Man City ta doke Chelsea har gida


ChelseaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A minti na 67 ne De Bruyne ya samu nasarar jefa kwallo a gasar Chelsea

Manchester City ta doke Chelsea da ci 1-0 a gasar firimiya da suka yi ranar Asabar a filin wasa na Stamford Bridge.

Ita ma takwararta Manchester United ta samu nasara a kan Crystal Palace da ci 4-0.

Yanzu United da City suna kankankan a gasar, sai dai City ce take saman tebur da bambancin kwallaye, yayin da United take biye mata.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka fafata a gasar kamar haka:

 • Huddersfield 0-4 Tottenham
 • Bournemouth 0-0 Leicester
 • Man Utd 4 -0 Crystal Palace
 • Stoke City 2-1 Southampton

Pogba zai yi doguwar jinya – Mourinho

Aguero ya karya kashin hakarkari

Adikon Zamani: Me ya sa mata ke amfani da tsumma yayin jinin al'ada?


 • Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da Halima Umar Saleh ta yi game da wannan batu, idan kuka latsa alamar lasifika da ke hoton sama.

Batun al’adar da mata ke yi na jinin haila duk wata, wani al’amari da ba a faye tattaunawa a kansa ba, musamman a kasashen da ke girmama al’adu kamar Najeriya.

Hakan ce ta sa mata ke shiga wani yanayi na rashin sanin ainihin abin da ya kamata su yi ta fuskar kula da kansu don gudun kamuwa da wasu cututtuka a sakamakon rashin tsafta.

Wasu alkaluma da kungiyar WaterAid mai fafutukar ganin an samar da tsaftataccen ruwan sha da yanayi mai tsafta a rayuwar bil-Adama ta fitar a watan Mayun bana, sun nuna cewa a kullum mata kusan miliyan dari takwas ne ke al’ada; sai dai galibinsu sukan rika boye-boye da kuma fuskanci muzgunawa a wannan lokaci.

A cewar kungiyar an yi watsi da bukatun mata da ‘yan mata game da al’ada, lamarin da ke haifar da asara iri-iri ga al’umma, kama daga asarar damar zuwa makaranta zuwa ga ta tattalin arziki.

Shin wadanne bukatu mata ke da su a lokacin al’ada?

Me ya kamata su yi? Wanne taimako ya kamata al’umma ta ba su?

Kungiyar ta ce mace daya cikin mata uku a ko ina a fadin duniya ba sa samun damar amfani da tsaftataccen ban daki a yayin da suke al’ada, wanda hakan yana nufin zai yi matukar wahala su samu walwala a lokacin da suke al’adar.

Da yawan mata musamman wadanda ke zaune a karkara ko wadanda ba su da hali sosai na amfani da kyalle ko tsumma a yayin da suke al’ada.

Sai dai wani bincike ya gano cewa, amfani da tsumma ko kyalle da mata ke yi wajen yin kunzugu a lokacin da suke jinin al’ada, na janyo kamuwa da cutuka da dama.

Dokta Yalwa likitar mata ce a asibitin Maitama da ke birnin Abuja, ta shaida wa BBC cewa, daga cikin cutukan da ake kamuwa da su sakamakon amfani da tsumma musamman marar tsafta a matsayin kunzugu, akwai kuraje da kaikayi, wani lokacin ma har da fitar da ruwa mai wari daga al’aurar mata.

Hyeladzira Shalangwa, jami’a a kungiyar WaterAid ta ce duk da cewa dalilai na rashin sukuni ke sa mata amfani da kyalle ko tsumma maimakon audugar mata ta zamani, hakan ba zai zama dalilin da zai hana su tsaftace shi ba ta hanyoyin da suka dace don magance kamuwa da cututtuka.

Dokta Yalwa ta ce: “Yana da kyau matan da ke amfani da kyalle su dinga sauya shi kamar sau uku a rana, su kuma dinga wanke shi da ruwan zafi da gishiri a kuma goge shi ko da da dutsen dugar gargajiya ne na gawayi, domin hakan zai taimaka wajen kashe kwayoyin cutar da suke kai.”

Mutane da dama dai na ganin tun da ba za a iya shawo kan wannan matsala ba saboda ganin cewa tana da alaka da wadatar mutum, to yana da kyau masana a harkar lafiya su dinga wayar da kai da ba da shawarwari ga mata kan yadda za su dinga tsaftace kyallayen da suke amfani da su.

Me zai faru idan aka fara yaki da Koriya ta Arewa?


Wadansu masana harkokin tsaron Amurka da Koriya ta Arewa sun yi wa BBC karin bayani game da abin da zai faru a makonni farko na fara yaki tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

“Kimanin mutum miliyan biyu za su rasa rayukansu a makonni farko na fara yaki tsakanin kasashen biyu,” kamar yadda tsohon sojan Amurka, David Maxwell ya yi hasashe.

Har ila yau, masanin ya ce yakin zai jawo a tafka mummunar asara tsakanin kasashen biyu musamman idan Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi amfani da makamin Nukiliyarsa.

Abin da ya sa nake damuwa da Nigeria – Bill Gates


Bill GatesHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Arewacin Najeriya yana fuskantar babban kalubalen kiwon lafiya’

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu sosai.

Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan al’umma a nahiyar Afirka.

“Wannan ne ya sa gidauniyarta ta Bill & Melinda Gates Foundation take ci gaba da aikace-aikacenta a can,” kamar yadda ya ce.

Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin kiwon lafiya a yankin arewacin kasar.

“Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun ‘yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da Borno a kokarinmu na ganin mun magance kalubalen kiwon lafiya a yankin,” in ji shi.

Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara a fadin kasar.

Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnatin kasar da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote – wanda dan kasar ne.

Me ya sa Nigeria ke son cire shingayen 'yan sanda a tituna?


Traffic JamHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hukumar ‘yan sanda ta ce ta dauki matakin ne domin a rage yawan lokacin da ake batawa a shingayen hanya da kuma saukaka yadda ake gudanar da aiki.

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba da umarnin cire dukkan shingayen binciken ‘yan sanda a fadin kasar da gaggawa.

‘Yan Najeriya da yawa za su yi maraba da wannan labarin domin galibi shingayen tamkar hanyar damar karbar na goro ne daga matafiya da kuma masu jigilar kayayyaki.

Amman sanarwar ‘yan sandan ta ce an dauki matakin ne domin a rage lokacin da ake batawa a shigayen binciken da kuma saukaka yadda ake gudanar da kasuwanci.

Me nene ke faruwa a shingayen bincike?

Haduwa da dan sanda a hanya ka iya gajiyar da mutum.

Bindigar Ak47 da suke sabewa a kafada ba ta iya kwantar wa mutum hankali cewa yana cikin tsaro yadda yadda ya kamata.

Yawanci ‘yan sanda maza ne, kuma za su bukaci mutum ya bayyana kansa ya kuma fitar da lasisin tukinsa.

Sannan za su nemi su dubi wajen duba kayan mutum.

Daga nan za su tabbatar da cewar kana da dukkan abin da doka ta tanada – na’u’rar kashe wuta a ko wacce mota, da wata alamar da ake sakawa a hanya idan mota ta baci, da inshora, da takardar cancantar mota a kan hanya da kuma sauran takardu.

Duk abin da aka rasa ka iya sa a bai wa mutum zabi tsakanin bin dan sandan zuwa caji ofis ko kuma ba da na goro domin ya taimaka a kashe wutar matsalar nan take.

Ko kana da cikakkun abubuwan da ake bukata, wannan ba ya nufin za ka iya ci gaba da tafiyarka.

Jami’in ‘yan sandan zai tambaya in kana da ‘abin da za ka bai wa yaran’, ko kuma ya nuna maka irin zafin da ake yi (saboda haka yana bukatar kudin shan ruwa).

Wannan ba wani abun da ke faruwa jifa-jifa ba ne, ya zama ruwan dare ta yadda har ‘yan barkwancin Najeriya sun sha yin shaguben yadda ‘yan sanda ke neman na goro.

Me ya kamata a gujewa a shingen bincike?

Amsa waya a wurin shingen bincike ka iya janyo karin bata lokaci.

Jami’an tsaro ba sa jin dadi su ga mutane suna waya a gabansu.

Lamarin ka iya kamari idan ka nemi ka dauki bidiyon abin da ke faruwa a wurin.

Ba sa lamuntar a dauke su a bidiyo.

A shekarar 2013 an kori Sajen Chris Omeleze bayan wani mutum ya dauki hoton bidiyonsa yana kokarin karbar na goro a filin saukar jirgi na Legas.

Mutumin ya wallafa bidiyon a Intanet.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

An kalli bidiyon sosai a shafukan sada zumunta kamar yadda Tomi Oladipo ya ruwaito

Ta yaya za ki gane shingen da aka kafa bisa doka?

Babu wata takamammiyar hanya ta bambanta tsakanin shingen gaske da kuma hanyar kwace wa mutane kudi.

Za ki iya ganin durom da launin ‘yan sandan Najeriya – shudi da dorawa da kuma kore- a tsakiyar hanya.

Da daddare hasken tocila ne kawai zai nuna maka cewar akwai shingen bincike a wurin.

Idan ka yi rashin sa’a kuma, zai iya kasancewa ‘yan fashi ne.

Yayin da aka gindaya wasu shingayen domin kama masu laifi, sauran shingayen hanyoyi ne na samun kudi daga ‘yan sanda masu karbar na goro.

Yawanci wadannan na tasowa ne da dare da karshen mako.

Shugaban ‘yan sandan ya ba da umarnin cewar ‘yan sanda su saka kayan aikin da ke dauke da sunayensu da lambobin aikinsu.

Saboda haka bincike a shafin ‘yan sandan zai iya taiamaka wa wajen gano ‘yan sandan domin a kai kararsu.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wa yake kiyaye tsaron Najeriya?

Adadin cin hanci?

Alkalluman hukumar kididdiga ta Najeriya kan cin hnaci da rashawa na shekarar 2017, sun ce kashi 32 cikin 100 na ‘yan Najeriya da suka mallaki hankalinsu wadanda suka yi mu’amala da ma’aikatan gwamnati sun ce an tamabaye su na goro.

Hukumar kididdiga ta kasar NBS, ta ce an biya jumullar naira miliyan 82 naira ga jami’an gwamnatin Najeriya a wata 12 da suka wuce.

Wannan na daidai da cin hanci daya ga mutum daya a ko wacce shekara.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Direbobin manyan motoci da tasi su ne neman na goro ya fi shafa

Cin hancin da ake nema daga direbobi ya kan kai naira 20.

Direbobin manyan motoci da tasi su ne aka fi karbar na goto a wajensu.

Ba kasafai irin wadannan mutanen ke kalubalantar hukumomi ba kuma suna ba su da lokaci, saboda haka sun gwammaci su biya cin hanci.

Rahoton kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa na shekarar 2013 ya ce kashi 92 cikin 100 suna ganin ‘yan sanda sun yi dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa.

Shin hana kafa shingen binciken zai yi nasara?

Wannan ba shi ne yunkurin farko na hana kafa shingen bincike a Najeriya ba.

A shekarar 2012, shugaban ‘yan sandan lokacin Mohammed Dahiru Abubakar, ya ba da irin wannan umarnin, kuma an dauke shigayen bincike 3,500.

Duk da haka, shingayen sun koma inda aka cire su.

Wannan sabon umarnin wani yunkuri ne inganta gamsuwar mutane da ‘yan sanda.

Sanarwar ta ce an tura wasu tawagogi na musamman domin domin kamawa da bincike da kuma hukunta duk wani dan sanda da ya saba wa wannan umarnin.

Yanzu ya zama dole ga ko wacce rundunar ‘yan sanda ta nemi yardar sufeto janar na ‘yan sanda kafin ta kafa shingaye.

Wannan daya ne daga cikin matakan da sufeto janar na ‘yan sanda ya dauka domin ya inganta mutuncin ‘yan sanda.

Amman zai dauki lokaci mai tsawo tare da kwararan dalilai kafin yawancin ‘yan Najeriya su yarda da taken da ake rubutawa a ofisoshin ‘yan sanda: “Dan sanda abokinka ne.”

'Rashin jin kamshi na da alaka da cutar mantuwa'


Dementia patientHakkin mallakar hoto
Getty Images

Masu ilmin kimiyya a Amurka sun ce rashin jin ƙamshi ko wari ka iya zama alamun farko na kamuwa da cutar mantuwa.

An gwada kusan mutum dubu uku a wani ɓangare na wani dogon nazarin masu bincike daga jami’ar Chicago.

Sun ƙarƙare cewa mutanen da ba za su iya tantance ƙamshin alewar minti ko na lemo ko na furanni ko kuma ƙarnin kifi ba, na da ninki biyu na yiwuwar kamuwa da cutar matsananciyar mantuwa bayan shekara biyar.

Daya daga cikin masu binciken Farfesa Jayant Pinto ya ce daina jin ƙamshi ko wari wata babbar alama ce cewa an gamu da matsala.

Ya ce akwai tarin nazarce-nazarcen da ke nuna cewa gaɓoɓin karɓar saƙwanni na jiki na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar manyan mutane da tsoffi.

Haka ma baiwar gani da ji, da kuma a yanzu shakar ƙamshi ko wari na ba da gudunmawa wajen tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Kuma wata kafa ce ta tantance mutanen da ke cikin hatsarin kamuwa, in ji Farfesa Pinto.

Sauya fasali ya fi dacewa ba raba Nigeria ba – Ohaneze


Jama’a dadama a Najeriya na kiraye-kirayen sake fasalta kasar, ciki har da mutanen kudu maso gabashin kasar wadanda suke ganin sake fasalta kasar ne zai magance dumbin matsalolin da ake fama da su.

Wannan batun ne ma ya kai ga majalisar wakilan Najeriya ta kafa wani kwamiti domin duba batun.

Cif John Nwodo shi ne shugaban kungiyar. Ya ziyarci ofishinmu na Landon a kwanakin baya, ya kuma tattauna da Editan Sashin Hausa na BBC, Jimeh Saleh a kan abin da ya sa suke goyon bayan sake fasalin mulki a Najeriya, da kuma adawar da suke yi da ballewar yankin Biafra daga kasar.

Ya bayyana cewar sauya fasalin Najeriya shi ya fi dacewa da muradun ‘yan kabilar Igbo na nan gaba maimakon fafatukar kafa kasar Biafra.

Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da Editan BBC Hausa Jimeh Saleh ya yi da John Nwodo, idan ku ka latsa alamar lasifika da ke sama.

Buhari ne da kansa ya ɓata lamarin – Kungiyar Igbo


IgboHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jagoran Ohaneze Ndigbo ya ce ba sa goyon bayan masu rajin ballewa daga Najeriya amma suna son a sake wa kasar fasali

Kungiyar Ohaneze Ndigbo a Najeriya ta zargi shugaba Muhammadu Buhari da abin da ta kira “bata lamari” ta hanyar watsar da al’ummar Igbo a gwamnatinsa.

Yayin hira da BBC lokacin wata ziyara, shugaban kungiyar, Cif John Nwodo ya ce batun mayar da ‘yan kabilar Igbo saniyar ware, ba boyayyen abu ba ne.

Hakan na faruwa ne, tun bayan jawabin da ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cewa zai bambanta tsakanin ‘yan kasar bisa la’akari da kuri’un zaben da suka ba shi.

A cewarsa: “Buhari ya fada wa duniya cewa zai bambanta kulawar da zai yi wa mutanen da suka kada masa kashi 97 cikin 100 na kuri’unsu da wadanda suka kada masa kashi biyar na kuri’unsu.”

Jagoran Igbon ya ce ba a ba wa ‘yan kabilarsa gwargwadon hakkokin da suka cancanci samu.

John Nwodo ya buga misali da gwamnatin jamhuriyar ta biyu. Inda ya ce kuri’ar da Shagari ya samu a yankin Kudu Maso Gabas ba ta kai wadda ya samu a yankin Middle belt ba, kuma ba ta sa shi nuna wa Igbo bambanci ba.

“Ka ga! Ni tsohon dan jam’iyyar NPN ne, na rike mukamin minista a gwamnatin Shagari, in ji shi.”

Ya ce bai kamata Buhari ya yi fatali da ‘yan kabilar Igbo, don kawai ba su kada masa kuri’a ba.

A cewarsa, shugaban kasa baban kowa ne, don haka bai dace ya kori ‘ya’yansa don kawai sun bijire masa ba.

Ka duba hukumomin tsaro a Najeriya, babu ko da daya da dan kabilar Igbo ke jagoranta.

“Mu, ba ga babban hafsan tsaro ba, mu ba ga babban hafsan sojin kasa ko na ruwa ko sojin sama ba. Ba a ba mu shugabancin hukumar kula da shige da fice ba, ko ta leken asiri ko ta tsaron farin kaya ko ta kiyaye hadurra ba.”

“Ba mu da komai. Wannan ta sa aka mayar da mu tamkar al’ummar da aka ci ta da yaki,” a cewarsa.

Ya yi ikirarin cewa an girke musu shingayen ‘yan sanda a duk manyan hanyoyin yankin Kudu Maso Gabas babu gaira babu dalili.

John Nwodo ya ce kusan illahirin kwamishinonin ‘yan sandan jihohin yankin Igbo, sun fito ne daga arewacin Najeriya.

“Babban kwamandan da ke kula da runduna ta 82 da ke Enugu, dan arewa ne. Shin sun san yankin ne?” Nwodo ya tambaya.

Cif John Nwodo ya ce yana alla-alla ya samu ganawa da Buhari don zayyana masa wadannan batutuwa da ke ci wa kabilar Igbo tuwo a kwarya.

Mata za su fara ba da fatawa a Saudiyya


MataHakkin mallakar hoto
Getty Images

A karon farko babbar majalisar bada shawara a Saudiyya ta kada kuri’ar amincewa da a bawa mata damar yin fatawar addini.

Majalisar ta amince da shawarar da aka gabatar, kwanaki kadan bayan janye dokar hana mata tuka mota a kasar.

Ana dai bukatar sarkin kasar ya yi wata doka da za ta samar da yawan matan da ake bukata da za su iya ba da fatawar addini.

A baya malaman addinin kasar sun sha ba da fatawowi da ke janye ce-ce ku-ce, da ake dauka cewa suna nunawa mata wariya.

Paul Pogba zai yi doguwar jinya – Mourinho


PogbaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Paul Pogba ya buga duka wasannin da Man U ta yi a kakar bana gabanin jin rauninsa

Dan wasan Manchester United Paul Pogba zai yi doguwar jinyar raunin da yake fama da shi, kamar yadda kafar yadda kocin kungiyar Jose Mourinho ya bayyana.

Dan wasan ya ji raunin a minti 19 lokacin da suke karawa da Basel a gasar Zakarun Turai.

Da farko an yi zaton cewa dan wasan zai yi jinyar wata guda ne biyo bayan raunin da ya ji a ranar 12 ga watan Satumba.

Sai dai kocin ya ce bai san ranar da dan wasan zai koma taka leda ba.

Ashura: An ta da bam a masallacin 'yan Shia


Afghan security officials inspect the scene of a suicide bomb attack targeting Shiite Muslims Mosque during Friday congregational prayers in Kabul, Afghanistan, 29 September 2017Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Bam din ya tashi ne lokacin da Musulmi ‘yan Shia suka halarci masallacin don sallar Juma’a

Wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa da kuma mutum biyar a wani masallacin ‘yan Shia a birnin Kabaul na kasar Afghanistan, yayin da ake shirye-shiryen ranar Ashura.

Maharin ya boye kansa ne a matsayin makiyayi don samun damar isa masallacin, kamar yadda wani jami’in dan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Maharin ya isa wurin ne da garken dabbobinsa gabanin ya tayar da bam din da ke jikinsa,” kamar yadda wani ganau ya ce.

Kungiyar da ke ikirarin kafa Daular Musulunci (IS) ce ta dauki nauyin kai harin.

Akalla mutum 20 ne suka jikkata sanadiyyar harin.

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce adadin mutanen da harin ya shafa zai iya karuwa.

Ana zaton cewa an hari masallacin ‘yan Shi’a na unguwar Qala-e Fatullah a birnin Kabul ne, amma sai bam din ya tashi gab da masallacin.

A bara ma kimanin mutum 14 suka mutu a hubbaren Karte Sakhi yayin shirye-shiryen ranar Ashura.

Galibin Musulmin Afghanistan mabiya Sunni ne, amma akwai mabiya Shi’a kimanin kaso 10 zuwa 20 cikin 100 na jama’ar kasar.

Cameroon za ta rufe iyakarta da Nigeria


Har ma a birnin Bamenda da ke Kamaru, masu fafatuka sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da wariyar da suka ce ana yi wa 'yan kasar masu IngilishiHakkin mallakar hoto
STRINGER

Image caption

Har ma a birnin Bamenda da ke Kamaru, masu fafatuka sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da wariyar da suka ce ana yi wa ‘yan kasar masu Ingilishi

Rahotanni daga Kamaru sun ce hukumomin kasar sun gindaya dokar ta baci a yankin kudu maso yammacin kasar mai amfani da harshen Ingilishi gabannin zanga-zangar masu neman ballewa daga kasar da aka shirya yi a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.

Wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta hana mutane fita daga maraice zuwa safiya, da kuma rufe kan iyakar kasar da Najeriya da sauransu.

Shugaba Paul Biya ya kuma bayar da umarnin shirya sojoji domin kare kasar tare da tabbatar da tsaro ga dukkan ‘yan kasar masu mutunta doka, in ji wata sanarwar da gwamnan yankin kudu maso yammacin kasar, Bernard Okalia Bilai, ya saka wa hannu.

Wata sanarwar ta daban da Bilai ya fitar ta bayyana ka’idojin takaita zirga-zirgar inda ya ce dokar za ta yi aiki ne daga 29 ga watan Satumba zuwa 2 ga watan Oktobar shekarar 2017, a fadin yankin kudu maso yammacin kasar.

Magoya bayan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Kamaru ta Kudu suna son gudanar da zanga-zanga a yankin domin tunawa da samun ‘yancin Kamaru ta Kudu daga Birtaniya a ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1961.

An dade ana takun saka tsakanin gwamnatin kasar da mutanen kudancin kasar da ke amfani da harshen Ingilishi kan abin da masu fafatuka suka kira rashin yi wa yankin adalci.

Mutum 22 sun mutu a turereniya a tashar jirgin kasa ta India


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Matafiya suna kokarin ceton wadanda suka sami rauni

Wata turereniya a tashar jirgin kasa da ke birnin Mumbai ta janyo mutuwar mutum 22 inda fiye da mutum 30 kuma suka jikkata, in ji jami’ai a kasar Indiya.

Iftila’in ya faru ne a lokacin da ma’aikata ke rububin zuwa wajen aiki da safe a tashar jirgin kasa ta Elphinstone, wacce mahada ce ga manyan layukan jirgin kasa guda biyu na cikin birnin.

Cunkoso ne ya jawo wannan iftila’in saboda yawan mutanen da ke neman fakewa daga mamakon ruwan saman da ya rinka sauka.

An tafi da wadanda suka sami rauni zuwa wani asibiti da ke kusa da tashar kuma manyan jami’an tashar jirgin kasan na wurin domin taimakawa.

Yaya lamarin ya faru?

“Iftila’in ya auku ne a daidai lokacin da ake mamakon ruwan sama na Monsoon a birnin Mumbai, kuma matafiya sun taru a tashar domin neman mafaka.

Sai kawai wadanda ke gaba suka zame, dalilin da yasa na bayansu suka zubo kansu. Daga nan sai aka fara turereniya”, in ji Ravindra Bhakar, kakakin kamfanin jirgin Kasa na Indiya a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Mun tabbatar da mutum 22 sun mutu, maza 14 da mata takwas… Kuma wasu fasinjoji 32 sun sami raunuka.”

Hakkin mallakar hoto
BBC Marathi

Image caption

Masu aikin ceto sun yi gaggawar zuwa wajen

Akash Koteja na cikin wadanda suka sami rauni, kuma ya ce: “A lokacin jiragen kasa na isa tashar kuma wasu fasinjojin na neman ficewa daga tashar, amma wasu kuma sun hana su ficewa.

“Da wasu suka gwada fita sai aka fara turereniya.”

Hotunan talabijin sun nuna wasu matafiya na kokarin ceto abokan tafiyarsu daga cikin wadanda aka danne, kuma wasu ana danna kirjinsu domin a farfado da su.

“Mun saka wadanda suka sami rauni a motoci, da motocin ‘yan sanda da motocin daukar ma’aikata wadanda suka tafi da su asibiti cikin gaggawa”, in ji daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin kamar yadda AFP ta ruwaito.

Me yasa iftila’in ya faru?

Wani bincike da aka kaddamar ya bankado sanadiyyar wannan hatsarin, amma cunkoso shi ne babban dalilin yawan hadurran da ke addabar hanyoyin jiragen kasan Indiya.

Wakiliyar BBC a Mumbai, Yogita Limaye, ta ce hatsarin ya sake bayyana halin tabarbarewar da bangaren sufuri na birnin Mumbai ke ciki.

Kuma an sha sukar yadda gwamnati ba ta sabunta jirage da taragun da ke safarar miliyoyin fasinjoji a hanyoyin jiragen kasa a kullum.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan uwan wadanda iftila’in ya faru sun tafi asibitin domin neman labarin halin da ‘yan wansu ke ciki

Boko Haram ta kashe malamai 2,295 a Borno – UNICEF


Wadansu da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin 'yan gudun hijira.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yara da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce har yanzu mafi yawan makarantun jihar Borno inda rikicin Boko Haram ya fi kamari a rufe suke, wanda aka danganta hakan da cewa ‘yan kungiyar na kai hare-haren ne da gayya don lalata fannin ilimi.

A wani rahoto da ta fitar a ranar Juma’a, UNICEF ta ce a kalla kashi 57 cikin 100 na makarantun Borno a rufe suke, a yayin da aka fara sabuwar shekarar karati, inda yawan malaman ya ragu kuma gine-ginen makarantun suke a lalace.

A wata sanarwa da UNICEF ya aikawa manema labarai ya ce, fiye da malamai 2,295 aka kashe, yayin da aka raba 19,000 da muhallansu, sannan kuma makarantu 1,400 suka lalace a shekaru takwas din da aka shafe ana rikici a yankin.

Makarantun sun kasance a rufe ne saboda yadda aka lalata su, wasu kuma suna yankunan da har yanzu babu tabbataccen tsaro, duk kuwa da irin yadda sojoji ke kokarin ‘murkushe’ ‘yan kungiyar tun a shekarar 2015.

UNICEF ya yi gargadi cewa lamarin na barazanar sanyawa a rasa yara masu tasowa, inda hakan zai rushe duk wani buri na makomarsu da makomar kasarsu idan har ba a yi komai ba kan hakan.

Mataimakin hukumar ta UNICEF Justin Forsyth, ya kai ziyara yankin arewa maso gabashin Najeriyar, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “koma bayan da hakar ilimi ta fuskanta sakamakon ta-da kayar baya ba tsautsayi ba ne.”

“Wannann wani abu ne da Boko Haram ta shirya yin sa da gayya, don hana yara samun ilimi,” a hirar tasa da AFP.

Mista Forsyth ya kara da cewa, kusan yara miliyan uku na bukatar taimakon gaggawa ta fannin ilimi, sai dai akwai wawagegen gibi a kudaden da UNICEF ke samar wa don yin ayyuka a yankin.

Kusan yara 750,000 ne suka samu komawa makaranta a bana a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, jihohin da su ma ayyukan Boko Haram suka yi wa illa.

Wadansu da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Sergio Aguero ya ji ciwo a hatsarin mota


Manchester City's Sergio AgueroHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sergio Aguero ya buga wasan da Manchester City ta doke Shakhtar Donetsk 2-0 ranar Talata

Dan wasan gaban Manchester City Sergio Aguero ya ji rauni a wani hatsarin mota a birnin Amsterdam, sa’o’i bayan ya halarci wani bikin rawa da kade-kade.

An ba da rahoton cewar dan kasar Argentina mai shekara 29 yana hanyar shi ta zuwa filin jirgin sama ne a motar haya bayan ya kalli wakar da mawaki Maluma ya yi.

City ta ce “ya kasance a kasar Holland ne a lokacin hutunsa, kuma ya ji raunuka”.

Ana tsammanin Aguero ya koma Manchester ranar Juma’a, kuma likitocin City za su gwada shi kafin tafiyarsu wasan gasar Firimiya a Chelsea ranar Asabar.

‘Yan sanda a Amsterdam sun tabbatar wa BBC cewar mutum biyu ne cikin motar tasi din da ta yi hatsari a unguwar De Boelelaan da ke cikin birnin.

Kafin hatsarin dai, dan kwallon ya wallafa hotonsa da mawaki Maluma a shafinsa na Instagram da sakon da ke cewa: “ina godiya da gayyatata”.

Hakkin mallakar hoto
KaWijKo Media

Image caption

Hatsarin ya auku ne a unguwar De Boelelaan na Amsterdam

Tsohon kulob din Aguero, Independiente, ya tura wa dan wasan sakon fatan alkhairi ta shafin Twitter, yana mai cewa”Kuzari tare da warkewa cikin gaggawa ga aguerosergiokun! Ilahirin @Independiente na tare da kai a wannan mawuyacin lokaci.”

Dan wasan gaban ya ci kwallaye bakwai a wasanni takwas a Man City a wannan kakar.

Kuma ya tallafa wa kungiyar Pep Guardiola ta hau saman teburin gasar Firimiya tare da yin nasara a wasanninsu biyu na farko a gasar zakarun Turai.

Hakkin mallakar hoto
10aguerosergiokun

Image caption

Sergio Aguero (daga hagu ) da Maluma a wani hoton da ya wallafa a shafin Instagram sa’o’i kafin hatsarin motar

Ba zan nemi gafara wajen Buhari ba – Buba Galadima


Buba GaladimaHakkin mallakar hoto
BUBA GALADIMA

Image caption

Buba Galadima ya ce ba wani sabani tsakaninsa da Shugaba Buhari, saboda haka ba zai nemi wata gafararsa ba, don a ba shi mukami

Daya daga cikin jigogin da aka kafa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, tare da kasancewa na gaba-gaba wajen fafutukar ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya samu mulkin Najeriya, Injiniya Buba Galadima, ya ce bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin ba.

A hirarsa da BBC Buba Galadima ya ce a yanayin salon jagorancin jam’iyyar da kuma mulkin da ake yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.

Ya ce abin takaicin shi ne Allah ya jarrabi Shugaba Muhamadu Buhari da rashin lafiya, kuma dadin dadawa sai jam’iyyar ta kasa samar da wani kyakkyawan shugabanci, wanda duka wadannan abubuwa sun shafi yanayin mulkin.

Game da rashin ba shi wani mukami ko tafiya da shi a gwamnatin Buharin, Buba Galadima ya musanta cewa akwai wani sabani a tsakaninsu da Shugaban, wanda ake rade-radin cewa saboda hakan ne ba a tafiyar da shi.

Ya ce a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka assasa tafiyar har ta kai an kafa gwamnati ba ya bukatar har sai ya yi kamun kafa, ko wani tumasanshi a wurin Shugaba Buhari kafin a san da shi har a ba shi wani mukami.

Injinyan ya ce rashin ba shi mukami bai dame shi ba, domin kusan duk wadanda suka faro tafiyar tabbatar da kasancewar Buharin ya zama shugaban kasa, babu wanda aka ba wa wani mukami, don haka ce shi ba komai ba ne, yana mai shagube da cewa: ”Ni ai a cikin miya ban kai komai ba.”

Dan siyasar ya dangantaka ba shi mukami ga lamari na Ubangiji, yana mai cewa duk abin da mutum ya samu Allah ne, haka kuma in mutum ya rasa Allah ne, amma ba ya nadamar gwagwarmayar tabbatar da Buhari Shugaban kasa, don bai samu mukami ba.

Ya ce ba wata gafara da zai nema daga Shugaban, ko zai waiwaye shi da mukami, domin shi a saninsa ba wani abu da ya yi na sabamasa.

Game da dantakarar da Buba Galadiman zai mara wa baya a zabe na gaba na 2019, ya ce lokaci bai yi ba tukuna, amma idan lokacin ya zo zai karkata ga ra’ayinsa, ko da kuwa za a kashe shi ne.

Sai dai ya ce in har Buhari ya neme shi a tafiyar 2019, idan zai yi takara zai iya mara masa baya, amma ba wai haka kawai ya kai kansa tafiyar ba, ba tare da an gayyace shi ba.

Amma ya ce ko a yanzu Buhari ya kirawo shi ya ba shi mukami zai karba, domin magana ce ta kokarin ciyar da kasa gaba da yi wa al’umma hidima, amma ya wuce a ce ya je ya nemi a ba shi aiki a gwamnatin.

Europa: Arsenal ta yi rawar-gani, ta doke Bate 4-2


Theo Walcott lokacin zura daya daga cikin kwallonsaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Theo Walcott ya ci wa Arsenal kwallo uku a wasa biyu da ya yi mata na karshen nan

Theo Walcott ya zura kwallo biyu a raga a wasan da Arsenal wadda bisa ga dukkan alamu ta farfado daga yanayin da ta shiga na rashin katabus, inda ta doke Bate Boristov a wasan Europa.

Wasan da suka tashi 4-2, ranar Laraba, ya kasance na biyu da Arsenal ta ci a rukuninsu na takwas (Group H) na gasar kofin Turai ta Europa.

Walcott ya fara daga raga ne a minti na tara da shiga fili, sannan ya kara ta biyu a minti na 22.

Rob Holding ya ci wa Arsenal kwallonsa ta farko a minti na 25, wadda ta kasance ta uku ga kungiyar, kafin kuma Giroud shi ma ya ci tasa a minti na 49 da bugun fanareti, kwallon da ta kasance ta 100 da ya ci wa kungiyar.

Bate ta samu kwallayenta ne ta hannun Ivanic a minti na 28 da shiga ili, yayin da a minti na 67 Gordeychuk ya ci musu ta biyu.

Arsenal ce kungiya ta farko da ta doke Bate a gida a wata gasar kofin Turai, tun bayan da Barcelona ta ci ta a wasan rukuni na kofin zakarun Turai a 2015- a wasa bkawai kenan.

Arsenal ce ta daya yanzu a rukunin da maki shida, yayin da Red Star Belgrade take zaman ta biyu da maki hudu, bayan da ta ci Cologne, wadda ta sha kashi a wasanninta biyu, da daya mai ban haushi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Nikola Vlasic ya ci wa Everton kwallon farko

Ga sakamakon sauran wasannin na Europa na ranar Alhamis :

Östersunds FK 1-0 Hertha BSC

Everton 2-2 Apollon Limassol

FC Astana 1-1Slavia Prague

Ath Bilbao 0-1 Zorya Luhansk

Lazio 2-0 SV Zulte Waregem

Nice 3-0 Vitesse

Rosenborg 3-1 Vardar

Zenit St P 3-1 Real Sociedad

Lugano 1-2 Steaua Buc

Viktoria Plzen 3-1Hapoel Be’er Sheva

FC Köln 0-1Crvena Zvezda

FC Red Bull Salzburg1-0 Marseille

Konyaspor 2-1Vitória Guimarães

Sheriff Tiraspol 0-0 FC Copenhagen

Lokomotiv Moscow 3-0 Zlín

Lyon 1-1 Atalanta

Ludogorets Razgrad 2-1 Hoffenheim

AC Milan 3-2 HNK Rijeka

AEK Athens 2-2 Austria Vienna

Sporting Braga 2-1 Istanbul Basaksehir

Skenderbeu 1-1 Young Boys

Partizan Belgrade 2-3 Dynamo Kiev

Zenit St Petersburg 3-1 Real Sociedad

Rosenborg 3-1 Vardar

Sanatocin Amurka sun soki Twitter


Tambarin shafin TwitterHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sanatocin sun zargi kamfanin Twitter da kin bayar da cikakkun bayanai kan zargin kutsen Rasha a zaben Amurka na 2016

An soki kamfanin shafin Twitter saboda ‘yar takaitacciyar bayyana wadda ba ta wadatar ba, da wakilansa suka yi a gaban kwamitin da ke binciken katsa-landan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata.

An gayyaci jami’an kamfanin na Twitter da su bayyana domin su bayar da bahasin da suke da shi na amfani da shafin wajen yada bayanan karya ga masu zaben Amurka.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron ganawar da jami’an kamfanin, dan majalisar dattawan Amurka, Mark Warner, ya bayyana bahasin da wakilan shafin suka bayar a matsayin babban abin takaici.

Ya zargi kamfanin da kin fahimtar muhimmancin lamarin, ta yadda kawai ya maimaita irin bayanan da masu shafin Facebook suka ba wa kwamitin.

Shi dai Sanata Warner yana fafutukar ganin an sanya wa kamfanonin fasaha ne tsauraran matakai kan ayyukansu, musamman ma a kan saba dokokin tallace-tallace ta intanet.

A wani sako da shafin Twitter ya wallafa ranar Alhamis, ya ce, kafar watsa labarai ta Russia Today, wadda ke da alaka ta kut da kut da fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta kashe dala dubu 274, wajen tallace-tallace a lokacin yakin neman zaben na Amurka.

Shafin na Twitter ya kuma ce ya gano tare da dakatar da shafuka daban-daban har 22 da ake amfani da su wajen yada bayanai da sakonni na karya.

IS ta fitar da sakon murya na al- Baghdadi


al-Baghdadi bai kara fitowa bayyanar jama'a an ganshi baHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tun bayan watan Yulin shekarar 2014, al-Baghdadi bai kara fitowa baynar jama’a ba

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta IS, ta wallafa wani sautin murya da aka nada wanda ta ce na shugabanta ne, Abu Bakr al-Baghdadi.

Sakon da mai maganar ke yi a cikin sautin, ga alama yana yi ne a kan barazanar da Koriya ta Arewa ke yi wa Japan da kuma Amurka.

Kazalika sautin muryar ya tabo batun yakin da ake yi a babbar tungar kungiyar ta IS da ke birnin Mosul, birnin da dakarun Iraqi suka karbe a watan Yulin da ya gabata.

al-Baghdadi, wanda aka sanya ladan dala miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da labarin in da yake, ba a kara ganinsa a bayyanar jama’a ba tun watan Yulin shekarar 2014, lamarin da ya janyo rade-radin cewa ko yana raye ko kuma ya mutu.

Karshen ganinsa da aka yi a baynar jama’a shi ne, lokacin da ya yi wa’azi a babban masallacin birnin Mosul wato al-Nuri, bayan IS din ta karbe ikon birnin.

Ko da aka tambayi kakakin rundunar sojin Amurka da ke yaki da IS, Ryan Dillon, ya ce tunda babu wata kwakkwarar shaida da za mu ce ya mutu, to za mu dauka yana nan da rai.

Abin da har yanzu mata ba su da izinin yi a Saudiyya?


Matan SaudiyyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Sarkin Saudiyya ya zartar da dokar da ta amince wa mata yin tukin mota, abin da ya kawo karshen bambancin da ake nuna wa, yayin da ita kadai ce kasar da ta haramta wa mata tuka mota a duniya.

Sai dai duk da cewa sai a watan Yunin badi ne dokar za ta fara aiki, amma kuma akwai abubuwa da dama da mata ba za su iya samu ba, a kasar da ke bin tsattsauran ra’ayin addinin musulunci.

Har yanzu dai akwai abubuwa da dama da sai mata sun nemi izinin maza kafin su aiwatar.

Wadannan abubuwa sun hada da:

 • Neman takardun yin tafiye-tafiye ko fasfo
 • Yin balaguro zuwa wasu kasashe
 • Yin aure ko neman saki
 • Bude asusun ajiya a banki
 • Idan za su fara wata harka ta kasuwanci
 • Idan za a yi musu aikin tiyata amma ba na gaggawa ba
 • Idan za su bar gidan kaso

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Har yanzu akwai abubuwan da ba a bai wa mata izinin yi ba

Wadannan ka’idojin dai, na tasiri ne a karkashin tsarin muharami na Saudiyya.

Tun bayan kafuwarta, kasar ta ke bin tafarkin addinin musulunci na masu tsattsauran ra’ayi – wahhabism.

Bayan boren da masu tsananin kishin Islama suka yi a 1979, aka sake karfafa ka’idojin.

A cewar wani rahoto na shirin tattalin arziki na duniya na 2016, tsarin ya taimaka wajen sa kasar ta zamo daya daga cikin kasashen da ke nuna bambanci tsakanin jinsuna a Gabas ta Tsakiya, tana gaban Yemen da Syria, wadanda kasashe ne da ake yaki.

Sai dai duk da haka, akwai wasu fannoni na rayuwar mata da ba a shinfida musu ka’idoji ba, fiye da yada ake tsammani.

Tun a shekarar 2015 ne mata suka samu damar kada kuri’a.

Ilimin boko wajibi ne ga yara mata da kuma maza, har sai sun kai shekara 15, kuma an fi samun mata da suka kammala karatun jami’a a kan maza.

Kusan 16% na ma’aikatan kwadago mata ne.

Ana bukatar mata a Saudiyya su saka abaya mai tsawo, wadanda ba su kama jiki ba, a wuraren da za su yi tozali da maza wadanda ba danginsu ba ne.

Sai dai akwai wasu, da wannan doka ba ta tasiri a kansu.

An yi wa matan da suka fito daga kasashen waje sassauci game da irin rigunan da za su saka, kuma idan ba musulmai ba ne an amincesu su bar gashinsu a bude.

Wasu mata da suka fito daga kasashen ketare da suka yi tattaki zuwa kasar, sun ce sai da suka saka abaya kafin suka bar filin jirgin sama.

Amma kuma an samu matan shugabannin kasashen waje da suka kai ziyara Saudiyyar, wadanda ba su saka abaya ko kuma suka rufe gashinsu ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Melenia Trump da Michelle Obama ma ba su rufe kansu ba a lokutan da suka kai ziyara Saudiyya

Kasashe kalilan ne suke amfani da dokoki da suka fayyace abubuwan da mata za su iya yi da wanda kuma ba za su iya yi ba, sai dai kuma akwai wasu wurare da aka haramta wa mata yin wasu abubuwa.

Ga wasu daga cikinsu:

China: Ma’aikatar ilimi ta China ta hana mata neman ilimin hakar ma’adinai, da na aikin gina hanyar da jirgin kasa yake bi ta karkashin kasa ko ruwa da kuma wasu darussa.

Ta ce ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsaron lafiyar mata.

Isra’ila: A Israila mata ba za su iya neman saki daga wurin mazajensu ba, saboda kotunan addini ne suke da hurumin yin haka.

A shari’ar da ba kasafai ake gani ba, alkalai a Birtaniya sun fada wa wata matar da ta nemi rabuwa da mijinta cewa hakarta ba zata cimma ruwa ba saboda mijinta ba ya son rabuwa da ita.

Rasha: Akwai wasu ayyuka da aka haramtawa mata a Rasha, ciki har da na kafinta da na aikin kwana-kwana da tuka jirgin kasa da kuma jirgin ruwa.

Indonesia: Haka kuma an haramta wa mata da ke wani gari a Indonesia zama a bayan maza a kan babur.

Magajin garin Lhoksuemawe ya bukaci mata su dinga zama a gefen babur domin kare dabi’un al’umma masu kyau.

A baya ma sai da hukumomin garin suka haramta wa mata saka wanduna masu kama jiki.

Sudan: A Sudan kuwa, hukuncin da ake yanke wa mata da suka saka wando shi ne bulala.

Bayern Munich ta kori Carlo Ancelotti


Carlo AncelottiHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kocin mai shekara 58 ya jagoranci Real Madrid tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sallami kocinta, Carlo Ancelotti, kwana guda bayan ta yi rashin nasara a hannun Paris St-Germain (PSG).

A ranar Laraba ne PSG ta doke Bayern da ci 3-0.

Ancelotti ya maye gurbin Pep Guardiola ne a kakar bara.

Ancelotti dan asalin Italiya ya taimaka wa Bayern ta lashen kofin Bundesliga a baya, amma kuma kungiyar ta iya kai wa wasan gab da na kusa da na karshe a kasar Zakarun Turai.

Mataimakinsa Willy Sagnol ne zai maye gurbinsa a matsayin kocin wucin gadi.

Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, yana neman shugabancin Nigeria


FayoseHakkin mallakar hoto
Fayose twitter

Image caption

Fayose ya fara zama gwamnan jihar Ekiti ne a shekarar 2003

Gwamnan jihar Ekiti a Najeriya Ayodele Fayose ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2019.

Mista Fayose wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, yana yawan sukan manufofin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, mai mulki.

Jam’iyyar APC, wanda ta karbi shugabancin Najeriya kusan shekara biyu da su wuce, ba kasafai ake jin duriyar jam’iyyar adawa ta PDP wanda take fama da rikicin cikin gida.

Jam’iyyar PDP wanda tayi shekara 16 tana shugabancin Najeriya kafin ta sha kayi a hannun a APC a shekarar 2015.

Fayose ya fara zama gwamnan jihar Ekiti wadda yankin take kudu-maso-yammacin kasar ne a shekarar 2003, kafin ya sake zama gwamnan jihar a shekarar 2014.

Zuwa yanzu dai shi ne mutum na farko da ya bayyana aniyyarsa ta neman shugabancin kasar a hukumance.

An sace mataimakin kwaminishin 'yan sanda a Nigeria


Nigerian policeHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan lamarin ya auku ne a lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya take cewa tana iya kokarinta wajen ganin ta dakile sace-sacen mutane a fadin kasar

Rahotanni a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sace wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda tare da matarsa a yayin da suke tafiya a mota. An sace mataimakin kwamishinan nan ne a wani dajin da ke tsakanin Funtua a jihar Katsina da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wata majiya mai karfi ta tsaro a jihar Kaduna ta shaida wa BBC cewa, mataimakin kwamishinan na ‘yan sandan na aiki ne a jihar Zamfara ko kuma a jihar Katsina.

Har yanzu dai rundunar ‘yansan da ta jihar Kaduna ba ta ce komai ba a bisa wannan batu, to sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar wanda wakilinmu na Kaduna ya tuntuba, ya ce suna wani taro, inda ya bukace shi da ya sake kiransa bayan taron.

Dajin da aka sace wannan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda dai dama sanannen wuri ne da aka yi amannar na kunshe da ‘yan ta’adda kamar ‘yan fashi da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Jihar Kaduna dai ta yi kaurin suna a sace-sacen mutane, kuma kwanakin baya an sace tsohon ministan kasar, Ambasada Bagudu Hirse a cikin birnin Kaduna.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cewar suna daukar tsauraran matakai domin magance matsalar tsaro a jihar.

Ana zubar da ciki sau miliyan 56 a duniya duk shekara – WHO


Wata mata na shan fama da azabar ciwon mara sakamakon zubar da ciki da tay a Jamhuriyyar Dimokradiyyar CongoHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wata mata na shan fama da azabar ciwon mara sakamakon zubar da ciki da tay a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta ce kashi 50 cikin 100 na zubar da ciki da ake yi a duniya na cike da hadari.

Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ambato wani rahoto na wani bincike da hukumar WHO ta gudanar, wanda ya nuna cewa ko wacce shekara ana zubar da ciki kusan sau miliyan 56 a fadin duniya, kuma kusan rabi na cike da hadari.

Yawan zubar da ciki da ake yi mai cike da hadari na faruwa ne a Afrika, inda zubar da ciki daya cikin hudu ne kawai ba ya zuwa da hadari, kuma a nan ne aka fi samun yawan mace-mace sakamakon zubar da cikin.

A cikin wani bincike da aka wallafa a wata mujallar lafiya ta Lancet, ya ce an zubar da ciki sau miliyan 55.7 a ko wacce shekara daga 2010 zuwa 2014 a duniya.

Binciken ya kuma ce miliyan 17.1 na cikin da aka zubar ya zo da hadari, saboda matan da suka aikata haka din sun sha magunguna ne da kansu ko kuma wasu kwararru sun taimaka musu amma ba ta ingantacciyar hanyar da ta dace ba.

Mutumin da ya kirkiro mujallar 'batsa' ta Playboy Hugh Hefner, ya mutu


This file photo taken on August 23, 2006 shows Hugh Hefner, CEO of Playboy Enterprises, posing for a photo during an interview with journalists at his mansion in Los Angeles, CaliforniaHakkin mallakar hoto
AFP

Hugh Hefner, dan Amurkar nan da ya kirkiro mujallar da ke nuna mata tsirara ta kasa da kasa Playboy, ya mutu yana da shekara 91.

Kamfanin Playboy Enterprises Inc ya ce Mista Hefner ya mutu ne a gidansa da ke Los Angeles.

Hefner ya fara buga mujallar Playboy ne a wajen da yake dafa abinci a shekarar 1953.

Mujallar ta zamo mujallar da ta fi ko wacce kasuwa a duniya inda take sayar da kwafi miliyan bakwai a ko wanne wata a lokacin da mujallar ta fi yin kasuwa.

Cooper Hefner, dansa, ya ce: “mutane da yawa za su” yi kewarsa.

Cooper ya yaba da rayuwarsa babansa “ta musamman mai gagarumin tagomashi,” inda yake ganin mahaifin nasa a matsayin wani mai fasaha a fannin ala’ada da kafafen watsa labarai.

Ya kuma bayyana babansa a matsayin mai fafatukar ‘yancin tofa albarkacin baki da ‘yancin jama’a da kuma ‘yancin jima’i.

Mujallar Hefner da ta kafa tarihi ta sa ana kallon nuna tsiraici ba komai ba ne a kafofin yada labarai, duk da cewar mujallar ta fara fitowa ne a lokacin da jihohin Amurka ka iya hana anfani da magungunan hana daukar ciki.

Mujalallar ta kuma mayar da shi miloniya, lamarin da ya haifar da wata daular kasuwanci da ta kunshi gidajen caca da gidajen rawa.

Mujallar ta farko tana dauke ne da hotunan Marilyn Monroe tsirara, wadanda asali an daukesu ne domin bugawa a wata kalandar shekarar 1949, amman shi Hefner ya sayi hotunan kan kudi $200.

Attajirin wanda aka san shi da yawan son saka kayan barci, ya shahara da dabi’arsa ta fifita sha’awa da nema tare da auren ‘yan matan da ke fitowa a mujallarsa tare da gudanar da bukin fitsara a kawataccen gidan Playboy da ke Los Angeles.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ga katafaren gidan Playboy wanda ya yi kaurin suna a Beverly Hills

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hefner da ‘yan matan da yake daukar hotunansu tsirara sun yi tafiya kan jirgin Playboy a lokacin da mujallar take tashe a shekarun 1970

A shekarun 1980, gogayya daga wasu mujallun da suka fi Playboy nuna tsiraici ta sa kasuwar mujallar ta ragu, kuma Hefner da kansa ya yi fama da mutuwar wani sashe na jikinsa a shekarar 1985.

‘Yara, Christie ta karbi jagorancin kamfanin bayan shekara hudu, kuma Hefner ya koma katafaren gininsa tare da wasu mata.

A shekarar 2014 ne Cooper Hefner ya taka gagarumar rawa a kamfanin bayan Christie ta yi murabus a shekarar 2009.

Mujalar ta yanke shawarar nuna tsiraici a watan Maris din shekarar 2016, amman ya sake shawara a farkon wannas shekara ta 2017.

Wani makwabcin Hefner ya sayi katafaren gidan Playboy kan kudi dala miliyan 100 a watan Augustan shekarar da ta gabata, amman ya amince da cewar Hefner ka iya ci gaba da zama a ciki har sai ya mutu.

Takaitaccen tarihinsa

An haifi Hefner ne a shekarar 1926 a birnin Chicago, kuma ya yi aikin sojin Amurka a tsakiyar shekarun 1940.

Ya kammala karatun digiri a fannin nazarin halayyar dan adam, kuma ya yi aiki a matsayin marubuci a mujallar maza da ake ce wa Esquire, kafin ya ranci kudi $8,000 domin ya fara wallafa Playboy a shekarar 1953.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Hefner ya mutu bar matarsa ta uku, Crystal Harris

Nigeria: Yaron da mayakan BH suka take da babur ya fara tafiya


Ali Ahmadu

Image caption

Masu ta da kayar baya na Boko Haram ne suka take shi da babur a shekarar 2014

Wani dan Najeriya dan shekara biyar, wanda ya ji mummunan rauni a lokacin da mayakan Boko Haram suka take shi da babur, ya fara tafiya a karon farko tun lokacin da ya ji ciwon.

Mayakan sun hau doron bayan Ali Ahmadu da babur ne a lokacin da yake neman tserewa tare da mahaifiyarsa daga farmakin da aka kai wa kauyensu, Chibok.

A yanzu dai Ali ya fara tafiya, bayan an yi masa aikin kashin baya a Dubai.

Wata kungiyar agajin Najeriya ce ta biya kudin aikin da aka yi masa bayan ta tara kimanin fam 45,000 domin a yi wa yaron aiki.

Ana tsammanin Ali zai zauna a Dubai na kimanin wata uku inda za a yi masa magani na motsa jiki domin a farafado da karfinsa.

Image caption

Ali yana dan shekara biyu ne kawai a lokacin da mayakan Boko Haram suka take shi

Shugaban kungiyar ba da agajin da ta shirya samar wa yaron magani, Nuhu Kwajafa na kungiyar Global Initiative for Peace, Love and Care, ya shaida wa shirin Focus on Africa na shahen Turancin BBC, cewar Ali bai samu ganin likita ba tsakanin lokacin da lamarin ya auku da kuma lokacin da ya isa Dubai.

“Yana kwance ne da ciwon a kashin bayansa,” in ji mista Kwajafa.

“Yana da wani nau’in tarin fuka wanda bai fara tasiri ba, tare da wasu cututtuka, kuma an bar shi a kauyen.”

A yanzu, bayan an yi masa aiki, “yana kai wa da komowa a daki, yana magana, yana surutu, ban taba ganinsa a cikin irin wannan halin ba.”

Kun san yadda za a kauce wa kamuwa da sankarar mama?


CancerHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hoton cutar daji da ke nuna kwayoyin halittan da suka hayayyafa fiye da yadda ya kamata

Wannan makala ce kan bayanai game da yadda ake kamuwa da cutar sankarar mama da yadda za a iya kauce mata, kuma wannan makala an yi ta ne don amsa tambayoyinku da ku ka turowa BBC kan batun, wadanda muka yi alkawarin amsa muku.

Sankara dai tana aukuwa ne a lokacin kwayar halitta mai illa ta fara hayayyafa fiye da yadda ya kamata. Wannnan hayayyafar kwayar halittar yakan kai ga matakin ciwo mai tsanani, kuma a wasu lokutan yakan kai ga mutuwa.

Sankara dai ta kan kama mata da maza a sassa daban-daban na jikinsu.

Alkalluma daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ce sankarar mama (breast cancer) ita ce sankarar da ta fi kama mata a duniya, inda mata miliyan daya da rabi ke kamuwa da cutar a ko wacce shekara.

Har wa yau, alkaluman sun nuna cewar, ita sankarar mamar ce ta fi kashe mata da yawa a duniya.

Kuma a shekarar 2015 sankarar mamar ta yi sanadiyyar mutuwar mata 570,000 a duniya.

Dr Zainab Bagudu, likitar mata da kanana yara, kuma matar gwamnan jihar Kebbi, wadda ta kafa gidauniyar MedicAid da ke yaki da cutar sankara a arewacin Najeriya ta ce: “A Najeriya, muna da karancin samun tabbacin yawan ko wacce cuta, ko mura ko malariya, balle ciwo mai tsanani kamar sankara.

“Amman an yi kiyasin cewar mutum sama da 250,000 ne kamuwa da cutar a ko wacce shekara a Najeriyar,” in ji ta.

Amman ta yaya ake kamuwa ta cutar sankaran mama?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suka aiko mana ta shafinmu na BBC Hausa.com bayan da muka bukaci su turo tambayoyin da suke so sani kan wannan batu.

Dr Zainab Bagudu ta ce cutar sankara tana da wahalar ganewa kuma ba a san takamaiman dalilin da ke sa a kamu da cutar ba.

Ita ma wata kwararriyar likita da ta taba aiki a asibitin kasa na Najeriya da ke Abuja, wadda a yanzu haka ta bude nata asibitin, Dr Hajara Yusuf, ta ce har yanzu ba a gano takamaiman dalilin da ke janyo cutar ba.

Amman ta ambato dalilai da ke taimakawa wajen kamuwa da cutar.

Dalilan sun hada da yawan shekaru (a Najeriya macen da ta kai shekaru 50 na iya kamuwa da cutar), da shan barasa, da amfani da sinadarin Estrogen da kwayoyin halittar da ke dauke da bayanai na gado wadanda ke iya haifar da cutar.

Likitar ta ce sankarar mama da ta mahaifa ne suka fi damun mata.

“Amman maruru ko kurji da ke iya fitowa kan mama ciwo ne na fata,” in ji Dr Hajara.

Likitar ta bayyana cewar kurji yana jikin fata ne, bai kai ga abin da ke cikin mama ba.

Sai dai kuma ba mata kadai ne suke kamuwa da cutar sankarar mama ba, maza ma suna kamuwa da cutar.

Masana sun ce kashi daya cikin dari na masu sankarar mama maza ne.

Hakkin mallakar hoto
DrZus Instagram

Image caption

Dr Zainab ta ce akwai bukatar mata su dinga zuwa ana duba su a asibiti akai-akai

Shima kululu ba shi da wata barazana?

Likitoci sun ce in har mace ta ji wani kululu ko wani kulli cikin nononta, ya kamata ta garzaya zuwa asibiti domin a yi maganin matsalar tun tana karama.

Sai dai kuma ba ko wanne kululu ne sankara ba. Sai an cire kululun an gwada kafin a gane cewar sankarar mama ne ko kuma ba shi ba.

Har wa yau likitoci na son macen da ta lura cewar wani nononta ya fi wani girma ta je asibiti a duba ta domin a iya dakile cutar dajin da wurwuri.

Kazalika in mace ta lura cewar kan nononta ya koma ciki ta yadda jariri ba zai iya kama kan nonon ba, ana son ta je a duba domin yana daga cikin alamomin sankarar nono.

Baya ga haka idan macen da ba ta shayarwa ta ga ruwan na fitowa daga nononta a hade da jini, ita ma ana son ta garzaya asibiti domin a duba.

Sai dai kuma ba ko wacce mace da ke da daya daga cikin wadannan alamun ne ke da ciwon ba, duk da cewa alamu ne da ke nuna cewa mace za ta iya kasancewa da sankarar mama.

Ta yaya za a guje wa Sankarar mama?

Masana sun ce za a iya guje wa sankarar mama ne ta hanyar fitar da gujewa abubuwan da ke taimaka wa sankarar mama irin su barasa da sinadarin Estrogen da sauransu.

“Da farko zan ce yana da kyau mutum ya ci abinci mai kyau. Abinci, ba wanda ake saya a kanti ko ake sarrafawa a zuba a robobi ko gwangwanaye ba, abinci wanda muke nomawa, wanda za a ci.

“Ba wanda ya yi shekara daya a cikin firiza ko kuma firji ba, ko kuma an dauko shi cikin gwangwani daga can kasashen waje, ya dade a tashar jirgin ruwa, sannan kuma a zo da su Najeriya,” In ji Dr Zainab Bagudu.

Wace illa sankarar mama ke yi wa yaro? Wannan ma tambaya ce da ta fito daga wajen mutane da dama kan batun.

Masana sun ce sankarar mama ba ta yi wa jaririn da ake shayarwa illa domin shi sankarar ba ta yaduwa da jini ko nono. Saboda haka ana ganin mace mai wannan larurar za ta iya shayarwa ba tare da wani fargaba ba.

Ta yaya ake maganin sankarar mama?

Ana maganin sankarar mama ne a manyan asibitoci inda ake da kayayyakin aikin da kwararru kan maganin sankara.

Ban da maganin sha, ana maganin sanakarar mama ta hanyar cire sankarar mama ya kama da kuma gasa wurin da ya kamu da ciwon ta yadda sankarar za ta mutu.

An yi wannan makalar ne kan sankarar mama bayan masu bibiyar Sashen Hausa na BBC suka turo mana tambayoyi game da larurar.

Ban san abin da ke damun Buhari ba – Lai Mohammed


A cikin wannan shekarar sau uku Shugaba Buhari na zuwa LandanHakkin mallakar hoto
NIGERIAN GOVERNMENT

Image caption

A cikin wannan shekarar sau uku Shugaba Buhari na zuwa Landan

Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce bai san takamaiman abin da ke damun Shugaba Muhammadu Buhari ba ta bangaren lafiyarsa, don haka ba zai iya yi wa ‘yan kasar karin bayani ba.

Alhaji Lai Muhammed ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da sashen Turanci na BBC Newshour.

Ga dai yadda hirar ta kasance:

Tambaya:Ko zan iya tambayarka dangane da shugaban kasa da yanayin lafiyarsa, inda ya zo nan London a makon da ya gabata, kuma ziyararsa ta uku kenan cikin shekara, inda a wancan karon ya shafe wata uku ana duba shi. To yaya lafiyarsa take?

Lai Mohammed: Ya samu sauki sosai, ya murmure.

Tambaya:To ko wacce irin cuta ce shugaban yayi fama da ita?

Lai Mohammed: Ina ganin cewa, shugaban ne kawai yake da ikon bayyaana ciwon da yayi fama da shi.

Tambaya:To ko kai kasan cutar da yayi fama da ita?

Lai Mohammed: Ban sani ba, kuma bana son na sani.

Da gaske, a matsayinka ministan watsa labarai?

Tambaya:Eh.

Tambaya:To menene yasa haka?

Lai Mohammed:Wannan wani abu ne da ya shafi shugaban kawai.

Tambaya:Amma wannan abu ne da yake da matukar muhimmanci da ‘yan Najeriya zasu so su sani?

Lai Mohammed: Ina ganin koda a matsayinka na shugaban kasa, kana da ikon kare sirrinka, a wasu lokuta, kuma ina ganin babu wani abin sirri kamar yanayin lafiyar mutum.

Tambaya:Na fahimci wannan ikon, amma kuma akwai alhakin sanin wanda ke rike da ragama, wa yake tafiyar da abubuwa, ko zai iya rike shugabanci saboda rashin lafiya,inda ya shafe watanni uku anan London don neman sauki?

Lai Mohammed: Mr Frank, baa taba samun gibi na shugabanci a wannan gwamnatin ba, ba a taba samu ba, idan da an samu wani gibi, tattalin arzikin bazai taba farfadowa ba.

Da akwai gibin shugabanci lokacin da shugaban yake Birtaniya, da ba zamu samu nasarar da muka samu a bangaren yaki da rashawa da dawo da zaman lafiya a yankin Niger Delta ba, don haka babu wani gibi, lallai da mun ace yana nan, mun yi kewarsa, amma fa babu wani gibi da aka samu.

Tambaya:Da alama babban lamari ne, idan har shugaban bazai iya samun cikakkiyar kulawar lafiyarsa a kasarsa ba?

Lai Mohammed: Ba wani sabon abune ba, mutum ya yi ciwo na wata uku, sannan ya samu cikakkiyar lafiya.

Tambaya:Eh amma ba kamar shugaban babbar kasa kamar Najeriya ba?

Lai Mohammed: Gaskiyar lamarin shi ne, akwai shugabannin kasashe da yawa, da da wuya ake ganin su.

Tambaya:Misali kana nufin kamar su Zimbabwe?

Lai Mohammed: Aa, aa bazan kira sunan kowacce kasa ba, abinda nake nufi shine babu wani laifi a rashin lafiya, da kuma samun sauki, tare da dawowa kan aiki.

Tambaya:Kana nufin ya samu sauki, ya murmure kenan.

Lai Mohammed: Eh tabbas shugaban kasa ya mumure sosai ma kuwa.

Bashi ya sa Najeriya ficewa daga wasu kungiyoyi


Najeriya na cikin kungiyoyi da dama wadanda ake bayar da gudunmuwa wajen tafiyar da suHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta dauki iya abin da take ganin za ta iya ne wajen mu’amala da kungiyoyi.

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar ficewa daga wasu kungiyoyin kasa da kasa kusan 90, sakamakon dawainiyar da ke tattare da mu`amala da kungiyoyin.

Majalisar zartarwar kasar ce ta dauki wannan matakin, tana cewa bashin kudin gudummuwar raya kungiyoyi kadai da ake bin gwamnatin ya zarta dala miliyan 100.

Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, akwai kungiyoyi birjik ko na tsakanin kasa da kasa ko na Majalisar Dinkin Duniya ko kuma na kungiyar hadin kan Afirka da Najeriya ta shiga cikinsu wadanda kuma dukkansu akwai bukatar gudummuwar da duk kasar da ke cikinsu sai ta bayar a karshen kowacce shekara.

Malam Garba Shehu, ya ce saboda irin wadannan kudaden gudummuwar tafiyar da kungiyoyin wadanda Najeriya ba ta biya ba, har ta kai idan aka je taro akan bukaci mi wkiltar Najeriya da ke wajen ya fita, saboda kawai ana bin kasarsa bashin kudin gudunmmuwar kungiyar.

Ya ce hakan ba karamin abin kunya ba ne ga Najeriya.

Don haka shugaba Muhammadu Buhari ya ce, to ya kamata a sake lale, inda za a baje irin wadannan kungiyoyin a faifai a zabi wadanda ke da amfani ga kasar dan a ci gaba da tafiya tare da su.

Kakakin shugaban Najeriyar, ya kara da cewa wasu basukan da ake bin Najeriyar ma, wani ko shugaban kasa ko kuma minista ne zai je tarukan irin wadannan kungiyoyi ya yi alkawarin cewa, ai Najeriya za ta bayar da gudunmuwar kaza wanda kudin ma babu su a kasa.

Ya ce: ”To irinsu ne suka taru suka yi wa Najeriya yawa, har ta kai ana kunyata ta a wajen taro.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a wannan bangare, gwamnatinsa za ta dauki iya abin da take ganin za ta iya ne wajen mu’amala da irin wadannan kungiyoyi.

Malam Garba Shehu, ya ce wadannan basukan ma da aka ce ana bin Najeriyar, tun na shekara da shekaru ne, don haka a kididdige shi ma abu ne mai kamar wuya.

Hak kuma ya yi nuni da cewa, ba matsi ne ya sa Najeriya za ta fice daga wadannan kungiyoyi ba, sanin ciwon kai ne kawai.

Zakarun Turai: Chelsea ta kafa tarihi bayan doke Atletico 2-1


Michy Batshuayi lokacin da ya zura kwallonsaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Cin da Michy Batshuayi ya yi shi ne na biyu a gasar kofin zakarun Turai a kakar nan

Chelsea ta bi Atletico Madrid har gida ta doke ta da ci 2-1 a wasansu na kofin zakarun Turai na rukuni na uku (Group C), a ranar Laraba.

Minti 40 da fara wasa Antoine Griezmann ya ci Chelsea da fanareti, bayan da David Luiz ya rike Lucas Hernandez lokacin da aka yo wani bugun gefe.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 59 sai Morata, wanda Chelsea ta sayo daga Real Madrid ya rama mata kwallon, kafin kuma a dakika ta kusan karshen wasan Michy Batshuayi ya ci wa Blues din ta biyu.

Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Wasan farko na kofin zakarun Turai kenan da Alvaro Morata ya yi wa Chelsea

Nasarar da Batshuayi wanda ya shigo wasan daga baya, ya sa Chelsean ta samu ta zo ne bayan damar da Cesc Fabregas da Morata suka barar.

Yanzu Chelsea ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta bi Atletico gida ta doke ta, kuma hakan ya kasance rashin nasara na farko a gasar Turai da kungiyar ta Spaniya ta yi a sabon filin wasanta.

Sannan hakan ya kawo karshen wasa 11 da Atletico wadda ta je wasan karshe biyu a shekara hudu da ta wuce ta gasar, ta yi ba tare da an doke ta ba a gida a gasar kofin na zakarun Turai.

Wannan shi ne karo na biyu da Atletico ta sha kashi a karkashin kociyanta Diego Simeone a wasa 24 na kofin zakarun Turai a gida.

Nasarar ta sa Chelsea ci gaba da kasancewa ta daya a rukunin (Group C) da maki shida, biyu kenan tsakaninta da Roma, sannan kuma biyar tsakaninta da ta uku Atleticon.

Sakamakon sauran wasannin na zakarun Turai na Laraba;

FK Qaraba 1- 2 Rom

Paris SG3-0 Bayern Mun

Anderlech 0- 3 Celtic

Juventus2- 0 Olympiakos

Sporting 0- 1 Barcelona

Zakarun Turai: Mourinho ya ce suna gaba da kaiwa matakin gaba


Romelu Lukaku lokacin da yake cin kwalloHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu Lukaku ya ci wa Manchester United kwallo 10 a wasa tara

Jose Mourinho ya ce gab suke da kaiwa matakin sili-daya-kwale a gasar zakarun Turai bayan da Manchester United ta bi CSKA Moscow har gida ta casa ta da ci 4-0.

Kociyan ya ce duk da cewa wasa hudu ne yanzu a gabansu a rukunin, kasancewar sun fara da kyau, yana ganin kamar ma sun kai mataki na gaba na gasar.

A wasan na rukuni na daya (Group A), wanda aka yi ranar Laraba, Romelu Lukaku, ya ci biyu sannan Anthony Martial ya ci da fanareti, kafin Henrikh Mkhitaryan kuma ya ci ta hudu.

Mourinho ya ce abin da ke da muhimmanci shi ne a wasa biyu suna da maki shida, sannan kuma ga su da kyakkyawan matsayi a gasar, in ji kociyan wanda kungiyar tasa ta doke Basel 3-0 a wasansu na farko.

Da wannan sakamako, yanzu Lukaku ya ci kwallo 10 a wasa tara, tun lokacin da ya koma United daga Everton a lokacin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa da ta gabata.

Yanzu dai a tarihi ba a doke Man United ba a wasa shida a waje da wata kungiya ta Rasha.

‘Yan wasan kungiyar ta Premier sun sanya rigarsu ta uku ne mai launin fatsa-fatsa, launin da rabonsu da sanyawa tun lokacin wasansu na Premier a gidan Southampton a watan Afrilu na 1996.

A wancan lokacin Southampton ta ci su 3-0 a kashin farko na wasan, abin da ya sa ‘yan United din suka sauya rigar, saboda wai ba sa ganin junansu.

To amma a wannan wasan da CSKA ba su gamu da wannan matsala ba, inda suka kwashi garabasa a karawar ta gabashin Turai.

A daya wasan rukunin tsohon dan gaba na Norwich Ricky van Wolfswinkel ya ci da fanareti, a wasan da Basel ta casa Benfica 5-0.

Manchester United ce ta daya a rukunin da maki shida, sai Basel da maki uku, yayin da CSKA mai maki uku ita ma take zaman ta uku, amma da bashin kwallo biyu, Benfica tana ta karshe ba maki ko daya.

Ronaldo ya buga wa Madrid wasa sau 400


Image caption

Ronaldo ya kafa tarihi a Madrid

Cristiano Ronaldo ya taka leda sau 400 a Real Madrid, ya kuma ci kwallo 412 a kaka tara da ya shafe a kungiyar. Dan kwallon shi ne na uku da ya kafa tarihin buga wasa sau 400 a kungiyar, bayan Roberto Carlos da kuma Marcelo.

Ya taka wa kungiyar leda a gasar La Liga shida, inda ya ci kwallo 267, ya yi wasa a gasar zakarun Turai ya ci kwallo 90, ya fafata a gasar Copa del Rey, ya ci kwallo 30, ya ci kwallo bakwai a gasar Spanish Super Cup, ya ci kwallo hudu a wasan Club World Cup da kuma UEFA Super Cup. Kuma a kakar wasan 2011/12 da 2012/13 ya fi murza leda fiye da kowanne lokaci, domin a lokacin ne ya buga wasa 55.

Ya kafa tarihi a kungiyar inda ya yi nasara sau 293, abinda ya ba shi damar lashe kofin zakarun Turai uku, da kofin UEFA uku, da kofin Club world biyu, da na La Liga biyu, da na Copa Del Reys biyu da kuma na Spanish Super Cups biyu.

Sojojin Kamaru na 'gallazawa' 'yan gudun hijirar Nigeria


A general view of the IRC (International Rescue Committee) health clinic in Bakassi IDP (Internally Displaced People) Camp in Maiduguri in north-east NigeriaHakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

‘Yan gudun hijira da yawa sun isa Kamaru daga jihar Barno, a arewa maso gabashin Naijeriya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watc, HRW ta zargi jamhuriyyar Kamaru da tursasawa daruruwan ‘yan gudun hijirar Najeriya komawa gida, lamarin da ta ce ya keta dokar kasa da kasa na kare hakkin ‘yan gudun hijira a duniya.

Kungiyar ta kuma sanya Kamaru cikin jerin wasu kasashen duniya da ta ce sun yi kaurin suna wajen tursasawa ‘yan gudun hijira komawa kasashensu.

Ta bayyana hakan ne yayin kaddamar da wani rahoton da ta fitar a kan hakan a ranar Laraba a Abuja.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa game da rawar da ta ce Najeriya ta taka wajen mayar da wasu ‘yan gudun hijirar gida.

Human Rights Watch na zargin sojojin Kamaru cewa suna taso keyar ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, da cin zarafin su da cuma keta musu haddi.

”Kamaru na hukunta ‘yan gudun hijira saboda hare-haren da ‘yan Boko Haran suka kai kasar,” in ji kungiyar.

Kamaru ta musanta zargin da aka mata a baya, inda ta ce ‘yan Najeriyar suna komawa gida ne bisa son ransu.

Wani rahoto na HRW din ya ce: ”Tun farkon shekarar 2015, hukumomin Kamarun sun tursasawa ‘yan Najeriya fiye da 100,000 komawa gida inda yaki bai sarara ba. wadanda a da suke zama a wasu yankuna da ke kan iyakar kasar da Najeriya.”

”Garin fitar da ‘yan Najeriya daga kasarsu, sojojin Kameru su kan dauki matakan cin zarafi da suka hada da duka.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

Mayakan Boko Haram na yawan kai hare-hare Borno, abin da ya sa mutane ke tserewa Kamaru don neman mafaka

Wani mutum dan shekara 43 daga jihar Borno ya fadawa HRW cewa dan uwansa ya mutu sakamakon raunin zubar jini da yawa da ya yi, bayan sojojin Kamaru sun masa dan banzan duka da sanda.

Ya ce: ”Sun azabtar da mu kamar dabbobi kuma sun mana duka kaman bayinsu.”

A farkon wannan shekaran, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta soki Kamaru da tursasawa daruruwan ‘yan gudun hijirar Najeriya komawa arewa maso gabashin Najeriyar.

Hukumomin Kamaru dai sun ce mayakan Boko Haram suna yin badda kama ne su shiga kasar a matsayin ‘yan gudun hijira.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tursasawa ‘yan gudun hijira su koma gida kamar keta dokokin hukumar ne.

Hukumar UNHCR ta ce tursasawar da Kamaru ke yi ga ‘yan gudun hijira su bar kasar mummunan karan tsaye ne ga yarjejeniyar hukumar wadda aka cimma a shekarar 1951 da kuma ta kungiyar Tarayyar Afirka da aka cimma a 1969, wadanda duk Kamaru ta sa hannu wajen amincewa da su.

A can baya dai hukumar ta yi kira ga Kamaru ta girmama yarjejeniyar ta kuma bar kan iyakokinta a bude don masu neman mafaka da ke gujewa rikicin Boko Haram su shiga.

Tun da farko an yi kira Kamaru don ta cika alkawarinta a karkashin yarjejeniyar kuma su ci gaba da ba da izinin shiga yankin da hanyoyin mafaka ga mutanen da ke gudun hijira daga Boko Haram .

Man U za ta fafata da CSKA Moscow ba 'yan wasanta uku


Man United za ta fafata da CSKA Moscow ba tare da 'yan wasanta uku baHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Man United za ta fafata da CSKA Moscow ba tare da ‘yan wasanta uku ba

Manchester United za ta fafata da CSKA Moscow a gasar zakarun Turai na ranar Laraba, inda za ta ziyarci kungiyar ba tare da Marouane Fellaini, dMichael Carrick da kuma Paul Pogba ba.

Fellaini ya yi rauni a wasan da suka kara da Southampton a makon jiya, inda suka yi nasara da ci 1-0.

Pogba bai taka leda ba tun bayan karawarsau da Basel inda suka yi nasara da ci 3-0.

Pogba bai taka leda ba tun bayan karawarsau da Basel inda suka yi nasara da ci 3-0.

Har’ila yau Carrick ma ya yi rauni, sai dai ana sa ran Phil Jones zai iya taka leda bayan dakatar da shi daga buga wasa a Turai.

United ta buga wasa takwas a bana ba tare da an doketa ba, ita kuwa CSKA ta yi nasara a wasanta na farko a rukunin A .

Sauya fasalin Nigeria tamkar samun kasar Biafra ne – Ohaneze


IPOBHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dubban matasa ‘yan kabilar Igbo suna bin kungiyra IPOB mai fafatukar kafa kasar Biafra

Shugaban kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta Ohaneze Ngigbo, John Nwodo ya ce Najeriyar da aka sauya wa Fasali, tamkar Biafra ce.

A hirar da aka yi da shi a shirin Newsday na sashen Turanci na BBC, Mista Nwodo, wanda ya shaida yakin basasar Najeriya, ya ce bai kamata a sake tayar da maganar yakin ko kuma sunan Bifra ba.

Ya bayyana cewar sauya fasalin Najeriya shi ya fi dacewa da muradun ‘yan kabilar Igbo na nan gaba maimakon fafatukar kafa kasar Biafra.

Ga fassarar hirar da aka yi da shi a shirin Newsday:

Bana tunanin ya kamata mu sake tayar da yakin (basasar Najeriya) kuma ko kuma maganar Bifara a yanzu.

Tambaya: Me kake nufi da a yanzu? IPOB ta ce Najeriya ba ta kiyaye hakkokin ‘yan kabilar Igbo dake kudu maso gabashin Najeriya, kuma saboda haka suna son kasarsu. Shin baka yarda da haka bane ko kuma ka yarda?

Nwodo:Dukkanmu mun yarda da ginshikin lamarin. Inda muka yi sabani shi ne hanyar da za a bi (a dakile matsalar). Na yi imanin cewar in aka sauya fasalin Najeriya, tamkar an samar da Biafra ne.

A Najeriyar da aka sauya wa fasali, za su samu ‘yancin kai na tattalin arziki da na siyasa a yankunansu kamar yadda muka samu a 1963.

Tambaya: Abin da kake so shine abin da ake kira cikakkiyar tarayya?

Nwodo: Wannan haka yake.

Tambaya: Amma ba kasa mai cin gashin kanta ba?

Nwodo:A’a.

Ta yaya za ka tinkari dubban matasan da ke gudanar da zanga-zangar goyon bayan IPOB da ke son kasa mai cin gashin kanta?

Nwodo: E, na ji haka a shekarar 1967. Na wuce irin wannan tunanin a yanzu, kuma na san abin da suke nema na da wuyar samu yanzu. Kuma na biyu,fafutukar Biafra din ba alheri ba ne a gare su nan gaba.

Idan kana son kasar Biafra mai cin gashin kanta, sai ka bi wadannan hanyoyin. Sai ka bi ta hanyar zaben raba gardama. Kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba da damar zaben raba gardama ba.

Zan iya ba ka wasu misalai kadan da suka zamo hargitsi kuma har yanzu suna fama. A Sudan yawan kashe-kashe ya tilasta musu su bai wa Sudan ta Kudu ‘yanci tun kafin a gudanar da zaben raba gardama.

A kasar Ethiopia da Eritria irin wannan lamarin ne ya faru. Kuma gabar da ke tsakanin bangarorin biyu na haddasa hasarar rayuka har yanzu a wadannan wuraren biyu.

A daya bangaren na Maroko da Kamaru kuma, har yanzu ba a san yadda za ta kaya ba.

Gaskiyar maganar ita ce bin daya daga cikin wadannan hanyoyin yana da wuyar gaske. Kuma in ka samu kudirin kan lamarin a kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ko kuma Majalisar Dinkin Duniya, za ka bukaci majalisar dokokin kasarmu ta amince da dokar.

Kuma bayan haka za ka bukaci a ware wa hukumar zaben kasarmu saboda ta samu ta shirya zabe. Wannan wani abu ne mai wuya.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da wasu jagorori a al’ummar Igbo ke nesanta kansu da ayyukan fafutukar kungiyar IPOB ba, ko a farkon wannan watan ma, gwamnonin yankin Igbo sun haramta IPOB.

Aman wutar duwatsu ya kori dubban mutane daga muhallansu


A grandfather entertains his granddaughter at the main evacuee camp at the sports stadium in Klungkung, Bali where as many as 4000 people from areas close to the volcano Gunung Agung are camped out in tents waiting for the eruption, the timing of which is unpredictable at the momentHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kwashe dubban mutane daga yankin tsibirin Bali na kasar Indonesiya don gudun afkuwar aman wutar duwatsu kusa da muhallansu

Gwamnatin Vanuatu da ke yankin tsibirin tekun Pacific ta ayyana daukar gagarumin mataki sakamakon karuwar aman wuta da duwatsu ke yi.

A kalla mutum dubu shida ne suka bar muhallansu a tsibirin Ambae, tun bayan da duwatsu suka fara aman wuta, lamarin da ya kara sanya fargaba a zukatan mutane.

Jami’ai a hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, sun ce duk mutumin da ke zaune a wurin da ke da nisan kilomita shida daga wajen da duwatsun ke aman wutar, to yana cikin hadari.

Ana tsoron cewa, ruwan guba zai iya lallata amfanin gona.

Haka ma mutum fiye da 75,000 a yankin tsibirin Bali a kasar Indonesiya, sun gudu daga gidajensu da ke kusa da Tsaunin Agung saboda ana tsammanin shi ma zai fara aman wuta.

Kwararru a kan iimin duwatsu masu aman wuta suna ta tattara bayanai a kan daruruwan adadin lokacin da kasa ta yi motsi, wanda hakan ya sa, suka gane cewa da alama duwatsun za su iya aman wuta.

An rarraba wa fiye da mutum 500,000 abin rufe fuska a yankin, yayin da ake kai abinci da ruwan sha kuma zuwa sansanonin da aka mayar da mutane.

'Tattalin arzikin duniya na tsaka-mai-wuya'


Taron tattalin arziki na duniya ya ce har yanzu tattalin arzikin duniyar na cikin matsalaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Taron tattalin arziki na duniya ya ce har yanzu tattalin arzikin duniyar na cikin matsala

Wani rahoto da taron tattalin arziki na duniya ya fitar, ya yi gargadin cewa har yanzu tattalin arzikin duniya na kan siradin fadawa cikin matsala, shekara 10 bayan matsalar da ya shiga.

Rahoton ya ce, bankuna ba su gama farfadowa ba, kuma manyan bankuna na duniya har yanzu suna da karfin da bai kamata a barsu su durkushe ba.

Kazalika rahoton, ya gano wasu sabbin hadurran da ke tattare da harkokin kasuwanci inda ake samun karuwar bayar da basuka a China da India.

Sannan kuma ga yadda faduwar farashin kayayyaki ke shafar bankuna a yankin Latin Amurka da Afirka.

Fim ba zai hana ni karatu ba – Maryam Yahya


Sabuwar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahya, ta ce sana’arta ba za ta hana ta ci gaba da karatu ba.

Tauraruwar Maryam ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko wato Mansoor.

A wata hira da Yusuf Ibrahim Yakasai, ta shaida masa ta taka rawar babbar jaruma a fim din duk da cewa shi ne fitowarta ta farko a fina-finan Kannywood, saboda ta kudurci aniyar taka rawar da masu shirya fim din suka umarce ta duk da kasancewarta sabuwar fitowa.

Mata 100: Ko mata za su iya kawo sauyi a mako daya?


President Sirleaf, Peggy Whison and Steph HoughtonHakkin mallakar hoto
Getty Images

Masu iya magana na cewa rana ba ta karya, Allah Ya kawo mu shekara ta kawo mu.

Bana ma za mu kawo muku shirin mata 100 rabin muryar al’ummar duniya kamar yadda muka yi a kowace shekara.

Zuwa yanzu an bayyana sunayen mata 60 ciki har da matar da ta je sararin samaniyya, Peggy Whitson, da Shugaban Laberiya Ellen Johnson Sirleaf da kuma ‘yar wasar kwallon kafar Ingila, Steph Houghton.

Za mu bayyana sunayen sauran guda 40 cikin watan gobe.

Jerin shirye-shiryen Mata 100 na shekara-shekara yana duba batutuwan da suke ciwa mata tuwo a karya ne – shin ko wannan shekarar za ta bai wa mata damar sauya al’amura.

Har ila yau cikin matan da za mu tattauna da su akwai mawakiya Rupi Kaur da Resham Khan (wadda aka watsa wa Acid) da kuma tauraruwar wani shirin talabijin, Jin Xing.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jerin shirye-shirye za su kunshi labarai na cin zarafin da rashin adalci da sauransu, wadanda suke sanya gwiwoyin mata su yi sanni.

Saboda haka muna bukatar mata su yi tunanin hanyoyin magance wadansu daga cikin rashin adalcin da ake musu.

Bana ce shekara ta biyar da ake gudanar da wannan shiri na musamman kuma za a duba batutuwa hudu ne|:

1. Mata da suka cimma wani babban mataki

2. Ilimin Mata

3. Cin zarafin mata a bainar jama’a

4. Nuna wariya ga mata a fannin wasanni

Mene ne shirin Mata 100?

Shirin Mata 100 yana bayyana sunayen mata 100 wadanda suka yi zarra da tasiri a fadin duniya kowace shekara.

A shekarar 2017, muna bukatarsu da su magance wadansu manyan batuwa guda hudu da suke jawo wa mata cikas a yanzu – cimma wani babban mataki da batun ilimi da batun cin zarafi da kuma nuna wariya musamman a fannin wasanni.

Da taimakonmu, za su lalubo hanyoyin magance matsalolin kuma muna so su ba da gudunmuwa da shawarwari.

Za a iya tuntubar mu a shafukanmu na Facebook da Instagram da Twitter da kuma ta hanyar amfani da maudu’in #100Mata


Wadansu daga cikin mutanen da ke cikin jerin Mata 100 za su yi aiki ne daga birane hudu a tsawon mako hudu na watan Oktoban bana, inda za su samar da hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin.

Sauran za su ba da gudunmuwarsu daga sauran sassan duniya.

Za a bayyana ragowar sunayen mata 40, yayin da mata ke ci gaba da shiga shirin da kuma ba da gudunmuwarsu da kwarewarsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Idan shirin Mata 100 ya yi nasara, an cimma hakan ne saboda mata daga sassan duniya sun taimaka wajen fahimtar wadannan matsaloli.

Saboda sun ba da gudunmuwarsu game abin da suka sani. Ko kuma sun zo da wani sabon abu da kansu.

Shirin Mata 100 zai tattauna da mata ta rediyo da intanet da kuma shafukan sada zumunta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Batun mata da suka cimma wani babban mataki za a tattauna ne a birnin San Francisco, batun ilimin mata kuma za a tattauna shi ne a birnin Delhi, yayin biranen Landan da Nairobi za su waiwayi batun cin zarafin mata, birnin Rio kuma ya duba batun nuna wa mata wariya musamman a fannin wasannni.

Sai dai tattaunawar za a yi ta ne a duniya baki daya kuma muna so mu ji daga mata a ko ina suke a fadin duniya.

“A shekarar 2015, an tattauna batutuwa 150 a harsuna 10 daga kasahe 30, a shakarar 2016 an kara sunayen mata guda 450 a shafin rumbun bayanai na Wikipedia kuma a bana za mu duba batun damawa da mata,” in ji editar shirin Mata 100 Fiona Crack.

“Zai kasance shiri ne mai kayatarwa, amma za mu ga basirar da Mata 100 da su zo da ita a wannan watan.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Muna da wadansu labarai na karfafa gwiwa, inda za mu dubi wadansu abubuwa tara da ba kowa ba ne ya san cewa mata ne suka kirkiro su.

Kuma za mu duba wadansu hanyoyin da mutane suka fito da su wajen magance matsaloli kiwon lafiya da kare mata daga matsaloli.

Za a iya tuntubar mu a shafukanmu na Facebook da Instagram da Twitter da kuma ta hanyar amfani da maudu’in #100Mata

Za a kara yawan haruffan sakon Twitter


Tambarin shafin TwitterHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shafin na Twitter zai yi sauyin ne domin rage damuwar da masu amfani da shi suke yi, da kuma jawo karin mutane cikinsa

Hukumar shafin sada zumunta da muhawara na Twitter ta ce tana duba yuwuwar kawo karshe takaita yawan haruffan da masu amfani da shafin ke yi na iya haruffa 140, inda za ta linka yawan biyu.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiro shafin na Twitter kuma babban shugabansa, Jack Dorsey, ya ce, rubutun da masu amfani da shafin suke yi zai ci gaba da zama dan takaitacce, amma dai yawan haruffan zai iya linkawa biyu, zuwa haruffa 280, a sako daya nan gaba.

Tuni dai aka fara wannan gwaji a tsakanin wasu masu amfani da shafin, ‘ya kadan.

Sabon tsarin dai na nufin fitattu daga cikin masu amfani da Twitter din, kamar Shugaba Donald Trump na Amurka, a yanzu za su samu karin damar bayyana ra’ayinsu cikin sauki.

A wani sako da kamfanin ya fitar game da shirin ya ce, ya fahimci cewa, dadadden tsarin takaita haruffan, abu ne da ya dade yana ci wa wasu mutanen tuwo a kwarya.

Sannan ya ce shi kansa shafin yana fama da matsalar rashin bunkasa yadda ya kamata, saboda haka, sauyin zai iya kasancewa wata hanya da shi kansa zai burunkasa, ya kuma samu sabbin masu amfani da shi.

Daya daga cikin manyan jami’an kamfanin shafin na Twitter Aliza Rosen, ta ce su kansu suna jin yadda abin yake da wuya da bacin rai, yadda za ka yi ta kokarin dunkule sakonka cikin ‘yan wadannan haruffa 140.

Jami’ar ta ce sun jarraba sabon tsarin, sun ga irin tasirin da zai yi, suka ga ya dace, duk da cewa shi ma dai takaitacce ne.

Wasu dai na ganin irin yadda ake samun karuwar damuwa a kan yawan kalamai na batanci da kyama da farfaganda da makamankansu, me zai sa shafin na Twitter ya tashi tsaye wajen ganin ya linka yawan haruffan da ake rubuta sakonni da su a cikinsa.

Cutar daji ta yi kamari a Nigeria


Cutar sankara ko daji babbar illa ce ga rayuwar mutumHakkin mallakar hoto
SPL

Image caption

Sankara ko daji na daya daga cikin cutukan da ke addabar mutane a Najeriya

Cutar sankara na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mata musamman a kasashe masu tasowa.

Uwar gidan gwamnan jihar Kebbi da ke Najeriya, Dakta Zainab Bagudu, kwararriyar likitar kananan yara ce wacce kuma ta kafa gidauniyar ‘Medicaid Cancer Foundation’ don tallafa wa mata masu irin wannan lalura, ta ce cutar sankara cuta ce mai matsalar gaske saboda tana da wuyar ganewa, ga kuma matsalar kula da ita.

Kwararriyar likitar ta ce, mutane da dama ba su fahimci ita kanta cutar ba, sannan kuma har yanzu ba a kai ga gano dalilin da ke sa a kamu da cutar ba a duniya ma baki daya.

Dr Zainab, ta ce akwai bukatar gwamnatocin jihohi da tarayya su samar da na’urorin da ake amfani da su wajen kula da masu lalurar a asibitoci.

Uwargidan gwamnan jihar ta Kebbi, ta ce, bincike ya gano cewa, mutum sama dubu 250 na kamuwa da cutar ta daji a Najeriya a duk shekara.

Kuma hakan ya sa Najeriya ta shiga cikin jerin kasashen da suka fi fama da masu cutar a duniya.

Dr Zainab ta ce, bayan samar da na’urorin kula da masu wannan cuta, ya kamata a shiga wayar da kan mata a birni da kauye, a kan su rinka zuwa asibiti da zarar sun ga wani kari a jikinsu, ko al’adarsu ta sauya, domin a gwadasu a san me ke damunsu.

Ta ce idan aka yi hakan, to ba mamaki a samu raguwar masu kamuwa da cutar a Najeriya.

Zakarun Turai: Real Madrid ta doke Dortmund 3-1, Kane ya kafa tarihi


Cristiano Ronaldo lokacin da ya zura daya daga cikin kwallonsa biyuHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Cristiano Ronaldo shi ne kan gaba wajen yawan kwallo a raga a gasar zakarun Turai, da 109

Cristiano Ronaldo ya zura kwallo biyu a raga yayin da mai rike da kofin Zakarun Turai Real Madrid ta ci gaba da jagora a rukuninsu na takwas(Group H), inda ta doke Borussia Dortmund 3-1.

Tsohon dan wasan na Manchester United yanzu ya ci kwallo 109 kenan a tarihin gasar, inda ya fara zura tasa a raga a minti na 49, sannan kuma ya kara ta biyu a minti na 79.

Tun da farko Gareth Bale ne ya fara ci wa zakarun na Spaniya a minti 18 da shiga fili. cutback and lashing in Real’s third.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya ci wa zakarun Jamus, wadanda har yanzu bayan wasa biyu ba su da maki ko daya, kwallonsu daya tilo a minti na 54.

A wasansu na farko ‘yan wasan na kociya Peter Bosz sun sha kashi da ci 3-1 a hannun Tottenham a filin wasa na Wembley.

A wasan rukunin na gaba zakarun na La Liga za su kara da kungiyar gasar Premier, Tottenham.

A sauran wasannin na rukunin na takwas, zakarun Turkiyya Besiktas sun ci gaba da nasara a wasansu na biyu inda suka doke RB Leipzig ta Jamus da ci 2-0.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan kallo sun kunna fitilun wayoyinsu lokacin da fitilar filin wasan ta mutu

An dakatar da wasan na tsawon minti 10, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, saboda fitilar filin wasan ta mutu.

A karawar da ke zama maimaicin wasan karshe na gasar ta Zakarun Turai ta 2004 tsohon dan wasan baya na Watford Miguel Layun ya zura kwallo a raga a wasan da Porto ta doke Monaco, wadda ta zo wasan kusa da karshe na gasar da ta wuce da ci 3-0.

A karawar da Tottenham ta bakunci Apoel Nicosia, Harry Kane ya ci kwallo uku rigis, inda suka tashi wasan da ci 3-0.

Kane, wanda daman ya ci biyu a wasansu na farko da Borussia Dortmund, ya fara daga ragar ne a minti na 39, sannan ya ci ta biyu a minti na 62, kafin minti biyar tsakani kuma ya kara ta uku.

Nasarar ta sa Tottenham ta zama da maki shida daidai da ta daya a rukuninsu (Group H), kuma mai rike da kofi, Real Madrid, yayin da Dortmund da Apoel Nic suka kasance ba maki ko daya a wasa biyu.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kwallo 34 da Kane ya ci a shekaran nan sun zarta na duk wani dan wasa a gasar Premier a 2017

Muhimmancin kwallo ukun da Kane ya ci:

Dan wasan gaban na Ingila, Kane, yanzu ya ci kwallo 11 ga kasarsa da kuma kungiyarsa a wannan watan, bayan da ya kasa cin ko daya a watan Agusta.

Yanzu ya ci kwallo 34 a wasan gasa 30 da ya yi wa kungiyarsa ta Tottenham a 2017.

Sakamakon cin kwallon yanzu Kane ya zura kwallo a ragar abokan karawa 46, a wasansa na kungiya da kuma karawa da kungiyoyi daban-daban 36 a taka ledar da ya yi wa Tottenham.

Kane yanzu ya ci kwallo a gasar zakarun Turai hudu a jere – ya kasance dan wasan Ingila na biyu da ya yi hakan a gasar, bayan Steven Gerrard, wanda ya ci kwallo a gasar biyar a jere.

Kwallo uku da ya ci na nufin yanzu ya yi bajintar cin kwallo uku-uku rigis a wasa daya, har sau shida kenan a 2017, kadai, kuma tara kenan a tarihin wasansa gaba daya a Tottenham.

Shi ne dan wasan Ingila na bakwai da ya ci kwallo uku a wasa daya a gasar zakarun Turai, bayan Cole da Newell da Owen da Rooney da Shearer da kumaWelbeck.

Yadda nake ilmantar da marayun Boko Haram – Zannah Mustapha


Malam Zannah shi ne wanda ya samar da daya daga cikin makarantun firamare kalilan da suka rage a birnin Maiduguri, inda ake fuskantar tashin hankali a Najeriya.

Har ila yau, tsohon lauyan ya taba taimaka wajen sako ‘yan matan chibok 82 da Boko Haram suka sace.

A wata makarantar addinin Musulunci mai suna Future Prowess, malaman da suke koyarwar suna karantar da daliban kyauta, su ba su abinci da kayan makaranta da magani duka kyauta.

Hakan ya taimaka masa wajen lashe lambar yabo ta Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a bana.

A ranar Litinin ne za a karrama Malam Mustapha da lambar yabon a a bikin da za a yi a birnin Geneva na kasar Switzerland.

An ba mata damar tuka mota a Saudiyya


Wata MataHakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumomin kasar Saudiyya sun bai wa matan kasar damar fara tuka mota, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

Matakin ya biyo bayan wata sabuwar doka ce da Sarki Salman ya yi wadda ta amince a bai wa matan lasisin tuki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito.

Kungiyoyin kare ‘yan cin dan Adam sun shafe shekaru suna kiraye-kirayen ba mata damar tuki da kansu a kasar.

Kuma hukumomi sun sha tsare matan da suka karya dokar haramcin tukin mota.

Costa ya koma Atletico Madrid


Ya ci kwallo 58 a wasa 120 da ya fafata a Blues, da suka hada da wasa 20 na firimiyar kakar da ta kare, inda Chealsea ta lashe kofin.Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Ya ci kwallo 58 a wasa 120 da ya fafata a Chelsea da suka hada da wasa 20 na firimiyar kakar da ta kare, inda Chealsea ta lashe kofin

Dan wasan Chelsea Diego Costa ya kammala koma wa tsohuwar kungiyarsa Atletico Madrid.

A watan jiya ne Chelsea ta cimma matsaya da Atletico Madrid kan sayar dan wasan.

Dan wasan, bai murza wa kulob din leda a bana ba, ya kuma shafe watan Agusta a kasarsa ta haihuwa Brazil.

Shekara uku da ta gabata ne haifaffen Brazil din ya koma Chelsea daga Atletico a kan kudin fam miliyan 32.

Ya ci kwallo 58 a wasa 120 da ya fafata a Blues, da suka hada da wasa 20 na firimiyar kakar da ta kare, inda Chealsea ta lashe kofin.

Benjamin Mendy zai yi jinya a Barcelona


Benjamin MendyHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mendy ya ji rauni ne a ranar Asabar

Dan wasan Manchester City Benjamin Mendy zai je wani asibitin kwararru a birnin Barcelona na kasar Spain, bayan raunin da ya ji a gwiwa a wasansu da Crystal Palace.

An sauya Mandy ne a minti na 29 a wasan da suka doke Crystal Palace da ci 5-0 a ranar Asabar.

Da yake magana game da batun da farko, kocin kungiyar Pep Guardiola ya ce yana ganin dan kwallon zai koma atisaye ne a ranar Litinin.

Sai dai ba a ga dan wasan a lokacin atisayen.

Ramon Cugat ne zai yi wa Mandy magani, wato likitan da ya taba yi wa Vincent Kompany da Kevin de Bruyne magani a kakar bara.

Nigeria: 'Kungiyar Boko Haram ta tarwatse'


Mohamed

Image caption

Mohamed bai san adadin mutanen da ya kashe ba

Boko Haram kungiya ce ta masu dauke da makamai da ke fitowa a lokaci zuwa lokaci a shafin intanet, sannan kungiya ce da ta yi kaurin suna.

Haka kuma kungiyar na ci gaba da ayyukan ta’addanci a arewacin Najeriya, inda hare-haren da take kai wa, musamman ma na kunar bakin-wake ke karuwa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a wannan shekarar.

Sai dai BBC ta samu wata dama da – ba kasafai ake samun irinta ba, na bayanan sirrin kungiyar daga bakin wani dan kungiyar da ya tsere a watan da ya gabata.

Ya bayyana cewa kungiyar ta warwatsu, abin da ke nuni da cewa kungiyar na cikin matsala.

Wakiliyar BBC Stephenie Hegarty ta gana da mutumin wanda aka sauya wa suna zuwa Mohammad, saboda daililan tsaro a birinin Maiduguri, birnin da ya yi suna a yakin da ake yi da Boko Haram, kuma inda kungiyar ta yi barna matuka kafin a kore ta daga cikin birnin.

Muhammed na hannun jami’an tsaro tun bayan da ya gudo daga maboyar kungiyar da ke dajin Sambisa a watan jiya. Ya kwashe tsawon shekara uku tare da Boko Haram kuma an kai hare-hare shida tare da shi. Amma ya ce shi kurtu ne a kungiyar.

Tun da fari dai sun zauna ne a mahaifarsa wato a garin Banki, inda yake sayar da wayoyin salula. Amma wata daya bayan ya shiga kungiyar ne kuma aka tursasa musu komawa Sambisa.

Image caption

Har yanzu ana fama da rashin tsaro a wasu sassan Arewa maso gabashin Najeriya

Muhammad ya zamo mai bai wa matar wani babban kwamanda kariya, ta hakan ne ya san sirrin kungiyar.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na kurtu bai taba ganin shugabansu Abubakar Shekau ba, saboda Shekau na turo ‘yan aike ne daga inda yake boye zuwa wajen kwamandojinsa.

Aikin Muhammed dai shi ne kare Aisha matar kwamandan, amma ba sunanta na gaskiya ba ne.

Sai dai Aisha ta fahimci cewa Muhammed daban yake da sauran ‘yan kungiyar.

Ta gane cewar yana da tausayi da saukin kai. Saboda haka sai ta gaya masa cewar tana son ta gudu daga dajin.

Image caption

Aisha ta bai wa Mohamed shawaran cewar su tsere

Shi ma ya shaida mata cewa yana son ya tsere, daga nan ne suka fara shirya yadda za su yi.

Muhammed yana tsoron cewa idan ya mika wuya sojoji ba za su barshi ba, amma Aisha ta gaya masa cewa babu komai.

Rannan suna cikin shirin tserewa, sai aka kama su aka kuma daure su.

Amman Aisha ta samu ta kwance kanta, sannan suka gudu kuma suka mika wuya ga sojin Najeriya.

Aisha da Muhammed sun ce sun samu tserewa ne saboda kungiyar ta watse.

Mamman Nour wani babban kwamanda ne kuma yana daga cikin jiga-jigan kungiyar.

A cewar Mohammed kwamandan ya bar kungiyar ne saboda babbancin akida. Kuma ya tafi da wasu kayayyakin yakin kungiyar.

Mohammed ya ce Mamman Nur ya bar Shekau ne saboda bai yarda da irin hare-haren kunar bakin waken da yake sawa ana kai wa fararen hula ba.

Sai dai a lokacin da Aisha da Mohammed suka tsere daga dajin Sambisa ba su kadai bane. Akwai wani kyakkyawan yaro da ya biyo su.

Aisha ba ta san sunan yaron ba, amma ta tuna cewa ta taba ganinsa tare da mahaifiyarsa.

Yayin da take magana da BBC, Aishar da Mohammed suna kallon yaron cike da kauna, tashin hankalin da suka fuskanta ya sa sun zamo tamkar iyali guda.

Image caption

An kashe shugaban Boko Haram na farko, Mohammed Yusuf, hannun ‘yan sanda 2009

Nigeria: Za a cire shingayen binciken 'yan sanda


Nigerian policeHakkin mallakar hoto
AFP

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya ba da umarnin a cire shingayen binciken ababen hawa a duk fadin kasar.

Ya ba da umarnin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa CSP Jimoh O. Moshood ya aikewa manema labarai.

Sanarwar ta ce, an umarci a cire shingayen ne musamman na hanyar birnin Legas zuwa Ibadan, da Shagamu zuwa Benin, da Benin zuwa Onitsha, da Okene zuwa Abuja.

Sai kuma Kaduna zuwa Kano, da Katsina zuwa Kano, da Otukpo zuwa Enugu, da Enugu zuwa babban hanyar Fatakwal.

Sanarwar ta ce Sufeton ya bukaci a cire shingayen nan take ba tare da bata lokaci ba, haka kuma an bukaci ayi hakan ne dan saukakawa ‘yan kasuwa da jama’a zirga-zirga daga arewaci zuwa kudancin kasar.

A karshe sanarwar ta bukaci gwamnatocin jihohi, da kananan hukumomi, hukumar karbar haraji ta jihohi da kungiyar direbobi, da kungiyar ‘yan kasuwa da su bai wa jami’an tsaron hadin kai don tabbatar da sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Sanarwar ta ce Sufeton ‘yan sandan Najeriyar ya dauki wannan mataki ne don tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya da kuma tabbatar da doka da oda.

Yadda wani ango ya bata kwalliyar angwancinsa wajen ceto yaro


Groom Clayton Cook saved a boy from drowningHakkin mallakar hoto
Hatt Photography / Facebook

Yayin da ake cikin daukar hoton liyafar wani aure a kasar Canada, kawai sai lamarin ya dauki wani sabon salo a lokacin da angon ya yi tsalle cikin wani rafi don ceto wani yaro da ya nutse cikin ruwan.

Clayton da Brittany Cook suna jeru don daukar hoto a kan gadar wani wajen shakatawa a birnin Cambridge na jihar Ontario, lokacin da Angon ya lura da wani yaro a firgice a cikin rafi.

Bai yi tunanin kayansa na angwanci ba, sai kawai Mista Cook ya yi tsalle cikin ruwan ya ceto yaro zuwa inda ya fito da shi bakin rafin.

Mai daukar hoton ne ya dauki hotunan yadda aka ceto yaron.

Hotunan sun yadu kamar wutar daji.

Clayton fa fadawa BBC cewa: ”Yaran suna ta bin mu na tsawon mintoci, ni kuwa ina ta lura da su saboda suna tsaye kusa da rafin.”

”A lokacin da Brittany take daukar hoto ita kadai sai na gano cewa yaran guda biyu na tsaye a bakin duwatsu.

Hakkin mallakar hoto
Hatt Photography / Facebook

”Sai na ga wani yaro a cikin ruwan yana kokarin dago kansa, a lokacin ne na yi tsalle na afka cikin rafin.

”Kawai sai na tsamo shi daga cikin ruwan, kuma ba abin da ya same shi.”

Matar Clayton ta ce da farko ta zaci wasa yake yi da ya yi tsalle cikin ruwan.

Ta ce: ”Ina ganin mutane da dama ma, irin wannan matakin za su dauka.”

”Juyawar da zan yi, sai na ga har ya fiddo da yaron bakin rafin,” in ji mai daukar hoto Darren Hatt a hirarsa da BBC.

”Don haka na ci gaba da aikina na daukar labaran ranar na hada har da wannan.”

Bayan an ceto shi, babu alamar da ke nuna cewa yaron ya yi rauni amma sai dai ya nuna alamar tsorata, sai ya tafi da yayansa.

Misis Cook ta ce tunanin da mijinta yake yi cikin hanzari da kuma kaunar jama’a da yake yi shi ya sa ta fara son shi da farko.

”Clayton nawa kenan abin sona, wannan kadan kenan daga cikin bajintarsa nan da nan ba bata lokaci,” a hirarta da kafar yada labarai ta CTV.

Yadda Hungary ta ci buri kan yaran da ke tasowa


Jonas Salk ne ya samu nasarar gano allurar rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarun 1950 (Science Photo Library)Hakkin mallakar hoto
(Science Photo Library)

Image caption

Jonas Salk ne ya samu nasarar gano allurar rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarun 1950

Bayan yaki, kasashen ko’ina sun yi karancin ‘yan kadagon da za su yi aikin kyautata rayuwar al’umma – ko da tsarin tattalin arzikinsu na jari hujja ko kwamunisanci ne.

Hungary ta shiga tsaka mai wuya: ba ta da bunkasar masana’antu don haka babu ma’aikatan da za su aikin gina kasar kwamunisanci.

Sai dai al’ummarta da suka rayu bayan yaki suna da karfin yin aiki matukar ba za a tuhumesu a matsayin masu hannu da shuni ko ‘yan tada kayar baya ba, wadanda suka yi yaki tare da Jamusawa ‘yan Nazi (mabiyan Hitler), ta yadda masu irin wannan manufa aka dauke su abokan gaba.

Lokacin da Birtaniya ke karfafa gwiwar masu son yin kaura daga kasashen da taba yi wa mulkinm mallaka don kara yawan ma’aikatanta, kasar Hungary ta tattara burinta kan kananan yara.

Ta ba su ilimi ingantacce da abinci da kula da lafiya kyauta, ta yadda za su girma su zama masu kwazon aiki, wato masu hakar ma’adanai da masu aikin karfe. “Duk inda ka duba za ka ga hotunan lafiyayyu masu tada kwanji na al’umma masi kwazon aiki.

Ba za ka iya kawar da kai ba. Mutum-mutumi da hotuna da jaridu da mujallu duk suna nuni da irin wanan manufa,” in ji Dora.

Don tabbatar da cikar wannan buri, gwamnati ta bullo da matakan karfafa gwiwar mata su haifi ‘ya’ya. Ba a ma damu da cewa ko ba su da aure ba.

Farfagandar zaburar da su cewa: “Haihuwa aiki ne da ya rataya kan matan aure, kuma matarba ce ga ‘yan mata marasa aure.”

A dora harajin musamman ga duk wanda ya kai shekara 20 bai haihu ba. Tun daga 1952 aka mayar da zubar da ciki laifi, tare da gurfanarwa a gaban hukuma (yarda da aikata laifin ma ba ta taso ba) ga matan da ake tuhuma da zubar da ciki da likitocin da suka yi musu aikin.

Don bai wa iyaye mata damar tutiya da jariransu a tituna da dandali-dandalin Hungary, sai kamfanin kera bas na Ikarus ya fara yin kujerun jarirai masu taya a shekarar 1954 – shekarar da Gyorgy ya kamu da cutar shan-inna.

Daya daga cikin mafi soyuwar hotunan da Dora ta gano a lokacin bincikenta na hotunan da aka dauka mafi kyawu a zamanin shi ne kujerar jarirai mai siffar bas (tare da mace tana kalami mai taushi) a gaban layin iyaye masu shiga bas-bas cike da alfahari.

Nazarin shan-inna ya nuna cewa cuta ce da ke far wa yara ta gurgunta su, inda annobarta ta farko ta auku a shekarar 1952, ta biyu kuwa ita ce wadda ta shanye wa Gyorgy kafafu a shekarar 1954.

A shekarar dai kasar Hungary ta sa ido kan yadda aka yi gwajin farko a duniya na rigakafin shan-inna, inda aka farad a yara fiye da miliyan guda a Amurka.

Gwajin allurar Salk ya yi nasara, hart a kai ga an yui mata lakabi da sunansa (Jonas Salk), masanin kimiyya Bayahuden da ya fito daga New York, wanda ya kirkirota ta hanyar amfani da kwayar cutar da ba ta motsi, inda nan da nan aka yadata a fadin Amurka.

A Afrilun 1955 dakin binciken Cutter na Amurka (daya daga cikin kamfanonin da aka bai wa lasisi samar da rigakafin) ya fitar da rukunin farko na kwayar cutar shan-inna mara motsi.

Sanadiyyar hakan kimanin Amurkawa 200 da aka yi wa rigakafin suka kamu da shan-inna. Jaridar Hungary ta yi hanzarin baza cewa, “saboda sakaci dubban yara an mayar da su dabbobin gwajin mummunar kariyar kyauta.”

Kungiyar Likitocin Amurka, daga bisani ta dora alhakin ‘kazancewar lamarin’ kan yawan gwaje-gwajen da aka yi har dakin binciken Cuttter ya yi kaurin suna.’

Kuma a Yunin wata shekarar bayan samun dimbin nasara a duniya sai aka tabbatar da kariya da ingancin rigakafin Salk, inda Hungary ta fara samar da ita a gida.

Ta ma fadada shirin inda ta tura masana kwayoyin cututtuka da Daraktan yin rigakafin cututtukan mutane da cibiyar bincike (kamfanin yin magungunan rigakafi) zuwa kasar Denmark, wata cibiyar binciken cutar shan-inna ta Turai a lokacin..

Ganin an bari sun tsallaka katangar karfe abinj farin ciki ne, bisa la’akari da cewa daukacinsu masana kimiyya ne, wadanda suka hada da likitocin dabbobi da na mutane, wadanda suka zama ja-gaba wajen bai wa al’umma kariyar lafiya kafin yaki.

Amurka ba ta wasarairai da masa kimiyyarta, har ta kai ga ta yi watsi fasfo 600 na neman izini shiga kasar bisa dalilan siyasa kafin shekarar 1958.

Sai dai likitoci dam asana kimiyya sun yi karanci. Mafi yawancinsu sun tsere lokacin da ‘yan Nazi suka mamayi Hungary a shekarar 1944.

Wasunsu suka komo daga Rasha a matsayin fursunonin yaki a sansani ‘ba za su iya yin aiki ba’ (sakamakon tawaya ko azaftarwa) ko an mayar da su kurkukun Saberiya saboda dangantakarsu da masu hannu da shuni. Tsananin bukata dai ya bai wa masana kimiyya ‘yancin walwala fiye da malaman jami’a a sauran fannonin ilimi, a cewar Dora.

“Jam’iyya (mai mulki) ta kawar da ido daga manufofinsu na siyasa da akidun zamantakewar rayuwa, kuma bayan wani lokaci sai likitoci da m asana kimiyya suka sake smaun irin matsayin da suke da shi a al’umma kafin yaki. Ba a samu sauyin zamantakewar al’umma yadda take kafin yaki – sai ma sababbin tsare-tsaren rashin daidaito (na adalci).

Watanni hudu sukar lamirin Amurka da Gwamnatin Hungary ta yi sai ya zame mata dole ta amince da cewa ta yi sakaci. Don haka gina sababbin asibitoci ya zama a kan gaba a tsarin gina kasa na shekara biyar, cikin shekarar 1950, an fitar da tsarin tattalin arziki da bunkasa masana’antu.

Amma a ran ar 19 ga Oktobar 1956, Ministan Lafiya Jozsef Roman ya sanar da shugabannin cibiyoyin kula da lafiya cewa babu wadda aka gina. Asibitocin da ake da su a cunkushe suke, don shawo kan matsalar sauran gine-ginen daba a yi su da nufin kula da lafiya ba, an mayar da su kananan asibitoci (an fara kafa ORFI a tsohon otal).

Roman ya yi ikrarin cewa an yi wasarairai da cibiyoyin kula da lafiyar al’umma da na hana yaduwar annoba.

Hakkin mallakar hoto
March of Dimes/Wikimedia Commons)

Image caption

Jaridun duniya sun yada nasarar da rigakafin shan-inna na Salk ya samu

Rashin zuba kudi a harkar kula da lafiya wauta ce, musamman tun da kula da lafiya kyauta babban jigo ne da shugabannin ‘yan kwamunisanci ke amfani da shi wajen fifita kimar darajar tsarinsu a kan jari hujjan Yammacin Turai, tattare da nuna cewa lafiyayyen jiki ke samar lafiyayyar kwakwalwa da za ta zabar muku mafificiyar akidar rayuwa.

“A dan takaitaccen lokaci rahotanni jarida sun kwata bankado maganganun mista daga kundin tarihi,” in ji Dora.

Kakanninta sun tabbatar da gaskiya. Asibitin da aka duba Gyorgy a Debreceen ya nuna gazawa wajen kula da dimbin yaran da ke fama da cutar shan-inna.

Jami’an kula da lafiya da Janos ke hulda da su sun ba shi shawara kan cewa ORFI na babban wurin kula da masu fama da cutar shan-inna, sannan suna da managartan kayan aikin gyaran gabobin da cutar shan-inna ta lauye, don haka ioyalan Vargha suka mayar da dansu zuwa Budapest kimanin kilomita 250 daga inda suke zaune.

Lokacin yana dan shekara uku, Gyorgy yanzu al’amura kadan zai iya tunawa da suka faru a loakacin da ya shafe a garin Debrecen, in da ya yi fama da ciwon laka (aka rika tsira masa allura a jijiya.

Kuma har farkon shekarun 1950 an a ganin aikin a matsayin tsohuwar dabnarar da aka daina aiki d aita, saboda zafinta, wajen tarairayar cutar shan-inna).

“Na tuna na yi rubda ciki kan teburin aiki, ina kukan zafin ciwo,” in ji shi. “Kuma na yi rigingine a kan gado, wanda ke karshen sakon dakin asibitin, inda ta yiwu muna tare da kimanin yara 12. Da malamar jinya ta zo gadona sai na fara kuka kafin ta iso kaina.”

Ma’aikaciyar British Airways ta ci zarafin ‘yan Nigeria a bidiyo

British AirwaysHakkin mallakar hoto
Getty Images

 

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na mallakin Birtaniya, British Airways, ya kaddamar da wani bincike kan wani bidiyo da bayyana, inda daya daga cikin ma’aikatan jiragensu ta yi wasu kalaman da ake danganta su da na nuna wariyar launin fata kan ‘yan Najeriya.

Ma’aikaciyar dai ta dauki bidiyon kanta ne a yayin da take kan hanyarta ta zuwa filin jirgi inda a ranar za ta yi aiki da jirgin da zai tafi Abuja babban birnin Najeriya daga filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

A wani sako da kamfanin BA ya aikewa BBC ya ce: “Tun bayan da aka jawo hankalinmu kan bayyanar bidiyon, muka fara bincike.

“Ba za mu yarda da kalaman da za su bata wa abokan huldarmu rai ba ko su musguna musu, don haka za mu dauki matakin da ya dace a ko yaushe.

Muna sa ran ma’aikatanmu su zama kwararru a duk lokacin da suke wakiltar British Airways.”

Ma’aiakaciyar dai ta dauki bidiyon ne a cikin motarta, inda daga bisani ya yadu a tsakanin abokan aikinta, wadanda su kuma suka sanar da kamfanin halin da ake ciki.

A cikin bidiyon dai matar tana cewa ne, “Yanzu zan hau jirgin wadannan ‘yan Najeriyar da za su damu mutum da yi min kaza da kaza, ko kuma a sauya min wajen zama, mazan ma har cewa za su yi suna son a mayar da su wajen da za su sake sosai.”

_98019747_ba

Wasu daga cikin irin tsokacin da ake yi a shafukan sada zumunta na Najeriya kan batun

Ma’aikaciyar ta kara da cewa: “Duk ‘yan Najeriya za su dinga damunka da ba ni Coca-Cola, ba ni naman shanu shi na fi so. Me ya sa naman ya kare?

“Sai ya kasance ba ni da abin cewa sai, ‘Yi hakuri naman ne ya kare.’

Ta kuma ci gaba da cewa: “Wannan dare na Juma’a ba zai min dadi ba don zan yi tafiya da mutanen da ba su da aiki sai damun mutum da tambaye-tambaye ko korafi.”

Kafar yada Labarai ta Daily Mail Online wacce ita ta fara yada wannan labari, ta ce an bai wa bidiyon suna: ‘Ba zan iya da azabar tafiya a wannan jirgin ba.”

Tuni dai wannan al’amari ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta na zamani a Najeriya, inda aka dinga mayar da martani ga kamfanin na BA. Ana kuma danganta kalaman matar da cewa kalaman nuna wariya ne.

Da yawan ‘yan Najeriya da ke tsokaci kan batun na nuna zallar bacin ransu ne kan abin da matar ta yi, tare da goranta wa kamfanin na BA cewa dama can ba su cika mutunta ‘yan Najeriya ba.

_98019745_gettyimages-828077072


Kamfanin British Airways na daga cikin manyan kamfanonin da ke yawan zirga-zirga zuwa Najeriya

Za a rantsar da sabon shugaban kasar Angola


Joao LourencoHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ana ganin akwai tarin kalubale a gaban Joao Lourenco wanda kusan zai yi shugabanci ne da sa idon Jose Eduardo Dos Santos

A ranar Talatar nan ne za a rantsar da sabon shugaban kasa a Angola, Joao Lourenco, wanda zai maye gurbin Jose Eduardo Dos Santos, wanda ya shafe kusan shekara 40 a kan mulki.

Ta wani fannin za a iya cewa wannan wani tarihi ne na sauyin mulki a kasar, inda shugaba daya tilo da miliyoyin ‘yan Angola suka sani a kan mulki, zai yi bankwana da kujerar mulki.

To amma fa, kila hakan da wuya ya kawo wani gagarumin sauyi a kan alkiblar tafiyar da horkokin mulkin kasar ta Angola.

Sabon jagora, Joao Lourenco, ya kasance a gaba-gaba a zuciyar jam’iyya mai mulki ta MPLA tsawon shekara da shekaru.

Mutumin da zai gada a mulkin, Jose Eduardo Dos Santos, zai ci gaba da rike iko da jam’iyyar, bayan ikon nada shugaban ‘yan sanda da na soji da zai ci gaba da rikewa, sannan kuma masu suka na cewa ‘ya’yansa, kamar matar da ta fi arziki a Afirka Isabel Dos Santos, an tsara yadda za ta rike ragamar tafiyar da tattalin arzikin kasar.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Joao Lourenco (a dama) ya jira kusan shekara 15 kafin samun yardar Shugaba Dos Santos

Duk da irin dimbin arzikin mai na Angola akwai gagarumin bambanci tsakanin jama’ar kasar, talakawa da masu hali.

Sabon shugaban kasar da tsohon tsarin gwamnatin za su fuskanci bukata ko kalubale na canji na ainahi.

Jam’iyyar MPLA ita ce ke mulkin Angola tun da ta samu ‘yanci daga Portugal a 1975.

Kasar ta yi fama da yakin basasa na tsawon shekaru da ‘yan tawayen tsohuwar kungiyar UNITA (National Union for the Total Independence of Angola ), ta marigayi Dakta Jonas Savimbi.

Yakin da ya zo karshe bayan halaka madugun ‘yan tawayen, a wani kwanton-bauna a ranar 22 ga watan Fabrairun 2002.

Bayan kisan shugaban ‘yan tawayen ne kungiyar ta rikide ta zama jam’iyyar siyasa, inda yanzu ta zama ta biyu a kasar ta Angola.

Da amincewar iyayena na fara fim – Maryam Yahaya


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Na shigo Kannywood da kafar dama – Maryam

Tauraruwar matashiyar jaruma Maryam Yahaya, mai shekara 20, ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko wato Mansoor.

A wata hira da Yusuf Ibrahim Yakasai, ta shaida masa ta taka rawar babbar jaruma a fim din duk da cewa shi ne fitowarta ta farko a fina-finan Kannywood, saboda ta kudurci aniyar taka rawar da masu shirya fim din suka umarce ta duk da kasancewarta sabuwar fitowa.

Ta kara cewa ainahi ba ita ce wadda za ta fito a matsayin jarumar fim din ba tun da fari, ta samu zama tauraruwar ne saboda rashin zuwan ainahin jarumar a kan lokaci, kuma daman tana cikin fim din sai dai fitowa biyu kadai aka shirya za ta yi.

Ta ce ”Ali Nuhu ne ya sanya aka zabo mu biyu a cikin wadanda za su yi fitowa ta musamman, ya ba mu rubutaccen labarin fim din muka karanta Allah cikin ikonsa sai na kasance wadda ta yi daidai abin da ya bukata, ka ji yadda akai na zama jarumar fim din Mansoor,” in ji jaruma Maryam.

Maryam ta kara da cewa: ”Da fari na dan ji tsoro, don ita dayar da aka ba mu labarin muka karanta tare ta ce kawai na je ina ta dari-dari. Ina farawa sai na ga an fara tafi da ihu kawai sai sarki Ali ya ce aje a fara aiki.”

Da aka tambaye ta ko yaya ta ji da aka ce ita ce, za ta zama tauraruwar fim din?

Sai ta kada baki ta ce ”Na ji wani dadi da ba zan iya fasalta yadda na ji ba, amma kam ina cikin tsananin farin ciki a wannan lokacin.” in ji Maryam.

Kishin kasa ya sa na rike mukamin minista har sau biyu — Okonjo- Iweala


Dr. Ngozi ta rike mukamin ministar kudi a Najeriya har sau biyuHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Dr. Ngozi ta rike mukamin ministar kudi a Najeriya har sau biyu

Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin muhimman dalilan da suka sa ta rike mukamin ministar kudi har sau biyu a kasar.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana haka ne a wani shirin turanci na rediyo da BBC ke gabatarwa mai suna “The Conversation” .

Tsohuwar ministar ta ce, mahaifinta ya koyar da ita kishin kasa, dan haka ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta bayar da gudunmuwar da ta dace a lokacin da ta ke rike da mukaman gwamnati.

Dr. Ngozi ta ce, a lokacin da ta rike mukamin minista a farko, ta yi kokari wajen kawo sauye-sauye, wanda har ta kai an samu nasarar yafe wa Najeriya wasu basuka da ake binta.

Tsohuwar ministar ta ce, a lokacin da aka ba ta mukamin minista na farko, ta yi fargaba, saboda rike mukamin ministar kudi ba karamin abu bane musamman a kasa kamar Najeriya.

Dr. Ngozi ta ce wa’adinta na farko a kan mukamin minista shi yafi ba ta wahala, amma ko da ta sake dawo wa a karo na biyu, ba ta ji komai ba, saboda ta san abubuwa da dama a game da mukamin ministar kudin da aka sake ba ta.

Arsenal ta dago sama bayan doke West Brom 2-0


Alexandre Lacazette lokacin da yake zura kwallon farko a ragar West BromHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alexandre Lacazette ya zama dan Arsenal na farko da ya ci kwallo a wasansa uku na farko na lig a gida tun bayan Brian Marwood a watan Satumba na 1988

Alexandre Lacazette ya zura kwallo biyu a raga, wanda hakan ya sa Arsenal ta doke West Brom a nasararta ta uku a jere a Premier bana a filin Emirates.

Dan wasan gaban na Faransa, wanda ya ci kwallo a dukkanin wasannin uku na gida, ya fara daga raga ne a minti na 20, bayan da mai tsaron ragar West Brom Ben Foster, ya kade kwallon da Alexis Sanchez ya dauko a wani bugun tazara, ta doki sandar raga ta dawo.

‘Yan West Brom sun yi korafi kan fanaretin da suke ganin ya kamata a ba su, tun kafin a zura musu kwallon farko a raga, lokacin da Shkodran Mustafi ya bige Jay Rodriguez.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ga alama Mustafi ya yi wa Rodriguez keta amma alkalin wasa Bobby Madley bai bayar da fanareti ba

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Arsenal ta samu fanaretin bayan da Allan Nyom, dan kamaru ya doke Aaron Ramsey.

Daga nan ne Lacazette ya buga fanaretin inda ya ci kwallon ta biyu a minti na 67, wadda ita ce ta hudu da ya ci wa Arsenal din tun lokacin da ta siyo shi a kan kudin da ba ta taba kashewa ba wurin sayen dan wasa, fam miliyan 46.5 daga Lyon.

Wannan nasara ta sa Arsenal ta daga zuwa matsayi na bakwai a tebur, maki daya tsakaninta da ta hudu Tottenhma, sannan kuma shida tsakaninta da ta daya Manchester City.

Ita kuwa West Brom, wadda dan wasanta na tsakiya Gareth Barry ya kawar da tarihin dan wasan da ya fi buga wasan Premier, ta koma ta 12, kuma har yanzu kwallo hudu kawai ta jefa a raga a bana.

Barry yanzu ya buga wasan Premier 633, inda ya kawar da tarihin tsohon dan wasan Manchester United Ryan Giggs

Duk da yadda West Brom ta farfado a salon kai harinta, yanzu ta yi wasa biyar kenan ba tare da nasara ba, kuma wasa daya kawai daga cikin 12 na waje na gasar lig ta yi nasara a 2017.

Shugaba Buhari ya koma gida


Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Shugaban ya koma gida ne da yammacin ranar Litinin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.

Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida.

Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan ba.

Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka.

Kafin tafiyarsa, shugaban ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.

Ana binciken 'yan sandan da suka lakadawa daliba duka


Dalibai da ke zanga-zanga a ranakun karshen makoHakkin mallakar hoto
ANURAG

Image caption

Dalibai mata na jami’ar BHU da suke zanga-zangar yaki da cin zarafin mata ta hanyar lalata da su

Hukumomin yankin arewacin India a jihar Uttar Pradesh, sun bukaci a gudanar da bincike, bayan wani dan sanda ya lakadawa wata dalibar jami’ar jihar duka, wadda ke cikin masu boren kin amincewa da cin zarafin mata ta hanyar lalata da su.

Lamarin dai ya fito fili, bayan wasu hotuna da aka yada a shafukan sada zumunta kan yadda dan sanda ya ke dukar dalibar jami’ar Banaras Hindu .

An dai dakatar da dan sanda daga bakin aiki bayan fitowar lamarin. Yayin da dakin kwanan dalibar a jami’ar suka tafi hutun wucin gadi.

Sai dai ‘yan sandan sun ce, dole ce ta sanya suka yi amfani da karfin iko ciki har da duka, bayan daliban sun fara tayar da tarzoma.

Sun kara da cewa, daliban sun yi ta jifarsu da duwatsu, da cinnawa motocin mutane wuta, da lalata gine-ginen jami’ar.

Sai dai daliban sun musanta wannan zargi.

Hukumomin jami’ar sun dora alhakin komai kan mutanen da ke wajen jami’ar wanda su ne suka fara rura wutar rikicin.

An ci gaba da zaman dar-dar a yankin Vanarasi inda jami’ar Banaras ta ke, an kuma girke jami’an tsaro a birnin don kwantar da tarzoma.

A ranar alhamis ne dai aka fara zanga-zangar, bayan daliban sun yi zargin hukumomin makarantar sun yi biris da korafin da suka yi na yunkurin cin zarafinsu ciki har da kokarin yin lalata da su.

Hakkin mallakar hoto
ANURAG

Image caption

Hukumomin jami’ar sun zargi mutanen da ke wajen jami’ar da rura wutar rikicin

Daliban sun ci gaba da zanga-zangar lumana har zuwa ranar Asabar, lokacin da ‘yan sanda da suke sanya ido kan masu zanga-zangar suka zargi dalibai 100 da suka taru a kofar shiga jami’ar da aikata ba daidai ba.

Sai dai hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta, sun nuna ‘yan sanda na dukan daliba da sanda, bayan sun tasa keyar wadandacan daliban.

Kuma da suka zo wajen babu jami’ar tsaro mace ko guda daya da suka zo da ita.

Shugaban jami’ar Girish Chandra Tripathi ya shaidawa BBC Hindi cewa za su gana da matan masu zanga-zangar.

Ya kuma ce hukumomin makaranta za su yi bincike cikin tsanaki dan tabbatar da gano bakin zaren.

Ya kara da cewa watakil a lokacin da daliban suke zanga-zangar ‘yan sandan sun ga wani abu da bai da ce ba.

Sai dai daliban sun yi zargin cewa, an karkatar hankali baki daya daga ainahin korafin da suke yi na cin zarafinsu ta hanyar lalata.

Wata daliba mai suna, Akanskha Gupta, ta ce jami’an da ke kula da dakunan kwanan dalibai ba su dauki korafinsu da muhimmanci ba.

”A lokacin da mukai korafin ana kokarin yin lalata da mu, babu abin da aka yi face neman dora mana laifin ta hanyar yi mana wasu tambayoyi marasa kan gado.

Ciki har da wai karfe nawa muke barin dakunan kwanan mu zuwa cikin makaranta da kuma lokacin da muke dawowa.

Saboda Allah wannan ai ba tambaya ba ce, kamata ya yi a bamu damar da za mu amayar da dukkan abubuwan da muke gani ko zarga kafin a san ta inda za a taimaka mana.”

Ita ma wata daliba da bata so a ambaci sunanta ba, ta ce: ”Matsalar cin zarafin mata ba sabon abu bane a nan.

Na yi farin ciki da Allah ya sa dalibai mata sun farga da matsalar tare da daga murya dan aji halin da muke ciki a kawo mana dauki.

Sai dai ana neman a maida abin wata siyasa, kuma hakan bai dace ba.”

A bangare guda kuma, ana shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a manyan biranen India, sai dai kawo yanzu ba a fadi lokaci ba.

Nigeria: 'Yan sanda uku sun mutu a harin gidan Zoo


Nigeria PoliceHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Ba kasafai ake kai irin wannan harin a wuraren yawon bude ido ba a Najeriya balle a kashe ‘yan sanda

A Najeriya ‘yan sanda uku sun mutu a wani harin da wasu da ba a san su ba suka kai wa gidan zoo din Ogba da ke birnin Benin a jihar Edo.

Wata sanarwar da Ministan Yada Labaran kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya fitar ta yi Allah-wadai da harin da aka kai ranar Lahadi, inda aka saci shugaban gidan namun dajin Dokta Andy Ehanire.

Mataimaki na musamman ga ministan, Segun Adeyemi, ya tura wata sanarwa ga manema labarai.

Wadda a cikinta ya ce harin da aka kai kan wani wurin ziyarar masu yawon bude ido zai jawo koma baya ga kokarin da gwamnatin kasar na farfado da harkar yawon bude ido.

Sanarwar ta ambato ministan yana cewa: ”Nasara ko kasawa na wuraren yawon bude ido ya dogara ne kan zaman lafiya.”

Ta kara da cewa irin wannan harin da aka kai gidan zoon ya saba wa yanayi na harkar yawon bude ido da kuma kokarin gwamnati na habaka fannin yawon bude idon a matsayin wata hanya ta ciyar da kasa gaba.

”Kashe ‘yan sanda uku da aka saka gidan zoon domin tabbatar da tsaro ga masu zuwa kallon dabbobi da sace shugaban gidan zoo din da kuma tashin hankalin da masu ziyara a gidan zoo din suka fuskanta lamari ne na bacin rai,” in ji ministan.

Alhaji Mohammed ya ce gwamnati za ta matsa kaimi wajen kara matakan tsaro a dukkan wuraren yawon bude ido, inda ya nemi wadanda suka sace Dokta Ehanire da su sake shi cikin gaggawa.

Ministan ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sandan da aka kashe a harin.

An dabawa likita wuka a kan hanyarsa ta zuwa masallaci a London


Altrincham and Hale Muslim AssociationHakkin mallakar hoto
Google Street View

Image caption

An daba wa Dokta Nasser Kurdy wuka ne a kan hanyarsa ta zuwa masallataci

An daba wa wani likita wuka a bayan wuyansa lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa masallaci a yankin Greater Manchester a kasar Ingila, wani al’amari da ake zargin nuna kiyayya ne.

An kai wa Likita Nasser Kurdy, wanda babba ne a bangaren tiyata, harin ne a wajen wata cibiyar Musulunci ta Altrincham and Hale, da misalin karfe 17:50 BST kuma an kai shi asibiti.

Tuni aka sallame shi daga asibiti, an kuma kama wasu mutane biyu masu shekaru 54 da 32 da ake tuhuma, ana musu tambayoyi.

‘Yan sandan yakin Greater Manchester suna bukatar ganau su kawo shaidu.

Majiyoyi a yankin sun ce Kurdy ya ji wasu na kalaman kin jinin musulunci a yayin da aka kai masa harin.

‘Yan sanda sun ce likitan mai shekara 58 shi ne mataimakin limamin masallacin yankin, kuma a ranar shi ne zai jagoranci sallah, a lokacin ne ya hango wani mutum a tsallaken hanya.

Jim kadan bayan haka ne, ya ji an daba masa wuka a wuyansa. Daga nan ne ya ruga a guje cikin masallacin, sannan ya kirawo masu bayar da agajin gaggawa.

Wani babban jami’in ‘yan sanda, Russ Jackson ya ce wannan kazamin hari an kai shi ne ba tare da mutumin da aka kai wa, wanda mutane ke kauna, ya ce uffan ba.

”Kalaman Batanci

Wani likita, Kalid Anis, mai magana da yawun masallacin, ya ce, ”Lamarin na iya fin haka muni .

Shi [Kurdy] ya ce ya lura da wani mutum a tsallaken hanya, sannan kuma sai kawai ya ji wani ya daba masa wuka ta bayansa.

”A lokacin da aka daba masa wukar, yana cikin gigita, don haka ba zan iya sanin irin kalaman da aka fada ba, amma na tabbata kalaman cin mutunci ne.”

Akram Malik, limamin masallacin cibiyar Altrincham and Hale ya kara da cewa: ” Abin bakin cikin ne mutuka game da yadda aka kai hari kan wannan jagora a kan hanyarsa ta zuwa masallaci.”

'Yadda aka fille kan mijina'


Tun a watan Oktoba tashin hankali ya barke a yankin Kasai na Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, hakan ya janyo mutuwar daruruwan farar hula.

Hakan dai ya biyo bayan fadan da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da wasu ‘yan gwagwarmaya da gwamnati ke marawa baya da aka fi sa ni da Bana Mura a bangare daya, da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta Kamuina Nsapu.

An dai kona kauyuka da dama, yayin da wani kiyasi ya tabbatar da akalla mutum sama da miliyan daya ne suka rasa muhallansu a yankin cikin shekara guda.

Wani mai daukar hoto John Wessels ya yi tattaki zuwa yankin Kasai domin ganawa da wadanda lamarin ya rutsa da su.

Bernadette Tchanda, 16

Bernadette na zaune a dandabaryar simintiHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Bernadette na zaune a dandabaryar siminti

“An daba min wuka, yayin da yara suka nutse a ruwa saboda mun tserewa gidanmu a lokacin da aka kone gidaje babu abin da muka tsira da shi.”

“Mutanen birnin Tshikapa suna da karamci, don sun taimaka mana. Anan da ka gan mu, muke rayuwa a dandabaryar siminti babu tabarma ko gado.”

”Ba za mu taba komawa gida ba, saboda tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci. Za su gane mu, babu makawa kashe mu za su yi da sun ji yaren da muke yi.”

Emmanuel Mtumbo

Emmanuel ya na tsaye a gaban rugujajjen gidansaHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Emmanuel ya na tsaye a gaban rugujajjen gidansa

“Makiyanmu ne suka shigo kauyen nan da rana tsaka, suka shaida mana sun zo su hallaka mu ne tare da kona gidajenmu.

”Bayan kwanaki kadan, sai sake dawowa da adduna da barandami a hannunsu. Na rasa komai da na mallaka, sun kashe matata, da ‘ya’ya na biyu mace da namiji. Sun kuma kashe yayana.”

A burnt down house.Hakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

“Sai kuma suka sake dawowa, suka kona duk wani abu da muka mallaka, ciki har da takardar shaidar kammala karatun Difiloma. Abin da na ke tunkaho da su kenan, amma ba su bar min komai ba, na san babu ta yadda za su dao.”

”A halin da ake ciki ban san yadda zan yi ba, ban ma san ta inda zan fara rayuwa ba.”

Anny Mufutani, 30

Anny a lokacin da za ta daura kallabi a kan taHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Anny a lokacin da za ta daura kallabi a kan ta

“Mayakan kungiyar Kamuina Nsapu sun shigo kauyenmu a lokacin da muke bacci. Dama dai mun ji jita-jitar wai za su kawo mana hari, don haka na tanadi wata ‘yar jaka da na zuba abinci a ciki.

“Don haka sai muka shirya tserewa, ni da mijina da kuma ‘ya’yanmu biyar daga shekara 11 zuwa wata shida, a lokacin da suke harbe-harbe sun samu mijina a bata kashin da suka yi da mutanen kauyenmu.

”Dama dai ina son tserewa gidan ‘yan uwanmu da ke birnin Kinsasha, to amma hakan ba za ta yiwu ba, saboda ina bukatar kudin mota har 60,000 kudin kasar mu wato daidai da kusan Fam 29 kowanne mutum daya, ba ni da wannan kudin. Ba kuma zan iya guduwa na bar ‘ya’yana su kadai ba.

”A halin da ake ciki na karaya, na sare ba ni da wani kuzari sam saboda zazzabin cizon sauro da ya kwantar da ni saboda zaman da muka yi a jeji a lokacin da muke gudun ceton rai, ga yunwa ta galabaitar da ni.”

Raphael Kabulewu

Raphael zaune a kofar wata cibiyar lafiyaHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Raphael zaune a kofar wata cibiyar lafiya

Tun a shekarar 1999 Raphael Kabulewu ya zama limamin Chici, a hoton da ke sama ya na zaune ne a kofar cibiyar lafiya ta Biyega da ke kauyen Tshikapa.

“Tun a watan Afirilu na ke bai wa marayu matsuguni, musamman yara da suka zo cibiyar lafiyar nan cikin mawuyacin hali jina-jina. A yanzu akalla akwai iyalai 200 a waje na.

Mutanen da suka rasa muhallansu na tsaye a kofar shiga cibiyar lafiya ta Biyega a kauyen Tshikapa.Hakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Mutanen da suka rasa muhallansu na tsaye a kofar shiga cibiyar lafiya ta Biyega a kauyen Tshikapa.

“Yawancin yaran akan idonsu iyayensu suka mutu, ba su da komai.

“A yanzu ciyar da su da ba su magani ya rataya ne a wuyana saboda su na fama da cutar amai da gudawa da zazzabin cizon sauro.”

Sara Mbindi, 33

Sara rike da jaririntaHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Sara rike da jaririnta

“Mako guda da ya wuce na haifi Da na Etienne. A lokacin da na tsere daga kauyenmu tare da ‘ya’yana biyu da kuma mijina, amma a hanya aka tsare mijina aka fille masa kai. A kullum na tuna abin nan sai na zubar da hawaye.

”A lokacin da muka iso wannan cibiyar lafiyar, ma’aikatan lafiya da Limamin Chocin su ne suka taimaka min.

”Ina fatan wata rana ‘ya’ya su koma makaranta, dan su samu rayuwa mai inganci.”

Anne Katshtemba

Yadda aka sarawa wata mace kai da AddaHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Yadda aka sarawa wata mace kai da Adda

“Wani ne ya shafta min adda a akai na, ba tare da bata lokaci ba na yanke jiki na fadi kasa. ‘Yan uwa na sun dauka na mutu saboda yadda na ke cikin jini.

”Allah ya kubutar da ‘ya’yana biyu, saboda sun aikata abin da na umarce su da yi, saboda sun kwanta a cikin jinin tare da sankarewa kamar sun mutu.

Wannan cibiya ita ce kadai wurin da ya rage mana da muke samun nutsuwar rai ba ma kuma fargabar za a biyo mu dan a kashe.”

Astride Bipua, 39

Wata 'yar gudun hijira, ta na gyara wani abu da ake abinci da shi mai suna Misili, zaune ta ke a wani gidan adana kaya da aka bai wa 'yan gudun hijirar suke zamaHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Wata ‘yar gudun hijira, ta na gyara wani abu da ake abinci da shi mai suna Misili, zaune ta ke a wani gidan adana kaya da aka bai wa ‘yan gudun hijirar suke zama

“Na zo wannan wuri ne daga garin Senge, tare da ‘ya’yana mata biyu da kuma Da na.

”A lokacin da muka taho nan ba su da lafiya, saboda sun sha matukar wahala tafiya ce muka yi ta tsahon mako biyu cikin daji, mun sha matukar wahala.

”A lokacin da muka iso, limamin Cocin ya taimaka mana sosai. An ba mu abinci da sutura.

” A garin mu ni malamar makaranta ce, amma abin takaicin na tsere tare da barin takardar shaidar kammala ckaratun Diploma ta. Mafarki na shi ne wata rana na gina makaranta dan ‘yara ‘yan gudun hijira.”

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira, da suke fakewa a wani gidan ajiye kayayyaki da ba a amfani da shiHakkin mallakar hoto
John Wessels / Oxfam

Image caption

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijira, da suke fakewa a wani gidan ajiye kayayyaki da ba a amfani da shi

Babu dama a yi amfani da dukkan hotunan sai da izini.

Macen 'da ta fi kiba a duniya Eman Ahmed Abd El Aty ta mutu'


Eman Ahmed Abd El Aty after the surgeryHakkin mallakar hoto
Saifee Hospital

Image caption

Eman Ahmed Abd El Aty ta ja hankalin duniya ne bayan masu fafutika a shafukan intanet sun yi kira a taimake ta

Macen nan ‘yar kasar Masar da aka yi ammana ta fi kowa kiba a duniya ta rasu a Hadaddiyar Daular Larabawa.

A farko shekarar nan ne aka kai Eman Ahmed Abd El Aty kasar Indiya domin a yi mata tiyatar rage kiba.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce an rage mata kilogiram 300 cikin kilogiram 500 na kibar da take da ita, amma ta rasu sakamakon tabarbarewar da halin da take ciki ya yi.

Wata sanarwa da asibitin ya fitar ta ce macen, ‘yar shekara 37, ta yi fama da ciwon zuciya da na koda.

“Muna yin jaje ga ‘yan uwanta,” in ji sanarwar asibitin.

Tun a watan Mayu ne aka kai Ms Abd El Aty birnin Abu Dhabi bayan an yi mata tiyata a wani asibiti da ke birnin Mumbai na kasar Indiya.

Hakkin mallakar hoto
Saiffee hospital

Image caption

An rage kibar Ms Abd El Aty bayan an rika ba ta abinci mai ruwa-ruwa a Indiya

Kafin a yi mata tiyata, iyayenta sun ce ta kwashe shekara 25 ba ta fita ko da kofar gida ba.

An dauke ta a wani jirgi da aka yi hayar sa zuwa Mumbai domin yi mata tiyata bayan ‘yar uwarta ta nemi a tallafa mata a shafukan intanet.

Amma an dauke ta daga asibitin bayan danginta sun samu rashin jituwa da hukumomin asibitin.

Dangin nata sun nuna shakka kan adadin kibar da asibitin ya ce ya rage daga jikin ‘yar uwarsu.

Za a fara yin shari'ar 'yan Boko Haram 1,600


Sojoji sun ce sun murkushe 'yan Boko HaramHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sojoji sun ce sun murkushe ‘yan Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya don gurfanar da mutanen da ake tuhuma da zama mayakan kungiyar Boko Haram sama da 1,600 a gaban kotu.

Ministan Shari’a na kasar Barista Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa za a fara yi wa mutanen shari’a ne a cibiyoyi daban-daban da ake tsare da su daga watan gobe.

Ma’aikatar shair’ar ta kara da cewa an bayar da shawarar sakin mutane 220 da ake zargi da zama ‘yan Boko Haram saboda babu wata cikakkciyar shaida da ke nuna hakan.

A cewar ministan, an samu alkalai na musamman guda hudu wadanda za su yi shari’ar.

Ya kara da cewa kawo yanzu an kammala shari’ar ‘yan Boko Haram 13, an samu tara da laifi, sannan kuma wasu manyan kotunan tarayya na ci gaba da shari’ar mutum 33.

Rundunar sojin kasar dai ta ce ta kusa murkushe ‘yan kungiyar ta Boko Haram bayan da ta kwace yankunan da a baya suka mamaye.

Sai dai har yanzu ‘yan kungiyar na kai hare-aren kunar-bakin-wake a wasu yankuna na jihar Borno lamarin da kan haddasa asarar rayuwa.

Jam'iyyar ƙin musulunci ta samu tagomashi a Jamus


German ProtetersHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu zanga-zanga sun auka kan tituna don nuna adawarsu kan tagomashin da AfD ta samu

Zaben majalisar dokokin Jamus ya ba shugaba Angela Merkel damar zarcewa wa’adi na hudu a kan mulki.

Ko da yake, ya rage mata kason kuri’un da jam’iyyarta ta samu zuwa 33 cikin 100, adadi mafi karanci a shekaru gommai.

Mrs Merkel za ta shiga tattaunawa mai wahala don kafa gwamnatin gambiza a wani yanayin siyasa maras alkibla.

Ana sa ran tattaunawa ce da sai an kai ruwa rana.

Image caption

Sakamakon zaben dai bai yi wa Angela Merkel dadi ba duk da nasarar da ta yi ta samun wa’adin mulki na hudu

Karon farko, bayan samun kasa da kashi 13 cikin 100, jam’iyyar AfD mai tsattsauran ra’ayin kishin kasa za ta karbi kujeru a majalisar Busdestag.

Wakilin BBC a Berlin ya ce jam’iyyar da ke gud’ar samun nasara yanzu, ita ce AfD mai janyo rarrubuwar kai, ta masu ƙin jinin baƙi da addinin musulunci.

“Kasa da shekara biyar bayan kafuwarta, mai yiwuwa a yanzu AfD ta tashi da kujera 100 a Majalisa,” in ji shi.

Haka zalika, sakamakon ya janyo fushi da nuna taraddadi a kasar ta Jamus.

Zanga-zangar nuna adawa da jam’iyyar AfD ta barke a birane da dama ciki har da Berlin, an ma kama adadin mutane da dama.

Jazaman ne sai gwamnatin da Merkel za ta kafa ta samu hadin kan jam’iyyu ƙanana guda biyu bayan ‘yan Social Democrat sun sanar cewa ba za su shiga gamin gambizar ba.

Hakan ya biyo bayan mummunan kayan da suka sha wanda rabonsu da ganin irinsa tun a shekarun 1930.

Rashin tabbas ya sa darajar takardar kudin euro tangal-tangal a kasuwannin Asiya bayan sanar da sakamakon zaben.

America ta hana 'yan Chadi shiga kasarta


Idris Itno Deby, Shugaban kasar ChadiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaba Donald Trump na sanya sabon tarnakin shiga Amurka a kan kasa takwas ciki har da a karon farko Chadi da Koriya Ta Arewa da Venezuela.

Haramcin ya biyo bayan bitar harkokin tsaro da kuma nasarar da umarninsa na ainihi wanda wa’adinsa zai kare ya cim ma.

Shugaba Trump ya ce yana ba da fifiko wajen mayar da Amurka, kasa mai aminci.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Tasirin dokokin dai ya sha bamban daga wannan kasa zuwa waccan, inda suke haramta wa ‘yan Syria da Koriya Ta Arewa shiga Amurka kwata-kwata, amma suka yi tarnaki ga jami’an gwamnatin Venezuela.

A yanzu dai Sudan ba ta cikin jerin kasa shida na akasari musulmai da ke cikin haramcin Trump na farko.

Karo na uku kenan ana sabunta haramcin wanda ke shan mujadala a gaban kotu.

An zargi 'yan Rohingya da kashe 'yan Hindu


RohingyaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Hare-haren da sojojin Myanmar ke kai wa ‘yan ta-da-kayar-bayan Rohingya sun tilasta wa ‘yan kabilar dubbai tserewa

Rundunar sojan Bama ta zargi Musulmi ‘yan ta-da-kayar-baya na Rohingya da kashe mace 20 da namiji takwas har ma da yara, wadanda ta ce ta gano gawawwakinsu a wani makeken kabari.

Sojojin sun ce gawawwakin da suka gano na ‘yan Hindu ne, wadanda dubbansu ke cewa ‘yan ta-da-kayar-bayan sun tilasta musu tserewa daga kauyukansu.

Ba a dai iya tantance sahihancin wannan bayani na rundunar sojan Myanmar ba.

Musulmai ‘yan Rohingya dubu 430 ne suka gudu daga Myanmar zuwa Bangladesh, sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa ‘yan tawayen.

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya fada wa BBC cewa ‘yan Rohingya suna cikin kunci da darura.

Zaben Jamus: Angela Merkel ta lashe wa'adi na hudu


germany electionHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Merkel ta lashe zabe a wa’adi na hudu

Sakamakon binciken yadda mutane suka yi zabe yau a Jamus, ya yi hasashen jam’iyyar shugaba Angela Merkel mai ra’ayin gargajiya, za ta ci gaba da zama mai rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Sai dai sakamakon ya nuna dukkan jam’iyyun, sun samu raguwar magoya baya fiye da a kowanne lokaci.

An yi hasashen jam’iyyar Christian Democratic Union ta Mrs Merkel, da CSU ta Bavaria wacce ra’ayinsu ya zo daya, sun lashe kashi talatin da uku cikin dari na kuri’un da aka kada.

Hasashen ya nuna babbar jam’iyyar hamayya ta ‘yan gurguzu, Social Democrats, ta samu kashi ashirin cikin dari na kuri’un.

Ana gani jam’iyyar da bata son baki, ta masu tsananin ra’ayin gargajiya ce za ta zo ta uku, da kashi goma sha uku cikin dari na kuri’u.

Ana gani jam’iyyar ta lashe wasu kujeru a majalisar dokokin kasar a karo na farko.

Shugaba Angela Merkel ta ce ta so a ce sakamakon da jam’iyyar ta, ta samu, yafi haka kyau, sannan ta ce za ta yi nazari game da damuwar wadanda suka zabi jam’iyyar da bata son baki, AFD.

Ta ce sun yi shekara 12 muna gudanar da shugabanci, kuma hakan ya sa jam’iyyar mu ta sake zama mafi girma. Sai dai za mu yi kokarin samun goyon bayan wadanda suka kada ma AFD kuri’a, musanman yayin da muke son bullo da muhimman manufofi.

Shugabar jam’iyyar AFD, Frauke Petry, ta ce abin da ‘yan kasar ta Jamus suka gani yanzu, wata girgizar kasa ce ta siyasa.

Daya daga cikin manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyar, Alexander Gauland, ya ce sun yi wa Mrs Merkel shiri sosai na kwato abin da ya kira kasar su.

Shugaban jam’iyyar Social Democrats, Martin Schulz, ya amsa cewa sun sha kaye, yana mai cewa wannan rana ce ta bakin ciki.

Ya ce zai ci gaba da yin jagorancin jam’iyyar, tare da kawo mata sauye-sauye, amma dai ba za su shiga gwamnatin hadaka da Mrs Merkel ba.

''Ozil na shirin komawa Man United''


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal za ta karbi bakuncin West Brom a ranar Litinin

Mesut Ozil na shirin kin yadda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, bayan da dan kwallon ke son komawa Manchester United in ji jaridar Daily Mirror.

Sunday Express ta wallafa cewar Liverpool ta bukaci Barcelona da ta daina matsawa Philippe Coutinho a lokacin da ta yi kokarin sayen dan kwallo, inda Liverpool ta ki sayar da shi.

The Sun kuwa cewa ta yi Manchester City ta damu matuka cewar Paris St-Germain za ta bai wa Arsenal makudan kudi domin ta dauki Alexis Sanchez.

An shaidawa Manchester United ta biya fam miliyan 75 idan tana son daukar dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, itya ma Manchester City na son sayen dan kwallon in ji Daily Express.

Everton za ta taya dan wasan Arsenal Olivier Giroud a watan Janairun 2018, har ma ta tanadi fam miliyan 40 in ji Daily Mirror.

Daily Mail kuwa ta wallafa cewar ran Arsene Wenger ya baci matuka da ya sayar da Kieran Gibbs ga West Brom, fiye da barin Alex Oxlade-Chamberlain da ya koma Liverpool.

Shagon Lawwali ya buge na Sanin Kwarkwada


Damben gargajiya

Image caption

A turmin farko Shagon Lawwali ya buge Shagon Sanin Kwarkwada

An fafata a damben gargajiya a wasannin da aka yi a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Ciki har da wasan da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya buge Shagon Sanin Kwarkwada daga Kudu a turmin farko.

Sauran wasannin da suka yi kisa sun hada da Bahagon Aleka daga Kudu da ya buge Shagon Nokiya daga Arewa da wanda Shagon ‘yar Tasa daga Arewa ya yi nasara a kan Shagon Bahagon Fandam daga Kudu.

Sauran wasannin canjaras aka yi:

 • Bahagon Sama’ila daga Kudu da Dogon Dan Ali daga Arewa
 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da na Abata Mai karami daga Kudu
 • Dan Fulanin Dogon Auta daga Kudu da Shagon Durago daga Arewa
 • Aljanin Autan Sikido daga Kudu da Shagon ‘Yar Balala daga Arewa
 • Shagon Dan Sharif daga Kudu da Bahagon Abban daga Arewa
 • Dogon Aleka daga Kudu da Nokiyar Dogon Sani daga Arewa
 • Dan Aminun Langa-Langa daga Arewa da Shagon Jimama daga Kudu
 • Sani Mai Kifi daga Arewa da Shagon Autan Faya daga Kudu
 • Shagon Dan Jamilu daga Arewa da Shagon Aleka daga Kudu

Shin nawa ne albashin Neymar a PSG?


PSGHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

PSG tana mataki na daya a kan teburin gasar Faransa da maki 18

Neymar bai buga wa Paris St-Germain gasar cin kofin Faransa wato Ligue 1 a karawar da ta tashi babu ci da Montpellier a ranar Asabar, sakamakon jinya da yake yi.

Dan wasan ya koma PSG da taka-leda kan fam miliyan 200 daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya a fagen tamaula.

Sai dai ana rade-radin cewar dan wasan na tawagar Brazil yana karbar fam 88,552 a kowacce rana, kimanin fam miliyan 2,718,126 a duk wata.

Mujallar Der Spiegel ce ta fitar da wannan rahoton inda ta kara da cewar Neymay yana karbar fam 3,542 a duk sa a daya kamar yadda Marca ta wallafa.

Wata mujallar Paris match ta ce an girke jami’an tsaro da suke kula da lafiyar Neymar a katafaren gidansa da ke kilomita 14 tsakaninsa da wurin atisayen PSG.

Har yanzu Ronaldo bai ci kwallo a La Liga ba


Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga da maki 11

Cristiano Ronaldo bai fara wasannin cin kofin Spaniyar La Liga da kafar dama, yayin da har yanzu bai ci kwallo ba a gasar.

Ronaldo bai buga wasa hudu da aka fara kakar bana ba, sakamakon dakatar da shi wasa biyar da aka yi kan jan katin da aka yi masa a karawa da Barcelona a Spanish Super Cup.

Dan kwallon ya fara buga wa Madrid La Liga a karawar da Real Betis ta yi nasara da ci daya mai ban haushi a ranar Laraba, inda ya kai hari sau 20, amma bai ci kwallo ba.

A wasan mako na shida a gasar ta La Liga Ronaldo ya buga wa Madrid wasa na biyu, inda ta yi nasarar doke Deportivo Alaves 2-1, Dani Ceballos ne ya ci wa Real kwallayen.

Sai dai kuma abokin hamayyar Ronaldo wato Lionel Messi ya ci kwallo tara a gasar ta La Liga kuma, Barcelona tana ta daya a kan teburi bayan da ta ci wasa shida a jere.

Ronaldo ya ci kwallo uku a kakar bana a European Super Cup da Spanish Super Cup da wanda ya ci Apoel a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Real Madrid za ta karbi bakuncin RCD Espanyol a wasan mako na bakwai a ranar 1 ga watan Oktoba, a kuma ranar ce Las Palmas za ta ziyarci.

Llorente ya tsawaita zamansa a Madrid


Real Madrid FCHakkin mallakar hoto
Real Madrid FC

Image caption

Llorente zai ci gaba da zama a Madrid har karshen kakar 2021

Dan wasan Real Madrid, Marcos Llorente ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Santiago Bernabeu zuwa shekara hudu.

Llorente ya buga wa Real Madrid wasannin tunkarar kakar 2015 inda ya buga wasan sada zumunta da kungiyar ta yi da Manchester City da Internazionale da kuma Valerenga.

Dan kwallon ya fara buga wasa a matsayin kwararren dan kwallo a ranar 17 ga watan Oktoba, ya kuma canji Mateo Kovacic a karawar da Madrid ta ci Levante 3-0 a gida.

A ranar 10 ga watan Agustan 2016, Madrid ta bayar da aron Llorente ga Deportivo Alaves zuwa karshen kakar wasan shekarar.

Dan kwallon ya buga wa ReaL Madrid wasa uku ya kuma lashe UEFA Super Cup na 2016.

An yi jan kati biyar a wasan Fenerbahce da Besiktas


Gasar TurkiyaHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Dan wasan Besiktas, Ricardo Quaresma ne ya fara karbar jan kati a fafatawar

‘Yan wasa biyar alkalin wasa ya kora a karawar hamayya tsakanin Fenerbahce da Besiktas a gasar cin kofin Turkiya da suka fafata a Istanbul a ranar Asabar.

Mai masaukin baki Fenerbahce ce ta fara cin kwallo ta hannun Giuliano sannan Vincent Janssen ya kara ta biyu, sai dai Besiktas ta zare kwallo daya ta hannun Ryan Babel.

Alkalin wasa ya fara korar dan kwallon Besiktas, Ricardo Quaresma sakamakon katin gargadi biyu da ya yi masa, sannan ya kaori Luis Neto daga karawar.

Bayan da aka ci gaba da wasan ne aka bai wa dan kwallon Besiktas Atiba Hutchinson jan kati.

Daf da za a tashi daga fafatawar alkalin wasa ya kori Ismail Koybasi na Fenerbahce daga wasan sakamakon keta da ya yi, sannan ya kuma kori Oguzhan Ozyakup bisa katin gargadi guda biyu da ya karba.

United ta bukaci faifan bidiyo kan cin zarafin Lukaku


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lukaku ne ya ci Southampton a gasar Premier da suka yi a ranar Asabar

Manchester United ta nemi da a ba ta faifan bidiyo da zai taimaka mata ta zakulo ‘yan kallon da suka ci zarafin Romelu Lukaku a karawar da kungiyar ta yi da Southampton a ranar Asabar.

Lukaku mai shekara 24, ya umarci ‘yan kallon tamaula da su daina cin zarafinsa a ranar Juma’a.

Sai dai kuma an rera wakar cin zarafin dan wasan a karawar da United ta ci Soutahmpton daya mai ban haushi a gasar Premier a filin wasa na St Mary.

A wata sanarwa da United ta fitar ta ce ”Kungiyar da dan wasan sun fayyace karara da a kawo karshen rera wakar cin zarafin da ake yi.

”United tana tattaunawa da jami’an tsaro ta kuma bukaci da a ba ta faifan bidiyon wasan da ta kara da Southampton.”

Magoya bayan United na yin kalamai kan girman mazakutar dan wasan gaban kasar Belgium.

Shugaba Buhari zai koma gida daga London


BuhariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jawabinsa ya burge jama’a

Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar ranar Lahadi bayan kammala abin da ya kai shi London.

Shugaban ya tafi London ne ranar Alhamis bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Amurka.

Daya daga cikin jami’an da suka raka shugaban Amurka ya tabbatarwar BBC cewa tsarin tafiye-tafiyen mai gidan nasa ya nuna cewa zai koma kasar ne ranar ta Lahadi.

Kafin tafiyar tasa London, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.

Da ma dai fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai je London bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai ta ce Shugaban “Zai je birnin London a kan hanyarsa ta komawa gida”.

Sai dai Mr Adesina bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.

Kuma da BBC ta tuntube shi a kan batun, ya ce shugaban kasar zai ya da zango ne kawai a London, yana mai cewa ba zai ce komai ba bayan hakan.

A watan jiya ne shugaban na Najeriya ya koma kasar daga London bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba.

A lokacin da yake jinya, ‘yan kasar da dama sun yi masa addu’ar samun sauki.

Amma wasu ‘yan Najeriyar sun yi ta zanga-zanga inda suka yi kira a gare shi ya koma Najeriya ko kuma ya sauka daga mulki.

Kwanaki kadan bayan zanga-zangar da suka yi a korar gidan da shugaban ya yi jinya ne, Muhammadu Buhari ya koma kasar.

Masu gangamin sun shaida wa BBC cewa matsin lambar da suka yi ne ya tilasta wa Shugaba Buhari komawa kasar.

A lokacin da ya koma Najeriya Shugaba Buhari, cikin raha, ya yi kira ga masu fafutikar su koma Najeriya kamar yadda ya koma, yana mai cewa yana fatan ba rashin kudi ne ya hana su komawa gida ba.

Rikicin Trump da Korea ta Arewa 'ya kai intaha'


Shugaban Amurka Donald Trump ya sabunta gargadinsa ga Koriya ta Arewa bayan ministan wajen Korea ya yi kalamai masu zafi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Asabar.

Ri Yong-ho ya bayyana Mr Trump a matsayin mutum “mai tabin hankali da ke yunkurin halaka” jama’a.

Shugaban na Amurka ya yi raddi ga Mr Ri da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da cewa idan suka ci gaba da barazanarsu, nan gaba kadan “za a yi ba su”.

Wannan sabuwar takaddama ta taso ne bayan jiragen Amurka masu luguden bama-bama sun yi shawagi daf da gabar tekun da ke gabashin Koriya ta Arewa, karon farko cikin karni na 21.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ta dauki matakin ne domin ta nuna irin karfin sojin da take da shi na iya murkushe duk wani mai yi mata barazana.

Hakan na faruwa ne bayan Koriya ta Arewa ta harba makamanta masu linzami sau da dama a ‘yan watannin nan.

Duk da wannan tayar da jijiyar wuya, masu sharhi na ganin da wuya kasashen biyu su gwabza yaki kai tsaye.

Hakkin mallakar hoto
US Pacific Command

Image caption

An dauki matakin ne domin nuna karfin sojin da Amurka ke da shi

Buhari na shirin Musulintar da Nigeria — CAN


Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari na yunkurin Musulintar da kasar.

Sakataren kungiyar Rabaran Musa Asake ne ya shaida wa BBC hakan sakamakon kaddamar da takardun lamuni na Musulinci da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi a makon jiya.

Sai dai ministan harkokin wasanni Barista Solomon Dalung ya gaya wa BBC gwamnatin tsohon shugaban kasar Goodlcuk Jonathan ce ta faro shirin, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta kammala shi ne kawai.

“Me ya sa kungiyar Kiristoci ba ta ce Shugaba Jonathan na yunkurin Musulintar da Najeriya a wancan lokaci sai yanzu? Ina ganin ba su fahimci shirin ba ko kuma suna so su mayar da shi siyasa”, in ji Barista Solomon Dalung.

Sai dai Rabaran Musa Asake ya ce tun a lokacin gwamnatin Shugaba Jonathan suke yin wannan korafi, yana mai cewa “sau biyu ina gudanar da taron manema labarai a kan wannan batu a lokacin gwamnatin Shugaba Jonathan amma ba a saurare mu ba”.

Shi dai tsarin sayar da takardun lamuni na Musulmi, wanda ake kira SUKUK, ya karbu a kasashen da ba na Musulmi ba irinsu Burtaniya, Amurka, China da kuma Rasha.

Bikin kafa Saudiyya ya kawo gwamutsa mata da maza


Saudi women in stadium for first timeHakkin mallakar hoto
Reuters

A karon farko an ba mata damar shiga wani filin wasanni don bikin samun ‘yancin kai a Saudiyya.

Filin wasa na Sarki Fahad a Riyadh babban birnin kasar, ya makare da daruruwan matan da suka yo dango don cin wannan gajiya.

Saudiyya dai na shagulgulan cika shekara 87 da kafuwarta a wannan mako.

Akasari dai filin wasan wanda ya saba karbar bakuncin manyan karawar kwallon kafa, maza ne zalla ke halartarsa bisa tsarin hana gwamutsuwa tsakanin jinsuna a Saudiyya.

Hakkin mallakar hoto
Al Arabiya

An ga mata a wasu lokuta cakude da maza a kan kujeru suna karkada tutocin Saudiyya albarkacin murnar ranar kafa Saudiyya.

Rahotanni sun ce bukukuwan wani yunkuri ne na gwamnatin Sarki Salman don yaukaka alfahari da kasa da kuma inganta matsayin rayuwar Sa’udi.

Yadda fina-finan talabijin ke sace hankalin mata


 • Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da Fatima Zarah Umar ta yi game da wannan batu, idan kuka latsa alamar lasifika da ke hoton sama.

Kallon fina-finan siris na Indiya ya zamar wa Murjantu jiki. Tana shafe tsawon rana wajen kallon fina-finan a tashoshin tauraron dan Adam (Satellite).

Karfe biyun rana take tashi ta fara kallon, idan ta zauna ta fara kallon kuwa ba ta tashi sai karfe takwas na dare.

Ko motsawa ba ta son yi bare ta dauke kanta daga kan talabijin din, saboda ba ta son wani abu ya wuce ta.

Ta yi wa kallon matsanancin sabo, inda ba ta jin dadi kwata-kwata kuma ba ta iya komai idan ba ta yi wannan kallon ba,domin kuwa kallon ya zamar mata tamkar magani.

A wannan makon muna tare da ma’abota kallon irin wadannan fina-finai, inda muka tambayesu ko akwai wani abu da suke karuwa da shi a kallon.

Za mu iya cewa ba dukkanin fina-finan ba ne ba su da kyau ba, saboda daya daga cikin bakuwarmu ta ce kallon fina-finan na taimaka mata a zamantakewar auranta.

Ta ce, kallon yadda matan indiya suke yi wa mazajensu na kara mata kaimi wajen kyautatawa mijinta.

Daya bakuwarmu kuwa cewa ta yi kallon ya mayar da ita ‘yar kwalisa ta fannin kwalliya da kuma gayu.

Baya da abin da yake faruwa a gida mene ne tasirin da mutane suke da shi a kan sha’awarsu ta nishadantuwa da fina-finan kasashen waje?

Da farko dai, ba abu ne mai kyau ba ga masana’antar shirya fina-finanmu na gida, inda mutananmu da dama suka fi nishadantuwa da kallon fina-finan kasashe.

Har ila yau kuma a hankali muna saba wa da kuma daraja al’adun da ba namu ba, inda muka yi sakaci da al’adunmu da muka gada tun iyaye da kakanni.

Duk lokacin da na tuna yadda matasanmu suke bayar da lokacinsu wajen irin wadannan kallace-kallace ina damuwa.

Abin da ya sa nake damuwa kuwa saboda yanda suka mayar da hankali a kan tsarin soyayya ta zamani, wacce ta ke dorasu kan mummunar hanya. Mafi yawancin yaran yanzu suna tasowa ne da dabi’u irin na al’adun Indiya da kuma Koriya.

Wannan ba karamin abin takaici ba ne.

Idan ka ga yadda matanmu suke koyan makirci da mugun abu a irin wananna finafinai ina matukar damuwa.

Dalili kuwa saboda yadda suke kauracewa al’adunmu na iyaye da kakanni da kuma kyautatawa, da taimakekeniya a tsakanin jama’a da kuma ganin mutuncin juna.

Ba Murjanatu ce kadai ke bata lokacinta a kallon talabijin ba, ba na jin tana damuwa.

Abin al’ajabin shi ne ba ita kadai ba ce, akwai irinta da yawa a arewacin Najeriya, wasu ma abun nasu ya fi ta’azzara.

Fina-finan za su iya zama suna nishadantarwa, amma abin tambayar a nan shi ne sun dace da a’ummarmu?

Me kyautar da Saudiyya ta yi wa Trump ke nufi?


President Donald Trump receives the Order of Abdulaziz al-Saud medal from Saudi Arabia's King Salman bin Abdulaziz al-Saud at the Saudi Royal Court in Riyadh.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Abdulaziz al-Saud na saka wa Trump kyautar sarka

A lokacin da Winston Churchill ya kai wa Sarki Abdul Aziz ibn Saud ziyara a watan Fabrairun 1945, ba jimawa ya gano turaren da ya kawo na dala 134 bai dace da alkyabbar ba, da takobi ,da wuka da kuma zobunan zinare da ya karba a komawarsa.

Duk da guguwar Yakin Duniya na Biyu, Firaiministan Birtaniya ya koma gida kuma ba tare da ba ta lokaci ba ya umarci daya daga cikin kamfanin kera motoci su kera mota a kai wa sarkin bayan wata bakwai.

A yau shugabannin duniya ba sa iya yin kyautar jirage ko motoci masu tsada, amma wasu kasashe na baya-bayan nan sun ba wa shugaba Donald Trump kyautar abubuwa 83 a lokacin da ya kai ziyara kasar Saudiyya, wanda ake daukarta a matsayin fariya a daular Larabawa.

Wacce kyauta Trump ya karba?

A lokacin da Shugaba Trump ya kai ziyara kasashen waje a karon farko, ya halarcin taron kasashen Larabawa da aka yi a babban birnin Saudiyya Riyadh, inda Sarki Salman ya ba shi manyan kyaututtuka da suka hada da takobi, da wukake, da gwala-gwalai, da gomman harami, da sauran tufafin Larabawa na gargajiya, da takalman fata da kuma turare.

Sai dai kuma kyaututtukan ba wasu na alfarma ba ne, in ji Ali Shihabi, daraktan gidauniyar Larabawa.

Mista Shihabi ya ce, “A shekarun baya gwamnatin kasashen Larabawa na bayar da kyautar fariya, inda suke bayar da agoguna masu tsada, da sarkoki da makamantansu.

Yanzu kuwa suna bayar da kyautukan ne na kayayyakin gargajiya, in ji shi.

Ellen Wald, wani dan Amurka kwararre a gabas ta tsakiya kuma marubuci, ya ce, a zahiri kyaututtukan na gargajiya ne, kuma ya nuna irin tafiyar da kuma mutanen da suka shiga tawagar rakiyar Trump zuwa Riyadh.

Mambobin wakilan Amurka da suka ziyarci Saudiyya a shekarar 2008, sun karbi irin wadannan kyaututtuka da suka hada da wukake, da sarkoki, da kuma rigunan sarauta, in ji ta.

Ko zai iya adana su?

Dokokin kasar Amurka ta haramta wa ma’aikatan gwamnati karbar duk wata kyauta daga gwamnatin wata kasar da ta kai kimar abin da ya fi dala 390.

An samo wannan dadaddiyar dokar ne tun shekarar 1966, wacce ta haramta karbar kyautar fiye da “abin da ya wuce kima”, don hana gwamnati hangen karbar wani abu daga diflomasiyyar Amurka da kyautar dawakai, da motocin alfarma wata kila ma kirar Rolls-Royc ko biyu.

A shekarar 1978, dokar ta bayyana cewa, mafi karancin kyautar dala 100, sakamakon hauhawan farashi da ake samu ake karawa duk bayan shekara uku.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An haramta wa ma’aikatan gwamnatin Amurka karbar kyautar abin da kimarsa ya wuce Dala 390 daga kasashen ketare

Kyautuka na baya da aka ba wa shugabannin Amurka da sauran shugabannin diflomasiyya ana ajiye su ne a gidan adana kayan tarihi, ko a dakin karatu na fadar shugaban kasa, ko kuma a yi gwanjon su.

Har’ila yau ana ba wa jami’an gwamnati zabin su sayi kyautar da suka karbo a kan farashin kasuwa.

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Clinton ta yi amfani da irin wannan zabin a shekarar 2012, a lokacin da ta sayi wata sarka da jagorar ‘yan adawa kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ta ba ta. Inda aka yi wa sarkar kudin da ya kai dala 970.

Ko wannan abu ne da aka saba gani?

Ziyarar shugabannin kasashe suka kawo musayar ra’ayi, wasu lokutan kuma a akan kyautukan ne.

Daraktan harkokin kasashen Larabawa na ma’aikatar Gabas ta Tsakiya, Gerald Feierstein ya ce, kyautar da ake bayar wa ba bakon abu ba ne a daular Larabawa.

Ya kara da cewa, ya tuna kyautar agogon da gwamnatin Bahrain ta ba shi, lokacin da suka kai ziyara yankin Gabas ta Tsakiya a shekarar 1990, a lokacin yana mataimakin darakta a ofishin harkokin yankin Larabawa da ke shiyyar kasar.

“Kamar irin wani abu ne da ba za a iya ba ni ba, kawai sun bayar da wadannan agogunan ne ga dukkan mambobin wakilan,” in ji shi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta taba bukatar gwamnatoci kasashen ketare da su daina bai wa Shugaba Bill Clinton kyautar sarewa

A lokacin da zai mika agogon mai tsada ga hukumar kula da harkokin waje, wacce take aikin adana kyautar diflomasiyya, ya shaida musu cewa, akwai “Dakin da yake cike da agoguna daga Bahrain”.

Mista Feierstein ya tuna lokacin da ma’aikatar harkokin waje ta hana gwamnatin wata kasa ba wa shugaba Ronald Reagan kyautar dawakai.

A shekarar 2015 ne, Barack Obama ya karbi wasu kayayyaki da suka hada da zanen hotunan wasu maza da suke kwallon kwando daga Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma kwanon zinare na dala 110,000 daga Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da kuma fiyano na kida daga Sarki Salman.

Mista Obama ya yi matukar mamaki a lokacin da ya ba wa Firai ministan Birtaniya Gordon Brown wani akwati mai dauke da faifain bidiyon fina-finan Amurka, wanda mutane da dama suke kallonsa a matsayin cin mutunci ga shugaban Birtaniya.

Ko jerin kyautar da aka yi wa Trump na nufin wani abu?

Misis Wald ta ce, “Trump ya soki abokiyar hamayyarsa ta jam’iyyar Democrat Hillary Clinton , a kan karbar kyauta daga Saudiyya wacce kuma ta jawo surutai da karin gishiri game da gwamnatin, tana yiyuwa kyaututtukan da ya karba ba za ta karfafa alakarshi da kasar ba”.

Ta yi bayanin cewa, “hakan ya nuna wata al’adar yankin ne fiye da kowacce alamar diflomasiyya ko wata dangantaka.”

Ta kara da cewa, bakon abu shi ne yadda Trump ya kai ziyara kasar ta wasu kwanaki, saboda an saba ganin haka ne kafin fara amfani da jirgin sama.

Jakadan Amurka na farko a Saudiyya , J Rives Childs, ya kan yi tafiyar kwana uku idan zai je kasar Saudiyya, lokacin da zai karbi wasu kayayyaki da suka hada da takobin zinare, da agogo da kuma wukar zinare.

Misis Wald ya kara da cewa, a wani taro da aka yi ya ki amincewa da damar yin kwarkwara a Riyadh.

“Aikin gwamnati ne mara wa masana’antun kasar baya ta hanyar yi wa shugaban Amurka kyauta da wasu kayayyaki,” in ji Mista Shihabi.

“Bayar da kyautuka na nuna karramawa da kuma karbar baki,” in ji shi.

Yakin cacar bakin Hungary kan shan-inna


Kwayar cuta ce dai ke haifar da shan-inna, kuma yara 'yan kasa da shekara 5 take shafaHakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Kwayar cuta ce dai ke haifar da shan-inna, kuma yara ‘yan kasa da shekara 5 take shafa

Daga Penny Bailey

15 ga Afirulun 2014

Lokacin zafi a shekarar 1954, birnin Kisvarda na kasar Hungary ya kasance babu kowa. Babu mai tuka abin hawa in dai ba ‘yan sandan asiri ba ne ko wadanda jam’iyya ta yi wa alfarma.

A cikin gida kuwa Iren da Janos Vargha sun zauna suna kallon idon dansu dan shekara biyu yana barci ga zazzabi ya kama shi. Alamar kamuwa da cutar da ta bayyana ita ce, kamar yadda aka fada musu, idan kwayar idon Gyorgy ta rika wulkitawa da sauri.

Ba a yi aune da cutar shan-inna ba. Domin ba a ganin muninta fiye da ko wacce da ke far wa kananan yara, inda akai-akai ta kan “juyo” da kai farmaki mai muni da ke kassara kwayoyin halittar jijiyoyin yaro, ya bar jikinsa a shanye tsawon rayuwa.

Idan ta lalata jijiyoyin da ke tarairayar huhu za su iya daskarewa, ta yadda Gyorgy ka iya mutuwa ko ya shafe daukacin rayuwarsa a huhun karfe da ke yi masa numfashi.

Sa’o’in da suka shude babu daya daga alamun da suka nuna cutar shan-inna ta kama shi, amma da safe bayan da Iren ta dora kan tebur don sanya masa tufafi, sai kafafunsa suka murde.

“A da ina tsayuwa cikin sauki,” in ji shi. “Yanzu zan iya tankwara kafafuna, amma ba zan iya mike su ba. A gareni wannan abin mamaki ne ganin yadda kafafuna ke yin wani abu daban. Sai dai Innata ta firgita.”

An yi hanzarin kai Gyorgy asibitin da ke da nisan kilomita 100 (mil 60) zuwa Debreen. Daga nan aka yi kara-kainar neman sinadarin garkuwar jiki na “gamma globulin.”

Sinadarin kariyar jikin shi kadai ne a lokacin da aka sani a matsayin maganin da ke karya lagon kwayar cutar shan-inna (poliovirus) da ke cikin jini, inda yake shawo kanta daga kai wa ga jijiyoyi.

Sai dai sinadarin an’ gamma globulin’ ya yi karanci. Iren da Janos sun yi ta kai-kawo kan babur daga wannan gari zuwa wancan, daga kauye zuwa kauye, da bin masu harhada magunguna cikin takaici suka karke da gyada kawunsa.

Daga bisani a yammaci, suna zaune a gidansu cikin tunanin yadda dansu zai yi fama da kansa shi kadai kan gado mai nisa (da gidansu), ana kwankwasa taga.

Bayan labulen suka hango jami’an ‘yan sandan asiri biyu – suna jira a kofa, sai wata babbar bakar mota kirar bakar ta tsaya gefensu.

A shekarun 1950 kasar Hungry karkashin Kwamunisanci, idan bakar mota ta tsaya a kofar gidanka da daddare, abin fahimta kawai shi ne: jami’an sirri (avos) sun zo tafiya da kai.

Da bude kofar Janos da Iren sai tsoro ya gushe hankali ya kwanta, sai suka rude. Mutanen suka yi musu bayani cewa sun tuko mota tsawon sa’o’i uku da rabi daga Budapest saboda sun samu labarin dan iyalan Varghas ya kamu da shan-inna.

Suka ba su hakuri tare da cewa sun kawo musu sinadarin ‘gamma globulin.’

Shekara 60 da suka wuce ‘yar Gyorgy masaniyar tarihi Dokta Dora Vargha ta ba ni labarin mahaifinta sa’adda muke shan gahawa a Bambi Presszo da ke birnin Buda a gefen Danube. Danta dan shekara uku ne, wato ya dara shekarun Gyorgy lokacin day a kamu da cutar shan-inna.

An haifi danta daidai lokacin da ta fara rubuta kundin bincikenta kan tarihin yakin cacar bakin shan-inna a Hungary.

“Al’amarin ya hargitse komai ya yi daban. Ina jin hadurra da tsoro. Sai na kai shi aka yi masa rigakafin shan-inna karon farko bayan kammala bincikena. Wanan shi ne lokacin jajircewa gareni.

Abin takaicin shi ne, bayan da ‘yan sandan asiri (avos) suka kawo magani tuni an makara domin Gyorgy na bukatar a yi masa aiki a kafufunsa sau shida da tarairayar gabobi.

A Hungary karkashin kwamunisanci, wuraren shan gahawa da wajen ninkaya matattarar masana da ‘yan tawaye ne, wadanda ke musayar basira suna bankar hayakin taba ko tiririn ruwan zafi.

Wannan al’ada an farata ne farkon karni na 19, lokacin da masu matsakaicin samu a Budapest suka gina gadoji masu kyau da wurin cin kayan makwalshe a nahiyar na farko, da wajen kiran tarho na farko a duniya, kuma titin Andrassy na da girma baibaye da tsirrai ta yarda ake kwatanta shi da Champs-Elysees da ke Paris.

Hakkin mallakar hoto
(Thimnkstock).

Image caption

Lokacin yakin cacar bakin annobar shan-inna da ta far wa Hungaru tsakanin shekarun 1952 da 1954

Marubuta da masu fasaha da masu kirkire-kirkire dam asana Falsafa kan taru a wuraren shan gahawa na birnin da wuraren wanka don tattaunawa kan muhimman al’amura da suka shafi makoma.

Wajen rabin karni daga baya, kyawawan shafen zayyana gine-ginen Budapest da tagogin gilashi da gadoji duk ‘yan Nazi (mabiyan Hitler) da suka janye daga filin daga sun tarwatsa su.

Kan duniya ya rabu biyu tsakanin karfafan kasashe bayan kammala yaki: Amurka mai bin tafarkin dimokuradiyya da Tarayyar Sobiyat mai bin kwamunisanci, wadda karkashin barazanar tarwatsa duniya da makamin nukiliya suke dabaibaye da akidar yakin cacar baki.

Ko wanne bangare na nuni da cewa shi ne kan tafarkin da ya dace duniya ta bi don gina sabuwar rayuwar, ta hanyar nuna karfin kere-kere da bunkasar tattalin arziki da farin ciki da lafiyar al’umma.

A Turai, rabuwar kan karara take kan akidar mahanga. Nahiyar ta rabu, inda rabi ke kankane da dimbin rundunar soja, a yankin da ya keta iyakar Yammacin Hungary.

Babu wanda zai iya tsallaka katangar karfe ba tare da izinin manyan jami’an gwamnati ba, kuma abin da ke wakana a ko wanne bangare, wanda ke daya bangaren ba lallai ne ya sani ba..

Sobiyat ta kafa Gwamnatin Kwamunisan a Hungary, kuma a gidajen shan gahawa akwai gwarzon masani mai fikira: dan kwadago ma’aikaci.

Mahangar alkiblar kasar da mafi yawan masu ra’ayin kwamunisanci ‘yan kasar suka amince da shi, ita ce gwamnati mai mulki a tsakiya da jihohi marasa fifikon daraja, wadanda ake raba albarkatunsu daidai-wa-daida ga kowa-da-kowa.

Zuwa shekarar 1950, daukacin ma’adanai da masana’antu da bankuna duk sun zama na kasar kuma daukacin kadarorin gidaje da filaye an raba wa talaka.

“Ba za ka iya mallaka waurin adana kaya na kashin kanka ko wurin kasuwanci. Sai dai mafi yawan mutane sun rike gidajensu, idan suna da kimar fadin gaske,” in ji Dora.

“Manyan gidaje an raba su kashi-kashi, inda aka bai wa iyalai gida-gida. Har yanzu akwai tasirin al’amarin a birnin Budapest: gida guda na da dakin girki, kuma gidan da ke makwaftaka da shi yana da babban makewayin wanka.

Haduwar iyalan Varghas da jami’an asiri na avos a shekarar 1954 al’amari ne mnai rikitarwa. Matsayin Janos na likitan dabbobin gundumar da ke kula da gonaki da kauyukan da ke kewaye da Kisvarda, ya kasance a tsohon rukunin masu matsakaicin samu, masu hannu da shuni da aka tsana.

Ko wanne dalili ya sanya ‘yan sandan asiri (avos) biyu suka yi tukin kusan sa’a’o’i hudu a tsakar dare don taimakon yaron da ba su taba gani ba? Bayan shekaru wadanan iyalai suka gano.

“Kakana ya kasance likitan dabbobin daya daga ciki masu harhada magunguna da ya tambaya sinadarin gamma globulin,” a cewar Dora.

“Kuma wannan mai hada magani yanba da suruki jami’in asiri na avo da ke Budapest a lokacin. Manufar tsarin kwamunisanci ita ce komai a raba shi daidai, amma gaskiuar lamari it ace samun kayan da suka yi karanci ya danganta ga wanda ka sani.”

'Yar Nigeria ta shiga jerin mawakan da ke tashe a Amurka


Simi

Image caption

Kundin wakokin Simi Ogunleye na farko ne ya janyo mata wannan daukaka zuwa jerin mawakan duniya

Wata mawakiya ‘yar Najeriya, Simi Ogunleye ta kafa tarihi, bayan ta shiga jerin mutanen da wakokinsu ke tashe a jadawalin wakokin da suka yi fice na Duniya a Amurka.

Da take zantawa da Sashen BBC Pidgin, Simi ta ce: “da ma na san za a rina, hakan kuma na nufin cewa kasuwata za ta bude kenan.

Ba zan taba sauya salon kidana ba, don kuwa shi ne mafarin duk wata daukaka da na samu yanzu.”

Simi Ogunleye dai na gauraya Ingilishi da Yarbanci ne a cikin wakar tata mai taken ‘Belle Sweet’.

Ta kuma yaba wa masu sha’awar wakokinta, don kuwa a cewarta “su ne suka kai ni duk matsayin da na samu kaina yau a cikinsa, su ne suka rika yayata kundin wakokinta, ba zan taba ba su kunya ba.”

Simi na daya daga cikin fasihan mawakan Afirka da suka samu shiga sahun mawakan duniya, inda wakarta ta samu gurbi na biyar a fitattun wakokin da suke tashe cikin jerin Billboard Charts.

Shi ne kudin wakokinta na farko da ta sanya wa lakabin “Simisola”.

Simisola ta fara waka ne da wakokin bege a coci, kafin ta shiga wasu wakokin a shekara ta 2014, lokacin da ta fitar da wakarta ta farko mai taken “Tiff and E no go funny.”

Bayan wake-wake, Simi tana kuma harkar kade-kade.

Hakkin mallakar hoto
Billboard Chart

Image caption

Mujallar Billboard a Amurka ce take fitar da jadawalin mawakan da ke tashe a duniya na Billboard mako-mako

Ana la’akari da adadin kwafen kundin waka nawa aka sayar cikin mako a fadin duniya, don sanya waka a jadawalin wakokin da suke tashe na Billboard Chart.

Jiragen yakin Amurka sun yi shawagi a kusa da Koriya ta Arewa


AmericaHakkin mallakar hoto
US PACIFIC COMMAND

Image caption

Irin jiragen yakin Amurka da suka yi shawagi a kusa da Koriya ta Arewa

Rundunar sojin saman Amurka ta tura wasu jiragen yakinta masu lugudan bama-bamai yin shawagi a sararin samaniyar tekun dake gabashin Koriya ta Arewa.

Ma’aikatar tsaro Pentagon ta ce wannan ne karon farko a karni na ashirin da daya, da jiragen yakin Amurkan suka yi nisan zango kusa da Koriya ta Arewar.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin saman ta Amurka, ya ce an tura jiragen ne domin a nuna da gaske Amurka take ta yi maganin rashin kan gadon Koriya ta Arewa.

Jim kadan bayan jiragen sun yi shawagi, ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa, a jawabin da yayi wa majalisar dinkin duniya, ya kare matakin kasar shi na kera makaman nukiliya.

Najeriya: Cutar kyanda ta barke a jihar Kebbi


measlesHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An yi wa wani yaro allurar rigakafi a arewacin Najeriya

Rahotanni daga Kebbi dake arewacin Najeriya sun ce fiye da mutane dari shida sun kamu da cutar kyanda ko bakon dauro a jihar.

Jami’in hukumar kula da lafiya a matakin farko a jihar, Mannir Jega wanda ya tabbatar da hakan ga ‘yan jarida ya ta’allaka lamarin a kan bijirewar da jama’a ke yi na zuwa rigakafi.

Ya ce jihar ba ta samu nasarar aikin riakafin da aka gudanar a 2016 ba sakamakon kin fitowa da jama’a suka yi.

Kwamishinan lafiya na Jihar Usman Kambaza ya ce za a tura ayarorin jami’an lafiya fiye da dubu daya domin gudanar da rigakafi na dakile yaduwar cutar zuwa wasu sassan jihar.

Ya ce gwamnati ta na shirin gudanar da wani gangamin yaki da cutar ta kyanda tare da taimakon hukumar kula da lafiya a matakin farko ta gwamnatin tarayya domin yaki da cutar.

Kotu ta ba Ghana gaskiya a shari'a da Ivory Coast


GhanaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ma’aikatar hakkan mai ta Ghana

Wata kotun kasa da kasa ta yanke hukuncin cewa Ghana ba ta keta ‘yan cin Ivory Coast ba, sakamakon aikin hakkan mai da take gudanar wa a tekun da a ke takaddama akai.

Shekaru uku kenan da Ghana ta kai batun ga kotun kasa da kasa dake shari’a kan takaddama a teku, bayan Ivory Coast ta zarge ta hakkan mai a cikin ruwa da yake mallakinta.

Ghana ta ce ta shafe shekara da shekaru tana aiki a yankin, kafin Ivory Coast ta yi ikirarin mallakin shi.

Duk da cewa Ghana ta na da dumbun arzikin mai a cikin teku, faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ta sa kudaden shigar kasar ya ragu sosai.

Ba zan fito a fim din da ya ci karo da Musulinci ba — Hadiza Gabon


Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta ce ba za ta fito a fim din da ya ci karo da addininta na Musulinci da kuma al’adunta ba.

Hakkin mallakar hoto
InSTAGRAM/HADIZA GABON

Image caption

Hadiza Gabon ta ce ta fito ne a matsayin ‘yar arewa

Ta bayyana haka ne sakamakon soma fitowa da ta yi a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.

Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa “Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.

“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim din.

“Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al’adata ba”.

Hakkin mallakar hoto
Instagram/Hadiza Gabon

Image caption

Hadiza Gabon ta yi suna sosai a Kannywood

A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a wani gajeren fim na turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.

Hadiza Gabon ta kara da cewa babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadin soma fitowa a fina-finan Nollywood”.

Hotunan yadda 'yan Afirka ke wahalar samun abinci


Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A kudu da hamadar Saharar Afrika, rikici da sauyin yanayi sun yi tasiri a kan kiyaye abinci. Al’ummomi a Nijar da Burundi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka suna fuskantar mummunan hadari na yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Chris de Bode ya ziyarci wuraren, ya tafi da da niyyar daukar hotuna wadanda zai iya amfani da su a wani shirin talabijin mai nuna hotuna.

Tare da binciko yadda tasirin siyasa da muhalli zai iya rage kwarin gwiwar mutane su noma abincin da za su ci, de Bode ya kuma nuna yadda ayyukan jin kai za su taimaka.

A young man holds up his tools.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

Daniel Nsabiyaremye dan shekara 28, ya koyi aikin kafinta ne amma sai dai ba shi da kayan aiki. Bayan jerin basussukan da ya karba don sayen kayan aiki kamar su guduma da kusosi da sauransu, a karshe ya samu damar fadada sana’arsa da a yanzu take samun tagomashi.

Ya ce: ”Na sayi kayan ne daya bayan daya, daga kudaden da na ranto wadanda ake turo min ta banki.”

”Yanzu, ina da hanyar wadata iyalina da abinci. Kafin wannan shirin, sau daya muke cin abinci, kuma abincin ba mai inganci ba ne. Amma yanzu sau biyu muke cin abinci. Hakan ya yi tasiri matuka wajen iganta lkafiyata da ta iyalina.”

Two men stand in front of a backdrop.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A group sit in front of a backdrop.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

Joseph da Nyambaronziza mambobi ne a al’ummar Batwa da ake tauye wa hakki. An san mutanen al’ummar Batwa da gajarta.

Dukkansu suna fadi-tashin ciyar da iyalansu, wadanda suke rayuwa a gidajen da suka zama kamar kufai a yankin Kabere da ke cikin kungurmin da ji kusa da duwatsu a kasar Uganda.

Suna samun kudi daga kananan ayyukan lebaranci da aikin gona ko kuma neman daham a cikin wani rafi da ke kusa.

A woman picks plants.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A bowl of beansHakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A family stand next to their house.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

Denise Nyamwiza ‘yar shekara 20, tana kula da kannanta ne bayan da iyayensu suka mutu shekara biyu da suka wuce sakamakon cutar maleriya.

Ta kan nemi aiki a wasu lokutan kuma tana sayar da fiya da wasu kayan lambun da take nomawa a ‘yar karamar gonarta.

Solange Wanibilo na tsaye ita da iyalanta a kofar gidansu a kauyen Bomandoro, da ke Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka. Dan autan Solange, Arthur da jikanta Frank suna fama da tamowa.

A family stand in front of their house.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A small boy's arm is measured.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A woman stands with her four children.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

Golden Marlenue tana tsaye da ya’yanta guda hudu.

‘Yan kananan yaran sune Naomi ‘yar shekara biyu da kuma Athanase ‘yar shekara daya wadanda duk suke fama da tamowa. Amma mako uku da suka wuce aka sake bude asibitin sha-ka-tafi na Ndanga, wanda a baya aka rufe shi, kuma yanzu yara suna iya samun kulawa da magungunan da su ke bukata.

Light streams into a woman's house.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A plant pushes through the soil.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A group sit in a field.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A Boganando da ke Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka, Josephine Zawele tana ta tsaye a wata gona ta wata makaranta tare da sauran mambobin al’ummar.

Wannan gonar manoma suna amfani da ita ne don koyan sababbin hanyoyin aikin gona da za su iya amfani da su a gonarsu.

Hadijatou Cheihou, ‘yar shekara 15, na zaune ne a kauyen Gao Moussa da ke Jamhuriyyar Nijar, wanda suka yi suna sosai a samar da man gyada. Hadijatou ta na daya daga cikin mambobin kungiyar mata 30 da aka ba su horo don samar da man gyada.

Yanzu mata fiye da 90 a kauyen suna samun horo. Mutane na yin tafiyar kilomita fiye da 45 don su sayi man.

A woman stands in her village.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

Legs of a family.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A woman smiles out from a group.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A kauyen Kosama da ke Jamhuriyyar Nijar, Hassana Abdourahamane na murmushi tare da wasu mambobin al’ummar manoma.

Suna noma kayan lambu a gonar da aka ba su aro, kamar su albasa da tumatir da dankali da karas da kabeji da sauran su. Wata kugiya mai suna Concern, ita ta dauki nauyin ba su horo da samar musu da iri, amma yanzu matan sun fara dogaro da kansu saboda sun sayar da amfanin gonar da suka girbe.

A bundle of vegetables.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A farmer holds a child.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A farmer stands amongst his animals.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

A da, Salifou Ahment, manomi mai shekara 70, na fadi-tashin ciyar da dabbobin da ya ke kiwatawa a lokacin rani.

Yanzu maimakon yin doguwar tafiya don sayen abinci, akwai wata bankin sayar da abincin dabbobi a kusa da gidansa. Bankin, wanda al’umma ke tafiyar da shi, na ajiye abincin dabbobi a ko wanne lokaci na shekara, kuma yana sayar wa da manoma a farashi mai rahuwa.

A dusty cup.Hakkin mallakar hoto
Chris de Bode

Ana iya kallon hotunan a harabar St Martin da ke dandalin Trafalgar a Landan daga ranar 19 ga watan Satumba.

Kun san 'yar siyasar da take kwana uku ba ta yi wanka ba?


Helen Zille leaves the parliament in Cape Town on February 12, 2015Hakkin mallakar hoto
AFP

Wacce irin sadaukarwa za ka yi domin alkinta ruwa?

Ita dai shugabar gwamnatin lardi ta Afirka ta kudu na ganin za a iya yin komai domin alkinta ruwa.

Firimiyar Yammacin Cape Helen Zille ta ce tana yin kwana uku ba ta yi wanka ba.

Duk da wasu na ganin hakan kamar bai kamata ba, a zahiri tana da dalilai masu karfi na daukar matakin.

Kun san dalilinta na yin wanka sau daya a kwana uku? Yankin Yammacin Cape – wanda ya yi suna wajen tsaunuka da bakin teku – yana fama da matsanancin karancin ruwan sha wanda ya yi kamari saboda farin da yankin ya fada a shekarar da ta wuce.

“Ina yin wanka ne a takaice, kuma sau daya a kwana uku. A sauran kwanakin makon kuwa nakan wanke hannayena ne. A baya nakan wanke gashin kaina a kullum, amma yanzu kwaskwarima kawai nake yi,” in ji Ms Zille a wata makala da ta wallafa.

“Sai dai kuma ina ganin gashi mai maiko a matsayin wata alama ta nuna matsayi.”

Duk da haka Ms Zille, wacce da ita aka kafa jam’iyyar hamayya ta Democratic Alliance (DA), ta bai wa mutane da dama mamaki da wadannan kalamai nata.

Ms Zille babakuwa ba ce wajen janyo ka-ce-na-ce. A kwanan baya ta janyo ce-ce-ku-ce bayan ta wallafa wani sakon Twitter inda ta ce wani bangare na mulkin-mallaka alheri ne.

‘Yan kasar Afirka ta kudu na ganin rashin yin wanka ba wani babban abin damuwa ba ne.

Mazauna yankunan marasa galihu na Cape Town na dogara ne da wani famfo da al’umar ta kafa wajen samun ruwan wanka, yayin da mazauna yankunan da ke samun matsakaicin kudin shiga ke samun ruwa a famfunan giadajensu.

Amma kalaman da shugabar ta yi wata hanya ce ta sake yin nazari kan yadda ake yin amfani da ruwa.

Yanzu me muka sani game da yadda daya daga cikin ‘yan siyasar Afirka ta kudu ke kula da kiwon lafiyarta?

A kwanan baya ne aka caccaki Ms Zille a wata makala da aka wallafa a TimesLive inda aka yi tambayoyi kan yadda shugabar lardin ke kashe harajin da ake karba wajen samar da ruwan sha a gidanta na gwamnati da ke Cape Town.

A yayin da take nuna cewa ta dauki matsalar karancin ruwan a matsayin wani babban al’amari, Ms Zille ta ce “Ni da mijina muna yin amfani da ruwa maras yawa ta yadda, a wasu lokutan nakan damu kan yanayin kiwon lafiyarmu.”

Wannan labari ka iya sa wa masu amfani da shafukan sada zumunta su sarara, amma ga mutanen da ke yankin da ke fama da karancin ruwa, batun ba na wasa ba ne.

Zurfin ruwan da ake da shi a yankin Yammacin Cape kashi 35 cikin 100‚ wato ya ragu da kashi 61 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar da ta wuce, in ji sashen samar da ruwan sha na lardin.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Cape Town residents are only allowed to use 87 litres of water a day

Yanzu kuma an sanya takunkumi kan yawan ruwan da za a yi amfani da shi a lardin, inda ba za a kyale kowanne mutum ya yi amfani da fiye da lita 87 a kowacce rana.

Za a ci tarar duk mutumin da ya yi amfani da ruwa da yawa, kuma za a dauki tsattsauran mataki kan wuraren kasuwanncin da suka yi amfani da ruwa fiye da kima.

Sai dai da wahala a tilasta wa mutane kan yadda za su yi amfani da ruwa, don haka an fi mayar da hankali waurin rarrashinsu.

Hukumomi sun ce daidaikun jama’a da wuraren kasuwanci ba sa yin biyayya ga wannan doka.

Lardin na dubawa yiwuwar bullo da wata hanyar ta samun ruwan sha, ciki har da sake yin amfani da ruwan da aka gama aiki da shi da kuma hako ruwan da ke karkashin kasa.

Iran ta yii gwajin sabon makami


IranHakkin mallakar hoto
Getty Images

Iran ta ce ta yi nasarar gwada sabon makaminta mai linzami kirar Khorram Shahr.

An bayyana makamin a wani faretin soja da aka gudanar jiya Juma’a a birnin Teheran kuma an ce yana iya cin nisan kilomita dubu biyu, idan an harba shi.

Tashar talbijin din kasar ta nuna hotunan gwajin da aka yi.

Wani makamin Khorramshahr da Iran ta gwada a watan Janairu ya yi bindiga yana cikin tafiya a sama.

Gwaji na baya-bayan nan ya zo ‘yan kwanaki bayan Shugaban Amurka Trump ya soki lamirin shirin Iran na kera makamai masu linzami a jawabin da ya gabatar cikin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Facebook zai fallasa bayanan kutsen zaben Amurka


Mark ZuckerbergHakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya ce kamfanin nasa zai mika wa majalisar Dattijan Amurka bayanan tallace-tallace 3,000 da aka alakanta su da kasar Rasha dangane da zaben shugaban Amurka.

Mista Zuckerberg ya sha alwashin baza komai a faifai daga yanzu dangane da labaran karya da aka rika yadawa a Facebook.

A farkon wannan watan ne aka gane cewa kamfanin Facebook ya gudanar da bincike dangane da tallan siyasa da kasar Rasha ta dauki nauyi – tuhumar da Rasha ta musanta.

Bayan fuskantar matsi daga jama’a, kamfanin Facebook ya yarda ya mika wadannan tallace-tallacen ga wani kwamitin majalisar Dattijan Amurka dake binciken kutsen da Rasha tayi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen shekarar 2016.

A cikin jawabin da yayi mai tsawon minti 9, Mista Zuckerberg ya ce shafin na Facebook zai rika fayyace wa masu amgfni da shafin inda kudaden tallan da ake saka wa suka fito.

Mista Zuckerberg ya ce: “Bayan bayyana sunan shafin da ya biya kudin tallan da kake da sha’awar sani, zamu kuma ba kowa damar ziyartar ainihin shafin da ya saka tallan domin ganin dukkan tallace-tallacen da ya saka a Facebook.”

Kamfanin ya ce yana da shirin amfanin da kwararru wajen tantance irin wadannan tallace-tallacen. Amma ana jin zai yi matukar wahala ganin girman aikin dake gabansa, inji Siva Vaidhyanathan, wani farfesan ilimin sadarwa dake jami’ar Virginia:

“A ganina kamar ba shi da iko a kan wannan tsarin da ya gina da hannunsa, Kamfanin Facebook ba zai iya daukan isassun ma’aikatan da zasu rika sayar wa wasu mutane guraben talla ba. A ganina tsarin na Facebook shi ne matsala”, inji Farfesa Siva.

An gano dalibi bayan kwana uku ba ci ba sha


Dance partyHakkin mallakar hoto
Getty Images

An ceto wani dalibi a jihar Indiana ta Amurka bayan takwarorinsa sun bar shi a baya inda ya shafe kusan kwana uku cur a cikin wani kogon da suke zuwa raye-raye.

Bayan rabuwar Lukas Cavar da ayarin abokansa, sai ya iske kofar kogon garkame da kwado.

Layin sadarwa ya yi kasa a wayarsa ta salula, kuma duk ihun neman dauki da ya yi tsawon sa’o’i bai iya kai wa ga kunnen wani mahaluki ba.

Lukas Cavar ya ce ya rayu ne ta hanyar tsotsar danshin da ke jikin ganuwar kogon tare da zuba wa kansa surutu.

Daga baya ne aka gano shi a kusa da kofar kogon yana sharar barci.

Ba a san yadda aka yi har ya rabu da abokan tafiyarsa ba.

Za a fara koyar da ilimin jihadi a makarantun Turkiyya


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli bidiyo kan takaddama kan sauya tsarin koyarwa a Turkiyya

Makarantun Turkiyya sun fara sabuwar shekarar karatu ta bana cike da takaddama sakamakon gabatar da sabuwar manhajar karatu mai cike da ce-ce-ku-ce, wacce aka cire koyar da ilimin cewa halittar dan adam ta sauya ne daga dabba zuwa mutum wato (Evolution), inda a madadin sa aka gabatar da ilimin jihadi.

A ganin gwamnati mai kishin Islama ta Turkiyya, an yi hakan ne domin sabbin dabi’un ilimi.

Masu suka sun yi tir da sabbin littatafan makarantun a matsayin masu wariya kan jinsi da kuma masu adawa da kimiyya, sun kuma sun yi korafi cewa hakan koma baya ne ga tsarin ilimin da ba ruwansa da addini.

Dan jam’iyyar hamayya ta CHP, Bulent Tezcan ya ce: “Suna kokarin gurbata tunanin yara ne ta hanyar saka karatun jihadi (a manhajar karatun yara) tare da irin fahimtar da ta tsunduma Gabas Ta Tsakiya cikin kashe-kashe.”

Amman gwamnatin kasar ta soki ‘yan hamayya da kokarin yada bakar farfaganda a wani yunkuri na raba al’ummar Turkiyya gabannin zabukan shekara 2019.

“Idan muka ce dabi’u, suna fahimtar wani abu ne daban. Muna alfahari da ra’ayinmu na ‘yan mazan jiya masu bin tafarkin dimokradiyya, amman ba ma son kowa ya zama kamar mu,” in ji ministan ilimi Ismet Yilmaz.

Kwato jihadi daga masu jihadi

Hakkin mallakar hoto
AFP

Ana bayar da littattafan da ke bayanai kan jihadi a makarantun koyon sana’a na Turkiyyya, wadanda aka fi sani da sunan makarantun Imam-Hatip. Daga nan kuma za bai wa ‘yan makarantar sakandare zabin darasin nan da shekara daya.

An ware wani littafi mai suna ‘Rayuwar Annabi Muhammad (SAW)’ domin yin tsokaci akai, kan zargin cewa an tabo batun wariyar jinsi da kuma bayanin kan jihadi da ya yi.

Kamus din cibiyar koyar da harshen Turkiyya ya bayyana jihadi a matsayin “yakin addini.” Amman jami’an ma’aikatar ilimi sun ce kungiyoyin da ke ikirarin jihadi irin IS mai da’awar kafa daular Musulunci suna bata ma’anar jihadi domin cimma wasu bukatunsu.

Hakkin mallakar hoto
Turkish education ministry

Image caption

Masu suka sun ce littatafan sun bayyana mata a matsayin uwa, yayin da suka bayyana na miji a matsayin wanda ya fi karfi

Ministan ilimin ya ce ya kamata a shigo da sunan jihadi a matsayin wani bangare na addinin Islama a mahangar “kaunar kasa”.

Ministan ya ce: “Jihadi wani bangare ne na addininmu. Nauyin da ya rataya a kanmu shi ne mu koyar da ko wanne abu ta yadda ya kamata tare da gyara abubuwan da aka yi wa mummunar fahimta”.

Har wa yau littafin mai cike da ce-ce-ku-ce ya bayyana cewar mace ta yi wa mijinta “biyayya” wani nau’i ne na “ibada”.

Amman jami’an gwamnati sun ce wannan ba abun mamaki ba ne tun da littafi ne na addinin Islama kuma ya ambato ayoyi daga Alkur’ani.

“Allah ne ya fada, ba ni ba. In yi masa gyara ne, ko mene ne?” in ji Alpaslan Durmus, wanda yake shugabantar hukumar ilimi.

Amma an gudanar da manyan zanga-zanga biyu a karshen makon da ya gabata, inda maudu’an #NoToSexistCurriculum da #SayNoToNonScientificCurriculum da kuma #DefendSecularEducation suka yi ta jan hankulan mutane a shafukan sada zumunta a Turkiyya.

Wani shugaban wata kungiya ya yi kira ga masu zanga-zanga su ce”tir da sabuwar manhajar da ta hana kimiyya a karni na 21″.

Hakkin mallakar hoto
Turkish education ministry

Image caption

Wannan littafin da ya yi magana kan yunkurin juyin mulkin watan Yulin shekarar 2016 ya yi amfani da Alkur’ani wajen cewa “jarumta na nufin fito-na-fito da azzalumi”

‘Yan hamayya sun zargi jam’iyyar AKP mai mulki ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan da maye gurbin ginshikin jamhuriyar Turkiyya mara addini da dabi’un Islama da na masu tsattsaruran ra’ayi.

Kalaman da suhgaban kasar ya furta kan samar da wata al’umma saliha sun janyo fargaba a zukatan wasu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Masu zanga-zanga a Ankara sun zargi jam’iyyar AKP mai mulki da yi wa tsarin karatun Turkiyya mara amfani da addini zagon kasa

Ma’akatar ilimin ta kuma ce masu suka “jahilai ne” domin sun yi da’awar cewar an cire ilimin cewa halittar dan adam ta sauya ne daga dabba zuwa mutum wato (evolution) gabadaya daga manhajar karatu.

Ministan ya ce za a karantar da wasu sassa na ilimin rikidar halittar (evolution) a matakin sakandare, amma ba da sunan na evolution ba.

Amman Aysel Madra daga cibiyar garambawul ga Ilimi a Turkiyya na ganin yin hakan zai rudar da yara ne kawai.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kiritsoci da Musulmai da suka yarda da cewar Allah ne ya yi halita sun yi watsi da ilimin rikida (evolution)

Kawunan kungiyoyin malamai ma sun rabu kan muhawarar jihadi.

Hakkin mallakar hoto
TURKISH EDUCATION MINISTRY

Image caption

Litattafan makarantun Imam-Hatip sun yi la’akari da ayoyi daga alkur’ani kan ayyana mumini da kafiri da kuma munafiki

Jagoran IPOB ya garzaya kotu


'Yan IPOBHakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa jamhuriyar Biafra a Najeriya ta kalubalancin umarnin kotun da ya ayyanata a matsayin kungiyar ta’addanci.

Lauyan kungiyar, Ifeanyi Ejiofor, ya shaida wa BBC cewa kungiyar ta shigar da kara a kotu domin kalubalantar matakin ayyanata a matsayin da ‘yan ta’adda.

Takardar karar wadda kungiyar ta shigar a ranar Juma’a, ta ce IPOB ba ta kaunar tashin hankali, kuma saboda haka hukuncin da wata kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na ayyanata a matsayin kungiyar ta’adda ya ci karo da doka.

Mista Ejiofor ya ce ba a yi wa Kanu adalci ba domin bai halarci zaman da kotu ta yi kafin a ayyana kungiyarsa a matsayin ta ta’adda ba.

A ranar Laraba ne dai gwamantin Najeriya ta samu hukuncin kotu da ya ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta’adda.

Hakazalika a ranar Laraba rundunar sojin saman kasar ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna ‘Operation Python Dance II.’

A ranar Litinin tawagar gwamnonin arewacin Najeriya, suka yi wani rangadin shiyyoyin kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar, a wani kokari na shawa kan rikicin.

A baya-bayan nan dai rikicin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin ya yi kamari.

Messi, Ronaldo na cikin fitattun 'yan wasa na duniya na 2017


Ronaldo da Carli Lloyd a bikin lashe kofin bara

Image caption

Ronaldo da Carli Lloyd a bikin lashe kofin bara

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta fitar sunayen wadanda za a zabi fitaccen ‘yan kwallo na duniya daga cikin su, wadanda suka hada da Cristiano Ronaldo daga Real Madrid da Lionel Messi daga Barcelona da kuma Neymar daga Paris St-Germain.

A bara ma Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasa, bayan da ya doke Messi da Neymar da kuma Antoine Griezmann.

Kocin Chealsea Antonio Conte na iya lashe kofin gwarzon koci bayan da ya ja ragamar kungiyar har suka kai da samun nasarar lashe kofin Premier a kakarsa ta farko a Stamford Bridge.

An sake gabatar da mai rike da kofin fitacciyar ‘yar kwallo ta mata Carli Lloyd a matsayin wacce za ta lashe kofin na bana.

Lieke Martens wadda ta ci kwallo uku a wasan neman shiga gasar Euro 2017 a Netherland, da kuma ‘yar kwallon Venezuela Deyna Castellanos su ne abokan karawar Lloyd.

A ranar 23 ga watan Oktoba ne za a gabar da wadanda suka yi nasara a dakin taro na Palladium da ke Landan.

Nigeria: An kori jami'an Kwastam 'kan shigo da makamai'


Wadannan su ne bindigogin da hukumar kwastam ta kama cikin wannan makon

Image caption

Wadannan su ne bindigogin da hukumar kwastam ta kama cikin wannan makon

Masana harkokin tsaro sun fara tofa albarkar baki musammam game da jami’an hukumar kwastam 28 da ake zargi, da hannu wajen kawar da kai ga makaman da ake satar shiga da su Najeriya.

Babban kwanturolan hukumar, Kanal Hamid Ali ya ce bayan kammala bincike da hukumar tasa ke da alhakin yi kan lamarin, ta mika makaman da wadanda ake tuhuma ga hukumar tsaro ta farin kaya ta kasar, kuma tuni an mika su ga kotu don a yi musu hukuncin da ya dace.

“Mu kuma namu jami’an da muka kama su da hannu a ciki tuni muka kore su daga aiki.”

A baya-bayan nan dai hukumar kwastam ta Nigeria ta kama bindigogi 470 a tashar jiragen ruwan Tincan Island a Lagos, wadanda aka shigo da su daga kasar Turkiyya, makonni kadan da shigo da kama wasu fiye da 1,000 da suma aka shigo dasu daga Turkiyyan.

Gwamnatin kasar ta ce dole ta hau teburin tattaunawa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke kasar.

Malam Kabir Adamu, wani mai sharhi ne kan harkokin tsaro, ya kuma shaida wa BBC cewa duk da yake babu cikakkiyar shaida mai alakanta irin wannan sakaci na jami’an kwastam, da shigar irin wadannan makamai hannun kungiyoyi irinsu Boko Haram, da masu satar mutane da kuma sauran masu gwagwarmaya da makamai, ana iya cewa al’amarin ba karamar barazana ba ce ga Najeriya.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakken bayanin da Malam Kabir ya yi wa abokin aikinmu Usman Minjibir:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanin Kabir Adamu kan hukumar kwastam

An hana malamin Saudiyya wa'azi saboda cin fuskar mata


Matan SaudiyyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Malamin ya ce kaifin tunanin mata rabin na maza ne, kuma da zarar sun kammala cefane idan suka je kasuwa to aikin kwalkwalwar tasu na zama rubu’in na namiji.

An haramtawa wani shaihin malami yin wa’azi a Saudiyya sakamakon bayyana rashin dacewar barin mata su tuka mota, a inda ya bayyana hakan da shashanci.

A wani bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, Sheikh Sa’ad al Hajari ya ce kaifin tunanin mata rabin na maza ne, kuma da zarar sun kammala cefane idan suka je kasuwa to aikin kwalkwalwar tasu na zama rubu’in na namiji.

Daman dai ba a amince wa mata su yi tuki ba a kasar duk da cewa babu wata doka kan hakan.

Tsokacin da Sheikh Sa’ad al- Hajari ya yi kan batun haramtawa mata a Saudiyya tuka mota, ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta da muhawara.

Al Hajari ya fara ne da cewa an halicci mata da kankanuwar kwakwalwa, don haka maza suka fi su kaifin fahimta.

Bai tsaya a nan ba sai da ya kara da cewa: “Mata ba su da cikakkiyar kwakwalwa, rabi aka ba su, da zarar kuma sun kammala sayayya a manyan shaguna, rabin kwakwalwar na koma wa kwata.”

Don haka ya dasa ayar tambaya, “Shin za a bar mutumin da ba shi da cikakkiyar kwakwalwa ya tuka mota?”

Martanin da mabiya shafinsa suka mayar ba mai dadi ba ne, hasali ma wasu na ganin bai kamata a matsayin da ya ke da shi na babban malamin addinin musulunci, ya yi kalami irin haka ba.

Wasu ma na ganin ya kamata ma hukumomin Saudiyya su dakatar da shi daga yi wa al’umma wa’azi ko yin Limancin Sallah.