

A bidiyon da ake yada wa a shafin Twitter, a lokacin da Ooni na Ife ya shiga dakin taro ya mika wa Rilwan hannu don su gaisa amma maimakon hakan, sai kawai ya daga masa hannu ya ki yarda su yi musabaha.

Bayan Akiolu ya ki mika wa Ogunwusi hannu su gaisa, sai kawai Ooni na Ifen ya juya ya koma inda aka ajiye masa kujerarsa ya zauna.

A kabilar Yarbawa dai ana yi wa Ooni na Ife kallon sarkin sarakuna kuma shi ne gaba da Oba na Legas.

An nada Mista Ogunwusi ne a baya-bayan nan, yayin da Akiolu ya shafe dogon lokaci a matsayin Oba na Legas.

Jama’a a Twitter dai sun yi Allah-wadai da abin da Oba na Legas din ya yi:

Ugochukwu Azonobi ya ce: “Ya kamata a gaya wa Oba na Legas cewa Ooni tsatson Oduduwa ne kuma ba sa’ansa ba ne”.

Yayin da Olajohn Olutumi ya ce: “Ban san abin da ya faru ba, amma koma mene ne, bai kamata Oba na Legas ya yi haka ba. Ya nuna rashin dattaku”.

Hakkin mallakar hoto
Twitter

Kotu na taka wa Donald Trump burki kan tsare-tsarensa


Image caption

Donald Trump ya tsaya kai da fata sai ya gina shinge tsakanin Amurka da Mexico

Wani babban alkali a birnin San Francisco na Amurka ya dakatar da umarnin da shugaba Donald Trump ya bayar na rike kudaden gudanarwar wasu birane da suka ki amince wa da su kama ‘yan cirani domin a mayar da su kasashensu na asali.

Mai shari’a William Orrick ya nemi da a dakatar da umarnin na shugaba Trump har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar da biranen suka kai gaban kotu.

A watan Fabrairu ne dai San Francisco da Santa Clara suka maka gwamnatin tarayyar Amurka gaban kotu kan dokar hana su kudaden gudanarwa sakamakon kin amincewa su cafke ‘yan cirani.

A watan Janairu ne shugaba Donald Trump ya rattaba wa dokar da ta ba wa jihohi damar cafke ‘yan cirani sannan kuma amayar da su kasashensu na asali.

Dokar ta kuma bai wa gwamnatin tarayya damar rike kudaden duk jihar ko birnin da ya ki bin umarnin cafke ‘yan ciranin.

A ranar Talata ne mai shari’a William Orrick ya nemi da a dakatar da dokar har zuwa lokacin da aka kammala shari’ar.

Alkali Orrick ya bayyana dokar da wani abu mai kama da tabin hankali.

Lauyoyin masu kara sun ce kudaden da ya kamata a rike na jihohin idan har hakan ya zama dole su ne na gudanarwa ga ma’aikatun shigi da fici.

Magajin garin New York, Bill de Blasio ya jinjinawa hukuncin kotun, a inda yake fadin cewa Shugaba Trump ya nemi ya wuce makadi da rawa.

Wannan hukuncin na wucin gadi dai ana ganin kari ne a kan hukunce-hukuncen da aka yanke a baya wadanda kuma ba su yi wa Mista Trump dadi ba.

Sau biyu aka yi wurgi da dokar shugaban ta hana wasu kasashen musulmi guda bakwai shiga Amurkar.

Image caption

Trump dai na son ganin an gina katangar mai tsawon mil dubu 2000

A wata dambarwar mai kama da wannan ma, shugaba Donald Trump ya yi amai ya lashe dangane da batun yi wa Amurkar shinge tsakaninta da Mexico.

Wannan batu dai na daya daga cikin manyan alkawuran da ya lashi takobin aiwatarwa idan ya hau karaga, a lokacin yakin neman zabensa.

Daman dai ‘yan majalisar dokokin kasar na jam’iyyar Democrat sun sha alwashin yi wa kudirin kutungwila idan har ya zo gabansu.

Za dai a iya cewa firgicin da kalaman mista Trump suka jefa al’ummar Amurka da duniya lokacin yakin neman zabensa, sun fara zama fadi ba cikawa.

An tuhumi Moyes saboda barazanar marin wakiliyar BBC


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kocin Sunderland David Moyes ya ce ya yi nadamar kalamansa ga wakiliyar BBC Vicki Sparks

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi kocin Sunderland David Moyes bayan da shaida wa wakiliyar BBC Vicki Sparks cewa za ta iya “shan mari”.

An nadi muryarsa a kamara yana yin kalaman bayan da kulob dinsa ya yi canjaras da Burnley a gasar Premier.

Moyes ya bayyana matukar “takaicinsa” kan kalaman da ya yi.

Hakan ya biyo bayan tambayar da Vicki ta yi masa kan cewa ko zuwan da Ellis Short ya yi, mamallakin kulob din, ya kara sa shi cikin tsaka mai wuya?

Moyes ya amsa mata da a’a, amma kuma bayan sun kammala hirar tasu, sai ya ce da ita gara ta rika yi a hankali, ta bar ganin ita mace ce, don wataran za ta sha mari.

Tsohon kocin na Everton da Manchester United dai ya bai wa Misis Sparks hakuri daga baya, inda ya ce ya yi matukar da na sanin fadar wadannan kalaman.

South Africa: An fara ƙosawa da mulkin Jacob Zuma


Image caption

Ana zargin Jacob Zuma da aikata cin hanci da kuma azurta kansa da ma abokansa

Kusan za’a iya cewa wasu ‘yan kasar Afrika ta Kudu sun fara ƙosawa da shugaba Jacob Zuma, bayan zarge zargen cin hanci sun daibaibaye shi.

Ana kuma zargin sa da azurta kansa da kuma abokansa, musamman tasirin da ake gani da wasu abokan sa ‘yan kasar India ke dashi wajen tafiyar da mulkin kasar.

An dai yi ta gudanar da zanga-zanga bayan da shugaban ƙasar ya sauke ministan kudin kasar, mista Gordhan daga kan muƙaminsa, mutumin da ake gani da kima a kasar, matakin da ya jefa tattalin arziki dama darajar kudin kasar cikin wani yanayi na rashin tabbas.

Matakin da Mista Zuma ya dauka na sauke Mista Gordhan daga mukaminsa ya fusata abokan adawa da kawayensa, abin da ya haddasa sabani a cikin mulkin jam’iyyar ANC, wadda ke mulki a Afrika ta kudu tun shekarar 1994.

Hakan ya sa wasu shugabanin ANC tababar ko ya kamata Mista Zuma ya ci gaba da mulkin kasar.

Magoya bayan ANC da jam’iyyar SACP da kuma babbar kungiyar kwadago ta kasar (COSATU) sun goyi bayan Zuma ya sauka da mulki.

A wata mai zuwa ne dai ‘yan Majalisar dokokin kasar za su kada kuri’a na goyon baya ko kuma yanke kauna game da gwamnatin sa.

Nigeria: Kun san tsarin biyan kudin aikin hajjin bana?


Hakkin mallakar hoto
AP

Image caption

An gano gawa a jirgin Nigeria mai jigilar alhazai yana mayar da su

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce a bana ba za a fitar da kudin aikin hajji na bai-daya a tsakanin jihohin kasar ba.

Shugaban hukumar, Abdullahi Mukhtar Muhammad, ya ce za a sanar da kudin hajji ne dai-dai da hidimar da kowace jihar za ta yi wa alhajinta.

Abdullahi Mukhtar ya kuma ce kawo yanzu ba a tsayar da kudin kujerar aikin hajjin bana ba.

Dangane da jin dadin alhazai, Mukhtar ya ce alhazai za su samu mahalli mai inganci kuma kusa da harami kamar yadda sauran kasashen duniya ke samu.

Ku saurari hirar Abdullahi Mukhtar tare da Aliyu Tanko:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Abdullahi Mukhtar

Ba cin amanar kasa jagoran 'yan adawar Zambia ya yi ba —Amnesty


Image caption

Da ma dai Hichilema na fuskantar tuhume-tuhume a kan tunzura jama’a su yi bore tun a watan Oktoban bara

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bayyana tuhumar cin amanar kasar da ake yiwa jagoran ‘yan adawa a Zambia da kuma wasu mutane biyar a matsayin gallazawa, in da ta yi kira a kan ayi watsi da tuhumar.

An kama Hakainde Hichilema ne bayan ya tarewa kwambar motocin shugaban kasa Edgar Lungu hanya.

Hayaniya ta ɓarke a lokacin da kwambar motocin shugaban ta yi ƙoƙarin shige na Hichilema.

‘Yan sanda sun ce kwambar motocin Hakainde Hichilema ta sanya rayuwar shugaban kasar cikin hadari.

An dai tsare jagoran ‘yan adawar da wasu mutane biyar ‘yan jam’iyyar United Party for National Development na tsawon makonni biyu, a kan abinda kungiyar ta Amnesty ta ce laifi ne na tsare hanya, ba wai cin amanar kasa ba.

Kungiyar ta Amnesty, ta yi kiran da a gudanar da binciken da mutanen suka yi zargin cewa an azabtar da su.

Cin amanar ƙasa tuhuma ce da ba a bayar da beli a Zambia, kuma ana iya ɗaure mutum mafi ƙaranci shekara 15 ko kuma ma hukuncin kisa.

Da ma dai Hichilema na fuskantar tuhume-tuhume a kan tunzura jama’a su yi bore tun a watan Oktoban bara, matakin da jam’iyyarsa ta ce yunƙuri ne na rufe masa baki.

Kotu ta tura tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu kurkuku


Hakkin mallakar hoto
Other

Image caption

Babangida Aliyu ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015

Wata babbar kotu a Minna babban birnin jihar Naija ta tura tsohon gwamnan jihar Mu’azu Babangida Aliyu kurkuku har zuwa ranar 4 ga watan Mayu bayan da aka gurfanar da shi kan zargin aikata wasu laifuka da suka shafi kudi.

Hukumar EFCC ce ta kai tsohon gwamnan kara a gaban kotu tana zarginsa da aikata wasu laifuka lokacin da yake kan mulki.

Mai shari’a Mohammed Mayaki ya bayar da umarnin a tsare tsohon gwamnan da kuma mutumin da ya yi wa jam’iyyarsa ta PDP takarar gwamna a zaben 2015, Umar Nasko.

Duka mutanen da ake zargin sun musanta tuhumar da ake yi musu.

A farkon watan nan ne hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan, inda ya shafe kwanaki a hannunta kafin a gurfanar da shi.

Tsohon gwamnan na Neja ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015.

Kuma ya fadi takarar kujerar majalisar dattawa da ya nema a zaben 2015.

Mai shari’a Mayaki ya dage sauraron karar har zuwa ranar 4 ga watan Mayu inda zai duba batun belin da wadanda ake zargin suka nema.

Takaddama kan matar da ta fi kowa nauyi


Image caption

Nauyin Eman ya kai kiligiram 500

‘Yar uwar Eman Abd El Aty ‘yar Masar da aka bayyana a matsayin wacce ta fi kowa kiba a duniya, ta zargi likitoci a India da karya kan lafiyar ‘yar uwarta.

A cikin wani sakon bidiyo, Shaimaa Selim, ta ce ‘yar uwarta, Eman Ahmed, na fama da rashin lafiya kuma ikirarin da asibitin ya yi, na cewa ta rage rabin kibarta karya ne.

A makon da ya gabata ne likitoci a asibitin Saifee da ke Mumbai, suka fitar da wani bidiyo da ya nuna cewa Eman din na zaune a kan gado.

Sun dai ce nauyinta ya ragu da kilo dari biyu da hamsin tun bayan da ta iso kasar a watan Fabrairun da ya gabata.

Likitocin sun musanta zargin kuma a cewarsu Emman a shirye take ta koma gida Masar.

Arsene Wenger na shirin sayen sabbin 'yan wasa


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Arsene Wenger na fuskantar matsin lamba daga wasu magoya baya kan ya bar kungiyar

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yana shirin sayen sabbin ‘yan kwallo domin tunkarar kakar wasa ta badi duk da cewa babu tabbas ko zai ci gaba da zama a kulob din.

A karshen bana ne kwantiragin Wenger za ta kare, kuma an ba shi damar sabunta ta na tsawon shekara biyu, amma har yanzu bai bayyana cewa zai karba ba ko kuma a’a.

“Zan ci gaba da aiki har ranar karshe ta kwantiragina,” a cewar kocin mai shekara 67.

“Sayen ‘yan wasa shi ne makomar kulob din kuma abu ne mai muhimmanci.”

Ya kara da cewa makomata ba ita ce almuhimmu ba, abu mafi muhimmanci shi ne makomar kulob din.”

A watan Fabrairu Wenger ya ce zai yanke hukunci kan sabon kwantiragin a watan Maris ko Afrilu kafin daga bisani ya ce “Na son abin da zan yi kuma kwanan nan za ku ji”.

Har yanzu babu wata sanarwa da aka bayar, kuma Arsenal na kokarin samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a badi – bata taba rasa wannan damar ba a shekara 21 da Wenger ya yi a kulob din.

A yanzu dai sun kai wasan karshe a gasar cin kofin FA bayan da suka doke Manchester City a Wembley ranar Lahadi.

Nigeria: 'Likita ya datse' hannun wata jaririya a Kebbi


Image caption

Gwamnatin jihar Kebbi ta kafa kwamiti don yin bincike kan lamarin

Rohatanni daga jihar Kebbi a Najeriya na cewa iyayen wata jaririya sun shiga halin zullumi sakamakon datse hannun jaririyar da wani likita ya yi, yayin nakudar haihuwarta.

Lamarin dai ya faru ne a garin Danko da ke cikin karamar hukumar Danko da ke Wasagu.

Wani dan uwan mahaifin jariryar ya shaida wa BBC cewa “likitan ya ce jaririyar matacciya ce sai an yanke hannunta za a iya fitar da ita”.

Ya kara da cewa uwar jaririyar na cikin koshin lafiya sai dai yarinyar bata da lafiya.

Ya ce hannun jaririyar ne ya fara fitowa a lokacin nakuda kafin su isa wajen likita.

Sai dai ya ce ba zai iya tantancewa ba ko likitan yana da laifi ko bashi da shi ba.

Ya kara da cewa hakkin hukumomi ne su tantance ko likitan na da laifi ko kuma a’a, amma su ba za su dorawa kowa laifi ba.

Gwamnatin jihar Kebbi ta kafa kwamitin bincike domin tantance abin da ya faru.

A Najeriya, kamar sauran wasu kasashe masu tasowa, a kan samu kuskure a wasu lokutan da likitoci ke kokarin yin tiyata.

Nigeria: An bayar da belin jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana zargin Nnamdi Kanui da cin amanar kasa, batun da ya musanta

Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta bayar da belin daya daga cikin jagororin masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Wannan ne karon farko da aka bayar da belinsa tunda aka fara sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Mista Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, tare da wasu mutanen uku, wadanda duka suka musanta zargin da ake yi musu.

Mai shari’a Binta Nyako ta ce ta bayar da belin ne kan dalilai rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sharuddan belin sune sai Mista Kanu ya gabatar da mutane uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

Mai shari’ar ta kara da cewa ba a yarda a ganshi a cikin taron jama’ar da suka wuce mutum 10 ba.

Ta kara da cewa “kar ya yi hira da ‘yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga”.

Tun da farko dai Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya halarci zaman kotun domin karfafa wa Kanu gwiwa.

Kawo yanzu babu tabbas ko gwamnati za ta sake shi kamar yadda kotun ta bukata.

Mista Kanu ya shafe sama da shekara guda a tsare.

'Man Utd na da niyyar sayen Antoine Griezmann'


Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Griezmann ya koma Atletico ne a watan Yulin 2014 a kan kudin da aka ce fan miliyan 24 ne

Wakilin dan kwallon Atletico Madrid Antoine Griezmann, ya ce Manchester United ce ta fi nuna sha’awar sayen dan wasan a duk cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa.

Eric Olhats ya shaida wa wani shirin gidan talbijin na Telefoot a Faransa cewa United sun tattauna yiwuwar biyan farashin yuro miliyan 100 din da aka sanya wa dan wasan.

“United ce ta fara zuwa domin tattaunawa da mu kuma su ne suka fi nuna bukata sosai,” a cewar Olhats.

Griezmann, mai shekara 26, ya zura kwallaye 25 a wasa 46 da ya buga wa Atletico a bana.

Mutumin da ya fi ci wa United kwallo a bana Zlatan Ibrahimovic ya zura 28 ne, sai dai shekararsa 35.

Kuma har yanzu bai cimma yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa ba wacce za ta kare a karshen kakar bana.

Ga shi kuma ya ji rauni wanda zai dauki lokaci kafin ya warke.

Ana sa ran Manchester City za ta bayyana nata tayin a wani kokari na saye dan kwallon na ksar Faransa.

Olhats ya kuma nuna cewa akwai wasu kulob din Turai da ke yunkurin sayen dan wasan wanda tauraruwarsa ke kara haskaka wa.

Boko Haram: Kamaru ta daure wani dan jarida shekara 10


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tuni Ahmed Abba ya riga ya shafe shekara biyu a kurkuku

Wata kotun soji a Kamaru ta yanke hukuncin shekara 10 a gidan yari ga wani jarida na sashin Hausa na gidan rediyon Faransa RFI, Ahmed Abba, bisa zarginsa da alaka da ta’addanci.

A makon jiya ne kotun ta same shi da laifin boye ayyukan ta’addanci da wanke ‘yan ta’adda a rahotanninsa.

Kungiyoyin masu fafutuka sun ce Mista Abba ya yi rahoto ne kawai kan kungiyar ‘yan Boko Haram.

Tun bayan samun shi da laifi kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa-da-kasa mai mazauni a birnin New York na Amurka, wato Committee to Protect Journalists (CPJ), ta yi watsi da hukuncin.

CPJ ta ce ba a yi adalci ba a hunkuncin da aka yanke wa Ahmed, sanna ta nemi a gaggauta sakinsa.

A wata sanarwar da ta fitar, kwamitin ta ce ” bai kamata a ce tun farko ma an tsare da kai kara da ma kama Ahmed Abba saboda aikinsa ba, balle ma har a kai ga yanke mai hukuncin shekara 10 a kurkuku”.

Gidan radiyon RFI da kuma lauyansa sun ce Mista Abba, wanda ya dage kan cewa yana da gaskiya, zai daukaka kara.

Ahmed Abba ya riga ya shafe kusan shekara biyu a gidan yari.

Kamaru ta dade tana shan suka a kan tsare dan jaridar, amma hukumomin kasar sun yi burus da koke-koken da ake yi musu.

Yau ce ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro


Hakkin mallakar hoto
SPL

Image caption

Cutar Malaria ta fi kashe kananan yara a kasashe maso tasowa

Yayin da a yau ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, wasu shugabanni a Najeriya sun danganta karuwar matsalar ga dabi’un jama’a na rashin tsaftace muhallan su.

Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya ce gwamnatocin kasar ana su bangaren na daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai ya ce wajibi ne al’umma sai sun bada gudunmuwa.

Wasu ‘yan Najeriyar dai na ganin rashin mayar da hankali daga bangaren shugabanni shi ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar zazzabin cizon sauro a kasar.

A cewar hukumar lafiya ta Majalisar Dinikin Duniya, wato WHO, daga shekarar 2001 zuwa yanzu, an samu nasarar hana kamuwa da cutar har sau miliyan 663 a yankin nahiyar Afirka kudu da hamadar Sahara, inda a nan ne ake samun kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar.

Ana dai amfani da hanyoyi daban-daban wajen hana kamuwa da cutar, amma kuma wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani da su din na da matukar hadari.

A wani labarin kuma, hukumar lafiya ta duniya, ta ce a karon farko za ta fara riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a kasashe uku na Afrika da suka hada da Ghana da Kenya da kuma Malawi.

Hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin.

Kimanin jarirai dubu da dari bakwai ne ake sa ran za su amfana da allurar wadda za a kwashei shekaru biyu ana yi.

Kasashen Afrika ne dai suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauron, kuma yawancin wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita yara ne.

Nigeria: 'Za a iya bincikar Jonathan idan an same shi da laifi'


Hakkin mallakar hoto
facebook

Image caption

Malami ya ce babu sani babu sabo

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce idan har bincike kan rashawa da cin hanci ya tankarar da tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan, babu makawa za a iya bincikar sa.

Malami ya ce aikin binciken masu laifi karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari babu zabe a ciki.

Abubakar Malami ya bayyana haka a kashi na biyu na hirar da editanmu na Abuja, Naziru Mika’ilu ya yi da shi.

Ku saurari yadda hirar tasu ta kaya.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami

Zan so mu yi wasanmu da Man Untd ba tare da alkalin wasa ba – Toure


Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Doke City da Arsenal ta yi na nufin a karon farko Pep Guardiola zai kare kakar wasa ba tare da kofi ko daya ba a aikinsa na kociya

Yaya Toure ya ce zai fi so su yi wasansu na hamayya na ranar Alhamis da Man United ba tare da alkalin wasa ba, bayan da ya soki alkalancin wasan da aka yi musu a lokacin da Arsenal ta fitar da Man City a Kofin FA.

A wasan da suka yi na kusa da karshe na Kofin na FA, alkalin wasa Craig Pawson ya hana kwallon da Sergio Aguero ya ci a kashin farko na wasan a Wembley, bisa dalilin cewa kwallon ta yi waje tun da farko kafin Aguero ya same ta.

Hotunan bidiyo da aka maimaita na wurin sun nuna ya kamata a ce alkalin wasa ya amince da kwallon a wasan da aka fitar da City da ci 2-1, bayan karin lokacin fitar da gwani.

Toure ya ce, abin ya ba shi takaici, yana ganin ya kamata alkalan wasa su daina haka, domin ba wannan ba ne na farko, akwai wasu lokutan da aka yi musu hakan.

Dan wasan ya ce, watakila ranar Alhamis za su samu alkalin wasan da ya fi kyau, ya kara da shaguben cewa ko ma dai su yi wasan ba tare da wani alkalin wasa ba, domin zai fi son ganin hakan.

Yanzu dai Manchester City ta mayar da hankalinta ga gasar Premier inda take ta hudu, amma United za ta yi mata tsallen-badake ta haure ta idan ta doke ta ranar Alhamis.

Nigeria: Ban gaji biliyan shida ba- Sarki Sanusi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masarautar Kano ta musanta zarge-zargen facaka da kudin da aka yi wa Sarki Muhammaduy Sanusi na II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce abin da ya gada bai wuce kimanin naira biliyan ɗaya da ɗigo takwas ba ne daga sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, maimakon naira biliyan shida da wasu kafofi ke yaɗawa.

A bayanin da ya yi wa manema labarai a ranar Litinin, Ma’ajin Kano wanda shi ne kuma Walin Kano, Bashir Wali, ya ce abin da Sarki Sanusi ya gada daga Sarki Ado Bayerro shi ne N2,875,163,431.17.

Bayanin na zuwa ne daidai lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fara bincike a kan zargin facaka da kudi da ake yi wa sarkin.

Ma’ajin Kanon ya kara da cewar kafin Sarkin Kano Ado Bayero ya rasu “an fitar da N981, 784,503.73 wanda aka biya kwamitin gina gandun sarki Ado Bayero na Darmanawa domin ci gaba da wannan aikin.”

Har ila yau, ma’ajin ya kuma ce “saboda haka abin da ya rage a wannan lokaci bai wuce N1,893,378,927.38 ba. Wannan shi ne abin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya daga.”

Alhaji Bashi Wali ya ci gaba da cewa bayan gadon kudin akwai ayyukan da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwanso (tsohon gwamnan Kano) ta ba da izinin gyara wasu gine-gine a cikin gidan sarki bayan wasu wuraren sun rurrushe.’

Ya ce ba a fara aikin ba sai lokacin da sarki Sanusi ya hau karagar mulki, ya kara da cewar gidan ya sauya siffa.

Alhaji Bashir ya ce gaskiya ne masarautar Kano ta biya Dabogate kudi N152, 627,723 inda ya yi bayanin cewar an bayar da kudin ne saboda gyaran fada da kuma sayen kujeru da sauransu saboda mafi yawancin abubuwan da ke fada na tsohon sarkin da ya shafe shekaru hamsin yana kan karagar mulki ne.

Ya ce motocin da tsohon sarkin ya bari na shi ne na kansa, kuma bayan rasuwarsa aka yi musu kudi inda masarautar Kano ta biya (miliyan 180) domin su zama mallakarta.

Game da zargin kashe naira miliyan 15 kan tafiye-tafiye, masarautar Kano ta ce ba haka lamarin yake ba. Ma’ajin Kano ya ce an kashe kudin kan gyaran zauren da ake fadancin dare a lokacin azumi.

Amman kuma masarautar ta amince cewar an kashe naira miliyan goma sha biyu kan kudin tikitin tafiyar ‘yan tawagar sarki, inda ta kara da cewar shi sarkin Kano da kudinsa yake sayen tikitin tafiya da kansa.

Masarautar ta musanta sayen motar kasaita kirar Rolls Royce da kudin gwamnati, inda ta ce gwamnatin jihar Kano ce ta ba ta umurnin sayen motoci masu sulke bayan harin da aka kai wa motar.

Kun san dan wasan da ya fi Messi da Ronaldo?


Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Adama Traore ne gwarzon dan wasa na daya a Turai…. idan ana maganar iya yanka a wasa ne

A fagen wasan kwallon kafa wata tambaya da aka dade ana yi a wannan zamani ita ce – wane ne ya fi? Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo?

To yanzu dai ta tabbata akwai wani dan wasa da ya fi su duka biyun, dan wasan kuwa ba wani ba ne illa Adama Traore na Middlesbrough.

Kamar yadda wani nazari da Cibiyar Nazarin Harkokin Wasanni ta Duniya (International Centre for Sports Studies (CIES)), ta yi, dan wasan mai shekara 21 dan Spaniya shi ne ya fi kowa a Turai, idan ana maganar iya yanka ne a wasa.

Cibiyar ta samu wannan sakamako ne bayan da ta kasafta yawan yankan da kowane dan wasa yake samun nasara a duk lokacin da ya yi yunkurin yin hakan, da kuma wadanda ba ya samun nasara.

Daga nan ne Cibiyar ta fito da sunayen ‘yan wasa 100 da suka kware a yanka a manyan gasar kwallon kafa biyar na Turai.

A zaben Traore ya zama na daya a gaban Eden Hazard na Chelsea, yayin da Messi na Barcelona ya zamo na shida, a bayan dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha.

Dan wasan gaba na Barcelona Neymar shi ne na hudu, a binciken, wanda Cristiano Ronaldo ko ambato shi ma ba a yi ba a gwanayen ‘yan wasan 100 da suka iya yanka a wasan na tamola.

To sai dai kuma gwanintar yankan ta Traore ba ta yi wani tasiri ba sosai ga kungiyar ta Middlesbrough, domin ba wta kwallo da ya ci mata, in banda daya kawai da ya bayar aka ci, yayin da kungiyar ke zaman ta biyun karshe a teburin Premier.

Kante ya zama gwarzon bana a Ingila


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

N’Golo Kante ya doke Hazard da Kane da Lukaku da Ibrahimovic da Sanchez a zaben

Dan wasan tsakiya na Chelsea N’Golo Kante ya ci lambar yabo ta gwarzon dan wasan kungiyar kwararrun ‘yan kwallon kafa ta Ingila ta kakar 2016-17.

Dan wasan na Faransa mai shekara 26, ya doke Eden Hazard da Harry Kane da Romelu Lukaku da Zlatan Ibrahimovic da kuma Alexis Sanchez, a zaben da takwarorinsa ‘yan wasa suke kada kuri’a.

Dan wasan Tottenham Dele Alli a karo na biyu a jere ya samu lambar yabo ta kungiyar ta gwarzon matashin dan wasa.

‘Yar wasan Manchester City Lucy Bronze ita ce ta ci lambar gwarzuwar ‘yar wasa ta kungiyar a bana.

Yayin da Jess Carter ta Birmingham ta kasance gwarzuwar matashiyar ‘yar wasa ta kakar.

Hakkin mallakar hoto
N’Golo Kante

Image caption

A watan Yuli ne N’Golo Kante ya koma Chelsea daga Leicester

Kante wanda ya yaba da zaben da ‘yan wasan suka yi masa ya ce babbar karramawa ce a gare shi, amma ya ce, ta samu ne da hadin guiwar abokan wasansa.

Dan wasan na tsakiya na kan hanyar sake daukar Kofin Premier da Chelsea, bayan da a kakar da ta wuce ya dauka da Leicester.

Tsohon Kyaftin din Ingila David Beckham ya samu lambar yabo ta kungiyar kwararrun ‘yan wasan na Ingila sabod irin gudummawar da ya bayar a wasan kwallon kafa, a yayin bikin ba da lambobin da aka yi a ranar Lahadi.

Kante ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar ban mamaki da Leicester ta yi ta daukar Premier a shekarar da ta wuce.

Kuma zai iya bajintar zama dan wasa na farko d ya dauki kofi a jere da kungiyoyi daban-daban, idan har Chelsea ta ci gaba da ba wa Tottenham tazara a bana.

Tun lokacin da Chelsea ta sayo Kante a watan Yuli, ta ci gaba daga matsayin da take na tsakiyar tebur zuwa sama, yayin da ya rage wasa shida a kammala gasar ta bana.

Dan wasan na Faransa ya taka leda a duk mintunan wasannin Premier na bana da kungiyarsa ta yi, in banda wasan da suka yi da Bournemouth, ranar 26 ga watan Disamba, a lokacin da aka dakatar da shi sakmakon katin gargadi da aka ba shi a wasansu da Crystal Palace, da kuma mintuna 11 da suka yi da Tottenham ranar 4 ga watan Janairu.

Babu siyasa a binciken masarautar Kano – Muhyi Magaji


Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kanoa a Najeriya, Muhyi Magaji, ya shaida wa BBC cewa babu siyasa a binciken da hukumar ta ke yi kan korafin facaka da kudaden jama’a da ke yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II.

Tuni dai fadar sarkin ta musanta zarge-zargen cewa ya kashe kudade ba bisa ka’ida ba, inda ta ce a shirye take ta bayar da hadin kai game da binciken da hukumomi suke yi.

A wani taron manema labarai da ya kira a fada a ranar Litinin, Walin Kano Mahe Bashir Wali, ya ce babu abin da aka aikata da ya saba wa ka’ida.

Ya kuma gabatar da wasu takardu da ya ce suna nuna yadda fadar ta kashe kudaden da ake magana a kai dalla-dalla kamar yadda doka ta tanada.

Ga abin da Muhyi Magaji ya shaida wa Naziru Mikailu:

Zan dawo da karfi fiye da da – Ibrahimovic


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ibrahimovic, mai shekara 35, ya tunkaro karshen kwantiraginsa na shekara daya a Old Trafford

Dan wasan gaba na Manchester United Zlatan Ibrahimovic ya ce zai dawo da karfinsa fiye da da, bayan da ya ji raunin da zai yi jinya ta tsawon lokaci, a guiwarsa.

Dan wasan mai shekara 35 ya ji raunin ne a kusa da karshen minti 90 na wasan da suka yi na dab da kusa da karshe na Europa, na zagaye na biyu da Anderlecht, a makon da ya gabata.

Ibrahimovic shi ne kan gaba wajen ci wa United kwallo a bana, inda ya ci mata kwallo 28, amma yanzu ba a san lokacin da zai dawo wasa ba.

Dan wasan dan Sweden ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, “zan yi jinya ta wani lokaci, amma ba maganar barin wasa a yanzu.”

Ya kara da cewa, ”a yanzu ina wasa da kafa daya, amma ba wata matsala ba ce wannan.”

Ibrahimovic ya koma Manchester United ne bayan da kwantiraginsa da Paris St-Germain ta kare a kakar da ta wuce, amma har yanzu bai amince da tsawaita kwantiraginsa na shekara daya ba da kungiyar.

Shi ma Marcos Rojo ya ji rauni a guiwarsa a wannan wasa da Ibrahimovic ya ji ciwon, inda ya yi karo da wani dan wasa, aka cire shi a minti na 23 da wasa.

Za a fara rigakafin malaria a Ghana da Kenya da Malawi


Hakkin mallakar hoto
D Poland/PATH

Image caption

An gudanar da gwajin rigakafin a kan yara fiye 15,000

Hukumar lafiya ta duniya ta ce a karon farko za ta fara rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a kasashe uku na Afrika da suka hada da Ghana da Kenya da kuma Malawi.

Hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara rigakafin.

Kimanin jarirai dubu da dari bakwai ne ake sa ran za su amfana da allurar wanda za a debi shekaru biyu ana yi.

Shellar da hukumar ta yi ta biyo bayan wani gwaji na matakin farko da aka yi, wanda ya nuna cewa allurar ta hana mutane hudu daga cikin goma kamuwa da zazzabin cizon tsauro.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce gwajin za iya magance matsalar cutar da kashi 40 cikin 100.

Cutar malaria dai tana hallaka mutane a kalla rabin miliyan a duk shekara.

An samu ci gaba a rigakafin maleriya

• Matsalar zazzabin cizon sauro a duniya

Hukumar ta zabi Ghana da Kenya da Malawi ne saboda suna gudanar da manyan shirye-shirye na magance cutar da amfani da gidajen sauro duk da cewa kasashen na fama da cutar zazzabin cizon sauron.

Sai dai duk da nasarar da wadannan kasashe suka samu akwai wadanda ke kamuwa da cutar miliyan 212 wanda ke janyo mutuwar 429,000 mutane.

Kasashen Afrika ne suka fi fama da cutar zazzabin cutar, kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne.

Tasirin nasarar Barcelona kan Real Madrid


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lionel Messi ya sha kwallonsa na 31st a gasar La Liga na kakar bana

Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallonsa ta 500, abin da ya sa kungiyar ta hau saman teburin gasar La Liga a nasarar da ta zo dab da a tashi a wasan.

Barca, wadda nasararta ta tura ta saman teburi saboda ta fi Madrid yawan kwallo, tana da sauran wasanni biyar, yayin da Real take da wasanni shida.

Casemiro ne ya ci wa masu karbar bakuncin wasan kwallon farko kafin Messi da Ivan Rakitic su sa Barcelona ta tsere wa Madrid inda daga bisani aka ba wa Sergio Ramos jan kati.

Messi da Cristiano sun barar da damar shan kwallaye daga farko .

Real wadda ta fi Barcelona yawan wasannin da za ta buga – ta ji ya kamata a ba ta bugun fenareti a lokacin da Samuel Umtiti ya yi wa Ronaldo keta minti biyu da fara wasa.

Hakkin mallakar hoto
BBC Hausa

Image caption

Irin nasarar da kulob-kulob suka yi a karawarsu da juna shi ake amfani da shi wajen bambanta matsayinsu idan makinsu ya zo daya.

Shin Barca ta fice daga matsala?

Kaiwa matakin kusa da dab da na karshe da kuma yin gogayya wajen lashe gasar La Liga zai yi wuya su kasance matsala ga yawancin kungiyoyin kwallon kafa, amman wannan Barcelona ce.

Yawanci lashe gasa ne abu mafi karanci da ake nema daga duk wani koci da ke jan ragamar Camp Nou. Magoya baya sukan tsammaci cin wasa cikin kwarewa kuma a baya sun nuna rashin amincewa da kwarewar kociya Luis Enrique, wanda zai bar kungiyar a karshen kakar bana.

Amman magoya bayan, wadanda suke kan hanya ba za su iya bayani kan jaruntakar da kungiyarsu ta nuna ranar Lahadi ba. Duk da haka Messi ya kayatar da su da kwallaye biyu kuma kwallon da Rakitic ya zura ya gamsar da su.

Za a iya daga duk wata maganar matsala a lokacin da kungiyar ke cigaba da tinkaho da Messi inda hatsabibin dan wasan yake nuna cewar har yanzu zai iya taimaka wa Barca ta kara da kungiyoyin kwallon kafa da suka fi kwarewa a duniya.

Dan baiwar kwallon kafan, ya ci gaba da taka rawar gani a Barcelona har bayan da Casemiro ya yi masa keta.

Ladan da Messi ya samu bayan haskaka tauraronsa fiye da na Christiano Ronaldo, shi ne kara dasa sunansa a tarihin Barcelona.

Har yanzu Madrid ce za ta iya barar da gasar da kanta

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Casemiro ne ya fara ci wa Real Madrid kwallo a minti na 28

Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai a kaka biyu cikin ukun da suka gabata, amman ba sa samun nasara a wasannin cikin gida. Ba su lashe gasar La Liga ba tun shekarar 2012 inda Barcelona ta lashe kofin sau uku kuma Atletico Madrid ta lashe sau daya.

Bayan an bai wa Ramos jan kati, kuma Madrid ta rama shan da Barca ta yi mata, kungiyar ta Zinedine Zidane ta yi kamar za ta sha kwallon da zai ba ta nasara.

Amman wannan ya bai wa bakin damar sha. Rashin kwarewa ne daga Zidane? Mai yiwuwa ne, amman tun da tana da sauran wasa daya a gasar fiye da sauran takwarorinta, da alama Real Madrid ce za ta iya barar da gasar da kanta.

Idan kungiyar Zidane, wadda ta kamo hanyar zama kungiya ta farko da za ta lashe gasar Zakarun Turai sau biyu a jere, za ta iya cin wasanninta shida da suka rage a La Liga, Zidane zai iya kawo karshen jiran lashe kofin cikin gidan wanda Real Madrid ta shafe shekara biyar tana yi.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Sai wa kuma? Lionel Messi ya sa Barca ta yi nasara a wasan da kwallaye biyun da ya ci ta yadda ya yi wa Barcelona a lokaci da dama,

Nigeria ta kama wiwi na naira miliyan 400 daga Ghana


Hakkin mallakar hoto
BRENDAN SMIALOWSKI

Image caption

A baya dai hukumar ta bayyana cewa kudin tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyin da ta kama za su kai naira biyan daya da dubu 200

Hukumar hana fasa kauri ta jihar Lagos a Najeriya, ta ce ta kama wasu jiragen ruwa makare da tabar wiwi da ake zargin an shigo da ita ne daga kasar Ghana.

Wannan shi ne kame mafi girma da hukumar ta yi a tashi guda a cikin shekaru biyun da suka gabata, kuma kudin wiwi zai kai naira miliyan dari hudu wato dala miliyan daya da dubu dari uku.

A baya dai hukumar ta sha yin kamen miyagun kwayoyi wadanda suka hada da hodar ibilis da wiwi da dai sauransu.

Sai dai hukumar ta kama tabar wiwi mafi yawa da ta yi zargin ana shigo da su ne daga kasar ta Ghana.

‘Yan majalisa sun amince da noman tabar wiwi a Netherlands

Nigeria: An cafke ganyen wiwi na miliyoyin Naira

Shaye-shaye na kamari a Nijar

Za a halasta shan tabar wiwi a Canada

Nigeria: Ana binciken Sarki Sanusi kan zargin facaka da kudin masarauta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sha sukar gwamnatoci a matakan jihohi da tarayya

Hukumomi a jihar Kano da ke Najeriya sun fara bincike Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammdu Sanusi na II a kan zargin kashe makudan kudaden masarautar ba bisa ka’ida ba.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar, Muhyi Magaji ya shaida wa BBC cewa sun samu korafe-korafe daga wajen jama’a kan zargin kashe kudaden asusun fadar da ake zargin Sarkin ya yi tun bayan da aka nada shi a shekarar 2015.

“Mun gayyaci wasu daga cikin manyan ma’aikatan fadar sarki guda biyu domin su amsa tambayoyi game da wannan zargi amma babu Sarki Sanusi a cikin wadanda aka gayyata,” inji Muhyi.

Sai dai bai yi karin bayyani ba kan yawan kudaden da ake magana a kai ba, wadanda rahotanni suka ce sun kai biliyoyin naira.

Kawo yanzu Sarki Sanusi bai ce komai game da wannan zargi ba, amma masu hidima ga masarautar sun musanta batun.

Muhiyi Magaji ya ce binciken ya zama dole saboda korafe-korafen da jama’a da dama suka gabatar a gaban hukumarsa.

Ya kara da cewa “muna yin wannan bincike ne domin mu kare masarautar Kano ta hanyar gano gaskiyar lamarin domin muna wani zamani ne na dandalin sada zumunta wanda ake yada labarai daban-daban.”

A cewarsa kawo yanzu wannan batu zargi ne kawai, babu wani mai laifi har sai an kammala bincike tukunna.

Binciken shi ne irinsa na farko a masarautar Kano a cikin gwamman shekaru.

Sai dai hakan na zuwa ne ‘yan makonni bayan sarki Sunusi ya soki matakin da gwamnatin jihar ta Kano ta dauka na karbar bashin kusan dala biliyan biyu daga kasar China domin gina layin dogo.

Ko da yake hukumar ta musanta cewa binciken da ta ke yi bita da kullin siyasa ne.