Messi ne gwarzon dan wasa – Valverde


Messi ya ci kwallo na 100 a wasannin nahiyar Turai

Image caption

Messi ya ci kwallo na 100 a wasannin nahiyar Turai

Kocin Barcelona Ernesto Valverde, ya ce Lionel Messi zai ci gaba da amsa sunansa na fitaccen dan wasa a duniya ko ya lashe kyautar Ballon ta bana ko bai lashe ba.

A farkon watan nan ne mujallar kwallon kafa ta Faransa ta fitar da sunayen fitatttun ‘yan wasan, inda mutane da dama suka yi amannar cewa Cristiano Ronaldo na Real Madrid zai iya lashe kyautar.

Ko da yake kocin ya gamsu cewa Messi ba ya bukatar wata kyauta da za ta nuna shi ne fitaccen dan wasa a duniya.

A ranar Laraba ne Lionel Messi ya ci kwallo ta 100 a wasannin nahiyar Turai, bayan da Barcelona ta ci Olympiakos 3-1 a gasar Zakarun Turai a Nou Camp.

Mourinho da Conte sun yi cacar -baki


Mourinho da Conte sun yi cacar baki

Image caption

Mourinho da Conte sun yi cacar baki

Cacar-baki ta barke tsakanin kocin Chelsea Antonio Conte da na Mancherster United Jose Mourinho, inda Conte ya ce ya kamata ya kashe wutar gabansa ya daina sa ido a harkokin wasu.

Mourinho ya yi suka akan koci-koci da suke korafi a kan ‘yan wasansu da suke jinya, bayan da kungiyarsa ta yi nasara a karawar da suka yi da Benfica da ci 1-0.

Mourinho ya ce, “Ba na magana akan wani dan wasana da ya ji rauni, amma wasu koci-kocin kuka suke yi idan dan kwallonsu ya yi rauni, a tunanina ba yi wa ‘yan wasan kuka ne mafita ba, mayar da hankali a kan ‘yan wasan da suke da lafiya shi ya fi dacewa don su samu kwarin gwiga. Da a ce zan yi kuka kamar yadda wasu suke yin kuka to da nayi kuka a kan Ibrahimavich, da Pogba, da Fellaini amma ban yi kuka ba saboda ba na yi.

“Kowanne lokaci Mourinho yana sa ido da kuma yin shisshigi akan a al’amuran da suke wakana a Chelsea, ni a ganina kamata ya yi mutum ya kashe wutar gabansa, ba ya sa ido a al’amuran wasu ba”. In ji Conte.

Nigeria: Atiku ya yaba wa Shugaba Buhari


Atiku ABubakarHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Atiku dai ya caccaki Buhari a baya-bayan kan yadda yake tafiyar da mulkinsa

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan umarnin da ya bayar na biyan jami’an tsaron da suka yi yakin Biafra wadanda aka yi wa afuwa, hakkokinsu na fansho.

Atiku Abubakar wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter ya ce, abin da Shugaba Buharin ya yi na nuna hadin kan Najeriya.

A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya amince da biyan fanshon ga jami’an ‘yan sandan da gwamnatin Najeriya ta yi wa afuwa tun a shekarar 2000 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Wadannan ‘yan sanda sun yi aiki ne a ‘haramtacciyar’ kasar Biafra a lokacin yakin basasar Najeriya da aka shafe watanni 30 ana yi.

Sai dai tun bayan da aka yi musu afuwar ba a biya su komai daga cikin kudaden fanshonsu ba.

A wata sanarwa da wata hukuma wadda ke kula da biyan fanshon ta fitar ta ce, za a biya mutum 162 yayin da mutum 57 kuma iyalansu ne za su karba a madadinsu a biyan farko da za a yi.

Hukumar ta kuma ce za a fara biyan farkon ne ranar Juma’a 20 ga watan Oktobar nan a birnin Enugu da ke Kudancin Najeriya.

Sai dai watakila wannan yabo da Atiku Abubakar ya yi wa Shugaba Buhari ya zo wa wasu da mamaki, ganin cewa a baya-bayan ya caccaki gwamnatin Buharin kan al’amura da dama da suka hada da korafin da ya yi na watsi da shi da aka yi a tafiyar da harkokin gwamnatin.

Gurbatar muhalli ya fi kashe talakawa — Rahoto


Mutane na mutuwa kafin tsufansu saboda gurbatar yanayiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gurbacewar iska ita ce sababi mafi girma da ya fi kashe mutane in ji rahoton

Alkaluman mace-macen mutane tun kafin karfinsu ya kare sun dauki kaso kimanin 16 cikin 100 na duk mutuwar da aka yi a fadin duniya a cewar wani rahoto.

Daya daga masu binciken, Richard Fuller, ya ce talakawa sun fi saurin mutuwa kafin karewar karfinsu saboda gurbacewar muhalli.

Kusan duk mace-macen da ake samu kafin tsufa, na faruwa ne a kasashen da ake da karanci ko matsaikaicin samu na duniya.

Kasashen Bangladesh da Somalia su ne kasashen da aka fi samun irin wannan matsalar a cewar nazarin, yayin da kasashen Brunei da Sweden kuma su ne ba a fiye samun mace-mace sakamakon gurbatar yanayi ba.

Yawancin mace macen da ake samu wadanda ke da nasaba da gurbatar muhalli sun hadar da ciwon zuciya da shanyewar barin jiki da kuma cutar kansa ko dajin huhu.

Shi ma, Farfesa Philip Landrigan da ke cikin masu binciken ya ce gurbacewar yanayi ba wai kalubale ne da ya shafi muhalli ba, wata gagarumar barazana ce da ta shafi lafiya da kuma walwalar al’umma.

Binciken ya ce daga cikin abubuwan da ke janyo gurbacewar muhallin akwai isakar gas din da ake shaka a kan tituna da kuma hayakin itace ko gawayin da ake konawa a cikin gidaje.

Binciken ya ce baya ga wadannan abubuwa da ke taimakawa wajen gurbatar yanayi, gurbacewar ruwa ma na da matukar illar ta yadda ke janyo mutuwar mutane da dama.

Haka kuma, binciken ya ce ana yawan samun mace-mace sakamakon gurbatar muhalli a kasashen da tattalin arzikin kasarsu ke bunkasa cikin sauri kamar India da China, inda aka sanya su a matsayi na 16 a cikin jerin kasashen da ake samun mutuwa sakamakon gurbatar yanayi.

Binciken ya ce kasashe kamar Birtaniya da Amurka da ma na Tarayyar Turai ciki har da Jamus da Faransa da Italiya da Spaniya da kuma Denmark, ana samun irin wannan matsala, sai dai su nasu bai kai yawan na kasashe masu tasowa da kuma wadanda ke fama da talauci ba.

Rahoton ya ce, da gurbacewar yanayi da fatara da rashin ingantacciyar lafiya da kuma rashin daidaito a tsakanin al’umma na da matukar alaka da juna.

'Wane dan Boko Haram ne ya taba karatu a Saudiyya?'


BHHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya ce ‘yan Boko Haram a Najeriya suka samu tsattsauran ra’ayinsu, don kuwa ba su taba zuwa Saudiyya karatu ba

Wani malamin musulunci a Najeriya ya kalubalanci ikirarin cewa kasar Saudiyya na koyar da fannonin ilmi da ke rura wutar tsaurin ra’ayin addinin musulunci a duniya, inda ya ce da gaskiya ne wannan zargi to da yanzu duniyar ma ba za ta zaunu ba saboda yawan masu zafin ra’ayi.

Dr. Muhammadu Sani Umar Rijiyar Lemo malami a Jami’ar Bayero Kano wanda kuma ya yi karatun digirinsa na farko har zuwa na uku a Saudiyya ya yi ikirarin cewa Allah ya yi yawa da daliban da kasar ta yaye a duniya, kuma da tsattsauran ra’ayin addini suka koya “da yanzu duk mu ma mun zama ‘yan ta’adda”.

“Muna nan irinmu ba iyaka. Ba na jin akwai wata kasa da ta yaye dalibai na ilmi wadanda suke karantarwa kamar Saudiyya, in ji shi.”

Ya ce yanzu idan ka dubi wadanda ake fama da su a nan kasar (‘Yan Boko Haram), dalibi nawa ne aka ce maka daga Saudiyya yake? Wane ne a cikinsu ya je Saudiyya ya yi karatu?

Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo na wannan jawabi yayin zantawa ta musammam da BBC game da yunkurin hukumomin Saudiyya na bude wata cibiya da za ta rika tantance sahihan hadisan Annabi Muhammadu (S.A.W), don hana masu tsaurin ra’ayi jirkita ma’anoninsu.

Ya ce kudurin bude wannan cibiya ya samo asali ne daga kiraye-kirayen malamai da masana kimanin tsawon shekara 20 da ta gabata don fadada wannan cibiya.

“Akwai Markazutu Hikmatu Sunnan Nabawiyya wanda sashe ne a cibiyar Mujamma’ana Malik Fahad da hadin gwiwar Jami’ar Islamiyya a kasar Saudiyya wanda ya faro wannan gagarumin aiki tun wancan lokaci.”

A cewarsa: “Jingina abin da wata matsin lambar Kasashen Yamma ga wannan yunkuri na Saudiyya, wata muguwar fassara ce da wasu ke yi, amma kwata-kwata babu wannan abin ko kadan,” in ji shi.

Dr. Sani Rijiyar Lemo ya ce irin aikin da wannan cibiya za ta yi, zai taimaka wajen fito da ma’anonin hadisan Annabi daga malaman farko.

“Bukhari da Muslim da sauran manyan litattafan hadisai suna da sharhin da malamai suka yi musu tun sama da shekara dubu.”

Ya ce hidima ta ilmi ba ta da alaka da wani wanda zai zo yana ta barna a bankasa, da sunan addini, maimakon haka ma ita ce za ta rushe abubuwan da yake fada da ba na gaskiya ba.

Masu shayi sun koka da tsadar burodi


An fi cin burodi da safe a wasu wurareHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jama’a da dama na kalacin safe da burodi

A Najeriya, wasu masu sayar da shayi na kokawa game da tsadar burodi, abokin tafiyar shayi.

Masu shayi wadanda ke cewa tun da yanzu kayan sarrafa burodi kamar fulawa, da yis da sauransu sun sauka, kamata ya yi masu gidajen burodi su rage farashinsa.

Haruna Suleiman da akafi sani da Maikudi mai shayi, shi ne sakatare na kungiyar masu shayi a jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, tunda farashin kayyakin hadin burodi sun yi sauki, to yakamata kungiyar masu yin burodi a ko ina a Najeriya su yi la’akari da halin da ka ciki a kasa musamman talakawa a rage farashin burodi.

Maikudi mai shayi, ya ce masu yin burodi su rage farashinsa saboda yawan bukatarsa ma da mutane ke yi, ta yadda ba zai gagari talaka ba.

To sai dai kuma, shugaban gidan burodin Tahir Bakery a jihar Kaduna, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masu burodi a Arewacin Najeriya, Alh.Bashir Tahir, ya shaida wa BBC cewa, an samu matsala kwanakin baya a lokacin da gadar Jaba wadda ake bi wajen shigo wa Najeriya daga Kuduncin kasar ta karye inda hakan ya janyo kayayyakin hadin burodin suka yi karanci a kasuwa.

Alh.Bashir, ya ce sakamakon karancin kayayyakin, sai farashin kayan hadin burodin ya tashi, to amma an gyara gadar yanzu kaya sun wadata a kasuwa amma duk da haka farashin kayan bai koma kamar na da ba.

Don haka ya ce, yadda ake tunanin kayan hadin burodin sun sauka, gaskiya ba su sauka ba.

A kwanan baya dai tsadar burodi ta tilastawa wasu masu cinsa daina wa musamman masu karamin karfi.

'Yadda wani ya ci zarafina ta hanyar taba min jiki'


A ci gaba da kawo maku rahotanni kan shirin mata 100 na BBC, wannan mako muna dauke ne da rahotanni kan yadda ake cin zarafin mata a wuraren taron jama’a.

Mai gabatar da shirye-shiryen talabijin da rediyo Anita Nderu ta bayar da labarin yadda aka taba cin zarafinta a motar bas a Nairobi.

Ta na fatan labarinta zai taimaki wasu matan su fito su bayar da labarin irin yadda aka taba cin zarafinsu.

Kamfanin man kara hasken fata na Nivea na tsaka mai wuya a Afirka


Man NiveaHakkin mallakar hoto
Folaranmi Twitter

Babban kamfanin man shafawa na Nivea yana fuskantar kalubale bayan da ya fitar da wani tallan man shafawa mai kara hasken fata a Afirka ta yamma.

An haska tallar man na talabijin an kuma sanya a allunan talla na kan titi, inda aka yi masa lakabi da “farar fata ta ainihi,” a Najeriya da Ghana da kamaru da kuma Senegal.

An kuma yi amfani da hoton wadda ta taba zama sarauniyar kyau ta Najeriya, Omowunmi Akinnifesi a tallar.

Wata mai tallan kayan kawa Munroe Bergdorf, wacce aka sallama kwanan nan daga wani talla na kamfanin L’oreal bayan da ta yi magana a kan wariyar launin fata a Amurka, na daya daga cikin wadanda su ka soki tallar ta Nivea, wanda ta sa a shafinta na Instagram.

Duk da mutane da yawa sun nuna cewa man shafawar ba sabon fitowa ba ne, ya zama abin cece-kuce a kan shafukan sada zumunta.

Kamfanin Nivea din ya nemi afuwa kan wannan abu, inda ya shaida wa BBC cewa ba su yi hakan da nufin su bata wa abokan huldarsu rai ba.

Ko a baya-bayan nan ma mutane sun yi ta sukar wani tallan kamfanin Dove da ya nuna alamar wariyar launin fata.

Mai tallan kayan kawar da ta fito a tallar ta Dove wacce ‘yar asalin Najeriya ce kuma ‘yar kasar Amurka, Lola Ogunyemi, ta fito ta tofa albarkacin bakinta kuma ta kare kanta a game da tallar inda ta ce mutane sun yi wa tallar mummunar fahimta ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sojin saman Nigeria ta tura jiragen yaki Jos


Rundunar sojin saman NajeriyaHakkin mallakar hoto
NAF

Image caption

Sojin saman Njeriya na taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a sassan kasar

Rundunar sojin saman Najeriya ta tura jiragen yakin sama da jami’anta zuwa Jos, babban birnin jihar Filato domin tallafa wa rundunar tabbatar da zaman lafiya da ke aiki a jihar.

Sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce hafsan sojin saman kasar, Air Marshal Siddique Abubakar ne ya bayar da umarnin tura jiragen yakin a wani mataki na bin umarnin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa a dakile tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan jihar.

Rundunar sojin saman ta tura jirgin sama samfurin L-39ZA da kuma jirgi mai saukar angulu samfurin EC-135, wadanda za su bayar da kariya ga rundunar da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Wannan dai ba shi ne lokaci na farko da rundunar sojin saman Najeriya za ta tura jiragen yaki wani bangare na kasar domin tallafa wajen tabbatar da zaman lafiya ba.

Wannan na zuwa ne sakamakon tashe-tashen hankulan da ake samu na baya-bayan nan, inda aka kashe a kalla mutum 35 aka kuma jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato a ranar Lahadin da ta gabata.

Tun a lokacin ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi sojojin kasar a kan su tashi tsaye wajan daukar matakan dakile tashen-tashen hankula da suka dawo a jihar ta Filato.

Hakkin mallakar hoto
NAF

Image caption

Shugaba Buhari ya nemi sojojin kasar da su tashi tsaye wajan daukar matakan dakile tashen-tashe hankula a Filato

Ban ga laifin tsare bayanmu ba – Jose Mourinho


Mile SvilarHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mile Svilar ya kusa yin hawaye a karshen wasan. Dan uwansa na kasar Bejium, Romelu Lukaku ya je ra rarrashe shi.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce babu laifi in kungiyarsa ta kware a tsaron baya, bayan United ta doke Benfica 1-0.

Marcus Rashford ne ya ci kwallo dayan da aka ci a wasan a lokacin da ya yi bugun tazara wadda ta zo wa sabon mai tsaron gida, Mile Svilar, da bazata.

An soki United kan salon wasan da ta yi a kece-rainin da suka tashi 0-0 da Liverpool ranar Asabar inda suka auna mai tsaron gida sau daya tak, amman an ci Red Devils kwallo shida ne kawai a kakar bana.

“Mu ne muke da karfin guiwa kuma mu ne muka juya akalar wasan,” in ji tsohon kocin Benfica Mourinho. “Ban taba tunanin cewa za a iya cinmu ko kwallo daya ba, mun tsare baya.

“A wasu lokutan sai in ji kwarewa a tsaron baya wani laifi ne, amman ba laifi ba ne. Kwarewa a tsaron baya wani mataki ne na samun sakamako mai kyau. Mun san matsin Benfica ba zai kai miniti 90 ba.

“Irin tsare bayan da Liverpool ta yi a wasanmu da su, Benfica ta gaza yin hakan zuwa karshen wasa. Ko babu matsi, mun san za mu ci kwallo.”

Wadanda suka yi belin Nnamdi Kanu na tsaka mai wuya


A watan Afrilu 2017 ne aka bayar da Nnamdi Kanu beli bayan ya shafe wata 18 a tsare.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Afrilu 2017 ne aka bayar da Nnamdi Kanu beli bayan ya shafe wata 18 a tsare.

A Najeriya, mutanen uku ciki har da wani dan Majalisar dattawan kasar da suka yi belin Shugaban kungiyar ‘yan ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu na tsaka mai wuya.

Hakan ya biyo bayan rashin bayyanar sa a gaban kotu ranar Talata, inda mai shari’a Binta Nyako ta bada umurnin su kawo shi.

Sanata Enyinnaya Abaribe da Immanuel Madu da kuma Torchokwu Uchendu sune suka yi belin Mr Kanu wanda ake yi wa shari’a a Kotun tarayya da ke Abuja kan zargin cin amanar kasa.

Shi dai lauyan Mr Kanu, Mr Ifeanyi Ejiofor ya shaida wa kotu cewa bai san inda wanda yake kare wa yake ba.

Mai shari’a Binta Nyako ta ce matukar wadanda suka tsayawa Mr Kanu suka kasa kawo shi gaban kotun, za su rasa Naira miliyan 100 da suka ajiye cikin sharuddan belin.

Me ake bukata wadanda suka tsayawa Kanu beli su kawo?

 • Dole sai sun kawo shi
 • Ko a tsare su
 • Ko kuma su rasa Naira miliyan 100 da kowannensu ya ajiye na beli

Ga dai cikakken bayani da Barista Muhammad Modibbo Bakare, masanin harkokin shari’a a Najeriyar ya yi wa Haruna Shehu Tangaza kan zabin da mutanen uku ke da shi.

Sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraro:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Hanyar da ta rage wa masu belin Nnamdi Kanu

Cinikayya: Wa yafi amfana China ko Najeriya?


Communist Party banner in BeijingHakkin mallakar hoto
AFP

A jiya Laraba ne jamiyyar kwaminisanci ta China ta gudanar da babban taronta a birnin Beijing, karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Chinar ke cika gaba da kulla kyakkyawar dangantaka ta fuskar kasuwanci da kasashen duniya, musamman nahiyar Afurka.

Najeriya na daga cikin kasashen da suka kulla alakar kasuwanci da gwamnatin Chinar, inda kasashen 2 suka fara ayyukan hadin gwiwa na ababen more rayuwa misali tashar Jirgin kasa ta zamani da aka bude a watan Yulin bara.

Tuni wasu matasa manoma ‘yan Najeriya na cikin wadanda suka fara cin gajiyar kula yarjejeniyar kasuwanci tsakanin su da wani kamfanin China.

Banagarorin biyu sun cimma matsaya akan yadda zasu rika gudanar da cinikin amfani gona irin su citta da itacen katako a tsakaninsu.

Mahmud Nuhu Sulaiman shi ne wakilin kamfanonin China da suka zo Najeriya domin kulla dangantakar kasuwanci da ‘yan kasuwar kasar, kuma ya bayyana wa BBC cewa kasar ta China ta riga ta kammala shirye-shiryen kulla dangantakar cinikayya da ‘yan kasuwar Najeriya:

“Duk ‘yan kasuwan da suke da kayan da China ke bukata zasu kai kayansu wata ma’aikata ta musamman a nan Najeriya inda zamu duba kayan kuma mu biya ‘yan kasuwan kai tsaye”, inji Mallam Mahmud.

Mahmud ya kuma bayyana cewa: “Akwai wani katako da ake kiransa Koso, wasu kuma na kiransa Madrid. To bayan mun sayi wannan katakon, sai mu sarrafa shi, wato mu tsaga shi kuma mu loda shi a cikin kontena. Daga nan sai mu tura kayan zuwa kasar Sin.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

BBC ta tambayi Babaji Ibrahim, wakilin wata kungiya ta manoma, ‘Bauchi Youth Farmers’ alfanun da suke fatar samu daga wannan dangataka ta kasuwanci.

Ya ce “Wannan yarjejeniyar ta kunshi kayan gona iri biyu zuwa uku. Na farko ita ce citta, sai kwallon yazawa wato ‘cashew nut’ na ukun kuma shi ne katako”.

Ya kara da cewa sun cimma wata matsaya dangane da cinikin katako, wanda har sun fara fitar da shi zuwa China.

“A bangaren citta kuma, mun kammala tattaunawa dasu jiya, inda suka bayyana mana yadda tsarin kasuwancin yake a China”, inji shi.

Fauziyya Sa’idu Salisu wata ‘yar kasuwa ce mai fitar da Citta zuwa kasashen ketare.

Ta ce, “yan kasuwanmu zasu sami karuwa mai yawa, saboda zamu rika sayen citta a lokacin da take kakarta sai mu adana ta har lokacin da farashinta ya tashi. Kaga zamu sami alfanu mai yawa”.

Amma ayar tambaya anan shi ne: Shin Wa yafi moriya da wannan shiri? Najeriya ko China?

Balarabe Shehu Ilela wani mazaunin kasar China ne, inda ya dade yana harkokin kasuwanci daga Najeriya zuwa China. Ya bayyana dalilin da yasa China ke neman kulla dangantakar ciniayya da nahiyar Afirka, musamman Najeriya:

“Idan kasa tayi karfi wajen bangaren tattalin arziki, tana bukatar fadada harkokinta a siyasance domin ta taka rawa a tsakanin kasashen duniya. A halin yanzu tattalin arzikin China ya bunkasa sosai har yana abin da masana ke kira ‘over-heating’ na kudaden zuba jari.”

Ya bayyana cewa, “Wannan ne yasa dole take turo kamfanoninta na cikin gida da su fita waje, domin idan ta bar su a gida za a sami matsala”, kuma tana son zama kasa mai karfin fada aji, kamar Amurka”.

Mutum 4 sun hallaka a Togo


Masu zanga zangar sun taho-mu-gama da 'yan sandaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu zanga zangar sun taho-mu-gama da ‘yan sanda

Mutum 4 suka hallaka a Togo a zanga zangar nuna rashin amincewa da gwamnati na baya baya nan .

Masu zanga zangar sun yi artabu da jamian tsaro a Lome, babban birnin kasar da kuma garin Sokode, inda suka kafa shigaye a kan tituna.

Yan sanda sun harba hayaki ma sa hawaye domin tawartsa masu zanga zangar.

Mace macen sune alamari na baya baya nan kan gangamin da ake yi domin nuna rashin amicewa da shirin shugaba Faure Gnassingbe na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Masu zanga zangar na son ya sauka daga mulki idan wa’adinsa ya zo karshe a shekarar 2020 kuma kada ya nemi karin wa’adi biyu akan karagar mulki.

Man United ta yi wasa 12 a jere ba a doke ta ba


Champions LeagueHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wasa nma 12 da Manchester United ta yi a jere ba a doke ta ba

Manchester United ta ci Benfica daya mai ban haushi a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a Portugal a ranar Laraba.

Marcus Rashford ne ya ci kwallon a bugun tazara, bayan da mai tsaron raga ya kama tamaular a cikin ragar.

Da wannan sakamon United ta yi wasa 12 a jere ba tare da an doke ta ba, tun fara kakar kwallon kafa ta shekarar nana.

Cikin wasa 12 da ta buga ta ci 10 sannan ta yi canjaras a fafatawa biyu, daga ciki ta buga Premier takwas da wasa a kofin Zakarun Turai sau uku da karawa a League Cup.

United za ta ziyarci Huddersfield a wasan mako na tara a gasar cin kofin Premier a ranar 21 ga watan Oktoba.

Chelsea da Roma sun ci kwallo shida tsakaninsu


Champions LeagueHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallo biyun da Hazard ya ci sune na farko da ya ci wa Chelsea a bana

Karawar da aka yi tsakanin Chelsea da Roma a gasar cin kofin Zakarun Turai sun tashi 3-3 a fafatawar da suka yi a Stamford Bridge a ranar Laraba.

David Luiz ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, sai kuma Eden Hazard da ya ci biyu rigis a karawar.

Ita kuwa Roma ta fara cin kwallo ta hannun Aleksandar Kolarov daga baya shi ma Edin Dzeko ya ci biyu a fafatawar.

Daya wasan rukuni na ukun tsakanin Qarabag da Atletico Madrid tashi suka yi babu ci.

Chelsea ce ta daya a rukuni na ukun da maki bakwai, sai Roma da maki biyar, Atletico maki biyu ne da ita da kuma Qarabag mai maki daya kacal.

Barcelona ta hada maki uku a kan Olympiacos


Champions LeagueHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ta hada maki tara a wasa uku da ta buga

Barcelona ta samu maki uku rigis a gasar cin kofin Zakarun Turai, bayan da ta doke Olympiocos 3-0 a karawar da suka yi a ranar Laraba.

Barcelona ta fara cin kwallo a minti na 18 da fara tamaula bayan da Dimitris Nikolaou ya ci gida.

Bayan da aka dawo ne Lionel Messi ya kara ta biyu sannan Lucas Digne ya kara na uku, sai dai kungiyar ta kammala karawar da yan wasa 10 a fili bayan da aka bai wa Pique jan kati.

Sai dai kuma daf da za a tashi daga karawar Olympiakos ta zare kwallo daya ta hannun Dimitris Nikolaou.

Daya wasan na rukuni hudu kuwa Juventus ce ta doke Sporting da ci 2-1.

Da wannan sakamakon Barcelona ta hada maki tara sai Juventus da maki shida sai Sporting da maki uku sannan Olympiokos ta karshe wacce ba ta da maki.

Gwamnatin Saudiyya za ta hana yada Hadisan karya


Sarkin Salman na SaudiyyaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sarki Salman ya ce manyan Malamai ne daga sassan duniya za su rika sa ido

Gwamnatin Saudiyya za ta kafa wata sabuwar cibiyar addini wacce za ta hana masu tsattsauran ra’ayin Musulunci da kuma ‘yan ta’adda jirkita wasu Hadisai domin aikata danyen aiki.

Mahukunta a kasar sun ce ”yan ta’adda” na gurbata fassarar hadisan Annabi Muhammad (SAW), domin kafa hujja da su wajen munanan ayyukan da suke yi.

Sarki Salman ne ya sanya hannu kan wani kudurin dokar wanda ya bayar da damar kafa wannan cibiya.

Kuma jami’an sun ce cibiyar za ta kasance ne a birnin Madinah mai tsarki.

Za a dauki Malamai kuma masana addinin Musulunci daga sassan duniya daban daban wadanda za su jagoranci cibiyar.

Za kuma su rinka aiki tukuru domin zakulo da kawar da duk wani Hadisi da ke da alamun kage ko wanda aka sauyawa ma’ana domin kafa hujjojin tayar da fitinah.

An dade ana zargin kungiyoyin masu tayar da kayar baya kamar su Al’Qaeeda da IS wajen sauya ma’anar ayoyin Al’Kur’ani da Hadisai domin kafa hujja kan ta’asar da suke aikatawa.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kungiyar IS ta rasa mafi yawan yankunan da ta kama a kasashen Iraki da Syria

Wannan mataki na zuwa ne watanni kadan bayan ziyarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya kai kasar ta Saudiyya, inda mahukunta suka yi masa alkawarin kawo gyara a yadda suke tunkarar batun tsattsauran ra’ayi.

Wasu dai na zargin cewa wadannan sauye-sauye ba za su rasa nasaba da matsin lambar da Amurka ke wa kasar ba, na ganin ta sauya yadda take tafiyar da al’amuranta na addini.

Sai dai jami’an Saudiyya sun musanta irin wadannan zarge-zarge.

Akwai dubban Hadisai da Annabi Muhammad (SAW) ya bari, da musulmai ke ci gaba da amfani da su wajen kara fahimtar addinin.

Baya ga Al’Qur’ani mai girma, Hadisin Annabi (SAW) shi ne mafi muhimmanci a tsarin shari’ar addinin Islama, amma ana samun wasu Hadisan da ake jirkita ma’anarsu, ko kuma wadanda ba su da asali.

A don haka ne Saudiyya da sauran kasashen musulmi suka ci gaba da nuna damuwa.

Sheikh Abdulrazak Ibrahim, Limamin Masallaci Unguwar Seven Sisters a arewacin London, ya ce dokar za ta iya yin tasiri sosai.

Ya shaida wa BBC cewa “Tana da muhimmanci” ganin yadda aka ce malaman da za su kula da cibiyar za su fito ne daga kasashen Musulmi da dama.

Sai nan gaba ne za a bayyana cikakken tsarin da za a bi wurin aiwatar da cibiyar da kuma lokacin da za ta fara aiki.

Gwamnatin Saudiyya za ta hana yada Hadisan karya


Sarkin Salman na SaudiyyaImage copyright
AFP

Image caption

Sarki Salman ya ce manyan Malamai ne daga sassan duniya za su rika sa ido

Gwamnatin Saudiyya za ta kafa wata sabuwar cibiyar addini wacce za ta hana masu tsattsauran ra’ayin Musulunci da kuma ‘yan ta’adda jirkita wasu Hadisai domin aikata danyen aiki.

Mahukunta a kasar sun ce ”yan ta’adda” na gurbata fassarar hadisan Annabi Muhammad (SAW), domin kafa hujja da su wajen munanan ayyukan da suke yi.

Sarki Salman ne ya sanya hannu kan wani kudurin dokar wanda ya bayar da damar kafa wannan cibiya.

Kuma jami’an sun ce cibiyar za ta kasance ne a birnin Madinah mai tsarki.

Za a dauki Malamai kuma masana addinin Musulunci daga sassan duniya daban daban wadanda za su jagoranci cibiyar.

Za kuma su rinka aiki tukuru domin zakulo da kawar da duk wani Hadisi da ke da alamun kage ko wanda aka sauyawa ma’ana domin kafa hujjojin tayar da fitinah.

An dade ana zargin kungiyoyin masu tayar da kayar baya kamar su Al’Qaeeda da IS wajen sauya ma’anar ayoyin Al’Kur’ani da Hadisai domin kafa hujja kan ta’asar da suke aikatawa.

Image copyright
AFP

Image caption

Kungiyar IS ta rasa mafi yawan yankunan da ta kama a kasashen Iraki da Syria

Wannan mataki na zuwa ne watanni kadan bayan ziyarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya kai kasar ta Saudiyya, inda mahukunta suka yi masa alkawarin kawo gyara a yadda suke tunkarar batun tsattsauran ra’ayi.

Wasu dai na zargin cewa wadannan sauye-sauye ba za su rasa nasaba da matsin lambar da Amurka ke wa kasar ba, na ganin ta sauya yadda take tafiyar da al’amuranta na addini.

Sai dai jami’an Saudiyya sun musanta irin wadannan zarge-zarge.

Akwai dubban Hadisai da Annabi Muhammad (SAW) ya bari, da musulmai ke ci gaba da amfani da su wajen kara fahimtar addinin.

Baya ga Al’Qur’ani mai girma, Hadisin Annabi (SAW) shi ne mafi muhimmanci a tsarin shari’ar addinin Islama, amma ana samun wasu Hadisan da ake jirkita ma’anarsu, ko kuma wadanda ba su da asali.

A don haka ne Saudiyya da sauran kasashen musulmi suka ci gaba da nuna damuwa.

Sheikh Abdulrazak Ibrahim, Limamin Masallaci Unguwar Seven Sisters a arewacin London, ya ce dokar za ta iya yin tasiri sosai.

Ya shaida wa BBC cewa “Tana da muhimmanci” ganin yadda aka ce malaman da za su kula da cibiyar za su fito ne daga kasashen Musulmi da dama.

Sai nan gaba ne za a bayyana cikakken tsarin da za a bi wurin aiwatar da cibiyar da kuma lokacin da za ta fara aiki.

Senegal ta gayyaci Mane mai jinya


Senegal

Image caption

Kocin Senegal ya ce yana fatan Mane zai warke kafin fafatawar da za su yi da Afirka ta Kudu

Tawagar kwallon kafa ta Senegal ta gayyaci Sadio Mane domin ya buga mata wasan shiga gasar cin kofin duniya a watan gobe, duk da jinyar da yake yi.

Dan kwallon ya yi rauni ne a lokacin da ya buga wa Senegal wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka kece raini da Cape Verde.

Senegal za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan da za su yi gida da waje, inda fafatawar farko za suyi ne a ranar 10 ga watan Nuwamba, sannan wasa na biyu ranar 14 ga watan.

A ranar 10 ga watan Oktoba Liverpool ta tabbatar da cewar Mane zai yi jinyar mako shida.

Ba a tabbacin ranar da Mane zai dawo fagen murza-leda kuma tuni Liverpool ta kara da Manchester United da Maribor ba tare da dan kwallon ba.

An sace Turawa 'yan Mishan a Nigeria


Sojojin Najeriya cikin kwalkwale a Nija-Delta.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sojoji sun kara zafafa yakin da suke yi da tsagerun Nija-Delta.

An yi garkuwa da wasu mutum hudu da ake zargin ‘yan kasar Biritaniya ne a jihar Delta ne da ke yankin kudancin Najeriya.

Kakakin ofishin ‘yan sandan jihar Andrew Aniamaka, ya ce mutanen ‘yan mishan ne da ke zama a wani kauye a yankin, inda suke ayyukan bayar da kiwon lafiya kyauta.

Cikin wadanda aka sace din har da wasu ma’aurata, inda da misalin karfe 2:00 na daren ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka dirar musu.

Mista Aniamaka ya ce ya zuwa yanzu dai kungiyar da ke kiran kanta Karowei wadda ake zargin ta da sace mutanen, ba ta bukaci kudin fansa ba tukunna.

Basarken kauyen ya shaida wa BBC cewa ‘yan mishan din likitoci ne da suka kwashe shekara goma suna zama a kauyen.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa dai ya zamo ruwan dare a yankin na Naija-Delta mai albarkatun man fetur, kuma ‘yan sanda na zargin akwai yiwuwar lamarin wani martani ne dangane da yakin da ake yi da ta’addanci a yankin.

An sace Turawa 'yan Mishan a Nigeria


Sojojin Najeriya cikin kwalkwale a Nija-Delta.Image copyright
AFP

Image caption

Sojoji sun kara zafafa yakin da suke yi da tsagerun Nija-Delta.

An yi garkuwa da wasu mutum hudu da ake zargin ‘yan kasar Biritaniya ne a jihar Delta ne da ke yankin kudancin Najeriya.

Kakakin ofishin ‘yan sandan jihar Andrew Aniamaka, ya ce mutanen ‘yan mishan ne da ke zama a wani kauye a yankin, inda suke ayyukan bayar da kiwon lafiya kyauta.

Cikin wadanda aka sace din har da wasu ma’aurata, inda da misalin karfe 2:00 na daren ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka dirar musu.

Mista Aniamaka ya ce ya zuwa yanzu dai kungiyar da ke kiran kanta Karowei wadda ake zargin ta da sace mutanen, ba ta bukaci kudin fansa ba tukunna.

Basarken kauyen ya shaida wa BBC cewa ‘yan mishan din likitoci ne da suka kwashe shekara goma suna zama a kauyen.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa dai ya zamo ruwan dare a yankin na Naija-Delta mai albarkatun man fetur, kuma ‘yan sanda na zargin akwai yiwuwar lamarin wani martani ne dangane da yakin da ake yi da ta’addanci a yankin.

Kun san yadda ake zabar shugaban China?


Ana gudanar da babban taron jam’iyyar kwaminisanci ta China NCCPC karo na 19 .

Taro ne na manyan shugabannin jam’iyyar wadanda za su yanke hukunci kan mukaman gwamnati, kuma ana yin zaben ne sau biyu a shekara.

Yayin da ake sa ran Xi Jinping zai yi ta zarce a matsayin shugaban jam’iyyar, akwai yiwuwar cewa za a samu manyan sauye-sauye a shugabancin jam’iyyar da za su yi ritaya.

Kun san kasar da ake tono gawarwaki a yi rawa da su?


Zai zamo wani abin al’ajabi ga wasu al’ummun idan suka ji labarin yadda a wasu sassa na duniya mutane ke tono gawarwakin ‘yan uwansu tare da cashe rawa da gawarwakin.

A tsaunukan Madagaska da ke nahiyar Afirka, wannan tsohuwar al’ada ce wadda aka fi sani da “juya gawarwaki”- kuma ana shirya gagarumin biki ne don tono gawarwaki da yin rawa da su.

Babbar jami'ar hukumar zaben Kenya ta yi murabus ta tsere Amurka


Roselyn AkombaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Roselyn Akomba

A daidai lokacin da ake dakon sake babban zaben Kenya, wata babbar jami’ar hukumar zaben Kenya, Roselyn Akombe, ta yi murabus tana mai cewa kasar ba za ta iya gudanar da sahihin zabe ba a mako mai zuwa.

Roselyn ta ce hukumar zaben kasar (IEBC) tana cikin wani matsi na siyasa, kuma ba za ta iya yanke shawara ba.

Jami’ar, wadda a yanzu haka tana Amurka ne, ta shaida wa BBC cewa ta ji tsoron wani abu na iya faruwa da ita a lokacin da take Kenya saboda an yi mata barazana sosai.

A makon da ya gabata ne, shugaban ‘yan adawa, Raila Odinga, ya janye daga zaben shugaban kasar da za a sake yi ranar 26 ga watan Oktoba.

A wata sanarwa da ta fitar, Mis Akombe ta ce ta shiga cikin tsananin damuwa kan daukar matakin barin hukumar zabe ta IEBC.

“Matakin da na dauka na yin murabus zai bata wa wasun ku rai, amma ban yi hakan saboda gazawa ba.

“Na yi bakin kokarina. Wasu lokutan dole ka hakura da wasu abubuwan musamman idan akwai barazana ga rayuwa. Hukumar ta zama wani bangare na rikicin da ke faruwa yanzu haka. Hukumar na cikin rudani.

“A yadda hukumar nan take a yanzu ba za ta iya tabbatar da aiwatar da sahihin zabe ba ranar 26 ga watan Okotoba.”

Napoli ba kanwar lasa ba ce – Pep Guardiola


Manchester city beats Napoli 2-1Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester City ta doke Napol 2-1

Duk da cewar Manchester City ta doke kungiyar kwallon kafa ta Napoli 2-1 a Etihad ranar Talata a fafatawar da suka yi a wani wasan gasar zakarun Turai, kociya Pep Guardiola ya ce kungiyar ta Napoli ba kanwar lasa ba ce.

Guardiola ya jinjina wa kungiyar kwallon kafar da ke taka leda a gasar Serie A.

“Na sani kafin mu yi wasa da kuma bayan mun yi wasan cewa Napoli daya ce daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai,” in ji Guardiola.

Ya kara da cewa: “Karawar da muka yi da su daya ce daga cikin fitattun wasanni.

“Na san kungiyar da muka doke. Kungiyoyin da suka kai matakinta ba cikin sauki ake doke su ba.”

Watakila Mourinho ya koma Faransa da koci

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pep Guardiola ya ce: “Karawar da muka yi da su daya ce daga cikin fitattun wasanni.”

Rashin biyan albashi abin takaici ne – Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa akan yadda ake cigaba da samun korafe korafe kan batun albashin ma’aikata a jihohin kasar.

Shugaban ya ce abin takaice ne cewa wasu jihohi sun kasa sauke nauyin da ke kansu na biyan aklbashin ma’aikata duk da makudan kudin da gwamnatinsa ta baiwa jihohin domin su biya ma’aikata hakkokinsu.

Shugaba Buhari ya ce rabin na daure masa kai yadda ma’aikata a jihohi ke iya daukan dawainiyar iyalansu su ciyar da su, kana su biya musu kudin makaranta duk da cewa gwamnonin basa biyansu albashi a kan lokaci.

Ya kuma ce da mamaki gwamna ya iya barci duk da cewa bai biya ma’aikata albashinsu ba na tsawon watanni.

Ya ce da bukatar a sake lale domin ganin an warware matsalar.

Amma shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce lamarin ya sha karfin gwamnonin ne saboda yawancinsu sun gaji matsalolin ne daga hannun tsofaffin gwamnoni a shekarar 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wannan matsalar ta rashin biyan albashi tayi kamari a Najeriya, a inda a wasu lokutan har ta kan kashe auren wadanda lamarin ya shafa.

Masu sharhi na ganin cewa duk da wadannan matsalolin, gwamnonin kasar basu daina gudanar da rayuwa irin ta kasaita ba da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma.

Somaliya na neman agajin jini


An kasa tantance da dama daga cikin mutanen da suka hallaka a cikin harinHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An kasa tantance da dama daga cikin mutanen da suka hallaka a cikin harin

Somaliya ta yi kira ga kasashen duniya akan su taimaka mata da agajin jini domin kula da wadanda suka ji raunuka a harin bam da aka kai da wata babbar mota a Mogadishu babban birnin kasar a ranar Asabar, wanda ya hallaka mutum 281.

Ministan yadda labarai na kasar Abdirahman Osman ya shedawa BBC cewa watakila adadin wadanda suka rasu ya sake karuwa kuma ana bukatar karin taimako.

Ya ce mutum fiye da 300 ne suka ji raunuka a harin ta’aadanci mafi muni da aka kai a kasar a cikin shekara goma kuma kawo yanzu akwai gawarwwakin mutane a karkashin gine ginen da suka ruguje.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana yi wa wadanda suka ji raunuka jiny

Turkiya da Djibouti sun tura da ma’aikatan agaji zuwa kasar a ranar Litini kuma jirgin sama sojin Turkiya ya wuce da wasu mutane 40 da suka ji raunuka zuwa kasar domin a yi mu su magani.

Kasar Kenya makobciya ta nuna anniyar kwashe wasu da suka ji raunuka zuwa birnin Nairobi da jirgin sama domin a yi mu su magana.Haka daruruwan mutane sun bada gajin jini

Ana gudanar da taron jam'iyyar kwamunisanci a Beijing


A man walks past a poster featuring Chinese President Xi Jinping with a slogan reading "Chinese Dream, People"s Dream" beside a road in Beijing on 16 October 2017Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

An lika manyan allunan shugaba Xi Jinping a sassa na birnin Beijing gabanin wannan babban taron

China ta fara gudanar da taron siyasa mafi girma da muhimmanci a Beijing babban birnin kasar.

Ana sa ran cewa fiye da wakilai 2,000 ne zasu hallara, inda kuma aka inganta tsaro a babban birnin.

Ana gudanar da wannan taron a kowace shekara biyar, kuma a lokacin taron ne ake zaban wadanda suke jagorantar kasar da kuma alkiblar da zata dauka cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shugaba Xi Jinping ya zama shugaban China a shekarar 2012, kuma ana kyautata zaton zai cigaba da rike mukaminsa na babban jagoran jam’iyyar kwamunisanci mai mulkin kasar. Ya gabatar da jawabin bude wannan taron ne a gaban wakilai kimanin 2,000 daga dukkan sassa na kasar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Shugaba Xi ya fara jawabinsa ne da bayyana jadawalin cigaban da kasar China ta samu tun da ya zama shugaban kasa, kuma ya ce “tsarin kwamunisanci irin salon na China ya shiga wani sabon karni”.

Ya kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar tasu da su “cigaba da kokarin samar da rayuwa mai inganci ga al’umomin kasar”.

A lokacin wannan babban taron ne za a zabi sabbin jami’an kwamitin koli dake gudanar da kasar, wato Politburo, kana a fitar da abon jadawalin alkiblar kasar na shekara biyar masu zuwa.

Ana sa ran a kammala babban taron a cikin mako mai zuwa.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

An haramta amfani da balan-balan da na’urori masu tashi a lokacin taron

An kayata birnin na Beijing da furanni da sauran kaya masu kawatawa domin wannan bababn taron.

Amma an inganta tsaro a dukkan sassa na birnin. A farkon makon nan, an rika ganin dogayen layuka a tasoshin jiragen kasa domin binciken da jami’an tsaro kan yi ga matafiya.

Taron kolin kuma ya janyo cikas ga cibiyoyin kasuwanci, inda aka rufe wasu gidajen abinci da na motsa jiki da kulob-kulob din shakatawa domin karuwar matakan bincike.

Domin shirin tsuke baki da shugaba Xi Jinping yake aiwatarwa, da alama wakilai a wajen taron na yau zasu fuskanci raguwar kayan more rayuwa, inda wasu rahotanni daga China ke cewa otel-otel a birnin zasu rage yawan kayan alatun da za a yi amfani da su.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Masu yawon bude ido a dandalin Tiananmen sun yi wa wurin tsinke suna daukar hotuna a gaban katafaren kaya masu kayatarwa

Yawancin masu lura da al’amuran da ke kai-kawo a kasar sun tabbatar cewa shugaba Xi zai yi amfani da damar da wannan taron zai ba shi domin ya fadada ikonsa a kan jam’iyyar.

Ana sa ran jam’iyyar ta sake rubuta tsarin mulkin da ake gudanar da ita domin a sanya shirinsa a ciki – wanda zai daukaka martabar shugaba Xi ta kai na tsofaffin shugabannin da suka gabata kamar Mao Zedong da Deng Xiaoping.

China za ta haramta amfani da mota mai amfani da fetir

China na bautar da yaran Afirka wajen tallace-tallace

An yi girgizar kasa sau 2 cikin sa’o’i 24 a kasar China

Tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar, shugaba Xi ya kara karfin ikonsa a jam’iyyar, kuma ya rika daukan matakan rage cin hanci da rashawa a cikin jam’iyyar da ma sauran sassan na rayuwa, inda aka rika sa ido akan tace dukkan abubuwan da ake wallafawa, kana an rika kama lauyoyi da masu rajin kare hakkokin jama’a

A karkashin shugab Xi, an habaka shirin China na zamanantarwa da jaddada cigaban kasar inda China ke nuna matsayinta da muhimmancinta a tsakanin kasashen duniya.

Babu shakka shugaba Xi na da goyon bayan ilahirin jama’ar kasar China.

Dokar Trump ta gamu da cikas


Kotu tayi watsi da dokar da ta hana baki zuwa AHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kotu tayi watsi da dokar da ta hana baki zuwa Amurka

Wani alkali a Amurka ya dakatar da dokar shugaba Trump ta baya baya nan wadda ta hana baki daga wasu kasashe zuwa Amurka, jim kadan kafin ta soma aiki.

Dokar wadda aka sanar a watan jiya ta shafi matafiya daga kasashen Iran da Libya da Syria da kuma Yemen.

Sauran sun hada da Somaliya da Chadi da Koriya ta Arewa da kuma wasu mutane daga Venezuela.

Alkalin da ya yanke wannan hukunci a Hawaii ya ce dokar ta sabawa dokokin shige da fice na Amurka kuma bata gabatar da wata kwakwarar hujja a kan cewa mutanen da suka fito daga wadannan kasashe na musulmi shidda zasu yi barazana ga Amurka.

Fadar White House ta ce hukuncin na cike da kura kurai kuma ma’aikatar sharia ta ce za ta daukaka kara.

Shin ana yin lalata da 'yan matan Kannywood?


Kannywood

Tun bayan da badakalar yin lalata da mata ‘yan fim din Amurka, wacce ta shafi fitaccen furodusan fina-finan Hollywood, Harvey Weinstein, ta bayyana bangarorin fina-finai daban-daban na duniya ke aza alamar tambaya: shin ana samun irin wannan batu a bangarorinsu?

Fitattun jarumai mata irinsu Ashley Judd da Angelina Jolie da kuma Gwyneth Paltrow sun zargi Mr Weinstein da yin lalata da su kafin ya sanya su a cikin fina-finansa.

Jarumai mata kusan 30 ne suka fito fili suka bayyana cewa fitaccen furodusan ya yi lalata da su tun bayan da jaridar The New York Times ta soma kwarmata batun ranar biyar ga watan Oktoba.

Sai dai Mr Harvey, wanda da farko ya musanta zargin, ya ce ya yi lalatar da su ne tare da amincewarsu.

Tuni dai ‘yan sandan birnin New York da London suka soma gudanar da bincike kan lamarin.

Me ake ciki a Kannywood?

An dade ana yi wa masu yin fina-finan Kannywood kallo a matsayin mutanen da ke bata tarbiyar al’umma.

Kazalika ana yi duba na mutanen da ke aikata masha’a kamar zinace-zinace da yin luwadi da sauransu.

Sai dai sun sha musanta wannan zargi.

A shekarun baya, wani bidiyo da ya bayyana na wata tsohuwar ‘yar fim inda wani ke lalata da ita, ya jawo wa ‘yan Kannywood matukar bakin jini, lamarin da ya sa gwamnatin Kano ta wancan lokaci ta haramta yin fim a jihar.

Hukumar da ke tace fina-finai ta lokacin ta matsawa masu yin fim abin da ya kai ga durkushewar kusan daukacin masu harkar fim.

Daga baya dai al’amura sun daidaita, kuma ko da yake babu wata ‘yar fim da ta fito fili ta ce wani furodusa ko kuma babba da ke cikin harkar ya taba neman yin lalata da ita, rahotanni da dama na cewa hakan na faruwa.

Sai dai rahotannin sun nuna cewa mata ‘yan fim na jin tsoron fitowa fili su fadi abin da ke cikinsu game da zargin yi musu lalata ne saboda, a Musulince, irin wannan zargi na bukatar kwakkwarar shaida kafin a amince da shi.

Wata fitacciyar jaruma ta taba shaida min cewa manyan masu ruwa da tsaki da dama sun nemi yin lalata da ita amma ta ki yarda.

Jarumar, wacce ba ta so na ambaci sunanta, ta shaida min cewa “Wallahi mutanen da nake gani da mutunci a harkar Kannywood ba su da yawa domin kusan kowa ka ce kana son shiga fim dinsa sai ya nemi ya yi lalata da kai”.

“Zan iya ce maka Jarumi Ali Nuhu ne kawai wanda bai taba nemana da irin wannan lamari ba.”

Daya daga cikin jaruman mata, Hauwa Waraka, ta shaida wa BBC cewa ko da yake babu wani da ya taba bukatar ta yi lalata da shi kafin ya saka ta a fim dinsa, ba za ta kawar da yiwuwar cewa hakan na faruwa ba.

“Ni dai babu wanda ya taba bukatar na yi lalata da shi kuma ban san wata da ta ce wani ya taba son yin lalata da ita ba. Sai dai ka san wannan harkar kowa da halinsa ya zo, babu wanda za ka bayar da shaida a kansa”.

Ta kara da cewa: “Su matan da suke indostri din ai ba yara ba ne, ba yadda za a yi a ce za a kama a neme su da karfi, dole sai sun yarda, don haka duk abin da ki ka ga an yi a harkar nan mutum shi ya so.”

Saurari jawabin Hauwa ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kan hotonta:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Jawabin Hauwa Waraka kan ko ana lalata da ‘yan fim

Da alama wannan batu nata na da alamun gaskiya saboda wani darakta ya shaida min cewa irin badakalar da ke faruwa a Kannywood ta sa “nake janye jikina daga cikinta.”

Sai dai da BBC ta tuntubi Ali Nuhu kan wannan batu ya musanta faruwar hakan, yana mai cewa a duk shekarun da ya kwashe cikin harkokin fim din Kannywood bai taba ganin wacce ta ce an yi lalata da ita ba.

“Ni gaskiya ba taba samun wacce ta ce an yi lalata da ita kafin a sa ta a fim ba, kuma ina ganin wannan zargi ba gaskiya ba ne domin kuwa mu muna kokarin kare addini da al’adunmu ne. Akwai kwamiti da ke sanya ido kan masu neman yin lalata da ‘yan fim da ma kula da yadda muke harkokinmu”.

Saurari jawabin Ali ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kan hotonsa:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanin Ali Nuhu kan cin zarafin mata a Kannywood

Shi ma fitaccen daraktan fina-finan na Kannywood, Mallam Aminu Saira ya shaida BBC a kwanakin baya cewa bai taba neman yin lalata da mace kafin ya sanya ta a fim dinsa ba.

A cewarsa, “Wannan batu ba gaskiya ba ne; hasalima wanna ne karo na farko da aka yi min irin wannan tambayar kuma ina gani da a ce ana samun irin wannan lalata da ‘yan matan fim da suka gabata sun yi korafi. kar ka manta wasu ‘yan fim mata sun yi aure. Da a ce haka batun yake da idan wasu sun yi shiru, wasu sai sun yi magana”.

Saurari jawabin Aminu Saira ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kan hotonsa:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanin Aminu Saira kan cin zarafin mata a Kannywood

Da alama dai zarge-zargen yin lalata da kuma bata tarbiya za su ci gaba da mamaye harkokin fina-finai, ba kawai na Kannywood ba, har da na Nollywood da Bollywood da sauransu saboda yadda wadannan bangarori suka zama tamkar hatsin-bara.

Liverpool ta durawa Maribo kwallaye


Champions LeagueHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wannan ne karo na biyu da Liverpool ta ci kwallo da dama a gasar cin Kofin Zakarun Turai

Liverpool ta ci Maribo 7-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka fafata a wasan cikin rukuni na biyar.

Wannan ne kwallaye da yawa da kungiyar ta ci a tarihin gasar tun bayan shekara 10, kuma hakan ya sa tana ta daya a kan teburi tare da Spartak Moscow da maki iri daya.

Fermino da Mohamed Salah kowanne ya ci kwallo bibiyu sai Coutinho da Oxlade-Chamberlain da kuma Alexander-Arnold da kowanne ya ci dai-dai.

Liverpool ta taba cin Besiktas 8-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Daya wasan rukuni na biyar din Spartak Moscow ce ta doke Sevilla 5-1.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka yi:

 • Feyenoord Rotterdam 1 : 2 Shakhtar Donetsk
 • Apoel Nicosia 1 : 1 BV Borussia Dortmund
 • Real Madrid CF 1 : 1 Tottenham
 • AS Monaco 1 : 2 Besiktas
 • RB Leipzig 3 : 2 FC Porto
 • Spartak Moscow 5 : 1 Sevilla
 • Manchester City 2 : 1 SSC Napoli – Italy

Ko me Shugaba Buhari zai je yi a Turkiyya?


Shugaba Buhari zai gana shugaban Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

Shugaba Buhari zai gana shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Turkiyya ranar Laraba don halartar taron koli na kasashe masu tasowa wato D8 da za a fara ranar Juma’a.

Wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce gabannin taron shugaba Buhari ya samu gayyata daga shugaban Turkiyyar Recep Tayyip Erdogan don ziyarar aiki a birnin Ankara.

Sanarwar ta ce bayan gana wa da shugaban Najeriyar zai yi da shugaba Erdogan, ‘yan tawagar shugaban kasar za su tattauna da takwarorinsu na Turkiyya kan batutuwan da suka hada da tsaro, da ilimi da kuma batun ‘yan ci-rani.

Yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai je Majalisar Dokokin Turkiyya a birnin Ankara inda zai gana da kakakin Majalisar Ismail Kahraman.

Sanarwar ta kara da cewa, lokacin taron koli na kasashe masu tasowar da za’a gudanar a birnin Santanbul da cibiyar kasuwancin Turkiyyar, Shugaba Buhari zai yi amfani da damar wajen kara karfafa dangantaka tsakanin Najeriyar da sauran shugabannin kasashen da ke kungiyar.

Kasashen su ne, Bangladesh da Masar da Indonesia da Iran da kuma kasar Malaysia.

Sauran kasashen su ne, Pakistan da kuma Turkiyya mai masaukin baki.

Daga cikin ‘yan tawagar Shugaba Buhari sun hada da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati da kuma shugaban hukumar kwastam ta Najeriya, kanar Hameed Ali mai ritaya.

Ana sa ran jami’an gwamnatin Najeriya za su tabo batun kame makamai da hukumar kwastam ta yi wadanda aka shigo da su kasar daga Turkiyyar yayin tattaunawar da za su yi.

A baya-bayan nan dai hukumar kwastam ta Najeriya ta kama bindigogi 470 a tashar jiragen ruwan Tincan Island a Lagos, wadanda aka shigo da su daga kasar Turkiyya, makonni kadan da aka kama wasu fiye da 1,000 da suma aka shigo da su daga Turkiyyar.

Gwamnatin Najeriyar dai ta ce dole ta hau teburin tattauna wa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke kasar.

Wannan ne dai karo na biyu da Shugaba Buhari zai je wata kasa tun bayan dawowarsa jinyar wata uku daga Birtaniya.

Ba ruwana da ko wacce Jam'iyya – Obasanjo


Cif Obasanjo ya ce abun da ya sa gaba shi ne yadda Najeriya za ta ci gabaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Cif Obasanjo ya ce abun da ya sa gaba shi ne yadda Najeriya za ta ci gaba

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya daina shiga dumu-dumu harkar duk wata jam’iyyar siyasa a kasar.

Cif Obasanjo ya shaida wa manema labarai hakan ne jim kadan bayan ganawa da shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Markafi da suka ziyarce shi a Abeokuta.

Tsohon shugaban kasar ya ce babban abun da ya sa a gaba yanzu shi ne ganin yadda Najeriya za ta ci gaba yana mai cewa: “batun ci gaban Najeriya mutu ka raba ne”.

Ya kara da cewa Najeriya tana bukatar babbar jam’iyya mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa da za ta rika sa ido kan yadda gwamnati ke tafiya don ci gaban dimokradiyya.

Da yake tsokaci game da ganawarsa da shugabannin Jam’iyyar PDP da suka ziyarce shi, Cif Obasanjo ya ce ya shaida wa Sanata Makarfi cewa a baya ya yi PDP amma yanzu shi ba ya wata jam’iyyar inda ya jaddada cewa shi ba ya yin amai ya dawo ya lashe.

An zargi Marcelo da kin biyan haraji


Real MadridHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tun a shekarar 2013 mahukuntan Spaniya suka fara binciken Marcelo

Mahukunta a Spaniya sun zargi dan kwallon Real Madrid Marcelo da kin biyan haraji da ya kai kudi fam 436,000.

Masu shigar da kara sun alakanta rashin bin ka’ida da dan kwallon ya yi ta hanyar bude kamfani a waje da yake kula da kudin da yake samu ta fuskar tallace-tallace.

Har yanzu dai Marcelo mai shekara 29 dan kwallon tawagar Brazil, bai ce komai ba dangane da zargin da ake masa.

Shi ne dan wasa na baya-bayan nan da mahukuntan Spaniya ke zargi da kaucewa biyan haraji, bayan Messi da Neymar da Ronaldo.

Lamarin ya faro ne tun daga shekarar 2013.

Leicester ta raba gari da koci Shakespeare


Leicester CityHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Yuni Shakespeare ya karbi aikin rikon kwarya a Leicester City

Leicester City ta sallami kocinta Craig Shakespeare wata hudu bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar jan ragamar kungiyar shekara uku.

Shakespeare mai shekara 53, ya maye gurbin Claudio Ranieri a watan Fabrairu, wanda kungiyar ta kora bayan da ya kasa taka rawar gani.

Bayan da Shakespeare ya tsallakar da Leicester daga hadarin barin gasar Premier a bara ne inda kungiyar ta yi ta 12 a kan teburin gasar ya sa aka ba shi aiki a watan Yuni.

Leicester City tana ta 18 a kan teburin Premier bana, kuma ba ta ci wasa ba a karawa shida da ta yi a jere, bayan da aka buga fafatawar mako takwas a gasar.

Kocin ya ci wasa takwas daga 16 da ya ja ragamar kungiyar a bara, sannan ya kai ta wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai wacce Real Madrid ta lashe.

'Yan Madrid 19 da za su kara da Tottenham


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real ce mai kofin Zakarun Turai har guda 12 jumulla

Real Madrid za ta karbi bakuncin Tottenham a gasar cin Kofin Zakarun Turai fafatawar cikin rukuni na takwas a Bernabeu a ranar Talata.

Real da Tottenham sun kara a baya a wasannin cin kofin zakarun Turai sau hudu, kuma Real ta yi nasara a fafarawa uku.

Madrid da Tottenham sune ke kan gaba a teburin rukuni na takwas da maki shida-shida, sai Borussia Dortmund da Apoel Nicosia.

Ga jerin ‘yan wasan da za su fuskanci Tottenham

Masu tsaron raga: Navas, Casilla and Moha.

Masu tsaron baya: Ramos, Varane, Nacho, Marcelo, Theo and Achraf.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Llorente, Asensio, Isco and Ceballos.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo, Benzema and Lucas Vázquez.

An gargadi 'yan Nigeria kan zuwa asibitocin kasashen waje


Babban asibitin kasa na NajeriyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana yawan koka wa kan tabarbarewar tsarin lafiya a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bukaci likitocin kasar da su yi taka tsantsan wajen tura majinyata zuwa asibitoci da ke kasashen waje.

Hakan ya biyo bayan shawarar ofishin masu gabatar da kara a Masar na bayyana sunayen wasu asibitoci hudu da ke a Alkahira, a wata shari’a ta mutane 41 da ake zargi da fataucin kodar jama’a.

Ma’aikatar lafiya ta Najeriya ce ta fitar da wannan gargadi a wata sanarwa da ta aike wa shugaban kungiyar likitocin kasar, inda aka bayyana sunayen asibitocin.

Asibitocin sun hada da asibitin Dar-al Shafa a Helwan na birnin Al-Kahira da asibitin Al-Bashar Specialist a Faisal na birnin Giza, da cibiyar lafiya ta Al-Amal da ke Giza da kuma asibitin Dar ibn Al-Nafis a Giza.

A sanarwar da ya sanya wa hannu, ministan lafiya na Najeriya Farfesa Isaac Adewole, ya bukaci ‘yan kasar da su yi taka tsantsan sosai wajen zabar asibitin da za su dinga zuwa a kasashen waje don gudun samun kansu cikin tashin hankali.

Rahotanni na cewa daga cikin mutanen da aka sace wa koda a Masar har da ‘yan Najeriya da dama, kuma wadanda suka sace musu din na cikin wadanda aka gurfanar a gaban kotu.

Hakan ce ma tasa gwamnatin Najeriyar fitar da wannan gargadi ga ‘yan kasar da su san irin asibitocin da za su dinga zuwa a kasashen waje.

Dubban ‘yan Najeriya na tafiya kasashen waje duk shekara domin zuwa asibiti saboda rashiningantaccen tsarin lafiya a kasar.

Hakkin mallakar hoto
Isaac Adewole Twitter

Image caption

Isaac Adewole ya yi kira ga likitoci da su dinga bai wa ‘yan kasar masu son zuwa asibiti a wasu kasashe shawara

An fara taro kan harkar noma a London


A ranar Talata ne aka fara wani taro kan aikin noma a birnin Landan, wanda ofishin jakadancin Birtaniya da ke Najeria ya shirya.

Taron dai zai yi nazari a kan yadda masu zuba jari daga kasashen waje za su shiga a dama dasu a fannin ayyukan noma a Najeriya.

Gwamnan jihar Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello na daga cikin wadanda ke halatar taron, kuma ya tattauan da Aliyu Abdullahi Tanko ya yin wata ziyara a ofishinmu dake Landan.

Biafra: Nnamdi Kanu ya ki halartar zaman kotu


Nnamdi kanuHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Afrilu ne aka bayar da Nnamdi Kanu beli bayan ya shafe wata 18 a tsare.

Shugaban kungiyar ‘yan ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya ki bayyana a gaban kotun tarayya da ke Abuja a shari’ar da ake yi masa kan zargin cin aamanar kasa.

Lauyan Mista Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya ce bai sani ba ko mutumin da ya ke karewa ya mutu ko kuma yana raye ba.

Ya ce tun da aka kai samame gidan da Mista Kanu yake zaune a watwan Satumba ba su sake ganinshi ba.

Sai dai lauyan gwamnati ya nemi a dage shari’ar tun da dai lauyan Kanu ba zai iya gabatar da shi ba.

Wakilin BBC a kotun, Ishaq Khalid, ya ce tun bayan da aka bude zaman kotu a ke ta tafka muhawara kan wannan batu.

Lauyan gwamnati ya kuma nemi a janye belin da kotu bai wa Mista Kanu tare da bayar da umarnin kama shi tun da dai bai bayyana a kotun ba.

A watan Afrilu ne aka bayar da Mista Kanu bayan ya shafe wata 18 a tsare.

Ba a dai sake ganisa a bainar jama’a ba tun bayan rikicin da aka yi tsakanin jami’an tsaro da magoya bayansa a watan Satumba.

Zinedine Zidane ya jinjina wa Harry Kane


Zinedine Zidane says Harry Kane is a complete playerHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon dan wasan tsakiyar Real Madrid da Juventus da kuma Faransa, Zinedine Zidane ya ksance daya daga cikin gwanayen ‘yan wasa a zamanin da yake taka leda

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane, ya bayyana dan wasan Tottenham, Harry Kane, a matsayin cikakken dan wasa kafin kungiyoyin wasan biyu su hadu a wasan gasar zakarun Turai ranar Talata.

Amman Zidane ya ki ya yi tsokaci kan ko zakarun Spaniyan za su sayi dan wasan gaban mai shekara 24.

Dan wasan Ingilan ya ci kwallaye 43 a wasanni 38 ga kungiyar kwallon kafarsa da kuma kasarsa a shekarar 2017.

“Yana da kyau ta ko ina, kuma ko da yaushe yana tunanin cin kwallo ne cikin ko wanne hali ,” in ji Zidane, mai shekara 45.

Macizai na sarar fiye da mutum miliyan biyar duk shekara – WHO


Macizai

Image caption

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da macijin ke barna sosai

Mutane kimanin miliyan biyar da dubu dari hudu ne dai maciji kan sara a duk shekara a duniya, adadin wadanda kan rasa rayukansu kuma ya kama daga 91,000 zuwa 130,000 kan rasa rayukansu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta bayyana.

Akwai kuma mutane da dama da ke rasa gabbansu da kuma nakasa sanadiyyar saran macijizai. Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da macijin ke barna sosai.

BBC ta ziyarci yankin Kaltungo da ke jihar Gombe, daya daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari a Najeriya.

Al’umomi da dama a kasar dai na rayuwa ne kullum cikin fargaba saboda da matsalar sarar majici, musamman yanzu da damina zuwa kaka.

Manoma da kuma kananan yara ne matsalar ta fi shafa.

Image caption

Macizan sun zama kamar tsumagiyar kan hanya fyade yaro, fyade babba

Da dama daga cikinsu akan kai su asibitin jinyar sarar maciji ne da ke garin Kaltungo, daya daga cikin cibiyoyi kalilan na musamman domin jinyar sarar maciji a kasar

An kawo wata yarinya mai suna Haraja, mai shekaru goma sha shida wannan asibiti a sume, kwana hudu bayan da maciji ya sare ta.

Cikin kasa da sa’o’i ashirin da hudu daga bisani kuma budurwar ta rasu.

Daga nan ne sai aka yi jana’izarta a wata makabarta da ke kusa da asibitin.

Kawunta mai suna Abubakar Muhammmad, ya shaida wa BBC cewa rashin kudin zuwa asibiti ne ya sanya jinkiri kai ta cibiyar ta sarar maciji.

Kubuwa ce ta fi kai wa mutanen wannan yankin farmaki, inda take sararsu ba babba, ba yaro.

Wata dattijuwa mai suna Misis Trihana Yayinus, wadda take kwance a gadon asibitin, ta shaida wa BBC cewa ta sha azaba a wajen kubuwa domin kwananta uku a sume bayan ta ya sare ta a gona.

Wata babbar matsalar dai ita ce yadda wadanda macijin kan sara ba sa samun magani yadda ya kamata.

Ba a yin maganin a Najeriya amma akan shigo da maganin ne daga kasar Birtaniya da kuma yankin kudancin Amurka bayan an kai samfurin macizan da kuma dafin daga Najeriya.

Wasu lokuta dai magani kan kare karkaf a cibiyar ta Kaltungo, amma a kullum marasa lafiya sai kwarara suke yi domin neman maganin.

Image caption

Kubuwa ce ta fi kai wa mutanen wannan yankin farmaki

Ko baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma wasu dubban a wasu yankuna na Najeriya wadanda macijin kan sara a duk shekara.

Kuma masana na cewa samar da magani a kan kari da kuma kai duk wanda maciji ya sara asibiti da wuri za su taimaka matuka wajen rage yawan mace-macen.

Hakan kuma zai kawo karshen wahalar da daya daga cikin halittu mafiya hadari a duniya ke haddasawa.

Mata na cikin hadari a Alkahira babban birnin Masar


Masu rajin kare hakkin mata sun ce mata na rayuwa cikin wahala a Alkahira

Image caption

Masu rajin kare hakkin mata sun ce mata na rayuwa cikin wahala a Alkahira

An bayyana Alkahira babban birnin Masar a matsayin birnin da ya fi hadari ga mata.

An gano haka ne daga kuriar jin ra’ayoyin jama’ar duniya ta farko da aka yi, a kan yadda mata suke rayuwa a cikin birane masu mazauna fiye da miliyan 10.

An gudanar da binciken ne a birane 19 inda aka yi wa kwararu kan harkar mata tambayoyi kan kariyar da ake basu kan batun da shafi cin zarafi.

Kuriar ta bayyana Landan a matsayin birnin da mata ba sa fuskantar takura ,kuma Tokyo da Paris na binsa a baya.

Magajin garin Landan Sadiq Khan ya ce mata na tasiri sosai a fanoni da dama a Landan, ciki har da ma’aikatun gwamnati da kasuwanci da kuma siyasa.

Masu rajin kare hakkin mata a Alkahira sun dora alhaki kan wasu al’adu da aka dade ana amfani da su dagane da wariyar da ake nuna masu. Haka kuma ba bu isassun asibitoci masu inganci na mata , kuma suna fuskantar matsalar rashin kudi da kuma ilimi.

Birnin Karachi na Pakistan da Kinshasa na Jamhuriyar dimukradiyar Congo da Delhi na India sune suke bayan birnin Alkahira a binciken da gidauniyar Thomson Reuters ta yi.

Yadda harin bam ya kashe yarinya ana gobe za ta zama likita


Maryam AbdullahiHakkin mallakar hoto
Anfa’a Abdullahi

Image caption

Maryam Abdullahi ta mutu a gobe za ta zama likita

Ana gobe Maryam Abdullahi za ta kammala karatun aikin likita ne harin bam mafi muni a tarihin kasar Somaliya ya yi ajalinta.

‘Yar uwar Maryam Abdullah, Anfa’a, ta shaida wa BBC cewa lamarin ya kidimata “kwarai da gaske”.

“‘Yan uwanmu sun girgiza sosai, musamman mahaifinmu wanda ya taho Mogadishi daga birnin Landan domin ya halarci bikin yayeta, amman maimakon hakan sai ya halarci jana’izarta.”

Anfa’a ta ce ta yi magana da ‘yar uwarta minti 20 kafin fashewar bam din da ya kashe daruruwan mutane ranar Asabar.

“A wanna lokacin tana cikin asibitin Banadir Hospital inda take aiki. Ta gaya min tana jiran wasu fayel-fayel daga asibiti.” Daga nan sai ta dauki alkawarin da Ubangiji bai ba ta ikon ciwa ba, “zan kira ki zuwa an jima,” in ji marigayiyar.

Hakkin mallakar hoto
Anfa’a Abdullahi

Wani wakilin Sashen Somali na BBC a wajen da lamarin ya auku ya ce Otel din Safari ya rufta kuma mutane da dama sun makale a barazugan ginin.

Wani shaida da ke zaune a birnin, Muhidin Ali, ya shaida wa AFP cewa ita ce “fashewa mafi girma da na taba gani, ta daidaita wajen gaba daya”.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An kai wa Mogadishu hare-hare masu yawa a baya, amman wanna ne hari mafi muni a tarihin birnin

Hakazalika, daraktan asibitin Madina Hospital, Mohamed Yusuf Hassan, ya ce matakin harin ya tayar mishi hankali.

“Abin da ya faru jiya ya wuce hankali, ban taba ganin irin wannan ba, mutane da dama sun rasa rayukansu, gawarwaki sun kone kurmus.”

An kashe jagoran IS na yankin Asia


The military had spent years trying to find militant Isnilon HapilonHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sojin sun shafe shekaru suna fafutukar neman Isnilon Hapilon ruwa a jallo

Dakarun soji a kudancin Philippines sun ce sun kashe Isnilon Hapilon, wanda aka fi sani da Abu Sayyaf kuma jagoran mayakan IS a kudu maso gabashin Asiya.

Sojoji sun ce an kashe Hapilon wanda ke cikin jerin ‘yan ta’adda da Amurka ke nema ruwa a jallo ne a Marawi tare da wani dan ta’adda mai suna Omar Maute.

Wani yanki na birnin ya na karkashin ikon mayakan ne tun lokacin da aka kai wani mummunan hari a watan Mayu.

An samu rahotanni kashe mayakan ne yayin da dakarun soji ke kara kaimi don kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa da mayakan.

Yankin ya kasance tamkar sansani ga kungiyoyin masu kaifin kishin Islama, wadanda da dama daga cikin su suka kafa kungiyar IS a shekarun baya-bayan nan.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An shafe watanni ana yaki a Birnin Marawi

Janaral Ano ya ce har yanzu dakarun sojin na yaki da mayakan IS da dama a yankin, kuma sun ceto kimamin mutum 20 da aka yi garkuwa da su.

Ya kara da cewa kwararru da kuma tsofaffin mayakan ne suka tabbatar da gawar shugabannin mayakan biyu.

Sakataren tsaro Delfin Lorenzana ya shaida wa manema labarai cewa bayan an bayar da rahoton mutuwar Hapilon, za su bayar da sanarwar takaita zirga-zirga a yankin na tsawon kwana biyu.

Ya kara da cewa, yanzu dai ana ci gaba yi wa gawar mutanen biyu bincike don tabbatar da kwayoyin halittar su.

Mutum uku ne suka kamu da cutar kyandar biri a Nigeria – WHO


Kimanin shakaru 40 ke nan rabon da Najeriya ta samu afkuwar cutar.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kimanin shakaru 40 ke nan rabon da Najeriya ta samu afkuwar cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa mutum uku ne suka kamu da cutar kyandar biri a Najeriya.

Professor Isaac Odewole, Ministan Lafiya na Najeriya ya ce a cikin mutum 43 da ake zargin sun kamu da cutar kyandar biri, mutum uku ne kawai aka tabbatar sun kamu da cutar.

Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai biyo bayan gwaje-gwajen da hukumar WHO ta yi a birnin Dakar a kasar Senegal.

A makon jiya an samu bulluwar cutar ne a jihohi takwas ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Kimanin shakaru 40 ke nan rabon da Najeriya ta samu afkuwar cutar.

Cutar ta samo asali ne daga jikin biri da sauran dabbobin kamar su bera da kurege da barewa.

Nigeria: An kashe mutum 35 a jihar Filato


An sha samun rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci a jihar Filato

Image caption

An sha samun rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci a jihar Filato

Akalla mutum 35 aka kashe yayin da aka jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Wasu ‘yan bingida ne dai suka kai hare-haren a ranakun Lahadi da kuma Litinin, inda suka lalata gidaje da dama.

Rahotanni sun ce hukumomi sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin inda aka tura karin jami’an tsaro.

A halin yanzu manyan jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Filato suna tattauna yadda za a kawo karshen tashe tashen hankula.

Mutane da dama ne suka mutu a ‘yan shekaru baya a tashe tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini a jihar.

Sai dai a ‘yan watannin baya, an samu kwanciyar hankali a jihar bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da bangarorin da ke rikici da juna.

Kenya: 'Yan sandan sun 'kashe' masu zanga-zanga 30


Wadansu masu zanga-zangaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A cikin watan nan ne za a sake gudanar da zaben shugaban kasar bayan soke wanda aka yi a watan Agustan da ya wuce

Akalla mutum 30 ake zargin ‘yan sanda sun kashe a birnin Nairobi na kasar Kenya, yayin wata zanga-zanga da ‘yan adawa suka yi.

A wani sabon rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar ta ce ‘yan sandan kasar ”suna da hannu dumu-dumu”.

Har ila yau, akwai wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba wadanda suke cewa ‘yan sandan sun kashe wadansu mutum 17 a birnin.

Sun na zargin ‘yan sandan da tayar da zaune tsaye ta amfani da karfin da ya wuce kima a yankunan da ake tunani cewa ana tashin hankali.

Kungiyar ta ce ‘yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima ne a wuraren da ake zaton rikici.

A makon da ya gabata ne jagoran ‘yan adwar kasar, Raila Odinga, ya ce ba zai shiga zaben sugaban kasa da za’a sake yi a cikin wannan watan.

Saboda ba shi da imanin cewa za a yi zabe adalci a zabe, a cewarsa.

Shugaba Buhari ya gana da yara masoyansa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da yaranHakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar farin cikin ganawa da yaran a fadarsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wadansu yara uku mata kanana wadanda ake cewa masoyan shugaban ne a fadarsa da ke Abuja.

Nicole Benson ‘yar shekara 12 wadda ta fito daga jihar Legas, sai Maya Jamal ‘yar shekara uku wadda take zaune a Abuja da kuma Aisha Gebbi mai shekara 10 wadda ta fito daga jihar Bauchi sun isa fadar ne tare da rakiyar iyayensu.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/Bashir Ahmad

Image caption

Maya mai shekara uku, ta isa fadar shugaban ne tare da mahaifinta

Yaran sun kwashe kimanin minti 30 a fadar shugaban kasar.

Kafofin yada labaran kasar sun sha ruwaito labarin daya daga cikin yaran wato Nicole a lokacin zaben shekarar 2015, inda suka ce ta taba tallafa wa shugaban da kudin abincinta.

Ba kasafai dai ake ganin shugaban yana ganawa da kananan yara ba.

Karanta karin wadansu labaran masu kayatarwa

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Aisha ‘yar shekara 10 tana karbar kyautar daga hannun Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Nicole ‘yar shekara 12 ta taba tallafa wa shugaban da kudi yayin da yake yakin neman zabe a shekarar 2015

Jesus ne matashin dan kwallo mafi kwazo bayan Messi


Jesus ya maye gurbin Messi a Man City

Image caption

Jesus ya maye gurbin Messi a Man City

Gabriel Jesus wanda ya ci kwallo biyu a wasan da suka buga da Stoke, “shi ne matashin dan kwallo mafi kwazo wanda ba a samu kamarsa ba tun bayan Messi, in ji Danny Murphy.

Tsohon dan wasan Ingila, Murphy, ya shaida wa BBC cewa bayan Lionel Messi, bai sake ganin wani matashin dan kwallo da ke taka leda kamar Jesus ba.

Manchester City ce kungiyar da take samun tagomashi kawo yanzu a bana, inda ta zazzaga wa Stoke kwallo bakwai a karawar da suka yi.

Kuma ita ce kungiyar da take jan ragama a teburin firimiya a yanzu inda ta bai wa Manchester United tazarar maki biyu.

Kawo yanzu City ta ci kwallo 29 a cikin mako takwas na fara wasan kakar bana, rabon da a samu irin wannan tun wasan da Everton ta yi a kakar 1894-95.

Gabriel Jesus, dan kasar Brazil, na haskakawa sosai tun bayan da ya koma City a kakar bara.

Tuni ya ci kwallo bakwai a wasa 11 da ya bugawa kasar.

A yauzu dai za a zuba ido a ga irin rawar da zai taka nan gaba a rayuwarsa, domin taka sahun Messi a fagen tamola ba karamin aiki ba ne.

Mutum-mutumin Zuma: Okrocha na shan suka


ZumaHakkin mallakar hoto
Twiitter

Gwamnatin jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta karrama Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta hanyar gina mutum-mutuminsa na tagulla tare da sanya wa wani titi sunansa.

Haka kuma an bai wa Mista Zuma wata sarautar gargajiya da kuma lambar yabo mafi girma a yankin, a yayin wata ziyara da ya kai jihar ta Imo a ranakun Asabar da Lahadi da ta wuce.

Sai dai hadakar kungiyar fararen hula na The Civil Society Network Against Corruption, a kasar ta yi tur da wannan girmamawar.

Haka kuma hadakar da ke da kungiyoyi 150 a karkashinta ta yi Allah-wadai da gwamnan jihar, Rochas Okorocha saboda yadda ya nuna Mista Zuma a matsayin wani gwarzo ga “matasan Afirka” duk kuwa da cewa an kwashe shekaru kusan goma ana zarginsa da aikata cinhanci da rashawa.

Sanawar da ta fitar ta dora ayar tambaya kamar haka:

“Shin gwamna Okorocha bai san cewa mutanen Afirka ta Kudu na neman Zuma ya sauka daga shugabancin kasar ba ne a halin yanzu, saboda abin kunyar da ya janyo musu da kuma tozarta kasar Nelson Mandela?”

Karramawar dai ta zo ne ‘yan kwanaki bayan kisan wata ‘yar Najeriya, Jelili Omoyele, mai shekaru 35 a Afirka ta Kudu.

Masu amfani dandalin sada zumunta na Twitter da dama ne suka bayyana mamakinsu a kan batun kamar haka:

Hakkin mallakar hoto
Twitter

Image caption

“An yi wani mutum-mutumin Jacob Zuma a Najeriya. Ban taba tunanin cewa Najeriya kasa ce mara alkibla ba,” in ji shi.

Yayin da muke murna da hukuncin da aka yanke a kan muryoyin da aka nada, muna fatan ganin Zuma ya sauka, sai gashi a Najeriya ana karrama shi.

With hundreds of counts of corruption charges against him, Jacob Zuma, somewhere in Nigeria 🇳🇬 stands as a deity. The gods must be crazy.

Jacob Zuma na fuskantar daruruwan zarge-zargen cin hanci da rashawa, sai gashi can a Najeriya, ana masa kallon wani abin girmamawa. Abincin wani gubar wani

Hakkin mallakar hoto
Twitter/ Made In Ibadan

Malami: Menene sakarci?

Ni: Rochas Okorocha ya kashe miliyan 520 wajen gina mutum-mutumin shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma a jihar Imo ta Najeriya, kamar yadda aka bayyana a sakon Twitter da ke sama

George Weah ya kai zagaye na biyu a zaben Laberiya


george WeahHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

George Weah ya samu kashi 39 cikin 100 na kuri’un da aka kada

Tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar Laberiya, George Weah, zai fafata da mataimakin shugaban kasar, Joseph Boakai, a zageye na biyu na zaben shugaban kasar.

Hukumar zaben kasar ta ce ta kammala kidayan kusan dukkannin kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar Talatar da ta wuce.

Mista Weah, wanda shi ne dan wasan kwallon kafar Afirka da ya taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya, ya samu kashi 39 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Shi kuma Mista Boakai ya samu kaso 29 cikin 100.

Ana sa ran a watan gobe ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben.

‘Yan takara 20 ne suka fafata a zagayen farko na zaben domin maye gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf, wadda ita ce shugabar kasa mace ta farko a nahiyar Afirka.

Sai dai har yanzu akwai wuraren da ba a kammala kidaya kuri’unsu ba.

Duka ‘yan takarar biyu da suke kan gaba sun yi tsammanin lashe zaben a zagayen farko.

Abin da ya sa har tsohon kocin Mista Weah wato Arsene Wenger, ya yi hanzarin taya shi murnar lashe zaben bayan samun wadansu rahotannin bogi wadanda suka ce dan wasan ne ya lashe zaben.

Mika filayen jiragen Najeriya ba dabara ba ce


Murtala Mohammed Airport, Lagos NigeriaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Kwararu da masu ruwa tsaki na ci gaba da nuna damuwa kan aniyyar gwamnatin Najeria, na mika filayen jiragen sama Abuja da na Lagos ga yan kasuwa.

Lamarin dai ya janyo suka daga ma’aikatan hukumar kula da gudanarwa filayen jiragen kasa watau FAAN.

Enjiniya Muhammad Sani Baba, tsohon shugaban hukumar ta FAAN ne kuma ya bayyana irin illar da mika filayen biyu ga ‘yan kasuwa zai yi ga gwamnati da kuma ma’aikata:

“Wadannan filayen jirgin sama guda biyu da ake magana a kansu, sune jigo dake rike sauran kananan filayen jirgin saman guda 18”, inji Enjiniya Muhammad.

Ya kara da cewa “Kaga idan ka dauke jigogin guda biyu ka ba wa ‘yan kasuwa, kabar gwamnati da sauran guda 18, wadanda basa kawo kudi wadanda kuma ana ciyar da su ne domin a gudanar da tsarin baki daya”.

Ya kuma bayyana cewa a karkashi wannan tsarin, kananan filayen ne ke tura jiragen daya ko biyu a kowane yini zuwa Legas, wanda shi ke sa filin na Legas ya sami kimanin jirage masu sauka guda 40 a kowane yini.

Ya ce idan aka dauki manyan filayen na Legas da Abuja aka mika su ga ‘yan kasuwa, za a daina raba kudaden da ake samu daga ayyukan da suke yi tare da kananan filayen. Wannan zai iya kawo koma bayan da ka iya gurgunta ayyukan sufurin jiragen sama gaba daya.

Da aka sanar da shi cewa kasashen da suka cigaba na gudanar da irin wannan tsarin ne na mika filayen jirgin samansu ga ‘yan kasuwa, sai ya ce sam ba haka batun yake ba:

“Ba haka bane. Bari in baka labarin kasar Ostreliya, nan wurinmu suka zo suka koyi tsarin. Indiya ma nan wurinmu suka zo suka koyi tsarin. Indiya suna da filayen jirgin sama 100, kuma a wurinmu suka koyi tarin gudanar dasu,” inji shi.

An kaddamar da shirin Mata 100 na BBC


BBC 100 womenHakkin mallakar hoto
Getty Images

A yau Litinin ne ake kaddamar shirye-shiryen mata dari da BBC ke yi a kowace shekara.

A wannan makon rahotannin za su mayar da hankali kan tsaron lafiyar mata a cikin ababen hawa kamar motoci, jiragen kasa da jiragen sama.

Hajiya Binta Shehu Bamalli, ita ce shugabar kungiyar Sure Start Initiative kuma ta yi ma BBC bayani akan kalubalen da mata suke fuskanta.

“Zan bada misali da kasar Indiya, inda zaka taras cewa a cikin jiragn kasa, ana ware wasu kujeri domin mata. Maza kan zauna a kan kujerian, amma da zarar wata mace ta shiga jirgin, sai kaga wani ya tashi ya bata kujerar,” inji Hajiya Binta Shehu Bamalli.

Ta kara da cewa “Hakazalika a cikin jiragen na kasa, akwai wadanda maza ba sa shiga, domin an ware su domin mata ne kawai.”

Sai dai Hajiya Binta Bamalli ta ce a kasarta Najeriya, akwai sauran aiki ga mahukunta wajen daukar matakan kare matan:

“Tun daga filin jirgin sama zuwa tashar jirgin kasa har ma zuwa tashar mota, gaskiya bamu da irin wannan tsarin a Najeriya.”

Ta kuma bayyana”A misali, lokacin da aka fara a Daidaita Sahu a Kano, mata ne kadai ke shiga ababen hawan da aka kebe musu, amma yanzu zaka taras maza sun mamaye ababen hawan.”

An raba 'yan biyu da aka haifa a hade


JACKLYN REIERSON, MAFHakkin mallakar hoto
JACKLYN REIERSON, MAF

An yi wa ‘yan biyu jarirai aikin tiyata.

An raba wasu ‘yan biyu da aka haifa a hade a wurin cibiya a wani kauye me nisan gaske, a jamhuriyar Dimukradiyar Congo, bayan da suka shafe sa’oi 15 kan babur domin a yi masu aikin tiyata. An dai wuce da su Kinshasa babban birnin kasar, inda wasu likitoci suka yi masu aiki. Jariran mata masu suna Anick da Destin zasu koma kauyensu nanda makwanni 3 masu zuwa.

A Watan Augusta ne aka haifesu , suna da makwanni 37 kuma sun hade a wurin cibiya.Likitoci sun ji mamakin cewa mahaifiyarsu ta haihu ne a gida a kauyen Muzombo da ke yammacin kasar. Iyayen jariran, Claudine Mukhena da Zaiko Munzadi suka kai su wani asibiti dake kusa da kauyensu.

Hakkin mallakar hoto
JACKLYN REIERSON, MAF

Sai dai rashin kayan aiki da kuma kwarewar ma’aikata ya sa likitocin sun wuce da su zuwa asibitin Kinshasha mai nisan mile 300.

Dr Junior Mudji da ke kula da jariran a asibitin Vanga Evangelican ya ce yana farinciki. Ya ce ba kasafai ake samun jarirai ‘yan biyu yan makwanni talatin da bakwai ba, da aka haifa a hade a gida .

Ya ce zasu cigaba da zama a asibiti har na tsawon makwanni uku domin a tabattar komai na tafiya dai-dai.

Dr Mudji ya yi ammanar cewa wannan shi ne karon farko da aka raba yan biyu da aka haifa a hade a jamhuriyar dimukradiyar Congo

CHAN: An bai wa Morocco karbar bakunci


cafHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

CAF, ta karbe izinin daga hannun Kenya wacce ta ce ta kasa shirye-shiryen bakuncin wasannin na CHAN

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta bai wa Morocco damar karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta ‘yan wasan da suke taka-leda a nahiyar wato CHAN.

A ranar Lahadi hukumar ta amince ta bai wa Morocco damar karbar bakuncin wasannin maimakon Equatorial Guinea wacce ita ma ta yi takara.

Moroccon ta maye gurbin Kenya wacce hukumar kwallon kafar Afirka ta ce kasar ta kasa shirye-shiryen karbar bakuncin wasannin kamar yadda ya kamata.

Ana gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta ‘yan wasan da ke buga tamaula a nahiyar tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairun 2018.

Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya


Wasu zababbun hotunan al’amuran da suka faru a Afirka makon nan.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Wadansu yara a Somaliya na shafe lokaci don watayawa ranar Juma’a, inda suke wasa da ninkaya a wata korama a tsohon wani gini a gundumar Hamarweyne da ke birnin Mogadishu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

A ranar Asabar ne wani ya yi kwalliya da kayan gargajiya a Afirka ta Kudu kafin fara wasa tsakanin Springboks da New Zealand.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Wani bangare a wurin da aka yi wata mummunar gobara a babban birnin Ghana wato Accra, bayan da wata tankar gas ta kama da wuta ranar Asabar.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Bikin nuna kayan ado da aka yi a birnin Abidjan da ke kasar Ivory Coast.

Hakkin mallakar hoto
EPA

A ranar Lahadi ne aka yi makon tallan kayan kawa na mata inda Nadir Tati take tafiyar rausaya da kwalisa a wurin.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

A ranar Lahadi ne aka yi wasa mai daukar hankali na neman shiga gasar cin kofin duniya tsakanin Masar da Congo Brazzaville a filin wasa na Borg El Arab a birnin Alexandria na kasar Masar.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Wadansu magoya bayan kasar Masar bayan an tashi wasan da kasarsu ta doke Congo da ci 2-1.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Mohamed el-Morabity na kasar Morocco yayin da yake wanke fuskarsa da ruwa bayan da ya yi gudu. Wasu masu wasan tsalle-tsalle da guje-guje suna shafe kwanakin karshen mako suna gudun kilomita 100 a hamadar Tunisiya.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Washegarin ranar da aka yi zaben Laberiya, inda magoya bayan Georgia Weah na jam’iyyar hadin gwiwa ke sauraron rediyo don jin wanda ya lashe gasar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

‘Yan sanda masu kwantar da tarzoma yayin da suka tsaya a gaban magoya bayan jam’iyyar adawa ta Kenya (Nasa) lokacin wata zanga-zanga a Nairobi ranar Laraba.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

An saka doka da kuma sa ido a kan magoya bayan Shugaban Kasar Uhuru Kenyatta.

Hakkin mallakar hoto
EPA

A ranar Laraba ne aka dauki hoton aikin wani aiki a birnin Johannesburg, inda aka nuna mutane suna kewaya birnin da kuma gabatar da mai yin fenti.

Hakkin mallakar hoto
EPA

A ranar Alhamis ne wasu masu rawa suka shirya tsaf domin shiga filin rawa a lokacin da suka gama bita.

Federer ya doke Nadal ya ci gasar Shanghai


Kwallon tennisHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Federer ne ya ci gasar kwallon tennis ta kwararru da aka kammala a Shanghai

Roger Federer ya doke Rafael Nadal ya kuma lashe gasar kwararru ta Shanghai, kuma kofi na shida da ya ci a shekarar nan.

Federer mai shekara 36, wanda sau hudu ya yi rashin nasara a 2017, ya doke Nadal ne da ci 6-4 da 6-3 a cikin minti 72 da suka fafata.

Kuma wannan ce nasara ta hudu da ya yi a kan Nadal, kuma ta biyar a jere a karawa da suka yi a wasanni daban-daban, jumulla ya ci 23 shi kuwa Nadal ya yi nasara 13.

Federer ya yi kan-kan-kan da Ivan Lendl wajen lashe gasa, kuma dan Amurka Jimmy Connors ne ke kan gaba da yawan lashe kofi 109

Watakila Mourinho ya koma Faransa da koci


Manchester UnitedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mourinho ya ci League Cup da kofin Europa a kakar farko a Manchester United

Koci Jose Mourinho ya ce ba ya jin cewar a Manchester United zai kawo karshen aikinsa na horar da tamaula.

Mourinho mai shekara 54, wanda ke shekara ta biyu a yarjejeniyar da ya kulla da United, bai taba yin kaka hudu ba a kungiyoyi bakwai da ya jagoranta.

A lokacin da ake hira da shi a wani gidan takabijin a Faransa, Mourinho ya ce Paris St-Germain kungiya ce mai kyau.

Ya kara da cewa, ”Ni koci ne mai buri da son yin wani abun sabo”.

Mourinho, wanda tsohon kocin Chelsea da Real Madrid da Inter Milan da kuma Porto ne, ya shaida wa TF1 Telefoot cewar ba ya jin zai yi ritaya a Manchester United.

Kocin, wanda ya ci League Cup da kofin Zakarun Turai na Europa a farkon kakar da ya jagoranci United, ya ce akwai wani abu na musamman a Faransa, kamar inganci da matasa.

Real ta kafa tarihin cin wasa 13 a waje a La Liga


Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid tana da maki 17 a wasa takwas da ta buga a gasar La Liga

Kungiyar Real Madrid ta kafa tarihin cin wasa 13 a jere da ta buga a waje a gasar La Liga, bayan da ta doke Getafe a wasan mako na takwas a ranar Asabar.

Real ta doke Getafe 2-1 kuma Karim Benzema ne ya ci kwallon farko kafin aje hutu, sannan ta kara ta biyu ta hannun Cristiano Ronaldo.

Da wannan sakamakon Real ta doke tarihin cin wasan waje 12 da Barcelona ta kafa a karkashin jagorancin Pep Guardiola a kakar 2009/10 ta ci wasa biyu sannan ta ci 10 a 2010/11 .

Wannan kuma ba shi ne karon farko da Madrid ta doke tarihin da Barcelona ta kafa ba, inda Madrid ta yi wasa 40 a jere ba a doke ta ba, bayan da Barcelona ta yi 33 a baya.

Real ta ziyarci Villarreal a ranar 26 ga watan Fabrairun 2016 ta kuma doke ta 3-2, tun daga lokacin ta dunga cin wasannin La Liga da ta yi a waje zuwa yanzu jumulla ta ci 13..

Damben da Bala ya buge Aminun Langa-Langa


Daya daga fafatawa bakwai da aka dambata a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria.

A wasan ne kuma Bahagon Dan Sama’ila daga Kudu ya buge Bahagon Shamsu daga Arewa a turmi na biyu.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton:

Sauran wasannin da aka yi canjaras kuwa

Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa da Shagon Dogon Auta daga Kudu

Garkuwan Mahautan Karmu daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu

Garkuwan Garba Dan Malumfashi daga Arewa da Shagon Dogon Jafaru daga Kudu

Sani Mai Kifi daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu

Shagon Fanteka daga Kudu da Sani Mai Kifi daga Arewa

Yadda aure ke sauya mutane a tsawon rayuwa


Ma'aurataHakkin mallakar hoto
United Archives GmbH / Alamy Stock Photo

“Wane dalili ya sa ake da dimbin mata masu shekaru talatin da doriya da ba su da aure a kwanakin nan Bridget?”

A dakin taron walima na shirin kundin Bridget Jone wanda ya yi matukar sabo da kowane rukunin mutane da suka saba haduwa da su, a kebe, kewaye da abokai masu aure a daki guda.

Duk da cewa masana aikin kwakwalwa ba su samu cikakkiyar fahimtar da za ta tabbatar da cewa ko aure na sanya wa mutane natsuwa da gamsuwa.

Kamar kawayen Bridget ko kuma ana ingiza mutane ne kawai su ji suna son yin aure.

Bincike ya nuna cewa wadanda suka jajirce wajen haduwa don zaman rayuwa da wani mutum hakika suna samun sauyi da kimar mutuntaka a yanayin jin dadi da wahala.. har mai rabawa ta raba mu.

Al’amarin na da ma’ana baya ga cewa, nuna haduwar zaman tare da wani mutum a bainar jama’a na nuni da biyayya da hangen gaba.

Ba ma a yi la’akari daukacin sauyin tsarin rayuwa ga wasu, tabbas zaman tare na yau da kullum da mutum guda na matukar bukatar hakuri da masalahar zaman lumana.

Hattara ma’auratan da suka gamsu da juna: duk da cewa ana samun jin dadi na takaitacen lokaci ne, domin bayan an daura aure, cikin shekara guda sabani na iya sanyawa a sake lale.

Dangane da kowane irin sauyin kyautata rayuwa aure ke da tasirin haifarwa, abin tunani da alamar tambaya a kai shi bincike ya bai wa fifiko a daukacin fadin duniya, tun da miliyoyinmu na daura aure a kowace shekara.

A gaskiya, binciken da aka gudanar kan tambayar mamakinta ba shi da kima.

Ta yiwu mafi kyawun hujja ita ce wacce ta bayyana a nazarin baya-bayan nan da aka gudanar a kasar Jamus, inda masu binciken suka bi kadin sauyin mutuntakar al’umma kusan 15,000 a tsawon shekaru hudu.

An gano cewa marasa aure irin Bridget Jones da suka jajirce kan lamarin sun fi farin ciki.

Muhimmmin al’amari dai shi ne mutum 664 da aka bibiyi harkokinsu sun yi aure ne lokacin da suke karatu.

Inda aka kyale Jule Specht a Jami’ar Münster da abokan aikinta suka gano yadda kimar mutuntakarsu (halayyarsu) ta sauya in an kwatanta da sauran wadanda ba su da aure da aka bibiyi kadin lamarinsu.

Hakkin mallakar hoto
mediaphotos

Masu binciken sun gano cewa masu auren da aka yi binciken kansu an samu raguwar baza harkokin rayuwarsu a bainar jama’a in an kwatanta da sauran.

Bambancin da aka samu matsakaici ne, amma duk da haka ta yi wu ya bayar da hujja ingantacciya kan zargin da gwagware ke yi cewa abokansu masu aure ba sa shakatawa da holewa kamar yadda suke yi.

Duk da abin mamakin da a ke bazawa, ma’aurat ba kasafai suke suke daukar dabi’un (ha;layar) junansu a tsawon lokaci ba.

Tsarin nazarin ya tabbata ne musamman a kan mata, kamar yaddda yake kunshe a wani kwarya-kwaryar bincikee da aka gudanar a Amurka aka wallafa shi a shekarar 2000.

Inda masu binciken suka yi gwaji kan halayyar mutane fiye da 2000 masu matsakaitan shekaru da aka bibiyesu sau biyu tsawon shekaru shida zuwa tara.

A wancan lokacin, mata 20 masu aure, yayin da wasu 29 aka sake su.

Idan an yi kwatanceceniya tsakanin masu aure da wadanda aurensu ya rabu, wadanda suka samu rabuwar aure sun fi sakin jikinsu a bainar jama’a, kamar wadanda aka cire musu sasarin igiyar aure.

Sababbin ma’aurata maza kuwa, alamu na nuna sun yi matukar fa’idantuwa in an kwatanta da takwarorinsu wadanda suka samu rabuwar aure, inda suke nuna matukar halin kula da kwazo, sannan damuwarsu ta yi matukar raguwa.

Halin kula da ke bai wa maza masu aure kwarin gwiwa haka kawai yake bijirowa.

Duk mutumin da ke da aure (ko tarayyar masoya ta tsawon lokaci) zai san cewa akwai dimbin basirar da ake amfani da ita don tabbatar da dorewar auratayya wajen tarairayar harkokin gida masu tangal-tangal da jirrgin ruwan masu aure.

Wadannan su ne hakikanin al’amuran da aka gano sabuwar makalar da ka wallafa cikin wannan shekarar.

Hakkin mallakar hoto
humonia

Maza masu aure sun fi nuna halin kula, kodayake a wasu lokutan sukan bar tufafinsu da suka yi dauda warwatse a daben daki.

Tawagar Jamusawan yamma masana aikin kwakwalwa, karkashin jagorancin Tila Pronk na Jami’ar Tilbug sun tabbatar da cewa mafi muhimmancin dabarar zamantakewar aure ko halayya shi ne iya tarairayar kai (yin dauriya da cijewa ta tsawon lokaci saboda aure) da yafiya.

Wato ta yadda za aka iya share abin da ya gabata na daga kuskure aboki/abokiyar zama a wani yanayi, wato kamar watsi da kayan sawa a kasa ko yabawa da nuna sha’awa makwafta.

Masu binciken sun dauki sababbin ma’aurata 199, inda suka auna kimar tasirin yafiya ga juna cikin watanni uku da aurensu wadanda aka bi Kadin lamarinsu an kiomanta amincewarsu da abubuwa kamar haka:

“Idan abokin zamana ya yi mini ba daidai ba, masalauha kawai in yafe kuma in manta” da yadda suke tarairayar kansu (wadanda aka bi kadin lamarinsu an kimanta aminceewarsu da al’amura kamar “Na iya kauce wa yaudarar daukar hankali”).

Wadanda aka bibiyi lamarinsu an sake maimaita gwaje-gwajen a kansu kowace shekara har tsawon shekaru hudu.

Sakamakon binciken ya yi nuni da cewa wadanda aka bibiyi al’amauransu sun kara kaimin yafiya da tarairayar kansu tsawon lokacin da aka gudnar danazarin.

Kididdigar alkaluma ta nuna karuwar yafiya ta kasance tsaka-tsaki, yayin da karin iya tarairayar kai (kamun kai) ya zama kadan, amma Pronk da abokan aikinta sun yi nuni da cewa karuwar daidai take da ta kame kai da aka gano a mutanen da ke tsarin tunani musamman kokarin da aka yi wajen kama kai.

Masa aikin kwakwalwa ba su warware abin da ake son ganowa kan ko mutane na samun gamsuwar rayuwa da daina shan wuya idan sun yi aure.

Mene ne dalilin da ya sanya ma’aurata ke watsar da gamsuwar jin dadin rayuwa?

Muhimmiyar hujja ta bayyana a wasu nazarce-nazarce da aka gudanar kan gamsuwar rayuwa da sauye-sauyen samun farin ciki bayan aure.

Rukunin marasa aure irrin su Bridget Jones masu shekaru 30 da doriya za su yi murnar jin cewa duk da gamsuwar dadin rayuwa na karuwa bayan aure, aka kuma samu dalilin da zai haifar da koma-baya a sake lale bayan shekara guda.

Sai dai a iya cewa daukacin abin da aka gano ba lallai haka yake akan kowa ba.

Mun sha yin batu kan wasu mutane da ake kimanta su a matsayin miji nagari ko mata tagari (yayin da wasu sun fi son kasancewa a rayuwar gwagwarci), wannan mahangar madogara ce, domin hujja ta yi nuni kan yadda ma’aurata ke samun sauyin rayuwar farin ciki ya bambanta bisa la’akari da kimar mutunta ko halayyarsu kafin aure.

A wajen wasu, aure na samar da madawwamin farin ciki: musamman abin da ya shafi kula da kai da kunyar mata da sakin jikin maza da ke nuni da karin annashuwa da gamsuwar rayuwa in an yi aure, karara yake a bayyane saboda sababbin ma’aurata na da tsarin rayuwa da ya yi daidai da kimar mutuntakarsu (irin halayensu), duk da cewa dai har yanzu ba a yi nazarin al’amarin ba.

Hakkin mallakar hoto
dragon2

Mutanen da ke da aure ba su cika sakin jikinsu ko kai tsaye su yi ganganci aikata wani abu ba.

Karshen al’amuran, ko me za a ce kan abin da aka baza cewa ma’aurata kan dauki halayen junasu tsawon lokaci?

Akwai tabbaci kan haka in an yi la’akari da yadda tsofaffin ma’aurata ke sanya riga ‘yar shara ko kayan motsa jiki szuna masu barkwanci.

Ta yiwu lamarin na da rikitarwar ban mamaki.

Idan haka kuwa, ana sa ran ma’auratan da suka dade da juna halayyarsu za ta yi daidai da ta abokan zamansu.

Sai dai masu bincike daga Jami’ar Jihar Michigan sun yi nazarin tantance halayyar ma’aurata fiye da 1,200, inda suka gano cewa alakar kadan ce ko ma babu ita sam kan wannan lamari.

Hakikanin gaskiya ita ce mutane da halayyarsu ta zamo iri guda sun fi auren juna karon farko.

Idan aka dauki al’amuran dungurrungum, binciken na nuni da cewa yana da matukar wuya a ce aure na sauya dabi’a.

Sai dai lamarin ba shi da alaka rudani da rikicin dan Adam da ka biyo baya, inda haihuwa ‘ya’ya ke zuwa akai-akai.

Kenya za ta hukunta masu sayar da kayan marmari a leda


A watan Agusta ne Kenya ta saka dokar haramcin yin amfani da ledar.

Image caption

A watan Agusta ne Kenya ta saka dokar haramcin yin amfani da ledar

Mutum 11 aka kama da laifin mallakar ledar da aka haramta yin amfani da ita wajen sayer da kayan marmari a birnin Mombasa da ke Kenya, kamar yadda jaridar Business Daily ta bayyana.

Jaridar ta kara da cewa, an kama mutanen da suka hada da masu sayar da kayan marmari da kuma rake a bakin hanya wadanda suke amfani da ledar, bayan da jami’an ma’aikatar kula da muhalli suka yi musu dirar mikiya.

Sai dai Mai shari’a Martin Rabera ya yi musu afuwa tare da bayyana cewa:

“Kotu ta muku afuwa ne saboda ku ne masu laifi na farko da aka kama. Kodayake muna jan kunnenku wadanda ake tuhuma, idan muka kara samunku da karya wata doka ba za ku ji da dadi ba”.

Har ila yau jaridar ta ruwaito mai shigar da kara Jane Alango yana cewa: “Baya ga gurbata da muhalli da ledar take yi, tana sanadiyyar kashe dabbobi da dama. Mutane suna iya yin amfani da kwanduna da sauran mazubi ba leda ba.”

Wadannan mutanen za su zama “darasi a wurin wadanda har yanzu suke amfani da haramtacciyar ledar.

A watan Agusta ne kasar Kenya ta saka dokar haramcin yin amfani da ledar.

Sabuwar dokar ta tanadi tarar da ta kai dala 38,000 ko kuma daurin shekara hudu a gidan yari ga duk wanda aka kama yana sayar da ledar ko yinta ko kuma aka same shi da ita.

Arhar kayan masarufi ka iya jefa tattalin arzikin duniya halin ka ka ni kayi — IMF


IMF ya ce, arhar kayan masarufi da rikicin siyasa barazana ne ga tattalin arzikin duniyaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

IMF ya ce, arhar kayan masarufi da rikicin siyasa barazana ne ga tattalin arzikin duniya

Asusun lamuni na duniya, IMF, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar bunkasar tattalin arzikin duniya ya ja da baya, sanadiyyar arhar kayayyakin masarufi da kuma rikice-rikicen siyasa.

A wani rahoto da aka saki a taron IMF da bankin duniya na shekara-shekara, asusun IMF, ya ce tattalin arzikin duniya bai kammala murmurewa ba, kuma a kasashe da dama bunkasar tattalin arzikin ba ta yi karfi ba.

Koda yake, asusun ya amince da cewar an samu karuwar hada-hadar harkokin tattalin arziki sanadiyyar karuwar zuba-jari da cinikayya da kuma samar da kayyayakin masana’antu, amma duk da haka ya yi gargadin cewa mutane da yawa a fadin duniya ba su ji wani sauyi a rayuwarsu ba.

Bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika shi ya fi cancanta — Dangote


Aliko Dangote ya ce yakamata kamfanonin kasashen Afrika su rinka bunkasa kasuwanci a tsakaninsuHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Aliko Dangote ya ce yakamata kamfanonin kasashen Afrika su rinka bunkasa kasuwanci a tsakaninsu

Manyan shugabannin kamfanoni da ‘yan kasuwa a Africa, sun gudanar da babban taro tare da wasu tsofaffin shugabannin kasashen nahiyar a birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Taron ya zo da zimmar kafa kungiya mai karfi wacce za ta bunkasa harkokin kasuwanci a Afrika, a maimakon dogaro da kasashen ketare.

‘Yan kasuwar sun ce ana shigo da akasarin kayayyaki ne daga kasashen turai da China, abinda ke kawo tarnaki ga bunkasar kasuwanci a nahiyar Afrika.

Attajirin da yafi kowanne bakin fata arziki a duniya, Aliko Dangote, shi ne ya jagoranci taron , inda ya ce yakamata manyan kamfanoni Afrika su hada kai da gwamnatocinsu ta yadda za a samar da ayyukan yi da kuma karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika, maimakon kasuwanci da kasashen turai.

Aliko Dangote, ya ce kasuwancin da ake yi a tsakanin kamfanonin Afrika bai wuce kaso 18 cikin 100 ba, dan haka akwai bukatar karfafa kasuwanci a tsakanin manyan kamfanonin Afrikan.

To sai dai ya ce idan har ana so a cimma wannan bukata, to dole ne kamfanonin su rinka yin kaya masu inganci.

Somalia: Bam ya kashe mutum 30 a Somalia


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wurin da aka kai harin a Mogadishu

Wani mummunan harin bam ya kashe mutum 30 a wata unguwa mai cinkoson jama’a a babban birnin kasar Somaliya, Mogadishu, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Hakazalika wadansu mutane da dama sun jikkata lokacin da wata babbar motar kaya da aka daura wa bama-bamai suka fashe a kofar shiga wani otel.

‘Yan sanda sun ce mutum biyu sun mutu a wani hari na biyu a wata unguwa mai suna Madina wadda take birnin Mogadishu.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma birnin ya saba fuskantar hare-haren kungiyar al-Shabab wadda take yaki da gwamnatin kasar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana fargabar cewa akwai mutanen da buraguzan gini ya danne

Bayan harin farko, jami’in dan sanda Mohamed Hussein ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: “An yi amfani da wata babbar mota ne wajen kai harin. Ba mu san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba tukuna saboda har yanzu wuta ce ke ci gaba da ci a wurin.”

Wadanda suka shaida al’amarin sun shaida wa BBC cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu.

Wakilin BBC ya ce ginin Safari Hotel ya ruguje, kuma ana zaton ya danne mutane.

Wani mazaunin unguwar Muhidin Ali ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “wannan ne harin bam mafi muni da ya taba gani, harin ya lalata duka wurin”.

Karanta wadansu karin labarai

Crystal Palace ta ba Chelsea mamaki


Wilfried ZahaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wilfried Zaha ne ya ci wa Palace kwallo ta biyu a minti na 45

Kungiyar Crystal Palace ta samu nasarar farko a kakar firimiyar bana bayan da ta doke Chelsea da ci 2-1.

Kungiyar ta yi rashin nasara a duka wasanni bakwai da ta buga a kakar bana ciki har da guda uku da ta buga karkashin jagorancin sabon koci Roy Hodgson.

Kuma rabon kungiyar ta zura kwallo a raga tun a watan Mayun da ya wuce.

Nasarar da ta samu ya ta dan matsa sama daga kasan teburin gasar.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga ranar Asabar
Liverpool 0-1 Man United
Burnley 1-1 West Ham
Man City 7-2 Stoke City
Swansea 2-0 Huddersfied
Tottenham 1-0 Bournemouth

Galibin malaman firamaren Kaduna sun ci jarabawarsu – Kungiyar Kwadago


 • Za ku iya sauraron cikakkiyar tattaunawar da aka yi da Shugaban Kungiyar Kwadagon da kuma Mai Magana da yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan a shirinmu na Ra’ayi Riga, idan kuka latsa alamar lasifika da ke sama.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Kwamred Adamu Ango, ya ce galibin malaman makarantar firamaren jihar sun ci jarabawar da gwamnatin jihar ta yi musu a kwanakin baya.

Gwamnatin jihar ta jaraba malaman firamare 33,000, inda ta ba su jarabawar dalibai ‘yan aji hudu.

Sai dai kashi 66 cikin 100 na malaman sun fadi jarabawar, a cewar gwamnatin jihar, inda ta ce malamai 21,780 ba su samu maki 75 cikin 100 ba.

Kwamred Ango ya ce sun samu rahoton wucin gadi wanda ya nuna cewa kashi 73.3 cikin 100 na malaman da suka zauna a jarabawar ne suka yi nasara, “wato wadanda suka samu maki kashi 60 cikin 100. To yaya kuma za a juya a ce sai wadanda suka ci kashi 75 cikin 100 ba,” in ji shi.

Sai dai Mai Magana da yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan ya musanta hakan, inda ya ce kamata ya yi “idan malami yana koyar da darasi, ya ci maki 75 cikin 100 a jarabawar darasin.”

'Dalibi ya kashe 'yan uwansa dalibai biyar a Kenya'


A map of Kenya

Akalla dalibai biyar da wani mai gadi sun mutu sakamakon wani hari da aka kai wata makarantar kwana a arewacin kasar Kenya.

Shugaban makarantar AIC Lokichogio Secondary School ya ce suna zargin wani dalibi wanda aka dakatar daga makarantar da jagorantar harin.

Ana zargin cewa dalibin tare da wadansu mutane biyu ne suka kai harin a ranar Asabar.

Wani ganau ya ce bayan kashe mutum shida, sun yi wa wadansu ‘yan mata biyu fyade da kuma jikkata wasu dalibai 18.

Kamar yadda shugaban makarantar ya ce yaron ya fito ne daga kasar Sudan ta Kudu kuma an dakatar da shi ne saboda ya yi fada da wani dalibi.

Sai dai yayin harin abokin fadan na shi ba ya makaranta a lokacin.

Jaridar Daily Nation ta ruwaito cewa dalibin da ake zargin ya taba shaida wa “takwarorinsa dalibai cewa zai kona makarantar ko kuma zai dawo ya dauki fansar dakatar da shi da aka yi”.

Karanta wadansu karin labarai

Ivory Coast: Mutum hudu sun mutu a hadarin jirgin sama


Ivory Coast

Wani jirgin saman kaya ya yi hadari a kusa da gabar tekun kasar Ivory Coast jim kadan bayan ya tashi daga filin jirgin saman birnin Abidjan.

Rahotanni sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu.

Jirgin yana dauke ne da wadansu kayayyakin sojin kasar Faransa, kamar yadda wata kafar yada labarai ta bayyana.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa akalla mutum hudu ne suka mutu.

Masu aikin ceto sun fito da gawawwaki guda biyu daga cikin jirgin, akwai kuma sauran biyun a cikin buraguzan jirgin, kamar yadda kamfanin Reuters ya ruwaito.

Sai dai wadansu rahotanni kuma sun ce galibin ma’aikatan jirgin sun tsira.

Adikon Zamani: Matsayin kayan lefe a addinin Musulunci


 • Akwai zantawar da Fatima Zarah Umar ta sakeyi game da kayan lefe musamman ta fuskar addini da kuma al’ada, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Daya daga cikin manyan batutuwan da suke tasowa game da batun aure a kasar Hausa shi ne kayan lefe.

Idan ana maganar lefe kowa ya san cewa batu ne na kudi musamman idan aka yi la’akari da gidan da amaryar ta fito.

Shin ta fito daga gidan masu hali ne ko kuwa ‘yan rabbana ka wadata mu.

Ta fito daga birnin ne ko kauye? Da kuma yadda ‘yan uwanta za su rika tambaya cewa akwati nawa aka kawo?

Wadannan kayayyaki aka sanya a akwatin? Manyan atamfofi nawa ne a ciki? Akwai atamfa Super ko Java?

Wadanne irin gyale aka sa a akwatin kuma ko kayan sun burge surukan angon?

Adikon Zamani: ‘Yar aiki ko baiwa?

Adikon Zamani: Yadda mata masu cutar HIV ke rayuwa

Yadda na fahimci abin shi ne kayan lefe wani abu ne da ya yi kama da kyauta amma ba wani abu ba ne da wajibi ya burge mutum. Ba wata dama ce ta bayyana yawan arzikin mutum ba.

Aure bai dogara kacokan a kan lefe ba.

Ko miji da gidansu sun yi lefe, ko ba su yi ba, nauyin samar wa mace tufafi ya rataya ne a wuyan mijinta.

Yadda muka ba lefe muhimmanci abin kamar ita amarya ba za ta kara sanya wasu kayan ba idan ba na lefe ba duk tsawon rayuwarta.

A wasu lokuta iyaye ba sa tambaya kan yadda ko ya dace a saye irin wadannan kayayyaki.

Yana da wuya ka ga wani yana tambaya game da yadda lefe zai amfani zamantakewar aure.

Mene ne amfanin kayan lefe a aure?

Ko wajibi ne sai an yi kayan lefe? Yana da wani tasiri wajen zamantakewa? Ko idan aka yi wa amarya akwatuna da dama na samar da kyakkyawan zaman aure?

Wane ne yake cin moriyar kayan lefe? Bayan mutanen da suke yada tsegumi da kananan maganganu?

A duk lokacin da na ga samari suna kokorin hada kayan lefe, nakan tausaya musu.

Bai kamata aure ya zama kamar wani cinikin kasuwanci ba. Aure ana so ne ya kasance har abada.

Ko al’umma za su daina damuwa da lefe da kayan daki, don su mayar da hankali kan kyawawan dabi’u da kuma tarbiyya?

Ina tausayawa ‘yan uwana wadanda suka fito daga yankin arewa-maso-gabashin Najeriya saboda hada kayan lefe a wannan yanayi na matsin tattalin arziki ba abu ba ne mai sauki.

Sai dai komai ya yi tsanani maganinsa Allah.

Har ila yau, ina tausayawa iyaye wadanda suke hada wa ‘ya’yansu kayan daki saboda yadda hakan yake cin makudan kudi.

Ya kamata ne kowannenmu ya sauke nauyin da ke wuyansa.

Mata da dama sun shaida min cewa bayan da aka yi musu lefe, mazajensu ba su damuwa wajen tufatar da su.

Lefe ba ya dauke nauyin tufatarwa da ya rataya a wuyan mai gida.

Mata da dama sun san cewa ana fara rikici ne da zarar dara ta fara karewa.

Wacce irin al’umma muke ciki wadda iyayen amarya suke yi wa ango kusan komai – ciki har da dara wadda takan kai tsawon kimanin shekara guda bayan aure, amma abin mamakin shi ne yadda har yanzu ake kara samun yawaitar mutuwar aure.

Jurgen Klopp: Samun koci irina, sai an tona


Jurgen KloppHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Klopp wanda tsohon kocin Borussia Dortmund ne, ya fara jagorantar Liverpool a shekarar 2015 ne

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce samun koci irinsa da zai yi aiki tukuru a kungiyar, sai an tona.

Kocin bai ci wani babban kofi ba tun bayan nada shi kocin kungiyar shekara biyu da suka wuce, biyo bayan sallamar Brendan Rodgers.

A ranar Asabar ne kungiyar za ta karbi bakuncin Manchester United.

Kuma idan ta yi rashin nasara hakan na nufin tana da maki 12 ke nan a wasanni takwas da ta buga – lissafin da ya yi daidai da na lokacin da aka kori Rodgers.

“Ba na jin cewa ni ban yin kuskure amma kuma yana da wuya a samu wadda zai fi ni,” in ji Klopp.

Sau daya Liverpool ta ci wasa a cikin wasanni bakwai da ta buga. Abin da ya sa take a mataki na bakwai a teburin gasar Premier.

Har ila yau an fitar da Liverpool daga Gasar Carabao kuma ba ta samu nasara a wasanni biyun da ta yi ba a Gasar Zakarun Turai.

Klopp ya ce: “Idan suka kori yanzu, ba na jin akwai wadansu kocakocan masu yawa da za su yi aikin fiye da ni.”

“Babu wata tazara sosai tsakaninmu da kungiyoyin da ke saman teburin gasar,” a cewarsa.

Mata 100: Kun san macen da ta yi zarra tsakanin mazan Nigeria?


Ta yi karatunta na lauya bayan ta yi aureHakkin mallakar hoto
Justice Bulkachuwa’s Albuma

Image caption

Ta yi karatunta na lauya bayan ta yi aure

Wannan makala ce da muka rubuta don amsa tambayoyinku a kan abin da ku ke son sani game da mace ta farko da ta fara rike mukamin shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, wato Justice Zainab Bulkachuwa. A sha karatu lafiya.

Idan ana batun ilimin ‘ya’ya mata a arewacin Najeriya a shekaru kusan 50 da suka gabata, tarihi ya nuna cewa an fuskanci manya-manyan kalubale da suka hana a bai wa mata damar neman ilimi, sai dai wadanda Allah Ya tsaga da rabonsu.

A wancan lokacin an fi mayar da hankali ne kawai wajen ganin an aurar da ‘ya’ya mata da zarar sun fara tasawa.

Kalilan ne suka samu damar kammala makarantar firamare ko sakandire, yayin da tsiraru suka je jami’a amma su ma yawanci daga dakin aurensu.

Justice Zainab Bulkachuwa na daga cikin wadanda suka yi sa’ar samun ilimi mai zurfi tun sekara 40 da suka gabata, kuma ta yi karatun shari’ar zamani ne a lokacin da ake ganin cewa irin wannan karatu ‘haramun ne, kuma duk lauya dan wuta ne,’ ba ma ga mata ba kawai har da mazan.

Shin wace ce Justice Zainab Bulkachuwa?

Wannan ita ce tambayar da mafi yawan masu sauraronmu suka aiko mana kamar su Ayuba Yayaha Isma’il Wudil da Abdulrashid Mohd Dan Ango da wasu da dama.

Image caption

Justice Bulkachuwa

A hirar da muka yi da ita, ta shaida mana cewa asalin sunanta Zainab Abubakar Gidado El-nafaty, an haife ta a garin Bauchi a ranar 6 ga watan Maris shekarar 1950. ‘Yar asalin jihar Gombe ce daga karamar hukumar Nafada.

“Tun ina yarinya ni mai sha’awar karatu ce kuma babana shi ya fara koya min karatun addini tun ina karama kafin daga bisani ya sani a makarantar firamare ta Tudun Wada Kaduna, a lokacin da na shekara bakwai.

“Na kammala a 1960, sai kuma na tafi makarantar sakandare ta Queen Elizabeth da ke Ilorin na kuma kammala a 1972.”

Justice Zainab ta ce daga nan ne batun aurenta ya taso, duk da cewa mahaifinta ya so ta yoi ilimi mai zurfi amma manyansa suka ce lallai aure za a yi mata. Sai dai ya dage wajen ganbin cewa lallai mijin da zai aure ta ya yi alkawarin mayar da ita makaranta bayan biki.

“Haka kuwa aka yi, duk da cewa babana bai ga aurena ba, amma mijin nawa ya cika alkwari na koma makaranta inda na karanta fannin shari’ar zamani a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, na kammala a 1975 sai na wuce makarantar koyon aikin shari’a a Lagos na gama a 1976.”

Justice Zainab Bulkachuwa ta shaida min cewa ta haifi uku daga cikin ‘ya’yanta a lokacin da take gwagwarmayar neman ilimi.

Wuraren da ta yi aiki

Wannan tambaya ce da jama’a da dama suka aiko mana a kan Justice Bulkachuwa kamar irin su Aminu Usman Katsina.

“Na yi aikin bautar kasa a ma’aikatar shari’a ta Kaduna, daga nan sai na fara’a aiki a kotun majistare ta Kaduna tun daga shekarar 1980 inda na dinga samun karin girma har zuwa shekarar 1985.

Daga nan kuma Justice Zainab ta koma jiharta ta Bauchi a wancan lokaci inda ta ci gaba da ayikinta a mataki-mataki har ta kai matsayin alkalin babbar kotu.

Daga bisani bayan da aka kirkiri jihar Gombe sai ta koma can a matsayin alkalin babbar kotun har zuwa watan Disambar 1998.

A shekarar 1998 ne Justice Bulkachuwa ta samu sauyin aiki zuwa kotun daukaka kara ta Najeriya a matsayin daya daga cikin alkalan kotun.

Image caption

Justice Bulkachuwa tare da babban mai shari’a na kotun kolin Birtaniya

Kalubale

Ko wanne al’amari na rayuwa na cike da kalubale daban-daban, to haka abin yake ga Justice Bulkachuwa.

Ta shaida min cewa a iya tsawon rayuwarta ta samu kalubale musamman a yayin da take karatu ga aure da haihuwa.

“Wani lokaci haka na yi ta fama da laulaye-laulayen ciki ga karatu, in yi ta amai amma dole na zage damtse wajen karatu ba kama hannun yaro, kuma cikin ikon Allah ban taba faduwa jarrabawa ba.

“Kazalika ban samu kalubale daga wajen maigidana na farko da ya rasu ba da kuma maigidana na biyu da na sake aurensa. Duk sun bani goyon baya shi ya sa ma wahalhaluna ba su yi yawa ba.

“Kuma duk da irin hidimomin aiki a haka na samu lokacin yi wa yarana shida tarbiyya, kuma Alhamdulillahi ga su nan duk sun girma sun zama cikakkun mutane.”

Sai dai mai shari’ar ta ce akwai lokacin da ta tafi hutun haihuwa bayan ta dawo ya kamata a kara mata girma zuwa alkalin babbar kotun jihar Bauchi, amma sai aka bai wa wani na kasa da ita.

“Sai daga baya nake ji ana cewa ashe a lokacin arewa ba ta shirya samun alkali mace ba shi ya sa aka yi min haka.”

Wannan bayani ya amsa tambayar dumbin masu sauraro da suka hada da Usman Uba.

Image caption

Justice Bulkachuwa ta shaida wa Halima Umar Saleh cewa neman ilimi cike da kalubale don haka akwai bukatar jajircewa

Shin an mata alfarma ne kafin ta samu wannan mukami?

Justice Bulkachuwa ta ce kamar yadda yake a tsarin aiki komai ana binsa ne daki-daki don haka babu wata alfarma da aka yi mata.

“Yadda ka zo haka za ka yi ta bin layi har abu ya zo kanka. Akwai matakai da yawa da ake bi don tantance ka kuma duk sai da na bi su.

Tallafawa sauran mata

“A fannin aikina dai na zama uwa don ko yaushe cikin gyara nake musamman mata masu tasowa da ke aikin lauya. Ina sa ido sosai don gyara a tarbiyyarsu da kuma aikinsu,” in ji mai shari’a Bulkachuwa.

“Ina kuma taimakawa yara mara sa galihu zuwa makaranta don su ma su amfana a nan gaba.

Akwai wata tambayar da masu sauraro suka aiko kan yadda take ganin ci gaban mata a Najeriya.

“Gaskiya an samu ci gaba sosai, misali a fannin shari’a mun samu mace ta farko da ta zama babbar mai shari’a ta kasa Justice Maryam Alooma. Sannan akwai bangarori daban da dama suka yi zarra.”

Hakkin mallakar hoto
Justice Bulkachuwa’s Album

Image caption

Wannan diyar mai shari’ar ce wadda ke son ta gaji mahaifiyarta a irin aikin da take yi

Justice Bulkachuwa ta yi kira ga mata masu dtasowa da su mayar da hankali wajen neman ilimi mai inganci su kuma rage buri na kyale-kyalen rayuwa.

“Ya kamata yaranmu masu tasowa su sani cewa dole su jajirce wajen inganta rayuwarsu da ta ‘ya’yansu da ta jikokinsu masu zuwa, duba da halin da ake sake shiga a rayuwa.”

Cin hanci

Masu sauraronmu da dama sun yi batun ko Justice Bulkachuwa na amince wa da karbar cin hanci da rashawa?

Amma a tattaunawarmu ta ce: “Alkwari na dauka fa tare da yin rantsuwa cewa ba zan cuci kasata da al’ummarta ba, to me zai sa na yi wani abu mara kyau?”

Wannan ne ma dalilin da ya sa wasu suke mata kallon mace mai tsauri kuma mara son wargi, musamman yayin da take kotu.

Justice Bulkachuwa ta samu sunan Bulkachuwa ne daga mijinta na yanzu wani toshon dan siyasa a jihar Bauchi, Alhaji Adamu Bulkachuwa, wanda ta aura bayan mutuwar mijinta na farko.

Tana da ‘ya’ya shida daga aure biyun da ta taba yi a rayuwarta. Kuma a cikin zuri’arsu mai matukar yawa, an fi kiranta ne da ‘Adda Zainabu’ don ganin cewa ita ce babba.

Hakkin mallakar hoto
Justice Bulkachuwa’s Album

Image caption

Ta ce: ‘Na haifi uku daga cikin ‘ya’yana a lokacin da nake karatu, kuma a haka na dage na yi musu tarbiyya.’

Iran ba ta martaba manufar yarjejeniya —Trump


Trump ya ce Iran ba ta biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla da ita a kan shirinta na nukiliyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Trump ya ce Iran ba ta biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla da ita a kan shirinta na nukiliya

Sauran kasashe shidan da suka kulla yarjejeniyar dakile shirin nukiliyar Iran sun ce za su ci gaba da aiki da ita duk da sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump, ya yi na janyewa daga yarjejeniyar.

Mr Trump ya ce, Amurka a shirye ta ke ta kawo karshen yarjejeniyar saboda matakan da ya ce Iran na dauka.

Shugaba Trump, ya ce gwamnatin Iran na ci gaba da rura wutar rikici da ta’addanci da kuma yamutsi a yankin Gabas ta Tsakiya da ma sauran sassan duniya.

Inda ya ce abin lura shi ne, Iran ba ta biyayya ga manufar yarjejeniyar.

Kasashen Jamus da Faransa da Burtaniya dai sun nuna damuwarsu game da matakin na Mr Trump.

Kasar Rasha kuwa, ta zargi shugaban kasar na Amurka ne da amfanin da kalmomi masu tunzuri a cikin jawabin nasa.

Ita kanta Iran ta ce Amurka ita kadai ba za ta iya sauya fasalin yarjejeniyar kasashe da dama ba.

Sai dai kasashen Isra’ila da Saudi Arabia wadanda duk makiyan Iran ne, sun yaba da wannan mataki na Mr Trump.

Ma'auratan da aka yi garkuwa da su shekara biyar sun samu 'yanci


Ma'auratan sun shafe shekara biyar ana tsare da su

Image caption

Ma’auratan sun shafe shekara biyar ana tsare da su

An saki wasu ma’aurata ‘yan yankin Arewacin Amurka, da wata kungiya mai alaka da Taliban ta sace su a Afghanistan, shekara biyar da ta wuce.

Mista Joshua Boyle, dan asalin Canada ne, ya yin da matarsa mai suna Caitlan Coleman, ta fito daga Amurka.

Ma’auratan sun haifi ‘ya’ya uku a lokacin da ake tsare da su.

An sace ma’auratan ne jim kadan bayan sun yi aure a Afghanistan.

Bayan sace su, sun dauki lokuta su na aiko da hotunansu da kuma wasiku, amma daga bisani sai aka ji shiru, sai a watan Disambar bara ne suka aiko da hoton bidiyonsu da kuma ‘ya’yan da suka haifa a lokacin da suke tsare, kuma a lokacin ne su ka yi bayanin halin da su ka tsinci kansu ciki tun daga lokacin da aka tsare su.

To tun daga wannan lokaci kuma su kai dib, sai a makon daya gabata ne aka kubutar da su.

An dai samu damar kubutar da su ne a Pakistan, bayan da wadanda suka sace sun su ka dauko su daga inda aka ajiye su, su ka kawo su inda aka sake su tare da ‘ya’yan nasu.

Nigeria: Majalisa za ta binciki asibitin fadar shugaban kasa


Majalisar wakilan Najeriya ta ce ana warewa asibitin fadar shugaban kasa kudi a kasafin kudin kasar

Image caption

Majalisar wakilan Najeriya ta ce ana warewa asibitin fadar shugaban kasa kudi a kasafin kudin kasar

A Najeriya, ‘yan majalisar wakilan kasar za su gudanar da bincike a kan mawuyacin halin da asibitin fadar shugaban kasar ke ciki.

‘Yan majalisar sun nuna damuwar cewa duk da irin makudan kudaden da ake warewa asibitin a kasafin kudin Najeriya , amma ana samun rahoton rashin kayan aiki a asibitin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta zargi asibitin da rashin kayan aiki a makon da ya gabata, lokacin da ta kai ziyara asibitin da ba ta da lafiya.

Hajiya Aisha, ta ce abin takaici ne yadda idan aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.

Mai magana da yawun majalisar, Hon Abdurrazak Namdaz, ya shaida wa BBC cewa, tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar da muke ciki, ana warewa asibitin fadar shugaban kasar kudade a kasafin kudin kasar, dan haka ya ce dole a bincika domin gano inda kudaden suka tafi.

Hon. Namdaz ya ce wani kwamiti na musamman ne aka bawa wuka da naman gudanar da bincike a kan inda kudaden kula da asibitin fadar shugaban kasar suka shiga.

Dan majalisar ya ce nan bada jimawa ba kwamitin zai fara aikinsa, kuma da zarar ya kammala binciken ya bayar da rahotonsa, za a sanar da jama’ar kasa komai dalla-dalla.

U-17: Nijar ta kai matakin zagayen gaba


Niger and South KoreaHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wannan ne karon farko da Nijar ta samu shiga gasar duniya

Nijar ta kai matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a Indiya na ‘yan kasa da shekara 17, yayin da aka yi waje da Guinea daga gasar.

Nijar ta dare matakin ne da maki 16, yayin da ta kafa tarihi a shiga gasar duniya, wanda ba ta taba samun wannan damar ba a tarihi.

Duk da rashin nasarar da Nijar ta yi a hannuna Brazil da ci 2-0 a matakin karshe na wasansu a rukunin D, Najeriya kuma ta matsa gaba inda take daya daga cikin fitattun kungiyoyi uku.

Jamus dai ta doke Guinea da ci 3-1 a rukunin C.

Nigeria: Buhari ya jajanta wa mutanen Kaduna


Akwanakin baya ma sai da haduran kwale-kwale ya kashe mutane a jihohin Kebbi da Neja da kuma LegasHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akwanakin baya ma sai da haduran kwale-kwale ya kashe mutane a jihohin Kebbi da Neja da kuma Legas

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan dalaban nan da ruwa ya ci a jihar Kaduna.

Ya kuma jajanta wa daukacin al’ummar jihar da kuma shugabanin makarantar da daliban suka fito.

A ranar Juma’a ne rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da cewa kogin Kaduna ya ci ‘yan makarantar sakandare biyar masu ziyarar karo ilimi.

Rundunar ta bayyana cewa daliban da suka fito daga makarantar Victory International School, sun hau kwale-kwale daga wata tashar zuko ruwa ta hukumar samar da ruwan sha mallakar jihar kusa da tashar jirgin kasa da ke a lokacin da lamarin ya faru da su.

Bayan daliban su goma sun kammala ziyarar karo ilimin a tashar hukumar samar da ruwan ne sai suka hau kwale-kwale domin haye kogin a ranar Laraba.

Sai dai kwale-kwalen da suka hau din ya dare biyu domin yawan mutanen da ke kai, lamarin da ya sa daliban suka nutse.

Masu aikin ceto sun samu damar ceto biyar daga cikin daliban. An kuma samu gawarwakin biyu daga cikinsu yayin da har yanzu ake neman sauran gawarwakin.

Mata sun yi kira da a kauracewa shafin Twitter


Shafin TwitterHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shafin Twitter na da dumbin mabiya

Jaruman fina-finai na Hollywood da masu fafitika sun yi kira don a kauracewa shafin sada zumunta na Twitter, bayan da kamfanin Twitter ya dakatar da Rose McGowan, wata jarumar fim wanda ta zargi Harvey Weinstein wani mai shirya fina-finai da yi mata fiyade.

Shafin na Twitter ya ce ta karya dokokinsu a cikin wadansu sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Masu goyon bayan Rose McGowan sun yi amanna cewa, an hana ta magana ne don tana amfani da shafin wajen yin korafi a kan Mista Wenstein da ma sauran wasu fitattun mutane, wadanda ta ce sun san abin da yake mata na cin zarafi amma ba su yi komai a kai ba.

Mista Weinstein ya karyata duk wani zargin cin zarafi.

Maudu’in da aka kirkiro don yada batun mai taken ‘Women Boycott Twitter’ wato ‘Mata su kautracewa Twitter’ ya ja hankalin mutane sosai, duk da cewa mata da dama sun kauracewa amfani da shafin.

Boko Haram: An sallami mutum 468 da ake zargi


Boko HaramHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Amnesty International sun yi kira da ayi wa wadanda ake zargin adalci

Wata babbar kotu mai zama a garin Kainji da ke jihar Niger a arewacin Najeriya, ta yanke wa wasu mayakan Boko Haram 45 hukuncin daurin daga tsakanin shekara 3 zuwa 31, bayan ta same su da laifi a shari’ar da aka yi wa wasu ‘yan kungiyar su 575 .

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a, ministan yada labarai da al’adu na kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kotun ta wanke mutum 468 wadanda ba a samu da laifi ba.

An yi watsi da shari’ar mutum 34, yayin da aka ajiye mutum 28 a gidan wakafi domin a yi musu shari’a a Abuja da Minna.

Kotun ta bayar da umarnin cewa a yi wa mutum 468 da ta wanke din hororwa na sauya tunani kafin a mika su ga gwamantocin jihohinsu.

An fara hukuncin shari’ar ta gama gari ne bayan kotu ta ajiye mutum 1,669 da ake zargi da kasancewa ‘yan Boko Haram na tsawon kwana 90 a gidan wakafi.

Kuma kotun ta bayar da umarnin cewa a gurfanar da su cikin wannan lokacin ko kuma a sake su ba tare da sharadi ba.

Kotun ta daga shari’ar da ake yi wa ragowar wadanda ake zargi da kasancewa ‘yan Boko Haram din zuwa watan Janairun shekarar 2018.

Guardiola ya raina mana wayo – Pochettino


Image caption

A gobe Asabar ne Tottenham za ta karbi bakuncin Bournemouth a Wembley.

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce, maganganun da Pep Guardiola ya yi na cewa kungiyar ta dogara ne akan Harry Kane “rainin wayo ne”.

Kocin Mancherster Cityn ya bayyana kungiyar a matsayin “kungiyar Harry Kane”. Ya yin da yake magana akan abokiyar hamayyartasa.

Dan kwallon ya ci kwallo 11 a wasa bakwai da kungiyar ta buga a bana.

Pochettino ya kara da cewa,”Guardiolan na cikin wadanda suka kawo nasara a Barcelona kuma ban taba cewa kungiyar Lionel Messi ba ce.

A gobe Asabar ne Tottenham za ta karbi bakuncin Bournemouth a Wembley.

'Kada ta kashe wata tsohuwa' a Australia


Anne CameronHakkin mallakar hoto
Queensland Police

Image caption

Tun ranar Talata ne Anne ta bata

‘Yan sanda wadanda suke neman wata mata a Australiya sun ce da alama kada ce ta kashe ta.

An kawo rahoto cewa ana cigiyar wata mata Anne Cameron mai shekara 79 da ta ke zama a wani gidan kula da tsofaffi kusa da garin Queensland na Port Douglas a ranar Talata.

An samu kaya da sandar dogarawa mai dauke da sunanta kusa da bakin kogi, kuma matar tana fama da ciwon mantuwa.

A ranar Juma’a ‘yan sanda sun samu ragowar bangarorin jikin mutum, kuma suna zaton cewa na Anne Cameron ne.

Mataimakin shugaban ‘yan sanda Ed Lukin ya ce: ”Muna zaton cewa da alama kada ce ta kai mata hari.”

”Za a gudanar da bincike don a gano ko bangarorin jikin mutum din da aka gano na Anne Cameron ne.”

‘Yan sanda suna zargin cewa kadar ta kai wa Anne Cameron hari ne a lokacin da ta shiga cikin wani jeji wanda yake da nisan kilomita biyu daga gidan kula da tsofaffin da take.”

Wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, ”Ta koma gidan kula da tsofaffin ne don ta zauna cikin sa’o’inta.”

Jami’an da ke kula da dabbobin daji za su saka tarkon kama kada a yankin da aka ga gawar.

Hare-haren da kada ke yawan kai wa sun yi sanadaiyyar mutuwar mutum tara a Queensland tun shekarar 1985, ciki har da wani masunci a watan Maris din da ya gabata.

Swaziland: Google ta amince da yada bidiyon 'rawa tsirara'


SwazilandHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rawar da ake kira “Reed Dance” (Rawar Kara) wata rawar al’ada ce wadda ake yi a ko wace shekara a Swaziland kuma a rawar mata marasa riga na cikin masu rawar

Kamfanin sadarwa na Google ya janye takunkumin da ya sa kan yada hoton rawar ‘yan mata ba riga da ake yi a kasar Swaziland kan shafinta na wallafa bidiyo na Youtube, in ji jaridar Mail and Guardian ta Afirka Ta Kudu.

Jaridar ta Mail and Guardian ta ambato wani wakilin kamfanin Google din yana cewa sun yanke hukuncin cire takunkumin daga bidiyon ne saboda ‘ba ya cikin manufarta na takaita bayyana tsiraici a irin wannan yanayin da al’ada ta amince da bayyana tsiraici”.

Matakin ya zo ne a matsayin martani ga wani kamfe da Lazi Dlamini, shugaban gidan talabijin na Yabantu, da ke watsa bidiyonta a kafar Intanet kuma take shirye-shirye masu karewa da adana da kuma mayar da dabi’un Afirka.

An kirkiri shafin da ake wallafa bidiyon al’adun Afirkar ne a You Tube a shekarar 2016 – kuma yana samun masu bibiya 3,000 zuwa 4,000 a ko wanne wata har zuwa lokacin da shafin na YouTube ya fara nuna alamar cewar shirye-shiryensa ba su dace ba.

Ya kuma saka wa shafin wata alama da ke nuna wa masu talle cewar shirye-shiryensa ba su dace da yawancin muradun masu talle ba.

Mista Dlamini ya ce shi ya tuntubi Google ne domin ya bayyana cewa shi kawai yana nuna al’adun mutanensa ne, amman kamfanin ya ce shirye-shiryen na kunshe da abubuwan da suka saba wa ka’idojinta.

Sa’annan ya shirya wani jerin zanga-zanga tare da kungiyoyin al’ada sama da 200 daga Swaziland, inda aka yi zanga-zanga ta farko ranar Asabar a birnin Durban.

Zanga-zangar ta kunshi a kalla mata 12 wadanda suka tsaya da mamansu a waje dauke da kwalaye da ke cewa: “Google na nuna wariya” da kuma “(ganin) nuna nono ba rashin dacewa ba ce”.

Nobukhosi Mtshali, wadda daliba ce a jami’ar Witz kuma mai fafatukar ‘yancinta na bayyana al’adarta ta Swazi, tana kallon takunkumin wani hari ne kan al’adarta.

“Ni, a matsayina na ‘yar Afirka Ta Kudu , ina son in yi alfahari da al’ada ta.

“In aka nuna cewa hotona bai dace ba, ko kuma na batsa ne, ina ganin wannan hari ne kai tsaye kan ala’adata. Ina ganin wannan wata alama ce ta jahilci…

“Idan ina tsayuwa ta hanyar da za ta ja hankali ne wannan wata aba ce ta daban, amman idan na wallafa hotona na cikin rigar tufafin al’adata, wannan wani abu ne daban.

Nigeria: Yadda ruwa ya tafi da dalibai biyar a Kaduna


kwale-kwaleHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ko a kwanan nan ma sai da haduran kwale-kwale suka kashe mutane a jihohin Kebbi da Neja da Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da cewar kogin Kaduna ya ci ‘yan makarantar sakandare biyar masu ziyarar karo ilimi.

Rundunar ta bayyana cewa daliban da suka fito daga makarantar Vitory International School, sun hau kwale-kwale daga wata tashar zuko ruwa ta hukumar samar da ruwan sha mallakar jihar kusa da tashar jirgin kasa da ke a lokacin da lamarin ya faru da su.

Bayan daliban su goma sun kammala ziyarar karo ilimin a tashar hukumar samar da ruwan ne sai suka hau kwale-kwale domin haye kogin.

Sai dai kwale-kwalen da suka hau din ya dare biyu domin yawan mutanen da ke kai, lamarin da ya sa daliban suka nutse.

Masu aikin ceto sun samu damar ceto biyar daga cikin daliban. An kuma samu gawarwakin biyu daga cikinsu yayin da har yanzu ake neman sauran gawarwakin.

Lamarin dai ya auku ne a ranar Laraba.

Shugaban kamfanin Samsung ya yi murabus


Ana dai zargin shugaban Samsung din da aikata cin hanciHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana dai zargin shugaban Samsung din da aikata cin hanci

Shugaban kamfanin kere-keren kayan lantarki na Koriya ta Kudu, Samsung, ya sauka daga mukaminsa.

Kwon Oh-Hyun, ya ce lokaci ya yi da kamfanin zai bude sabon shafi tare da matashin shugaba.

Hakan ya biyo bayan hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku da aka yi wa tsohon shugaban kamfanin, Jay Lee, a watan Agusta bisa laifin cin hanci da rashawa.

An dai sa ran Mr Kwon zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kamfanin.

Amurka da Isra'ila za su fice daga UNESCO


Amurka ta ce dalilai biyu ne suka sa ta yanke shawarar ficewa daga UNESCO

Image caption

Amurka ta ce dalilai biyu ne suka sa ta yanke shawarar ficewa daga UNESCO

Kasashen Amurka da Isra’ila sun sanar da ficewarsu daga hukumar bunkasa ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, saboda abinda su ka kira kin jinin da take nunawa Isra’ila.

Ma’aikatar hulda da kasashen wajen Amurka ta ce abinda ya kara mata kaimin ficewa shi ne dimbin bashin da UNESCO ke bin kasar, bayan da ta dakatar da ba da kudin tallafi shekaru shida da suka wuce saboda karbar wakilcin Palasdinawa da hukumar ta yi.

Piraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana matakin na Amurka a matsayin wani abin jarumta da kuma kare mutunci.

Shugabar UNESCO, Irina Bokova ta ce ba ta ji dadin matakin ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, janyewar za ta kankama a karshen shekara mai zuwa.

Nigeria: Ba za mu amince da kisan 'yan kasarmu a wata kasa ba


Gwamnatin Najeriya ta ce ba zata lamunci kisa da cin zarafin 'yan kasarta da ke kasashen waje baHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Gwamnatin Najeriya ta ce ba zata lamunci kisa da cin zarafin ‘yan kasarta da ke kasashen waje ba

Babbar jami’a mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin ‘yan kasar da ke zaune a kasashen waje, Honourable Abike Dabri, tace, an kashe ‘yan Najeriya hudu a cikin makwanni uku a Africa ta Kudu a hare-haren nuna kyama da ake kai wa ‘yan kasar a wasu kasashe.

Kalaman nata na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi a India su ka kama mutum biyar da ake zargi da lakadawa wani dan Najeriya dukan kawo wuka bisa zargin sata bayan wani hoton bidiyo da yayi ta yawo a intanet.

Abike Dabiri, ta ce tun bayan da suka samu labarin abinda ya faru da dan Najeriyar a India, suka tuntubi ofishin jakadancin Najeriyar da ke India, inda ya ce ana bibiyar lamarin har ma hukumomin kasar ta India sun fara daukar mataki.

Ta ce a yanzu haka an kama mutanen da ake zargi da hannu a kan wannan lamarin.

Babbar jami’ar ta ce sun bukaci kasar India da ta hukunta wadanda aka tabbatar suna da hannu a wannan aika-aikar da aka yiwa dan Najeriya domin sun dauki doka a hannunsu ne abinda kuma bai da ce ba.

Abike Dabiri ta ce daga shekarar 2015 zuwa yanzu an kashe ‘yan Najeriya 116 a Afirka ta Kudu, kuma fiye da rabinsu ‘yan sanda ne suka kashe su.

Don haka ta ce, gwamnatin Najeriya ba zata amince da kisan da ake yiwa ‘yan kasarta dake zaune a wasu kasashe ba, shi ya sa ta ke bukatar kasashen da ake cin zarafin ‘yan Najeriya a can da su rinka daukar matakan da suka dace a kan wadanda ke aikata laifin, koda kuwa jami’an tsaro ne.

Abike Dabiri, ta ce rashin hukunta masu aikata irin wannan laifin, shi ke sa ake cigaba da aikata laifin, amma da ana hukunta su yadda yakamata da za a samu raguwar aikata laifin.

Karnukan Amurka 'sun fi mutanen Najeriya' gata a asibitoci


A patient lies on their back in a radiotherapy machine in Khartoum.Hakkin mallakar hoto
AFP

Ikirarin: Kare a Amurka ya fi samun damar a yi masa gashin cutar sankara fiye da mutum a Najeriya.

Gaskiyar lamarin: Na’u’rorin kona kwayoyin cutar sankara da ake da su domin mutane a Najeriya ba su kai wadanda aka tanada domin karnuka a Amurka ba.

Amman sai dai dabbobi ‘yan lele masu dauke da cutar sankara a Amurka sun fi mutane masu cutar samun gata a Najeriya – kuma na’u’rorin kona cutar sankara da ake da su na dabbobi kawai sun fi na wadanda ake amfani da su gutanen Najeriya.

A watan da ya gabata ne, Sean Murphy ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sa da zumunta.

Dan kasuwar ya wallafa wani hoton kare da yake amfani da wata irin na’u’rar konaa cutar sankara, kuma ya ce irin wadannan na’u’rorin da ke yi wa karnukan Amurka magani sun fi wadanda suke yi wa ‘yan Najeriya magani.

Ya ce wannan na nufin kare a Miami ya fi wata mata a Legas damar samun maganin sankara. Maganar tasa ba ta zo wa mutane da dama da mamaki ba, amman duk da haka ta fusata su.

Amman da alamar gaskiya a ikirarin nasa? Shin karnukan Amurka sun fi ‘yan Najeriya damar samun na’u’rar kona sankara?

Kayan aiki

Ba ko wanne mai cutar sankara ke bukatar gasa sankara ba – akwai wasu nau’o’i na magani, irin su hanyar shan magani domin dakile cutar sankara.

Amman ikirarin Mista Murphy ya yi ne kan damar samun na’u’rar kona sankara, saboda haka bari mu tsaya a kan wannan na’urar kawai.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya tana da jerin sunayen wuraren da ke da na’u’rorin gasa sankara a fadin duniya.

Matattarar bayanan cibiyoyin na’urorin gasa sankara ta hukumar (Dirac) tana samun bayanai ne daga kasashe daban-daban. Amman a makon da ya gabata ne kawai aka tattara bayanai na baya-bayan nan.

Matattarar ta ce abun ya fi yadda Mista Murphy ya bayyana shi muni.

Nau’rorin gashi uku ne ke aiki a Najeriya a halin yanzu, kuma babu na zamani irin wanda Mista Murphy ya ambato a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Dirac ta ce a kan hada na’ura ta hudu a Abuja, kuma wannan din ma ba za ta kasance irin ta zamani da Murphy ya ambata ba.

Akwai karin na’u’rori da ake amfani da su wajen shirya ba da magani irin su na’u’rorin daukar hoton kashi.

Kuma Dirac ta ce babu wata cibiyar ba da magani da ta sani da take bai wa mara lafiya gashi kan dashe, wadda ita ce hanyar ba da maganin cuta irin sankarar mahaifa.

Babu tabbacin karin na’u’rorin nawa ne za a iya samu a asibitoci masu zaman kansu – amman jaridar The Nation ta ce wadannan sun fi karfin mara sa galihu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Yawan na’u’ro’rin ga mutane ya fi na Najeriya yawa sau tara a Kenya

Bayanai daga bankin duniya sun nuna cewar yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 186. Da zarar an kammala hada na’u’rar ta hudu, za a samu na’urar gashi daya ga mutum miliyan 46.5 a Najeriya.

Idan ma na’urori takwas da Najeriya ta ke da ita a shekarar 2010 suna aiki har yanzu – adadin mutanen da za su dogara da na’u’rar gashi daya zai kai mutum miliyan 23.2 .

A Kenya, akwai na’urar gashi daya ga mutum miliyan 5.4 million.

A Indiya kuma mutum miliyan 2.2 suna da na’ura daya, ga mutum 188,000 suna da na’urara gashi daya a Birtaniya yayin da mutum 84,000 ke da na’urara gashi daya a Amurka.

Ta yaya lamarin yake idan aka kwatanta da karnukan Amurka?

Kona cutar sankara a jikin maguna da karnuka

Muna son dabbobin lelen Amurka suna da damar samun na’u’rorin gashi fiye da na’urorin da ake da su a Najeriya – a shekarar 2010, wani bincike da Margaret McEntee da John Farrelly suka gudanar ya kirga irin na’urar gashin da ke Najeriya, a kalla 76 suna yi wa dabbobi hidima a fadin Amurka.

A gaskiya, wata matattarar bayanai da kungiyar likitocin cutar sankarar ta nuna cewa mai yiwuwa ne adadin na’urorin ya fi na adadin da aka sani yanzu.

Cibiyar cutar sankara ta Amurka ta ce akwai karnuka ‘yan lele miliyan 65 a Amurka.

Wannan na nufin cewa a kalla akwai na’ura daya ga maguna da karnuka miliyan 1.28 a Amurka.

Wa yake bukatar magani?

Amman kwatanta adadin na’urori da yawan mutane da dabbobi ka iya gaza taimakawa kan wannan batun.

Hakan ya faru ne saboda dabbobin lele sun fi mutane yiwuwar kamuwa da ciwon sankara.

Kimanin maguna da karnuka miliyan 12 suna kamuwa da cutar sankara a ko wacce shekara – wannan na nufin akwai na’urar gwaji ga karnuka da maguna 158,000 masu cutar sankara.

Alkaluma na baya-bayan nan daga Hukumar Lafiya ta Duniya sun ce an gane cewa mutum 102,100 sun kamu da cutar sankara a Najeriya cikin shekarar 2012.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dirac ta ce ana hada wata na’urara gashi a asibitin taryyar Najeriya ta Abuja – amman rashin na’ura ba sh8i kadai ne yake hana ‘yan Najeriya samun gashi na sankara a kasar.

Ga dabbobin lelen Amurka da mutanen Najeriya tsadar rayuwa wani abu ne da ke hana samun magani ko na’urorin na aiki.

Gashi ga dabbar lele ka iya kai kudi $10,000 – abun da kila ya sa binciken John Farrelly ya nuna cewa karnuka 1,376 dogs da maguna 352 aka yi wa gashi a Amurka a shekarar 2010.

Kazalika, wani bincike da aka gudanar a asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan ya nuna cewa takwas daga cikin masu cutar sankara goma a Najeriya ba za su iya biyan kudin gashi ba ba tare da taimako ba, inshorar gwamanti ba ta daukar nauyinsa.

Mun tambayi gwamnatin Najeriya ta yi tsokaci kan karancin na’urorin gashi masu aiki, amman har yanzu ba ta ce ko uffan ba.

A wani taro a Abuja da aka yi da farkon watannan, ministan lafiyar Najeriya, Isaac Adewole ya ce gwamantin kasar ta tsaya tsayin daka domin ganin ta dakile cutar sankara a Najeriya. Ya yi alkawarin cewa za a kara na’urori takwas zuwa sha biyu, amman ba bu tabbacin nawa ne daga cikinsu za su kasance na gashin sankara.

Samun na’urar kona cutar sankara mai aiki babbar matsala ce a fadin Afirka.

Matsalar Najeriya gagaruma ce domin a yanzu haka na’urorin kona cutar sankara uku kadai take da su da ke aiki a halin yanzu.Yadda giwar ruwa ke cin kwari miliyan 40 a rana


Giwar ruwaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Daga Ella Davies

11 ga Afirilun 2017

Tsananin son cin abinci da matsananciyar yunwa da galabaita. Daukacinmu akwai ranakun da mukan yi fama da yunwa, amma ko yunwarka ta kai ga bukatar cin ton hudu na halittar ruwa?

Batu na gaskiya, shudin hamshakin kifi (the blue whale) giwar ruwa ita ce babbar dabbar da ta fi kowace girma a duniya, inda ta sha gaban komai a zakuwar son cin abinci.

A kullum wannan kasurgumar dabba tana lakume kananan kwari miliyan 40, wadanda ake yi wa lakabi da kananan kifaye

Sai dai akwai sauran dabbobi da ke cin abinci ba na wasa ba, ta yadda wasunsu za su ba ka mamaki.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Denis-Huot/naturepl.com).

Image caption

Giwar Afirka (Loxodonta africana) abincin rana

Tamkar hamshakin shudin kifi, wannan katafariyar dabbar doron kasa tana cin abinci daidai da dundumemen jikinta.

A cewar kwararrun masana kan giwar Afirka, Norman Owen-Smith na Jami’ar Witwatersrand da ke Johannesburg a Afirka ta Kudu, inda namijinta ke lakume kaso guda cikin 100 na nauyinta a kan busasshen tundurkin kasa a ko wacce rana, yayin da ta-macen da ke shayarwa ke cin kashi 1.5 cikin 100 don su ci gaba da rayuwa.

Panda na cin abincin da nauyinsa ya kai kilo 12.5 na kwangwala ko wacce rana.

Namijin yana da nauyin ton 6, don haka abin da yake ci nauyinsa ya kai kilo 60 na busasshen abinci ba tare da an hada da yawan ruwan da ta kwankwada ba, al’amarin da ka iya nunkawa da rubi hudu.

Hamshakan dabbobi masu shayarwa kan shafe tsawon rana wajen kai-kawon cin korayen tsirran da ke ba su kuzarin rayuwa. Sukan iya shafe sa’o’i 18 suna cin abinci a rana, gwargwadon abin da ya samu.

Haka kuma hamshakiyar yanyawar Sin (Panda) kan shafe sa’o’i 14 tana gwagwiyar kwangwala.

Masu bincike sun yi nuni da cewa wanan abincin bai cika kosar da dabbobin ba, wadanda tsarrin sarrafa abincinsu na iya sarrafa ko wanne irin nau’in abinci, wanda da sarrafa dimbin tsirrai ba.

Wannan ke nuni da dalilin da ya sanya yanyawar Panda ke cin dimbin abincin da nauyinsa ya kai kilo 12.5 na kwangwala a ko wacce rana don samun isasshen abincin da suke bukata, kuma shi ne hujja da ke nuni da kimar kashinsu.

Daukacin maciyan tsirrai kan shafe tsawon lokaci suna bibiyar dimbin gayayyaki da itatuwa don samun isasshen abincin da zai ba su kuzari, yayin maciyan nama kan mayar da hankali kan kayan makwalashe (abincin da ake dafawa cikin gaugawa).

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Visuals Unlimited/naturepl.com)

Image caption

Jemage mai launin ruwan kasa (Myotis lucifugus)

Brock Fenton na Jami’ar Western da ke Canada ya ce adadin an “zuzuta shi,” sakamakon rudanin da aka samu a tsakanin nau’ukan binciken biyu mabambanta da aka gudanar kan nau’ukan jemage a shekarun 1950.

Nau’ukan jemagen Japan kan shirya shirin cin abinci na gaba kafin ma ya lakume wanda ke gabansa.

Fenton ya ce daya daga binciken da aka gudanar ya yi nazari ne kana bin da ke cikin jemage mai launuka uku bayan ya gama cin abinci, yayin da dayan kuwa ya bi kadin nau’ukan jemage kananan masu launin kasa-kasa a dakin binciken kan yadda yake kama sauraye da kudajen da ke zarya kan ‘ya’yan itace.

Babu daya daga cikin binciken da ya bayar da adadin na gaskiya kan yawan kwarin da karamin jemage mai launin kasa-kasa ke lakumewa a daji.

Kuma karamin jemage mai launin kasa-kasa na cin dimbinci ba wai sauraye kadai ba: sun ma fi son abubuwan masu girma, kamar tsutsotsi, a duk lokacin da suka samu damar kama su.

Wani bincike da aka gudanar kan jemagu a kasar Canada ya yi nuni da cewa sauraye wani yanki ne kadan daga abincinsu.

Don haka ta yiwu fadadawa aka yi cewa suna iya lakume sauro a ko wacce dakika 3.6.

Sai dai akwai hujjar da ke nuni da cewa ire-iren jemagu sukan kara kaimin farautar abincinsu doin samun gwargwadon abin da ya wadata da suke ci.

A shekarar 2016 bincike ya nuna cewa Jemagun Japan kan shirya cin abinci na gaba kafin ma su lakume wand ake gabansu.

Sabanin yadda ake ganin tashinsu, jemagun kan tsara shawaginsu bisa la’akari da irin abin da za su iya sura a hanya.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Artur Tabor/naturepl.com)

Image caption

Karamar jabar dawa- A pygmy shrew (Sorex minutus)

Akwai sauran kananan kasa-kasan dabbobi masu shayarwa wadanda ke cin abinci babu kakkautawa: nau’ukan jabar daji (the shrews).

A kalla ko wacce tsiryar Amurka hummingbird na lakume sukarin da ya kai rabin nauyinta a ko wacce rana.

Jabar dawan da aka sani dole ta ci abin da ya yi daidai nauyinta da kashi 80 zuwa 90 cikin 100 a tsakanin sa’o’i 2 zuwa 3.

Karamar jabar dawa, wadda ta kai rabin girman ‘yar uwarta tana cin kashi 125 cikin 100 na abincin da ya kai nauyin jikinta a kowace rana.

Irin wadannan dabbobi masu shayarwa suna da saurin sarrafa abinci, al’amarin da ke nuni da cewa nan take zai narke ya ba su kuzari cikin hanzari.

Don haka sai sun ci abinci akai-akai dibge da abinci mai kara lafiya na protein da dabbobi masu kasha ke ci ko yunwa ta halaka su.

Duk wata tattaunawa kan sarrafa abinci to za ta bi kadin tsiryar Amuyrka (hummingbirds).

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Mike Potts/naturepl.com)

Image caption

Kudan tsiryar Amurka (A bee hummingbird) (Mellisuga helenae), tsaikon wucin gadin tsakanin lokutan cin abinci

Wadannan halittu masu tashin ban mamaki sun fi shan zakin sukari don samun kuzarin tashi. Sukan bubbuka fuka-fuklinsu sau 50 a kowace dakika, irin wadannan tsuntsaye sun fi saurin sarrafa abinci a jerin dabbobi masu kashi.

Ta yiwu ka ji labarin cewa akalla tysiryar Amurka na lakume zakin sukari da ya kai kimar rabin nauyin jikinta a kowace rana, inda take cin abinci bayar kowane minti 15 a furannin kallo.

Akan sarrafa dimbin sinadarin kuzari da ke tare don bunkasa karamin dan tayi zuwa tsutsar siliki.

“Yawan zakin furen kallo da tsiryar Amurka ke lakumewa na iya bambanta,” a cewar Adam Hadley, ja-gaban masu binciken tsiryar Amurka (hummingbird) a Jami’ar Jihar Oregon.

“Musamman tunda suna da mabambanta girman jiki, wanda ya kama daga giram 2.5 na kudan tsiryar Amurka (bee hummingbird) zuwa babbar tsiryar (giant hummingbird).”

Yayin da manya ke kwankwadar dimbin zakin furanni, suna sarayar da makamashin kuzarinsu ne a hankali fiye da kananan tsuntsaye. Wannan na nuni da cewa, in an kwatanta, kananan halittu sun yi fama da matsananciyar yunwa.

Hadley ya ce tsuntsaye na adana makamashi har zuwa lokacin da suka bukaci amfani da shi. “Abin sha’awar shi ne yadda suke adana abin da ya kai kashi 17 cikin 100 na nauyin jikinsu na maiko, ta yadda za ta kasance kowace tsiryar amurka za ta yi amfani da 30lb a rana guda.”

Sauran nau’ukan halittu na nuni da cin abincin ban mamaki a wani yanayin lokaci na rayuwarsu. Alal misali, akwai bukatar dimbin makamashin kuzari don bunkasar dan-tayi zuwa tsutsar siliki.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Barry Mansell/naturepl.com)

Image caption

Kwarin tsutsar siliki (Antheraea polyphemus)

Kwaron tsutsar siliki (The Polyphemus moth) an yi masa lakabi ne da sunan gwarazan Girkawa da Homer ya bijiro da su a labaran ban mamaki, saboda a kowane fufffike yana da alamar kwayar ido.

Sai dai daukacin halitta mai cin mutum da tsutsa mai lakume tsirrai abu guda ne wajen zakuwar son cin abinci da yawa.

Don mu kamo tsutsa, sai mun rika cin abincin da nauyinsa ya kai laba 50 zuwa 200 na latas a kowace rana.

Kamar yadda Kundin shahararrun al’amuran duniya Guinness ya tattara cewa, kwaron tsutsa irin “caterpillar” na cin abincin da nauyinsa ya rubanya na jikinta sau 86,000 a kwanaki 56.

Amma Andrei Soirakov jagoran masu tattara bayanai a gidan kayan tarihin albarkatun kasa na Florida cewa ya yi, akwai tababa kan adadi.

Wanan kawai tamkar ka auna abin da mutum ke ci ne tsawon rayuwar yarintarsa, sannan ka kwatanta shi da nauyinsu a lokacin da suke kamar jariri sabuwar haihuwa.

Sourakov ya ce aikin da aka gudanar kwanan nan a Jami’ar Florida ya gano cewa kwaron luna, wanda yake kwatankwacin girin irin wadannan halittu, kawai suna cin abin da ya kai rabi ko biyu bisa uku na nauyin jikinsu a ko wacce rana.

“Har yanzu dai lamarin da kayatarwa,” inji Sourakov. “doin su yi daidai da kwaron tsitsar ‘caterpillar’ to sai mun ci laba 50 zuwa 200 na latas kowace rana.”

Karara yake, a cewar Eric Carle yunwar kwaron tsutsar caterpillar ta shahara ba kai makurar da ake nuni da ita ba.

Dabba ta karshe da muke bin kadin tsananin yunwarta a duniya ba lallai su kasance mashahuran abubuwan da ake nuni da su a littattafan labarai na yara.

Ko da yake yanayin cina bincinsu na musamman an tattaro shi ne don ceton rayuwar mutane, inda aka siffanta su da dodanni masu ban tsoro.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Willem Kolvoort/naturepl.com)

Image caption

Tsutsa mai shan jini (Hirudo medicinalis)

Ana amfani da tsutsotsi masu zukar jini don warkar da gyambo karnoni da dama. Sai dai mafi yawan nau’ukan tsutsotsin 700 suna lakume halittu marasa kasha, wato tamkar yadda tsutsar tsibirin Borneo mai ban tsoro ke farauta.

Jagoran nazarin tsutsa mai shan jini ya taba ganin “hamshakiyar” tsutsar da aka tsareta, inda take samun abinci ba tare da sun cutar da kowa ba.

“Manyan tsitsotsin da na taba gani samfuran manyuan tsutsotsin dajin Amazon ne da ake yi wa lakabi da ‘Haementeria ghilianii’ da bajimin tsutsar Asiya mai lakabin Hirudinaria manillensis,” in ji Siddall.

Ya kara da cewa, “Wadannan daidaikun tsutsotsin babu tantama su suka fi zukar jini.”

Sai dai a daji, damar samu ke da tasirin kan son cin abinci.Tsutsotsin kungurmin daji sun yi kankanta da farauta, don haka suke jiran abin da za su iya lakumewa ya kawo kansa.

Saboda tsawon jiran da suke yi, ba abin mamaki ba ne su yi ta hadama su cika cikinsu da zarar dama ta samu sai su ci har girmansu ya rubanya nauyin jikinsu sau bakwai bayan sun kwankwadi jini.

Wannan shi ne isasshen abin da kowane zai lakume.

Shiga rukunin mutum fiye da miliyan shida da ke sha’awar shirin BBC kan doron kasa, ta hanyar latsa maballin kauna a shafinmu na Facebook ko a bniyo mu a shafinmu na Twitter da Instagram.

Falasdinu: Hamas da Fatah sun sasanta


Kungiyoyin Hamas da Fatah sun sanya hannu kan yarjejeniyar sasanta tsakaninsu a birnin Alkhahira na kasar Masar, a wani yunkuri na kawo karshen barakar da ke tsakaninsu.

Masar, wadda ta karbi bakuncin tattaunawar, ta ce hukumomin Falasdinawa da ke samun goyan bayan Fatah, za su karbe dukkanin aikace-aikacen gudanarwa a zirin Gaza daga hannun kungiyar Hamas, kama daga ranar 1 ga watan Disamba.

Har ila yau za a mika mashigar Rafa daga Gaza zuwa Masar nan ba da jimawa ba ga ikon wata gwamnatin hadin-kai.

Kasar Masar ce ta jagoranci tattaunawar sulhu tsakanin kungiyoyin biyu a birnin Alkhahira, inda yanzu kuma kungiyar Falasdinawa ta Hamas ke cewa ta cimma yarjejeniyar sulhu da abokiyar hamayyarta wato Fatah, domin kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu a tsawon fiye da shekara 10.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hamas tana iko da Gaza ne yayin da Fatah ke iko da gabar yamma da kogin Jordan

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya ce wannan yerjejeniyar ita ce tattaunawar zaman lafiya ta karshe tsakanin kungiyoyi biyun da basa ga-majici-da-juna.

A watan da ya gabata ne dai kungiyar Hamas ta ce ta soke kwamitin da ke gudanar da yankin Gaza tare da mika ikon yankin ga gwmanatin Fata a gabar yammacin kogin Jordan.

Kungiyar Hamas dai ta karbe ikon yankin Gaza ne, yayin da takwararta ta Fatah take iko da gabar Yammacin Kogin Jordan bayan mummunan fadan da suka yi a shekarar 2007.

Rikicin ya barke ne bayan Hamas ta samu nasarar lashe zabe.

Zakaria al-Agha wani babban jami’in kungiyar Fatan ne, a yankin zirin Gaza ya kuma tabbatar da cewa an kulla yarjejeniyar.

Ya ce: “Mun cimma yarjejeniyar danganen da duka abubuwan da muka tattauna a kansu a wannan tattaunawar da aka yi a a kasar Masar yau da safe.”

Ya ci gaba da cewa: “Kuma mun cimma matsaya akan ilahirin bambance-bambancen da ke tsakaninmu.”

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Firayim ministan Falasdinawa, Rami Hamdallah (a dama) ya rike hannun shugaban kungiyar Hamas a Gaza, Ismail Haniyeh

Mista Al-Agha ya ce yana fatan Shugaban Falasdinwa Mahmoud Abbas zai ziyarci yankin Gaza a cikin wannan watan, bayan shafe shekera goma ba tare da ziyartar yankin ba.

Ya ce: “Ina fatan idan Allah Ya yarda a samu yin wata tattaunawa da za ta hada shugabanin duka bangarorin biyu a kasar Masar, zuwa karshen watan nan, bayan haka kuma da yardar Allah a cikin wannan watan Mahmud Abas ya ziyarci yankin zirin Gaza.”

An dai raba Falasdinawan da ke zaune a zirin Gaza da wadanda ke zauni a gabar yamma da Kogin Jordan da juna ne tun lokacin da rikici ya barke tsakanin kungiyoyin biyu a shekarar 2007 wanda kuma ya haddasa asarar rayuka.

Tun shekarar 2006 ne dai kasar Masar da Isra’ila suka rufe kan iyakokinsu da yankin na Gaza.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Falasdinawa sun yi murnar sanarwar sasantawar

Isra’ila dai na matukar adawa da shigar kungiyar Hamas cikin gwamnatin Falasdinawa.

Tana mai daukar kungiyar ta Hamas a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, inda ta ce ba za ta tattauna da gwamnatin Falasdinawa wacce ke kunshe da ‘yan Hamas a cikinta.

Mazauna zirin Gazan dai na fatan yarjejeniyar za ta saukaka harkokin kan iyaka tare da kawo habakar tattalin arziki.

Scotland ta raba-gari da kocinta Gordon Strachan


Hakkin mallakar hoto
SNS

Image caption

Scotland ta raba-gari da Gordon Strachan

Gordon Strachan ya bar mukaminsa na kocin Scotland bayan da suka cimma matsayar amincewa tsakaninshi da kungiyar.

An yanke shawarar ne tare da hadin gwiwar hukumar kwallon kafa ta Ingila, bayan da kasar ta kasa zuwa manyan wasannin kasa-da-kasa guda biyu a jere.

Strachan da mataimakinsa Mark McGhee sun sauka daga mukamin ba tare da bata lokaci ba.

“A madadin hukumar ina mika godiya ga Gordon a kan jajircewarsa a kungiyar”. In ji shugaban hukumar Stewart Regan.

A watan Janairun 2013 ne aka nada Strachan a matsayin kocin kungiyar, wanda ya maye gurbin Craig Levein a matsayin wanda zai taka rawa da kuma sa ido a wasan neman shiga gasar duniya ta 2014.

Kun san kasashen da 'yan mata ke wahalar samun ilimi?


South SudanHakkin mallakar hoto
Unicef

Image caption

An saka sunan Sudan Ta Kudu a matsayin wurin da ya fi muni a duniya a bangaren ilimin mata

Galibin muhawara da ake yi game da makarantu a kasashen da suka ci gaba ana yi su ne a kan siyasar me ya kamata a fi bai wa muhimmanci, wadanne darussa za a fi bai wa muhimmanci, wa yake da bukatar karin taimako, kuma wanne bangare ne ya fi bukatar gwamnati ta fi kashe wa kudi.

Sai dai ga iyalai da dama a yawancin kasahen da suka ci gaba, batun ilimi bai ma kai haka ba, to babbar tambayar ma ita ce ko ana samun damar zuwa makarantar?

Alkaluma daga Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, ba a samu wani ci gaba ba a shekara 10 da suka shude wajen yaki da rashin guraben karatu a wasu kasashen da suka fi talauci a duniya.

Wani rahoton kuma ya bayyana darajar ilimi, kuma MDD ta ce abin da aka gano din, da kusan sama da yara miliyan 600 ne suke makaranta amma ba sa koyar komai.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A Nijar hudu daga cikin mata biyar ba sa makaranta

Ko da yake a wasu kasashen yamma, mata sun sha gaban maza a karatu, amma a yankin kasashen da ba su da arziki a duniya, musamman yankin Saharar Afirka, alamu sun nuna ba lallai ne mata su samu damar karatu ba.

Yankunan da ake rikici

A fadin wadannan kasashe 10, yawanci daga cikin wadanda ba su da gurbin karatu yara mata ne.

Wadannan kasashe ne masu rauni, inda iyalai da dama ke fuskantar talauci da rashin lafiya da rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin matsugunni sakamakon yaki da tashin hankali.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Rikici ya raba wasu da muhallansu a Sudan Ta Kudu

Yara mata da dama sun fi yin aikatau maimakon su tafi makaranta. Kuma yawanci an fi aurar da kananan yara, inda daga karshe ba z asu samu damar yin karatu ba.

Alkaluman MDD sun nuna cewa yara mata da dama ne ke fuskantar barazanar rashin samun ilimi a yankunan da suke fuskantar rikici.

Hakkin mallakar hoto
Unicef

Image caption

rikici ya ruguza ilimin gomman miliyoyi a Chadi

A wasu kasashe irin su Siriya, babu isassun bayanai daga majiya mai tushe daga wurinsu da za a saka su a cikin lissafi.

Wadannan ne kasashe 10 da yara mata suke fuskantar barazanar ilimi:

1. Sudan Ta Kudu: Ita ce kasar da ta fi ko wacce fuskantar rikici a duniya, da rushe makarantu da kuma raba iyalai da muhallinsu, kusan kashi daya bisa uku na yara mata a kasar ko makarantar firamare ba sa zuwa.

2.Jamhuriyar Tsakiyar Afirka: Dalibai 80 ne a karkashin malami daya

3.Nijar: Kashi 17 cikin 100 na mata tsakanin shekara 15 zuwa 24 ne kawai suka yi karatu.

4.Afghanistan: Akwai tazara mai nisa tsakanin maza da mata domin maza sun fi mata zuwa makaranta.

5.Chad: Abubuwa da dama da suka hada da talauci na hana mata da ‘yan mata samun ilimi

6.Mali: Kashi 38 cikin 100 na mata ne kawai suke kammala karatun firamare

7.Guinea: Lokacin da mata da suka haura shekara 25 ke amfani da shi wajen koyon ilimi bai wuce shekara daya ba

8.Burkina Faso: Kashi daya cikin 100 na mata ne kawai suke kammala makarantar sakandare

9.Liberia: Kusan kashi daya bisa uku na shekarun ‘yan firamare ba sa zuwa makaranta

10. Habasha: Mata biyu daga cikin biyar suna yin aure kafin shekara 18

Karancin malamai ya zama ruwan dare a kasashen da suke fama da talauci.

A bara ma, MDD ta ce ana bukatar wasu malamai miliyan 69 a fadin duniya zuwa shekarar 2030, idan har alkawuran da kasashe suka yi a kan ilimi ya tabbata.

Image caption

Florence Cheptoo ta koyi karatu tana da shekara 60, lokacin da jikokinta suka kai littattafan dakin karatu gida

Rahoton ya ce akwai bukatar karkasa tattalin arziki muddin ana so yara mata su je makaranta.

Kuma ko wanne zai samu kaso mai gwabi, kamar su Florence Cheptoo, wacce ta zauna a wani kauye mai nisa a Kenya kuma ta koyi karatu tana da shekara 60.

Gayle Smith shugaban wata kunigyar fafutuka, ya ce: “Sama da yara mata miliyan 130 ne yanzu haka ba sa zuwa makaranta, kuma a cikinsu za a iya samun injiniyoyi da malamai da manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da zasu shugabanci duniya.”

Nigeria: 'Yan sanda za su tuhumi Davido kan mutuwar abokinsa


DavidoHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Davido shahararran mawaki ne a Najeriya

‘Yan sanda a Najeriya za su gayyaci mawakin zamanin nan David Adedeji Adeleke da aka fi sani da Davido, don tuhumarsa kan mutuwar abokinsa Tagbo Umeike.

Tagbo Umeike ya mutu ne ranar 3 ga watan Oktoba, kuma ba a gane musabbabin mutuwarsa ba duk da cewar bincike ya nuna cewa ya mutu ne sakamakon shake shi da aka yi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Olarinde Famous-Cole, ya ce rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga Davido da ‘yan uwansa da kuma abokan Tagbo Umeike su bayyana a gaban ofishin ‘yan sandan.

Famous-Cole ya shaida wa BBC cewa: ”Abin da muke yi yanzu shi ne muna son mu san tare da waye Tagbo yake kuma ina ya je ranar da ya mutu?”

”Wani hoton bidiyo da wasu bayanai sun fito kuma a yanzu muna kiran sauran mutane ciki har da Mista Adeleke domin tambayoyi saboda mu gane hakikanin abun da ya faru.”

‘Yan sanda sun ce wannan wani bincike ne da ake ci gaba da yi, kuma ba za su iya kara bayani game da ko Davido na da hannu a ciki ko babu ba, har sai an samu kwararan hujjoji game da abin da ya kashe Mista Tagbo.

Har wa yau wani abokin Davido, Olugbemiga Abiodun, DJ Olu ya mutu kwanaki bayan mutuwar Tagbo.

‘Yan sanda sun ce da ‘walakin goro a miya’ dangane da mutuwarsa ba.

Sun samu gawar DJ Olu da Chime Amechina a cikin mota a wani gareji karkashin kasa a unguwar Ikoyi.

Davido ya wallafa sakonnin juyayin rasuwar abokanan nasa a shafin Instagram.

‘Yan sanda sun ce in suka kammala bincike, za su sanar da mutane hakikanin abin da ya faru.

Zainab Bulkachuwa: Me ku ke son sani kan shugabar kotun daukaka kara ta Nigeria?


Zainab Bulkachuwa

Image caption

Zainab Bulkachuwa ce macen da ta fara dare wannan mukami a Najeriya

Justice Zainab Bulkachuwa ita ce shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, kuma ita ce mace ta farko da ta rike wannan mukamin a kasar.

Me ku ke so ku sani game da ita, da tarihinta da gwagwarmayar da ta sha da kuma ayyukanta?

BBC Hausa za ta tuntubeta a madadinku don ta amsa tambayoyin naku.

Dan wasan Arsenal, Mustafi, zai yi jinyar mako shida


MustafiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mustafi ya fice daga wasan karshe na neman shiga gasar cin kofin duniya da Jamus ta buga ne da dingishi

Dan wasan bayan Arsenal, Shkodran Mustafi, ba zai buga wa kungiyar kwallon kafar wasa ba na mako shida bayan ya ji ciwo acinya, in ji kociyan Gunners Arsene Wenger says.

Dan wasan dan asalin Jamus mai shekara 25 ya fice daga fili ne da dingishi bayan ya ji ciwo kafin a ba da hutun rabin lokaci a wasan da kasar mai rike da kofin kwallon kafa na duniya ta kammala wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya dinta da nasarori ta hanyar lallasa Azerbaijan 5-1 ranar Lahadi.

“Za mu rasa Mustafi na tsawon mako hudu ko shida,” in ji kociyan Gunners, Arsene Wenger.

“Ba na tunanin zai iya buga mana wasa kafin a sake ba da hutun bai wa ‘yan wasan damar taka wa kasashensu leda.”