Aguero ya dawo atisaye bayan da ya yi hatsarin mota

98267820_7749a4ea-ca81-497e-8b23-00425c30fc65.jpg


Sergio Aguero ya ci wa Mancherster City kwallo 176Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sergio Aguero ya ci wa Mancherster City kwallo 176

Dan kwallon Manchester City Sergio Aguero ya dawo atisaye bayan ya shafe kwana 11 yana jinyar rauni sakamakon hatsarin mota da ya yi a Amsterdam.

Dan wasan mai shekara 29 ya yi tsammanin zai yi jinyar ta tsawon makonni da dama, amma sai ya dawo yin atisaye ranar Talata.

City ta ce dan kwallon Argentinan zai dawo ganiyarsa a kwanaki masu zuwa, inda yake zumudin dawo wa kungiyar karon farko.

City wacce ita ce ta farko a teburin firimiya, wacce kuma ta sha gaban Mancherster United a cin kwallaye, za ta fafata da Stoke ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *