An kama wadanda suka 'jibgi' dan Nigeria a India

98266587_d91f4ac7-ee61-4940-9613-61b97994cc67.jpg


An kai wa 'yan Najeriya hare-haren a yankin Greater Noida kusa da Delhi a watan AfriluHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An kai wa ‘yan Najeriya hare-haren a yankin Greater Noida kusa da Delhi a watan Afrilu

‘Yan sanda a Delhi babban birnin Indiya sun ce sun kama mutum biyar wadanda ake zargi da yi wa wani dan Najeriya dukan kawo wuka.

A ranar Talata ne kafofin watsa labarai a Indiya suka nuna bidiyon da ke nuna yadda wasu gungun Indiyawa suka lakadawa wani dan Najeriya duka a birnin Delhi.

‘Yan sanda sun kuma tsare mutumin Najeriyar wanda ayarin wasu magidanta a Delhi suka zarga da sata.

A cikin bidiyon, an ga mutane guda hudu ko biyar na amfani da sanduna suna rafka wa mutumin, bayan an daure shi a jikin wani turke.

Ko lokacin da yake roko Allah-Annabi a yi masa afuwa wani mutum ya kama kafafuwansa, inda wani ya rika zane shi a tafukansa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun afkuwar irin wannan lamari ba a Indiya, ko a watan Afrilun da ya gabata ma an kai wa wasu dalibai ‘yan Najeriya hari a Delhi, inda aka musu duka.

A wancan lokacin har sai da jakadun ƙasashen Afirka a Delhi suka yi Allah wadai da hare-haren da aka kai din.

Kazalika an sha kai wa ‘yan wasu kasashen Afirka da dama hari a sassa daban-daban na Indiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *