Hira da Abba Kyari kan yadda 'kotuna ke sakin 'yan fashi'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sake masu laifi bayan an kama su na sa ‘yan Najeriya suna yanke tsammani daga karfin kotunan kasar na iya hukunta masu laifi

A cigaba da hirar da Ahmed Abba-Abdullahi ya yi da ACP Abba Kyari da ya yi fice wajen kama masu laifi, dan sandan ya fadi dalilan da suka sa ba’a hukunta wasu masu laifin da jami’an tsaro suka kama. Ya kuma yi karin bayani game da irin wahalar da shi da yaransa suka sha wajen kama Evans da ake zargi da kasancewa madugun satar mutane ne a Najeriya.

Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Saurari yadda ‘yan fashi suke fita daga gidan maza domin sata

Kallon fina-finan bincike ya sa Abba Kyari ya zama gagarabadan dan sanda

Lionel Messi yana shirin yin aure


Hakkin mallakar hoto
AFP / Getty Images

Image caption

Lionel Messia da amaryarsa Antonella Roccuzzo suna da yara

Tauraron kwallonm kafa Lionel Messi zai auri kawarsa ta yarinta a garinsu Rosario a Argentina ranar Juma’a.

Dan wasan na Barcelonan zai koma birnin Rosario domin ya auri Antonella Roccuzzo, da suke da alaka kafin ya koma Spaniya a lokacin da yake dan shekara 13.

Jaridar Argentina Clarín ta bayyana auren a matsayin “auren da ya fi ko wanne a wannan shekaran” da kuma “auren da ya fi ko wanne a wannan karnin”.

Baki 260 ake fatan za su halarci shagalin bikin auren, ciki har da takwarorin Messi a taka leda Luis Suárez da Neymar.

Yawancin bakin sun isa da jiragensu.

An kara yawan ‘yan sanda domin a tabbatar da tsaro a harabar otel din za a yi aren, yayin da wani kamfani tsaro mai zaman kansa zai yi aiki ciikin otel din domin hana wadanda ba gayyata ba shiga.

An yi wa kimanin ‘yan jarida 150 rijistan shiga wani wurin manema labarai na musamman, amman ba za su samu cikakkiyar daman shiga wurin da za a cashe bikin ba, in ji masu shirya taron.

A ina amarya da ango suka hadu?

Hakkin mallakar hoto
AFP / Getty Images

Image caption

Mai zane Lisandro Urteaga yana zana wani shararren hoton Messi a wani bango garin Rosario gabannin auren

Messi, mai shekara 30, ya hadu da amaryarsa ne a lokacin da yake dan shekara biyar.

‘Yar uwa ce ga babban abokinsa, Lucas Scaglia, wanda shi ma ya zama dan wasan kwallon kafa.

Messi ya yarda da yarjejeniyar taka wa Barcelona leda ne a lokacin yana dan shekara 13, bisa sharadin cewar kungiyar za ta dauki nauyin nema masa maganin wata cuta.

Ya yi bayani kan irin kalubalen da ya fuskanta na barin abokan arzikinsa a baya da kuma tsohuwar kungiyarsa ta kwallon kafa.

Ango Messi da amaryarsa, wadanda suke zaune a yanzu a birnin Barcelona, suna da yara maza biyu.

A watan Mayu, an yi watsi da daukaka karar da ya yi kan hukuncin daurin wata 21 da aka yi masa sakamakon kin biyan haraji a Spaniya.

Zai yi wuya ya shiga kurkuku domin za a iya hukunta shi ta wa’adin gyara hali ko kuma biyan tara.

Me muka sani game da babbar ranar?

Za a yi bikin ne a otel din City Center da ke garin Rosario, wanda yake da gidan caca a gefensa.

Hakkin mallakar hoto
CityCenter Rosario

Image caption

Yadda aka shirya otel din City Center da ke garin Rosario domin wani buki na baya

Su waye ne kan jerin sunayen baki?

Rahotanni sun ce Messi ya gayyaci tawagar ‘yan wasan Barcelona, ciki har da Gerald Piqué da kuma matarsa, taurariyar waka Shakira.

Takwarorinsa na tawagar wasan kwallon kafa na Ajentina, ciki har da Sergio Agüero, za su kasance a taron.

Clarín ta ruwaito cewar bai gayyaci kowa daga cikin koca-kocansa na baya-bayanan ba, har da kocin Mancester City na yanzu, Pep Guardiola.

Rahotanni daga kasar sun ce gwarzon dan wasan Ajentina Diego Maradona yana cikin wadanda za su halarci bikin.

Hakkin mallakar hoto
AFP / Getty Images

Image caption

Dan wasan Uruguay Luis Suárez ya sauka a Rosario domin ranar bukin dan kulob dinsa

A ina Rosario ya ke?

Birni mai tashar jirgin ruwa na Rosario yana gabar kogin Paraná, kimanin kilomita 300 arewa maso yammacin Buenos Aires a tsakiyar kasar .

Wani shararren dan Ajentina da ya fara rayuwarsa a wannan wuri shi ne Ernesto “Che” Guevara.

An fi sanin Messi da suna Lío a wannan wuri.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Madugun ‘yan kwamisanci Che Guevara sananne ne a garin inda ya fara rayuwarsa

Tun da ya koma Spaniya, Messi ya lashe kyautar Fifa ta Ballon d’Or guda biyar.

Kallon fina-finan bincike ya sa Abba Kyari ya zama gagarabadan dan sanda


Image caption

Mataimakin kwamishina Abba Kyari dan sanda ne da sai ta baci ake nemansa

Abba Kyari ya yi fice wajen kama gagararrun barayi da masu garkuwa da mutane.

Amma labarin rayuwarsa ba ta fara da nasara ba, domin ba aikin da ya fi so ya yi yake yi ba.

A hirar da ya yi da Ahmad Abba-Abullahi, Abba ya bayyana abun da ya sa ya zama dan sanda maimakon matukin jirgi:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda kallon fina-finan bincike ya sa Abba Kyari ya zama gagarabadan dan sanda

Saudi Arabia ta kara wa 'yan ci-rani wa'adin ficewa daga kasar


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Saudiyya ta ba wa ‘yan ci-rani marasa takardun zama a Saudiyya karin lokacin ficewa daga kasar

Saudiyya ta kara tsawon wa’adin kwana 90 ga ‘yan ci-rani marasa takardun zama a kasar, in ji jaridar Fana mai alaka da gwamnatin Habasha.

A ranar Talatar data gabata ne ya kamata shirin afuwar ya kare, amma akwai dubban ‘yan Habasha da har yanzu suke makale a kasar saboda lokaci ya kure musu, in ji gwamnatin ta Habasha.

Ministan Sadarwa, Negeri Lencho, ya fada wa BBC cewa gwamnatin kasar ta nemi Saudiyyar ta kara wa ‘yan kasar lokaci domin su fice daga kasar.

A baya dai Saudiyyar ta bukatar ‘yan ci-ranin marasa takardun zama su fice kafin karshen watan Maris din da ya wuce.

Saudiyya ta yi wa marasa izinin takardun zama afuwa daukar mataki a kansu, amma ta bukaci su fice daga kasar.

Amma jaridar Arab News ta intanet ta ba da rahoton cewa an kara tsawon shirin afuwar da kwana 30 ne kawai.

Evans ya shigar da 'yan sandan Nigeria kara a Kotu


Hakkin mallakar hoto
Idris facebook

Image caption

‘Yan sandan Najeriya sun shafe shekaru bakwai suna farautar Evans

Mutumin da ake zargin shi ne madugun satar mutane a Najeriya, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya shigar da karar ‘yan sanda a kotu.

Evans na zargin supeton ‘yan sandan kasar, Ibrahim Idris da kuma wasu jami’an ‘yan sanda uku a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Lagos, inda yake zargin ‘yan sandan da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Lauyan mutumin ne ya shigar da karar a madadin Evans, inda ya nemi kotu da sa wadanda yake karar su gurfanar da shi ba tare da bata lokaci ba.

Karar wadda aka shigar a makon jiya ta bukaci kotu ta sa ‘yan sanda su tuhume shi idan suna zarginsa da wani laifi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A farkon wannan watan na Yuni ne dai aka cafke Evans tare da wasu mutum shida da suke ayyukan satar mutane.

Kuma tun a shekarar 2013 ne dai aka yi yekuwar nemansa ruwa a jallo.

Sai dai kakakin ‘yan sanda, Jimoh Moshood ya shaida wa BBC cewa sun samu umarnin wata kotun tarayya wadda ta ba su damar tsare Evans har sai sun kammala bincikensu.

Rundunar ‘yan sandan Ghana ma ta sanar da kaddamar da bincike a kan madugun wanda ke da fasfon din kasar, haka kuma iyalinsa ma na zaune ne a Ghanan.

Muna neman haƙuri da ƙarin goyon baya – Buratai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Janar Buratai ya ce suna neman goyon bayan jama’a kan ƙoƙarinsu na ci gaba da samun nasara a kan Boko Haram

Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai ya ƙalubalanci dakarun da ke yaƙi da Boko Haram da cewa su ne da alhakin raba ƙasar da ayyukan ta’addanci.

Da yake jawabi yayin wata hira da BBC, Janar Buratai ya ce ya sha bayani game da batun sassauya sojojin da ke fagen daga wajen yaƙi da ‘yan ta-da-ƙayar-baya idan sun shafe wani lokaci a can.

A cewarsa, wani soja ya taɓa tambayarsa a kan batun karon farko da ya kai ziyara arewa maso gabas, cewa sun yi shekara biyu zuwa uku a yankin.

Buratai ya ce amsar da ya ba shi ita ce: “wannan ƙasar, ƙasarmu ce. Ina ne za a canza ka, ka je? Da a ce muna ƙasar waje ne, an san cewa bai kamata ka jima fiye da kima ba.”

“Amma wannan ƙasarka ce, dole mu zauna mu kare ta.”

Babban hafsan ya ce yakan umarci kwamandojinsa a kan su riƙa ba wa sojojinsu hutun da suka cancanci samu.

“Ina gaya wa kwamandojinsu, su dinga ba su hutu suna tafiya,” in ji shi. “Ya kamata kowa ya riƙa zuwa hutu, sai dai idan wani ya ce an hana shi hutu, to su yi mana bayani, za mu san matakan da za mu ɗauka.”

A cewar Buratai, hare-haren ƙunar-baƙin-wake da ake ci gaba da fuskanta a yankin arewa maso gabas, abu ne da ke buƙatar ƙarin haƙuri.

“An samu nasara, insha Allahu, kuma wannan nasara ta riga ta tabbata. Insha Allahu za mu samu ƙarin nasara a gaba.”

Ya ce yana neman ƙarin goyon baya da haƙuri daga wajen jama’a, da nufin daƙile Boko Haram da waɗanda “‘yan koren” da ke ba wa ƙungiyar bayanai a cikin jama’a.

Janar Buratai ya ce babu tabbas kan iƙirarin da wasu ke yi cewa mai yiwuwa musayar da aka yi da ‘yan matan Chibok ta hanyar sakin wasu kwamandojin Boko Haram ta sake ƙara wa ƙungiyar ƙaimin kai hare-hare.

Da me za ka tuna ɗan ƙwallon Nigeria Nwankwo Kanu?


Image caption

Gidauniyar kula da masu ciwon zuciya ta Kanu tana tallafa wa yara masu larurar ciwon zuciya

Ɗaya ne daga cikin fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka, Nwankwo Kanu na Najeriya ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da ƙasar ta samu yayin gasar Olympics da aka yi a Atlanta cikin 1996. Ya kuma lashe kusan duk kofunan da ake da su a wasan ƙwallon ƙafa, ko da yake, ya fi son a tuna shi da ceton rai fiye da ƙwallon ƙafa. Watanni kaɗan bayan ya ci lambar zinariya a gasar Olympics, ciwon zuciya ya tilasta masa barin ƙwallo har tsawon wata tara. Lamarin da ya sanya shi kafa gidauniyarsa ta kula da masu ciwon zuciya a shekara ta 2000, inda ya fi mayar da hankalinsa.

Kanu ya ce rasuwar ɗan wasan ƙasar Ivory Coast a China ya kamata ya wayar da kan mutane game hatsarin da ke tattare da cutukan zuciya.

Tiote wanda ya mutu yana da shekara 30 a duniya, bayan ya yanke jiki ya faɗi lokacin da yake atisaye a China inda ya taka wa ƙungiyar kwallon kafa ta Beijing Enterprises leda.

Kanu, wanda shi ma ya yi fama da ciwon zuciya a lokacin da yake wasa, ya ce lokaci ya yi da za a cikin filin wasa da wajensa. Dan Najeriyan bai buga wasa ba har tsawon wata tara bayan likitocin Inter Milan sun gano wata tawaya a zuciyarsa.

Kanu ya ce: “Labarin rasuwar Tiote ba mai dadi ba ne. Wannan ba karon farko kenan ba. Mun rasa Marc-Vivien Foe. Ya mutu, kuma babu abin da aka yi. Tiote ya riga mu gidan gaskiya , kuma babu abin da ake yi a kansa.”

Tiote ya shiga jerin ‘yan wasan Afirka da suka mutu a cikin filin kwallo sakamakon ciwon zuciya.

Tsohon dan wasan Ajax Amsterdam da Inter Milan da Arsenal da kuma Portsmouth FC ya ce zai yi iyakar kokarinsa wajen magance matsalar. Yana kokarin gina asibitin ciwon zuciya a kan dala miliyan 17 a Abujan Najeriya. Baya ga haka yana son gina asibitoci irin wannan a wasu kasashen Afirka- daya a gabashin Afirka, daya arewaci, daya kuma a kudancin nahiyar.

Ya ce “Ina magana da abokaina saboda mu iya yin wani abu domin mu sake wayar da kan jama’a, mu yi kokarin taimaka wa yara a Afirka. Mutum daya ba zai iya yin komai da komai ba. Abin da ya faru da Tiote darasi ne ga dukkanmu. Dole a ci gaba da magana a kai. Ba za mu iya bari haka ta ci gaba da faruwa ba, domin matsalar babba ce.”Kasancewarsa, dogo maras jiki da zura kwallonsa mai hatsari da kuma dabarunsa, Tiote ya fita daban a cikin sauran ‘yan kwallo.

Kanu ya fi mayar da hankali kan batun cututtukan zuciya ne yanzu.

Abia Onyebuchi, jagoran gidauniyar kula da masu cututtukan zuciya ta Kanu, ya tuna lokacin da Kanu ya fara mayar da hankali a kan batun.

Abia Onyebuchi ya ce : “An yi masa aiki a Cleveland Ohio a jihar Ohio da ke Amurka. matashin ya dawo, lokacin da Najeriya ta lashe lambar zinariya a gasar kwallon kafa ta Olympics kenan, kwatsam sai aka ji yana da matsalar ciwon zuciya kuma mai yiyuwa ne ba zai sake taka leda ba.”

Ya kara da cewar : ” ‘Yan Najeriya sun taimaka masa da addu’a. Da ya dawo ya ce hanya daya da zai bi ya saka wa abin da ‘yan najeriya da ‘yan Afirka suka yi masa wajen nuna masa goyon baya a lokacin da yake fama da wannan ifti’ila’i, shi ne kafa gidauniyar kula da masu ciwon zuciya ta Kanu.”

An yi wa Kanu tiyata a shekarar 1996 domin kawar da wata cuta da aka gano lokacin gwaje-gwaje a kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan. A lokacin ya samu duniya domin yana cikin murnar lashe zinariya a gasar Olympics da kuma komawa Inter Milan daga Ajax Amsterdam. Labarin matsalar zuciya ya durkusar da kwallonsa. Wannan lamarin ne ya sauya rayuwarsa har abada, abin da ya sa shi kafa gidauniyar zuciya irin wannan a shekara ta 2000. Ya hadu da wakilin BBC a London kuma ya yi karin bayani game da abun da yake shirin yi.

Kanu ya ce :”Burinmu shi ne mu gina asibiti daya a Najeriya da kuma kasashen Afirka hudu. Matsalar dai ta kudi ce. Amman idan muka samu kudin ko kuma muka gina asibitin, zai taimaka matuka saboda a yanzu haka muna kai yara Indiya ne kuma yana da tsada sosai. Yana ba mu wahala. Saboda haka muna kokarin duba yiwuwar daukar mataki ta hanyar gina asibiti ga yara marasa galihu masu matsalar ciwon zuciya.”

Gidauniyarsa tana son taimaka wa matasan Afirka da ke fama da cutukan zuciya iri-iri. Kawo yanzu dai gidauniyar ta yi nasarar yi wa mutum 538 tiyata a Ingila da Indiya da kuma Isra’ila. Karo uku ne kawai ba a yi nasara ba. Wani dalibi a jami’ar Legas, Enitan Adesola, daya ne daga cikin mutane biyu da suka fara cin gajiyar aikin.

“Dole ne in gode masa domin daukar wani babban mataki na taimaka mini saboda ba kasafai ake taimaka wa wanda ba a sani ba. Tamkar Uba yake a gare ni. Ya taimaka mini matuka. Na gode sosai, in ji Enitan Adesola.

Irin wadannan kalaman ne suka sa Kanu yake son ci gaba da taimakawa.

Kanu: “Abu mai kyau ne, idan ka ga mutane suna zuwa suna cewa sun gode. In ka tambaye su me ya sa, sai su ce suna cikin wadanda suka ci gajiyar gidauniyar ciwon zuciya ta Kanu ne. Wannan babban abu ne. Ya fi lashe duk wata gasa dadi.”

Daga ofishoshin gidauniyar da ke Surulere ta Legas, inda a wasu lokuta injin janareta yake samar da wuta, Kanu yana son ci gaba da burinsa na ceton rayuka, kuma yana hada kai da gidauniyar Nelson Mandela a Afirka ta Kudu domin tara kudin gina asibitin ciwon zuciya.

Abia Onyebuchi, jagoran gidauniyar shi yake shirya gangamin tara gudunmawar kafa asibitin.

Abia Onyebuchi: “Gwamnatin tarayya ta ba mu wani fili a Abuja domin gina asibitin. In Allah Ya yarda, fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na Afirka za su buga wasan sada zumunci don gidauniyar zuciya ta Kanu da kuma gidauniyar Nelson Mandela. Abu ne namu na Afirka. Abu ne da muke yi domin kanmu saboda samun sauki.”

Ali Nuhu ya ƙaddamar da fim ɗin Mansoor


Hakkin mallakar hoto
@realalinuhu

Image caption

A cewar Ali Nuhu tsoron masu satar fasaha ya sa ba za a saki fim ɗin ba yanzu sai bayan an gama nuna a silimu

Fim ɗin Mansur, wanda fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya shirya kuma ya ba da umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba da fatiha.

Mahaifiyar Mansur ta yi ƙoƙarin ɓoye masa wannan sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al’amari.

Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.

An ƙaddamar da fim ɗin Mansoor ranar Alhamis ta hanyar nunin farko, a wani gawurtaccen biki cikin wata silima da ke birnin Kano, kuma sai a nan gaba ne za a fitar da faya-fayensa na bidiyo.

Sama da shekara goma da fara tunanin wannan fim, wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana tsarawa da haɗa shi.

Daraktan fim ɗin, Ali Nuhu ya ce jigon Mansoor shi ne juriya da tawakkali don samun waraka ga wani halin alhini da ɗan’adam ka iya fuskanta a rayuwa.

“Akwai soyayya a cikinsa, amma jigonsa ba soyayya ba ce. Darasin da yake ƙoƙarin isar wa al’umma shi ne duk abin da ka ga ya samu mutum a rayuwa…kar ka yi masa gori.

Kar ka tsangwame shi a kan wannan abu. Domin mai yiwuwa hanyar da Allah ya jarabce shi kenan, kamar yadda kai ma a matsayinka na ɗan’adam akwai hanyar da Allah ya jarabce ka.”

Saɓanin yadda aka saba ganin fitattun jarumai a fina-finan Kannywood, a wannan karon an yi amfani da wasu sabbin fuskoki a matsayin manyan jarumai, da suka haɗar da Umar M Sharif da Maryam Yahaya.

Sama da shekara 20 kenan da fara harkar fina-finan Kannywood, amma masu sharhi na sukar cewa ba a sanya fasahar zamani sosai a cikin fina-fianan.

Sai dai masu fim ɗin Mansoor sun ce sun yi ƙoƙarin tunkarar wannan ƙalubale wajen haɗa shi, don haka ne ma a cewarsu, fim ɗin ya kasance mafi tsada a duniyar Kannywood, don kuwa an kashe kusan naira miliyan takwas wajen hadawa da tallata shi.

Zakarun Nahiyoyi: Jamus ta fitar da Mexico da ci 4-1


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ana rade-radin cewa Leon Goretzka zai koma Arsenal a bazara

Jamus ta kai wasan karshe na gasar kofin zakarun nahiyoyi bayan da ta doke Mexico a wasan kusa da karshe da ci 4-1, a gasar da ake yi a Rasha, a ranar Alhamis.

Leon Goretzka na kungiyar Schalke, wanda ake cewa zai koma Arsenal a bazara, wanda ya ci kwallo biyu a wasan shi ne ya fara daga raga a minti na shida da kuma na takwas da fara taka leda.

Sai kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 59, Timo Werner ya ci wa Jamus kwallo ta uku wadda ya kamata a ce ta karya lagon ‘yan Mexicon amma suka ci gaba da matsa Jamusawan.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Timo Werner ne ya ci wa Jamus kwallo ta uku wadda ta sa ya zama daya da Leon Goretzka wajen fin cin kwallo a gasar-uku-uku

Sai a minti na 89 ne hakar ‘yan Mexicon ta fara cimma ruwa bayan da Marco Fabian ya lalo wata kwallo daga kusan tsakiyar fili wadda ba ta zame a ko ina ba sai a ragar Jamus.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

To amma kuma zakarun na duniya ba su sarara ba domin bayan minti 90 na wasan ana shirin tashi sai dan wasan Jamus din na kungiyar Ajax, Amin Younes, ya ci musu kwallo ta karshe kuma ta hudu.

A ranar Lahadi Jamus za ta kara da Chile a wasan karshe, amma kafin sannan a ranar Portugal za ta fafata da Mexico domin samun matsayi na uku.

Ronaldo ya tabbatar da samun tagwaye bayan an doke Portugal


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

An ce Ronaldo ya bar tawagar Portugal a Rasha ne domin ya je ya ga ‘yan biyun nasa

Sa’o’i kadan bayan da Chile ta fitar da Portugal daga gasar cin kofin zakarun nahiyoyi a wasan kusa da karshe a Rasha, Cristiano Ronaldo ya sanar da cewa an haifar masa tagwaye.

Tsawon kwanaki kafafen watsa labarai na Portugal sun bayar da rahoton cewa wata mata da aka sanya wa cikin tayin ‘yan tagwayen a Amurka ta haife su.

To amma duk tsawon lokacin sai bayan da aka fitar da Portugal daga gasar ta Rasha ne a bugun fanareti, Cristiano ya tabbatar da haihuwar.

Inda ya sanar a wani bayani a shafinsa na Facebook cewa, a karshe dai yana matukar farin ciki tafiya domin ya gana da ‘ya’yansa a karon farko.

Daman dai yana da mai suna Cristiano Ronaldo karami , wanda dadaddiyar budurwarsa mai tallata kayan zamani Georgina Rodríguez, ta haifa masa a watan Yuni na 2010.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ronaldo ya fito fili da budurwarsa Georgina Rodriguez da dansu Cristiano Ronaldo Jr lokacin da Real Madrid ta ci kofin Zakarun Turai a farkon watan nan

Wasu rahotanni daga Portugal din sun ce ba jimawa da haihuwar tagwayen mahaifiyar gwarzon dan wasan na duniya Dolores Aveiro ta tafi Amurka.

A yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Portugal ta ba wa dan wasan dama ya tafi ranar Alhamis din nan da safe, domin ya ga ‘yan biyun nasa, wanda hakan ya sa ba zai buga wasan neman matsayi na uku ba na gasar ta zakarun nahiyoyi a ranar Lahadi.

Kafafen watsa labarai na Portugal sun yi ta baza jita-jita cewa ita ma tana da juna biyu, bayan da Cristianon ya sanya wani hotonsa da ita a shafin intanet, inda suke zaune sun dora hannuwansu a kan cikinta, alamar cewa tana da ciki.

Hakkin mallakar hoto
PA/CRISTIANO RONALDO

Image caption

A watan da ya wuce Cristiano Ronaldo ya sanya wannan hoton a shafinsa na Instagram tare da budurwarsa Georgina Rodriguez

Sai dai a lokacin ta yi watsi da rade-radin, inda ta sanya wasu hotunanta a wurin atisaye, da ke nuna ba ta dauke da juna biyu, ko da yake ba a san lokacin da ta dauki hotunan ba.

An fasa sayar da Sunderland, kuma ta shiga zawarcin kociya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kungiyar za ta gana da Simon Grayson wanda shi ne koci na biyu da ya fi dadewa a gasar Championship

An ba wa Sunderland damar tattaunawa da kociyan Preston North End Simon Grayson domin zama kociyansu, kuma an tabatar da dakatar da maganar sayar da kungiyar.

A sanarwar da hukumomin kungiyar suka fitar sun ce mutumin da ya mallake ta Ellis Short zai ci gaba da daukar nauyinta da kansa, bayan da tattaunawar da ake yi da wani katafaren kamfanin Jamus kan sayen kungiyar ta zo karshe.

Sunderland na neman kociyan da zai maye gurbin David Moyes, dan yankin Scotland wanda ya ajiye aiki a watan Mayu bayan da kungiyar ta fadi daga gasar Premier.

A farkon watan nan na Yuni kungiyar ta ce ta dakatar da maganar neman sabon kociya, yayin da take ci gaba da tattaunawa kan yadda za a sayar da ita.

Mutanen Taraba 3000 na gudun hijira a Kamaru


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dama akwai dubban ‘yan Najeriya da ke zaman gudun hijira a Kamaru

Wasu rahotanni na cewa sassan jamhuriyyar Kamaru da suka yi iyaka da jihar Taraba a Najeriya na karbar wasu sabbin dubban ‘yan gudun hijira.

Akasarin ‘yan gudun hijiran Fulani ne makiyaya maza da mata da kuma kananan yara, wadanda suke ficewa sakamakon rikici tsakaninsu da Mambilawa a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba a Najeriya.

An kiyasta cewa kusan ‘yan gudun hijira 3,000 ne suka shiga wasu garuruwa kamar Mayo-Darle a Lardin Adamawan, inda aka sauke a makarantun boko.

Rahotanni daga Mayo-Darle a Lardin Adamawan Kamaru na cewa sabbin ‘yan gudun hijira daga Jihar Taraba a Najeriya na kwararowa domin neman mafaka.

Yayin da wasu ‘yan gudun jihar kuma suka sauka a wajen dangi da ‘yan uwansu da ke Kamaru.

Haka kuma akwai rahotannin da ke cewa akwai wasu dumbin ‘yan gudun hijirar da ke samun kulawa a asibitin Fanso sakamakon raunukan da suka ji.

Dama can kasar ta Kamaru na kula da dubban ‘yan Najeriya da suka tserewa rikicin Boko Haram.

Jermain Defoe ya sake komawa Bournemouth


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jermain Defoe ne na bakwai a jerin ‘yan wasan da suka fi cin kwallo a tarihin Premier

Tsohon dan wasan gaba na Sunderland Jermain Defoe ya koma tsohuwar kungiyarsa Bournemouth bayan da kwantiraginsa ya kare da Sunderland din.

Dan wasan na tawagar Ingila, mai shekara 34, wanda ya kulla yarjejeniyar zaman shekara uku da Bournemouth a yanzu ya ce ya ji dadin dawowa, kuma abin da zai tabbatar da zai yi shi ne cin kwallo.

Lokacin da Defoe yake matashi ya yi kakar wasa ta shekara 2000-01 a matsayin aro a Bournemouth daga West Ham, inda ya ci kwallo a wasa goma a jere.

Tsohon dan wasan naTottenham da Portsmouth da West Ham da kuma Charlton shi ne na bakwai a jerin wadanda suka fi cin kwallo a tarihin gasar Premier, inda ya ci 158 a wasa 468 da ya yi.

Defoe ya koma Sunderland a watan Janairu na 2015 bayan dan lokacin da ya yi a kungiyar Toronto FC ta Amurka.

Kuma bayan ya ceto kungiyar daga faduwa daga Premier a kakar 2015-16 da kwallo 15 ya tsawaita zamansa har zuwa 2019.

Sai dai a yarjejeniyar zamansa a kungiyar akwai sharadin zai tafi idan yana so idan Sunderland din ta fadi daga gasar Premier, wanda wannan shi ne ya ba shi damar barinta bayan da ta gama kakar da ta kare a matsayin ta karshe a tebur.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jermain Defoe ya ci kwallo 18 lokacin da yake zaman aro a Bournemouth a kakar 2000-01

Defoe ya fara taka wa Ingila leda a shekara ta 2004, kuma ya buga mata gasar cin kofin duniya ta 2010, amma kuma bai yi mata wasa ba a tsakanin 2013 da 2017.

Bajintar da yake nunawa a bana ta sa kociyan Ingila Gareth Southgate ya sake gayyato shi tawagar kasar, kuma ya ci mata kwallonsa ta 20 a wasan da suka yi da Lithuania a watan Maris, na neman damar zuwa gasar cin kofin duniya.

Lyon ta ki sallama wa Arsenal Lacazette


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alexandre Lacazette ya ci wa Lyon kwallo 100 a wasa 203, kuma ya ci wa Faransa 1 a wasa 11

Kungiyar Lyon ta ki sallama wa Arsenal dan wasanta na Faransa Alexandre Lacazette mai shekara 26, amma dai suna ci gaba da tattaunawa.

Haka kuma babu tabbas cewa Gunners din za ta samu dan wasan tsakiya na Monaco Thomas Lemar, mai shekara 21, domin a nan ma an yi watsi da tayinta.

Sannan har yanzu ba kungiyar da ta nuna wa Arsenal din bukatarta ta sayen dan wasan gaba na Chile Alexis Sanchez mai shekara 28.

Sauran shekara daya ta rage wa Sanchez a kwantiraginsa, amma kuma Arsenal din za ta iya barinsa ya tafi idan ta samu kudin da ta ga ya dace a kansa.

Sai dai kuma sakin dan wasan ya dogara ne ga wasu abubuwan, kamar irin ‘yan wasan da Arsenal din ta samu da za su kara mata karfi, da kuma kungiyar da ta neme shi, domin ba za ta so ta sayar da shi ga wata kungiya ta Ingila ba.

Amma kuma duk da haka Arsenal din na fatan Sanchez, wanda shi ne ya fi ci mata kwallo a kakar da ta kare zai sabunta kwantiraginsa.

A Niger mutum hudu sun mutu a hari kan sansanin 'yan gudun hijira


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yankin Diffa na karkashin dokar ta-baci

A jamhuriyyar Nijar, rahotanni daga jihar Diffa na cewa wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a sansanin ‘yan gudun hijiran Nigeria da ke garin Kablewa cikin gundumar Gigmi.

Mutane hudu ne dai suka halaka ciki har da ‘yan kunar bakin waken mata biyu a ranar Laraba da daddare, yayin da wasu mutum goma kuma suka jikkata.

Wasu rahoatnni sun ce masu kunar bakin wake hudu ne suka je sansanin, maza biyu da mata biyu.

Sai dai mazan sun labe ne daga nesa, inda suka ruga zuwa yankin tafkin Chadi bayan matan sun tayar da bama-baman da ke jikinsu.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun samu shiga sansanin ne duk da cewa akwai jami’an tsaro a wurin, ko da yake a yanzu an kara karfafa matakan tsaro a ciki da wajen sansanin bayan harin.

Harin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kungiyar tarayyar Afrika and shugaban kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde ya yi kira ga kasashen Afrika su dogara da kansu wajen yaki da yan ta’adda a yankin Sahel.

Shugaban ya bukaci kasashen nahiyar da su yunkura su samar da sojojin da za su yi yaki da ta’addanci, ganin kungiyar rundunar Majalisar Dinkin Duniya, MUNISMA da ke Mali ba ta tabuka wani abin a zo a gani ba.

Mista Conde ya furta wannan maganar ce a yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar Chadi a ranar Laraba.

Ko da yake kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin

Sai dai kasashen Najeriya, Nijar da Kamaru na daga cikin kasashen da kungiyar Boko Haram take yawan kai hare-hare a yankin tafkin Chadi.

Tuni dai aka kafa wata rundunar hadin guiwa ta kasashen yankin tafkin Chadi da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

An gurfanar da wani kan daukar bidiyon mace tana tatsar ruwan nono


Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Ana kara nuna bukatar kamfanoni su samar da wurin da mata za su iya shayar da jariransu

Wata mata ta kai karar wani abokin aikinta kotu, bisa zarginsa da daukar hoton bidiyonta a asirce tana tatsar ruwan nono, a wajen aiki a kasar Afrika ta Kudu.

An zargi mutumin wanda jami’ar Cape Town ta dakatar, da sanya bidiyon da ke watsa abu kai tsaye a wani daki a jami’ar a ranar 13 ga watan Yuni.

Matar ta rubuta a shafinta na intanet cewa ta fusata da ganin cewa samar wa jaririnta abinci ya zamo “wata hanya mara ma’ana ta samun biyan bukata”.

An gurfanar da mutumin kuma tuni aka fara bincike a kan lamarin.

‘Yan sandan yammacin Cape sun tabbatar da cewa an fara binciken ma’aikacin jami’ar mai shekara 38 a duniya.

Kafafen yada labarai na kasar sun bayyana yadda matar da yada “bacin ranta” a kan lamarin, cewa ta dauka tana wani daki ne a ‘kebe inda babu kowa kuma a kulle’ sai ta fara tatsar ruwan nonon kafin ta farga cewa ana daukar hoton bidiyonta.

Ta ce “Abin haushi ne ainun ace muna rayuwa a duniyar da iyaye mata ta duk yadda muka zabi mu shayar da jariranmu, sai an samu wani ya ci mutuncinsu saboda suna da rauni.”

A fadin duniya dai ana nuna bukatar ma’aikatu su samar da kebantaccen wurin da iyaye mata za su iya shayar da jariransu.

Nigeria za ta fara fitar doya zuwa Birtaniya


Hakkin mallakar hoto
Pascal Deloche /GODONG

Image caption

Najeriya tana neman kara hanyoyin samun kudaden kasashen waje

Ranar Alhamis ce Najeriya za ta kaddamar da shirin fara fitar da doya daga kasar zuwa Birtaniya.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da shirin, ministan noma na Najeriya, Audu Ogbeh, ya ce abun kunya ne a ce Najeriyar da take samar da kashi 61 cikin 100 na doya a duniya ba za a samu doyarta a kasashen waje ba.

Mista Ogbe ya ce kasar Ghana tana neman samun dala biliyan hudu daga doya a ko wace shekara, yana mai karawa da cewar dole Najeriya ta fitar da dukkan abun da kasashen waje suke nema domin ta kara hanyoyin samun kudaden kasashen waje.

Ya ce gwamnatin tana shirin kera sabon garma da zai iya yin kunyan doya da yawa lokaci kadan domin kasar ta kara yawan doyan da take nomawa.

Amman wasu ‘yan kasar sun fara nuna fargaba game da shirin suna masu cewar shirin zai sa doya ya kara tsada.

Ministan noman kasar ya ce shirin ba zai kawo tamowa ba domin kasar ba ta da matsalar karancin abinci kuma ana asarar doya mai yawa saboda rashin wuraren adana doya.

Ya ce gwamnatin kasar ta ce za ta samar da na’urori na adana doyar.

Dalilin barin jirgin Buhari a filin jirgin sama na London


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ki cewa uffan kan batun rikicin na APC

Kakakin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa jirgin saman shugaban kasar na ajiye a filin jirgin sama na Stanstead dake birnin Landan, tun da ya kai shugaba Buharin Ingila domin neman lafiya.

Amma ya musanta cewa ana kashe makudan kudaden wajen biyan kudin ajiyar jirgin.

Garba Shehu, wanda shi ne kakakin shugaba Buhari ya bayyan haka ne a cikin wasu bayanai da ya raba wa maneman labarai, inda ya kara da cewa “Abu ne mai muhimmanci a gane cewa domin dalilan tsaro, da na diflomasiya, da martaba, babu wani shugaban kasa a duniya da yake tafiya wata kasa ba tare da an tabbatar da an samar da jirgin komawarsa gida ba cikin gaggawa, idan hakan ya zama wajibi”.

Ya kuma kara da cewa “Jami’an sojin kasar nan ba zasu bar aikinsu na kula da babban kwamandan sojojin Najeriya ba a duk irin halin da ya sami kan shi.” Inda kuma ya ce “Wannan shi ne tsarin da ake bi a kowace kasa ta duniyar nan”.

Kakakin ya karyata masu sukar gwamnatin a shafukan sada zumunta, inda suke cewa gwamnatin na kashe kimanin dalar Amurka 4,000 a matsayin kudin ajiyar jirgin shugaban a kowace rana.

“Wadannan alkaluman babu gaskiya a cikinsu. An tabbatar mana cewa a kan ba shugabannin kasashe wani farashi na musamman wanda bai kai na ‘yan kasuwa ba.”in ji kakakin.

Ya kara da cewa “Kudin da ake cajin Najeriya ba zai wuce fam 1,000 ba a kowan yini, abin da bai wuce kwatan wanda ake bazawa ba”

Idan ba a manta ba, mutane sun yi ta baza labaran irin kudaden da gwamnatin Najeriya ke kashewa wajen ajiyar jirgin saman shugaba Buhari wanda ya shafe kwanaki 50 a yau yana jinya a birnin Landan.

Habasha ta bukaci Saudiyya ta kara wa'adin afuwa ga baki 'yan ci-rani


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dubban Habashawa ne ke zuwa Saudiyya da nufin samun ayyukan yi

Gwamnatin Saudiyya ta bai wa dubban bakin ‘yan ci-rani da suka shigo kasar ba bisa ka’ida ba, wa’adin kwana 90, kamar yadda hukumomin Ethiopia suka bayyana.

Ministan sadarwar kasar Negeri Lencho ya shaidawa BBC gwamnatin Habasha ta roki hukumomin Saudiyya su karawa ‘yan ciranin wa’adin.

Ya kara da cewa fiye da ‘yan kasar 45,000 ne suka dawo gida, kuma har yanzu akwai wasu dubban da su ke jiran lokacin komawa kasarsu.

Mutanen Habasha dai na ayyukan da suka shafi gine-gine, da aikatau a gidajen larabawa.

Mista Negeri ya ce gwamnatinsu na jiran amsar da Saudiyya za ta ba su, wanda ya ke fatan za ta zamo mai armashi.

A watan Maris da ya wuce, ministan cikin gidan Saudiyya yarima Mohammed bin Naif bin Abdulaziz,ya sanar da yi wa ‘yan cirani mazauna kasar ba bisa ka’ida ba an ba su wa’adin watanni uku su fice daga Saudiyyar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ba za ta hukunta wadanda suka kawo ‘yan ciranin ba, da gidaje ko kamfanonin da suka dauke su aiki, duk da cewa sun take dokar kasar ta hanyar zama cikin ta ba tare da takardar shaida zaman kasa ba wato Iqama.

A shekarar 2013 ma hukumomin Saudiyyar sun yi irin wannan afuwar, amma duk wanda aka samu da ketare wa’adin zai fuskanci fushin hukuma, da suka hada da zaman gidan kaso da biyan tara.

Haka kuma, a wannan lokacin an hallaka ‘yan Habasha da dama a wata zanga-zanga da suka yi taho mu gama da ‘yan sanda, lokacin da gwamnati ta sha alwashin tasa keyarsu kasashen su.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Yan cirani a motocin safa-safa za a fice da su daga kasar Saudiyya shekarar 2013

Mista Negeri ya kuma ce mutane sun yi hasashen daman Saudiyya ka iya tasa keyar ‘yan ciranin kasashen su bayan kammala azumin watan Ramadan.

A bangare guda kuma hukumomin Habasha sun sanar da ware wasu kudade dan tarbar ‘yan kasar da za su dawo gida, da sama musu muhalli.

Auren wuri na kawo koma bayan tattalin arziki?


Hakkin mallakar hoto
kano state government

Image caption

Auren zawarawa ma na kawo koma bayan tattalin arzikin?

Wani rahoto da bankin duniya ya fitar ya ce aurar da mata da wuri na kawo koma bayan tattalin arzikin duniya.

Rahoton ya ce auren wurin yana janyo asarar biliyoyin dala.

A cewar rahoton idan aka daina yi wa ‘yan mata auren wuri, za a samu karin walwala da habakar tattalin arziki.

Rahoton ya bayar da misali da kasar Uganda wadda aka samu raguwar haife-haife lamarin da ya sa kasar ke iya tanadin $2.4bn.

Dr Adamu Isa, wani masani kan harkokin da suka shafi rayuwar mata, kuma shugaban sashen kula da lafiyar al’umma a jami’ar tarayya da ke Dutse a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa wadanda suka fitar da rahoton suna kallon rayuwa ta fuskoki da yawa.

“Daya daga cikin su shi ne da a ce ba a yi wa yarinya aure da wuri ba, an bar ta ta yi karatun jami’a za a dama da ita, ta samu aikin yi. Sannan kuma za ta iya rike babban mukami da za ta iya tallafawa iyali da danginta”.

Sai dai wasu ‘yan kasar na ganin auren wuri yana da amfani domin kuwa wasu mazan za su bar ta ta yi karatu har ma ta samu akin da za ta taimake shi da ma iyalinta.

Wane ne Danbaba Suntai?


Hakkin mallakar hoto
NO CREDITI

Image caption

Jinyar da Suntai ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce sosai a Taraba

An haifi Danbaba Danfulani Suntai ne a ranar 30 ga watan Yunin 1961 a kauyen Suntai da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya.

Ya yi karatun sakandarensa a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano tsakanin 1975-1980 sannan ya halarci makarantar share fagen shiga Jami’a da ke Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria tsakanin 1980-1981.

Ya yi karatun digirinsa a fannin hada magunguna a Jami’ar Ahmadu Bello University inda ya kammala a 1984.

Danbaba Suntai ya samu horo na sanin makamar aiki a asibitin kwararru na Yola kuma ya yi hidimar kasarsa a wani asibitin Ijaiye da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun tsakanin 1985-1986.

Daga nan ne ya soma aiki a asibitin Ganye da ke tsohuwar jihar Gongola har shekarar 1991.

Suntai Suntai ya tsunduma cikin harkokin siyasa inda aka zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar Bali tsakanin1989-1993.

A lokacin zabukan shekarar 1999, ya zama shugaban jam’iyyar All People’s Party (APP) na jihar Taraba.

An nada shi a matsayin kwamishinan ilimi tsakanin 2000-2003, da na lafiya tsakanin 2003-2005 kafin ya zama sakataren gwamnatin jihar Taraba tsakanin 2005-2007.

Gabanin zaben 2007, abokin Danbaba Suntai, wato Danladi Baido ya lashe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP amma daga bisani an haramta masa takara.

Wata biyu bayan haka ne, PDP ta maye gurbinsa da Danbaba Suntai, wanda bai tsaya zaben fitar da gwanin ba.

Baido ya goyi bayan Suntai, kuma a watan Afrilun 2007 aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Taraba.

An zabe shi a karo na biyu ranar 26 ga watan Afrilun 2011.

Tsohon gwamnan jihar ta Taraba ya yi hatsari a jirgin da yake tukawa ne a watan Oktoban 2012, inda ya samu matsala a kwakwalwarsa.

Suntai ya rasu ranar 28 ga watan Yunin 2017 yana da shekara 56.

Obama da iyalansa na shakatawa a Indonesia


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mista Obama da ‘yarsa Malia sun yi wasanni a lokacin hutun na su.

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama da iyalansa sun tafi hutu kasar Indonesia, inda suke ta kai ziyarar fitattun wurare a kasar ciki har da wuraren bauta.

Obama da mai dakinsa da kuma ‘ya’yansa mata biyu, sun fara sauka ne a tsuburin Bali, daga bisani kuma suka kai ziyara wurin bautar addinin Budda da ke Java a ranar Laraba.

Obama dai sanannen mutum ne a kasar, ya kuma samu tarba ta musamman daga mutane inda suka yi ta daukar su hotuna.

A zamanin kuruciyarsa, Obama ya taba zama a Indonesia na tsahon shekara hudu.

Ya fara zama a kasar ya na da shekara shida, lokacin da mahaifiyarsa ta auri wani dan Indonesia bayan mutuwar auren ta da mahaifinsa dan kasar Kenya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mista Obama ya kai ziyara wurin bautar mabiya addinin Budda, mai dadadden tarihi

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Ya’yan shugaban ba su raka mahaifinsu da mahaifiyarsu Indonesia ba a shekarar 2010, lokacin da suka kai ziayara.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Masoyan tsohon shugaban kan taru da jinjina masa, ya yin da a lokuta irin wannan ake kara matakan tsaro dan bashi kariya

A shekarar 2010 ya sake dawowa kasar tare da mai dakinsa Michelle, a matsayin shugaban kasar Amurka.

Bayan kammala wa’dinsa a matsayin shugaban Amurka, ‘ya’yansa na yawan yi wa iyayensu rakiya idan za su yi balaguro.

Haka kuma a tafe suke da jami’an tsaro, domin ba su kariya.

A ranar Juma’a ne ake sa ran Mista Obama zai gana da shugaba Joko Widodo na Indonesia, a fadar gwamnatin kasar da ke kudancin birnin Jakarta.

Zakarun Nahiyoyi: Chile ta yi waje da Portugal da 3-0


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Claudio Bravo ne ya zama gwarzon wasan, inda ya doke dukkanin fanareti uku da ‘yan Portugal suka buga

Chile ta yi waje da Portugal a wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun nahiyoyi da ci 3-0 a bugun fanareti a gasar da ake yi a Rasha.

Bayan minti 90 da kuma karin minti 30 na fitar da gwani, ba kasar da ta zura kwallo, hakan ya sa aka je bugun fanareti.

Chile ce ta fara daukar fanaretin inda Arturo Vidal ya jefa ta a raga, sai kuma Ricardo Quaresma ya daukar wa Portugal inda golan Chile kuma dan Manchester City Claudio Bravo ya kade ta.

Aranquiz da Alexis Sancez dukkaninsu sun ci wa Chile bugunsu, yayin da Joao Moutinho da Nani suka barar da tasu, inda Claudio Bravo ya rika kade kwallon.

Wannan ne ya sa ba sai an kai ga ci gaba da bugun ba, abin da ya sa Ronaldo bai kai ga bugawa ba domin Chile ta ci uku Portugal ba ta zura ko daya ba.

A ranar Lahadi Chile za ta yi wasan karshe tsakaninta da Jamus ko Mexico, wadanda su kuma sai a gobe Alhamis za a san gwani a cikinsu.

Kafin wasan na karshe za a yi wasan neman matsayi na uku tsakanin Portugal da wadda za a fitar tsakanin Jamus da Mexico.

Me yasa mata a India ke rufe fuska da kan shanu?


Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Hotunan sun janyo masa farin jini da kuma bakin jini

Wasu hotunan da aka dauka na matan da ke rufe fuskarsu da kan saniya a Indiya, ana tambayar ko shanu sun fi mata daraja a kasar ya ja hankali matuka a shafukan intanet a kasar. Lamarin da kuma ya janyo fushin wasu ‘yan kasar a kan mai daukar hoton, wani matashi mai shekaru 23.

“Na damu matuka da abin da ke faruwa a kasata, ace an fi bai wa shanu muhimmanci fiye da mata, ta yadda idan aka yi wa mace fyade ko aka muzguna mata sai ya dauki mai tsawo lokaci kafin a bi mata hakkin ta, fiye da shanu da mabiya addinin Hindu ke bautawa.” Sujatro Ghosh mai daukar hoto kuma mazaunin birnin Delhi ya shaida wa BBC.

Kasar ta indiya dai ta yi suna wajen aikata laifukan fyade a kan mata, inda wasu alkaluman gwamnati suka nuna cewa ana samun rahoton yi wa mace fyade a duk mintoci 15.

“A kan dauki shekarau ana irin wadannan shari’u a kotu kafin a hukunta wanda ya aikata laifin, amma idan aka ce batun ya shafi yanka sa ne , yanzu za ka yi mabiya addinin Hindu sun je sun kashe ko kuma sun yi wa wanda suke zargi da yanka wa dukan tsiya.”

Wannan abin da ya yi a cewarsa “wata hanya ce ta nuna adawa” a kan tasirin da kungiyoyin kare shanu wadanada ke kara karfi tun bayan da jam’iyyar mabiya addinin Hindu ta BJP da firai minista Narendra Modi ta hau mulki a shekarar 2014.

“Abin da ya faru na kisan Dadri inda aka kashe [a lokacin da wasu mabiya ‘yan Hindu suka kashe wani musulmi bisa zargin ya ci naman saniya ya kuma boye wani naman] da kuma wasu hare-hare na addini da a kan Musulmai da masu kare shanu ke kaiwa. ” In ji Ghosh.

Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Mabiya addinin Hindu sun yi masa barazana

Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Wasu mata daga wasu sassan duniya na son suma su saka kan saniyar

A ‘yan watannin baya-baya sa ya zamo dabbara da ake matukar kimarsa a India.

Jam’iyyar ta BJP ta jadadda cewa dabba ce mai tsarki saboda haka dole a kare ta. An haramta yanka shanu a jihohi da dama, inda aka sanya horo mai tsauri a kan duk wanda ya keta dokar, a yayin da kuma majalisa ke shirin yin wata dokar da zata kai ga hukuncin kisa ga wanda ya aikata laifin.

Sai dai cin naman saniya halal ne ga Musulmi da Kirista da miliyoyin mutane wadanda masu kare shanu ke kaiwa hare-hare.

An kashe kimanin mutum 12 a cikin shekaru biyun da suka wuce saboda shanu. Ana kai hari kan mutum ne da an rafa jin jita-jita kuma wasu muslmin ma an kai musu harii ne don sun dauko shanun domin a tatsi nono a jikinsu.

Ghosh wanda ya fito daga birnin Kolkata da ke arewacin kasar ya ce ya fara gano wannan “amarin mai cire da hadari ne na hada addini da siyasa” bayan ya komo Delhi a ‘yan shekarun da suka wuce. Haka kuma a cewarsa “wannan abin da na yi wata hanya ce ta nuna adawa cikin ruwan sanyi da zai yi matukar tasiri”.

A farkon wannan watan ne ya sani kan sa (ba na gaske ba) a wani shago a birnin New York, kuma bayan ya koma gida ne ya fara daukar hotunan mata a gaban wuraren bude ido da gine-ginen gwamnati da kan tituna, wasu a cikin gida ko kwale-kwale da ma jirgin kasa don nuna cewa “mata na fuskantar barazana a ko ina suke”.

Ya ce “Na dauki hotuna mata daban-daban, inda na fara dauka daga birnin Delhi, babban birnin kasar kuma matattarar siyasa da addini har ma muhawara daga nan take farowa.

“Na dauki hoton farko a gaban mashigin India, inda masu yawon bude ido suka fi zuwa a Indiya. Sai na dauki wata mai tallar kayayyakin zayyana a kofar fadar shugaban kasa, wata kuma a cikin kwale-kwale a kan kogin Hooghly da ke Kolkata da gadar Howrah ta baya.”

Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Mabiya addinin Hindu na daukar saniya wata abar bauta ce

Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Batun yanka saniya ya janyo asarar rayukan mutane, musamman musulmi a Indiya

Matan da suke cikin hotunansa wadanda ya sani ne saboda a cewarsa “batu ne mai sayar da jijiyar wuya, saboda haka zai yi wuya ka nemi wadda baka sani ba ta yi maka.”

Lokacin da ya wallafa hotunan a dandalin sa da zumunta na Instagram a makonni biyu da suka wuce “an yaba sosai. kuma a makon farko ne miliyoyin mutane suka kalli hotunan, masu fatan alheri da ma mutanen da ban sani ba sun dinga yabawa.”

Amma bayan kafafen yada labaran Indiya sun dauki labarin sun sanya shi a shafukansu na Facebook da Twitter, sannan ne kuma aka fara yi mini raddi.

“Wasu ma sun yi mini barazana wasu sun yi ta aibata ni , wasu ma na cewa ni da matan da ke cikin hotunan kamata yayi a kai mu masallacin Jama na Delhi a yanka mu kuma a bayar da namanmu ga mace ‘yar jarida. Su ce za su so suga mahifiyata na kuka a kan gawata.”

Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Hotunan na hannunka mai sanda ne ga jam’iyyar BJP mai mulki

Hakkin mallakar hoto
Sujatro Ghosh

Image caption

Hotunan na nuni da muhimmancin da aka baiwa sa fiye da matan da ake yi wa fyade a kasar

Wasu ma sun kai koke ne ga ‘yan sandan Delhi, “suna zargin cewa ina yunkurin tayar da zaune tsaye saboda haka yakamata a kama ni”.

Ghosh bai yi mamakin abin da aikinsa ya janyo masa ba, inda ya amsa cewa “hannunka mai sanda ya ke yi wa” jam’iyyar BJP.

“Na yi wani bayani ne da ya shafi siyasa, amma idan aka kalle shi da kyau za a ga fifikon da ake bai wa mabiya addinin Hindu, kuma dama can haka batun yake, sai dai a yanzu ya fi fitowa fili ne saboda su suke jan ragamar kasar tun shekaru biyu da suka wuce.”

Barazanar da ake yi masa ba ta sa ya ji tsoro ba. “Bana wani fargaba domin na san abin da na yi zai yi tasiri mai kyau a kan al’umma da dama,” In ji mai hoton.

Sai wani abu mai kyau da ya samu daga wannan abun shi ne mata da dama na kiransa daga sassa daban-daban na duniya suna yi masa tayin cewa su ma suna so su sanya kan saniyar a fuskarsu domin su shiga wannan kamfe din da yake yi.

Abin da ke nufin cewa kan san zai ci gaba da yin bulaguro.

Tsohon gwamnan Taraba, Danbaba Danfulani Suntai, ya rasu


Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Marigayi Danbaba danfulani Suntai ya yi jinyan sama da shekera hudu bayan sakamakon hatsarin jirgin sama

Tshohon gwamnan na jihar Taraba Danbaba Danfulani Suntai ya rasu yana da shekara 56, bayan shafe kusan shekara hudu yana jinyar hatsarin da yayi cikin jirgin saman da yake tukawa.

Da yake tabbatar da mutuwar, tsohon kwaminishinan watsa labaran jihar, Emamanuel Bello, ya ce gwamnan ya rasu ranar Laraba.

Dan Fulani Suntai ya zama gwamnan jihar Taraba ne ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, kuma ya sake komawa kujerar a shekarar 2011, amman jirgin da yake tukawa da kansa ya yi hatsari ne ranar 25 ga watan Oktoban 2012, a Yolan jihar Adamawa.

Bayan ya samu kulawa a asibitoci a birnin Yola da Abuja, sai aka garzaya da shi Jamus da Amurka domin samun karin kulawa.

A wanna lokacin dai jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya ta shiga dambarwa siysa game da lafiyar gwamnan, kuma bayan ya shfe wata goma yana jinya a kasar waje, Danfulani Suntai ya dawo jihar ranar 23 ga wata Agustan shekarar 2013 a lokacin da magoya bayansa ke cewar ya na da lafiyar da zai iya ci gaba da mulkin jihar.

Amman bayan rikice-rikicen siyasa na makonni, an gano cewar gwamnan ba shi da lafiyar da zai iya ci gaba da mulkin jihar, Kuma mataimakinsa Garba Umar ya ci gaba da zama mukaddashin gwamna kafin guguwar rikicin siyasar jihar ta cire shi.

Wani jami'in EFCC ya kubuta a hannun 'yan bindiga


Hakkin mallakar hoto
EFCC

Wani babban jami’in Hukumar hana yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude masa wuta a birnin Port Harcourt na jihar Rivers.

Mista Austin Okwor, wanda jami’i ne ofishin EFCC a Port Harcourt, ya bar ofishin hukumar bayan ya tashi aiki a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude masa wuta. Ya yi sa’ar tsere wa maharan amma sai da ya sami raunuka domin sun cigaba da harbinsa.

Babban jami’in shiyyar Port Harcourt na hukumar EFCC ya ce an riga an shaida wa ‘yan sanda wannan lamarin.

Mista Okwor na cikin jami’an da ke binciken batutuwan da suka shafi wasu baragurbin jami’an bangaren shari’a.

Kafin wannan harin, jami’in ya sha samun sakonnin barazana. An sanar da ‘yan sanda sako na baya-bayan nan da ya samu a watan Mayun bana.

Idan ba a manta ba, a watan Satumba na 2014 aka kashe jami’in hukumar mai kula da sashin bincike, Abdullahi Mu’azu a Kaduna. Watanni shida kafin wannan lamarin an kai wani harin a kan motar dake dauke da wasu jami’an hukumar masu shigar da kara a wata kotu a birnin Owerri na jihar Imo.

A sanadiyyar harin aka kashe Sajent Eze Edoga kuma aka raunata Joseph Uzor, babban lauyan hukumar.

Tennis : An ba wa Geneva damar gudanar da wasan kofin duniya na farko


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Argentina ta doke Croatia a wasan karshe na Davis Cup a 2016

Hukumar kwallon tennis ta duniya ta zabi Geneva a matsayin inda za a gudanar gasar farko ta cin kofin duniya na wasan a 2018.

Gasar za ta hada da wasannin karshe na cin kofin gasar maza ta hukumar kwallon tennis ta duniya wato Davis Cup da kuma gasar cin kofin wasan mata na hukumar wato Fed Cup.

Za a yi wasan ne a filin wasa na Palexpo convention centre tsawon shekara uku daga watan Nuwamba na 2018.

Shugaban hukumar tennis din ta duniya (ITF) David Haggerty, ya ce akwai bukatar samar da canji domin cin cikakkiyar moriyar wasannin biyu masu matukar tarihi.

Hukumar gudanarwar ITF ita ce ta zabi birnin Geneva a lokacin taronta a birnin Frankfurt na Jamus, daga cikin jerin birane shida, wadanda suka hada da Copenhagen (denmark) da Miami (amurka) da Istanbul (turkiyya) da Turin (italiya) da kuma Wuhan (china).

Za a bukaci babban taron hukumar na shekara-shekara da ya amince da sauye-sauyen da aka bullo da su a yayin taron da za a yi na bana a birnin Ho Chi Minh na Vietnam, a watan Agusta na 2017.

Argentina ce ke rike da kofin Davis (na gasar maza) yayin da Jamhuriyar Czech kuma ta ci kofin Fed Cup ( na gasar ta mata) a 2016.

Ina dan Afirka na farko da ya taka leda a gasar Firimiya?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Peter Ndlovu ya taka wa Coventry City leda ne a lokacin babu kudi sosai a gasar Firimiya

Peter Ndlovu ya fara buga kwallon kafa ne da buga kwallon roba a kan titunan birnin Bulawayo, birni na biyu mafi girma a Zimbabwe.

A cikin irin wannan wasanni na kan titi mai kura ne Peter ya sha kwallaye 11 a wasa daya, lamarin da ya dauki hankalin kociyan matasa na kunigiyar kwallon kafa ta Highlanders da ke Bulawayo.

Lokacin ne sanar kwallon kafa ta Peter Ndlovu ta soma kuma ya kama hanyarsa ta zama baki dan Afirka na farko da ya fara taka leda a gasar Firimiya ta Birataniya.

A wancan lokacin kungiyar Coventry City ta kai ziyara kasar Zimbabwe domin buga wani wasan gabannin kakar wasanni da tawagar kwallon kafa ta Zimbabwe da kuma kungiyar Highlanders. Ya buga wasanni biyu, kuma jami’an Coventry City sun yi sha’awar yadda ya yi wasan.

Ndlovu ya ce: “Zan iya tunawa bayan wasan kociyan Coventry City, John Sillett, ya ce ba zan bar yaron nan a nan ba, da haka na fara sana’ar kwallo.”

Ndlovu ya kara da cewa ya ji wani dadi na musamman na kasancewa dan Afirka na farko da zai fara buga wasa a gasar da za a iya cewa ta fi kowacce a duniya.

“A wancan lokacin akwai ‘yan kwallon Afirka da yawa amman kasancewa dan Afirka na farko mai taka leda a gasar Firimiya yasa na fita daban. Wannan babban abu ne. Na ji matukar dadi, na rasa abin fada domin babban abu ne,” in ji Ndlovu wanda ya bude hanya ga jerin ‘yan wasan Afirka wadanda suka biyo bayansa kamar su Didier Drogba da Samuel Eto da Michael Essien da ire-irensu.

Dan asalin Zimbabwen ya buga wasansa na farko ne a wasan da Coventry City ta fafata da Arsenal a kakar 1991/1992 kuma ya sha kwallon da ya baiwa kungiyarsa nasara.

“Shan kwallo a wasa na farko babban abu ne ga dan wasa. Wasa zai yi maka kyau, amman zai fi tasiri in ka sha kwallo. Na tuna wasa na na farko a Arsenal. Na shiga wasan ne a lokacin da aka yi canji kuma na sha kwallon da ya ba da nasara a wasan saboda haka abun farin ciki ne. ” In ji shi.

Ndlovu ya sha kwallo sau 43 a wasanni 176 da ya buga wa Coventry City a tsakanin 1991 da 1997.

Ya ce duk da cewa kwallonsa na farko yana da muhimmanci sosai, ya fifita kwallaye uku da ya sha a Anfield a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 1995, a matsayin wasansa mafi kyau. Wadannan kwallaye sun sa ya zama dan kwallon kungiya mai ziyara ta farko da ta fara shan Liverpool kwallaye uku a Anfield tun shekarar 1962. Coventry ta ci wasan da 3-2.

“Ina tuna abubuwa da dama game da shan Liverpool, kungiyar da na goyi baya a lokacin da ina yaro,” In ji Ndlovu wanda aka fi sani da sunan “Harsashin Bulawo” a harkar kwallon kafa.

Ndlovu ya shiga fagen tamaular Ingila a lokacin da ake samun matsalar wariyar launin fata tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa, amman ya ce shi bai fuskanci wani kalubale ba ta wannan fuskar.

“Babu kalubale masu yawa ta nan. Abun da ya dame ni shi ne mayar da hankali kan taka leda. Ban hadu da mutanen da suka nuna mini wariyar launin fata ba, amma akwai lokutan da masu goyon baya za su zage ka, amman ka san abun da ya kamata ka yi shi ne ka mayar da hankali a kan aikinka ka sha kwallaye sannan za su yi shiru,” In ji Ndlovu.

A yanzu haka yana aiki ne a matsayin kociyan kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sundowns, Zakarun Afirka masu tashe da ke birnin Pretoria, a kasar Afirka ta Kudu.

Ya ce yana amfani da dabarun da ya koya a lokacin da ya buga wa Coventry City kwallo a aikinsa na yanzu.

Ya ce dan wasan Arsenal, Lee Dickson, shi ne abokin hamayya mafi karfin hali da ya taba buga wasa da shi.

Da-na-sanin da yake yi kawai shi ne rashin buga wasa a lokacin da gasar Firimiya ke da kudi kamar yanzu.

Cikin murmushi Ndlovu ya ce “A lokacin da nake wasa ana kai mana sara sosai, amman da zai fi kyau da a yanzu nake taka leda saboda akwai kudi mai yawa.”

Gasar Kofin Duniya : Ingila ta bayar da cin hanci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Qatar aka ba wa damar gudanar da gasar kofin duniya ta 2022 a 2010, yayin da Rasha ta samu ta gasar 2018

Shirin da Ingila ta yi na wasan sada zumunta a kasar Thailand domin kasar ta Asiya ta mara mata baya a neman karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 wani salo ne na cin hanci, kamar yadda aka sheda wa masu bincike.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila Geoff Thompson shi ne ya bayyna hakan lokacin da ake yi masa tambayoyi yayin bincike a kan batun neman karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 da ta 2022.

A ranar Talata ne hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta fitar da cikakken rahoton binciken na shekara ta 2014.

Wannan ya biyo bayan wasu bayanai na rahoton ne da aka tsegunta wa jaridar Bild ta Jamus, wadanda ita kuma ta wallafa.

Tsohon mai bincike mai zaman kansa, kan ka’idojin Fifa, Michael Garcia shi ne ya rubuta rahoton mai shafi 422.

Ya ajiye aikin domin nuna kin amincewarsa da bayyana shafi 42 kawai na rahoton nasa da aka takaita.

Wanda takaitaccen rahoton ya wanke Rasha da Qatar, wadanda suka samu ikon gudanar da gasar ta kofin duniya ta 2018 da ta 2022 daga zargin rashawa.

Amma kuma ya tuhumi abubuwan da wasu manyan jami’an Fifa da kuma ‘yan kwamitocin neman karbar gasar na kasashe suka yi ciki har da ‘yan Ingila.

Rahoton ya bayar da misalin wata tattaunawa da babban jagoran kwamitin nema wa Ingila damar karbar bakuncin gasar ta 2018 Thompson a kan shirin tawagar wasan Ingila na zuwa Thailand domin samun kuri’ar kasar a zaben.

Ingila ta gabatar wa Thailnad wannan dama ce ta zuwa su yi wasan sada zumuntar kwana takwas kafin kada kuri’ar a shekara ta 2010 domin zabar kasar da za a ba wa damar gudanar da gasar 2018 da kuma ta 2022.

Bayan mako uku da gabatar da tayin sai Ingila ta janye daga shirin zuwa Thailand din, wanda a lokacin an riga an kada kuri’a, wadda ta tabbatar kasar ba ta mara wa Ingila baya ba domin samun damar.

Ya kamata maza su rika karawa da mata a tennis – John McEnroe


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

John McEnroe ya ce da Serena Williams ta biyu a duniya, a cikin maza take tennis da ta 700 za ta zama

Tsohon gwanin wasan tennis John McEnroeya bayar da shawarar a rika hada gasar da maza za su rika karawa da mata domin tabbatar da gaskiyar ikirarinsa cewa idan da Serena Williams a gasar maza take da za ta kasance ta 700 a cikin gwanayen a duniya.

McEnroe wanda ya dauki manyan kofunan tennis bakwai na duniya ya ce Williams ita ce babbar gwana a tsakanin mata amma idan da a cikin maza take to da labarin ya sha bamban.

Serena Williams mai shekara 35, wadda ta dauki manyan kofunan duniya na tennis guda 23 ta mayar wa Mcroe mai shekara 58 martani ta twitter, inda ta bukace shi da ya mutunta ta ya fita daga sha’aninta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Serena Williams ta bukaci McEnroe ya fita daga sha’aninta

Shi ma dan wasan da yake matsayi na 701 a tsakanin gwanayen tennis din a duniya, dan Rasha, Dmitry Tursunov, a ranar Talata shi ma ya ce yana ganin zai iya doke Ba’amurkiya Williams, wadda ake sa ran za ta haihu a lokacin kaka.

Tursunov mai shekara 34, wanda ya taba kaiwa har na 20 a duniya, ya ce ba ya jin McEnroe yana son ya raina tennis din mata ne, amma ya ce gaskiyar lamari ita ce gaba daya maza sun fi mata karfi.

Qatar ta yi tur da kin amincewa da tattaunawa da Saudiyya ta yi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ministan harkokin wajen Qatar ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka a Washington a ranar Talatar da ta gabata

Ministan harkokin wajen Qatar ya yi tur da kin amincewar da makwabtanta suka yi na a tattauna bukatun da suka mika wa kasarsa kafin su janye takunkumin rufe iyakokinsu na kasa da ruwa da kuma sama.

Sheikh Mohammed Al Thani ya ce matsayin da suka dauka “ya sabawa dokokin” dangantakar kasa da kasa.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce akwai yiwuwar Qatar ta fuskanci karin takunkumi daga abokan hamayyarta na kasashen Larabawa.

Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawan a Rasha, Omar Ghobash, ya shaida wa jaridar The Guardian cewa sabbin matakan za su hada da neman abokan cinikayyarsu su zabi wanda za su yi hulda da shi tsakanin su da Qatar.

Saudi Arabia da hadaddiyar daular larabawa da Bahrain da kuma Masar na zargin Qatar da tallafawa ta’addanci – zargin da ta musanta.

Kasashen sun mika wasu bukatu da suke son Qatar din ta yi, bukatun da ministan harkokin wajen Saudi Arabia ya ce “ba sa bukatar wata tattaunawa” a ranar Talatar da ta gabata.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Qatar za ta dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa duniya ta duniya a shekarar 2022

Takunkumin dai ya shafi Qatar, kasar da ke da arzikin iskar gas wadda ta dogara da shigo da abubuwan bukatu na rayuwa daga kasashen waje ga jama’a miliyan biyu da dubu dari bakwai.

A ranar juma’a ne kasashen Larabawan hudu suka mikawa Qatar bukatun 13 da suka hada da rufe gidan talabijin na Al Jazeera da rufe sansanin sojinta da ke Turkiyya da yanke hulda da kungiyar ‘yan uwa Musulmi da kuma rage karfin dangantakarta da kasar Iran.

Gungun 'yan Nigeria na hada baki da 'yan mafiya a Italiya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu matan ana yaudararsu da cewa za a sama musu aikin yi ne a Italiya, amma idan suka je sai a tilasta musu shiga karuwanci

‘Yan sanda a Italiya sun ce wani gungun masu aikata laifuka na ‘yan Najeriya da ke zaune a birnin Sicily, na hada baki da kungiyoyin mafiya wajen sanya mata karuwanci da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Wata jami’a a cibiyar da ke nazarin ayyukan da suka kauce wa tsarin doka, a jami’ar Oxford da ke Ingila, Charlotte Baarda ta shaida wa shirin turanci na BBC, Newsday cewa kawancen kungiyoyin mafiyar da na ‘yan Najeriya dadadden abu ne.

“A shekarun 1980 akwai matan Najeriya da dama da suka je Italiya saboda ana matukar bukatar masu aiki a cikin gida, sai dai daga bisani sun fahimci cewa anfi samun riba daga karuwanci kuma tun bayan nan ne matsalar karuwanci take ta karuwa.”

Inda ta kara da cewa gungun masu aikata laifukan kamar kungiyar Black axe wadda ta samo asali a jami’oin da ke kudancin Najeriya, na bai wa kungiyoyin ‘yan Mafiya na Italiya kudi domin a basu kariya a wuraren da suke aiki ko zama, amma a yanzu tasirin kungiyoyin ‘yan mafiyan ya ragu bayan an garkame da dama daga cikin jagororinsu.

“Hakan yasa ‘yan Najeriya ke iya kwace wurare ko yankunan da ake karuwanci ko safarar mutane cikin sauki ba tare da sun fuskanci turjiya ba, kuma su ne ke yanke hukunci a kan ko wa za’a bai wa damar shiga Italiya tare da ba da takardun izinin zama na bogi” In ji Charlotte.

Jami’ar ta yi karin haske a kan dalilan da yasa ‘yan sandan Sicily suka kasa daukar mataki a kan gungun masu aikata laifukan na ‘yan Najeriya.

“Yan sanda sun ce suna fuskantar matsala wajen samun bayanai ko kuma wadanda zasu iya tattara bayanan sirri da kuma masu tafinta, saboda yanki ne da kowa ya san kowa, mujami’a daya suke halarta saboda haka da wuya su samu hadin kai. Yayin da su kuma wadanda aka yi safararsu zuwa Italiyar ba zasu iya magana da ‘yan sanda ba, saboda suna ganin rayuwarsu ta dogara kacokan ne a kan alumma. “

Sai dai ta ce a kasashe irinsu Belguim da Spaniya suna da jamian tsaro na musaman a kan yammacin Afrika, wadanda kan ziyarci wuraren da ‘yan Najeriyar suke zaune, kuma su kan je har inda suke shan barasa domin su yi magana da mata ‘yan Najeriya masu karuwanci.

Inda ta kara da cewa ko da yake suna samun bayanai a kan abin da ke faruwa, amma kuma abu ne mai sarkakiya.

Wasu bayanai dai sun nuna cewa jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta yi kaurin suna wajen safarar mata zuwa Italiya domin karuwanci.

Najeriya ta kafa hukuma ta musamman da ke yaki da safarar mutane ta NAPTIP, wadda ke yunkurin dakile matsalar.

Sai dai hukumar ta ce karfin kungiyoyin da abin ya shafa na kawo mummunan tsaiko wajen kawo karshen matsalar safarar mutane da kuma sanya mata karuwanci a kasashen ketare, musamman a kasar ta Italiya.

Tarayyar Turai ta ci Google tarar dala 2.7bn


Hakkin mallakar hoto
Google

Image caption

Tallan da Google ke saka wa na kayansa na ture na sauran kamfanoni kasa

Hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai ta ci tarar kamfanin Google euro biliyan 2.42 (dala biliyan 2.7; fam biliyan 2.1) bayan da hukumar ta ce kamfanin ya ba kansa fifiko wajen tallata nasa kayan a saman shafukansa na samar da bayanai.

Wannan ita ce tara mafi girma da hukumar ta taba kakaba wa wani kamfanin da ake tuhuma da laifukan hana daidaiton cinikayya da wasu kamfanonin.

Hukuncin kuma ya umarci kamfanin na Google da ya daina halayen yi wa dokokin cinikayyar Tarayyar Turai karen tsaye cikin kwanaki 90, ko ya fuskanci karin matakai.

Kamfanin na Google na iya daukaka kara.

Amma idan Google ya kasa sauya halayyar tasa a cikin watanni uku, a na iya tilasta wa kamfanin da ya biya kashi 5 cikin dari na jimillar cinikin da uwar kamfanin na Google, watau Alphabet ke yi a dukkan fadin duniya.

Idan haka ta kasance, Google zai rika biyan dala miliyan 14 kenan a kowace rana.

“Abin da Google ya yi laifi ne a karkashin dokokin Turai,” in ji Margrethe Vestager wacce ita ce kwamishinar samar da daidaito na kasuwanci a tsakanin kamfanoni dake Tarayyar Turai.

“Kamfanin ya hana sauran kamfanoni damar yin gasa da kuma samar da sabbin dabarun kasuwanci, kana kamfanin ya hana Tarayyar Turai amfana da zabin da irin wannan gasa ke samarwa.”

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

KALLI: Margrethe Vestager na bayyana tasirin halayyar kamfanin Google da yadda ya shafi kasuwanci

A nashi bangaren, kamfanin Google ya ce ai kamfanonin Amazon da eBay sun fi kowa amfana, kuma ya ki amincewa da tuhumar da a ke yi masa.

“Idan ka shiga intanet domin sayen kaya, kana bukatar samun bayanai game da kayan cikin hanzari da sauki,” in ji wani kakakin kamfanin bayan da aka bayyana hukuncin.

“Ba mu amince da hukuncin da aka bayyana ba a yau. Za mu duba bayanan hukuncin, kana mu duba yiwuwar daukaka kara”.

Gagarumin cigaba

Google kan nuna kayan da suka fi alaka da hotunansu, tare da sunayen shagunan da ake sayar da kayan.

Hakkin mallakar hoto
Google

Image caption

Idan aka duba bayanan kayan sayarwa da wayar hannu, na Google kan ture na sauran kamfanoni kasa

Binciken shekara bakwai

Hukumar ta Tarayyar Turai ta shafe kusan shekara bakwai tana binciken sashen kasuwanci na Google.

An gudanar da binciken ne sabili da wasu koke-koke da hukumar ta samu daga kamfanin Microsoft da wasu kamfanonin.

Kamfanin na Microsoft bai ce uffan ba bayan da aka bayyana wannan hukuncin,

Amma daya daga cikin masu koken, kamfanin Foundem ya yi maraba da hukuncin.

Shugaban Foundem, Shivaun Raff ya ce “Hana Google yin wadannan ababen da kuma tarar euro biliyan 2.42 da aka ci kamfanin zai yi tasiri wajen dakile irin wannan halayyar a gaba.”

Dani Alves ya bar Juventus bayan kaka daya a Italiya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dani Alves ya koma Juventus daga Barcelona a shekarar 2016

Dani Alves da Manchester City take nema ya bar zakaran Serie A, Juventus bayan ya shafe kaka daya tak a Italiya.

Alves, mai shekara 34 kuma dan asalin Brazil ya tabbatar da barin Juventus din ne ta sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Ya ce: “A yau huldarmu ta wasa ta kare kuma ba zan manta da dukkan wadanda suka sanya Juve ta kasance babbar kungiya ta hanyar soyayya da kyawawan halayaen da suka nuna min ba.”

An alakanta City da sayen Alves, inda Juve ta ce za ta sallame shi daga kwantiraginsa.

Alves ya kara da cewar: “Zan so in mika godiyata ga dukkan magoya bayan Juventus, da abokan wasana wadanda suka karbe ni hannu bibbiyu yadda kwararru ke yi a madadin kungiya mai nasara.”

Wasa na karshen da ya buga wa Juventus shi ne kuma wasan karshe na gasar Zakarun Turai inda Real Madrid ta doke Juventus din 4-1 a Cardiff.

Alves ya buga wasanni 33 a yayin da kungiyar ta lashe gasa biyu na cikin gida a karo na uku cikin shekara uku.

Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela


Hakkin mallakar hoto
Instagram

Image caption

Dan sandan da ya kai harin ya bayyana kan shi da suna Oscar Perez a shafin sa na Instagram

Wani jirgi mai saukar ungulu ya jefa bam a ginin kotun kolin Venezuela, a wani mataki da shugaba Nicolas Maduro ya kira fa aikin ta’addanci.

‘Yan sanda sun ce wani jami’insu ne ya dauki jirgin helikofta, kana ya jefa gurneti ta sama kan kotun kolin kasar.

Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda jirgin ya tashi sama ya yi shawagi a sararin birnin Caracas, sannan ya saki gurneti.

An yi amanna da cewa jami’n dan sanda ya kwace jirgin ne, inda ya yi ta shawagi daga baya kuma sai aka ji karar fashewar gurnetin.

Babu dai wanda ya ji rauni ko ya rasa rai a harin ba.

Kasar dai na fama da rikice-rikicen siyasa da tattalin arziki, kusan kullum sai an yi boren kin jinin gwamnatin shugaba Nicolas Maduro tare da bukatar ya yi murabus.

Fiye da mutane 70 ne aka hallaka, a tashin hankalin da boren 1 ga watan Afirilu da ya wuce, kamar yadda ofishin babban mai shigar da kara ya bayyana.

Shugaba Maduro ya ce maharin da gurneti ya yi amfani, kuma ya sha alwashin jami’an tsaro za su kama masu hannu a kai harin.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Gwamnatin shugaba Maduro na fuskantar bore kusan kowacce rana

Shugaba Maduro ya shaida wa dandazon magoya bayan shi a wajen fadar gwamnatin kasar Miraflores ce wa ya bai wa jami’an tsaro umarnin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

”Nan ba da jimawa ba, za mu kama jami’in da ya tuka jirgin helikoftar, za mu kama duk wani mai hannu a harin ta’addancin da aka kai mana”, inji shugaba Maduro.

Jami’in dan sandan ya wallafa wani hoton bidiyo a shafin Instagram, ya kira kan shi da suna Oscar Perez, wasu mutane da fuskarsu ke rufe da kyalle dauke da makamai sun kewaye shi.

Ya yi kira ga al’umar kasar su yaki mulkin kama karya.

An ci zarafin mata Musulmi a Poland


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Yan matan Musulmi sun yi mamakin wannan wariya

‘Yan mata Musulmi ‘yan wata makarantar Jamus da suka kai ziyara wuraren da ake ajiye kayan tarihin tunawa da kisan kiyashi a gabashin Poland sun ce mazauna yankin sun nuna musu wariyar launin fata.

Matan, ‘yan makarantar birnin Berlin, sun shaida wa gidan rediyon Deutschlandfunk abubuwan da suka fuskanta lokacin ziyarar. Hudu daga cikinsu suna sanye da hijabai kuma sun ce an ci zarafinsu.

Wata daga cikinsu ta ce wani mutum ya tofa mata yawu a kan titin Lublin, yayin da ‘yan sanda ke tsaye suna kallo suna kuma murmushi ba tare da sun dauki mataki ba.

‘Yar uwarta kuma ta ce an kore ta daga wani kantin sayar da kaya saboda ta yi magana da harshen Fasha.

A lokacin, magana take yi da dan uwanta a wayar tarho.

Ta gaya wa gidan rediyon cewa, “Masu kantin sun zo wurin da nake suka ce ‘ki tafi ki bamu wuri domin kina damun mutane’. Don me suka yi min haka? Kawai saboda na yi magan da harsahen Fasha kuma ni ‘yar kasar waje ce.”

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Lublin ta fitar ranar Talata ta ce “matan ba su kai wani korafi ga jami’an ‘yan sandan Lublin ba”.

Cibiyar tunawa da kisan kiyashin Jamus ce dai ta dauki nauyin ziyarar da matan suka kai Poland.

Shugabanta Hans-Christian Jasch ya ce : “Na yi matukar girgiza da jin abin da ya faru da ‘yan matan da muke kula da su a lokacin ziyarar tasu – ita kanta ziyarar na cikin kwas din da muke koyarwa kan nuna wariyar launin fata.”

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

1943: ‘Yan nazi sun tsangwami Yahudawa

"An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba"


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Soji sun ce kisan da aka yi wa Fulani ya fi wanda Boko Haram ke yi

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar a matsayin kisan-kare-dangi.

Babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ya bayyana hakan, ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila.

Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a fadar Sarkin Mambila da ke jihar ta Taraba yayin wani taro da shugabannin al’ummomin yankin.

A cewarsa, “An yanka kananan yara ‘yan shekara biyu, an kashe mata masu ciki; abin da aka yi musu ya fi abin da ‘yan Boko Haram ke yi, domin ‘yan Boko Haram ba sa kashe kananan yara. Niyya aka yi ta yi musu kisan-kare-dangi”.

Birgediya Janar Ahanotu ya kara da cewa, “Binciken da na yi ya yi yadda ake matukar nuna kiyayya ga Fulani a nan, sannan kuma an yi musu barna sosai; yanzu babu wani dan Fulani a wannan yanki in ban da wadanda suka gudu domin tsira, da kuma wadanda ke zaune a cikin gari. An yi yunkurin share su daga doron kasa ne.”

Ya ce har a ranar Litinin jami’an soji sun gano gawarwakin Fulanin da aka kashe, yana mai cewa rundunarsa ta tura karin dakarunta domin tabbatar da zaman lafiya.

Daruruwan mutane ne ake fargabar sun mutu a tashin hankalin ya barke a makon jiya tsakanin Fulani da Mambilawa a karamar hukumar Sardauna.

Masu amfani da Facebook sun kai biliyan biyu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana sukar Facebook saboda gaza magance ta’addanci

Fiye da kashi daya cikin hudu na al’umar duniya na yin amfani da Facebook kowanne wata, a cewar shugaban shafin na sada zumunta.

Mark Zuckerberg ya wallafa a shafinsa cewa “Da safiyar nan masu amfani da Facebook suka kai mutum biliyan biyu”.

Facebook ya kai wannan matsayi ne shekara 13 bayan Mr Zuckerberg ya bude shafin lokacin yana Jami’ar Harvard.

Ya watsar da karatunsa na Jami’a bayan ya bude shafin na Facebook.

A watan Oktoban 2012 ne shafin na intanet ya sanar da cewa masu amfani da shi sun kai biliyan daya, abin da ke nufin masu amfani da dandalin sun ninka cikin kusan shekara biyar.

Ci gaban da shafin Facebook ke samu ya zarta tunanin masu sharhi wadanda suka yi hasashen cewa zai samu koma baya tun lokacin da shafin Snapchat da ke gogayya da shi ya karbe wasu daga cikin masu mu’amala da shi.

A farkon wannan shekarar ne Facebook ya yi gargadin cewa kundin da yake samu ta hanyar tallace-tallace za su ragu.

Amma duk da haka burin Mr Zuckerberg bai ragu ba.

Ya shaida wa jaridar USA Today cewa ba su zuzuta samun masu amfani da shafin biliyan biyu ba saboda “bamu hada kowa da kowa da shafin ba”.

“Abin da muke son yi shi ne kowa ya bude shafin Facebook,” in ji shi.

Salif Diao: Na so zama malamin makaranta ne


Image caption

Diao ya kafa gidauniyar renon yara ‘yan wasa a Senegal

Ya bar garinsu na Kédougou da ke kudancin kasar Senegal yayin da yake da shekara 13 don ya cimma burinsa na zama shahararren dan kwallon kafa.

Ya fara isa birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal wurin da a wasu lokuta yake kwana a wajen filin wasa kuma yake wanke kwanukan abincin sojoji don ya samu abincin da zai ci.

Hakan wani mataki ne wanda ya kai shi kulob din Liverpool, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya.

Bayan kimanin shekera 17 a matsayin shahararren dan wasa, Salif Diao, ya yi ritaya inda ya koma gida Senegal wurin da ya fara wasan.

Shaukin zama dan wasan kwallon kafa ya sa Diao ya yi watsi da karatunsa. Wanda hakan yake mai takaici yanzu.

“Abin babu sauki tun daga lokacin da nake da shekara 13 a duniya zuwa lokacin da na yi ritaya daga wasa,” in ji Diao yayin da yake zaune a ofis dinsa da ke birnin Dakar.

“Na so na yi karatu ne a makarantar Prytanée Militair wadda tana daga cikin manyan makarantu a Senegal.

Amma hakan bai yiwu ba, kodayake na samu na yi wasan kwallon kafa. Ba abu ba ne mai sauki mutum ya hada kwallon kafa da kuma karatu a lokaci guda.”

Diao bai samu ya yi karatu ba saboda yadda yake son zama shahararren dan wasan kwallon kafa.

Saboda yadda bai cimma burinsa na yin karatu, shi ya sa Diao ya kafa wata gidauniyar kimanin shekara uku da suka gabata.

Babban burin gidauniyar shi ne renon da yara ‘yan wasan kwallon kafa da suke da ilimi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salif Diao yana cikin tawagar da wakilci Senegal a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002

“Ina kaunar karatu saboda a yanzu ga inda muka samu kanmu, na yi ritaya, ban samu na yi karatu yanzu me zai yi ke nan,” in ji shi.

Duk da cewa kwallon kafa ya ba shi duk abin da yake bukata a rayuwa, ya ce hanya daya da zai taimaki al’ummarsa ita ce ta samar wa yara abin da za su yi idan suka shiga mawuyacin hali.

“Idan ba ka da ilimi rayuwa tana da wuya, akwai wuya kuma musamma ma a Afirka, cikin ‘yan wasa 1000 watakila guda daya ne zai zama shahararren dan wasa,” in ji shi.

Image caption

Diao ya ce yana da kyau a ba yara ‘yan wasa ilimi ta yadda za su ji dadin tafiyar da al’amura yayin da suka samu daukaka

Duniyar wasan kwallon kafa ciki take da ‘yan wasan da suka yi ritaya da bashin kudi a wuyansu.

Diao ya ce yana da kyau a ba yara ‘yan wasa ilimi ta yadda za su ji dadin tafiyar da al’amura yayin da suka samu daukaka.

Ya ce kafin a karbi yaro a gidauniyarsa ta horar da ‘yan wasa sai an tabbatar yana zuwa makaranta.

Ginauniyar tana samun gudummuwa daga tsofaffin kungiyoyin da ya yi wasa wato Liverpool da Stoke City.

Akwai cibiyoyin renon ‘yan wasa kwallon kafa da yawa a kasar Senegal, amma cibiyar Diao ta gindaya sharadin cewa sai yaro ya gabatar da takardun da ke nuna cewa yana zuwa makaranta kafin a karbe shi.

“Muna abin da muka kware a kansa ne wato kwallon kafa. Amma yana da kyau mu ba ilimi muhimmanci sosai kuma abin da muke yi ke nan a gidauniyar,” in ji Diao.

Idan aka dubi ‘yan wasan Senegal kamarsu Sadio Mane da Idrissa Gana Gaye da suka samu daukaka, da wuya yara ‘yan wasa masu taso su yarda cewa sanya karatu a gaba shi abin da ya dace.

“Suna kaunar wasan, suna so su yi suna kuma suna so su fita daga kangin talauci. Lokacin da nake yaro, so na yi na zama malamin makaranta ne amma yanzu so nake na zama mai horar da ‘yan wasa ko koci. Saboda yadda suke da ikon cewa yara su tafi makaranta. Abin da ya sa ke nan muka kafa Gidauniyar Salif Diao – ko Cibiyar Wasanni, inda muke cewa yara idan suna so su zo nan, to wajibi ne su je makaranta,” in ji Diao.

“Ya dace ‘yan wasa masu tasowa su fahimci muhimmancin ilimi.”

Yara suna son zama a gidauniyar. Suna sanya riguna wasa ne iri guda da na yara ‘yan wasa da ke cibiyoyin horar da kwallon kafa na kungiyar Liverpool da Stoke City a Ingila.

Tsohon takwaran Diao, Stephen Gerrard ne yake ba su kyautar takalman da suke amfani da su.

Wasu daga cikin takalman ma suna dauke da sa hannunsa wanda wannan ba karamin abu ba ne ga yara ‘yan wasa masu tasowa.

An ba tsohon ministan Nigeria kyautar duniya kan noma


Hakkin mallakar hoto
World Food Prize

Image caption

Dokta Adesina zai karbi dala 250,000 daga Gidauniyar Borlaug da ke Amurka

Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka Akinwumi Adesina ya samu kyauta kan muhimmiyar gudunmuwar da ya bayar wajen samar da abinci a duniya.

Dokta Adesina wanda shi ne tsohon ministan aikin gonar Najeriya, ya ce wadata miliyoyin manoma da iri da kuma takin zamani su ne muhimman abubuwan da za su kawo ci gaba ga aikin gona a nahiyar.

Ya kara da cewa kashi 98 cikin 100 na mutane miliyan 800 da ba sa samun wadataccen abinci suna Afirka ne.

A shekarar 1986 ne aka fara ba da kyautar abinci ta duniya don kara ingancin da kuma yawan abincin da ake nomawa a fadin duniya.

Dokta Adesina ya shaida wa BBC cewa yana alfahari da wannan kyautar da ya samu.

“A wajena, wannan kyautar ba ta kara daukaka sunana ba ce, tana nuni ne da bukatar bunkasa aikin gona a nahiyar Afirka,” in ji shi.

Har ila yau, ya ce babban matsalar aikin gona a Afirka bai wuce karancin amfani da ake girbewa ba.

Hakkin mallakar hoto
World Food Prize

Image caption

An fara ba da kyautar ne a shekarar 1986

“Daya daga cikin abin da na dukufa yi shi ne kara kaimin ayyukanmu,” in ji Adesina.

“Ka san ana iya samun lemun kwalba na Coca-Cola ko Pepsi a kusan kowane yankin karkara da ke nahiyar Afirka, to me sa ba a samun iri ko takin zamani haka?”

“Abin da ya sa hakan yake faruwa shi ne har yanzu tsoffin hanyoyin samar da iri muke amfani da su, wadanda suka dogara da gwamnati, kuma ba sa aiki yadda ya kamata.”

“Hakan ya sa nake ganin cewa ya fi dacewa a tallafawa mazauna yankunan karkara don su rika sayar da taki da iri da kansu daga shaguna.”

“Mun fara harkar dillancin kayan aikin gona kuma sun fara isa sassan Afirka da dama. Wannan tsarin na kawo irin da manoma suke bukata kusa da su kuma yana karfafa kasuwanci a karkara.”

Dokta Norman E Borlaug wanda ya taba lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya, shi ne ya kirkiro kyautar aikin noman a shekarar 1986.

Na'urar ATM ta cika shekara 50 a duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Na’urar ATM ta kawo sauyi a cinikayya a duniya

Shekaru 50 ke nan da fara amfani da na’urar fitar da kudi daga banki wato ATM Machine a duniya.

A ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 1967 ne wani wani banki a birnin Landan ne ya fara amfani da na’urar.

An samar da na’urar ne domin saukakawa mutane al’muransu musamman ta fuskar cire kudi idan bukatar gaggawa ta taso.

Ana dai amfani da na’urar ne wajen cire kudi, da sayen katin waya da biyan kudin makarantar yara ko biyan wani abu daban.

Hakazalika ana amfani da ATM din wajen tura kudi zuwa kowane bangare na duniya.

Kasar Koriya ta Kudu ita ce kasar da ta fi kasashen duniya yawan wannan na’urar inda ta ke da guda dubu 278, sai Australia da ta bi mata, sannan Japan.

A sahun kasashen nahiyar Afirka kuwa, Afirka ta Kudu ita ta fi sauran kasashen nahiyar Afirka yawanta.

Najeriya ma na daga cikin kasashen Afirkan da suke da yawan ATM.

Kiyasi ya nuna cewa, akwai na’urar guda miliyan uku a duniya.

Sharhi: Aisha Shariff Baffa

Na’urar tana da alfanu da kuma kalubale.

Daga cikin alfanun akwai samun kudi cikin sauki ba tare da ba ta lokaci ba; kuma ba sai mutum ya je banki ba.

Kalubalen kuwa shi ne, a wasu lokuta wannan na’ura na ba ta wa mutane rai ko lokaci, saboda a kan samu dogayen layin jama’a masu jiran su ciri kudi.

Wani lokacin kuma, zai nuna an kwashe maka kudi a asusun ajiyarka idan ka yi amfani da ita, amma ba tare da ya biya ka kudinka ba.

Ko kuma a wasu lokutan ya kan rikewa mutane katinsu banki, sai mutum ya sha wuya kafin katinsa ya dawo.

Kun san hazikin dan sandan da ke farautar masu laifi a Nigeria?


Image caption

An sa kyautar naira miliyan 30 ga duk wanda ya ba da bayanai da za su taimaka wajen kama Evans

Jami’in dan-sandan da ya jagoranci cafke madugun da ake zargi da garkuwa da jama’a da dama domin neman kudin fansa a Najeriya, ACP Abba Kyari, ya shaida wa BBC irin jan aikin da suka yi wajen cafke madugun.

A farkon wannan watan ne jami’an ‘yan sanda a Legas suka yi nasarar kama Mista Chukwudi Onuwamadike wanda aka fi sani da sunan Evans bayan sun kwashe shekara bakwai suna farautarsa.

“Ya gagari dukannin jami’an tsaron Najeriya a tsawon kusan kimanin shekara bakwai,” in ji Abba Kyari a wata hira da BBC.

Satar mutane ‘na kara kamari a Nigeria’

An kama masu garkuwa da mutane a Kaduna

An sace tsohon ministan Najeriya, Amb Bagudu Hirse

Har ila yau, Kyari ya ce Evans ya kwashe fiye da shekara 20 yana aikata laifuka a kasar.

“Ya kware sosai. Yana da layukan waya fiye da guda 100,” in ji Kyari.

Sai dai har yanzu ba a gurfanar da Evans gaban kuliya ba domin jin ko zai amsa ko musanta laifukan da ake tuhumarsa.

Don karanta cikakken labarin sai ku kasance da shafinmu na bbchausa.com da shafunkanmu na Facebook da Twitter da kuma Instagram a ranar Juma’a.

Hakazalika ga masu sauraron rediyo za su iya jin cikakkiyar hira da Abba Kyari a ranar Asabar a shirinmu na Gane Mini Hanya a shirinmu na safe.

An fara kewaye Jami'ar Maiduguri da ramuka don kariya daga Boko Haram


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shettima ya ce za a haka ramummukan ne domin dakile duk wani yunkuri kai harin da za iya fuskanta a jami’ar nan gaba.

Hukumomi a Najeriya sun fara aikin zagaye Jami’ar Maiduguri da ramuka don kare makarantar daga hare-haren kungiyar Boko Haram.

Sanarwar fara aikin wanda zai kai nisan kilomita 27 kuma zai ci naira miliyan 50 ta zo ne kwana guda bayan wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari jami’ar, inda suka kashe kansu da kuma wata ma’aikaciya.

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya sanar da aikin fara gina ramummukan, yayin da ya kai ziyara jami’ar don duba ta’adin da maharan suka yi.

Gwamnan ya ce za a haka ramummukan ne domin dakile duk wani yunkuri kai harin da za iya fuskanta a jami’ar nan gaba.

Sojoji sun dakile harin kunar-bakin-wake a Borno

‘Akwai ‘yan Boko Haram a shugabannin Borno’

Borno na bukatar agajin gaggawa – MSF

Sai dai bai bayyana taswon lokacin da za a kammala aikin ba.

Har ila yau, Shugaban Jami’ar Aliyu Shugaba ya ce sun gabatar da aikin ginin wata doguwar katanga wadda za ta kewaye jami’ar a wani mataki na kara kare jami’ar daga hare-hare.

Jami’ar Maiduguri dai ta zama wani wuri da ke yawan fuskantar hare-haren ‘yan Boko Haram a ‘yan watannin nan.

Shin, ina Nigeria ta dosa?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana ci gaba da tabka muhawara a kan makomar kasar ta fuskar mulki da zamantakewa.

Yayin da wasu shugabannin al`umma da `yan siyasa ke bukatar a sauya fasalin zaman tarayyar da ake yi, saboda a ganin su ana tauye hakkin wasu bangarorin kasar, wasu kuma maganar ballewa suke yi.

A karon farko dai su ma al`umomin bangaren arewacin Najeriyar, wadanda ke kukan cewa ana musu kallon cima-zaune sun fara daga-murya suna cewa ya zama wajibi a sauya tsarin zaman da ake yi a kasar, idan ba haka ba, to kowa ya kama gabansa.

Shin, ina Najeriyar ta dosa?

Batun sauya fasalin mulki da zama irin na tarayya a Najeriya dadadden al`amari ne, wanda masana ke cewa an fara maganarsa tun bayan hadi irin na baubawan-burmi da aka yi wa larduna uku na Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa, wato da lardin arewa da na kudu da kuma yammacin kasar sama da shekaru dari da suka wuce.

Haka dai aka yi ta tafiya ana dago batun daga lokaci zuwa lokaci, lamarin da ya yi sa wasu gwamnatoci, da suka hada da na soji da kuma na siyasa suka shirya wasu taruka da nufin tattaunawa a kan makomar kasa don samun mafita.

Rashin aiki ya karu a Nigeria

Nigeria: An yi gargadi kan saka hijabi

‘Yan Nigeria na fama da yunwa – Saraki

Sai dai a dan tsakanin nan, an sake zafafa kiraye-kirayen sauya fasalin zama da mulkin Najeriyar.

Kuma sabanin yadda aka saba jin wannan da`awa kan fito daga bakunan al`momin kudancin Najeriya, yanzu hatta wasu daga cikin mnyan `yan siyasa a arewacin Najeriya, irin su tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun fara bin sahu:

“Najeriya ba ta tafiya yadda ya kamata. Yadda aka fasalta kasar da tsarin mulki suna daga cikin dalilan da suka haddasa haka. Musamman ma tun shekarun 1960,” in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ya ci gaba da cewa “gwamnatin tarayya ta girman sosai. Kuma ta tara iko mai yawa idan aka kwatanta da gwamnatocin jihohi. Akwai bukatar yin gyara ga wannan lamarin.”

Za ku iya sauraron rahoton musamman kan wannnan batun (sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don ku saurara)

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ina aka dosa game da batun sake fasalin Najeriya?

Bertrand Traore ya koma Lyon a kan fam 8.8m


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Traore ya yi kakar bara ne a kulob din Ajax a matsayin aro

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Bertrand Traore, ya koma kulob din Lyon a kan fam miliyan takwas da dubu 800.

Traore, mai shekara 21, wanda dan asalin kasar Burkina Faso ne ya yi kakar bara ne a kulob din Ajax a matsayin aro.

Ya koma Chelsea ne a shekarar 2014 kuma ya yi wasa sau 16, inda ya zura kwallo a raga sau hudu.

Ajax ya buga wasa sau 13 ciki har da wasan karshe na Gasar Europa da Manchester United ta doke su.

Traore ya amince da kwantaragin shekara biyar ne a Lyon.

Qatar: Wani Sanata zai hana Amurka sayar wa Saudiyya makamai


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Bob Corker ya ce matakan da kasashen yankin Gulf ke dauka babu inda zai kai su face janyo tashin hankali

Fitaccen dan siyasar nan na Amurka na jam’iyyar Republican Bob Corker ya ce zai dakatar da sayar wa kasashen yankin Gulf makamai, har sai sun magance takaddamar da ke tsakanin su.

Shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje a majalisar dokokin Amurka, ya yi gargadin cewa ana yi wa yaki da ta’addanci na kungiyar IS kafar ungulu.

Makwanni uku kenan da kasashen Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain da kuma Masar suka yanke duk wata alaka da kasar Qatar, ciki har da rufe sararin samaniya da iyakokinsu.

Kasashen sun zargi Qatar da taimakawa ‘yan ta’adda, da alaka da kasar Iran, zargin da ta musanta.

A ranar Juma’a ne kuma kasashen suka sanya mata sharudda 13 da suke son Qatar ta cika kafin su ci gaba da mu’amala da ita, ciki har da rufe gidan talabijin na Al-Jazeera da yanke mu’amala da kungiyar ‘yan uwa musulmi, da takaita alakar diflomasiyya da Iran.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Jaragen Qatar da ke zuwa wasu kasashen yankin larabawa sun gamu da cikas sakamakon takaddamar da ta taso

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin Qatar, ya sanar da cewa matakin da wasu kasashen larabawa suka dauka ba komai ba ne face yin katsa landan kan harkokin kasar, kuma iyakokin da suka rufe sun sabawa dokokin kasa da kasa.

Rufe iyakokin dai babbar barazana ce ga attajirar kasar da ta shahara wajen samar da mai da iskar gas, wadda ta kuma dogara da kasashe makofta ta fuskar kayan da ake amfani da su ciki har da kayan abinci.

Idan hakan ta ci gaba da kasancewa, Qatar mai al’uma kusan miliyan uku, za ta dandana kudarta.

A bangare guda kuma kasashen Morocco da Iran sun aike da jiragen dakon kaya makare da kayan abinci da na bukatun yau da kullum zuwa Qatar, duk da cewa Morocco ta ce kayan na agaji ne kawai ba da wata manufa sukai hakan ba.

Amurka ta gargadi Syria kan hari da sinadari mai guba


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sinadari mai guba ya kashe fiye da mutum 80 a lardin Idlib a watan Afrilu

Amurka ta ce ta gano wani shiri da gwamnatin Syria ke yi na kai hari da sinadari mai guba kuma ta gargade ta kan hakan.

Fadar White House ta ce shirin da Syriar ke yi ya yi kama da wanda ta yi gabanin harin da ta kai da sinadari mai guba a watan Afrilu.

Mutane da dama ne suka mutu a wancan harin, lamarin da ya sa shugaban Amurka Donald Trump ya yi gaggawar bayar da umarni a kai hari kan sansanin sojin saman Syria.

Amurka ta yi gargadin cewa Shugaba Bashar al-Assad zai “yi matukar da-na-sani” idan kasarsa ta sake kai hari irin wancan.

Sanarwar da fadar ta fitar ta ce “harin sinadari mai guba da gwamnatin Assad za ta sake kai wa” zai iya haddasa kashe dubban farar-hula.

“Kamar yadda muka fada a baya, Amurka ta shiga Syria ne domin kawar da kungiyar IS da ke Iraqi da Syria. Idan Mr Assad ya sake yin amfani da makami mai guba ya kashe dubban mutane za mu kai masa farmakin soja, ” in ji sanarwar.

Shugaba Assad ya musanta cewa dakarun kasarsa ne suka kai wancan harin a garin Khan Sheikhoun da ke lardin Idlib.

Farar-hula da dama, ciki har da yara da yawa ne suka mutu.

Jiragen ruwan Amurka da ke jibge a kogin Meditareniyan sun mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami samfurin Tomahawk guda 59 a kan sansanin sojin saman Syria na Shayrat wanda ke yammacin birnin Homs, inda aka ce a can ne ake ajiye makamai masu guba.

'Yan ci-rani 52 sun mutu a saharar Jamhuriyar Nijar


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tafiya ta Sahara na da matukar hatsari

An gano gawar ‘yan ci-rani 52 wadanda suka mutu a tsakiyar saharar Jamhuriyar Nijar, kusa da Séguédine.

Rukunin ‘yan ci-rani 75 ke tafiya a cikin mota uku amma masu safarar mutane suka gudu suka bar su saboda tsoron haduwa da jami’an tsaro.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa an binne ‘yan ci-rani da dama, kuma na kai 23 daga wadanda suka tsira cikin gari, ko da yake daga bisani daya daga cikinsu ya mutu.

‘Yan ci-rani daga Afirka kan bi ta sahara zuwa Turai bayan sun wuce Libya da Bahar Rum.

Sai dai wannan tafiya na da matukar hatsari, domin kuwa akan makare su ne a cikin motocin a-kori-kura sannan kuma yawancinsu ba su da wani isasshen abinci.

Mako biyu da suka wuce, dakarun Jamhuriyar Nijar sun ceto ‘yan ci-rani 92 wadanda ke daf da mutuwa a Sahara.

An yi watsi da mutanen ne, wadanda suka hada da mata da kananan yara, ba tare da abinci da ruwan sha ba.

Kotu ta amince Trump ya hana Musulmi shiga Amurka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutane sun yi ta zanga-zanga lokacin da aka hana Musulmi zuwa Amurka a watan Janairu

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke wanda ya ba shi damar hana Musulmi daga wasu kasashe shiga kasar, yana mai cewa hakan “wata nasara ce ga tsaron kasa”.

Kotun kolin ta kuma amince da wani bangare na bukatar fadar White House ta hana ‘yan gudun hijira shiga kasar.

Alkalan kotun sun ce a watan Oktoba ne za su yanke hukunci na karshe kan ko za a bai wa shugaban kasar damar hana Musulmin shiga Amurka kwata-kwata ko kuma za a yi watsi da bukatar tasa.

Mr Trump ya bukaci hana Musulmi kasashe shida shiga Amurka na kwana 90 nan take da kuma hana ‘yan gudun hijira shiga kasar na kwana 120.

Shugaban na Amurka ya yi marhabin da hukuncin kotun na hana masu kai ziyara kasar daga kasashen Iran, Libya, Somalia, Sudan, Syria da Yemen, wadanda ya bayyana a matsayin kasashen “da ke da kyankashe ‘yan ta’adda”.

“A matsayi na na shugaban kasa, ba zan bari mutanen da za su yi mana illa su shigo kasar nan ba,” in ji shi.

Tuni dama Mr Trump ya ce dokar za ta soma aiki cikin kwana uku bayan amincewar kotun.

Me kotun ta ce?

Abin da hukuncin kotun kolin na ranar Litinin ke nufi shi ne: “A aikace, hakan na nufin [ikon shugaban kasar] ba zai hau kan ‘yan kasashen waje wadanda ke da kwakkwaran dalili na wata dangantaka da mutum ko kungiya da ke zaune a Amurka ba.

“Dukkan ‘yan kasashen waje na fuskantar yiwuwar gamuwa da ikon da shugaban kasar ke da shi.”

Hukuncin ya amince a hana dukkan ‘yan gudun hijira shiga Amurka tsawon kwana 120, don haka za a bai wa gwamnati damar hana masu ikirarin gudun hijira wadanda ba su da wani dan uwa ko kungiya da ke zaune kasar damar shiga kasa.


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wata ‘yar kasar Yemen rungume da mahaifiyarta a filin jirgin saman Virginia a watan Fabrairu bayan kotu ta dakatar da Shugaba Trump daga hana Musulmi shiga kasar

El Hadji Diouf: Ni ba mutumin banza ba ne


Image caption

El Hadji Diouf yana zaune yanzu a kasar Senegal

El Hadji Diouf wani gwarzo ne a kasar Senegal. Duk wurin da ya taka kafarsa jama’a magoya bayansa yara da manyan ne suke kewaye shi. ‘Yan kasar ba sa mantawa da muhimmiyar rawar da ya taka a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002, wanda kasashen Japan da Koriya ta Kudu suka karbi bakunci.

Amma a kasar Ingila, ana tunawa da shi da kan yadda ya rika jawo ce-ce-ku-ce fiye da gogewarsa a wasa.

Tsohon dan wasan ya yi wasa kungiyoyi da dama ciki har da Liverpool da Blackburn Rovers da Bolton Wanderers da kuma Rangers ta yankin Scotland.

Diouf yana da saurin fushi, yana tasamma abokan wasansa da jami’an wasa.

Sai dai yanzu da ya yi ritaya, yana ba da labarin abin da ya faru.

Bana daukar kaddara

“Zaki nake, bana daukar kaddara kuma babu wata matsala idan mutum ya kasance haka,” in ji Diouf ya magana game da halayyarsa lokacin da yake wasa.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

El Hadji Diouf: I’m fit, sexy and helping Senegal

“Ina da dabi’u masu kyau kuma ana so mutane su kaunace ni.”

Diouf wanda ya koma babban birnin Senegal, Dakar, ya ce mutane ba sa fahimtarsa lokacin da yake wasa a Ingila.

Ya ce: “Ni ba mutum ne mai sauki ba. Yana da tsauki a yi maganar El- Hadji Diouf kuma ina barin mutum ya fadi albarkacin bakinsa, amma ni na san cewa ni mutumin kirki ne. Iyalina ya san haka, jama’a sun san haka, nahiyata ta san cewa ni mutumin kirki ne, hakan shi ne abin da ya fi komai. Sauran babu abin da ya sha mini kai.”

Duk da yadda ya rika kare kansa, Diouf ya ce ya yi wasu dabi’u da ba su dace ba.

Da aka tambaye shi me ya sa, misali, yadda yake tofa wa abokan wasansa yahu, ya ce: “Wata kila suna fada mini wani abu ne da bana kaunar ji. Na yi haka, na biya kuma yanzu na gama.”

‘Gerrard bai taba yi wa kasarsa komai ba

Diouf ba ya jituwa da wasu daga cikin takwarorinsa a Liverpool kamarsu Jamie Carragher da kuma Steven Gerrard.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Steven Gerrard da Diouf sun yi wa kungiyar Liverpool wasa tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004

Ko yanzu, Diouf da Gerrard sun ci gaba da takaddama da juya ta kafafen yada labarai. Mene ne asalin matsalar?

“Ba ni da wata mtsala da shi,” in ji Diouf. “

“Gerrad yana da tasiri sosai kuma ni ma ina da tasiri sosai. ‘Stevie G’ dan wasa ne mai kyau. Mutane suna kaunarsa sosai a Liverpool amma bai taba yi wa kasarsa komai ba. Ni ne Mista El Hadji Diouf, Mista Senegal amma shi shi ne Mista Liverpool kuma Senegal tafi Liverpool kuma ya kamata ya san haka.”

Diouf yana aiki ne a Senegal a matsayin jakada. Shi ne yake bai wa Shugaba Macky Sall shawara kan wasanni kuma yana tafiyar da wani kamfanin jaridar wasanni a birnin Dakar – kuma gungun mutane suna kewaye shi duk lokacin da ya je wurin motsa jiki.

“Rayuwata ta wasanni ce amma gwamnati ba za ta iya komai ba ita kadai, tana bukatar taimako daga mutane irina,” in ji Diouf.

“Shugaban kasa ya yi amanna da ni kuma wannan ne ya sa da na yi ritaya daga wasa sai ya kirani ya ce yana so na taimaka saboda yaran da ke tasowa sun yi amanna da ni. Ni wani babban misali ne a gare su.”

Hakkin mallakar hoto
El Hadji Diouf

Image caption

Diouf ne mashawarcin Shugaba Macky Sall kan wasanni

Da aka tambaye shi ko yana da burin shiga saiyasa, Diouf ya ce ya mayar da hankalinsa wajen ganin ya bunkasa kasarsa – amma ba zai kore yiwuwar shiga siyasa a nan gaba.

Ya ce: “Ina da sha’awa saboda sai mun sauya al’amura. Mutane kamata za su iya sauya al’amura.”

“Muna da kasar da muke so mu gina da kuma nahiya, to me zai hana mutum shiga harkkokin siyasa a gobe?”

Mun sanya Senegal a sahun kasashen duniya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002 ne ya kara fito daga Diouf (wanda yake tsakiya)

Sau biyu yana lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Afirka, Diouf ya cikin tawagar kasar Senegal da ta kai wasan kwata final a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002, a cikin kasashen da suka doke har da kasar Faransa.

Ya bayyana lokacin da kololuwar nasarar da ya samu a matsayinsa na dan wasa – yana kwatanta rawar da ya taka da wadda Diego Maradona ya taka yayin da Argentina ta lashe Kofin Duniya.

“Mun sanya Senegal a sahun kasashen duniya,” in ji. “Gabanin wasan Kofin Duniyan babu wanda ya san da kasar Senegal, amma bayan wasan Kofin Duniya kowa yana ya san inda take.”

“Abin da Maradona ya yi wa kasarsa, ni ma shi ne abin da na yi wa Senegal. Ina daya daga cikin manyan ‘yan wasa a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002.”

“Faransa ce ta yi mana mulkin mallaka. Gabili su ne suke tafiyar al’amura a Senegal saboda doke su da muka a gasar ba karamin abu ba ne.”

“Kafin wasan sun ce ba za su sanya manyan ‘yan wasansu ba saboda galibin ‘yan wasan sun yi wasa a lig din Faransa.”

“A lokacin ni ina Lens, Salif Diao yana Sedan, Khalilou Fadiga yana Auxere, galibin ‘yan wasan suna wasa ne a Faransa amma mun sha fadin cewa: ‘A bi a hankali kafin a kashe zaki.'”

Diouf ya ce yana so ya ci gaba da taimakawa wajen bunkasa kwallon kafa a nahiyar Afirka, amma ya ce akwai bukatar sauya tsare-tsaren da ake da su yanzu.

“Hukumar Fifa ta sauya kuma lokaci ya yi da Hukumar Kwallon Kafar nahiyar Afirka za ta sauya,” in ji shi.

'Muryar Buhari ta ba ni tsoro'


Hakkin mallakar hoto
Whatapp

Image caption

Dokta Kabiru Danladi Lawanti na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya

Wasu masu sharhi a Najeriya suna fargabar cewa rashin lafiyan Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya tabarbare bayan da ya aike musu da sakon saukin muryarsa ranar Asabar.

Jama’a sun rika bayyana ra’ayoyinsu a kafofin sada zumunta a kasar, inda wasu suke cewa “muryarsa tana nuna cewa rashin lafiyarsa ya yi tsanani.”

Yayin wasu kuma suke cewa muryarsa ba ta sauya ba daga yadda suka santa ranar da zai tafi jinya Birtaniya.

Dokta Kabiru Danladi Lawanti na Fannin Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Ahamdu Bello ta Zariya, ya ce halin rashin lafiyar da shugaba ya yi tsanani.

“Duk wanda ya san Shugaba Buhari kuma ya saurari muryar da aka sanya ranar Asabar to wajibi ne ya tsorata. Za ka ji muryar tana shakewa kamar wanda ya kamu da mura.” in ji Dokta Lawanti

Ya ci gaba da cewa: ‘Idan ka saurari muryar da kyau za ka ji babu kuzarin da aka sa ji idan yana magana.”

Aisha Buhari ta tafi London ganin mijinta

Kiran Buhari ya yi murabus ya janyo ɓaraka

‘Ku daina yarda da jita-jitar mutuwar Buhari’

Ko lokaci ya yi da Buhari zai yar da kwallon mangoro?

Har ila yau, malamain jami’ar ya yi tsokaci game da kiraye-kirayen da wasu suke cewa shugaban ya yi murabus.

“Abu ne mai tsarkakiya gaskiya. Abu ne na doka da kuma siyasa, amma idan ya kasance bai iya tafiyar da mulki to abu mafi alheri a gareshi shi ne ya yi murabus,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Yanzu ka ga ya yi kwana 40. Ni a wana ra’ayin idan dai zai yi wata uku a wannan hali – babu abin da ya sauya. To ni ma ina da ra’ayin gara kawai ya yi murabus. Don lafiyarsa ta fi komai.”

Chelsea na daf da sayen Bakayoko daga Monaco


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bakayoko ya koma Monaco ne a shekarar 2014

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana daf da sayen dan wasan tsakiyar kulob din Monaco Tiemoue Bakayoko.

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce dan wasan mai shekara 22 zai taka muhimmiyar rawa a kulob din Chelsea.

Managar sayen dan wasan ta yi nisa wanda zai zama dan wasa na farko da zakarun firimiyar za su saya a kakar bana.

Bakayoko yana cikin ‘yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa yayin da kulob din Monaco ya kai wasan kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai ta bana.

Ya koma Monaco ne daga Rennes a shekarar 2014 kuma ya fara buga wa tawagar Faransa wasa ne a wani wasan sada zumunta da Spain ta doke su a watan Maris.

Trump ya ki shiryawa Musulmi liyafar sallah


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Akwai rahotannin da ke cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson (daga hagu) shi ne ya ki amincewa da bukatar shirya liyafar

Shugaban Amurka Donald Trump ya ki yin liyafar sallah a fadar White House kamar yadda sauran shugabannin Amurka da suka gabace shi suka saba yi.

Bana shekara 20 ke nan da Shugaban Amurka Bill Clinton ya fara shirya Musulmi liyafar sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.

Bikin sallahar idi shi ne yake kawo karshen watan azumin Ramadan.

Tun daga zamanin Clinton ne aka ci gaba da raya al’adar shiryawa al’ummar Musulmin Amurka liyafa har zuwa bara zamanin Shugaba Barack Obama.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ki aminci a shirya liyafar ba.

A watan Mayu kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Mista Tillerson ya ki amincewa da wasu bukatocin ma’aikatar harkokin wajen Amurka kan al’amuran da suka shafi addini.

Ana sukar Mista Trump saboda yadda yake yawan bayyyana kalaman kin jinin Musulmi ciki har bukatarsa ta hana wasu Musulmi shiga kasar.

Kodayake Shugaba Trump ya aike da sakon sallah, inda ya ce: “Amadadin Amurkawa da mai dakina Melania da kuma ni kaina ina taya Musulmi murnar bikin Eid al-Fitr.

Sai dai shugaban bai yi karin haske ba game da abin da ya sa fadarsa ba za ta shirya liyafar sallah ba ga Musulmin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Duk shugabanin da suka biyo bayan Clinton sun rika shirya Musulmi liyafar ciki da Barack Obama a bara

Shugaban Amurka Thomas Jefferson ne a shekarar 1805 ya fara shiryawa Musulmi liyafar buda baki a fadar White House lokacin azumin Ramadan.

A shekarar 1996 ne sai uwargidan Shugaban Amurka Bill Clinton wato Hillary ta fara raya al’adar.

An rika gudanar da liyafar ne kowace shekara daga shekarar 1999, inda shugabannin al’ummomin Musulmi a Amurka da masu aikin diflomaiyya da kuma ‘yan majalisa suku halarta.

'Yan sanda sun hana taron 'yan luwaɗi a Turkiyya


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Shekara uku kenan hukumomin kasar Turkiyya na hana gudanar da taron

‘Yan sanda a kasar Turkiyya sun hana gudanar da wani haramtaccen taro da masu auren jinsi daya suka shirya.

Masu shirya taron a duk shekara, sun sha alwashin ci gaba da fafutuka da matsa lamba har sai sun cimma nasara duk kuwa da cewa hukumomin kasar ne suka haramta shi, wadanda ke fuskantar matsin lamba daga masu ra’ayin mazan jiya.

A kasar Turkiyya, an haram ta luwadai da madigo ba kamar wasu kasashen musulmi ba, amma duk da haka masu wannan ra’ayi na ci gaba da matsa lambar halatta shi.

Shugaba Tayyip Erdogan, wanda jam’iyyar sa ta ‘yan mazan jiya kuma masu ra’ayin addinin musulunci ce, ya ki amincewa da bukatar tasu, da kin amincewa a sanya harkokin addinin gargajiya cikin kundin tsarin mulkin kasar, sai dai ya bai wa ‘yan kasar damar gudanar da addinan da suke yi cikin bainar jama’a ba tare da tsangwama ba.

Sai dai ana zargin shi da karawa kan shi karfin iko cikin shekarun da suka wuce.

Har an saba da hakan

Wannan shi ne karo na uku cikin shekara uku ana haramtawa ‘yan luwadi gudanar da babban taronsu a Turkiyya.

Wakilin BBC Mark Lowen da ke birnin Santambul ya ce irin jami’an ‘yan sanda da aka jibge a titin yankin Istiklat ya haramtawa masu gangamin fara taron anan wanda daman nan aka shirya fara shi.

Ya kara da cewa duk wanda ya daga tuta launin bakan gizo, tare da kokarin wucewa ta wurin ‘yan sanda na hana shi.

Haka kuma ‘yan sanda dauke da makamai, da feshin ruwan da ake yi wa masu macin shi ya tilasta musu ja da baya.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Masu tattakin sun ce su na mutunta kundin tsarin mulkin kasar

Jaridar Hurriyet ta rawaito akalla mutane 10 ne ake tsare da su.

Yayin da jaridar De Telegraaf ta kasar Hollan, ta wallafa a shafin ta na Twitter cikin wadanda ake tsare da su har da mai daukar hoton ta Bram Janssen.

Tun da fari a jiya Lahadi, masu shirya macin goyon bayan ‘yan Luwadi suka fitar da wata sanarwa mai taken: “Mu ba matsorata ba ne, ba za mu sauya ba, ba kuma inda za mu je, ku ne matsorata, za ku sauya, za kuma ku saba da hakan. Mun sake fitowa don nuna muku za mu yi fito-na-fito da duk wanda ke son danne mana hakkinmu.”


An sake kai hari a Jami'ar Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
NEMA

Image caption

An sha kai hare-hare a Jami’ar Maiduguri

‘Yan kunar bakin wake sun tashi bama-bama da ke jikinsu a Jami’ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu da ma wasu ma’aikatan Jami’ar.

Kakakin Jami’ar Farfesa Danjuma Gambo ya shaida wa BBC cewa maharan sun tashi bama- baman ne a wurare uku da ke Jami’ar.

“Mace ta farko ta tunkari jami’an tsaron da ke aiki a jami’ar ne inda ta tayar da bam din da ke jikinta. Daya daga cikin jami’an tsaron ta mutu sannan an kai uku asibiti. Ta biyu kuma ta shigo ta gabashin Jami’ar amma jami’an tsaro suka gan ta kuma nan take suka harbe ta. Bam na uku kuma ya tashi ne a can nesa da jami’ar don haka ba mu sani ba ko mace ce ko namji suka yi yunkurin kai harin”.

Farfesa Gambo ya ce hukumomi na ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Jami’ar, yana mai cewa ana kai irin wadannan hare-hare ne saboda girman da Jami’ar ke da shi kuma ba a katange dukkanta ba.

A wannan shekarar dai an sha kai hare-haren kunar bakin wake a Jami’ar ta Maiduguri, abin da wasu ke ganin na da nasaba da rashin inganta tsaro a Jami’ar, ko da yake hukumomin tsaron na cewa suna yin bakin kokarinsu.

Da gaske Buhari yake yaki da cin hanci – Ribadu


Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, ya ce da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki da cin hanci da rashawa.

Mallam Nuhu shaida wa BBC cewa kudaden da ake kwatowa da wurin barayi da kuma gurfanar da su da ake yi a gaban kuliya sun nuna cewa gwamnatin Buhari ta kama hanyar kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya.

A cewarsa, “Gwamnati na kokari matuka. Da ma niyya ake so mai kwari; idan aka samu shugaba na gari wanda ya ce ba ya son cin hanci, to za a samu mafita. Sannan an karbe dukiyoyin da aka sace. Idan ka je babban bankin Najeriya za ka ga kudin da aka kwato. Wannan aiki ne na bangaren zartarwa”.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku saurari hira da Nuhu Ribadu

Tsohon dan takarar shugaban na Najeriya ya roki sauran bangarorin gwamnati – alkalai da majalisa – sun zage dantse wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Ya ce lokacin da yake jagorancin EFCC, an kama mutane da yawa kuma an hukunta su, yana mai yin watsi da zargin da ake yi masa na cewa ya zama karen farautar tsogon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo inda ya rika tuhumar masu adawa da waccan gwamnatin.

“Na sha kalubalantar mutane cewa su kawo hujjar cewa ina zabi ɗai-ɗai a yakin da nake yi da cin hanci amma har yanzu ba su kawo ba. Kar ka manta akasarin mutanen da na sa aka daure a wancan lokacin ‘yan jam’iyyar PDP ta tsohon shugaban kasa ce”.

Zai yi wahala Qatar ta cika sharuɗan da su Saudiyya suka sanya wa Qatar – Amurka


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An rufe kan iyakar Qatar da kasashen hudu

Amurka ta ce wasu daga cikin sharuɗan da kasashen Larabawa huɗu suka sanya wa Qatar kafin su janye takunkumin da suka aza mata za su yi wahalar cikawa.

Sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson, wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa amma sharudan sun bayar da wata kafa da za ta sa a samu mafita ga rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.

A ranar Asabar, ministan harkokin wajen Qatar ya yi fatali da sharuda 13 da Saudiyya da kuma kawayenta wadanda suka hada da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain suka gindaya wa kasarsa.

Sun zargi Qatar da goyon bayan ta’addanci – zargin da ta musanta.

Qatar ta fada cikin ce-ce-ku-ce na diflomasiyya da takunkumin karya tattalin arziki fiye da mako biyu da suka wuce, inda Iran da Turkiyya ke kai mata kayan abinci da sauran kayan more rayuwa.

Kasashen hudu na son cikin kwana goma Qatar ta janye dangantakar da ke tsakaninta da Iran sannan ta rufe sansanin sojin Turkiyya da ke kasarta.

Cikin sharudan da aka gindaya wa Qatar, har da rufe gidan talabijin na Al Jazeera, wanda kasar ke gudanarwa.

Mr Tillersonya ce Qatar na yin nazari kan bukatun da aka sanya mata, yana mai cewa hakan ya nuna cewa an “soma gano hanyoyin yin sulhu”.

Ya yi kira ga kasashen su zauna tare domin kawo karshen ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Ko Harry Kane zai iya komawa Man Utd?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kane ne dan wasan da yafi zura kwallo a raga a kakar firimiyar bara.

Kocin Manchester United ya fada wa kulob din bukatar sayen dan wasan gaban Tottenham Harry Kane, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta bayyana.

Jaridar wadda ake bugawa a Birtaniya ta ruwaito cewa Mourinho ya ce ya fi so a saya masa Kane maimakon tsaohon dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo.

Ana danganta Ronaldo da komawa Man U ne tun bayan da ya bayyana aniyyarsa ta barin kasar Spain.

Bayan da ta bayyana cewa Ronaldo zai ci gaba da wasa a Madrid ne, Mourinho ya bukaci kulob din Man U ya fara zawarcin Kane da kuma dan wasan gaban Madrid Alvaro Morata.

Manchester United ta lashe kofin Europa wanda hakan zai ba ta damar zuwa Gasar Zakarun turai na badi, duk da cewa ta kammala Gasar Firimiyar ba ne a matayi na shida.

Yemen ta fada annobar kwalara – MDD


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Babu wani bangare na kasar Yemen da annobar ta kai ba, in ji Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Yemen tana cikim mummunar annobar amai da gudawa irin wadda ba a taba ganin irin ta ba a tarihin duniya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

A wata sanarwa da hukumar Unicef da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka fitar sun ce yawan mutanen da suka harbu da cutar a kasar ya haura mutum 200,000.

Kawo yanzu mutum 1,300 ne suka mutu – daya bisa uku na wannan adadin yara kanana ne – yayin da ake ganin yawan wadanda suka mutu zai ci gaba da karuwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana daukar matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.

“Muna fuskantar mummunar annobar kwalarar da duniya ba ta taba ganin irin ta ba,” in ji sanarwar.

Ta ci gaba da cewa: “A cikin wata biyu, cutar kwalara ta karade duka fadin kasar Yemen wadda yaki ya daidaita.”

“In just two months, cholera has spread to almost every governorate of this war-torn country”.

Ana samun rahoton sabbin kamuwa da cutar kwalara kimanin mutum 5,000 a kowace shekara a Yemen.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Annobar ta fi shafar yara kanana

Fannin kiwon lafiyar Yemen ya gurkushe yayin da ake fuskantar karancin ruwa saboda shekara biyu da kasar ta yi cikin yaki, wadda ake yi tsakanin dakarun gwamnati wadanda Saudiyya take mara wa baya da kuma ‘yan tawayen Houthi.

Babban birnin kasar Sanaa da sauran garuruwan kasar suna karkashin ikon ‘yan tawayen ne.

Federer ya lashe gasar Halle Open


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Federer ya fara lashe gasar Halle Open ne a shekarar 2003

Dan wansan tenis ya doke Alexander Zverev abin da ya bashi damar lashe gasar Gerry Weber Open da ake yi a kasar Jamus har sau tara.

Dan kasar Switzerland, Federer mai shekara 35, ya doke ke shi ne da ci 6-1 6-3 a minutna 53 da fara wasan.

Dan wasan kasar Jamus Zverev shi ne ya doke Federer a wasan kusa da na karshe a bara.

“Ban san ko zan kara samun nasara a wannan gasar ba, saboda haka nake jin dadin wannan nasarar sosai,” in ji Federer.

Wannan nasarar da ya samu ita ce ta hudu a shekarar nan.

Federer ya lashe gasar Australian Open da BNP Paribas Open a Indiya da kuma gasar Miami Open duka a shekarar nan.

Portugal ta kai wasan kusa da karshe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kasar Portugal ita ce a matakin farko a rukunin A

Tawagar wasan kwallon kafar Porugal ta kai wasan kusa da na karshe a Kofin Zakarun Nahiyoyi bayan da ta doke New Zealand da ci 4-0.

Hakazalika, tawagar wasan Mexico ita ma ta kai wasan kusa da na karshen bayan ta doke Rasha da ci 2-1.

Kasar Portugal ita ce a matakin farko a rukunin A, yayin da New Zealand ta fita daga gasar saboda ta sha kayi har sau uku a jere.

Sai dai dan wansan bayan Portugal Pepe ba zai samu damar yin wasa ba a wasan kusa da karshen, saboda yana da katin gargadi har guda biyu.

Har ila yau, watakila dan wasa, Bernardo Silva, ma ba zai buga wasan ba, saboda raunin da yake fama da shi.

A ranar Lahadi ne Chile za ta kara da Australia, yayin da Jamus za ta kece raini Kamaru duka a rukunin B.

Mutum 140 ne suka mutu a Pakistan


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana kyautata zaton cewa wani mashayin taba sigari ne ya jawo gabarar

Akalla mutum 140 suka mutu bayan da wata babbar mota da ke dauke da man fetur ta fara ci da wuta a wani gari da ke gabashin Pakistan, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Rahotanni sun ce wasu gungun mutane ne suka isa wurin da tankar ta fadi don su diba man da ke tsiyaya ana cikin haka zai gobara ta tashi.

Mutane da dama ne aka garzaya da su asibiti.

Wasu sun ce tayar tankar ce ta fashe yayin da take kokorin yin kwana a kan hanyar da take tafiya.

Masu aikin ceto sun shaida wa BBC cewa tana iya yiwuwa wani masahin taba sigari ne da ke kusa ya haddasa gobarar.

“Wani cikin mutanen da ke wucewa ne ya kunna sigari kuma daga ne sai mummunar al’amarin ya faru,” in ji Jam Sajjad.

Firai ministar Kasar Nawaz Sharif ya katse ziyarar da yake yi a Landan saboda faruwar al’amarin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Pakistan APP ya bayyana.

Pakistan ba ta hanyoyi masu kyau kuma ana yawan samun tukin ganganci daga direbobi wanda hakan ya ke ci gaba da jawo hadurra a kasar.

Hana 'yan mata masu ciki karatu ya janyo cece-kuce a Tanzaniya


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaba Magufuli ya ce ‘yan mata masu juna biyu ba za su rika mayar da hankali ba a makaranta

Furucin Shugaban Kasar Tanzaniya, John Magufuli na cewa duk wata yarinyar da ta haihu ba za a barta ta ci gaba da karatu ba, ya janyo korafe-korafe daga ‘yan kasar da dama.

Hakan ya kai ga har an fara tattara korafe-korafen ta intanet don neman shugaban ya janye kalamansa.

Mista Magufuli ya yi gargadin ne ga ‘yan mata dalibai a ranar Litinin din da ta wuce: Inda ya ce “Muddin kika dauki ciki to taki ta kare ke nan.”

A shekarar 2002 ne dai aka kafa dokar da ta amince a kori duk wata dalibar da ta dauki ciki a kasar.

Dokar ta ce za a kori yarinya daga makaranta saboda “laifukan da suka shafi rashin tarbiyya” da kuma “aure”.

Korafe-korafen da ake tatara wa a dandalin sada zumunta na Twitter ya yi nuni da cewa, goyon bayan dokar da shugaban ya yi zai kawo karshen karatun ‘yan mata da dama a kasar, kuma “zai janyo nuna bambanci.”

Maimakon hakan an bukaci a bi hanyoyin da za su hana ‘yan matan daukar cikin a yayin da suke karatu.

‘Yan kasar Tanzania na sukar kalaman shugaban kasar tare da bayyana irin mawuyacin halin da ‘yan mata ke shiga, a yayin da suka dauki ciki suna makaranta.

Makonni biyu da suka wuce ne dai mataimakin shugaban kasar, Samia Suluhu, ya yi kira da a mayar da ‘yan matan da suka riga suka haihu makaranta, yana mai cewa bai dace a hana su damar samun ilimi ba.

Daurin shekara30 ga maza

Mista Magufuli, wanda ke magana a wajen wani taron gangami a garin Chalinze da ke da nisan kilomita 100 daga yammacin birnin Dar es Salaam, ya ce ‘yan matan da suka zama iyaye ba sa maida hankali a karatu idan sun koma makaranta:

“Da an fara darasin lissafi , sai ta ce wa malamin da ke ajinsu: Jaririna na kuka, bari na je waje na ba shi mama.”

Shugaban kasar ya ce su kuma mazan da suka yi wa ‘yan matan ciki, kamata ya yi a yi musu daurin shekaru 30 a gidan kurkuku, sannan a sa su aikin noma a lokacin da suke zaman jarun.”

Shugaban ya kuma soki kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ke matsa lamba a kan gwamnati sai ta janye dokar korar ‘yan matan masu ciki daga makaranta:

“Kungyoyin su je su bude wa ‘yan matan makarantu. Don ba za su tilasta wa gwamnati sai ta mayar da ‘yan matan makaranta ba,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “Ina ba da ilimi kyauta ga daliban da suka nuna cewa da gaske suke yi za su yi karatu, yanzu kuma kuna so in ilmantar da iyaye ne?”

Wakilin BBC, Sammy Awami, da ke Tanzania ya ce taron jama’ar da ke wurin sun rika tafa wa shugaban kasar yayin da yake jawabi.

Akalla ‘yan mata 8,000 ne a kasar ke barin makaranta a duk shekara, saboda sun samu ciki, a cewar rahoton hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch.

Adikon Zamani: Kun san girman matsalar cutar kanjamau tsakanin ma'aurata?


Ƙasidar wannan makon ta duba yadda za a shawo kan cutar kanjamau yayin zamantakewar aure, da hanyoyin kiyaye yaduwarta tsakanin kishiyoyi da mai gida da kuma muhimmancin gwaji.

Kamar yadda aka sani, cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam da ciwon AIDS ko SIDA sun zama ruwan dare gama duniya.

Babbar hanyar da aka fi kamuwa da cutar ita ce ta jima’i.

Hakan ya sa wasu matan aure da ke da kishiyoyi kamuwa da cutar, saboda matan suna da miji guda ne wanda ke zagayawa daga wannan matar zuwa waccan matar daga lokaci zuwa lokaci.

Na san wata matar kirki wacce mijinta ya yi mata kishiya. Ita kishiyar tana da cutar kanjamau, amma ba ta bayyana wa mijin ba.

Bayan wasu shekaru, sai maigidan ya kamu da cutar, hakazalika ita matar.

Da ace mijin ya kai amaryar aka gwada ta a asibiti, da wannan mummunan al’amarin bai faru ba.

Abin takaicin shi ne dukkansu sun mutu a sanadiyyar cutar.

Wannan abu ne da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a cikin al’ummominmu, kuma ya dace mu dauki matakan kawar da wannan cuta da gaggawa.

A matsayin ki na matar aure, shin kina da yakinin samun cikakkiyar kariya daga kamuwa daga cutar kanjamau daga kishiyarki ta wurin saduwa da mijinki?

Sau nawa ya kamata ke da kishiyoyinki ku yi gwajin ciwon kanjamau a asibiti?

Akwai alfanu kuma abu ne mai karbuwa idan matar aure ta nemi ita da mijinta su rika zuwa wajen gwaji a asibiti tare.

Sai dai idan matar aure ta kamu da cutar, wadanne matakai ne za ta iya dauka?

Kuma yaya irin wannan al’amarin zai shafi zamantakewar aure a gidan da ke da kishiyoyi?

Kuna ganin yarje wa miji ko mata zai iya kare su daga kamuwa da wannan cutar?

Kuma yaya batun soyayya take idan aka gano akwai wannan cutar tare da wanda za a aura, ko wacce za a aura?

Abu na farko shi ne, idan mijinki yana son yin wani auren, shin za ki nemi mijinki ya kawo shaidar cewa matar da zai aura ba ta da cutar HIV mai karya garkuwar jiki?

Akwai alamar zaki samu goyon bayan mutane idan kika kafe sai an yi gwajin cutar HIV akai-akai?

Jami’an kiwon lafiya na kira ga mata da su tabbatar an gwada matan da mazajensu ke son su aura, kafin a daura auren.

Kana suna shawartan miji da matarsa su rika zuwa a gwada su akalla sau biyu a kowace shekara, idan suna son su tabbatar da ba su da cutar.

A yayin da nake tattaunawa da jami’an kiwon lafiya, na gane cewa wadanda ke dauke da cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam na iya samun rayuwa mai armashi tare da abokan zamansu saboda irin ci gaban da aka samu a fagen samar da ingantattun magungunan da suke dakile habakar cutar a jikin masu fama da cutar.

An kai lokacin da matar da ke dauke da kwayar cutar HIV za ta iya haihuwar ‘ya’yan da ba sa dauke da cutar.

Idan hakan ya ci gaba da wanzuwa, lallai zamu samu karfin gwuiwar a fatanmu na ganin karshen mummunar cutar nan ba da dadewa ba.

Kafin nan, ina kira da babbar murya a garemu duka da mu daina kyamar masu fama da cutar SIDA.

A maimakon haka, kamata ya yi mu rungume su kuma mu rika nuna masu kulawa da tausayawa.

Ba lallai ne wanda ya kamu da cutar ya zama ya samota ne ta hanyar banza ba.

Amma gaskiya lamarin shi ne masu wannan cutar marasa lafiya ne.

Kuma yana da kyau mu fahimci cewa ba a kamuwa da cutar ta hanyar gaisawa, ko runguma, ko kuma yin mu’amala da masu dauke da ita.

Wannan zai taimaka masu wajen gudanar da rayuwa mai amfani har ma su zama abin alfahari ga al’ummomin da suke tare da su.

Kirana ga kowa shi ne a rika gwada mu akai-akai, ko mai aure, ko mara aure domin ku san irin halin da kuke ciki.

Wannan ne zai taimaka muku, har da iyalanku wajen samun kariya daga kamuwa da wannan cutar.

Ga masu saurarenmu a rediyo akwai tattaunawa a kan batun da Dokta Habiba Ibrahim, da Alhaji Alwan Hassan (sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don ku saurara)

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon zamani na wannan makon

Abubuwan da ake buƙata Musulmi ya yi ranar sallah


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Malaman addinin musulunci kan ce an so mutumin da ya yi azumin watan Ramadan, ya cika ibadarsa da sallar Idi.

Ustaz Hussaini Zakariyya ya yi bayani kan wasu abubuwa da ake son mai azumi ya yi, a ranar sallar Idi kamar haka:

 • Samun sallar asubar ranar Idi a jam’i
 • Wankan zuwa Idi
 • Ba da zakkar fid-da-kai ga mabuƙata
 • Cin abinci kafin tafiya masallaci
 • Sanya tufafi masu kyau
 • Takawa zuwa masallaci
 • Zikiri yayin tafiya
 • Ba a sallar nafila a filin idi
 • Sauraron huɗuba bayan sallar idi
 • Gaisawa da juna bayan sallah
 • Sauya hanyar tafiya wajen dawowa
 • Yara da mata da tsoffi duka na zuwa idi
 • Mata masu haila za su iya zuwa sallah amma za su tsaya a gefen guda na masallaci

Ga kuma karin bayani daga Dokta Ahmed Gumi

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Dokta Ahmed Gumi

Masar ta sallama wa Saudiyya iko da tsibirai


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tiran {na kusa) da Sanafir (na nesa) ba kowa a cikinsu sai sojoji da jami’an wanzar da zaman lafiya

Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da taƙaddama wadda ke miƙa ikon tsibiri biyu da babu kowa cikinsu a tsakiyar Tekun Maliya ga Saudiyya.

An cim ma yarjejeniyar sarayar da tsaunukan Tiran da Sanafir ne a lokacin wata ziyara da Sarki Salman ya kai Masar bara. Kuma majalisar dokoki ta mara mata baya a cikin makon jiya.

Batun ya haddasa zanga-zangar da ba kasafai ake yi ba a Masar, inda aka zargi shugaba Sisi da “sayar” da iyakar ƙasar don samun tallafin Saudiyya.

Sai dai, an ci gaba da tafka shari’ah kan matsayin tsibiran.

Wata kotun ƙasar ta soke shawarar miƙa wa Saudiyya tsibiran, yayin da wata kotun daban ta tabbatar da ita. Yanzu dai ana dakon hukuncin kotun tsarin mulkin Masar don ta yi nata hukunci a kan ɓangaren mulkin da ke da ikon ƙarshe a kan batun.

A cikin makon jiya ne, majalisar dokoki ta mara wa ƙudurin baya, inda ta ce tana da hurumi a cikin batun. Matakin da ya sake haddasa zanga-zanga a birnin Alƙahira.

Shugaba Sisi dai ya ce da ma can tsibiran mallakar Saudiyya ne, kawai dai ta nemi Masar ta jibge dakarunta ne a shekarar 1950 don kare su.

‘Yan adawa sun zargi shugaban Masar ɗin da keta tsarin mulki tare da sallama iko da tsibiran da nufin daɗaɗa wa Saudiyya rai, wadda ke ba shi goyon baya na kuɗi tun lokacin da ya jagoranci juyin mulkin soja don kifar da zaɓaɓɓen magabacinsa, Mohamed Morsi a shekara ta 2013.

Image caption

‘Yan adawa sun zargi shugaba Sisi da “sayar” da tsibiran waɗanda ke cikin teku ga Saudiyya

 • Sanafir da Tiran, tsibirai ne da ke kilomita huɗu a tsakani cikin Tekun Maliya.
 • Tiran yana nan a bakin mashigin ruwan Aqaba, a wani muhimmin ɓangaren teku da ƙasar Isra’ila ke amfani da shi wajen shiga Maliya
 • Babu kowa a cikin tsibiran face sojojin ƙasar Masar da dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙasashen duniya.
 • An jibge dakarun Masar ne a tsibiran tun a 1950, bayan Saudiyya ta nemi haka
 • Isra’ila ta ƙwace tsibiran a shekarar 1956 da 1967, daga baya kuma ta dawo da su ga Masar a lokutan biyu.

Wani ƙwaro ya faɗa bakin shugaban ƙasa


Hakkin mallakar hoto
@pzactual

Image caption

Bayan ya taune rinar shugaba Luis Guillermo ya riƙa ƙiƙƙifta idanu

Shugaban ƙasar Costa rica, Luis Guillermo Solis ya taune ƙwaron da faɗa bakinsa lokacin da yake jawabi kai tsaye a wani taron manema labarai.

Shugaba Luis Guillermo na jawabi a gaban wasu ‘yan jarida cikin makon jiya a garin Puntarenas, lokacin da wata rina ta yiwo shawagi daidai bakinsa.

Kuma kafin ya ankara, sai ta yi wuf ta faɗa ciki, shi kuma ya taune ta ya haɗiye.

Al’amarin dai ya ba wa mutanen da ke wajen tausayi da kuma mamaki, kuma ala dole aka dakata da jawabin har ya kurɓi ruwa.

An ji shugaban ƙasar a cikin bidiyon yana cewa na taune ta, na taune rina.

Hakkin mallakar hoto
@pzactual

Image caption

Bayan faruwar al’amarin shi da mutanen da suke wajen sun kece dariya

Hakkin mallakar hoto
@pzactual

Image caption

Luis Guillermo ya kwankwaɗi ruwa kuma ya ci gaba da hirar

Hakkin mallakar hoto
@pzactual

Image caption

Shugaban na Costa rica ya mai da al’amarin raha

Luis Guillermo ya riƙa ƙiƙƙifta idanu kamar zai yi amai amma ya dake.

Daga nan sai shi da ‘yan jaridar da ke wajen suka kece da dariya har yana cewa: “ai wannan abinci ne mai gina jiki zalla.”

Bayan shugaba Luis Guillermo ya sha ruwa kuma ya share bakinsa, sannan ya ci gaba da hira ga ‘yan jaridar.

Zama lafiya a Nigeria muke addu'a kullum – Buhari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Karon farko kenan da aka ji muryar shugaba Buhari bayan kwana 48

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya nemi al’ummar ƙasar su guji maganganun tayar da hankali, su rungumi zaman lafiya da juna.

Ya ce “zama lafiya a Nijeriya, shi muke roƙon Allah kullum.”

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin saƙonsa na bikin ƙaramar sallah, karon farko bayan kwana 48.

Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya ce ga alama shugaban na bayani ne game da musayar kalaman nuna ƙiyayya “tsakanin wasu ɓangarori na Nijeriya”.

A iya fahimtata saƙon sahihi ne, murya ce ta shugaba Muhammadu Buhari kuma murya ce wadda ta nuna an naɗe ta, ba da jimawa ba, in ji Tangaza.

Ya ce don kuwa ta yi bayani kan wasu batutuwa da ake ciki, da suka haɗar da bikin sallah da kuma damuna gami da uwa-uba kalaman nuna ƙiyayya.

A baya- bayan nan dai, Muƙaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ta gudanar da taruka da wasu fitattun mutane da sarakuna don kwantar da ƙurar da ta taso.

Dambarwa ta ɓarke ne lokacin da wasu ƙungiyoyin matasa a arewacin ƙasar suka ba ‘yan ƙabilar Igbo wa’adi na su fice daga yankin.

A cewarsu, saboda ƙaruwar kiraye-kirayen da wasu ƙungiyoyin Igbon ke yi don neman kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabas.

Lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da tankiya har ma da musayar ba da wa’adi a tsakanin wasu ‘yan ƙasar.

A cikin jawabin, Buhari ya gode wa ‘yan Nijeriya kan yadda suke yi masa addu’o’in samun lafiya.

Ya kuma yi fatan saukar damuna mai albarka don samun abinci cikin sauƙi.

Muhimmiyar zakkar fidda kai ga Musulmi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana so ne mutum da fitar da zakkar da nau’in abinci da ya fi amfani da shi

Yayin da ake kammala azumin watan Ramadan, ana so Musulmi maza da mata, yara da manya da suka yi azumin watan Ramadan za su fitar da zakkar fidda kai kafin tafiya masallacin idi.

Ita dai zakka zakkar fidda kai sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah SAW.

Ga dai tattaunawar da abokiyar aikinmu Aisha Sharif Baffa ta yi da Ustaz Husseini Zakariya ya yi karin bayani kan zakkar.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ustaz Husseni Zakariya da ke Abuja

Indiya: An kashe Musulmi 'don ya ci naman sa'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An kama wani mutum a kasar Indiya bisa zargin yana cikin gungun mutanen da suka kai wa wasu Musulmi hudu hari don sun ci naman saniya.

Mutumin wanda aka bayyana sunansa da Ramesh, an ce ya kai wa Musulmin hari ne ranar Juma’a yayin da yake cikin maye.

Daya daga cikin Musulmin ya rasu kuma an bayyana sunansa da Junaid Khan, mai kimanin shekara 16 da haihuwa.

Mabiya addinin Hindu suna martaba saniya kuma an haramta yankata a jihohi da dama da ke kasar.

An kashe Musulmi biyu kan satar saniya

Jagoran Musulmi a India ya rasu

Yayin da yake magana, Ramesh ya ce “abokaina ne suka ce na kai wa yaran Musulmin hari don sun ci naman saniya.”

Mahaifin marigayin ya ce an kai wa yaran harin ne saboda kayan Musulmi da suke sanye da su.

Har ila yau, an ruwaito wani dan uwan marigayin yana cewa “maharan ba su ko kula da kalaman da yaran suke yi cewa su ba sa dauke da wani naman saniya.”

Mabiya addinin Hindu su ne kashi 80 cikin 100 na jama’ar kasar Indiya, yayin da Musulmi suke kashi 14 cikin 100.

Alvaro Arbeloa ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arbeloa ya yi wa Liverpool wasa fiye da sau 200

Tsohon dan wasan Liverpool, Real Madrid da kuma West Ham Alvaro Arbeloa ya yi ritaya daga kwallon kafa.

Dan wasan mai shekara 34, wanda tsohon wasan tawagar Spain ya koma Madrid daga Liverpool a shekarar 2009.

Arbeloa ya taba lashe La Liga sau daya da kuma Kofin Zakarun Turai sau biyu a Madrid, kafin ya koma kungiyar West Ham a watan Agustan bara.

“Lokaci ya yi da zan yi bankwana. Har yanzu ina da karfin kara ci gaba da wasa,” in ji shi.

Ya yi wa Liverpool wasa fiye da sau 200, har ila yau ya, kasance a Madrid da kuma West Ham tsakanin shekarar 2007 zuwa 2017 kuma sau 56 yana wa tawagar Spain wasa.

Qatar ta yi watsi da bukatun kasashen Larabawa


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Qatar tana da arzikin iskar gas ne

Ministar Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya yi watsi da bukatun da Kasashen Larabawa suka nemi kasar ta cika su guda 13, gabanin su dawo da hulda da ita.

A ranar Juma’a ne kasashen Saudiyya da Bahrain da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka miƙa wa Qatar buƙata 13 da suke son ta cika, ciki har bukatar rufe gidan talbijin na Al Jazeera.

Sun kuma ce ta rage hulɗa da ƙasashen Iran da Iraqi, sannan ta rufe wani sansanin sojan sama na Turkiyya duk a cikin kwana goma.

A farkon watan nan ne kasashen suka yanke hulda da Qatar saboda zargin tana goyon bayan ta’addanci.

Zargin da Qatar ta musanta.

Saudiyya ta kori raƙuman Qatar

Qatar na neman sulhu da kasashen Larabawa

Morocco za ta aike da kayan abinci Qatar

Ministan ya ce abin da kasashen suke nema daga Qatar ba mai yiwu ba ne.

Kafar yada labaran Al Jazeera wadda take mallakin kasar Qatar ce ta mayar wa Kasashen Larabawa martani ranar Juma’a, inda ta ce hakan yunkuri ne na “hana ‘yancin fadin albarkacin baki”.

Yadda ake kammala azumin Ramadan a duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana kawo karshen azumin watan Ramadan ne da sallar Eid al-Fitr, inda jama’a suke fitar da zakkar fidda kai da yin sallar idi cikin sabin tufafi.

Sai dai sanin takamaiman ranar da za a yi sallar abu ne mai wuya, kamar da Ahmen Khawaja da Amir Rawash suka yi bayani.

Muhimmancin ganin wata

A yayin da watan azumin Ramadan yake zuwa karshe, galibin Musulmi biliyan daya da miliyan 800 suna fatan ganin jinjirin watan da zai kawo karshen watan azumi.

A addinin Musulunci ana amfani ne da tsarin kalandar hijiriya. Watan Ramadan shi ne na tara.

A kowace shekara ana samun bambancin kwana 11 ne tsakanin kalandar da ta miladiya.

Amfani da lissafin kalandar hijiriya yana da matukar amfani ga Musulmi kuma daya daga ciki shi ne yadda ake lissafin watan Ramadan a kowace shekara.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani kantin hijabi gabanin bikin Idi a birnin Jakarta

Musulmi suna azumtar watan Ramadan ne, inda suke kauracewa abinci da abin sha daga fitowar Al fijir zuwa faduwar rana.

Ana samun bambance-bambance nan da can a fadin duniya, inda wasu mutane a sansan duniya suke kwashe lokaci mai tsawo yayin azumi wasu kuma kankanin lokaci.

Saboda yadda ake amfani da tsarin kalandar ganin wata, a duk bayan shekara 33 ne yanayin da ake ciki yake koma yadda yake wato yanayin zafi ko sanyi.

Ana yin Eid al-Fitr ne ranar daya ga watan 10 wato Shawwal.

Galibin Musulmi suna dogaro ne da sanar ganin watan da hukumomi suke ba su maimakon su duba watan da kansu.

Akwai wadanda suke amfani da na’urorin kimiyya don ganin watan. Har il yau, akwai kuma wasu da suke cewa su sai sun ga watan da idanunsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu Musulmi suna amfani da na’ura don ganin jinjirin watan Shawwal

Ba a yin ranar idi rana guda a duk fadin, amma dai bambancin ba ya wuce na kwana daya ko biyu.

Misali, mahukunta a Saudiyya – kasar da galibi mabiya Sunni ne kuma nan ne asalin addinin Musulunci. A can ana sanar da fara azumin ko ajiyewa ne bayan an tabbatar da ganin watan.

Galibin Musulmi da ke sauran kasashen duniya haka suke yi.

Amma a Iran, wadda galibin jama’arta ‘yan Shia da kuma tsirarun mabiya Sunni ne tana amfani ne da hanyoyi biyu – daya daga sanarwar Shugaban Addinin Kasar Ayatollah Ali al-Sistani, sai daya sanarwar daga malaman sunnin kasar wadda mabiya sunni ke bi.

A rana guda mabiya Sunni da takwarorinsu na Shia suka yi idin karamar sallah a shekarar 2016, karo na farko a shekaru masu tsawo.

A kasar Turkiyya wadda ba ruwanta da addini, ana amfani ne da lissafin masana kimiyya don dauka ko ajiye azumin Ramadan.

A nahiyar Turai kuma galibin mutane suna jirin sanarwarce daga shugabannin al’ummarsu – kodayake hakan yana dogara ne da ganin watan wasu kasashe.

Matar da ke taimakon marasa lafiya su mutu cikin sauki


Image caption

Mongolia ta hada iyaka da kasashen China da Rasha

Shekara 15 da ta wuce babu abin da ake kira kula da marasa lafiyar da ke gaf da mutuwa a kasar Mongolia.

Sai dai a yanzu an samu hakan, sanadiyyar wata mata mai suna, Odontuya Davaasuren, wadda ta shawo kan cibiyoyin lafiyar kasar kan cewa yakamata a taimaka wa mutane su daina mutuwa a cikin azabar ciwo.

Mahaifin Odontuya Davaasuren ya mutu a Mongolia, bayan fama da cutar sankarar hanta a lokacin tana da shekara 17, kuma tana karatun kwarewa a fannin likitanci da ya shafi kananan yara a Leningrad da ke kasar Rasha.

“Ban samu damar kulawa da mahaifina ba ballantana mu yi sallamar karshe,” in ji Odontuya.

“Lokacin da na dawo Mongolia, ‘yar uwata ta shaida mini cewa mahaifinmu ya yi fama da tsananin ciwo.”

Shekaru da dama bayan nan, lokacin da ta fara aikin likita kuma tana tare da surukarta wadda ke fama da cutar sankarar hanta, ta shaida yadda radadin ciwo ke hana mutane su mutu cikin sauki.

“Na kula da ita, na dinga ba ta abinci na wanke tufafinta na sauya mata kayan jikinta, amma duk da haka ban iya yin komai game da radadin ciwon da ke damunta ba don ban san yadda zan yi hakan ba,” a cewarta.

Maganin da kawai ake da shi ga mutanen da ke gab damutuwa a Mogolia shi ne maganin ciwon jiki ko na ciwon kai, amma ba na radadin ciwon sanadin wani tsuro a ciki ba.

Babu wani magani da sauran cututtuka kamar na tashin zuciya da kuma amai.

“Na ji matukar kunya cewa ni ba likita ba ce ta gari domin ban san yadda zan taimaka ba,” in ji ta.

Kamar hakan bai isa ba, a wajen aikinta ta sha ganin yaran da ke fama da amosanin jini suna cikin azabar ciwo ko iya murmushi ko magana ba sa yi.

Har ila yau, ta ga wata mata wadda ta dinga rusa kuka tana neman a kashe ta ko ta huta da tsabar azabar cutar daji na cikin ciki.

“Marasa lafiya da dama sun mutu a gida cikin tsananin ciwo na sarari da kuma na boye.”

“A mafi yawacin lokuta iyalai kan koma kan maganin gargajiya wasu kuma na sayen magani masu tsada, sai dai duk da haka ba ta sauya zani ba.”

Amma tsarin kulawa da mutanen da ‘yan watanni ko wasu ‘yan shekaru ne ya rage musu a duniya ko wata hanyar saukaka musu babu shi a Mongolia.

A lokacin da ta kai ziyara zuwa Sweden a shekarar 2000 domin halartar wani taron kungiyar masu ba da kulawa don sassauta yanayin ciwon da mutane ke ciki a nahiyar Turai ya sa ta gano bakin zaren.

Wanda ta hakan ne ta maida Mongolia kasar da ake saukaka mutuwa.

“Kafin na je taron na Stockholm a shekarar 2000, ban taba jin kalmar ‘ba da kulawa don sassauci ba,” in ji likitar.

“Don babu irin hakan a Mongolia ko wani yanki na al’umomin da ke bin tsarin gurguzu.”

Da komawarta gida sai ta kai kukanta ga ma’aikatar lafiya ta Mongolia, amma kuma sai aka yi biris da ita.

“‘Me ya sa za mu kashe kudade a kan mutanen da suka kusa mutuwa,’ suka tambayeta ‘yayin da ba mu da isassun kudaden kashewa marasa lafiyar da suke raye?'”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Al’ummar kasar makiyaya ne a gargajiyance

Wata iska mai sanyi da za ta iya daskarar da yatsunka a cikin ‘yan dakoki na kadawa a kan duwatsun da ke wajen Ulan Bator, babban birnin Mongolia.

Ba ka iya ganin gini ko daya ko fitilar kan hanya sai dai tanti da ake kira gers, wanda a gargajiyance makiyaya kuma manoma ke amfani da su.

Davaasuren wadda yanzu shekarunta 59 a duniya kuma tana da jikoki, ta shiga daya daga cikin tantin mai shudin kaure na katako, inda ta hadu da meets Timurbat.

Yana jingine da bango a kan wani gado na katako, kuma a bayan gadon wani yadi ne mai adon furanni da aka kewaye jikin tanti da shi.

Marar Timurbat’s rabu gida biyu, fatarsa ta yi ruwan dorawa kuma idonsa ya zama ruwan goro a yayin da yake fama da cutar kansa huhu.

Image caption

Cutar hanta kan yi wa mutum kisan mummuke ne

Timurbat ya kwashe tsawon rayuwarsa yana kiwon dabbobi akan doki, kamar dai wadanda suka gaba ce shi.

Amma a yanzu ko magana ma da kyar yake yi ballanta na ma ya tsaya a tsaye.

“Kafafuna da hannuwana na yi mini ciwo, kaina na sarawa,” yana magana yana runtse idanu.

“Bana iya bacci, ina ma ace bana jin wannan azabar ciwon.”

Davaasuren ta tsuguna a gabansa ta taba cikinsa.

Ta ce “Kana iya ganin cutar kansar (cutar daji) a mararsa.”

“Wannan matakin da cutar take babu magani sai dai zan so a ce baya jin azabar ciwon da yake ji a yanzu.”

Har ila yau, ta tambayi matar Timurbat, Enkjargal, ko wane irin magani ake ba shi, inda ta bayar da shawarar a kara yawan maganin rage radadin ciwo na Morphine.

“A baya yana shan kwayar maganin daya a kowane sa’o’i hudu, amma a yanzu yana bukatar fiye da hakan don dayan baya isa,” in ji likitar.

A wajen tantin yayin da Davaasuren ke shirin tafiya sai, Enkjargal ta fara zubar da hawaye.

Davaasuren ta rungume ta ta yi mata rada a kunne.

Kasar Mongolia kasar da aka fi mutuwa a sanadiyyar cutar kansa ko sankarar hanta – hakan ya rubanya sau shida irin yadda ake samun mutuwar a wasu kasashen duniya. – kuma alkaluman karuwa suke yi.

Ana kamuwa da kwayar cutar ne ta hanyar ciwon hantar ne nau’in B ko C.

Kuma yana yaduwa ne ta jini da saduwa (musammanma cutar nau’in B).

Fiye da kashi daya bisa hudu na mutanen Mongolia cutar ta yi musu mummunan kamu.

Cutar da kisa ne da sannu-sannu. Kuma a kan dauki shekaru cutar na cin hanta, sannan kuma ta janyo tsuro a jikin wasu masu fama da cutar.

Sai dai a lokacin da za a ga alamominta babu wani abin da za a iya yi.

“Mutuwa mai kyau… da kuma kyakkyawar rayuwa kafin mutuwa hakkin ne na dan Adam,” in ji Davaasuren says.

Domin tabbatar da abin da take fada bayan komawarta gida, likitar ta dauki bayanan marasa lafiyar da suka kusa mutuwa a gida, inda ta dauki hoton bidiyonsu ta kai wa ma’aikatar lafiyar.

A wancan lokaci aka sallami marasa lafiyar da aka san sun kusa mutuwa daga asibiti ne su koma gida.

Kuma saboda ba su da maganin da zai rage musu radadin ciwon mafiya yawansu na kashe kansu ne.

“Mutane da dama na rokon in kashe su,'” a cewarta.

“Sun gwammace su mutu da su shiga wannan yanayin radadin ciwo. Bayan na dauki bidiyon ne sai na zauna da yamma in kalle su in yi ta kuka saboda ganin wuyar da suke sha.”

Kuma saboda alkaluman da kasar ke da su na masu fama da cutar hanta, Davaasuren ta san iyalai da dama za su fada cikin wannan yanayi na ciwo.

Hakarta ta cimma ruwa ne a shekarar 2002, a lokacin da aka amince ta fito da wani shiri na sassauta zafin ciwo ga marasa lafiya domin taimakawa wadan da ke gaf da mutuwa da makusantansu.

Image caption

Odontuya (a tsakiya) da wasu ma’aikatan jinya guda biyu

Bayan shekaru 15 kuma kowane asibitin lardin suna samar da wannan kular, haka ma dukkanin asibitoci tara da ke Ulan Bator.

Biyar daga cikinsu na bayar da kulawa ga marasa lafiyar da suka kusa mutuwa a asibiti da kuma a gida.

Wani sauyi da likitar ta kawo shi ne kara yawan maganin rage radadin da ake bayarwa.

Kafin ta taimaka wajen sauya dokar amfani da maganin ta kasa, mutane da dama sun yi imanin hakan zai kara sa wa a samu damar kara shaye-shaye.

Hakazalika, likitar ta bayyana cewa “A yanzu shagunan sayar da magani na iya rarraba maganin Morphine kyauta ga dukkannin masu fama da cutar hanta har zuwa mutuwarsa.”

Ta kuma taimaka wajen bayar da horo ga dubban likitoci kan yadda za su bayar da maganin, sannan kulawa ta musamman ga marasa lafiyar da ke gadon mutuwa, tana mai cewa duka biyu suna da muhimmanci.

“Kulawa ta fannin addini ya fi shan maganin rage radadin muhimmanci,” in ji ta.

“Irin wannan kulawar kan gusar da zafin ciwo yana kuma kwantar da hankalin marasa lafiya tare da kawar da fargabar da suke da ita da rashin bacci……kuma akwai yiwuwar su yarda da kaddarar da ta same su na mutuwa.”

Image caption

Likitoci na amfani da nau’rar zamani domin gano tsuro a cikin marasa lafiya

A dakin bayar da kulawar da ke babban asibitin kansa na Mongolia, Davaasuren na magana da wani mutum wanda fata ta kare masa da ke zaune a kan wani gado a kusa da taga.

“Sunansa Renchin kuma yana aikin gini ne a daji,” Davaasuren ta yi karin bayani.

“Yana da ‘ya’ya biyar, kuma yana cin cewa mutuwarsa ta kusa, sai dai a wasu lokutan idan ‘ya’yansa na nan ya kan ce ya samu sauki kada su damu,”

“Amma yanzu na gaya masa lokaci ya yi da zai san abin da zai gaya musu da yadda zai gaya musu domin ina jin lokacinsa ya yi.

Gara a gaya musu gaskiya maimakon boyewa. Ya yi murmushi ba tare da ya yi kuka ba.”

Likitar ta yi magana da ‘yar Renchin wadda ke zaune nan kusa.

Dan murmushin da ke fuskatarta nan da nan ya gushe a yayin da suke magana, kuma kwalla ta fara zuba daga idanunta, sannan jikinta ya fara rawa.

“Na shaida mata cewa mahaifinta zai mutu,” “Ta ce da tana da fatan zai iya warkewa, amma na shaida mata cewa cutar ta kai makura. Yanzu ba lokacin da za a yi ta dura masa magani ba ne lokaci ne da za ku nuna masa kauna. kuma ta ce ta gode ta fahimce ni.’

“Har yanzu abin na yi mini wuya, don a wasu lokutan ma tare da marasa lafiyar za mu yi ta kuka.”

Ana fargabar ƙasa ta binne mutum 140 a China


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana fargabar akwai gomman mutane da ƙasa ta binne sakamakon zaftarewar lakar

Masu aikin ceto a China na ci gaba da bincike don neman fiye da mutum 140 da ake fargabar wata gawurtacciyar zaftarewar laka sakamakon ruwan sama ta binne su.

Iftila’in ya faru ne a wani yanki mai cike da tsaunuka cikin lardin Sichuan daf da iyakar kasar da yankin Tibet.

Kimanin gidaje 40 ne suka lalace a ƙauyen Xinmo cikin yankin Maoxian, bayan wani ɓangare na wani tsauni ya rufta a cikin daren Juma’a.

Ma’aikatan ceto kimanin 400 ne suka duƙufa don lalubo masu sauran shan ruwa a gaba da duwatsu suka binne a cikin ƙasa.

Ana kokarin ceto mahaka ma’dinai a China

An hana China fataucin fatu da naman Jaki

Mun ga ribar haihuwa fiye da ɗaya — China

Hotunan da jaridar People’s Daily ta wallafa sun nuna motocin buldoza na ƙoƙarin kawar da manyan ɓaraguzai da tarin ƙasa yayin da aikin ceto ke ci gaba.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

An kai motocin haƙar ramuka don kwashe ɓaraguzai a ƙoƙarin zaƙulo mutane

An gano wasu ma’aurata da jaririnsu, inda aka garzaya da su asibiti bayan ma’aikatan ceto sun yi amfani da igiyoyi wajen kwashe manyan duwatsu, yayin da wasu ke binciken ɓaraguzai a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

A cewar kamfanin dillancin labaran China Xinhua zaftarewar lakar ta katse tsayin kilomita biyu na wani kogi.

‘Yan sandan yankin sun ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a baya-bayan nan cikin yankin, kuma lamarin ya ƙara ta’azzara sakamakon rashin tsirrai a yankin.

Xinhua ya ce an rufe titunan yanki ga duk masu abubuwan hawa a ranar Asabar face ma’aikatan agaji.

'Miliyoyi ne ke fama da cutar amosanin jini a Nigeria'


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

Ana gadon cutar amosanin jini ce wadda ba ta maganin warkewa daga wajen iyaye

Wata matashiya da ke fama da cutar amosanin jini a Nijeriya ta ce tana shiga mawuyacin hali a duk lokacin da ciwon ya tashi.

Ta ce sai dai a ɗauke ta, don kuwa ba ta iya tafiya, kuma takan shafe tsawon sa’a 24 tana murƙususu saboda ciwo.

Likitoci sun ce a yankin kudu da Hamadar Sahara, mutum miliyan 12 zuwa 15 ne ke fama da cutar amosanin jini kuma kashi sittin cikin 100 suna Nijeriya.

Wani likita a babban birnin Nijeriya, Dr. Ibrahim Kwaifa ya ce ba a san haƙiƙanin yawan masu cutar amosanin jini ba, amma dai ƙwararru na cewa mutum miliyan ashirin zuwa miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ita a duniya.

Haka kuma duk shekara ana haifar mutum kimanin 2,400 masu wannan cuta.

Hakkin mallakar hoto
SPL

Image caption

Lafiyayyun ƙwayoyin halittun jini na da siffar ƙawanya, waɗanda suka nakasa kuma sukan tanƙware

Ya ce ana gadon cutar ne daga wajen iyaye masu halittun ƙwayoyin jinin da suka samu nakasa.

Fauziyya Madaki ta ce idan ciwon ya tashi: “Ba sassauci, zugi ko ta ina. Tun daga kaina har ƙarshen yatsuna na ƙafa.

Nakan ce a matsa min jikina, (amma) ko an matsa, ba amfani, sai dai in yi ta addu’a. Wani lokaci sai na shiga surutai da ba ma’ana saboda tsabagen ciwo”

Ta ce a wasu lokuta sai an kai ta asibiti don yi mata ƙarin ruwa da ba ta magunguna da za ta ji sassauci.

Ta ce ba shakka takan fuskanci ƙyama, musammam ta fuskar auratayya.

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa mahaifiya ce da ke da ‘ya’ya masu larurar amosanin jini kuma har ta kai ga kafa cibiya don tallafawa masu cuta.

Ta ce ta sanya kanta cikin sha’anin tallafa wa masu cutar ne saboda ta san irin raɗaɗin da suke ji.

“Irin magungunan da na ga yarana na sha don su zauna cikin ƙoshin lafiya su ne na ga ya kamata in dinga rabawa masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ba za su iya saye ba.”

Ta ce amosanin jini, cuta ce da ke buƙatar shan magani har iyakar rayuwar mai fama da ita.

Kuma ta ce tana raba takardu ne na jerin magungunan da masu amosanin jini ke buƙata don samun tallafi daga mutane.

Dr. Ibrahim Kwaifa ya ce ta hanyar ɗaukar matakan wayar da kai da gwada nau’in jini a tsakanin masu niyyar yin aure ana iya guje wa haifar ‘ya’ya cutar masu amosanin jini.

Saudiyya ta daƙile kai hari Masallacin Ka'aba


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta ce wani gini ya ruguje lokacin da ɗan harin ƙunar-baƙin-wake ya tarwatsa kansa a ciki

Ƙasar Saudiyya ta ce ta daƙile wani “yunƙurin harin ta’addanci” da aka so kai wa Masallacin Harami a Makkah – wurin ibada mafi tsarki ga musulmi.

Wani ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa lokacin da dakarun tsaro suka zagaye ginin da yake ciki, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida.

Ginin ya ruguje, inda ya jikkata mutum 11 ciki har da ‘yan sanda. Jami’ai sun ce an kuma kama wasu ‘yan ta-da-ƙayar-baya guda biyar da ake zargi.

Miliyoyin al’ummar Musulmi ne daga faɗin duniya ke taruwa a Makkah don aikin Umrah a ƙarshen azumin watan Ramadan.

Jami’an Saudiyya ba su fitar da ƙarin bayani a kan harin ta’addancin da suka daƙile ba.

A shekarun baya-bayan nan, ƙasar Saudiyya ta fuskanci jerin munanan hare-hare, ƙungiyar IS mai iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin kai da dama a cikinsu.

Akasarin hare-haren, ana kai su ne kan tsiraru mabiya ɗariƙar Shi’a na ƙasar da kuma dakarun tsaro.

A watan Yulin shekara ta 2016, an kashe jami’in tsaro huɗu a wani harin ƙunar-baƙin-wake da aka kai kusa da Masallacin Annabi a Madina.

Saudiyya dai na cikin rubdugun mayaƙan da ke gwabza faɗa da ƙungiyar IS da sauran wasu ‘yan bindiga masu iƙirarin jihadi a ƙarƙashin jagorancin Amurka a Syria da Iraqi.

An kama masu kitsa kai hare-hare biranen arewacin Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan sandan fari kaya suna aiki tare da ‘yan sandan kayan sarki ne wajen tabbatar da doka da oda a Najeriya

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta kama wasu masu shirin kai hare-hare was birane a arewacin kasar.

Wata sanawar da Tony Opuiyo na hukumar ya fitar, ta ce hukumar ta bankado wani shirin kai hare-hare kasuwanni da wuraren shakatawa da kuma wuraren ibada a jihohin Kano da Sokoto da Kaduna da kuma Maiduguri.

Hukumar ta ce dakile harin ya biyo bayan kama wani mai suna Yusuf Adamu da Abdulmumini Haladu a Sokkwoto, wadanda ke shirin jagorantar kai hare-hare a Kano da safiyar Juma’a.

Sanarwar ta ce hukumar ta kama wani gwanin hada abubuwan fashewa, Bashir Mohammed a karamar hukumar Kumbosto da ke jihar Kano a ranar 20 ga watan Yuni inda aka samu bindigogi takwas kirar AK47 da gurneti 27 da harsasai 793 a gidansa.

Har wa yau an samu kwanson albarushi 20 cike da harsasai a gidan tare da komfutar tafi da gidanka uku, da wayar salula daya da kuma tukunyar gas.

Hukumar ta kara da cewar ta bankado shirin masu tada kayar bayan na shiga cikin jerin gwanon da ‘yan shi’a ke yo a ranar tunawa da Birin Kudus.

An naɗa Mauricio Pellegrino sabon kocin Southampton


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A shekarar 2012 ne Pellegrino ya zama cocin Valencia

Kungiyar Kwallon Kafa ta Southampton ta nada Mauricio Pellegrino a matsayin sabon kocinta.

Kocin dan kasar Argentina, mai shekara 45, zai maye gurbin Claude Puel wanda aka sallame shi a farkon watan Yuni bayan ya yi kakar wasa daya.

Pellegrino ya ajiye aikin jagorancin kungiyar Alaves ne a karshen watan Mayu, bayan Barcelona ta lashe su a wasan karshe na Kocin Spain kuma suka kammala gasar La Liga a matsayi na tara.

“Falsafata da kuma tsare-tsarena za su dace sosai da kulob din Southampton,” in ji Pellegrino wanda ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara uku da kulob din.

Ya ci gaba da cewa:”So nake na rika cin wasanni, na samu nasara ta yadda zan gina kulob wanda kowa zai rika ba da gudunmuwa 100 bisa 100.”

Pellegrino ya taba zama mataimakin kocin kulob din Liverpool tsakanin shekarar 2008 zuwa 2010, yayin da a shekarar 2012 ya zama kocin Valencia.

An kai harin ƙunar bakin wake Kamaru


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An kai harin kunar bakin wake guda biyu a garin Mora da ke arewacin kasar Kamaru.

A safiyar ranar Juma’a ne wasu mutane ne da ake zaton ‘yan Boko Haram suka yi kutse a garin.

Sai dai bayan jami’an tsaro sun gano su, daya daga cikinsu ya tada bam din da yake dauke da shi.

Hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa da dayan maharin da kuma wani mutum daya.

Akwai karin bayanin da Blama Malla tsohon dan Majalisar dokoki na yankin Mayo-Sava ya yi kan halin da ake ciki a yankin.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Blama Malla yana bayani kan harin

Harin kunar-bakin wake a Kamaru

An kai hari kan barikin jami’an tsaro a Kamaru

A kwanakin baya ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a garin Bargaram.

Messi zai biya tara maimakon zaman gidan yari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An ci dan wasan tarar euro miliyan biyu

Akwai yiwuwar shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi zai kaucewa daurin wata 21 a gidan yari inda ya zabi ya biya tara, kamar yadda rahotanni daga kasar Spain suka bayyana.

Wata kotu ce a Spain ta samu dan wasan da laifin zambar haraji.

Babban mai gabatar da karar kasar zai musanyawa Messi zaman gidan yari zuwa biyan tarar euro 255,000 wato zai biya euro 400 a kowace rana idan da zaman gidan kason zai yi.

Kotunan Spain ne suke da ikon yanke hukuncin karshe game da batun.

Ɗaurin shekara nawa za a yi wa Ronaldo, Messi da Neymar?

An tabbatar da hukuncin daure Messi a gidan yari

Ana zargin Ronaldo da ƙin biyan haraji

An samu Messi da mahaifinsa Jorge da laifin zambar haraji a Spain fiye da euro miliyan hudu tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.

An ci dan wasan tarar euro miliyan biyu, mahaifinsu kuma euro miliyan daya da rabi.

A watan jiya ne kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da Messi ya yi.

Aston Villa tana zawarcin John Terry


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zaman Terry a Chelsea zai kare ne a ranar 30 ga watan Yuni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Aston Villa tana zawarcin tsohon kaftin din Ingila John Terry.

Kodayake an yi nisa a batun cinikin dan wasan bayan, ana saran kammala cinikinsa ne zuwa mako mai zuwa.

Terry, mai shekara 36, zamansa zai kare a Chelsea ne a ranar 30 ga watan Yuni.

Kungiyoyi da dama ne suka bayyana bukatarsu ga dan wasan ciki har da abokiyar hamayyar Aston Villa wato Birmingham.

Dan wasan yanzu yana atisaye ne a kasar Portugal, wadda daga can ne yake wallafa hotunansa a shafukan sada zumunta.

Ciki har da wani hoto wanda ya dauka tare da kocin Aston Villa, Steve Bruce, wanda shi ma yake hutu a kasar Portugal.

Salah ya koma Liverpool a kan fam miliyan 34


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salah ya so ya koma Liverpool a shekarar 2014, amma sai ya koma kulob din Chelsea.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta kammala sayen dan wasan Roma Mohamed Salah a kan fam miliyan 34.

Dan kasar Masar, Salah mai shekara 25 da haihuwa, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da Liverpool.

A shekarar 2014 dan wasan ya so ya koma Liverpool, amma sai ya koma kulob din Chelsea.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana jin dadinsa ga sayen dan wasan.

Ya ce: “Salah yana gogewar da sosai kuma abin farin ciki ne da ya yarda ya kasance tare da mu.”

Salah zai rika sanya rigar mai lamba 11 ne yayin da Roberto Firmino zai koma sanya mai lamba tara.

Salah ya taka muhimmiyar rawa a kakar Serie A ta bara a Roma, inda kungiyar ta kammala gasar a mataki na biyu.

Kuma ya buga wasa 31 ne, ya zura kwallaye 15 a raga.

Nigeria: An tura ƙarin jami'an tsaro jihar Taraba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya yi wani taron gaggawa da Gwamnan Jihar Taraba Darius Dickson Ishaku

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya yi umarnin aikewa da karin jami’an tsaro wasu garuruwa da kauyukan jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.

A farkon makon nan ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin Fulani da ‘yan kabilar Mambila a karamar hukumar Sardauna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

An sanya dokar hana fita a Taraba

Nigeria: ‘Dalilin rikicin Fulani da Tibi a Taraba’

A ranar Alhamis ne mukaddashin shugaban ya yi wani taron gaggawa da Gwamnan Jihar ta Taraba Darius Dickson Ishaku, da kuma manyan hafsoshin tsaron kasar kan yadda rikicin ya ke kara kamari.

Har ila yau, Farfesa Osinbajo ya yi Allah-wadai da masu tada zaune tsaye, inda ya ce za a hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

Mista Osinbajo ya ba da umarnin aika wa da bataliya daya ta sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wuraren da rikicin ya shafa.

'Ya kamata masu kuɗi su biya wa talakawa inshora'


Hakkin mallakar hoto
NHIS

Image caption

Shirin inshorar lafiyar ya ce da ajiyar naira dubu goma sha biyar a shekara, mutum na iya samun kula da lafiya har na kimanin naira miliyan ɗaya.

Majalisar wakilan Nijeriya ta gayyaci hukumar shirin inshorar lafiya na ƙasar NHIS, don yi mata bayani kan ƙarancin ‘yan Nijeriya da suka yi rijista da tsarin.

Nijeriya dai na da yawan al’umma kimanin miliyan 180, amma ƙasa da mutum miliyan uku ne kawai ke da inshorar lafiya.

Babban sakataren tsarin Farfesa Usman Yusuf ya ce kowanne mutum ya cancanci shiga tsarin inshorar lafiya ba sai lallai ma’aikata ba.

Ya ce suna da wani tsari mai suna VCSHIP wanda ta hanyar sanya naira 15,000 a shekara, mutum na iya cin gajiyar samun kulawar lafiya mafi dacewa.

“Yanzu idan ka kacaccala naira dubu goma sha biyar kullu yaumin wato naira arba’in da ɗaya ne.

To dubu goma sha biyar za ka iya zuwa asibiti ka ga likita har aiki a yi maka a dubu goma sha biyar. Ko (naira) miliyan aka caje ka, hukumata za ta biya.”

Farfesa Yusuf ya ce ko da yake, ba kowa ba ne zai iya ajiye wannan kuɗi a shekara ba, amma masu hali na iya biya wa masu ƙaramin ƙarfi.

Ya jama’a, kuna iya biya wa wasu (da ke da ƙaramin ƙarfi), in ji shi.

A cewarsa, ba wata ƙasa a duniya da za a ce gwamnati za ta iya ɗaukar nauyin kowa.

Har masallatai yake zuwa da sauran wuraren ibada don wayar da kan jama’a game da muhimmancin yin tanadi don samun kula da lafiya cikin rangwame.

Ya ce ya shafe tsawon shekaru a Amurka, “kuma ta fi kowa kuɗi a duniya. Ko ita ba ta iya ɗaukar nauyin kowa.”

Ƙasashen yankin Gulf sun nemi a rufe Al Jazeera


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Saudiyya ta rufe kan iyakar ƙasa guda ɗaya rak da Qatar ke da ita

Ƙasashen yankin Gulf da suka katse hulɗa da Qatar a farkon wannan wata sun miƙa mata buƙata 13 da suke son ta cika.

Saudiyya da Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar sun nemi mahukuntan Qatar su rufe gidan talbijin na Al Jazeera.

Sun kuma ce ta rage hulɗa da ƙasar Iraqi sannan ta rufe wani sansanin sojan sama na Turkiyya duk a cikin kwana goma.

Kuwait wadda ke ƙoƙarin shiga tsakanin a rikicin ita ce ta damƙa wa Qatar jerin waɗannan buƙatu.

Haka zalika, ƙasashen na yankin Gulf sun nemi Qatar ta kwance duk wata alaƙa da ƙungiyar ‘Yan’uwa Musulmi.

Ƙasashen dai sun zargi Qatar da samar da kuɗi ga harkokin ta’addanci, zargin da ƙasar ta musanta.

A farkon wannan mako ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce mamaki ya dabaibaye ta kan yadda ƙasashen ba su fitar da ƙarin bayani kan ƙorafe-ƙorafensu ba.

Ya matan da aka mutu aka bari ke rayuwa a Nigeria?


Image caption

Har yanzu akwai matan da rikicin Boko Haram ya raba da mazajensu na da yawa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri

Wasu alƙaluma na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa matan da mazansu suka mutu a duniya, sun kai kimanin miliyan 245 kuma miliyan 115 a cikinsu suna fama da matsanancin talauci.

Nijeriya mai yawan jama’a kimanin miliyan 180 na da gagarumin kaso na irin waɗannan zawarawa.

Majalisar Duniya dai ta keɓe duk ranar 23 ga watan Yunin kowacce shekara, don tunawa da halin da matan da suka rasa mazajensu ciki da kuma bukatar tallafa musu.

A wasu lokuta, akan bar matan da mazansu suka mutu da ɗawainiyar ‘ya’yan da aka bar musu.

Abin da ke sa wasunsu cikin mawuyacin hali da ƙasƙanci ciki har da yawon bara don tsira da rai.

Wata mace da BBC ta zanta da ita a wani masallaci cikin birnin Abuja, yayin karɓar sadakar abinci ta ce tun bayan rasuwar maigidanta wanda ya bar mata ɗa shida, abincin da za su ci ma yake gagara.

Ta ce daga jihar Katsina suka zo birnin tarayyar, don neman abin da za ta ciyar da kanta da ‘ya’yanta.

“Shi ya sa yanzu ko, muka zo wurin karɓar abinci, saboda ba mu da abin da za mu ba yaran.”

A cewar uwar marayun, yaran ba sa zuwa makaranta, don kuwa ba ta da halin ciyar da su ma balle a yi batun karatu.

Ta ce tana da burin ‘ya’yanta duka su yi karatu, amma a cikinsu, ɗaya ce kawai ke zuwa makaranta.

“Ɗawainiya kam, sai dai Allah ke taya ni amma ni ke neman abin da za su ci su sha.”

Nijeriya dai ƙasa ce mai tasowa, don haka ake samun iyalai ko gidaje masu yawan zuri’a.

Baya ga irin waɗannan mata da mazansu suka mutu suka bari a wasu yankunan Nijeriya, a yankin arewa maso gabas kuwa ɗumbin wasu ne rikicin Boko Haram ya mai da zawarawa.

Irin waɗannan mata da ‘ya’yansu musammam a Maiduguri, na cikin halin tagayyara sakamakon raba su da mazan da suka dogara da su donn rayuwa.

Akasarin matan ba su da aikin yi, ko wata sana’a, lamarin da ke sa wasu yin bara don neman abin da za su ci.

A kwai ma wasu dubban irin wadannan mata da ‘yan tada-ƙayar-baya suka kashe mazajensu da ke samun mafaka a gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki, wasu kuma a gidajensu na gado.

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sanchez ya ci Jamus kwallon da ta sa ya zama wanda ya fi ci wa Chile kwallo a tarihi – guda 38

Jamus da chile su ka tashi kunnen doki 1-1 a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan.

Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez shi ne ya ci wa Chile kwallonta minti shida da fara wasa bayan da Arturo Vidal na Bayern Munich, ya zura masa kwallo.

Wasa ya yi nisa saura minti hudu a tafi hutun rabin lokaci sai Lars Stindl na kungiyar Borussia Mönchengladbach ya rama wa Jamus.

Sakamakon ya sa Chile ta zama ta daya a rukunin na biyu da maki 4 da kwallo biyu, sai Jamus ta biyu ita ma da maki 4 amma da yawan kwallo biyu.

Australia tana matsayi na uku da maki daya da bashin kwallo daya a ragarta, yayin da Kamaru take ta hudu (karshe) da maki daya, da kuma bashin kwallo biyu.

A ranar Lahadi kasashen za su yi wasansu na rukuni na karshe, inda Kamaru za ta hadu da Jamus sai Chile ta fafata da Australia.

Kafin sannan a ranar Asabar za a yi wasan karshe na rukuni na daya (Group A), lokacin da Rasha mai masaukin baki za ta kara da Mexico, New Zealand kuwa ta hadu da Portugal.