An kama mai gadin da ya yi lalata da yara mata 54

98268953_schoolchildren.jpg


'Yan makarantar a AfirkaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yara ‘yan matan firamare biyu masu shekaru 8 da 12 ne suka kai karar mai gadin wajen ‘yan sanda

Hukumomi a Afrika ta Kudu sun tsare wani mai gadi bisa zarginsa da laifin cin zarafin yara ‘yan firamare mata su 54.

A ranar Litinin aka soma bincike kan batun, bayan da wasu dalibai mata biyu suka kai kara, kuma tuni gwamnati ta tura jami’ai zuwa makarantar da ke Soweto a kudancin Johannesburg.

Yara ‘yan mata biyu ‘yan shekaru 8 da kuma 12 ne suka je ofishin ‘yan sanda a ranar Litinin —- inda suka kai kara cewa wani mai gadi ya yi lalata da su a wata makarantar firamare da ke Soweto.

Tun lokacin da aka soma bincike, —-sai aka gano cewar mutumin ma ya ci zarafin dalibai mata 52.

Kuma ya shafe watai 18 yana tafka ta’asar.

A ranar Laraba ne ake sa ran mai gadin zai bayyana gaban wata kotun Majistre a Soweto.

A halin yanzu kuma sashen ilimi na yankin ya tura jami’ai domin taimakawa ‘yan yaran da aka ci zarafinsu sannan kuma a fadada bincike.

Afrika ta Kudu ta kasance daya daga cikin kasashe da aka fi aikata fyade da kuma cin zarafin mata a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *