Yadda fasto ya kare Musulmi 2000 a cocinsa


Wata motar rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar hari daga kungiyar gwagwarmayar Kristoci ta anti-Balaka.

Fasto Juan José Aguirre Munoz ya ce Musulmin ‘yan gudun hijiran ba za su bar harabar cocinsa ba a birnin Bangassou da ke kudu-maso-gabashin kasar, sai bayan ya samu tabbaci kan tsaron rayukansu.

Ya ce Musulmin da ya ba mafaka suna “fuskantar barazanar kisa” ne daga wurin mambobin kungiyar anti-Balaka.

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya Stephen O’Brien ya yi gargadin cewa akwai alamun aikata kisan kare dangi a makon jiya.

Ya ce rikicin kasar yana kara ta’azzara kuma al’amarin yana kara muni.

“Tashin hankalin yana karuwa, ana tsoron kada a kara maimaita mummunan rikicin da ya faru a kasar kimanin shekara hudu da suka wuce,” in ji shi.

Mista O’Brien ya kara da cewa: “Akwai alamomin da ke nuna yiwuwar faruwar kisan kiyashi don haka wajibi ne a dauki mataki.”

Mene ne hukuncin daukar hoto a wuraren Ibadah?


Selfie HajjHakkin mallakar hoto
AHMAD GHARABLI

Image caption

Mahajjata sukan dauki hotuna a lokacin ibada musamman a kasar Saudiyya

Daukar hoton a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su gani su kuma yi tsokaci ko magana ko kuma yayata hoton.

Ba sabon abu ba ne mutun ya dauki hoto a masallacin idi ko na harami a Makka ko Madina ko kuma a filin Arfa.

Bugu da kari wasu na daukar hotuna na bidiyo a lokacin dawafi ko kuma lokacin hawa Arfa kuma su wallafa a shafukan sada zumunta na zamani.

Wata kila wasu na yin hakan ne domin su nuna wa duniya cewa sun samu zuwa wannan waje, yayin da wasu kuma suna son su nuna wa wadanda suke gida yadda wurin ibadar yake ne.

To amma wani lokacin hakan ba ya rasa nasaba da aikin riya da Musulunci ya hana.

Hakkin mallakar hoto
AHMAD GHARABLI

Image caption

Daukar hoto domin wallafawa a shafukan sada zumunta batu ne da mutane suka saba da shi a shafukan sada zumunta

Irin wannan dabi’ar ta samo asali ne tun zamanin da, inda mahajjata ke dawowa gida da kallo-kallo daga aikin hajji inda yara da sauran mutane da ba su samu zuwa aikin hajji ba za su samu ganin wuraren aikin hajji ta hotunan da ke cikin kallo-kallon.

Riya ce?

Wasu na tunanin cewar daukar hoto a irin wadannan wuraren ibadan son a-sani ne, wato riya ce. Amman mene ne hukuncin irin wannan dabi’ar a Musulunci?

Ustaz Hussaini Zakariya, ya ce, “Maganar daukar hoto idan aka je Harami ko Madina, malamai sun rabu gida biyu kan wannan batu.”

“Daya mai tsanani kwarai da gaske, shi yana ganin cewa hoton ma haramun ne a ko ina aka yi, ba sai lallai cikin Harami ba, kuma yi a cikin Haramin ma ya fi muni.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mahajjata sukan dauki hotuna a lokacin ibada a kasar Saudiyya

“Amma akwai wadanda suke ganin cewa daukar hoto ba aikin ibada ba ne. Ba wanda zai dauki hoto ya ce ya yi sunnah ko mustahabi ko kuma ya yi farilla.”

Malamin ya kara da cewa: “Don haka ba aikin ibada ba ne balle a ce in ka yi jama’a sun gani, aikinka ya baci. Don haka yana ganin cewa halal ne matukar dai mutum ba wai ya yi wannan abin don jama’a su ga cewa yana wajen wata ibada kuma burinsa ya cika ba ne.”

“Ya kwadaita wa wadanda Allah bai ba su ma su roki Allah Ya kai su wannan wurin, kuma ya sanar da danginsa da abokansa cewa ga shi Allah Ya kawo shi wurin da duk Musulmi yake son ya zo.”

“Ina ganin wani abu ne na raba abin farin cikin da ya samu mutum da ‘yan uwansa da abokansa.”

Saboda haka Ustaz Zakariya ya ce yana ganin wannan ba aikin addini ba ne kuma ba riya ba ce.

Ga yadda amsar Malam Haussaini Zakariya ta kasance:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Mene ne hukuncin daukar hoto a masallatai tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta?

Shi kuma Dokta Abdulkadir Sulaiman na Sashen koyar da addinin Musulunci a jami’ar Abuja cewa ya yi daukar hoto kansa ba ya halarta.

Amma batun ko daukar hoto tare da wallafashi a shafukan sada zumunta zai iya janyo riya, ya ce wannan wani lamari ne mai sarkakiya.

Malamin ya yi bayanai tare da kawo hadisai da ke nuna cewa yanke hukuncin riya ba hurumin dan Adam ba ne domin wannan al’amari ne da ke zuciyar dan Adam, kuma Allah (SWT) ne kawai zai iya sanin abin da yake zuciyar bawansa.

Ga yadda amsar Dokta Abdulakadir Sulaiman ta kasance kan mas’alar:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Akwai riya a daukar hoto a masalatai tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta?

Hakkin mallakar hoto
MOHAMMED AL-SHAIKH

Image caption

Ana daukar hoton dauki-kanka har ma a filin Arfa

Takaddamar cinikin ranar karshe da aka yi a Premier


ChelseaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Torres ne dan kwallon da aka saya mafi tsada a duniya a 2011

A ranar Alhamis 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa ta Turai ta bana, wacce za a sake budewa a watan Janairun 2018.

Ana bude kasuwar ce domin bai wa kungiyoyin Turai damar daura damarar tunkarar kalubalen tamaula a sabuwar kaka.

Ga jerin cinikin ranar rufe kasuwar da aka yi takaddama a Premier:

Benjani

Dan wasan tawagar Zimbabwe, Benjani ya makara zuwa Etihad domin ya saka hannu kan yarjejeniyar komawa Manchester City, bayan da bacci ya kwashe shi a filin saukar jirgin sama na Southampton a Janairun 2008.

Makarar da dan wasan ya yi ya kusan sa a soke yarjejeniyar da aka kulla tun farko, daga baya aka warware matsalar bayan da aka kammala sa hannu a dukkan takardun da suka dace a kan kari.

Benjani ya fara buga wasa a City da kafar dama inda ya ci Manchester United a wasan hamayya da suka kara.

Daga baya dan kwallon ya kasa yin komai, hakan ya sa ya bar Etihad a shekarar 2010 bayan da ci kwallo biyar.

Yossi Benayoun da Mikel Arteta

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bayan da Arsenal ta sayar da Cesc Fabregas da kuma Samir Nasri ta samu kudi fam miliyan 60 a shekarar 2011, daga nan ne Arsene Wenger ya dunga jan lokaci kafin ya sayo wadanda za su maye gurbinsu.

Sai a ranar da za a rufe kasuwa ne Wenger ya sayo Benayoun da kuma Arteta, ya kuma sayo Arteka kan fam miliyan 10, inda ya yi shekara biyar a Gunners, shi kuwa Benayoun Chelsea ya koma wasa aro daga baya ba ta sayi dan kwallon ba.

Peter Odemwingie

Dan wasan Najeriya, Peter Odemwingie ya dauki hukunci a hannunsa a wani abu kamar almara da bai taba faruwa ba a Ingila, inda ya so komawa QPR daga West Brom da karfin tsiya a Janairun 2013.

Odemwingie ya tuka motarsa zuwa QPR daga West Brom, amma aka ce ya koma inda ya fito, saboda kungiyoyin biyu ba su kulla yarjejeniya ba, kuma tun da ya koma West Brom ba ta kara saka shi a wasa ba.

Rafael van der Vaart

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kocin Tottenham, Harry Redknapp ya matsu ya dauki Rafael van der Vaart daga Real Madrid a shekarar 2010.

Sai dai rashin kammala sa hannu kan yarjejeniya ya kusan hana dan kwallon komawa Ingila da murza-leda, amma daga baya mahukuntan Premier suka amince da cinikin bayan da aka rufe kasuwa.

Van der Vaart ya yi kaka biyu a White Hart Lane, inda ya ci kwallo 23.

Fernando Torres da Andy Carroll

Bayan da Liverpool ta amince ta sayar wa da Chelsea Fernando Torres kan fam miliyan 50 a ranar 31 ga watan Agustan 2011, Liverpool kuma a lokacin ta sayi Andy Carroll kan fam miliyan 35 daga Newcastle United.

An yi ta mamakin dalilin da ya sa Liverpool ta sayi Carroll kan kudi mai yawa haka, daga baya ‘yan wasan biyu suka kasa taka rawar gani a kungiyoyin da suka koma.

A kuma shekarar ce Luis Suarez ya ci kwallo 69 a yarjejeniyar shekara uku da rabi a Anfield, amma ta sayar da shi ga Barcelona a kudi mai tsoka.

David De Gea

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea ya kusan komawa Real Madrid a ranar da za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a 2015.

Tuni United da Madrid suka amince da kudin da ya kusan kai fam miliyan 30, sai dai kungiyoyin biyu sun kasa cike takaddun ka’ida da ya kamata dan kwallon ya koma Spaniya da taka-leda, hakan ya sa suka hakura da cinikin De Gea.

Andrey Arshavin

A lokacin da za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan Turai a karshen Janairun 2009 ne Arsenal ta sayi Andrey Arshavin daga Zenit St Petersburg kan kudi mai tsada da ya kai fam miliyan 15.

An samu tsaiko wajen cimma yarjejeniyar kudin dan wasan, inda sai washe gari ne Arsenal ta fadi kudin da ta dauki dan kwallon.

Mahukuntan Premier sai da suka yi bincike ko Arsenal ta karya ka’idar sayen dan wasan, daga baya aka wanke ta.

Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya


MahajjataHakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu alhazan Najeriya bakwai sun mutu a Saudiyya gabanin a fara aikin Hajji.Alhazan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna.

Sannan wata Hajiya daga Jihar Kogi ta Haihu a Madina. Shugaban NAHCON Abdullahi Mukhtar, ya ce za a hukunta jihar da matar ta fito ta hanyar rage mata kujeru a badi, da kuma hukunta shugabannin hukumar aikin hajji ta jihar

Alhazan Nigeria Kusan dabu 90 ne ke halartar aikin hajjin bana.

Tottenham ta sayi Serge Aurier daga PSG


Serge AurierHakkin mallakar hoto
Getty Images

Tottenham ta kammala sayen dan wasan baya na Paris St-Germain Serge Aurier kan fam miliyan 23.

Dan kwallon na Ivory Coast, mai shekara 24, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar har zuwa 2022.

Batun samun izinin aiki ne ya kawo tsaiko a cinikin saboda hukuncin daurin je-ka-ka-gyra-halinka da aka yanke masa saboda cin zarafin dan sanda a bara.

“Wannan kamar wata sabuwar rayuwa ce a gare ni. A shirye nake na nuna kwarewa a ciki da wajen filin kwallo,” a cewar Aurier.

“Magoya baya sun ne mafiya muhimmanci a kowanne kulob kuma a shirye nake na nuna musu cikakken Serge Aurier.”

Aurier shi ne na hudu da Spurs ta saya a bana, bayan mai tsaron gida Paulo Gazzaniga da Juan Foyth da Davinson Sanchez.

Boko Haram: Birtaniya ta rage agajin da take bai wa Nigeria


Priti PatelHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Priti Patel ita ce mai kula da tallafin da Birtaniya ke bai wa kasashen waje

Birtaniya za ta rage yawan kuɗaden da take bai wa Najeriya a matsayin agaji domin ayyukan jin kai nan da ‘yan shekaru masu zuwa.

A shekarar 2016 Birtaniya ta kashe fam miliyan 100 wurin tallafawa ayyukan jin kai a Najeriya.

Amma a cikin shekara hudu masu zuwa ta yi alkawarin fam miliyan 200 kadai. Fam miliyan 50 ke nan a kowace shekara.

Ana san ran za a yi amfani da kuɗaden wurin tallafawa wadanda hare-haren Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin kasar.

A wata ziyarar kwanaki biyu da Sakataren Harkokin ci gaban kasashen waje ta kasar, Priti Patel ta kai Najeriya, ta nemi hukumomin kasar su kara daukar matakai na yakar masu tsattsauran ra’ayi.

Ta kara da cewa kamata ya yi wasu ƙasashe waje su taimaka wajen ba da tallafi.

Hare-haren kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar raba mutum miliyan 1.5 daga muhallansu.

Hakan kuma ya shafi harkar noma a kasar wanda ke haifar da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Nigeria: Ethiopian Airlines na son karfe iko da Arik Air


Ethiopian AirlinesHakkin mallakar hoto
AFP

Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines na tattaunawa domin duba yiwuwar karbe ragamar gudanar da kamfanin Arik Air na Najeriya wanda ke fama da matsaloli.

Gwamnatin Nigeria ta karbe ragamar gudanar da kamfanin a farkon bana bayan da ya sanar da yin gagarumar asara.

Wani babban jami’i a kamfanin Esayas Woldemariam, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa tattaunawar ta biyo bayan bukatar hakan ne da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta Najeriya ta yi masa.

“Hakika muna so kuma a shirye mu ke mu karbi ragamar gudanar da Arik Air,” a cewarsa.

Ethiopian Airlines shi ne kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi samun riba a nahiyar Afrika, a cewar jaridar Business Daily.

Yadda yawan ciwon kai ke jawo mantuwa da rudin kwakwalwa


Lamarin ya auku ne ga Paul lokacin hutun zafiHakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Lamarin ya auku ne ga Paul lokacin hutun zafi

Shekara biyu da ta wuce, Paul Bolding mai shekara 63 ya yi hutu a Croatia, inda ya ziyarci gabar kogi a wani karamin tsibiri tare da matarsa Kirsty.

Sai suka yanke wa kansu yin ninkaya da bututun shakar iska, inda suka rika yin juyi, wannan ya shiga wannan ya fita ya kula musu da kayansu.

Paul ya yi kurme sai barci ya kwashe shi a kan tabarmar gabar teku da ke shimfide kan kananan duwatsu na wani lokaci. Da farkawarsa bai san inda yake ba, ko ya aka yi ya iso wurin.

Babu mamakin jin cewa Paul ya firgita. Matarsa ta kai shi inuwa, inda ta zaku da ganin cewa ta kwantar masa da hankali ya samu natsuwa don warware matsalar da ke tattare da shi.

Ta bayyana mini a wani shirin rediyo mai taken daukacin al’amuran tunani (All in the Mind) cewa, ta gano cewa bai zai iya tuna komai ba, domin tambayoyi iri guda yake ta yi.: Kina jin zafi ne ya baibaye ni? Kina jin cewa na yi barci a rana ne?” Al’amarin da ya yi ta faruwa kenan fiye da sau 20.

Ya kasa tuna al’amuran da suka faru kwana 10 da suka yi na hutunsu.

Kirsty na ta kai-kawo a tunani cike da dar-dar jin cewa ko ya kamu da cutar mantuwa. Taraddadin cewa ko za ta shafe tsawon rayuwa tana kula da shi, sai ta dawo da shi garin da suke zaune, cike da fatan ganin al’amuran da ya saba da su ko za su dawo masa da tunaninsa.

Ita ta rika karbo masa abincin rana domin bai ma san abin da yake so ba. Ya kasa tunani kwana 10 da suka gabata na hutunsu, duk da cewa wasu al’amuran sun shaf ganawa da wasu ‘yan uwa a karo na farko.

Can tsakar rana sai ya fara warwarewa, al’amarin da ke nuni da cewa ya shirya yin tattakin da suka tattauna yinsa kafin wannan rana, wato dai ya fara tuna al’amura. Cikin sa’a guda ya dawo garas yadda yake – komai ya yi daidai ba ya ga mantuwar sa’a shidan da ya yi, al’amuran da har zuwa yau ba su dawo ba.

Da komawarsa gida Birtaniya sai ya ziyarci likitansa, wanda ya fada masa cewa ya ratsa bagiren duniyar mantuwa, wani lamari da ya saba shafar mutanen da shekarunsu suka dara 50 (kamar Paul).

Sashen kula da hadurra da kulawar gaugawa a asibiti na ganin mutum biyu zuwa uku wadanda suka auka cikin matsalar a ko wanne wata.

Lokacin aukuwar lamarin, mutane na sane da yadda ake tuki da tafiya, amma a matsala irin ta Paul ba za su iya tuna abubuwan da suka kasance suna yi a kwanakin da suka gabata ba.

Yawan maimaita tambayar wasu, kamar yadda Paul ya yi a gabar teku, nan ne jigon warware matsalar.

Sashen kula da hadurra da kulawar gaugawa a asibiti na ganin mutum biyu zuwa uku wadanda suka auka cikin matsalar a ko wanne wata.

Har yanzu musababbin matsalar bai bayyana ba.

Da farko likitoci na tsammanin irin wannan farmakin alama ce ta farfadiya ko rabin ciwon kai, ko ta yiwu an dan samu sandarewar gabban jiki.

A halin yanzu an tabbatar lamarin ba shi da alaka da sauran matsalolin rashin lafiya.

An yi hasshen cewa dunkulen sashen kwakwalwa da ke sarrafa tunani ne ke da alhakin tattara bayanai na tsawon lokaci, don haka ake ganin shi ne jigon shawo kan matsalar.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Illar matsalar na iya yin muni har ta kai ga mutane sun manta da kansu

Adam Zeman, Farfesan massarafar tunani da matsalolin kwakwalwa a Makarantar horar da Likitoci a Jami’ar Exeter ya yi nunmi da cewa: “abin da ake tsammanin yana faruwa shi ne masarrafar tunani (hippocampi) ke kullewa na wucin gadi.

Abin da ya faru ga Paul fitacce ne. Za ka manta abin da ya faru makonni da suka wuce, kuma ba za ka iya tuna sababbin al’amura lokacin da matsalar ke ci gaba ba.

Nazarin hoton kwakwalwa ya inganta wannan mahangar, inda aka gano matsalolin wucin gadi tattare da masarrafar tunani yayin aukuwar matsalar.

Mutanen da suka saba fama da yawan ciwon kai su suka fi yawan fama da matsalar.

Da ka bibiyi kadin al’amuran daidaikun mata 142, wadanda suka ratsa bagiren duniyar mantuwa, likitocin Faransa sun gano cewa, irin wadanan matsalolin dugunzumar damuwa ke haifar da su, al’amuran da suka hada da takaddamar muhawara, yayin da maza kuwa sun fi samun nasu ne lokacin da suke fama da matsin lamba ko nutso a ruwan sanyi.

Mutanen da suka saba fama da yawan ciwon kai su suka fi yawan fama da matsalar.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Cutar na nufin mutane na iya mantuwar sa’o’i ko kwanakin rayuwarsu har abada

Akai-akai, mutanen da ke fama da matsalar na da bambancin yanayin da ake kira ratsa bagiren farfadiyar mantuwa, wanda ake dauka cewa shi ne ratsa bagiren duniyar mantuwa, amma irin wannan farfadiyar.

Lamura ne na wucin gadi da ke faruwa akai-akai, da zarar an tayar da mutum daga barci.

Zeman ya ce a mafi yawan lokuta warware matsalar cutar na da sauki: “Idan ka ga wani bayan aukuwar lamarin, kuma suka bayar da bayani irin na Paul, to babu tababa a ciki.

“Idan ka hadu da su a tsakiyar aukuwar lamarin, to sha’anin na da matukar wahala, don haka sai ka yi tunanin farmakin wasu matsalolin da suka hada da sandarewa ko shanyewar gabobin jiki da farfadiya ko rudanin mantuwa.”

Babban bambancin da ke tattare da rudanin mantuwa shi ne majiyyatan ba sa iya tuna kansu, amma za su iya tuna sababbin al’amura.

Kyakkyawan batu game da matsalar ratsa bagiren duniyar mantuwa shi ne, lamari ne da ke faruwa a rudanin kwatsam ba tare da nuna alamar wasu cutttuka ba.

Sai dai kaso kadan ne daga cikin wadanda suka yi fama da yanayin za su sake kwata makamancinsa. Amma idan ya faru gareka, tabbas zai iya zama lamari mai tsananin firgitarwa.

Paul ya yi fatan ka da lamarin ya sake aukuwa har abada. Sai dai idan ya auku, to Kirsty na da masaniya kan ko mene ne.

''Yan siyasa ne kawai ke jin dadin Nigeria'


Wani masanin tattalin arziki na tambayar ko ‘yan siyasar Najeriya na ganin abun da ‘yan kasar ba sa gani ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya gamsu da tattalin arzikin kasar.

President Muhammadu Buhari meets with Finance Minister Kemi Adeosun and othersHakkin mallakar hoto
Nigerian Presidency

Image caption

Mutane ba su san abun da Shugaba Buhari da ministocin da ke kula da tattalin arzikin kasar ke gani ba

Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya murna da yadda tattalin arzikin Najeriya ke habaka, wani masanin tattalin arziki a kasar ya ce shi bai ga abin da shugaban ya gani ba da ya sa ya furta kalaman ba.

“Mutane a Najeriya ba sa jin dadin tattalin arzikin kasar. Idan aka samu wani wanda ya gamsu da tattalin arzikin kasar, to dan siyasa ne,” in ji farfesa kan tattalin arziki da harkar kudi, Ayodele Momodu, a hirarsa da BBC.

Shugaban Najeriyar ya ce shi ya gamsu da yadda tattalin arzikin kasar ke habaka ne bayan ya gana da ministar kudin kasar, Misis Kemi Adeosun, tare da ministan kasafin kudi da na tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ranar Litinin.

Ita ce ganawar farko da ya yi da wadansu manyan mukarraba gwamnatin da ke kula da tattalin arzikin kasar bayan dawowarsa daga jinyar kwana 104 a Landan kan rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

A ganawar ministocin da gwamnan babban bankin Najeriya sun shaida wa shugaban kasar cewar tattalin azrikin kasar na habaka.

Amman kalaman shugaban kasar bayan ganawar sun bata wa wannan farfesan rai, lamarin da ya sa yake tamabayar cewa ko sun ga abun da ‘yan Najeriya da kwararru ke gani.

Ga sautin hirar da BBC ta yi da wani masanin tattalin arziki na tambayar ko ‘yan siyasar Najeriya na ganin abun da ‘yan kasar ba sa gani ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya gamsu da tattalin arzikin kasar.

Sai a latsa domin a jin yadda hirar ta kasance.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da masanin tattalin arzikin Najeriya

Buhari ya tafi bikin Sallah a Daura


Gwamnatin Buhari ta gurfanar da mutane da dama a gaban kuliyaHakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

Gwamnatin Buhari ta gurfanar da mutane da dama a gaban kuliya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina ta arewacin kasar domin yin bikin babbar Sallah.

Hotunan da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta sun nuna manyan jami’an gwamnati da Sarakuna suna tarbar shugaban kasar.

Cikin wadanda suka tarbe shi har da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da sarakunan Katsina da Daura.

A ranar 19 ga watan nan ne Shugaba Buhari ya koma Najeriya, bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a birnin London.

Hakkin mallakar hoto
Nigeria presidency

Image caption

Shugaba Buhari ya sha alwashin yaki da masu cin hanci

Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

‘Yan Najeriya da dama sun yi addu’a ga Shugaba Buhari lokacin da ba shi da lafiya

EFCC na shirin taso keyar Diezani Allison-Madueke


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku saurari hirarmu da Ibrahim Magu

Shugaban riko na hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ya ce nan ba da dadewa za su sa gwamnatin Birtaniya ta tiso keyar tsohuwar ministar mai Diezani Allison Madueke.

Ibrahim Magu ya shaida wa BBC cewa “Muna nan muna kokarin ganin an taso keyarta domin ta zo nan”.

Ya kara da cewa a wannan shekarar kadai, EFCC ta yi nasarar kwato kimanin Naira Biliyan 409 da kuma Dala Miliyan 69 daga hannun mutane daban-daban da ake zargi da sace kudaden gwamnatin a wannan shekarar.

A cewarsa, an gurfanar da mutanen a gaban kuliya, yana mai cewa EFCC ta samu nasara kan kararraki 137 a shekarar 2017.

Mr Magu ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da ministan shari’ar Abubakar Malami, yana mai cewa “wannan labarin sharrin ‘yan jarida ne kawai. Amma buri daya muke son cimmawa”.

Shugaban na EFCC ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da ba shi hadin kai a yakin da hukumar ke yi da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati.

Dattawan United za su kara da na Barcelona


LegendsHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United ce za ta karbi bakuncin Barcelona a Old Trafford

Dattawan Manchester United za su karbi bakuncin na Barcelona a wasan sada zumunta domin tuna wadan da suka mutu a harin ta’addacin da aka kai biranensu.

Tsoffin ‘yan wasan da za su buga wa United karawar sun hada da Edwin van der Sar da Ruud van Nistelrooy da Ji-sung Park da kuma Wes Brown.

Ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Old Trafford da Edgar Davids da Patrick Kluivert da Gaizka Mendieta da kuma Eric Abidal.

Dattawan za su daura bakin kyalle a hannunsu da kuma sunan biranensu a bayan rigunan da kowa zai saka a fafatawar da za su yi a ranar Asabar a Old Trafford.

A cikin watan Mayu ne aka kai harin ta’addanci a birnin Manchester daga baya aka kai hari a birnin Barcelona da na Cambrils a farkon watan nan.

Aikin shekara nawa za ku yi kafin ka samu albashin dan kwallo?


Kasuwar musayar ‘yan kwallo na nufin irin makudan kudin da ake kashewa a ciniki a kasuwar. Cinikin Neymar da aka yi kan kudi fam miliyan 198 daga Barcelona zuwa PSG na nufin dan wasan zai dinga samun kudi fam 775,477 duk mako. Nawa ne albashinka idan aka kwatanta da na wani babban dan kwallo? Yi amfani da kwakuletarmu don gano hakan.

Manhajarka ba za ta iya bude wannan abin ba

Masu kungiyoyin kwallon kafa a Turai har yanzu suna da sauran lokacin kashe kudade masu yawa kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara a ranar Alhamis da daddare. Yawan kudin da aka kashe a Gasar Premier a bana tuni ya zarce na bara inda aka kashe fam biliyan 1.165.

A shekarar 2001 lokacin da Sol Campbell ya bar Tottenham zuwa Arsenal, albashinsa a mako ya kai fam 100,000, wanda hakan ya sa ya zama dan kwallo na farko a Birtaniya da yake karbar albashin dubu daruruwa. Shekara 16 bayan nan sai Sergio Aguero na Manchester City da Paul Pogba na Manchester United su ma suka fara karbar albashin fam 200,000 a mako.

Matsakaicin albashin da aka biya ‘yan wasan Premier a kakar wasan bara shi ne fam miliyan 2.4, a cewar wani rahoto na jaridar da ake wallafawa a intanet ta Sporting Intelligence. Wannan ya yi daidai da fam 46,000 duk mako, wanda ya fi abin da matsaikacin ma’aikacin gwamnati ke dauka duk shekara a Birtaniya.

Hanyar bincike: Sashen Wasanni na BBC ne ya bayar da rahoton adadin kudin da ‘yan wasa ke samu wanda aka yi amfani da shi a wannan bincike. Adadin yana nuna yawan kudin ne kafin a cire haraji, kuma bai hada da abin da dan wasa ke samu daga tallace-tallace ba. Kungiyar Kwadago Ta Duniya ILO, ce ta samar da kididdigar matsakaicin albashin kasa-kasa da na duniya baki daya. Bayanan ILO ya lissafa abin da masu albashi kawai ke samu ne, ba abin da masu aiki na kashin kansu ke samu ba. Domin kwatanta albashin da sauran kasashe, wannan kwakuleta na sassauya adadin ta hanyar amfani da musayar kudi da Bankin Duniya ya samar. An samu bayanan rigunan ‘yan kwallo ne daga shafinsu na intanet a watan Agustan 2017.

Wadanda suka shirya: Nassos Stylianou, Nathan Mercer, Paul Fletcher, Chris Osborne da kuma John Stanton. Wanda ya yi taswirar ‘yan wasan Zoe Bartholomew da Laura Cantadori. Wadanda suka tsara Laura Cantadori da James Offer. Wadanda suka inganta Aidan Fewster, Rosie Gollancz da kuma Becky Rush.

Yaushe rabon Buhari da yin taron ministoci?


Buhari a taron ministociHakkin mallakar hoto
Novo Isioro

A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar ministoci na farko cikin bayan tafiyarsa jinya Birtaniya, wata uku da suka gabata.

Mai magana da yawun shugaba Buhari kan yada labarai Femi Adesina ne ya wallafa shigar shugaban taron a shafinsa na Twitter.

A zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban ya karbi bakuncin kungiyar kwallon kwando ta mata ta kasar, D’Tigress.

Shugaban ya koma Najeriyar ne daga Birtaniya a ranar 19 ga watan Agusta, inda ya shafe kwana 104 yana jinya.

A lokacin da baya nan Mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ne ya dinga tafiyar da al’amuran gwamnati, yake kuma jagorantar taron majalisar ministocin.

A wancan makon ne Shugaba Buharin ya soke taron, wanda aka sa ran shi ne na farko da zai jagoranta bayan dawowarsa daga jinyar.

Sai dai a ranar ce shugaban ya karbi rahoton binciken da ake yi wa sakataren gwamnatin kasar da aka dakatar kan zargin cin hanci Babachir Lawal, da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar Ayo Oke.

Ana sa ran taron na ranar Laraba zai tattauna kan batun yajin aikin da Malaman Jami’a ke yi.

Hakkin mallakar hoto
Novo Isioro

Image caption

Buhari ya gana da tawagar kwallon kwando ta mata kan nasarar da suka yi

Hakkin mallakar hoto
Novo Isioro

World Cup 2018: Nigeria za ta kara da Kamaru


Super EaglesHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nigeria ce ke mataki na daya a rukuni na biyu da maki shida

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta karbi bakuncin ta Kamaru a ranar Juma’a a wasan shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci.

Super Eagles za ta buga wasan ne ranar 1 ga watan Satumba a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.

Kwanki uku tsakani ne Super Eagles za ta ziyarci Kamaru a wasa na biyu da za su fafata a Yaounde.

Super Eagles ce ta daya a rukuni na biyu da maki shida bayan da ta yi nasara a kan Zambia da Algeria, Kamaru ce ta biyu da maki biyu wacce ta yi kunnen doki da Algeria ta tashi babu ci da Zambia.

Kocin Kamaru, Hugo Bross ya ce idan har ba su samu maki hudu ba a kan Nigeria a fafatawar da za su yi gida da waje zai yi wahala su halarci Rasha a badi.

Ga wasannin da za a buga a karshen mako:

 • Alhamis: Litinin:
 • Uganda v Egypt (Grp E)Cameroon v Nigeria (Grp B)
 • Guinea v Libya (Grp A)Libya v Guinea (Grp A in Tunisia)
 • Juma’a: Talata:
 • Ghana v Congo (Grp E)Congo v Ghana (Grp E)
 • Nigeria v Cameroon (Grp B)South Africa v Cape Verde (Grp D)
 • Cape Verde v South Africa (Grp D) Ivory Coast v Gabon (Grp C)
 • Morocco v Mali (Grp C)DR Congo v Tunisia (Grp A)
 • Tunisia v DR Congo (Grp A)Burkina Faso v Senegal (Grp D)
 • Asabar:Egypt v Uganda (Grp E)
 • Zambia v Algeria (Grp B)Mali v Morocco (Grp C)
 • Gabon v Ivory Coast (Grp C)Algeria v Zambia (Grp B)
 • Senegal v Burkina Faso (Grp D)

Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu


Inside traditional healer's house

Image caption

Police found several human body parts during a raid in a traditional healer’s house

An tsinci gawar wata matashiya da ta fara rubewa mako guda bayan da wani mai maganin gargajiya ya mika kansa ga ‘yan sanda ya ce ya gaji da cin naman dan adam.

Mutanen yankin KwaZulu na cike da fargaba bayan da aka gano gawar Zanele Hlatshwayo mai shekara 25, an ciccire wasu sassan jikinta, a kuayen Shayamoya a Afirka Ta Kudu.

Iyayen yarinyar wacce ta bata tun a watan Yuli, sun yi amannar cewa tana daga cikin wadanda masu cin naman mutane ne suka kashe, inda tuni aka kama biyar daga cikinsu.

Da farko dai ‘yan sanda sun ki saurarar batun mutumin da ya mika musu kan nasa, amma sai suka yarda da abin da yake fada a lokacin da suka ga jini dumu-dumu a hannayensa da kafafuwansa, suka kuma kama shi.

Mutumin ya kai ‘yan sandan gidansa, inda aka samu kunnen mutum har takwas a cikin tukunya.

An yi amannar cewa ya yi niyyar sayarwa abokan huldarsa ne, wadanda aka shaida wa cewar suna da sirri na taimakawa mutum ya yi kudi ko ya samu mulki.

An kuma samu wasu sassan jikin da dama a wani akwati.

Image caption

An tsinci gawar Zanele Hlatshwayo a cikin duwatsu

An samu tufafin Ms Hlatshwayo da jini kaca-kaca a jiki a dakin mai maganin gargajiyar da aka samu sassan jikin mutanen.

Iyayenta ne suka gane tufafin nata.

Haka kuma, ‘yan sansa na jiran sakamakon gwaje-gwajen kwayoyin halitta domin a tabbatar ko daga cikin sassan jikin mutanen akwai na wata mata mahaifiyar wani yaro dan shekara biyu.

Har yanzu iyayen Ms Hlatshwayo ba su binne ta ba. A yayin da na shiga gidansu Hlatshwayo, ba abin da nake ji sai koke-koken ‘yan uwanta.

Babbar yayarta Nozipho Ntelele, ta ce min a lokacin da take share hawaye, “Muna jin ciwon salon da aka bi aka kasheta, an mata kisan wulakanci.”

Image caption

‘Yan uwan Hlatshwayo suna zaman makoki

Ta kara da cewa, “Duk tufafinta ya yi duku-duku da dattin kasa, alamar ta sha artabu wajen ganin ta ceci ranta,” “in ji Ms Ntelele.

Warin rubabben naman mutum

Mai maganin gargajiyar na zaune ne a wata bukka a Rensburgdrift kusa da Estcourt.

Ana kiransa da “Mkhonyovu” wanda ma’anarsa ke nufin “mai tafka almundahana” a yaren Zulu na kasar.

Ya karbi hayar gidan ne daga wajen Philani Magubane, wanda shi ma ake zargin kaninsa da irin wancan laifin.

Image caption

Wannan ne dakin da mai maganin ya kama haya

Image caption

‘Yan sanda sun samu kunne takwas a dakin mutumin da kayan tsafi

“Na kadu matuka da jin cewa kanina ya yarda da tatsuniyar mai maganin gargajiyar nan, inda ya yi musu alkawarin arziki bayan kuwa shi talaka ne futuk,” in ji Mr Magubane.

Ya ce daya daga cikin masu zaman haya a gidan ya yi ta korafin cewa yana jin warin rubabben nama na fitowa daga gidan makwabcinsa.

“Mkhonyovu bai fi wata biyu da tarewa a gidan ba, ban taba sanin cewa yana ajiye sassan jikin mutane ba saboda ni ba anan nake zama ba,” in ji Mr Magubane.

Mr Magubane ya ce ya tabbata kaninsa da sauran mutanen sun rudu ne da karairayin mai maganin da ya ce zai musu tsafi su yi arziki.

Ana zargin cewa yana aika mutane su tone kaburburan jama’a ne da tsakar dare don ya hada wani tsafi da ake kira “muti”.

Yadda mutane suka ci naman mutum suna sane

Mthembeni Majola, wani dan siyasa a garin ya kira taron al’ummar yankin jim kadan bayan da daka gabatar da masu cin naman mutanen a gaban kotu.

Image caption

Mthembeni Majola ya ce daya daga cikin mazauna garin ya san cewa naman mutum yake ci

“Mazauna garin da dama suna zaune cikin tsoro tun bayan fallasuwar siriin mutanen, amma Mr Majola ya ce wasu mutanen ba su yi mamaki ba.

“Wasu da dama sun tabbatar da cewa sun san abin da mai maganin ke yi har ma sun ci naman mutum suna sane,” in ji shi.

“Amma abin da ya bata mana rai shi ne yadda mutanenmu suka zama sakarkaru, yawancin wadanda suke zuwa wajen mai maganin barayin shanu ne wadanda yake cewa zai ba su sa’a su dinga bacewa ko ba su maganin karfe don ko ‘yan sanda sun harbe su bindiga ba za ta same su ba, in ji Mr Majola.

Phepsile Maseko, wata jagora ce a kungiyar masu magain gargajiya ta Afirka Ta Kudu, ta kuma yi Allah-wadai abin da masu cin naman mutanen ke yi.

Ta ce, “Mkhonyovu mai maganin karya ne wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya shigo da mugun abu cikin sana’armu.

Image caption

Phepsile Maseko ta ce, “Mkhonyovu mai maganin karya ne wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya shigo da mugun abu cikin sana’arsu

“Kashe mutane da yin tsafi da sassan jikinsu ba ya cikin tsarin maganin gargajiya, abin da ya yi ya bata mana rai saboda a yanzu dole sai mun fito mun kare aikinmu da kyau gudun bacin suna,” in ji Ms Maseko.

Mutane biyar din da aka kama wadanda aka gurfanar da su a kotu ranar Litinin sun yi watsi da belinsu da aka bayar, za kuma su sake gurfana a gaban kotun a karshen watan Satumba.

Juventus ta kusa kammala daukar Howedes


JuventusHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jamus ce ta lashe kofin duniya a Brazil a 2014, bayan da ta ci Argentina 1-0 a wasan karshe

Dan wasan tawagar kwallon Jamus, mai taka-leda a Schalke, Benedikt Howedes yana Juventus ana duba lafiyarsa a shirin komawa can da buga tamaula.

Howedes mai shekara 29, ya yi wasanninsa na tamaula tun yana da kuruciya a Schalke, ya kuma yi kyaftin dinta shekara shida.

An nuna hoton dan kwallon a shafin intanet na Juventus domin a duba lafiyarsa a ranar Laraba.

Howedes ya buga wa Jamus wasa 44 har da na gasar cin kofin duniya a 2014 da kasar ta zama zakara a Brazil.

Arsenal ta ki sayar wa da City Sanchez


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal ta yi rashin nasara a wasa biyu daga ukun da ta buga a Premier

Arsenal ta ki sallama tayin fam miliyan 50 da Manchester City ta yi wa Alexis Sanchez domin ya koma Ettihad da murza-leda.

A karshen kakar badi yarjejeniyar Sanchez mai shekara 24 za ta kare da Gunners, kuma yana son ya koma buga tamaula a Manchester City.

Arsenal ba ta yadda da duk wani kokarin da City ke yi na sayen Sanchez ba, kuma tana son Raheem Sterling ya koma Emirates da wasa a cikin cinikin kafin ranar Alhamis.

Shi kuwa kocin Manchester City, Pep Guardiola yana son sayen Sanchez ba tare da bayar da Sterling ba.

Sterling ya buga wa City wasa uku da ta yi a Premier, amma ba a yi masa alkawarin saka shi a wasa akai-akai ba, sakamakon sayen Bernardo Silva da ta yi daga Monaco.

Chamberlain ya fi son Liverpool kan Chelsea


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chamberlain ya koma Arsenal daga Southampton a 2011

Dan kwallon Arsenal mai tsaron baya, Alex Oxlade-Chamberlain ya ki yadda ya koma Chelsea da taka-leda duk da Gunners ta amince da tayin fam miliyan 40.

Chelsea na son yin amfani da Chamberlain a gurbin mai tsaron baya daga gefe, shi kuma dalilin da ya sa yake son barin Arsenal saboda baya buga wasa daga tsakiyar fili.

Dan kwallon tawagar Ingila mai shekara 24, na son ya koma Liverpool, kuma kungiyar tana son sayen sa.

Ana sa ran Liverpool za ta taya dan Chamberlain kafin ranar Alahmis, watakila kasa da fam miliyan 40 da Chelsea ta ce za ta biya.

Sai dai Arsenal na fatan kammala sayar da tsohon dan kwallon Southampton din ba tare da ba ta lokaci ba, wanda yarjejeniyarsa da Gunners za ta kare a karshen kakar badi.

Arsenal ta ki sayar da Sanchez, Liverpool za ta sayar da Coutinho?


Tottenham ta kusa sayan dan Ajentina mai shekara, mai shekara 19, Juan Foyth daga Estudiantes kan kudi fam miliyan 8 kuma tana sake kokarin kammala cinikin Serge Aurier kan kudi fam miliyan 23, in ji Guardian.

Hakkin mallakar hoto
ALEJANDRO PAGNI

Image caption

Juan Foyth

Liverpool ta yarda ta sayar da dan wasan Brazil mai shekara 25, Philippe Coutinho, ga Barcelona a wata yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 148, in ji Yahoo Sports.

Duk da haka jagoran Liverpool, Peter Moore, ya nuna cewar ba za a sayar da Coutinho ba a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter kafin lokacin a rufe kasuwar ‘yan wasan ranar Alhamis, in ji Liverpool Echo.

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan gaba, Alexis Sanchez, mai shekara 28, idan yarjejeniyar ta yi mata kyau, in babban wakilin Daily Mirror kan kwallon kafa, John Cross.

Hakkin mallakar hoto
Dean Mouhtaropoulos

Image caption

Ana ta rade-radi kan makomar Sanchez a kwanakinnan

Inter Milan ta sake sabon tayi wa dan wasan gaban Arsenal mai shekara 25, Shkodran Mustafi, in ji Sky Sports.

Tottenham tana tunanin ko za ta jinkirta taya dan wasan tsakiyar Everton, Ross Barkley saboda matsalolin ciwon da dan shekara 23 din yake da su, in ji London Evening Standard.

Dan wasan West Brom na baya, mai shekara 29, Jonny Evans, zai ki komawa Arsenal saboda yana son komawa Manchester City, in ji Daily Mail.

‘Yan Baggies din sun shirya domin sayan dan wasan Poland mai shekara 27, Grzegorz Krychowiak daga Paris St-Germain, in ji Sun.

Hakkin mallakar hoto
Michael Steele

Image caption

Jonny Evans

West Brom, za ta kammala sayan dan wasan bayan Arsenal Kieran Gibbs kan kudi fam miliyan 7 nan da sa’o’i 24, in ji Daily Mirror.

Dan wasan bayan Southampton Virgil van Dijk, mai shekara 26, yana da fatan komawa Liverpool, duk da cewar Arsenal da zakarun Firimiya Chelsea ka iya taya shi, in ji Independent.

Crystal Palace za ta goyi bayan kociya Frank de Boer da sayayya uku, in ji Daily Star.

Stoke City tana son sayan dan wasan tsakiyar Manchester City, Fabian Delph, mai shekara 27, kuma a shirye take ta taya dan wasan da aka saya daga Asoton Villa fam miliyan 8 , kan kudi fam fam miliyan 12, in ji Daily Telegraph.

Kociyan Newcastle United, Rafael Benítez, zai sayar da dan wasan gaba mai shekara 26, Dwight Gayle kan kudi fam miliyan 18, in ji Guardian.

Nigeria: Evans ya amsa lafinsa na 'satar mutane' a kotu


Evans lauyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya Evans ya yi karar rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa zargin suna tsare shi ba bisa ka’ida ba

Madugun nan da ake zargi da satar mutane don karbar kudin fansa a jihar Legas da ake kudancin Najeriya, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na hada tuggu don sace mutane ya yi garkuwa da su a gaban wata babbar kotu a Legas.

An gurfanar da Evans ne a ranar Laraba a babbar kotun Legas da ke Ikeja a gaban mai shari’a Akin Oshodi.

Tun a farkon watan Yuni ne aka cafke Evans da wasu mutum biyar inda daga bisani aka gurfanar da su a gaban babbar kotun kan tuhumarsu da satar mutane don karbar kudin fansa.

Abba Kyari: ‘Evans ya so ya gagari jami’an tsaron Nigeria’

Evans ya shigar da ‘yan sandan Nigeria kara a Kotu

‘Yan sandan Nigeria: ‘Evans yana nan bai mutu ba’

Kotu ta ci tarar lauyan Evans

Image caption

‘Yan sanda na cikin shirin ko-ta-kwana don raka Evans gidan yari

Hakkin mallakar hoto
AFP

A ranar Talata ne wani sashe na babbar kotun ya sanya ranar 5 ga watan Satumba don sauraron uzurin lauyan Evans da lauyoyin ‘yan sanda a kan dalilin da ya sa kotu ba za ta yanke hukunci kan karar da Evans ya shigar kan tauye ‘masa hakki’ na ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi gaban shari’a ba.

A ranar Talata ne kuma, wadda tun farko alkali ya so yanke hukunci kan korafin Evans din, lauyan ‘yan sanda David Igbodo, ya shaida wa manema labarai cewa, “Yin hakan rashin adalci ne ba tare da jin nasu uzurin ba.”

Ya kuma kara da cewa, binciken da ‘yan sanda suke yi kan Evans din ya kusa kammala.

Mr Igbodo ya kuma ce binciken da suke yi din ne dalilin da ya sa suke ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi a gaban shari’a ba, kuma kotu ce ta ba su wannan umarnin.

“Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su san mece ce makomar Evans kan irin abin da ya aikata,” in ji Mist Igbodo.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce Evans ya kwashe fiye da shekara 20 yana aikata laifuka a kasar.

Tun a shekarar 2013 ne dai aka yi yekuwar neman Evans ruwa a jallo.

Hajj 2017: Alhazan duniya sun fara aikin Hajji a yau


Mahajjata a filin ArfaHakkin mallakar hoto
AP

Maniyyata fiye da miliyan biyu ake sa ran zasu halarci aikin hajjin bana a kasar Saudiyya, ayyukan ibadan da zasu shafe kwanaki 5 masu zuwa.

Dubban daruruwan maniyyata musulmi na ta isowa Saudiyya daga sassa dabam-daban na duniya domin aikin hajjin bana, kuma maniyyatan kasar Iran na halartar aikin hajjin, bayan da suka kauracewa aikin a bara saboda turereniyar shekarar 2015 da tayi sanadin mutuwar kimanin maniyyata 2,000.

Maniyyata na fuskantar kalubalen sauke farali, inda Saudiyya kuma ke fuskantar kalubalen samar da yanayi mafi kyau da ingantaccen tsaro ga maniyyatan.

Abin alfahari

A bana kawai, kasar ta samar da fiye da dakaru dubu dari domin tabbatar da tsaro da doka da oda a wuraren da ake gudanar da ayyukan na Hajji.

Dakaru sun yi fareti na musamman domin tabbatar da shirin ko-ta-kwana dangane da samar da tsaro.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Amma ba lamarin tsaro ba ne kawai ke damun hukumomin Saudiyya. Karuwar maniyyata masu isa kasar ya kasance batun dake daukar hankalin hukumomi.

Saudiyya ta samar da jiragen kasa masu gudu, kuma ta fadada hanyoyi domin rage cunkoso a wurare daban-daban.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Shekaru biyu da suka gabata fiye da maniyyata dubu biyu suka rasa rayukansu a sanadiyyar turereniya. Kasar Iran ta rasa wasu daga cikin ‘yan kasarta, dalilin da yasa ta dora wa Saudiyya alhakin lamarin.

A bara Iran ta hana maniyyatan kasarta zuwa aikin hajji, amma sun dawo a bana. A wani bangaren kuma akwai batun siyasar yankin — misali batun rikicin Saudiyya da Qatar ya shafi maniyyata daga kasar, wadanda a da har sun cire rai da halartar aikin hajjin a bana.

Ban da wannan kuma akwai batun kiwon lafiya.

Shugaban kungiyar Red Crescent a Saudiyya yace sun kammala shirye-shirye tare da ma’aikatar lafiya domin tunkarar barkewar cututtuka ko annoba a lokacin wannan aikin hajjin.

Gwamnatin Buhari 'ta kai karar mutum 6,646 kotu a shekara daya'


Shugaba BuhariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yaki da cin hanci na cikin manyan alkawuran da Shugaba Buhari ya yi

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi karar mutum 6,646 a kotu bisa aikata laifuka daban-daban a tsakanin shekarar shari’a ta 2015-2016.

Wata sanarwa da kakakin ministan shari’a Abubakar Malami, ya aikewa manema labarai ta ce 325 cikin laifuka 1,330 kanane.

Kakakin, Comrade Salihu Othman Isah, ya ce an yanke hukuncin da ya goyi bayan gwamnati kan kashi 90 cikin dari na karar da ta shigar.

Ya kara da cewa gwamnati ta yi tsimin sama da N119 bn da kuma $14bn a cikin wadannan kararraki.

Kazalika, a cewar sanarwar, gwamnati ta hana masu laifi guje wa biyan harajin da ya wuce N10bn wanda ya kamata su biya hukumar kwastam.

“Wadannan kararraki sun hada da na manyan laifukan, ta’addanci, satar mai, kisan kai, fyade, fashi da makami da mallakar makami ba bisa ka’ida ba dai dai sauransu”, in ji sanarwar.

Gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ta dare kan mulki a shekarar 2015, ta sha alwashin yaki da cin hanci da ta’addanci da makamantansu.

Sai dai masu sharhi na ganin har yanzu gwamnati ba ta daure manyan jami’an da ake zargi da wawure kudin kasar ba.

Arsenal za ta sayar wa da West Brom Gibbs


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dan wasan yana tattaunawa da Watford da kuma Galatasaray

West Brom ta kusa kammala daukar dan wasan Arsenal mai tsaron baya, Kieran Gibbs mai shekara 27.

Arsenal ta amince ta sayar da Gibbs kan kudi fam miliyan biyar, haka kuma dan kwallon na tattaunawa da Watford da kuma Galatasaray ta Turkiya.

Gibbs na bukatar a duba lafiyarsa kafin ya saka hannu kan yarjejeniya.

Haka kuma Arsenal ta bi sawun Manchester City da Leicester wajen zawarcin mai tsaron baya na West Brom, Jonny Evans.

Mene ne bambancin son jima'i tsakanin mace da namiji?


Mene ne bambancin son jima'i tsakanin mace da namiji?Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Makalun kimiyya kadan ne suka bayar da tabbacin cewa mutane sun yi ce-ce-ku-ce da muhawara fiye da ikirarin sanin bambancin yadda ake zaburarwar likon alakar kwakwalwar mace da namiji.

Daukacin abin da ake ta kai-kawo a kai su ne dabi’un da ke tattare da tarawar jima’i. Sai dai an sha samun hujjojin da ba su da nagarta imma har ba a yanke cewa daukacinsu shaci-fadi ne.

Haska hoton kwakwalwa da aka yi ya nuna cewa wuraren da ke lailaye da launin toka-toka “mabubbbugar farin ciki” a maza da mata ba su nuna hakikanin sassan sarrafa al’amura da ke cikin kokon kai.

Al’amarin kamar shaci-fadi ne yadda wasu masanan bunkasar kwakwalwa da ke nuni da cewa kwakwalen maza da mata dole suna da mabambantan muhimman kullin alakar, bisa la’akari da bambancin dabi’a.

Ta yiwu ka yi hasashen cewa saboda cunkoson masu tafiya makaranta da safiyar nan, sabanin jiya, tuni da an karkatar da akalar hanyar bisa dole.

Lamarin a bayyane yake ganin yadda wata makala ta bi kadin bambance-bambancen darsuwar tunkarar tarawar jima’i a tsakanin maza da mata da ke da alaka da hakikanin bazuwar tartsatsin sakonni a jijiyoyi.

Saura da me, bayan gano likon alakar da gungun masu bincike na majisalar likitanci da ke da dakin binciken kimiyyar rayuwar halittu a Cambridge da ke Ingila, al’amari ne mai sauki da ke nuni da bijirowar darsuwar jima’i tamkar kunnawa da kashewar bazuwar lantarki; ingiza jijiyoyi su fitar da sinadaran aikewa da sakonnin ankararwa ga jijiyoyi ta wata hanya ga maza, da kuma wata hanyar daban ga mata.

Abin da aka fahimta bai yi nuni da dabi’ar mutum da muke magana akai ba. Sai ma dai a ce an yanka ta tashi.

Abin da ke ingiza darsuwa da daukar al’amura bai daya a jikin wannan da waccan, lamari ne da masu bincike suka yi takatsantsan wajen kauce masa, ko da yake sun yi kwatanceceniya da jaba.

Misali kamar yadda aka fitar da su ta yadda za su dauki hankalin abokin Barbara ko tantance cewa abokin hadin Barbara shi ne na hakika.

Daukacin batutuwan shahararrun mujallu, abin mamakin shi ne, duk abin da suka yi nuni da shi kadan ne aka gano game da sinadaran aikewa da sakonnin tarawar jima’i a mutum.

Sinadarin “steroid androstenone” da ake ce yana daukar hankalin mata idan maza suka fitar da shi, kuma yana ankarar da maza cewa kwayayen mata na bukatar kyankyasar maniyi, amma dai babu wata kakkwarar hujja kan haka.

Mun fahimci cewa dai sakon ankararwar sinadaran tarawarar jima’i ba shi da makama. Akwai wani sinadari na musamman da ake yi wa lakabi da cVA (11-cis-vaccenyl acetate) da ke da maganadisun jawo macen kuda su yi ta soyayya, al’amarin ya hadar da waka da rawa daga nan kawai sai su hada baki da al’aura.

Amma a jikin maza sinadarin cVA tasirin aikinsa akasin haka ne; tauye soyayya, a wasu lokutan ma yakan harzuka musu tada jijiyar wuya, al’amarin da ke nuni da gasar namiji.

Kulla alaka

Abin tambaya a nan shi ne ko mene ne ke haifar da mabambantan salon tunkarar lamarin. A wasu daya daga cikin jinsunan ne ke yin “warin sinadarin jan hankalin jima’i,” saboda yana da managarciyar makarbiyar sinadaran protein da ke shigar da sinadarin ankararwar.

Sai dai akai-akai, sinadarin cVA, wanda ke bijiro da darsuwar dabiar son jima’i a maza da mata irin guda ne, don haka za su iya gano shi, tare da ‘fahimtar’ sauye-sauyen salonsa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ayyukan binciken da suka gabata bambanci kadan suka nuna a tsakanin maza da amta, inda daukacin tartsatsin sakonnin mafi akasari nan take da zarar sinadarin cVA ya bijiro da shi, sannan sakonnin kan yi juyin sadarwa (karo na biyu a tunkudowar tartsatsinsu).

Gregory Jeffens da abokan aikinsa a Cambridge sun gano bambancin da ke tattare a matakin tartsatsin sakonni na gaba wato juyin sadarwa na uku. Bambanci na da ban mamaki kai tsaye; wadannan tartsatsin sakonni kullin alaka ne a hanyoyi daban-daban, wadanda ke ankararwa a wani sashe na kwakwalwar kuda (mai zukar furanni), sabanin turakun tafiyar tarragon jirgin kasa mabambanta.

Samun irin wadannan bayanai na tattare da aiki na kwarewa da jajircewa wajen gwaji a fannin kimiyyar kai-kawon sakonnin jijiyoyi a kwakwalwa.

Masu bincike sun hada hotunan mitsi-mitsin kwakwalwar kuda, al’amarin da ya yi nuni da raunin hanyoyin tafiyar sako guda, wanda ke “juya akalar” ma’aunin tafiyar tartsatsin sakonni a zirin silin jijiya.

Ta haka ne za su iya gano sashen ankararwa a kwakwalen namiji da mace, sannan a nuna bambancin da ke tsakaninsu bayan sun kai ga juyin sadarwar sakonni karo na uku.

Wadanne al’amura suka haifar da bambancin alaka? Jefferis da abokan aikinsa sun danganta ala’amarin da kwayar halitta guda, da ake kira “fruitless – mara-katabus,” wadda masana kimiyya suka san cewa tana da muhimmanci a dabi’ar namiji.

Kwayar halittar ke tattare bayanai game da sinadaran proteins, sannan masu bincike sun nuna cewa samar da wadanann sinadaran proteins a juyin sadarwar sakonni mataki na uku shi ke kulle su a tsarin kwakwalwar namiji.

Da masu binciken suka jirkita wadannan tartsatsin sakonni a kwakwalwar mace sai aka samar da sionadaran proteins, kuma kwakwalwar mace ta kulla alaka da su tamkar ta namiji.

Shin juya wannan gudan sakon sadarwar ya isa yin tasirin sanya mace ta darsu da salon matakin namiji ga sinadarin cVA?

Saura dai a jira a gani, kuma ta yiwu irin wanan juyin-juya halin jinsi na bukatar Karin wasu “su juya irin na namiji” a samu kwaranyar sinadarin darsuwar jima’i.

Amma abin takaici ne a ce a kalla kan al’amarin da ya shafi tarawar jima’i, akwai al’amura karara game da bambancin da ke damfare a tsakanin kwakwalwar namiji da mace.

Man City na son daukar Sanchez kafin Alhamis


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An ci Arsenal wasa biyu a karawa uku da ta buga a gasar Premier ta bana

Manchester City na son ta sayi dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai a ranar Alhamis.

Sanchez mai shekara 24, ya ci kwallo 24 a Premier bara, sai dai yarjejeniyarsa za ta kare da Arsenal a badi, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa a Emirates ba.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola na son sayen Sanchez kai tsaye kuma ba tare da ba ta lokaci ba.

Sai da kuma idan Sanchez ya koma City, makomar Raheem Sterling za ta zama kila-wa-kala a kungiyar.

Sterling ya buga wa City wasa uku da ta yi a Premier, amma ba a yi masa alkawarin saka shi a wasa akai-akwai ba, sakamakon sayen Bernardo Silva da ta yi daga Monaco.

BBC ta fahimce cewar Sterling zai so ya koma Landan da taka-leda, idan har Arsenal na bukatar hakan a cikin yarjejeniyar cinikin Sanchez.

City ba ta taya Sanchez ba, amma ana sa ran za ta sayi dan kwallon nan ba da dadewa ba.

Chelsea na daf da daukar Chamberlain


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal ta buga wasa uku a Premier ta bana ta ci karawa daya aka doke ta sau biyu

Dan kwallon Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain ya kusa ya koma kungiyar Chelsea mai rike da kofin Premier da taka-leda kan fam miliyan 40.

A karshen kakar badi ne yarjejeniyar Chamberlain mai shekara 24 za ta kare a Emirates, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa a kungiyar ba.

Oxlade-Chamberlain bai yanke shawarar kungiyar da ya kamata ya koma ba tsakanin Chelsea ko Liverpool, sai dai Chelsea ce kawo yanzu ta taya dan wasan.

Sai dai Arsenal na fatan kammala sayar da tsohon dan kwallon Southampton din ba tare da ba ta lokaci ba.

Dan wasan ya buga wa Arsenal wasannin Premier uku da ta buga a bana, ciki har da karawar da Liverpool ta ci Gunners 4-0 lokacin da aka cire shi a karawar.

Chamberlain zai zama na biyar da Chelsea ta dauka a bana bayan Alvaro Morata da mai tsaron raga Willy Caballero da mai tsaron baya Antonio Rudiger da mai wasan tsakiya Tiemoue Bakayoko.

Ko Dembele zai taka rawar da Neymar ya yi a Barca?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dembele ya koma Barcelona a matsayin na biyu mafi tsada da aka saya a tarihin tamaula

A ranar Litinin Osmane Dembele ya kammala komawa Barcelona daga Borussia Dortmund a matsayin na biyu mafi tsada da aka saya a duniya kan fam miliyan 135.3.

Barcelona ta dauki dan kwallon ne domin ya maye gurbin Neymar wanda ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 a matakin wadda aka saya mafi tsada a duniya.

Tuni Barcelona ta bai wa Dembele riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a Barca, shin ko Dembele zai taka rawa irin wacce Neymar ya yi?

Ga jerin kungiyoyin da ya buga wa tamaula da kwallayen da ya ci:

 • Cikakken suna:Ousmane Dembélé
 • Ranar Haihuwa:15 May 1997 (age 20)
 • Wurin da aka haife shi:Vernon, France
 • Tsawonsa:1.78 m (5 ft 10 in)[1]

Taka-leda a matsayin matashin dan kwallo

 • 2004-2009Madeleine Évreux
 • 2009-2010Évreux
 • 2010-2015Rennes

Taka-leda a matsayin kwararren dan wasa

 • 2014-2015Rennes II wasa 22 kwallo 13
 • 2015-2016Rennes wasa 26 kwallo 12
 • 2016-2017Borussia Dortmund wasa 32 kwallo 6

Wasanni a tawagar kwallon Faransa

 • 2013-2014 Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 wasa 8 kwallo 4
 • 2014-2015 Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 18 wasa 5 bai ci kwallo ba
 • 2015 Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 19 wasa 3 kwallo 1
 • 2016- Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 wasa 4 bai ci kwallo ko daya ba
 • 2016- Babbar tawagar France wacce ya yi wa wasa 7 ya ci kwallo 1

An gayyaci 'yan Madrid 17 tawagar kasashensu


Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid ta tashi wasa 2-2 da Valencia a ranar Lahadi a wasan mako na biyu a La Liga

Kimanin ‘yan kwallon Real Madrid 17 aka gayyata tawagar kasashensu, domin zuwa wasan gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 da na ‘yan kasa da shekara 21.

‘Yan wasan da za su buga wa kasashensu fafatawar shiga gasar kofin duniya sun hada da Marco Asensio da Dani Carvajal da Isco da Nacho da Sergio Ramos da Lucas Vazquez.

Sauran sun hada da Cristiano Ronaldo da Luka Modric da Mateo Kovacic da Keylor Navas da Gareth Bale da Casemiro da Marcelo da Toni Kroos da kuma Achraf.

Su kuwa Borja Mayoral da Dani Ceballos za su buga wa Spaniya wasan matasa ‘yan kasa da shekara 21 na sada zumunta da Italiya da na neman shiga gasar Zakarun Turai da Estonia.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na uku a gasar La Liga a ranar 9 ga watan Satumba, kwanaki hudu tsakanin ta buga wasan gasar cin kofin Zakarun Turai da Apoel Nicosia a Santiago Bernabeu.

Koriya ta haraba makami mai linzami ta saman Japan


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda aka tashi da bala’in giftawar makami mai linzami a Japan

Koriya Ta Arewa ta harba wani makami mai linzami ta sararin samaniyar Japan, wani al’amari da Firai Ministan Jaan Shinzo Abe ya ce hakan wata babbar barazana ce da ba a taba samun irin ta ba.

An harba makamin ne a ranar Talata da sassafe agogon Koriya, wanda ya bi ta tsibirin Hokkaido kafin daga bisani ya fada cikin teku.

Ana sa ran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa don mayar da martani kan lamarin.

A baya-bayan nan ne Koriya Ta Arewa ta aiwatar da wasu gwaje-gwajen makamai masu linzami, amma wannan ne karo na farko da ta harba mummunan makami mai linzami ya bi ta samaniyar Japan.

A karo biyu a baya da rokokinta suka bi ta samaniyar Japan a shekarar 1998 da ta 2009, Koriya Ta Arewa ta ce tana kaddamar da tauraron dan adam ne ba makamai ba ne.

Wakilin BBC a Tokyo Rupert Wingfield-Hayes, ya ce ga alama wannan makami na farko da aka harba wanda ka iya daukar makamin nukiliya.

An umarci mazauna kasar su nemi mafaka

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

N Korea’s Japan missile: The key questions

Rundunar sojin Koriya Ta Kudu ta ce an harba makami mai linzamin ne ta gabas kafin karfe 6:00 na safe, wanda ya yi daidai da karfe 9:00 na daren Litinin agogon GMT, daga Pyongyang, babban birnin kasar, wanda ba a cika samun hakan ba.

Wani sharhi da aka yi na farko ya nuna yadda harbin makamin ya kasance:

 • ya yi tafiyar fiye da kilomita 2,700
 • ya yi kama da samfurin Hwasong-12, wani sabon samfurin makami da ba a dade da kera irinsa ba
 • nisansa daga kasa ya kai kilomita 550, wanda hakan shi ne gwajin da ya fi yin kasa-kasa a duk gwaje-gwajen makamin da Koriya ta yi a baya-bayan nan
 • ya fada tekun Arewacin Pacific kilomita 1,180 kusa da gabar tekun Japan, bayan ya ragargaje zuwa gida uku

Japan dai ba ta yi wani kokarin harbo makamin ba amma ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan kasar da ke Hokkaido da su nemi mafaka a gine-ginen da suke karkashin kasa.

Kwanan nan ne dakarun Amurka da na Japan suka kammala wani atisaye na hadin gwiwa a Hokkaido yayin da ake ci gaba da wani atisayen na dubun-dubatar dakarun Koriya Ta Kudu da Amurka a Koriya Ta Kudun.

Koriya Ta Arewa na kallon wannan atisaye na hadin gwiwa da ya hada da sojojin Amurka a matsayin wata tsokana, inda suke ganinsa a wani yunkuri na kai mata hari.

Shugaban kasar Koriya Ta Kudu Moon Jae-in, ya bayar da umarnin dakarun kasar su fito su yi gagarumin atisaye don mayar da martani ga harin. Jiragen yakin Koriya Ta Kudu sun yi ta atisayen harba bama-bamai a ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Firai Minsitan Japan Shinzo Abe ya yi mummunar suka ga harin

Mr Abe ya ce ya yi magana da Shugaba Donald Trump kuma duk su biyun sun amince a kara matsa wa Koriyta Ta Arewa lamba.

Sai dai cibiyar tsaro ta Amurka ta ce wannan hari ba barazana ce ga kasar ba, amma sojoji na aiki don tattara bayanan sirri game da harin.

China ta yi gargadi cewa tashin hankali ya kai kololuwa a yankin Koriya, amma ta ce Amurka da Koriya Ta Kudu ne abin zargi. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron China Hua Chunying, ta soki kasashen biyun da ci gaba da atisayen sojin da suke yi wanda ke zama kamar matsin lamba ga Koriya Ta Arewa.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov, ya ce, kasar ta damu matuka a kan yiwuwar tabarbarwar da lamarin zai yi, amma ya ce atisayen da sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudu ke yi yana kara harzuka Koriya Ta Arewa.

Sharhi: Rupert Wingfield-Hayes, na BBC a Tokyo

Ana ganin wannan ne gwajin makami mai linzami mafi muni da Koriya Ta Arewa ta yi a lokaci mai tsawo. Kwarai jiragen Koriya Ta Arewa na bi ta sararin samaniyar Japan a da, amma wannan ne karo na farko da Pyongyang ta harba makamin nukiliya ta saman Japan.

Sharhin farko da aka yi ya nuna cewa makamin samfurin Hwasong-12, wanda aka fara ganinsa a wani babban faretin soji a Koriya Ta Arewa a watan Afrilu. Daga bisani kuma aka fara harba shi cikin teku a watan Mayu.

Me ya sa Koriya Ta Arewa ta zabi yin hakan a yanzu? Na farko dai tana son nuna jajircewarta. Tana nuna cewa barazanar Amurka ba ta bai wa kasar tsoro, kamar yadda Shugaba Trunp ya fada mako biyu da suka gabata.

Na biyu, Koriya na son sake gwada makamin nata a gwaji na hakika. Na uku irin wannan gwaji na zama matsin lamba ga kawancen Amurka da Koriya. Yana sa Japan na jin rauni sosai yayin da yake kalubalantar jajircewar Amurka.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An yi ta tura wa mutane sakon kar-ta-kwana a Hokkaido ana gaya musu su nemi mafaka


'Buhari ne ya jefa Nigeria a yunwa da talauci'


Shugaba Buhari ya ce 'yan Najeriya za su daraHakkin mallakar hoto
PRESIDENCY

Image caption

Shugaba Buhari ya taba cewa ‘yan Najeriya za su dara

Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin kan yadda tattalin arzikin kasar ya fara gyaruwa ne, wasu ‘yan kasar suka fara yi masa raddi musamman a kafofin sada zumunta.

Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

Shugaban ya gana da su ne har tsawon kimanin sa’o’i biyu ranar Litinin, kamar yadda Mataimakinsa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana.

Sai dai masu muhawara a shafinmu na Facebook sun bayyana mabambantan ra’ayoyi kan hakan.

Ga kadan daga cikinsu:

Haruna Suleiman Utono ya ce, “Har yanzu talakan Najeriya bai san da farfadowar tattalin arziki ba. Saboda har yanzu babu abin da ya sauya”.

“To a ina arzikin yake farfadowa bayan kun jefa kasa cikin talauci da yunwa”, in ji Usman Ibrahim

Shi kuwa Abubakar Kawu Girgir yabawa ya yi da kalaman shugaban kasar yana mai cewa Hakika muna godiya da irin kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na ganin ya dawo mana da tattalim arzikinmu”.

Shi ma Abdurahaman Gangarawa cewa ya yi, “Allah Ya sa alheri kan farfadowar tattalin arzikin Najeriya, ya ninninka farfadowarsa, ya ba mu ikon amfana da shi.”

Kotu ta sake mallaka wa gwamnati kudi N7.6bn na Diezani


Diezani Alison-MaduekeHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana zargin Diezani da sata, zargin da ta sha musantawa

Wata kotun tarayya da ke birnin Laegas na Najeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar N7.6bn, kudin da ake zargin tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Madueke ta sace.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati, EFCC ce ta gano kudin a wani banki, inda ta yi zargin cewa tsohuwar ministar ta same su ne ta hanyar da bata dace ba.

EFCC ta ce an ajiye kudin ne a asussa da dama.

Alkalin kotun mai shari’a Abdulaziz Anka ya yanke hukuncin ne bayan da EFCC ta nemi kotun ta mallakawa gwamnati kudin dindindin.

A farkon watan nan ma wata babbar kotun da ke Lagos ta mallaka wa gwamnatin Najeriya kaddarorin tsohuwar ministar man da suka kai $40, wato kimanin naira biliyan 14.

Kotun ta mallaka wa Najeriya wani katafaren gidan Ms Diezani da ke yankin Banana Island da ke Lagos, wanda kudinsa ya kai $37.5m, kimanin naira biliyan 13.

Haka zalika, mai shari’a Chuba Obiozor ya mallaka wa gwamnatin Najeriya naira sama da naira miliyan 84 da kuma sama da dala miliyan biyu, wasu kudaden da aka karba a matsayin na haya na gidan na Banana Island.

A kwanan baya dai kotun ta bai wa gwamnatin kasar damar kwace kadarorin na wucen gadi, bayan hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta nemi kotun ta mallawaka wa gwamnati kadarorin.

Bayan haka ne dai kotun ta ba da umarnin a buga hukuncin a kafafen yada labarai, domin duk wanda ke da wani dalilin da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin na din-din-din ba ya kawo dalilinsa gaban kotun.

A watan Afrilun 2016, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai naira miliyan 593 daga hannun tsohuwar ministar.

Ana zargin ta da sace wa da kuma yin facaka da kudin kasar a lokacin da take ministar man, ko da yake ta sha musanta zargin.

A watan Fabrairun 2017 ma, wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince a halatta tare da mallakawa gwamnatin kasar kudaden da aka samu daga wajen tsohuwar ministar man, Diezani Allison-Madueke.

'Ko Buhari ya tambaye su aikin yi nawa aka samar?'


Nigeria economyHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An sha takaddama a Nijeriya cewa bayanan da hukumomi kan fitar game da ci gaban tattalin arzikin kasar kan saba da yadda rayuwa take zahiri a wajen ‘yan kasa.

Wasu masana tattalin arziki a Nijeriya, sun fara kalubalantar shugaban kasar Muhammadu Buhari game da farin cikin da ya nuna kan bayanin farfadowar tattalin arzikin da ministocinsa suka ce ya yi.

Dr. Nazifi Darma ya ce kamata ya yi shugaban ya tambayi ministocinsa ko mutum nawa aka samarwa ayyukan yi sakamakon ci gaban da suke ikirarin (tattalin arzikin) kasar ta samu. “Ayyuka miliyan nawa aka samar?”

“Kuma game masana’antun da suka durkushe, guda nawa ne suka bude suka ci gaba (da aiki). Kuma me suka sarrafa?”, ya tambaya.

An sha jayayya don nuna cewa alkaluman bunkasar tattalin arziki da hukumomin Nijeriya kan fitar ba sa zuwa daidai da yadda ainihin rayuwar talaka take a zahiri.

Shugaba Buhari ya bayyana farin cikin ne bayan ganawar da ya yi da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da takwaranta na Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele.

Sai dai, masanin ya ce akwai bambanci tsakanin alkaluma na ci gaban tattalin arziki da kuma ainihin yadda rayuwar mutane ta kasance a wannan kasar wanda zai yi daidai da wadannan alkaluma.

Dr. Darma ya kara da tambayar wacce irin raguwa aka samu game da hauhawar farashin kayayyaki idan an kwatanta kan yadda (abin) yake kafin (yanzu)?

“Ta yadda mutane za su samu dama, su iya sayen kayayyaki da sauki, da kuma masu yawa a kan yadda suke saya da kafin shiga matsin tattalin arziki.”

Kimanin shekara biyu kenan da Nijeriya ta shiga wani mummunan matsin tattalin arziki, wanda ya janyo gagarumar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

'Yawancin alhazan Nigeria manoma ne'


Shugaban hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) Abdullahi Muktar ya ce an kammala kwashe alhazan Najeriya wadanda suka yi rijista ta hannun jihohi kimanin guda dubu 65 ranar Lahadi.

“Ba wani Alhaji jiha yanzu da ya rage duk an riga an kwashe su zuwa Saudiyya,” kamar yadda ya shaida wa BBC ta waya yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya ranar Litinin.

Ya ce adadin alhazan ya dara wanda aka samu bara, don bara alhazai kimanin dubu 61 suka sauke farali.

Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da abokin aikinmu, Haruna Mararabar Jos ya yi da shi idan kuka latsa alamar lasika da ke hoton sama.

Na ji dadin farfadowar tattalin arzikin Nigeria – Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi arin ciki da farfadowar tattalin arzikin Najeriya.

Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

Shugaban ya gana da su ne har tsawon kimanin sa’o’i biyu ranar Litinin, kamar yadda Mataimakinsa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana.

Adesina ya ce sun tattauna batutuwan manofofin kudin kasar da tattalin arziki da dai sauransu.

Shugaban ya kara jadaddawa ministocin da gwamnan CBN da cewa gyara tattalin arziki shi ne babban alkawarin da jam’iyyarsa ta yi wa ‘yan kasar, kamar yadda ya ce.

Adesina ya ce shugaban ya nuna “farin cikinsa da yadda al’amura suke tafiya bayan shekara biyu da tabarbarewarsu.”

Shugaban ya bukaci ministocin da su ci gaba da ba da himma don babban aikin gwamnati shi ne samarwa ‘yan Najeriya saukin rayuwa.

Me kuke son sani kan birnin Awamiya da 'yan Shia'a suka fi yawa a Saudiyya?


Masu fafutika sun ce sama da farar hula 20 da 'yan bindiga biyar ne suka mutu sakamakon rikicin da ake yi a garinHakkin mallakar hoto
REUTERS/FAISAL AL NASSER

Image caption

Masu fafutika sun ce sama da farar hula 20 da ‘yan bindiga biyar ne suka mutu sakamakon rikicin da ake yi a garin

Birnin Awamiya na Saudiyya shi ne garin da mafi yawan mazauna cikinsa mabiya Shi’a ne, sai dai a baya-bayan nan rahotanni ke nuna yadda ake ba-ta-kashi tsakanin mazauna garin da dakarun kasar.

Me kuke so ku sani game da wannan gari da kuma wainar da ake toyawa a cikinsa?

Bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa birnin Houston Amurka


Ambaliya a HoustonHakkin mallakar hoto
Rex Features

Kamar yadda jami’ai a jihar suka nuna Houston na cikin juyayi bayan shaida wata babbar guguwa mai tafe da ruwa a cikin tarihin jihar Texas.

An shaida saukar ruwan sama mai yawan centimita 75, yayin da guguwar hurricane harvey ke ratsawa ta koguna – al’amarin da ya janyo ambaliyar ruwa a kan hanyoyi ya mayar da titunan birnin kamar koguna.

Ana dai hasashen cewa cikin wannan makon a bana yankin zai shaida saukar ruwan sama mai yawa. An rawaito cewa mutum biyar sun hadu da ajalinsu a yayin da kuma jirage masu saukar ungulu ke ciccibo mutanen da suka makale a kan runfunan gine-ginen gidaje.

Daukin da ake kai wa mutanen dai na neman gazawa – wannan ne ya sa mutane ke ta kokari tsira da kansu.

An dai yi kiyasin guguwar hurricane za ta kai girman ma’auni na hudu . To amma daga bisani aka rage girma ma’aunin zuwa guguwa da ke keta dazuzzuka.

Kimanin mutum 2,000 ne aka ceto daga ciki da kuma kewayen Houston – birni na hudu mafi girma a Amurka. Birnin Houston dai na da yawan bil’adama kimanin miliyan shida da dubu dari shidda.

Tuni dai aka janye wani gidan kula da gajiyayyu a Dickson ta jirgi mai saukar angulu zuwa wani waje mai nisan kamar kilomita hamsin (50km) da ke a kudu maso gabashin wajen birnin.

Wannan kuwa ya biyo bayan wasu hotuna da aka warwatsa ta hanyoyin sadarwa irin na zamani a kan yadda tsoffi d ake zaune a gidan gajiyayyu ke neman a kai musu dauki.

Hukumar kula da yanayi da saukar iska ta bayyana cewa al’amarin da ya faru ya zo musu a ba zata. Ana dai ci gaba da shaida barazanar ambaliyar ruwa a wasu yankuna sa’annan har zuwa wannan lokaci akwai yankunan da kaiwa a gare su ke bai wa hukumomi wahala.

Dubban gidaje ne aka yanke musu hasken lanatarki, tun bayan afkuwar wannan al’amari. Da yawa daga makarantu na ci gaba da zama a rufe. Sa’ilin da biyu daga manyan filayen jirgin sama ambaliyar ruwa ta yi makil a cikinsu.

Birnin Houston na cikin matsala- a cewar James Cook na BBC.

A yanzu ruwan sama ya mamaye daukacin birnin -an kulle shaguna da sauran harkokin kasuwanci. An killace hanyoyin mota da a ke bi a cikin birnin. Sa’annan kuma an kulle tasoshin filin jirgin sama – akwai yiwuwar tafiye-tafiye su fuskanci matsala watakila ba masu yiwuwa ba ne.

Bayan ka iwa mutane dauki, an kuma tashi wani asibiti – dab da lokacin da injiniyoyi ke ci gaba da aiki bil hakki don a saki ruwan da ya bakam daga madatsun ruwa biyu.

Ana ci gaba da gargadin masu gidaje da ke makwabtaka a kusa da madatsar ruwa da su kwana da shirin fuskantar ambaliyar ruwa cikin wasu sa’oi masu zuwa.

Wasu daga mazauna wadannan yankuna dai na zaune cikin damara tun bayan da ruwan ya nausa zuwa yankin Gulf a Mexico a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Akwai wani yanki da ke makwabtaka da wadannan yankuna da suka fara shaida ambaliyar ruwa – wasu mutane na cike da fushi tun bayan da aka sanar da su cewa su kaurace yankunansu cikin dare daya.

Wannan dai ya zo a lokacin da ruwan ke tinkaro su da tsanani.

Hukumomi dai na ci gaba da gudanar da ayyukansu To sai dai ana duba ko ta wacce hanyar ce za su samarwa shugaban kasar Donald Trum muhalli a daidai lokacin da ayke shirin kai wata ziyara jihar Texas a Talatan nan. In har shugaba Trump y ace zai ci gaba da kai ziyara birnin to lalle idanunsa za su gane ma sa yadda birni mai arzikin mai ya zama abin tauayi

Anya ana samun saukin kawar da ambaliyar ruwan?

Za a ce babu alama. Bisa la’akari da yadda ruwan mai tafe da guguwa ke ci gaba da ragargazar kudu maso gabashin Texas. Sa’annan ruwan na ci gaba da tumbatsa kuma ke nausawa zuwa Houston.

Magajin garin Houston Sylvester Turner, ya fadawa mazauna birnin cewa, ‘Kar ku yi gaggawar kusantar hanyoyi birnin. Kar ku yi tunanin cewa wannan guguwa ta zo kuma ta wuce.’

Dubban mutane ne da aka umarce su da su bar yankin Fort Bend kamar tsawon kilomita hamsin da biyar kudu maso yammacin Houston – wani yanki da ake tinanin kogunan yankin za su cika su batse.

Kawo wannan lokaci hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a game da shirin janye mutane daga yankin ba.

Kome ya sa basu bayar da sanarwar ba?

Magajin garin Turner a wannan Lahadin da ta gabata ya kare kansu daga shirin da aka yi na kwashe mutum kimanin miliyan biyu da dubu dari uku.

Ya bayar da misali da abin da ya faru a Houston a yayin da aka dauke mazauna yankin a dab da lokacin da mahaukaciyar guguwar Hurricane ta sauka a watan satumba a shekara ta 2005.

Mutane sun makale sama da sa’a 20 a kan hanyoyi ba tare da an kai musu dauki ba. Hakan ya haifar da mutuwar gomman mutane.

Ana dai hasashen cewa guguwar Rita za ta nausa zuwa Houston ta tsallaka zuwa gabashin birnin.

Masu kula da al’amura dai na bin bahasin yadda aka yi jigilar mutane ta hanyoyin da ba su dace ba kafin saukar mahaukaciyar guguwar Hurricane Katrina da ta ci yankin Nw Orleans a cikin watan Agustar da bala’in ya sauka.

Dubban mutane sun yi zaman wahala a wani yanayi da suka fuskanci karancin ruwa.

Wacce illa guguwar Harvey za ta yi ga tattalin arzikinsu?

Yankin gabar tekun Texas wani bangare ne mai muhinmanci ga harkokin man fetur da isakar gas a kasar Amurka. Dalili kuwa wasu daga manyan matatun man fetur da ke a jihar Texas sun dakatar da ayyukansu.

Wannan na haifar da damuwa bisa la’akari da cewa zai jefa al’ummar kasar cikin matsalar karancin man fettur da kuma tashin farashin man fetur.

Ana dai ci gaba da kiyasta hasarar da guguwar mai tafe da ruwan sama ta haifar.

Kwararru a kan harkokin Inshora kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, suna cewa babu mamaki wannan bala’i ya kasance wani mafi girma da Amurka ta taba shaidawa.

Idan akayi la’akari da cewa guguwar Katrina ta haifar da hasarar kimanin dala biliyan 15 da ambaliyar ta haifar a jihar Liousiana.

Magoya bayan Barca na son shugabanta ya sauka


BarcelonaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A bana ne Real Madrid ta doke Barcelona 5-1 gida da waje a Spanish Super Cup

Bikin gabatar da sabon dan kwallon da Barcelona ta saya, Ousmane Dembele ya ci karo da cikas, bayan da magoya bayan kungiyar suka yi ta rera wakokin neman shugabanta ya yi ritaya.

Dembele mai shekara 20, ya zama na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin tamaula a duniya kan fam miliyan 135.5, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain da murza-leda kan fam miliyan 200.

Bikin ya ci karo da cikas bayan da aka yi jinkirin sa’a biyu, sakamakon rashin samun takardun rijistar dan kwallon daga Dortmund.

A lokacin ne magoya bayan Barcelona 18,000 suka rinka busa usur da rera wakokin cewar Bartomeu ya yi ritaya.

Mahukuntan Barca na shan matsi kan yadda kungiyar ke koma-baya a wasanninta da kuma sayar da Neymar da aka yi zuwa PSG.

Taron bikin bai kai yawan magoya bayan Barcelona 50,000 da suka tarbi Neymar a Nou Camp a shekara hudun da suka wuce ba.

Liverpool ta sayi Keita mafi tsada a tarihi


LiverpoolHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sai a ranar 1 ga watan Yulin 2018 Keita zai koma Anfield da taka-leda

Liverpool ta amince ta sayi dan kwallon Leipzig, Naby Keita a matsayin mafi tsada a kungiyar, amma sai a ranar 1 ga watan Yunin 2018 zai koma Anfield.

Liverpool ta yadda ta biya fam miliyan 48 kudin da Leipzig ta gindaya idan yarjejeniyarsa ba ta kare da kungiyar ba, kuma zai koma Anfield da taka-leda a badi.

Jurgen Klopp ya dade yana zawarcin Keita daya daga cikin ‘yan kwallon da ya so ya saya a bana, amma Leipzig ta ki amince wa ya bar Jamus a bana.

Kudin da Liverpool za ta sayi Keita ya dara fam miliyan 35 da kungiyar ta dauko Andy Carroli daga Newcastle United.

Liverpool za ta taya Lemar fam miliyan 60


LiverpoolHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Thomas Lemar ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasa biyar

Liverpool na shirye-shiryen taya dan kwallon Monaco, Thomas Lemar kan fam miliyan 60 kafin a rufe kasauwar saye da sayar da ‘yan wasan tamaula a ranar Alhamis.

Jorgen Klopp ya dade yana bibiyar wasan Lemar mai shekara 21, amma har yanzu Liverpool ba ta tuntubo Monaco ba kan cinikin dan wasan.

Sayan Lemar da Liverpool ke son yi, bai shafi makomar Philippe Coutinho a Anfield ba.

Liverpool ta ki sallama tayi uku da Barcelona ta yi wa dan kwallon Brazil da kudi ya kai fam miliyan 114.

Barcelona ta kammala sayen Dembele


BarcelonaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ta gabatar da Dembele a gaban magoya bayanta a Nou Camp a ranar Litinin

Barcelona ta kammala daukar Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 96.8 daga baya zai kai fam miliyan 135.5 idan aka hada da tsarebe-tsarabe.

Dan wasan mai shekara 20 dan kwallon Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Nou Camp a gaban shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu a ranar Litinin.

Dembele shi ne na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain daga Barcelona kan fam miliyan 200.

Barcelona ta ce ta gindaya kudi fam miliyan 400 ga duk kungiyar da ke son sayen dan kwallon idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Nou Camp.

Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a Barcelona.

Dortmund ta maye gurbin Dembele da Yarmolenko


DortmundHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yarmolenko ya koma Dortmund domin ya maye gurbin Dembele

Borrusia Dortmund ta dauki Andriy Yarmolenko kan yarjejeniyar shekara hudu, domin ya maye gurbin Ousmane Dembele wanda ya koma Barcelona da taka-leda.

Yarmolenko mai shekara 27 wanda ya buga wa Dynamo Kyiv wasa 228 daga tsakanin 2008 zuwa 2017 ya ci mata kwallo 99, ya sauka a Signal Iduna Park filin wasa na Dortmund.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Ukraine wanda ya fara buga wa tamaula tun yana da shekara 19, ya yi mata wasa 68 kuma ya ci kwallo 29 kawo yanzu.

Dambele ya koma Barcelona kan fam militan 135.5 a matsayin wanda ta dauka mafi tsada a bana, kuma na biyu da aka saya kudi da yawa bayan Neymar da ya koma PSG daga Barcelona.

Ban mayar da Osinbajo saniyar-ware ba — Buhari


Buhari da Osinbajo da KyariHakkin mallakar hoto
Presidency

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce mataimakin Shugaba Buhari na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, kuma ba a mayar da shi saniyar-ware ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.

Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buharin ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, bayan da wata jarida ta ce tun bayan dawowar Shugaba Buhari daga jinya wasu daga cikin ‘yan fadarsa da suka yi baba-kere sun ware Farfesa Osinbajo inda ba a damawa da shi a harkokin gwamnati.

“Wannan magana karya ce da jita-jita, maganganu ne marasa tushe da ake kirkiro don ganin an shiga tsakanin wadannan shugabanni masu kwazo,” in ji sanarwar.

“Wannan maganar ba abar kamawa ba ce, a ce daga dawowar shugaban kasar cikin mako guda har an fara batun ware mataimakinsa cikin harkokin mulki.

“Abin da nake so a sani shi ne, shi Mr Osinbajo shi ne mutum na kut-da-kut ga shugaban kuma mashawarcinsa na musamman.”

Malam Garba Shehu ya kara da cewa, cikin mako guda da ya gabata bayan dawowar Shugaba Buhari, Farfesa Osinbajo ya halarci tarurruka daban-daban a madadin shugaban, ‘in ban da sallar Juma’a.’

Ya kuma yi nuni da cewar masu yada wannan kalamai na karya suna danganta batun ne da cewa Shugaban Ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, shi ne yake yin ruwa da tsaki wajen gabatar da al’amura a fadar, da kuma kin shigar da Farfesa Osinbajo cikin al’amuran gwamnati.

“Babu wani shugaban ma’aikata ciki kuwa har da shi Abba Kyari, da zai aikata irin wannan abu sannan kuma ya ci gaba da kasancewa kan kujerarsa. Wannan mukami ba ya bukatar yada irin wadannan karairayin,” in ji Garba Shehu.

Ya kara da cewa a lokacin da Shugaba Buhari yake jinya a London, ya bai wa Mr Osinbajo goyon baya sosai, “don kuwa ya san maigidansa Shugaba Buhari ba zai so wani abu mara dadi ya faru ba.”

Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Fadar shugaban kasa ta ce ana kokarin kawo rarrabuwar kawuna ne tsakanin manyan na hannun damar Shugaba Buharin biyu

“Ni ina ganin Abba Kyari na samun matsala da mutane ne saboda yana son ubangidansa sosai, ba zai dinga bai wa mutane kudi kawai don ya faranta musu rai ba.

“A takaice ma Abba Kyari kudi ba sa gabansa, don ya ki karbar naira miliyan 200 da ake bai wa ofishinsa duk wata don tafiyar da al’amura. Don yana ganin ba a bukatar wannan makudan kudin don tafiyar da al’amuran ofishin nasa,” a cewar Garba Shehu.

Dama dai ko a karon farko da SHugaba Buhari ya tafi jinya Birtaniya, an sha yada maganganu irin wadannan da ke cewa wasu ‘yan fadar shugaban kasar ba goyon bayan mataimakin shugaban, yayin da wasu kuma ke cewa suna hakan ne don Mr Osinbajon ya fi Shugaba Buhari iya rike mulkin kasar.

Kenya ta haramta amfani da leda


Leda na gurbata muhaliHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jakar leda matsale ce

A fadin kasar Kenya, an haramta amfani da leda.

Dokar haramcin za ta fara aiki ne daga yau Litinin, kuma duk wanda aka kama da jakar leda zai ya bawa aya zakinta.

Wannan haramci ya shafi masu sarrafa ledar a kamfanoni da masu sayarwa ga jama’a da ma jama’ar da ake sayarwa ledar domin saka kaya ko kuma yin wata bukata ta daban.

Daga wannan lokaci , yin mu’amala da ledar a kasar ta Kenya zai sa mutum ya fuskanci tarar da za ta kai dala 38 ko kuma yi zaman wakafi har na tsawon shekaru 4 tare da yin aikin karfi.

Ministan ma’aikatar kare muhalli a kasar, Judy Wakhunghu, ya sanar da cewa, wannan haramci zai taimaka gaya wajen kare muhalli.

To sai dai wani hanzari ba gudu ba, masu sana’ar ledar da ke sarafata a kamfanoni da kuma masu sayarwa ga jama’a, sun ce wannan haramci zai sa dubban mutane su rasa aikin yi a.

Kazalika sun shigar da kara a babbar kotun kasar domin kalubalantar matakin da gwamnatin ta dauka.

To amma kotun ta yi watsi da karar da suka shigar a gabanta .

Akwai dai kasashen da suka haramta amfani da ledar kamar Rwanda da kuma Eritrea.

Niger : Ambaliyar ruwa ta yi barna a Yamai


Ruwan sama sun yi gyara a YamaiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ambaliya ruwan sama a Niamey jumhuriyar Niger

Mutane 16 sun mutu daga watan Yuni zuwa yanzu sanadiyar ambariyar ruwan sama a birin Yamai na jumhuriyar Nijar.

Hukumomin kasar sun yi kira ga jama’ar da ke zaune a kewayen wuraren da ruwan sama ke wa barazana da su gaggauta barin gidajensu.

Ruwan saman da ake yi kamar da bakin kwarya, ya sa an samu mummunar ambaliya a wasu unguwani na birnin, ganin cewa jama’a sun yi gine-gine a kan tsoffin magudanan ruwa.

Bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin na Yamai, wadanda masana kimiyya suka kiyasta cewa, yawan ruwan ya haura milimita 100 , kwatankwacin sama da inci 4, kuma ruwan ya zuba ne a cikin sa’o’i kalilan.

Hakan ne ya hadasa ambaliyar da ta yi sanadiyar faduwar wasu gidaje a ranar Asabar a wasu shiyoyi na birnin Yamai, inda har wani magidanci da dan sa suka rasa ransu.

A yanzu haka gidaje da dama da aka gina a kan tsofaffin magudanan ruwa a wasu unguwani kamar Guntu Yena, da suke bakin kwazazaben kogin kwara wato gulbin Isa -Fleuve Niger, sun cika makil da ruwa, inda su ke fuskantar hadarin faduwa.

Ruwan saman ya yi sanadiyyar rusa da gidaje sama da 300 tare da jikkata mutane da dama a kauyen Gabagura da ke yammacin birnin na Yamai.

Yanzu haka mutane da dama na fakewa wa ne a cikin azuzuwan wasu makarantun boko.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ambaliyar ruwa a Niger

Tuni dai mahukunta a birnin na Yamai, su ka yi kira da babbar murya ga wadanda ke zaune har yanzu a wuraren da ke fuskantar ambaliyar da su tattara na su ya na su su bar wuraren.

Rahotanni sun sanar da cewa tun farkon damunar bana zuwa yanzu, adadin mutanen da suka mutu a hukumance, sanadiyar ambaliyar ruwa a fadin kasar ta Nijar , sun kai mutun 41, kuma sama da 68, 000 ne lamarin ambaliyar ya shafa.

A bara kuma a dai-dai wannan lokaci, ambaliyar ta kashe mutum 50, tare da tagayyarar wasu 145, 000, musaman a yankin Tahaoua da Agadez, duk da cewa yankunane na hamada masu kekasashshen yanayi.

Mun kusa murkushe 'yan Boko Haram— Kuka Sheka


Sojojin Najeriya sun ce suna samun nasara a yakin da suke da Boko HaramHakkin mallakar hoto
NIGERIAN ARMY TWITTER

Image caption

Sojojin Najeriya sun ce suna samun nasara a yakin da suke da Boko Haram

Makonni bayan da gwamnatin Najeriya ta umarci manyan hafsoshin sojin kasar su koma birnin Maiduguri da zama a ci gaba da yaki da Boko Haram, ganin yadda ake samun karuwar hare-haren kungiyar, rundunar sojin Najeriyar na cewa wannan mataki ya fara yin tasiri sosai.

Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, shi ne kakakin rundunar mayakan kasa ta Najeriyar ya shaidawa BBC cewa, kamar yadda ake gani rundunar ta su ta yi kokari wajen kakkabe ‘yan Boko Haram, abin da ya rage kalilan ne kawai.

Ya ce yanzu sun bullo da wasu sabbin dabaru da kuma kayan aiki domin samun nasara a yakin da rundunar sojin ta ke da ‘yan Boko Haram.

Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya kuma yi karin bayani a kan inda aka kwana a umarnin da aka ba su na cewa ko su kamo Shekau ko kuma su kasheshi cikin kwana 40, inda ya ce suna nan suna kokari dai-dai gwargwadon hali.

Ya ce akwai wata rundunar da suka kebe daga cikin sojojin na su wadanda aka basu horo na musamman da kuma makamai, kuma da taimakon sojan sama na Najeriya ana kai farmaki duk inda ake zaton akwai ‘yan ta’adda.

Birgediyan ya ci gaba da cewa, kafin cikar wa’adin da aka dibar musu, za’a samu cimma buri.

Sanata Misau ya sa zare da 'yan sandan Nigeria


Sanata Misau

Image caption

Sanata Misau yana mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya ne a majalisar dattawan Najeriya

Wani dan majalisar dattawa a Najeriya ya zargi rundunar ‘yan sandan kasar da karbar na goro kafin ta yi wa wasu daga cikin jami’anta karin girma.

Sanata Mohammaed Hamma Misau wanda yake wakiltar shiyyar jihar Bauchi ta tsakiya, ya yi zargin cewa: “ana karbar kimanin naira miliyan biyu da rabi a wurin jami’an ‘yan sanda da ke bukatar karin girman.”

Sai dai zargin da dan majalisar ya yi bai yi wa runduar ‘yan sandan kasar dadi ba, domin kuwa sau biyu tana fitar da sanarwa musanta faruwar hakan.

Da farko dai sanatan, ya yi ikirarin cewa a matsayinsa na tsohon jami’in rundunar ya samu korafe-korafe daga manya da kananan jami’an ‘yan sanda wadanda suka yi zargin cewa sai mai uwa a gindin murhu ko kuwa wanda aljihunsa ke cike da naira ake yi wa karin girma.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta gayyaci sanatan domin ya yi mata karin bayani a kansa, amma ya ki zuwa, kamar yadda kakakin rundunar CSP Jimoh O. Moshood ya shaida wa BBC.

Ya ce, “ba gaskiya ba ne cewa rundunar ‘yan sanda na karba cin hanci kafin ta yi wa jami’anta karin girma.”

“A lokacin da ya fara yin wannan zargi, sai da babban sufeton ‘yan sanda ya kafa kwamiti na musamman domin ya duba batun sannan aka gayyace shi sau biyu domin ya bayar da ba’asi amma ya ki zuwa,” in ji rundunar ‘yan sandan.

CPS Moshood ya kara da cewa “duk da haka sanatan Misau ya ci gaba da bata wa rundunar ‘yan sandan suna saboda cimma wata bukatarsa ta siyasa, shi ya sa a cewarsa ya fito da sabon zargi cewa babban sufeton yan sandan ya wawure naira biliyan 10 na kudin shigar da ‘yan sandan suka samu.”

Sai dai dan majalisar dattawan ya ce bai kai kansa gaban kwamitin ba ne saboda ba a bi ka’ida ba wajen kafa shi.

Sau da dama dai ana zargin hukumomin gwamnatin Najeriya wurin karbar na goro kafin ko dai su dauki mutum aiki ko kuma su kara masa mukami, zargin da suka sha musantawa.

Yadda Alasan Dantata ya ci ribar fam 9000 a shekarar 1901


Alhaji Hassan Sanusi Dantata jika ne ga hamshakin attajirin nan Alhaji Alasan Dantata wanda ya yi wa BBC karin bayani game da tarihin marigayin.

Alhaji Hassan shi ne ya rubuta littafin tarihin attajirin kuma ya bayyana irin gwagwaryamar da ya sha a fannin kasuwanci a tsakanin shekarun 1880 zuwa 1955.

Za ku iya sauraren cikakkiyar hira da Ahmad Abba Abdullahi ya yi da jikan dan kasuwan, idan kuka latsa alamar lasika da ke sama.

Liverpool ta lallasa Arsenal da ci 4-0


'Yan wasan LiverpoolHakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa takwaranta ta Arsenal da ci 4-0.

Roberto Firmino ne ya fara daga ragar Arsenal minti 17 da fara wasa.

Yayin da Sadio Mane ya kara kwallo ta biyu minti biyar kafin zuwa hutun rabin lokaci.

Sai Mohamed Salah da ci tasa kwallon a minti na 57.

A minti na 77 kuma Daniel Sturridge shi ma ya ci tasa.

Messi ya ci kwallo sama da 350 a La Liga


BarcelonaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Messi ya ci Sevilla kwallo 23 a gasar La Liga yayin da ya ci Real Madrid 22

Dan wasan Barcelona da tawagar kwallon kafa ta Argentina Lionel Messi ya ci kwallo sama da 350 a gasar La Liga.

Dan wasan ya ci 349 kafin ya kara biyu a karawar da Barcelona ta ci Deportivo Alaves 2-0 a ranar Asabar a wasan mako na biyu a gasar ta La Liga a ranar Asabar.

Messi ya zama na biyu da ya fi cin kwallaye da yawa a kungiya daya tsakanin manyan gasar kwallon kafa ta Turai, bayan Gerd Muller da ya ci wa Bayern Munich kwallo 365.

Cikin kwallo 351 da ya ci a La Liga, guda 274 da kafar hagu ya ci sannan ya zura 63 a raga da kafar dama, kuma 14 da kai ya ci su.

Messi ya ci Espanyol a kakar wasan 2007 da hannu, an kuma karbi kwallon a cikin wadanda ya ci da kai.

Haka kuma Messi ya ci guda 200 a Nou Camp, sannan ya zura 151 a raga a wasannin da ya buga a waje.

Ga jerin kwallayen da ya ci a kakar La Liga:

 • 2004-05: 1
 • 2005-06: 6
 • 2006-07: 14
 • 2007-08: 10
 • 2008-09: 23
 • 2009-10: 34
 • 2010-11: 31
 • 2011-12: 50
 • 2012-13: 46
 • 2013-14: 28
 • 2014-15: 43
 • 2015-16: 26
 • 2016-17: 37
 • 2017-18: 2

Ga jerin kungiyoyin da ya fi zura wa kwallo:

 • Sevilla: 23 goals
 • Atletico Madrid: 22
 • Valencia: 21
 • Osasuna: 21
 • Deportivo La Coruna: 17

Ra'ayi: Mene ne matsayin addinin Musulunci game da sakin aure?


Ranar Talatar nan ce kotun koli a Indiya ta zartar da hukuncin da ya hana wa Musulmin kasar yi wa matansu saki uku a tashi guda. Ko mene ne matsayin addinin Musulunci game da saki? Ya matsalar take a yankunanku? Ko akwai yiwuwar kafa irin wannan doka ta Indiya? Wasu daga cikin batutuwan da muka tattaunawa ke nan a filinmu na Ra’ayi Riga.

Chelsea ta ci Everton a ruwan sanyi


PremierHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chelsea ta hada maki shida a wasa uku da ta yi a gasar Premier ta bana

Chelsea ta doke Everton da ci 2-0 a wasan mako na uku a gasar Premier da suka kara a Stamford Bridge a ranar Lahadi.

Chelsea ta ci kwallo ta hannun Cesc Fabregas tun kafin aje tuhu, kuma bayan da aka dawo ne ta kara na biyu ta hannun sabon dan wasan da ta saya a bana Alvaro Morata.

Chelsea ce ta mamaye wasan da kaso mafi rinjaye, kuma karawa ta biyu kenan da kungiyar ta yi nasara a gasar ta Premier kakar nan, bayan doke ta da Burnley ta yi a wasan farko.

Kuma Chelsea ta kai hare-hare da dama ta hannun Victor Moses da Pedro a fafatawar.

Wasan hamayya na uku kenan da Everton ta buga a kwana bakwai, kuma ta kasa yin nasara a fafatawa 23 da ta yi a Stamford Bridge kenan.

Chelsea za ta ziyarci Leicester City a wasan mako na hudu a gasar ta Premier, ita kuwa Everton za ta karbi bakuncin Tottenham.

Guardiola ya bukaci dalilin jan katin Sterling


Man CityHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester City ce ta ci Bournemouth 2-1 a wasan mako na uku a Premier a ranar Asabar

Koci Pep Guardiola ya bukaci hukumar kwallon Ingila ta yi masa karin bayani kan dalilin da ya sa aka bai wa Raheem Sterling jan kati a karawa da Bournemouth.

Raheem Sterling ne ya ci wa Manchester City kwallo na 2-1 a gasar Premier a ranar Asabar, daga nan ya ruga cikin magoya bayan City domin su taya shi murna.

Nan da nan alkalin wasa, Mike Dean ya daga masa katin gargadi na biyu kuma daman ya yi laifi a baya can, dalilin da ya sa ya ba shi jan kati nan take kenan.

Guardiola ya shaidawa BBC cewar ”Ni bai gane ba, ina fatan za su kirani su yi min bayani kan dalilin da aka ba shi jan katin”.

Gebriel Jesus ne ya fara ci wa City kwallo daga baya Charlie Daniels ya farke wa Bournemouth.

Damben Shagon Mada da Shamsu Kanin Emi


Turmi biyu suka taka tsakanin Shagon Mada daga Kudu da Shamsu Kanin Emi daga Arewa kuma babu kisa a safiyar Lahadi a Abuja.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Daya daga wasannin da aka dambata a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a safiyar Lahadi a Abuja, Nigeria.

Sauran wasannin da aka yi canjaras aka tashi:

 • Shagon Shagon Dan Kanawa daga Kudu da Shagon Bahagon Sanin Kurna daga Arewa
 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Dan Sama’ila daga Kudu
 • Shagon Mai Keffi daga Kudu da Garkuwan Mutanen Karmu daga Arewa
 • Bahagon Dan Sama’ila daga Kudu da Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa
 • Dan Hussaini daga Arewa da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu
 • Aliyun Langa-Langa daga Arewa da Bala Shagon Kwarkwada daga Kudu
 • Dogon Aleka daga Kudu da Shagon Mafarauta daga Arewa
 • Sani Mai Kifi daga Arewa da Dan Daba Shagon Sikido daga Kudu

China na bautar da yaran Afirka wajen tallace-tallace


Children pose for a group picture behind a black board.Hakkin mallakar hoto
Featured on Taobao

Image caption

Hoto guda yana kai wa dala daya zuwa hudu

Hanyoyin yin sayayya na intanet a China wato Taobao sun kawar da ‘yan tallan da ake ce-ce -kuce a kansu, wadanda suke daukar bidiyo da hotunan yaran Afirka masu yin talla, hakan ya biyo bayan korafin da ake samu a game da cin zarafi.

A China masu sayen kaya suna biyan kudin talla da yaran Afirka suke yi don jayo hankalin mutane.

Alibaba wanda shi ne mai kamfanin Taobao ya ce sun dauki mataki a kan kawar da wadannan masu ciniki.

Ya shaida wa BBC cewa, “Muna sane da irin wadannan mutane da suke tallata hajarsu a shafin cinikin Taobao , kuma tuni muka dauki mataki a kan kawar da su kuma zamu ci gaba da yin haka”.

Ba mu sani ba ko mahukunta za su dauki mummunan mataki a kansu, wanda ya kawo mahawara a kan batun da kuma shafikan sa da zumunta na zamani,

Tun da farko an tabbatar da Taobao na gudanar da bincike kan wasau daga cikin masu cinikin.

Hakkin mallakar hoto
Featured on Taobao

Image caption

Yaran sun rike alluna suna tallan kamfanoni da kayayyaki a China

Wannan hotunan yaran ne rike da allo suna cewa, “Idan kana bukatar mota bashi ka zo kamfanin Brother Long. Ka tara kudi, ka rabu da takaici. Za ku samu farin-ciki a wurinsu”.

A wani allon kuma,” Idan kana bukatar keke ka zo kamfanin Red Star, ku amince da mu”.

Ya kuma tabbatar da cewa tallan hanya ce ta samun kudi kuma yana janyo hankalin masu sayan kaya.

Da aka tambaye shi ko kudin da ake bayarwar yana isa ga yaran sai ya ce,”Me ya sa zan damu kaina haka? Na fi damuwa da harkar kasuwancina”.

Hakkin mallakar hoto
Taobao

Image caption

Wadansu yaran Afirka na rike da allon talla

Wasu daga cikin masu tallan Taobao sun zana wadannnan bidiyon a shafukansu, inda suke cewa yawancin kudin na tafiya a wurin yaran.

Sai dai a gaskiya yanayin yana da matukar rikitarwa fiye da yadda aketunani.

Jaridar Beijing Youth Daily ta tuntubi wani mai daukar hoton inda ya ce, abinci kadan ake ba wa yaran ko kuma a ba su kudin da ba su taka-tara ba a matsayin ladansu.

Wata mai bincike a hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar William Nee, ta bayyana yadda ake gallazawa yaran.

“A gaskiya wannnan ganganci ne, domin za a iya cin zarafin wadannan yaran. A kwai yaran da suke aiki ta hanyar rike irin wadannan hoyunan. Daga hasashen da hukumar kare hakkin dan Adam ta yi, tana iya yiyuwa daya daga cikin babban kalubalen da za a fuskanta shi ne cin zarafin yaran”.

A bara ma tallan wani sabulun wanki ya jawo hargitsi da wani dan Chinar. Mai kamfanin Qiaobi ya ce bai gano cewa ba ‘yan kasar ba ne har sai da ce-ce kuce ya barke.

Kuma tun shekarar 1990 ma, kamfanin man goge baki Darlie sunan wani gida ne a China, da China sunan yana nufin “man goge bakin bakar fata”.

Mr Nee ya karfafa cewa, “Hakan yana nuna wasu daga cikin bambancin al’adu…….musamman idan ka zo bakar fata a Afirka”.

Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya


Wasu daga cikin kyawawan hotuna daga ko’ina cikin nahiyar Afirka da kuma na ‘yan Afirka dake zaune a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

A picture taken on August 19, 2017 shows a woman wearing a decorative attire during the annual Chale Wote Street Art Festival at James town in Accra.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A babban birnin kasar Ghana kenan, inda wata mace ta caba ado a kan titin Chale Wote gabanin fara bukukuwan al’ada

hoton da aka dauka ranar 19, ga watan Agusta 2017 a bikin gargajiya da aka gudanar a birnin Accra.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Daruruwan masu wasan kwaikwayo na cikin gida da na kasashen waje ke nishadantar da dandazon ‘yan kallon da suka halarci bukuwan da aka gudanar ranar Asabar da wasanni daban-daban

wasu mata na rungumar junansu a bikin gasar dafa dukar shinkafa da aka gudanar a birnin Lagos, ranar 20 ga watan Agusta 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Haka kuma a wannan ranar ce wadannan matan ke wasa a bikin dafa-dukar shinkafa a birnin kasuwanci na Lagos da ke tarayyar Najeriya, an shirya bikin ne domin bayar da dama ga masoya da su dandana ko wacce irin dafa-dukar shinkafa a yankin yammacin Afirka, domin gano kasar da ta fi iya hada dafa-dukar.

magoya bayan jam'iyya mai mulki ta MPLA a babban birnin kasar Angola suke gangamin yakin neman zabe ranar 19 ga watan Agusta 2017.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A ranar Asabar ne kuma magoya bayan jam’iyya mai mulki ta MPLA a babban birnin kasar Angola suke gangamin yakin neman zabe. Ana sa ran dan takarar jam’iyyar ne Joao Lourenco zai zama shugaban kasar na gaba, bayan da shugaba mai ci Jose Eduardo dos Santos ya yanke shawarar sauka bayan shafe shekara 38 yana kan karagar mulki.

hotunan magoya bayan Isaias Samakuva (not pictured), dan takarar jam'iyyar UNITA rike da bakin zakara, wanda shi ne alamar jam'iyyar.a gangami na karshe na yakin neman zaben kasar a birinin Luanda na AngolaHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A rana ta biyu kuma magoya bayan babbar jam’iyyar adawa da Isaias Samakuva ke yi wa takara suka gudanar da nasu gangamin rike da bakin zakara, wanda shi ne alamar jam’iyyar ta Mista Samuka.

Magoya bayan dan takarar jam'iyyar adawa na kasar Kenya Raila Odinga kenan ke zanga-zanga a birnin Nairobi ranar Juma'a.,Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A nan kuma magoya bayan dan takarar jam’iyyar adawa na kasar Kenya Raila Odinga na zanga-zanga a birnin Nairobi ranar Juma’a. ‘Yan adawar sun zargi ‘yan sanda da amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zangar bayan zaben kasar ranar 8 ga watan Agusta. ‘Yan sanda dai sun karyata wannan zargin.

Gwamnonin jihohin Najeriya sun tarbi shugaban kasar Muhammadu Buhari a babban filin jirgin saman kasar da ke Abuja, ranar 19 ga watan Agusata, 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Asabar da ta gabata ne wasu gwamnonin jihohin Najeriya suka tarbi shugaban kasar Muhammadu Buhari, a filin jirgin saman babban birnin tarayyar kasar Abuja, bayan dawowarsa daga jinyar da ya kwashe sama da wata uku yana yi a Birtaniya.

Ranar Asabar kenan mazauna birnin Ouagadougo babban birnin kasar Burkina Fasso ke gudanar da zanga-zanga rike da kwalaye da ke dauke da sakonnin dake cewa "ba ma son ta'addanci".Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ranar Asabar kenan inda mazauna birnin Ouagadougo babban birnin kasar Burkina Fasso ke gudanar da zanga-zanga rike da kwalaye da ke dauke da sakonnin da ke cewa “ba ma son ta’addanci”. Bayan da aka yi zargin cewar ‘yan ta’adda ne suka kaddamar da hari kan sanannen gidan abinci na Turkish Restaurant da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum 18 ranar 13 ga watan Agusta.

An dauki wannan hoton ne ranar 15, ga watan Agusta 2017, a kusa da kan iyakar kasar Chadi da Kamaru.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A wannan hoton kuma da aka dauka rana Juma’ar da ta gabata, yara ne ke wasa a kogin Chari da ke N’Djamena babban birnin kasar chadi

A ranar Juma'ar ta gabata kenan wasu iyaye a birnin Alqahirar kasar Masar ke koya wa jaririnsu ninkaya a ruwa a wata makaranta irinta ta farko a kasar, ranar 15, ga watanm Agusta 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Juma’ar ta gabata kenan wasu iyaye a birnin Alqahirar kasar Masar ke koya wa jaririnsu ninkaya a ruwa

Hotuna daga AFP da EPA da Getty Images da kuma Reuters

An fara kallo a Cinema a Gaza bayan shekara 30


An shafe shekaru da dama ba bu gidajen kallo a Gaza

Image caption

Mutum 300 ne su ka yi kallo a cinemar

A karon farko cikin fiye da shekaru 30, mazauna yankin Gaza da ke Palasdinu sun je gidan kallo wato Cinema.

Gidan kallo na Samer da ke birnin Gaza ne ya haska wani fim na musamman akan yadda Palasdinawa ke rayuwa a gidajen yarin Isra’ila.

Mutane kusan 300 ne suka halarci cinemar domin kallon fim din.

An dai rufe cinemar ta Samer ne tun shekarun 1960, yayinda a shekarun 1980 kuma aka rufe manyan allunan cinemar sakamakon rikicin Intifada da ya barke.

Tun daga wancan lokaci sai dai a rinka nuna fina-finai jefi-jefi a wasu wuraren da ake bayar da haya.

Yanzu haka dai al’ummar Gazan sun ce suna a cigaba da haska fina-finai a Cinemu, saboda debe kewa a nishadi.

Congo: Mutane milyan 4 sun tserewa rikici


Shugaban kasar Congo, Joseph KabilaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban kasar Congo, Joseph Kabila

Tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci sun sa mutane milyan 4 baro yankin kudanci Kasai na kasar Congo.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, ta sanar da cewa a yankin na kudancin Kasai, rade-radi na cewa ana kashe mutane tare da yi wa mata fyade.

Tun dai bayan kisan wani basarake na wata kabila da ke kudancin Kasai ,sojan sa kai ‘yan kabilar suka dauki makamai,Kuma su ke ta arangama da dakarun gwamnatin kasar a wani mataki na mayar da martani kan kisan basaraken dan kabilar su.

Yanayin da masu baro yankunan na su ke ciki bashi da dadin fadi kamar yadda wasu kafofin dillancin labarai suka ruwaito.

Kasar Congo dai ta kasance wani dandalin yake-yake da tashe -tashen hankula da suka ka ki karewa tsawon shekara da shekaru.

Da alamu raguna za su yi kwantai a Nigeria


Ba bu cinikin raguna a NajeriyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba bu cinikin raguna a Najeriya

A dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 7 a gudanar da bukukuwan babbar sallah, a Najeriya raguna na nan jibge a kasuwanni ba bu masu siya .

A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayan Raguna da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwa ba har zuwa yanzu.

Masu sayar da dabbobi a kusuwanni sun ce, duk da kudadan ragunan sun banbanta da na bara ,ba a zuwa ana saya sosai.

Masu siyan ragunan da yanzu suka siya, sun shaidawa BBC cewa, farashin ragunan a bana da sauki idan aka kwatanta da na bara.

A bara dai dai sai da aka kai raguna sayarwa a kasuwanin Jamhuriyar Nijar daga Najeriya sanadiyar tabbarbarewar darajar da kudin kasar wato Naira ya yi.

Tambayar ita ce, shin ko a bana ma saboda rashin cinnkin raguna yayinda Sallah ke karatowa zai sa ‘yan kasuwa fita da ragunan na su zuwa kasashen waje?

Me ya sa mutuwar aure ke da matukar sauki a kasar Hausa?


 • Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yigame da matsalar mace-macen aure, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Wata matashiya wadda ba ta wuce shekara 20 ba ta zo ofishina don ba ni labarin halin da ta tsinci kanta ciki.

Yarinya ce sosai da har kusan cikin bacin rai na tilasta mata ta koma makaranta.

Ta fada min cewa shekarta 22 kuma tana da ‘ya’ya biyu.

Ta yi aure tana da shekara 19, inda ta auri wani mutum a bisa zabin iyayenta.

Na girma na taso inda na yi imani da yarda da bin zabin iyaye, don haka na yi mamaki me zai sa biyayya ta zama matsala.

Ta cire mayafinta ta nuna min tabo kaca-kaca a jikinta kama daga hannunta da wuyanta da bayanta.

Mijinta ne yake mata wannan dukan saboda wai a cewar mijin ba ta iya girka ba, abin ya firgita ni har na yi tunanin neman mijin nata don na ji ta bakinsa.

Wani abin mamaki da na hadu da shi sai ya nuna min lamarin ba wani gagarumi ba ne a wajensa.

Ya gaya min cewa tuni ya auri wata matar kuma ba shi da ra’ayin tsohuwar matarsa da ‘ya’yanta.

Ya shaida min cewa shi fa ya yanke duk wata hulda tsakaninsu don haka ta yi ta kanta kawai.

Zuciyata ta yi matukar nauyi, don haka na fara tunanin nema wa yarinyar nan mafitar da za ta taimaka mata ta tsaya da kafafunta.

Tambayar da ta lullube zuciyata ita ce, “Me ya sa maza ba sa jin wahalar sakin matansu ne?”

Me ya sa al’ummarmu ke nuna halin ko in kula kan al’amuran aure?

Yaya za a yi mutum ya gujewa nauyin da ke kansa kuma al’umma ta nuna ba wani abu ba ne?

Shirin Adikon Zamani zai kawo jerin shirye-shirye kan wannan batu, inda za mu tattauna don amsa wadannan tambayoyi da kuma kokarin kawo mafita don magance yawan mace-macen aure.

Abu ne mai sauki aure ya mutu a arewacin Najeriya saboda kawai gishiri ya yi yawa a miya.

Shin wannan ba abin damuwa ba ne?

Ina farin cikin gabatar muku da Dokta Zahra’u Muhammad Umar ta hukumar Hisba da ke Kano.

Tana da tarin misalai kan irin wadannan matsaloli.

Labarinta da ta ba ni ya sake tsorata ni ba kadan ba kan yadda mutanenmu ke jin saukin yin saki.

Har ina tunanin ko dai dama tun lokacin da za a yi auren ne ba a gina shi kan tafarkin da ya dace?

Ko kuwa dai kawai an mayar da sakin ne abin kwalliya.

Yayin da wasu masu sharhi ke danganta yawan mace-macen aure ga rashin samun tarbiyya tun daga gida, wasu kuwa na dora laifin ne a kan mazajen.

Venezuela ta daura damarar kare iyakokinta


Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, ya ce a shirye suke su kare kasarsu daga duk wata barazanaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, ya ce a shirye suke su kare kasarsu daga duk wata barazana

Gwamnatin Venezuela ta ce dakarunta dubu 200 da kuma fararen hula dubu 700 sun bi sahun atisayen soji na ranar farko da aka yi.

An shirya atisayin ne bayan Amurka ta sanar da sanya takunkumin tattalin arziki a kan gwamnatin shugaba Maduro.

Amurka dai na zargin Mr Maduro da yin mulkin kama karya.

Shugaba Maduro ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, al’ummar Venezuela da ma dakarun kasar, za su rinka kare iyakokinmu da ma martabar kasarmu.

Tun a farkon watan da muke ciki ne, shugaba Trump ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar tura sojoji zuwa Venezuela bisa la’akari da wutar rikicin siyasar da ke ruruwa a kasar dama matsalar da tattalin arzikinta ke fuskanta.

Tamowa ta fara kama 'yan gudun hijirar Najeriya— ICRC


Mata da kananan yara ne suka fi shan wahala a cikin 'yan gudun hijiraHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Miliyoyin ‘yan gudun hijira na fama da kuncin rayuwa

Kungiyar bayar da agaji ta International Committee of the Red Cross, ta ce har yanzu ‘yan gudun hijirar da kungiyar Boko Haram ta fatattaka daga gidajensu a yankin tafkin Chadi na cikin mawuyacin hali.

Kungiyar ta ce ziyarar da ta kai wasu yankuna da bala’in hare-haren boko Haram ya shafa, ta nuna mata cewa akwai sauran rina akaba game da tallafin da ake bai wa ‘yan gudun hijirar, tana mai cewa babu abin da miliyoyon ‘yan gudun hijirar ke so kamar samun zaman lafiya da komawa gidajensu.

Babban jami’in da ke kula da ayyukan bayar da agaji a yankin tafkin Chadi, Mamadou Sow, wanda ya kwashe kwana goma a arewa maso gabashin Najeriya ya shaidawa BBC cewa,halin da ya tarar da ‘yan gudun hijirar na da matukar muni idan akayi la’akari da cewa mutum miliyan biyar daga jihohin Adamawa da Borno da Yobe na matukar bukatar abinci.

Ya ce miliyan biyu daga cikinsu sun bar gidajensu ba su da damar komawa, ba su kuma da damar yin noma da kiwo da kuma kamun kifi.

Mamadou Sow, ya ce ba bu wanda wannan matsala ta fi shafa a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma yankin tafkin Chadi kamar mata da kananan yara, domin zaka ga mace mai shayarwa ko mai ciki amma ta na fama da tamowa, haka yara ma.

A saboda haka yakamata a kara akan taimakon da ake ba su musamman a irin yanayin da ake ciki na damuna.

Jami’in ya ce, duk ‘yan gudun hijirar na samun taimako daga kungiyoyi da dama, dole gwamnatin Najeriya ma ta rubanya abinda ake ba su, bisa la’akari da cewa suma ba a san ransu suka kasance a wannan yanayi ba.

Liverpool za ta karbi bakuncin Arsenal


PremierHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Liverpool tana ta shida a kan teburi, ita kuwa Arsenal tana ta 12

Arsenal za ta ziyarci Liverpool domin buga wasan mako na uku a gasar Premier da za su kara a ranar Lahadi a Anfield.

A wasan farko a gasar da Liverpool ta buga ta tashi 3-3 tsakaninta da Watford, sannan ta ci Crystal Palace 1-0.

Ita kuwa Arsenal ta fara da doke Leicester City da ci 4-3, daga nan ta yi rashin nasara a hannun Stoke City da ci 1-0 a wasa na biyu.

A kakar bara da kungiyoyin biyu suka fafata a gasar ta Premier Liverpool ce ta ci Arsenal 4-3 a Emirates, ta kuma doke ta 3-1 a Anfield.

Da kyar Man United ta ci Leicester City


PremierHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester United ta ci kwallo 10 a wasa biyu, kuma babu kungiyar da ta zura maka kwallo a Premier ta bana

Manchester United ta ci Leicester City 2-0 da kyar a wasan mako na uku a gasar Premier da suka fafata a ranar Lahadi a Old Trafford.

Sai da aka dawo daga hutu ne United ta ci kwallo ta hannun Marcus Rashford da Marouane Fellaini, wadan da suka shiga wasan daga baya.

United ta barar da fenariti ta hannun Remelu Lukaku, inda mai tsaron ragar Leicester City, Kasper Schmeichel ya hana ta shiga raga da sauran hare-hare da United ta dunga kai wa.

Tun farko an yi hasashen cewar United za ta zazzagawa Leicester kwallaye a karawar, ganin a bara a fafatawa ukun da suka yi United ce ta cinye wasannin, daya ma da ci 4-1.

United ta hada maki tara a wasa uku a Premier bana kenan, bayan da ta ci West Ham 4-0 ta kuma doke Swansea ita ma da ci 4-0.

United za ta ziyarci Stoke City a wasan mako na hudu, yayin da Leicester City za ta fafata da Chelsea a Stamford Bridge.

Barcelona ta hada maki uku a Alaves


La LigaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Messi ya ci kwallo biyu a wasa biyu da ya buga wa Barcelona a La Liga ta bana

Deportivo Alaves ta yi rashin nasara a gida da ci 2-0 hannun Barcelona a wasan mako na biyu a gasar La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Barcelona ta ci kwallo ne ta hannun Lionel Messi wanda ya ci ta farko bayan da aka dawo daga hutu a minti na 55 sannan ya kara ta biyu a minti na 66.

Tun farko sai da Messi ya barar da fenariti saura minti shida a tafi hutun rabin lokaci.

Da wannan nasarar, Barcelona wadda ta ci Real Betis 2-0 a wasan farko a Nou Camp ta hada maki shida kenan a karawa biyu a La Ligar bana.

Barcelona za ta karbi bakuncin Espanyol a wasan mako na uku a ranar 9 ga watan Satunba a Nou Camp.

Premier: Everton za ta ziyarci Chelsea


PremierHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Everton tana ta takwas a kan teburin Premier, ita kuwa Chelsea tana ta 11

Kungiyar Chelsea za ta kara da Everton a wasan mako na uku a gasar Premier a ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Chelsea ta sha kashi da ci 3-2 a wurin Burnley a Stamford Bridge a wasan farko a gasar ta Premier, sannan ta ci Tottenham 2-1 a Wembley a wasa na biyu a Wembley.

Ita kuma Everton ta fara cin Stoke City 1-0, sannan ta yi kunnen doki 1-1 da Manchester City, kuma Wayne Rooney ne ya ci mata kwallayen.

A kakar bara a gasar ta Premier Chelsea ta doke Everton da ci 5-0 a Stamford Bridge sannan ta ci ta 3-0 a Goodison Park.

Barcelona ta bai wa Dembele rigar Neymar


BarcelonaHakkin mallakar hoto
Marca

Image caption

Ousmane Dembele shi ne dan wasa na biyu da aka saya mafi tsada a tarihi a bana

Sabon dan kwallon da Barcelona ta saya mafi tsada a bana, Ousmane Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a kungiyar.

Barcelona ta sayi dan wasan ne daga Borussia Dortmund kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 135.5 domin ya maye gurbin Neymar.

Dan wasan ya isa Spaniya a ranar Lahadi, zai kuma saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, bayan an duba lafiyarsa, sannan a gabatar da shi a gaban magoya baya da ‘yan jarida a ranar Litinin.

Dembele shi ne dan wasa na hudu da Barcelona ta saya a bana da suka hada da Paulinho da Nelson Semedo da kuma Gerard Deulofeu.

A cikin watan Agusta ne Neyma ya koma Paris St Germain kan kudi fam miliyan 200, a matsayin wanda aka saya mafi tsada a tarihi a fagen tamaula a bana.

Neymar ya ci kwallo uku a wasa biyu da ya buga wa PSG a gasar cin kofin Faransa ta bana.

An gano zoben zinaren da ya bata a bishiyar karas bayan shekara 13


zobeHakkin mallakar hoto
SUBMITTED PHOTO

Wata tsohuwa ‘yar kasar Canada ta tsinci tsohon zobenta na zinare a jikin wani karas bayan shekara 13 da bacewarsa.

Tsohuwar mai suna Mary Grams, mai shekara 84, ta yi matukar damuwa da bacewar zoben nata a lokacin da take shuka a lambunta a garin a Alberta shekarar 2004.

To sai dai ta ki bayyana wa kowa labarin batan zoben nata, fiye da shekara 10, sai danta kawai.

A kwanakin baya ne surikar tsohuwar ta ji labarin bacewar zoben bayan da ta ganshi a jikin wani karas.

Karas din dai ya fito ne ta tsakiyar zoben, inda ya hakan ya bai wa zoben damar fitowa daga kasa bayan shafe shekaru a boye cikin kasa.

Ta ki bayyayanawa mijinta batan zoben saboda tsoron kada ya yi mata fada, amma kuma ta gaya wa danta.

Ta je kasuwa ta sayo wani zoben makamancinsa, wanda kuma bai kai shi daraja ba, inda ta sanya shi a yatsarta kamar ba abin da ya faru.

“Za a iya cewa na yi ba daidai ba, amma hakan ne mafita kawai,” in ji matar.

Babu wanda ya san abin da ya faru, har sai wannan makon lokacin da surikarta Colleen Daley ta ce tana bukatar karas dpn yin abincin dare.

Hakkin mallakar hoto
SUBMITTED PHOTO

Image caption

Matar ta ji dadin samun zoben

Mis Daley, wacce yanzu ke zaune a gonar da Misis Grams ke zama a baya, ta je gidan gonar ne don debo kayan marmari. Ta gano zoben ne yayin da take wanke karas din da ta debo.

Daga nan sai mijinta wanda daman tuni ya san labarin zoben, ya yi sauri ya kira mahaifiyar tasa.

Yayin da take tuna baya, Misis Grams ta ce ta yi da-na-sanin rashin fada wa mijinta wanda ya rasu shekara biyar da suka wuce, gaskiyar abin da ya faru.

Ta ce mutum ne mai raha, wanda ko da yaushe ke cikin yanayi na raha da farin ciki. Yanzu da ta samu zoben nata, ta ce za ta kara kula da shi sosai.

“Duk lokacin da zan fita, ko zan je wani wuri zan rika boye shi a wuri na musamman. Wannan shi ne abin da zan rika yi,” in ji ta.

Wannan ba shi ne karo na farko ba aka taba tsintar zoben zinare a jikin karas ba. A shekarar 2011, wata mata ‘yar kasar Sweden ta tsinci zoben aurenta bayan shekara 16 da bacewarsa.

Ko Benzema zai koma Arsenal?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Benzema ya koma Madrid ne a shekarar 2009 daga Lyon

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta iya neman dan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema, idan Alexis Sanchez ya bar kungiyar, kamar yadda jaridar Diario Gol ta bayyana.

Tottenham tana zawarcin dan wasan Paris St-Germain (PSG) Serge Aurier a kan fam miliyan 23 gabanin rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan Turai, in ji jaridar Guardian.

PSG ta kammala cinikin sayen Kylian Mbappe daga Monaco da kuma dan wasan tsakiya Fabinho, a cewar jaridar Daily Record.

Kodayake Chelsea tana duba yiwuwar sayen Fernando Llorente na Swansea City, kamar yadda jaridar Daily Telegraph ta wallafa.

Arsenal za ta sayar da Shkodran Mustafi gabanin rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan Turai a ranar Alhamis idan aka samu mai sayensa a kan fam miliyan 35, farashin da suka sayo dan kwallon daga Valencia a bara, in ji jaridar Daily Mail.

Jaridar ta ce Juventus da Inter Milan suna zawarcin dan wasan.

Niger: Manoma da makiyaya na samun horo kan zaman lafiya


An jima ana samun rashin jituwa tsakanin manoma da makiyayaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An jima ana samun rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya

Rikici tsakanin manoma da makiyaya abu ne mai tsohon tarihi a Jumhuriyar Niger.

Tun shekaru da dama da suka gabata, tashin hankali tsakanin bangarorin biyu ya kasance tamkar ruwan dare a yankunan karkara.

Lamarin fada tsakanin manoma da makiyaya yafi gudana ne a a lokacin damuna.

A mafi yawan lokuta barnar da ake cewa dabbobin makiyaya na yi a gonakin manoma da mayar da wurin kiwo gona da dai sauran su, na daga cikin ire-iren abubuwan da ke haddasa rikicin.

Image caption

Manomi a Niger

Shi dai irin wannan rikici da zarar ya wakana sai an samu asarar rayuka da dukiya.

Ganin irin dumbin asarar rayuka da dukiya da ake samu sanadiyar irin wannan rikice-rikice na jahilci a kasar ta Niger, yanzu haka a jihar Damagaram da ke gabas masu kudanci da kuma ta kasance wani yankin da al’ummomin biyu ke zaune a tsakanin su , na bayar da horo ga bangarorin biyu ta yadda za su zauna da juna lafiya.

Image caption

Kiwo tushen arziki

Wata kungiya ce mai suna FENAP ta shirya wannan bayar da horon da nufin taimaka wa bangarorin fahimtar juna, abun da ya gagara shekara da shekaru a tsakaninsu.

Noma da kiwo sun kasance manya-manyan hanyoyin samar da arziki a kasar ta jumhuriyar Niger.

Mene ne zai magance mutuwar al'aura?


Na'urar "The Orgasmatron" (Stuart Meloy)Hakkin mallakar hoto
Na’urar “The Orgasmatron” (Stuart Meloy)

A wannan wata labarai sun bazu a duniya game da rahoton abin mamaki na dashe maballin zunguro dadin jima’i.

Na’urar Orgasmatron mallakar fasahar Dokta Stuart Meloy ce, a wani dan karamin akwati da ake soka wayarsa ta cikin jijiyar laka da ke aikewa da sakon dadi a duk lokacin da mai amfani da ita sha’awa ta bijiro masa.

Ta kan lume cikin ta yadda wannan fasaha ke bijiro da jin dadin ban mamaki.

“Kila kai ne mai neman labarai na shida ko na bakwai da ya kira ni, don haka nike mamakin abin da ke faruwa,” Meloy ya fada mini cikin rudani.

Rudaninsa a bayyane yake. Ba da dadewa ba rahotanni kan na’urar sun kebanta ne a Mujallar Masana Kimiyya ta New Scientist mai shekara 13, wadda ba da dadewa bat a bazu a shafin sadarwar Reddit, wata matattarar alkinta tarihin al’amura masu ban sha’awa.

Tsawon lokaci Meloy ya sha fama wajen neman jan hankalin wadanda za su bayar da tallafin kudin kera na’urar, ba tare da ya yi nasara ba.

Meloy likita ne kuma abokin hadin gwiwar kafa babban asibitin tarairayar zafin ciwo na Advanced Interventional Pain Management, inda ake yi wa masu jin tsananin zafin ciwon magani.

A wannan cibiya ta fara aikin dashen na’urorin lantarki.

Abin da ake likawa a jijiyoyin laka zai ta tura tartsatsi a hankali, a hankali da ke dusashe matsanancin zafin ciwo.

Sai kawai a irin wannan aiki na dashe, wani majiyaci ya bayar da rahoton jin wani abu daban, amma ba mara dadi ba: na’urar ta cusa zakwadin dadi.

Meloy ya fahimci cewa managarciyar fasahar da ke hannunsa na iya zama waraka ga maza da matan da ke fama da mutuwar al’aura.

Bayan shekara 10, lokacin da Meloy ya samu nasara a likitanci, sai aikin na’urar zaburar da jin sha’awar jima’i ta Orgasmatron ta samu cikas.

Daya daga matsalolin shi ne na’urorin lantarki da ake amfani da su za su lakume kudi har Dala dubu 25 ($25,000).

Meloy na da kwarin gwiwar cewa na’urar Orgasmatron za ta iya sarrrafa makamashi kadan na sa’a guda ko wacce rana.

“Harbawa ba kakkautawa na tsawon kwanaki ba ita nike ganin za ta taimaka wajen shawo kan matsalar mutuwar al’aura ba,” in ji shi.

“Wasu daga cikinmu dole su je wurin aiki. “Abin takaici babu abin da zai maye gurbinsa, kuma ya kasa jan hankalin masu kera kayan aikin likitanci su yi guda.

Sai batun biyan kudin dashen na’ura ya taso har ake tunanin wane ne zai biya. “Kamfanonin inshora ba za su biya kudin abin da ake ganin gwaji ne ba,” kamar yadda ya bayyana.

Duk da haka Meloy ya yi wa daruruwan majiyata dashen na’urar don tarairayar shawo kan zafin ciwo (wasu daga cikinsu sun bayar da rahoton kyakkyawan tasiri), don haka dashenta don warkar da rashin kuzarin al’aura keta doka ne.

Duk da zuzuta labarin na’urar da aka yi har yanzu ba ta nuna managarcin tasirin warkar da matsalar mutuwar gaba ba, kuma duk wanda ke tunanin yin karyar zafin ciwo don samunta, to yana tattare da jin takaici.

Don samun amincewar Hukumar kula da ingancin abinci da magani (FDA), Meloy sai ya yi “muhimmin gwaji,” al’amarin da zai ci kudi har dala miliyan shida. “Wannan shi ne kudin da ba ni da su a halin yanzu,” in ji shi.

Kadarkon dadi

Abin mamakin shi ne, Meloy ba shi ba ne mutum na farko da ya yi tunanin cusa maballin dadi a jikin mutum.

A shekarun 1950, wani likitan Amurka, mai suna Robert Gabriel Heath, lokacin da yake kokarin magance matsalar kwakwalwa a sashen nazarin aikin kwakwalwa da sakon intata a Jami’ar Tulane da ke New Orleans.

Heath ya so kirkiro wani abu mai tasiri kamar goshin masarrafar kwakwalwa da ake amfani da shi wajen warkar da hauka wanda har yanzu ana amfani da shi, sannan ba shi da wata illa sosai.

Heath ya gano cewa ta hanyar farfado da mahadar hagu da damar zuciya zai iya zaburar da zakwadin dadi da ke tauye mummunar dabi’ar tashin hankali a wasu marasa lafiyar.

Kuma da zarar an bijiro musu da dadi marasa lafiyar sai su kasance cikin annashuwa.

Daya daga marasa lafiya ya kwashi tartsatsin 1,500 cikin sa’a uku, amma gaba daya sun nuna kyakkyawar samun natsuwa. (Sabanin beraye da aka kwata musu irin aikin, al’amarin da cushen a kashin kai ya kusa kai wa ga sukewa).

An samu rahoton yadda maballin bijiro da dadi na Heath ya sanya aka kawo masa ziyara daga Hukumar leken asiri ta CIA, wadanda suka so sanin ko wannan fasahar za ta iya haifar da zafin ciwo, ta yadda za su yi amfani da ita kan masu adawa da gwamnati ko su rika juya akalar kwakwalwarsu.

Sai Heath ya kori mutumin daga dakin bincikensa. “Idan ina son zama jami’in leken asiri, da na zama dan leken asiri,” kamar yadda ya kwarmata wa jaridar New York Times a hirarsa. “Na fi son zama likita mai maganin cututtuka.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu da suka yi zamani da Heath sun yi tunanin mummunar illar da ke tattare da karya lagon karsashin kwakwalwar dan Adam.

Jose Manuel Rodriguez Delgado, daya daga cikin masu binciken da suka gano dabarar sarrafa jin dadi a kwakwalwar marasa lafiya. Kuma ya ware tartsasin lantarkin kwakwalwa managarciya da ake juya akalarta.

Sai dai tunanin mutane game da cushen kwakwalwa ya tsananta lokacin da ya wallafa littafinsa “Zahirin juya akalar kwakwalwa: hanyar bunkasa tunanin al’umma a shekarar 1969, inda Delgado (a iya cewa ya bayyana karara) ya kwantar da ruruwar kwarmaton salon marubuci George Orwell da aka yi wa na’urar, ya kuma karfafi gwiwar al’umma su rungumi fasahar.

Idan kowa zai amince a yi masa dashe don kawo daukin shawo kan bacin rai da jin zafin ciwo, duniya za ta kasance wuri mai dadi, a cewarsa.

Masu bincike biyu da suka dan yi aiki tare da shi sun yi kwarmaton cewa za a yi amfani da na’urar ne wajen kashe karsashin zanga-zangar bakaken fata a cikin biranen Amurka.

Sai aka daina samun tallafi, sannan bayan samun managartan kwayoyin magani da ke warkar da cutar tabin hankali, sai tartsatsin lantarkin kwakwalwa ya bace tare da dimbin akwakun bijiro da dadi.

Ko da yake Meloy shi ne mafi zakuwa kan alfanun da ke tattare da na’urorinsa, inda amfani da su ke nuni da juya akalar al’umma ba “ita ce manufar aikinsa ba.”

Yana da kwarin gwiwar cewa sabuwar sha’awar na’urar “Orgasmatron” za ta sake bayar da damar tabbatuwarta.

Idan hakan ya kasance, za mu sa ran ganin maballin bijiro da dadi like a jikin mutane? Ba da wuri ba, a cewar Dokta Petra Boynton, mai bincike kan jima’i a Jami’ar Kwalejin Landan.

“Har yanzu ban ga na’urar ba da magunguna ko kayan da ke shawo kan matsalolin jima’i fiye da magungunan bakam (makwafin magani da ba na gaske ba),” a cewarta.

“Na fi damuwa da aikin kawo daukin shawo kan matsalolin da kamata ya yi a ce an magancesu ta hanyar kyautata tunani, ko bayanai kan matsalolin jima’i, da samar da makwafin jin dadi, tare da fahimtar yadda jikinmu ke aiki.”

Don haka idan na’urar “Orgasmatron” ta samu shiga kasuwa, sai ka dauka kawai ka mallaki akwakun bijiro da tartsatsin lantarkin dadi mai karfi manne a kafadarka.

Ga masu son ta’ammali da wanan fasahar kirkira, kawai sai mutum ya yi kokarin sanin wanda ke rike da akalar maballanka.

Wasu maniyyata a Najeriya sun fara fitar da rai da sauke faralli


Wasu maniyyatan bana a Najeriya sun fara kokonton zuwan su kasa mai tsarki domin sauke faralliHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Lahadi ne za a rufe filin jiragen sama ga mahajjatan bana a Saudi Arabia

Yayinda a gobe Lahadi ne ake sa ran hukumomin Saudi Arabia za su rufe filin jiragen sama na Jiddah ga jiragen mahajjatan bana, wasu maniyyata a Najeriya sun fara fitar da rai da zuwa kasa mai tsarki.

Maniyyatan da zuwa yammacin ranar Juma’a ba su samu tashi ba cikinsu ya duri ruwa domin suna ganin kamar za a hau arfar bana ba bu su.

Maniyyatan Jihar Neja ta arewacin Najeriya na cikin wadanda har yanzu ba su da tabbas a kan ko za su samu tashi.

Maniyyatan sun ce ana musu yawo da hankali, domin sai a kira su a kan cewa za su tashi, idan suka zo kuma sai a ce ba haka ba.

Kazalika sun kokawa da cewa har sun fara taba guzurinsu.

To sai dai kuma hukumar jin dadin alhazan jihar ta Neja ta musanta wannan zargin, inda ta ce ta na sa ne da halin da suke ciki kuma za a share masu hawaye.

Matasan arewa sun yi abin da ya da ce — ACF


Matasan arewacin Najeriya sun janye wa'adin ga 'yan kabilar IgboHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matasan arewacin Najeriya sun janye wa’adin ga ‘yan kabilar Igbo

Kungiyar tuntuba ta dattawan arewacin Najeriyar, ta ce tun da matasan suka bayar da wa’adi na cewa al’ummar Igbo su tattara na su ya na su su koma yankunansu kafin 1 ga watan Oktoba mai zuwa, su ke ta tattaunawa da su domin samun maslaha.

A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai a Kaduna, ACF, ta ce matasan sun nuna da’a, da girmamawa ga shugabanninsu da kuma nuna son zaman lafiya a Najeriya baki daya.

Kazalika ACF, ta ce janye wa’adin da matasan suka yi zai rage zaman dar-dar din da aka shiga.

ACF, ta kuma yi kira ga shugabannin kabilar Igbo da su ma su kira matasansu su nuna musu illar wannan fitina da ta ta so.

Duk da janyewar wa’adin da gamayyar kungiyoyin matasan Najeriyar ta yi, ta bayar da wasu sharuda ga gwamnatin tarayyar da kuma gwamnatocin jihohin arewacin kasar.

Sharudan dai sun hada da cewa gwamnatin tarayya ta tanadi dokar da za ta bada dama ga dukkan mai son ballewa ko ficewa ya fice, da kuma gurfanar da Kanu gaban kuliya, sannan kuma kamfanonin da ke aiki a arewacin Najeriya, dole su tanadi guraben aiki da kaso 40 cikin 100 ga matasan yankin.

An harbi wani mahari a Brussels


Wani mutum ne ya kai wa wani jami'in tsaro hari da wukaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani mutum ne ya kai wa wani jami’in tsaro hari da wuka

An harbe wani mutum a tsakiyar birnin Brussels a kasar Belgium bayan ya nemi ya daba wa sojoji biyu wuka, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hotuna daga wajen sun nuna cewa ‘yan sanda sun kebe wurin da al’amarin ya faru da shingaye.

Wani ganau Ryan MacDonald, ya ce ji kara harbin.

Babu tabbacin ko maharin ya tsira ko kuma a’a. Rundunar ‘yan sandan birnin ba ta yi wani karin haske ba game da lamarain ba.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani…

An samu manoma da laifin kisan bakar fata a Afirka ta Kudu


ReutersHakkin mallakar hoto
Reuters

An samu wasu manoma jar fata ‘yan Afirka ta Kudu guda biyu da laifin yunkurin hallaka wani bakar fata, bayan saka shi cikin akwatin gawa da kuma yi masa barazanar kona shi da rai.

Mai shari’a Sheilan Mphakele, ta ce ta bayyana karara mutanen Willem Oosthuize da Theo Jackson na shirin hallaka mista Victor Mlotshwa wanda duka aka kawo so kotun.

Wakiliyar BBC ta ce a dakin kotun da magoya bayan bakar fatar da manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu da dama, mai shari’a Shilan Mphakele ta ce ta gamsu da yadda aka yanke hukuncin fiye da yadda wasu sukai zato.

An kama manoman biyu, bayan wallafa hoton bidiyon yadda suka yi wa mista Victor, a shafukan sada zumunta.

A nasu bangaren a kokarin kare kan su, sun ce wai suna “son koyawa bakar fatar hankali ne, saboda katsalandan din da ya yi musu na shiga gonarsu, amma ba su yi nufin su hallakashi ba.”

Na fi Buhari ba 'yan Nigeria 'yanci — Jonathan


Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jonathan ya kwashe kimanin shekara biyar yana mulkin Najeriya

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mayar da martani ga yunkurin gwamnatin kasar na yin dokar da ta haramta furta kalaman nuna kiyayya tsakanin al’ummomin kasar.

Mista Jonathan ya sake wallafa wani hoto a shafinsa na Facebook wanda ya yake dauke da rubutu kamar haka:

“Ni ne shugaban da aka fi zagi da suka a duniya, amma za a tuna da ni idan na bar mulki saboda cikakken ‘yancin da gwamnatina ta bai wa jama’a,” kamar yadda sakon ya ce.

Ya wallafa wannan sakon ne a shafin ranar Alhamis bayan wallafawar farko a watan Disambar shekarar shekarar 2014.

A makon jiya ne Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ce gwamnati za ta fara daukar amfani da kalaman nuna kiyayya a matsayin ta’addanci.

Hakazalika a jawabin da Shugaba Buhari ya yi wa al’ummar kasar ranar Litinin, ya tabo batun yadda wasu suke kalaman da suke ketara ikokin dokokin kasar a kafofin sada zumunta.

Abin da ya sa wasu ‘yan kasar suke ganin wata kila gwamnati ba ta jin dadin yadda jama’a suke sukarta musamman a kafofin sadarwa na zamani.

A ranar 12 ga watan Agustan nan ne gwamnatin Najeriyar ta ce ta fara shirye-shiryen aike wa da wata bukata zuwa ga majalisar dokokin kasar da ke neman yin dokar da za ta fayyace irin hukuncin da za a yi kan wadanda aka samu suna furta kalaman kiyayya ga wani jinsi a kasar.

Gwamnati ta yanke shawarar yin hakan ne saboda yadda zaman tankiya ke karuwa tsakanin a kabilu da addinai da kuma yankunan kasar daban-daban, inda har wasu ke kiran da a raba ta ko a sake mata fasali.

Europa League: Arsenal tana rukuni da Cologne


EuropaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal za ta kara da Liverpool a wasan mako na uku a gasar Premier

Arsenal tana rukunin da ya kunshi BATE Borisov da Cologne da kuma Red Star ta Belgrade a gasar Europa League da aka raba jadawali a ranar Juma’a.

Wannan ne karon farko a shekara 20 da Gunners, wacce ta yi ta biyar a kan teburin Premier da aka kammala za ta buga gasar ta Europa a bana.

A jawalin da aka raba da ya kunshi kungiyoyi 48, Everton tana rukuni daya da Lyon da Atalanta da kuma Apollon Limassol ta Cyprus.

Za a fara wasannin cikin rukuni a ranar 14 ga watan Satumba:

Ga yadda aka raba kungiyoyin:

Rukunin A: Villarreal, Maccabi Tel Aviv, Astana, Slavia Prague.

Rukunin B: Dynamo Kiev, Young Boys, Partizan Belgrade, Skenderbeu.

Rukunin C: Sporting Braga, Ludogorets, Hoffenheim, Istanbul Basaksehir.

Rukunin D: AC Milan, Austria Vienna , Rijeka, AEK Athens.

Rukunin E: Lyon, Everton, Atalanta, Apollon Limassol.

Rukunin F: FC Copenhagen, Lokomotiv Moscow, Sheriff Tiraspol, FC Zlin.

Rukunin G: Vitoria Plzen, Steaua Bucarest, Hapoel Beer-Sheva, FC Lugano.

Rukunin H: Arsenal, BATE Borisov, Cologne, Red Star Belgrade.

Rukunin I: Salzburg, Marseille, Vitoria Guimaraes, Konyaspor.

Rukunin J: Athletic Bilbao, Hertha Berlin, Zorya Luhansk, Ostersund.

Rukunin K: Lazio, Nice, Zulte Waregem, Vitesse Arnhem.

Rukunin L: Zenit St Petersburg, Real Sociedad, Rosenborg, Vardar.

Barcelona ta dauki Ousmane Dembele


BarcelonaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dembele ya zama dan wasa na biyu da aka saya mafi tsada a bana a tarihin tamaula a duniya

Kungiyar Barcelona ta amince ta dauki dan kwallon Borussia Dortmund, Ousmane Dembele kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 135.5.

Hakan ya sa dan kwallon ya zama na biyu mafi tsada a duniya a tarihin tamaula da aka saya a bana, bayan Neymar da ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 daga Barcelona.

Barca za ta fara biyan fam miliyan 96.8 daga baya ta cika sauran kudin dan kwallon mai shekara 20, wanda ya amince da yarjejeniyar shekara biyar.

Kungiyar ta Spaniya ta ce ta gindiya fam miliyan 400 ga duk kungiyar da ke son daukar Dembele idan kwantiraginsa bai kare da ita ba.

Dan wasan zai ziyarci Spaniya a ranar Litinin domin likitocin Barcelona su duba lafiyarsa.

Dortmund ba ta sallama tayin da Barca ta fara yi wa dan kwallon a baya ba a watan Agusta, har ma ta dakatar da dan kwallon bayan da ya ki zuwa atisaye.

Nigeria: 'Yan PDP sun je duba Shugaba Buhari


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon ziyarar ‘yan PDP ga Buhari

A ranar Juma’a ne shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP da na jam’iyyar APC mai mulki suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a fadar gwamnati da ke Abuja.

Tawagogin sun kai ziyarar ne a lokaci daya da misalin karfe 11 na safe, inda Ahmed Makarfi shugaban jam’iyyar PDP ya jagoranci tawagarsa, John Odigie-Oyegun na jam’iyyar APC kuma ya jagoranci tasa tawagar.

Da yake jawabin yi musu maraba, Shugaba Buhari ya nuna matukar godiyarsa da suka samu lokaci duk da irin ayyukan da ke gabansu, suka je yi masa maraba da dawowa gida.

“Wannan ziyara na nuna cewa Najeriya kasa daya ce mai hadin kai. Ba taron jam’iyya ba ne. Ba taron siyasa ba ne. Alama ce ta hadin kan kasa. Wannan na nuna cewa dimokradiyyarmu ta halin girma ce,” in ji Shugaba Buhari.

Ya kara da cewa, “”Dimkoradiyyar jam’iyyu da yawa ….. Adawa ba ta nufin tashin hankali ko kiyayya ko gaba. Dimkoradiyya na bukatar bangaren hamayya mai karfi amma mai sanin ya kamata.

Shugaban ya kuma bukaci dukkan bangarorin da su mika sakon godiyarsa ga jama’arsu a fadin Najeriya kan addu’o’in da suka yi masa na samun sauki.

Da yake yin nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP Ahmed Makarfi cewa ya yi, “A shirye PDP take ta yi adawa mai ma’ana. Za mu yi hakan ne don mu tabbatar gwamnatin na yin abin da aka zabe ta ta yi domin amfanin Najeriya baki daya.

“Ba za mu taba yi wa wani fatan rashin lafiya ba, ballatana ga mutumin da aka dorawa nauyin shugabantar kasarmu Najeriya.”

Ya kara da cewa, “Muna tabbatar maka da cewa za mu baka hadin kan da duk wata jam’iyyar adawa za ta iya baka, duk kuwa da cewar burin ko wacvce jam’iyyar adawa shi ne ta karbi mulki a hannunta.

Hakkin mallakar hoto
Presidency

'Muna kan bakanmu bera ne ya yi barna a ofishin Shugaba Buhari'


BuhariHakkin mallakar hoto
Garba Shehu Facebook

Image caption

Shugaba Buhari yana aiki ne daga gida tun dawowarsa daga jinya

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ba za ta sauya matsayarta kan uzurin da ta bayar na cewa beraye ne suka yi barna a ofishin Shugaba Muhammadu Buhari ba, wanda hakan ne ya sa zai dinga aiki daga ofishinsa na gida, bayan dawowarsa daga jinyar wata uku a Landan.

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriyar, kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu ne ya sake nanatawa BBC wannan batun, inda ya ce, duk wanda ya san Abuja, to ba abin mamaki ba ne don an ce bera sun yi barna a wani waje.

“Ko wanne dan Najeriya yana da damar ya fahimci abu yadda tunaninsa ya ba shi, amma gaskiyar magana ita ce su wadannan beraye sun lalata wayar na’urar sanyaya daki ta ofishin ne daga waje, har suka samu hanyar shiga ciki,” in ji Malam Garba Shehu.

Tun bayan fadar shugaban ta bayyana cewa shugaban zai rika aiki daga gida maimakon ainihin ofishinsa, saboda beraye da sauran kwari sun yi barna a ofishin, mutane da dama a ciki da wajen kasar sun yi ta shagube da gugar zana da ma kalamai iri daban-daban na nuna shakku a kan maganar.

Ga dai yadda tattaunawar Malam Garba Shehu ta kasance tsakaninsa da abokin aikinmu Muhammad Kabir Muhammad, kan yadda suke ji sakamakon irin maganganu da kallon da ake musu kan wannan sanarwa da suka yi:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Martanin Garba Shehu kan batun bera a ofishin Buhari

Fim ne ya hana ni zama farfesa — Bosho


BoshoHakkin mallakar hoto
Bosho Instagram

Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim ce ta hana shi zama farfesa.

Na samo sunan Bosho ne saboda lokacin da nake makarantar sakandare ina yawaita karatu. Na kan kwashe kwana 40 ban yi cikakken bacci ba saboda yawan karatu.

Shiga ta harkar fina-finai ce ta hana ni zama farfesa,” in ji Bosho, a hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa.

Dan wasan ya ce sha’awarsa wajen karatu ce ta sanya yake amfani da wasu kalmomi na boko a fina-finansa.

“Za ka ji ina yawaita cewa ‘A shekarar 1778 da na je Ingila sarauniya ta bukaci a dafa min shayi amma na ce tuwo nake so’ ko kuma na cewa ‘wane ne ubanka a Northern Nigeria’, in ji Sulaiman Yahaya.

Bosho, wanda ya kwashe fiye da shekara 30 yana fitowa a fina-finan Hausa, ya kara da cewa ya rungumi bangaren barkwanci ne saboda shi dama mutum ne mai yawan son raha.

A cewar Bosho, “Na soma fim tun lokacin da ake wasan kwaikwayo na dandali; ni mutum ne mai son bunkasa al’adun Hausa da addinin Musulinci, shi ya sa na zabi zama dan wasan kwaiwayo.

“Na dauki al’adarmu da matukar muhimmanci kuma na soma fim ne tun lokacin da ake yin wasannin kwaikwayo a Gidan Dan Hausa da ke birnin Kano. ‘Yan wasa irin su Danhaki da Mallam Mamman su ne gwanayena”.

Hakkin mallakar hoto
Bosho Instagram

Image caption

Bosho ya ce yana son fim din barkwanci

Dan wasan na Hausa ya nuna bakin cikinsa kan yadda masu shirya fina-finan Kannywood ba sa mayar da hankali wurin bunkasa al’adar Hausa, yana mai cewa, “hakan ne ya zubar da mutuncinmu a idanun masu kallo”.

Ya kara da cewa saboda irin mummunan kallon da ake yi wa ‘yan fim ya bude kamfanin hada fim wanda zai mayar da hankali wurin tallata al’adun Hausa.

Bosho ya ce akwai dangantaka mai kyau tsakaninsa da marigayi Rabilu Musa Dan Ibro.

“Ibro ya kan taso daga garinsu Danlassan ya zo nan [cikin birnin Kano] mu sha hira; shi mutum ne mai kokarin zumunci.

“Ni ma na kan je garinsu na sada zumunci kuma har yanzu ina ci gaba da zuwa mu gaisa da iyaye da iyalansa. Kafin ya rasu mu kan bai wa juna shawara kan al’amuran rayuwa. Allah ya jikansa”, a cewar Sulaiman Yahaya.

Mene ne yake kawar da sha'awar jima'i ga mata?


mataHakkin mallakar hoto
Getty Images

Barbara Gattuso lokacin tana da shekara 30 da wani abu ta fara ganin ta fara juya wa mijinta baya game da harkar jima’i. “Na daina yi masa magana kan lamarin, domin ban damu da jima’i ba,” a cewarta.

Tsawon shekaru Gattuso, wadda yanzu ta kai shekara 66 ta yi wayon boye wa mijinta don ka da ya zo mata ta ki tara wa da shi kai tsaye; sai ta rika kwanciyar barci da wuri, sannan ta farka kafin ya tashi.

“Bayan wani lokaci hakan al’amarin ya kasance, ko me ke faruwa a nan? Ina son mijina, mun yi auren jin dadi, tare da samun kyawawan ‘ya’ya; ko me ke faruwa?”

Matsalar ta sha’awa ce. Duk da cewa mafi yawan mutanen da suka dade da aure za su tabbatar da cewa karsashin sha’awa kan dusashe tsawon lokaci, Gattuso ba ta ma da sha’awar tarawar jima’i ko kadan. Ba ma ga mijinta kadai ba; ba ta ma sha’awar kowa.

Masana tantance tasirin kwakwalwa kan dabi’ar jima’a sun yi ikirarin cewa irin wannan sauyin bijirowar sha’awar jima’i al’amari ne da aka saba gani, musamman ga mata in sun fara tsufa.

Wasu kuwa na ganin raguwar karsashin sha’awa ciwo ne; sakamakon rashin daidaiton sinadarai a kwakwalwa. Ta yiwu yanzu a samu maganin cutar.

A ranakun 3 da 4 ga Yuni, Hukumar kula da ingancin abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) za ta tattauna da kwararru su bayar da shawar ko amincewa kwayar Flibanserin a matsayin maganin zaburar da son jima’i na mata “female Viagra” don masu larura su yi amfani da shi ko a jefar da shi a kwandon shara.

Matsalar ta raba kan masana gida biyu, inda wadanda suka amince da masu adawa suka jajirce.

Matsalar kewayar sakonni

Ko mene ne ke kawar da sha’awar jima’i, kuma yaya maganin Flibanserin zai taimaka? Ba mata kadai ne ke kyarar jima’i da sun fara tsufa ba; shaharar gagai samfurin ‘Viagra’ wani tabbaci ne kan hakan.

A cewar mai barkwanci George Buirns: “Jima’in mai shekara 90 kamar jikqa igiya a ruwa ne.” Sai dai yanayin matsalar ya bambanta a tsakanin jinsi (maza ko mata).

Akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima’i: sha’awa, sha’awa da sha’awa

“Akwai maganar da ake fada a likitanci cewa matsaloli uku ne ke kashe sha’awar jima’i karfin mazakuta, karfin mazakuta da karfin mazakuta,” a cewar Stephen Stahl, masanin tasirin kwakwalwa kan dabi’u da ke Jami’ar California a San Diego. “Sannan akwai dalilai uku da ke haifar wa mata rashin son jima’i: sha’awa, sha’awa da sha’awa”

Hakikanin abin da ke kashe sha’awa al’amari ne da ya boyu ga masana kimiyya, ko da yake sun fahimci cewa yana da alaka da zagayen sinadarai.

Daya daga mahangar ita ake kira mutuwar gaba ko mazakuta (HSDD) – a mata kuwa ana yi wa lamarin lakabi da dusashewar sha’awar jima’i sakamakon kin kullewar goshin kwakwalwa da ke yin tarin ayyuka a kullum, kamar tunawa da tura sakon ranar haihuwa ko warware matsalolin aiki.

Sakamakon zagayen sinadarai, wadanda ke tarairayar zaburarwa da annashuwa ya kasance a tauye.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Getty Images)

Image caption

Maganin karfin maza

Tun da gaigai din Viagra ya samu nasarar warkar da matsalar jima’in maza (ba tare da ambaton garabasar kamfanin da suka sarrafa shi ba), wasu sun yunkura wajen samar da irin wannan kwayar maganin ga mata, amma wadda za ta shawo kan matsalar kwakwalwa fiye da kafar al’aura.

Flibanserin na daya daga jerin wadanda ke kan gaba.

Da farko an samar da maganin da ke shawo kan dugunzumar damuwa, wanda aka gano tasirinsa kadan ne a kan yanayin mutane. Sai dai matan da aka yi gwajin kwayar magnain a kansu sun bayar da rahoton illar da ba a zata ba; zakuwar son jima’i.

Alamun aikin Flibanserin na nuni da daidaiton sinadaran da ke kewaya kwakwalwa, wato dp[amine da noradrenaline da serotonin.

“Muna jin cewa ko ana daidaita musu zama ko a maye gurbin abin da bai daidaitu ba, ta yadda za su ci gaba da kewayawa,” in ji Stahl.

“Tabbas akwai yiwuwar yana taimaka wa mata wajen kauce wa cibiyar zagayen goshin kwaklwalwa da ke tauye sha’awar jima’i.”

Bijiro da sha’awa

Duk da cewa kwayar maganin an ajiyeta a gefe a matsayinta na mai kawar da dugunzumar damuwa, saboda takaituwar tasirinta, an sake bunkasata don bijiro da sha’awa ga mata da ke fama da mutuwar kafar al’aura (HSDD).

Sai dai an ci gaba da bibiyar gwaje-gwajen, inda mata suka ruwaito cewa ana samun karuwar “gamsuwar jima’i,” sun dai kasa tabbatar muhimmin tasirinta wajen bijiro da sha’awar jima’i.

Sakamakon hakan Hukumar FDA ta ki amincewa da maganin a shekarar 2010.

Ku san a iya cewa Ba’amurkiya kan yi jima’i a kalla sau uku a wata; idan mai fama da larura ba ta yi jima’i sau uku ba, shin ko wannan na nufin kwayar maganin ta gaza?

Nazarin da aka kara yi ya tabbbatar da cewa tana kara zaburar da sha’awar jima’i daga bisani, ko da yake tasirinta ya yi bazata.

“Matsalar dai ita ce, yaya za a kimanta ci gaban da aka samu? Tambayar da Susan Scanlan ta yi, wato Shugabar kun giyar fafutikar kare lafiyar jima’in mata ta Even The Score campaign, wadda ta ciri tuta wajen samar da maganin mutuwar al’aura (HSDD).

(Abin da ya kamata a lura shi ne ta yiwu kamfanoin sarrafa magunguna ya biya Scanlan wani kudi ta ja zugar fafutikarta). Ta yi nuni da cewa tarairayar sauyi ta yi karanci. Kusan a iya cewa Ba-Amurkiya kan yi jima’i akalla sau uku a wata; idan mai fama da larura ba ta yi jima’i sau uku ba, shin ko wannan na nufin kwayar maganin ta gaza?.

A gaskiya matan da ke amfani da kwayar maganin Flibanserin sun bayar da rahoton mu’amalar jima’i sau biyu da rabi cikin kwanaki 28, in an kwatanta da daya da rabi (1.5) na matan da ke fama da mutuwar al’aura (HSDD), wadanda ba sa shan maganin.

Tabbas, wasu daga cikin masu matsalar da aka yi gwajin a kansu sun samu tabbacin gyaruwar lamuran. Gattuso ta shiga jerin wadanda aka yi wa gwajin a shekarar 2011.

Da farko an ba ta makwafin maganin sarrafa tunani (placebo), abin da ta ce bai yi aiki ba, duk da cewa ta yi kokarin zaburar da sha’awar jima’inta.

Sai dai bayan gwaji an ba ta damar yin amfani da maganin gaske. “Cikin makonni kadan na yi matukar samun sauyi,” in ji ta.

“Na kan tashi cikin dare in rungume maigidana. Kasancewar kusancin kud-da-kud da sha’awar makalkale wa juna ya zama 100 bisa 100.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ma’aurata na yawan samun matsala idan daya baya sha’awar yin jima’i, ya yin da dayan ya ke so

Sai dai daya daga cikin abin damuwar shi illolin da ke tattare da nasarorin sun hada da juwa da layi da tashin zuciya. Ko da yake Scanlan ta yi nuni da cewa matsalolin ba su taka-kara sun karya ba, in an kwatanta da na ‘Viagra’ da sauran magungunan shawo kan mutuwar gaba.

“Bari mu bibiyi wasu daga cikin illolin da ke tattare da magunguna 26, wadanda aka amince maza su yi amfani da su don maganin matsalar mutuwar mazakuta,” in ji Scanlan. “Mun ji akwai bugun zuciya da makanta da mutuwar fuju’a da kuma wanda ya fi jan hankalina shi ne, raunin mazakuta.”

Wasu kuwa na fargabar in an amince da Flibanserin za a ingiza mata su rika neman maganin matsalar da kamata ya yi a ce sun warwareta ta hanyar tuntubar mai bayar da shawarar zamantakewar ma’aurata maimakon likita, ko shawo kan matsalolin da suka danganci jibga wa kai dimbin aiki ko dugunzumar damuwar.

“Idan aka yi batun sha’awa, dangantakar ma’aurata na da muhimmanci, yanayi muhimmi ne, daukacin halin da aka samu kai, wanda ya hada da fasalin bayyane da na boye duk suna da muhimmanci,” a cewar Cynthia graham, babbar malama a fannin kula da lafiyar kwakwalwa ta Jami’ar Southampton da ke Birtaniya.

Akwai wadanda ke jin cewa watsi da Flibanserin zai haifar da rudanin neman magani mafi nagarta.

Ko da a hakan ma ta yarda cewa magani zai yi matukar taimakawa a nau’ukan yanayin. “Ina jin cewa wasu mata na fama da matsalar sha’awa, karshe dai sai an samo kwayar maganin matsalar matan.

Sai dai akwai bukatar a tabbatar kwayar maganin na da amfani a likitance, kuma akwai bukatar sanin illolin da ke tattare da ita,” in ji graham.

Wasu na fargabar cewa watsi da Flibanserin zai haifar da rudanin neman makwafin maganin mafi nagarta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Makurar gaci

Tabbas wannan ba matsala ce da kowa ke ganin za a shawo kanta nan da nan, ba tare da la’akari da wasu al’amura ba, wadanda suka hada da gajiyarwa da sauran magunguna da dugunzumar damuwa da matsalolin zamantakewa, wadanda suka kamata a fara shawo kansu tun farko.

“Idan ba ki da sha’awar jima’i, akwai bukatar ki bincika; mijinki ne kadai ko kuwa kina raya sha’awar makwafcinki na kusa, ko rashin sha’awa ce dungurungum? Kwayar magani ba ta warware matsalar zamantakewar aure,” in ji Stahl.

Gattuso ta yarda cewa akwai bukatar tuntubar kwararrun mashawarta in akwai matsalar zamantakewa, amma ta jajirce kan cewa ba lallai tasirin kadan ne wajen gyaran zamantakewar aure.

“Idan kana fama da rashin lafiya kamar ciwon suga, za ka iya yin bayani tun daga safe har dare, sai dai ba za a samu waraka ba,” in ji ta.

“Mutuwar gaba (HSDD) rashin daidaiton sindarai ne a kwakwalwa.”

Masu larura irinta na ganin Flibanserin a matsayin iyakar makurar kai gacin maganinsu. “Lokacin da aka fada mini cewa an yi watsi da kwayar maganin na damu matuka, amma saboda dubban daruruwan mata da ke fama da matsalar,” inji ta. “suna bukatar kwayar maganin.”

An yanka ta tashi a kan maganar wa'adi ga 'yan kabilar Igbo


taswirar Najeriya

Image caption

Taswirar jihohin Najeriya

Gamayyar kungiyoyin matasan Najeriyar nan da su ka ba wa ‘yan kabilar Igbo wa’adi na su bar arewacin kasar kafin ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, sun sanar da janyewar wa’adin da suka bayar .

Hadakar kungiyoyin ta sanar da janye wa’adin ne a wani taro da ta gudanar a Abuja babban birnin tarrayar kasar da yammacin ranar Alhamis.

A dai cikin watan Yuli ne hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Najeriyar suka fitar da wata sanarwa a Kaduna, inda a ciki suka bayar da wa’adi har zuwa ranar daya ga watan Oktoba na 2017.

Sannan, suka kuma nemi ‘yan kabilar Igbo da ke arewa da su kuma yankin da suka fito haka ma ‘yan arewa da ke yankin na Igbo da su baro wurin.

Maganar bayar da wa’adin dai ta kasance wani mayar da martani ga masu kira da kafa kasar Biafra.

Duk da janyewar wa’adin da hadadiyar kungiyar ta yi, ta kuma bayar da wasu sharuda ga gwamanatin tarayyar da kuma gwamnatocin jihohin arewacin kasar baki daya.

Sharudan dai sun hada da cewa gwamnatin tarayya ta tanadi dokar da za ta bayar da dama ga dukkan mai son ballewa a bashi dama, da kuma gurfanar da Kanu a gaban kuliya, sannan duk kamfanonin da ke aiki a arewacin Najeriya, dole su tanadi guraben aiki da kaso 40 cikin 100 wanda za a bawa matasan yankin.

Shin ko har yanzu ana amfani da biro wajen rubutu?


Yanzu kasuwar biro ta ja baya saboda shigowar abubuwan rubutu na zamaniHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Biro

Tun bayan bullar sabbin hanyoyin rubutu kamar Komfuta da wayoyin salula, kasuwar alkalami ko kuma biro ta ja baya.

A Najeriya ma dai haka abin ya ke, domin da yawa daga cikin al’ummar kasar musamman matasa da manya ma’aikata, su kan jima ba su yi rubutu da biro ba, saboda sun fi amfani da wayoyinsu na salula ko kuma idan a wajen aiki ne da Komfuta.

A halin da ake ciki a yanzu, ko da sako ne mutum zai rubuta, to da sabbin hanyoyin rubutun na zamani ake amfani.

Yawanci dai a yanzu dalibai ‘yan makarantun Firamare da na gaba da ita wato Sakandire ne ke amfani da biro wajen rubutu.

Masu sayar da irin abubuwan rubutu wadanda ba na zamani ba sun ce gaskia tun bayan bullar abubuwan rubutun na zamanin, kasuwarsu ta ja baya ba kamar da ba.

To amma sun ce, duk da bullar abubuwan zamanin na rubutu, dole a cigaba da amfani da biro, dan akwai abubuwa kamar zana jarrabawa.

A baya dai ba rubutu kadai ake yi da biro ba, har ma da ado, domin kuwa akan sanya shi a gaban aljihun riga musamman ga maza.

To amma yanzu al’amura sun canja, dan sau da dama zaka hadu da manyan mutane rubutu zai ta so sai kaji suna cewa ko akwai mai biro?

Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Turai


UEFAHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Karo na uku kenan Ronaldo ya ci kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Turai

Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ya fi yin fice a Turai a shekarar nan a bikin da aka yi a Monaco.

Dan wasan ya doke abokan takararsa da suka hada da Lionel Messi na Barcelona da mai tsaron ragar Juventus, Gianluigi Buffon.

Ronaldo ya taimakawa Real Madrid ta ci kofin Zakarun Turai da aka kammala, kuma na 12 jumulla, inda ya ci kwallo 12 a wasannin.

Nasarar da dan kwallon tawagar Portugal ya yi, ya sa ya lashe kyauta ta uku kenan, ya dara Messi da guda daya.

‘Yan wasan Barcelona, Lieke Martens ce ta ci kyautar mata a matakin babu wacce ta kai ta iya taka-leda a Turai a bana.

Ta kuma yi nasara ne a kan ‘yar wasan Wolfsburg, Pernille Harder da Dzsenifer Marozsan mai buga tamaula a Lyon.

Premier: An kashe fam biliyan 1.17 a sayen 'yan wasa


Premier League

Image caption

Lukaku ya ci wa United kwallo uku a wasa biyu da ya buga mata gasar Premier

An kashe fam biliyan 1.17 a sayen ‘yan wasa a kakar Premier ta bana tun kafin kasuwar ta watse a karshen watan Agustan nan in ji mujallar da ke sharhi kan kasuwanci Deloitee.

Kungiyoyi 20 da ke buga gasar sun kashe kudin ne tun daga lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai har zuwa Laraba, wanda ya dara fam biliyan 1.165 da aka biya a bara.

A banar nan Manchester United ta sayi Romelu Lukaku fam miliyan 75 daga Everton, Chelsea kuwa ta dauko Alvaro Morata daga Real Madrid kan fam miliyan 70.

A daidai wannan lokacin a bara kungiyoyin na Premeier sun kashe fam miliyan 865 ne.

Jirgin sojin saman Nigeria ya yi hatsari a Kaduna


Jirgin sojin NajeriyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jirgin sojin Najeriya

A ranar Alhamis ne wani karamin jirgin yakin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Kaduna da ke arewacin kasar, a lokacin da yake wani aiki.

A wata sanarwa da rundunar sojin saman kasar ta aikewa manema labarai ta ce, matukin jirgin wanda shi kadai ne a ciki lokacin da hatsarin ya afku ya mutu.

Har yanzu ba a san abin da ya jawo hatsarin ba, amma tuni hafsan sojojin sama na kasar ya bayar da umarnin kafa kwamitin bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin.

Wannan hatsari dai a cewar sanarwar, tuni ne kan yadda aikin tukin jirgin sama ke da matukar hadari.

Rundunar sojin saman ta aike da sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, wanda ya kasance kwararren matukin jiragen yakinta ne da ya san aikinsa.

Champions League: Real Madrid tana rukuni da Tottenham


Champions LeagueHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Madrid ce ke rike da kofin zakarun Turai kuma 12 jumulla

Mai rike da kofin Zakarun Turai, Real Madrid tana rukuni daya da Tottenham a jadawalin gasar bana da aka fitar a yammacin Alhamis.

Madrid tana rukuni na takwas da ya kunshi Tottenham da Borussia Dortmund da kuma Apoel.

Chelsea tana rukunin uku da ya kunshi Atletico Madrid da Roma da Qarabag, yayin da Manchester United da Benfica da Basel da kuma CSKA Moscow ke rukunin farko.

Za a fara wasannin rukuni tsakanin 12 zuwa 13 ga watan Satumba.

Ga yadda aka raba jadawalin kofin Zakarun Turan:

Rukunin A: Benfica, Manchester United, Basel, CSKA Moscow

Rukunin B: Bayern Munich, Paris St-Germain, Anderlecht, Celtic

Rukunin C: Chelsea, Atletico Madrid, Roma, Qarabag

Rukunin D: Juventus, Barcelona, Olympiakos, Sporting

Rukunin E: Spartak Moscow, Sevilla, Liverpool, Maribor

Rukunin F: Shakhtar Donetsk, Manchester City, Napoli, Feyenoord

Rukunin G: Monaco, Porto, Besiktas, RB Leipzig

Rukunin H: Real Madrid, Borussia Dortmund, Tottenham, Apoel

Lokutan da za a yi wasannin rukuni:

Wasannin ranar farko: 12-13 Satumba

Wasannin rana ta biyu: 26-27 Satumba

Wasannin rana ta uku: 17-18 Oktoba

Wasannin rana ta hudu: 31 Oktoba zuwa 1 ga Nuwamba

Wasannin rana biyar: 21-22 Nuwamba

Wasannin rana ta shida: 5-6 Disamba

Facebook barazana ne ga Dimokradiyya – Jon Snow


Jon Snow, Mark ZuckerbergHakkin mallakar hoto
PA/Getty Images

Image caption

Jon Snow, Mark Zuckerberg

Mai gabatar da shirin Joh Snow, ya ce ya kamata ya yi Facebook ya dauki mataki kan yada labaran da ba su da tushe balle makama, ya kuma samar da sahihiyar kafar yada labarai mai inganci.

Tsohon dan jaridar da ke gabatar da labarai tun a shekarar 1989, ya gabatar da wata kasida a bikin kalankuwar talabijin, inda ya ce shafin Facebook na yi wa Dimukradiyya barazana saboda abubuwan da ya ke yadawa.

Sai dai mamallakin Facebook din wato Mark Zuckerberg, ya ce kamfaninsa na taimakawa kafafen yada labarai.

Abin da ya kamata a yi

Cikin jawabin da ya dauke shi minti 50, Mista Snow ya ce, Facebook ya taimaka tare da janyowa Channel 4 karin mutanen da ke bibiyar labaran da suke yadawa, sai dai masu wallafe-wallafe na fama da masu bibiyar shafukan sada zumunta.

Ya kara da sukar lamirin kamfanin, da ya yi zargin yana yada labaran karya. Ya kuma ce shafin Facebook shi ya sanya wani labarai da ke cewa ”Paparoma ne ya daurewa Donald Trump gindi ya zama shugaban Amurka”, alhalin sam labarin ba haka yake ba.

“Sai dai hakan ya janyo sama da mutane miliyan daya suka yi ta tofa albarkacin bakinsu a lokacin zaben shugaban Amurkar, duk da cewa labarin ya shahara amma ta inda ya fito shi ne abin dubawa.

”Don haka Facebook yana da jan aiki a gabansa, don yin tankade da rairaya tare da kaucewa yada labaran karya” in ji Mista Snow.

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Jon Snow kenan a lokacin da ya ke gabatar da kasidar a Edinburgh

Ya kara da cewa Facebook na biyan masu wallafa masa labarai don kudi kalilan kan duk labaran da aka samu, wanda dan abin da ake ba su bai taka kara ya karba, ba kuma zai biya su wahalar da suka sha wajen samar da labaran da za su tabbatar da sahihancinsu da kuma bincike irin wanda ‘yan jarida ke yi ba.

Tashar BBC ta Channel 4 ta wallafa cikakkiyar kasidar da Snow ya gabatar.

Mayar da martani

A ranar Laraba ne mamallakin kamfanin Facebook Mista Zuckerberg ya ce suna kokari don tantance labaran da suke yadawa, da muka inganta albashin ma’aikata.

A martanin da ya mayar da kuma ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce a daidai lokacin da mutane da dama ke samun labarai a shafin sada zumuntar daga sassa daban-daban na duniya, suna kokarin kawo daidaito da inganta labaran da suke wallafawa.

Zuckerberg ya kara da cewa za a samar da wata hanya da mutane za su dinga duba dukkan labaran da shafin ke yadawa, don tabbatar da sahihancinsa.

Ya ce manufar sauye-sauyen da suke son kawowa ita ce tantance labaran gaskiya da na karya, ga duk wanda ya kawo labari za a dinga sanya tambarinsa a kasan labarin yadda idan an samu matsala shi za a tuntuba dan ya kare kansa kan labarin da ya wallafa.

”Bai wa mutane damar yin magana ba shi kadai ne abin da ake bukata ba, ana bukatar samar da wata kungiya da aikinta baki daya shi ne tankade da rairayar labarai.

Za mu kara samar da wasu hanyoyin don taimakawa bangaren watsa labarai, sannan masu dauko rahotanni da masu wallafawa za su yi aikin su yadda ya kamata,” in ji Zuckerberg.

Sai dai abin da ya wallafa din, ba wai yana maida martani ko sukar lamirin Mista Snow ba ne.

Tun da ko a lokacin da yake gabatar da kasidar, Mista Snow ya ce yana daya daga cikin masoya shafin sada zumunta na Facebook.

Ya ce, ”Shafin Facebook yana da dadin mu’amala, a wasu lokutan kuma bashi da maraba da mummunan mafarki.

“Ba na daga cikin mutanen da suke saurin bayar da kai bori ya hau.”