Pogba da Ibrahimovic za su buga wasan Newcastle


Ibrahimovic and PogbaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zlatan Ibrahimovic da Paul Pogba suna cikin ‘yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa yayin da United lashe kofin Europa

Zlatan Ibrahimovic da Paul Pogba za su taka leda a wasan da Manchester United za ta kara da Newcastle ranar Asabar, bayan kammala doguwar jinyar raunin da suka ji.

Ibrahimovic, mai shekara 36, bai buga wasa koda daya ba a kakar bana saboda raunin da ya samu a gwiwa a watan Afrilu.

Pogba, mai shekara 24, shi ma ya fara jinya ne a watan Satumbar wanda kuma tun daga lokacin rabonsa da ya taka leda.

Hakazalika dan wasan bayan United, Marcos Rojo, zai buga wasan na ranar Asabar kuma kocin kungiyar Jose Mourinho ya ce “duka ‘yan wasan uku ne zai yi amfani da su”.

Rojo ya ji rauni ne a wasan da Ibrahimovic ya samu rauni wato a wasan kungiyar da Anderlecht a gasar Europa.

Karanta wadansu karin labarai

Buhari zai kashe naira biliyan daya a tafiye-tafiye a 2018


Shugaba Buhari na mika kasafin kudiHakkin mallakar hoto
Nigeria presidency

Image caption

Buhari ya ce yana son amfani da kasafin kudin wajen inganta rayuwar al’umma

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana shirin kashe kimanin naira biliyan daya a badi wajen tafiye-tafiye, kamar yadda daftarin kasafin kudin kasar wanda ofishin kula da kasafin kudin kasar ya bayyana.

Kamar yadda hukumar ta ce shugaban zai kashe naira miliyan 751.3 wajen tafiye-tafiyen kasashen ketare, yayin da zai kashe naira miliyan 250.02 wajen tafiye-tafiyen cikin gida.

Haka zalika daftarin kasafin kudin ya bayyana cewa za a kashe naira miliyan 907 wajen sayen sabbin motoci da kuma sayo kayayyakin gyaransu a shekarar 2018.

Har ila yau za a sayi tayoyin motoci masu silke a kan naira miliyan 83.77 da sauran motoci da motocin daukar marasa lafiya da sauransu.

Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo zai kashe jimullar naira miliyan 301.04 a kan tafiye-tafiye.

A makon jiya ne Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.6 ga majalisar dokokin kasar.

A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin naira tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai.

Ya kara da cewa Najeriya tana hasashen cewa za ta sayar da gangar mai sama da miliyan biyu a ko wacce rana.

Mugabe ya bayyana a karon farko bayan 'kwace masa mulki'


Mugabe da GraceHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Har yanzu ba a san inda Grace Mugabe take ba

Shugaba Robert Mugabe ya bayyana a gaban al’umma a karon farko tun bayan da sojoji suka kwace ikon kasar a ranar Laraba da safe.

A ranar Juma’a ne aka ga Shugaba Mugabe na tafiya kan jar darduma sanye da kayan bikin kammala karatun digiri, inda ya shiga cikin taron daliban jami’a da ke bikin kammala karatu suna kuma rera taken kasar.

Wannan abu ne da dama Mista Mugabe ya saba yi duk shekara, sai dai ba a yi tsammanin zai yi hakan ba a bana, saboda yadda sojoji suke masa daurin talala tun ranar Laraba.

Har yanzu dai Janar-Janar din sojojin suna tattaunawa da Mista Mugabe kan yiwuwar ya yi murabus, don kawo karshen takun-sakar siyasar da ta yi kamari a kasar.

Da sanyin safiyar Juma’a ne rundunar sojin ta ce tana samun ci gaba wajen hakon masu laifi da suke zagaye da Mista Mugabe.

Wasu masu sa ido sun ce har yanzu Mugabe mai shekara 93, yana son ci gaba da mulkinsa.

Babban dalilin da ya sa har yanzu sojojin ke bin sa ta ruwan sanyi, shi ne ganin yadda za a iya samun sarkakiya da kuma tafiyar hawainiya a tattaunawar.

Dortmund ta dakatar da Aubameyang


DortmundHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallo 31 a wasa 32 a gasar Bundesliga da ya buga a bara

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang a matakin da ta dauka na ladabtar da shi.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Gabon ba zai buga wa Dortmund wasan Bundesliga da za ta fafata da VFB Stuttgart a ranar Juma’a ba.

Dortmund ta sanar da dakatar da dan kwallon mai shekara 28 bisa mayar wa da wani magoyin baya martani da ya yi tambaya a shafin sada zumunta na Twitter, amma kungiyar ba ta fayyace komai ba.

A bara ma sai da Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang, bayan da ya je Italiya ba tare da sanin kungiyar ba.

Wasa ya fara juya wa Dortmund baya, inda ta yi rashin nasara a fafatawa uku daga hudu da ta yi kwanan nan a Bundesliga ta kuma koma ta uku a kan teburin gasar bana.

Za'a ba wa kare lambar yabo


Kare Mally ya taka muhimmiyar rawa a yakin AfghanistanHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kare Mally ya taka muhimmiyar rawa a yakin Afghanistan

A yau ne wani kare da ya samu horon soji wanda kuma ya yi matukar taimakawa wajen ceton rayukan sojoji a Afghanistan zai karbi babbar lambar yabo wadda Burtaniya zata bayar ga dabbar ta yi namijin kokari a wani fada ko yaki.

Karen mai suna Mally, za’a bashi lambar yabon ne da aka yiwa lakabi da Dickin.

A shekarar 2012 Mally, wanda aka yi masa horo a kan yadda zai gano abubuwan fashewar da aka binne ko aka boye dama abokan gaba ya fara aiki da dakaru na musamman daga Burtaniya da Afghanistan domin fatattakar masu tayar da kayar baya na kungiyar Taliban daga wani gini a Kabul.

Sau biyu dai Mally na samun rauni bayan da ya shiga wuta a dalilin aiki inda ya je hutun jinya, bayan ya warke kuma ya dawo bakin aiki.

Mece ce makomar Robert Mugabe bayan kwace masa iko?


Robert MugabeHakkin mallakar hoto
AFP/Getty

Image caption

The military still refers to Robert Mugabe as “his excellency, the president”

Bayan da ya shafe shekara 37 kan mulki a Zimbabwe, a yanzu an yi wa Robert Mugabe daurin talala bayan da sojoji suka kwace iko a kasar.

Jamian diplomasiya daga kasashen Afrika ta kudu da wani limami cocin a Zimbabwe na kokarin shiga tsakani domin yin sulhu tsakaninsa da sojojin kasar. Shin ko me nene makomar shugaba Mugabe da kuma Zimbabwe ? Ga dai wasu abubuwa da ake ganin zasu iya faruwa.

1:Mugabe ya yi murabus

Bayan wasu sa’oi da Manjo janar Sibusiso Moyo ya yi shellar cewa sojoji sun kwace iko a gidan talibiji na gwamnati, an dinga jita-jitar cewa shugaba Mugabe me shekara 93 shi ma zai yi wa alummar kasar jawabi, inda zai sanar cewa ya yi murabus.

Wannan dai be gamsar ba , amma ana ganin abu ne da zai iya faruwa. Haka kuma wannan zai ba tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa damar dare wa kan kujerar shugaban jamiyyar Zanu-PF me mulki. An yi ammanar cewa korarsa da aka yi a makon daya gabata, ita ce dalilin daya sa sojoji kasar suka dauki wannan mataki.

2: Mugabe ya ci gaba da zama kan mulki

Kawo yanzu sojoji na cigaba da kiran Robert Mugabe, “your excellency shugaban kasa”.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Daily life goes on in Harare, despite the military takeover

Da dama daga cikin sojojin kasar da kuma ‘ ya yan jamiyyar Zanu-PF me mulki na goyon bayan shugaba Mugabe .

Ba su da matsala da shi, sai dai ba su gamsu da abinda suka dinga gani ba, watau yunkurin karbe iko na matarsa, Grace wadda take son ta gaje shi.

Wakilin Zanu- PF a Birtaniya, Nick Mangwana ya shaidawa BBC cewa Mr Mugabe zai cigaba da rike mulki har sai bayan an kamala babban taron jamiyyar da zaa yi a watan Disemba mai zuwa, a lokacin da watakila zaa rantsar da Mr Mnangagwa a matsayin shugaban jamiyyar da kuma na kasa.

Sai dai kamfanin dilanci labaru na Reuters ya ruwaito cewa shugaba Mugabe ya nanata cewa zai kamala sauran wa’adinsa kan mulki. Wannan zai ba shi damar tsayawa har sai bayan zaben shugaban kasa da za a yi a badi.

3. An tilastawa Mugabe gudun hijira

Shin ko me nene zai faru idan ‘ya yan jamiyyar Zanu PF suka kasa cimma matsaya? Toh watakila hakan zai sa shugaba Mugabe ya yi gudun hjira.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

The army is still present on the streets of Harare

Makobciyya Afrika ta kudu za ta iya kasance wurin da zai iya samun mafaka, sai dai lamura sun sauya a baya baya nan.

Ana girma Mr Mugabe a Afrika ta kuduun, saboda rawar da ya taka wajen kawarda da mulkin wariyar launin fata.

Tuni jamiyyar adawa ta EFF ta nemi gwamnati kasar akan ta shirya wajan yi masa “maraba idan ya nemi mafaka”.

Rahotani sun ce iyalin Mugabe sun malaki kadarori a Afrika ta Kudu.

Sai dai tambayar a nan ita ce shin ko ya makomar Grace matarsa zata kasance?

An dai bata damar amfani da rigar kariya ta diplomasiya game da zargin cin zarafin wata mata me talata kayan kawa a wani otel a watan Augustan daya gabata a birnin Johannesburg.

Sai dai Gabriella Engels na kokarin ganin cewa ta jingine rigar kariyar, kuma wannan na nufin cewa Grace Mugabe za ta iya fuskantar sharia idan ta nemi mafaka a Afrika ta kudu.

Shin ina zata je , ban da Afrika ta kudu?

Watakila ta je Singapore ko Malaysia, wadanda kasashe ne da iyalin Mugabe suke da kadarori.

4. Gwamnatin hadin giwa da kuma zaben shugaban kasa

Jogoran yan adawa na jamiyyar MDC- Morgan Tsvangirai ya koma Harare bayan ya dawo daga jinyar da ka yi masa kan cutar sankara a kasar Afrika ta Kudu, abinda ya kara ruruta rade radin da ake yi a kan cewa watakila za a yi tattaunawar kafa gwamnatin hadin giwa.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty

Image caption

Morgan Tsvangirai is back in Harare

Ana dai ganin kasashen yama da dama da kuma ‘yan adawa zasu amince da wannan mataki.

Wani jagoran yan adawa, Tendai Biti ya ce zai siga cikin jamiyyar hadin gwiwar idan Mr Tsvangirai na ciki.

5: Shin Mugabe ya sauya hali ne?

Sa dai ikon da sojoji suka kwace, ba wai ya na nufiin an samu sabuwar gwamnati bace. Takarddama ce ta cikin gida tsakanin ‘ya yan jamiyyar Zanu-PF kuma har yanzu ita ce take rike da mulki a kasar.

Haka kuma ana ganin rundunar sojin kasa kamar wani reshe ne na jamiyyar ta Zanu-PF.

Kuma mutumin da suke marawa baya, Emmerson Mnangawa ya taimaka ma Robert Mugabe wajan aiwatar da wasu sauye sauye da suka rika janyo ce-ce ku -ce.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Emmerson Mnangagwa is the man the military wants to take over

Wasu sun ce ya fi shugaba Mugabe rashin mutunci.

Kawo yanzu dai ba bu cikakken bayyani kan ko idan an kifar da gwamnatin Mugabe, hakan zai inganta rayuwar yan kasar.

6: Mugabe ya maida martani kan juyin mulki da aka yi masa

Jamian tsaron da ke gadi fadar shugaban kasa na cikin sojojin da ke yiwa Mugabe biyaya.

An yi wa wurin da suke zama kawanya lokacin da sojoji suka kwace iko.

Sai dai a wani mataki da ba kasafai ake gani ba, masu rike da mukaman janarar janarar ne suka jagoranci karbe iko a Zimbabwe

Wasu manyan kusoshii 90 a rundunar sojin kasar suka tsaya tare da Gen Contantino Chiwenga a makon daya gabata lokacinda ya yi gargadi a kan abubuwan da kan iya biyo baya game da korar

da aka yiwa Mr Mnangagwa

'An mayar damu saniyar ware' — Niger Delta


'Yan yankin Neja Delta sun ce rashin tsayayyun shugabanni a yankin na musu matukar illaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan yankin Neja Delta sun ce rashin tsayayyun shugabanni a yankin na musu matukar illa

Wasu Shugabannin a yankin Neja Delta na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da barazanar da wasu masu tada kayar baya a yankin suka yi cewa zasu koma farfasa bututan mai a yankin.

Farfesa Akasoba Zainab Duke-Abiola, matar wani basarake ce a yankin, kuma shugabar wata kungiyar wanzar da zaman lafiya a Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, duk da kundin tsarin mulkin kasa ya basu damar su yi bore, ai bai ba su damar su tayar da hankalin jama’a ba.

Ta ce abin da ta ke gani ya harzuka masu tayar da bayan har suka yi wannan barazana shi ne, saboda ba a kula da su, an mayar da su saniyar ware tamkar baki a cikin kasarsu.

Farfesar ta ce, duk wani tago mashi da ‘yan Najeriya ke samu, ba bu ‘yan yankin Neja Delta a ciki,don haka me ake so suyi? gwamnati ce yakamata ta dubi lamarinsu.

Shugabar kungiyar ta ce, ba bu wani kwakkwaran shugabanci a yankin Neja Delta, shi ya sa ganin shugaban kasa ma su kai kokensu ke musu matukar wuya.

Farfesa Akasoba, ta ce yakamata a hadu da ainihin shugabannin da suka fito daga yankin don a lalubo bakin zaren matsalolin da yankin na Neja Delta ke fama da su, saboda gaskiya tura na kai wa bango.

Ta ce mutanen yankin ba su da isasshen abinci, don hatta masara idan aka dafa ba a cinta cikin dadi saboda fetur din da ake haka a yankin na su na bata musu abinci.

Shugabar kungiyar ta ce, baya ga rashin abinci, hatta ruwan sha mai tsafta ba su dashi a yankin, saboda hakar mai.

Farfesa Zainab ta ce, duk da wadannan matsaloli da yankin na su ke fuskanta, tana mai bawa masu fasa bututan mai shawara a kan su daina fasawa su kuma daina abinda suke yi saboda yin hakan ba a dauko hanyar zaman lafiya ba.

A bangaren gwamnatin kuma farfesar ta ce, yakamata gwamnati ta tattauna da mutanen da ya kamata, sannan ayi kokarin karbe sauran makaman da ke hannun masu tayar da kayar baya.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Najeriya ta ce a shirye take ta zauna da masu tayar da kayar bayan don jin korafin su game da matsalolin da suka addabi yankin.

Nigeria: Za a fara rijistar jarrabawar shiga jam'ia


JAMBHakkin mallakar hoto
FACEBOOK/JAMB

Image caption

A yanzu dai ana rubuta jarabarawar shiga jami’ar ne ta hnayar Intanet

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce hukumar za ta fara yi wa masu sha’awar shiga makarantun gaba da sakandare a 2018 rijista ranar 22 ga watan Nuwamba.

Farfesa Ishaq ya ce za a shafe wata biyu ana yi wa masu sha’awar shiga jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma kwalejojin ilimi rijista sabanin wata daya da aka yi ana rijistar a shekarar 2017.

Shugaban hukumar, wanda da ya yi jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a kan jarrabawar, ya ce za a yi jarrabawar ta shekara mai zuwa ne tsakanin ranar 9 zuwa 17 ga watan Maris na shekarar 2018.

Ya jaddada cewa hukumar a shirye take wajen ganin domin rijista tare da gudanar da jarabawar, yana mai cewa hukumar tasa za ta gudanar da ayyukanta kamar yadda jadawalin da ta fitar ya nuna.

Jarrabawar shiga jami’a da kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha aba ce wadda matasa da iyaye suke sha’awar yin nasara akai domin ci gaban yara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matasa da yawa a Najeriya suna da burin karatu a jami’a, amman gurbin karatun ya yi musu kadan

Mourinho bai da tabbas a Man United


Manchester UnitedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United tana ta biyu a kan teburin Premier bayan wasa 11 da ta buga a bana

Kocin Manchester United, Jose Mourinho bai fayyace ko zai cika yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar ta shekara uku ba.

Kocin ya ce ya mayar da hankali wajen bunkasa United da kuma lashe kofin Premier da sauran gasar da suke buga wa kafin yarjejeniyar ta sa ta cika.

Mourinho dan kasar Portugal, ya kusan yin shekara daya da rabi a United, inda ya lashe League Cup da kofin Europa a bara, wanda hakan ya kai kungiyar gasar kofin Zakaraun Turai ta bana.

Mourinho mai shekara 54, ya shaidawa Daily Mirror cewa ya shiga yarjejeniyar shekara uku da United, ya kuma mai da hankali kan bunkasa kungiyar a fagen tamaula.

Ana rade-radin Mourinho zai koma Faransa kungiyar Paris-

United tana ta biyu a kan teburin Premier bayan wasa 11 da ta yi, kuma wannan ne karon farko da kungiyar ta tagaza tun bayan da ta ci kofin Premier a 2012-13 a karkashin Sir Alex Ferguson.

Arsenal za ta kara da Tottenham


PremierHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal tana ta shida a kan teburin Premier, ita kuwa Tottenham tana ta uku a kan teburin

Kungiyar Arsenal za ta karbi bakuncin Tottenham a gasar Premier wasan mako na 12 da za su fafata a ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal tana mataki na shida a kan teburin Premier da maki 19, ita kuwa Tottenham tana ta uku a kan teburin da maki 23.

Kungiyoyin biyu sun kara sau biyu a bara, inda a Emirates suka tashi 1-1 a ranar 6 ga watan Nuwambar 2016, Tottenham ta ci wasa na biyu 2-0 a ranar 30 ga watan Afirilun 2017.

Arsenal za ta ziyarci Burnley a wasan mako na 13 a ranar 26 ga watan Nuwamba, ita kuwa Tottenham za ta karbi bakuncin West Bromwich Albion a ranar 25 ga watan na Nuwamba.

Tottenham ta kai wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai, yayin da Arsenal ta kai wasannin gaba a gasar Kofin Zakarun Turai amma ta Europa.

Nigeria ce ta uku da aka fi mutuwa saboda ta'addanci a duniya – Rahoto


Wani rahoto game da alkaluman kashe-kashen ta’addanci a duniya na 2017, ya bayyana Najeriya a matsayi na uku a duniya da ‘yan kasashensu suka fi mutuwa saboda ayyukan ‘yan ta’adda.

Duk da haka rahoton ya ce an sami gagarumar raguwar kashe-kashen mutane da kashi 80 cikin 100, sakamakon galabar da kasar ta samu kan kungiyar Boko Haram.

Dangane da rahoton, Mukhtar Adamu Bawa na BBC Hausa ya tuntubi Malam Kabiru Adamu, masanin harkar tsaro a Najeriya, inda ya fara da tambayarsa ko yaya ya ga wannan rahoto?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kashe dubban mutane tun daga shekarar 2009 lokacin da kungiyar Boko Haram ta fara ayyukanta a Najeriya

Man United ta samu fam miliyan 141


Man UnitedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United tana ta biyu a kan teburin Premier, bayan wasa 11 da ta buga a gasar

Manchester United ta sanar da samun kudin shiga da ya kai fam miliyan 141 a wata ukun farko, amma albashin da take biyan ‘yan wasa ya karu sakamakon buga gasar Zakarun Turai da take yi.

A watan Janairu ne United ta zama ta daya a duniya wajen arziki a tsakanin kungiyoyin tamaula a karon farko a kididdigar da Deloitee ta fitar, rabon da ta taka wannan matsayin tun 2005.

A rahoton kudin da United ta sanar ta samu a ranar Alhamis a farkon wata uku zuwa karshen watan Satumbar 2017, ta samu karin fam miliyan 120.2 daidai da yadda ta samu a bara.

United ta kashe kusan fam miliyan 145 a farkon kakar bana wajen sayo sabbin ‘yan wasa da suka hada da Romelu Lukaku daga Everton da Nemanja Matic daga Chelsea da kuma Victor Lindelof daga Benfica.

Haka kuma bashin da ake bin kungiyar ya kai fam miliyan 268 zuwa karshen Satumbar 2017, sai dai kuma ya ragu kenan zuwa fam miliyan 69.6.

United ta ci wasa hudu da ta yi a gasar cin kofin Zakarun Turai sannan ta kai daf da na kusa da karshe a kofin Carabao, sannan tana ta biyu a gasar cin kofin Premier.

Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane a Lagos


Nigeria TrainHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya dai tana kokarin farfado da layukan dogonta

A kalla mutum uku ne suka mutu bayan an yi hatsarin jirgin kasa a unguwar Agege da ke birnin Legas a kudancin Najeriya.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar jiragen kasa ta Najeriya da ke da hedikwata a Legas, Yakubu Mahmud, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar tirela da take kokarin tsayawa ta daki jirgin kasan.

Jirgin dai ya taso ne daga yankin Ijoko zai tafi yankin Ido da suke cikin birnin Lagos din.

Jami’in ya ce wadanda suka rasa rayukansu suna cikin wadanda suka fado daga bakin kofar jirgin.

Wasu rahotanni na cewa akwai yiwuwar yawan wadanda suka mutu ya karu domin akwai mutane da dama da suka ji munanan raunuka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba kasafai ake samun hatsarin layin dogo a Najeriya ba

Ba a dai cika samun hatsarin jirgin kasa a Najeriya ba kamar su Indiya inda aka fi amfani da layin dogon.

Karanta karin wasu labaran:

Ko kun san Victor Moses?


Lokacin da Victor Moses ya waiwayi tarihin wasansa, akwai yiwuwar dan wasan Najeriyan da kuma kungiyar Chelsea, ya ce kakar shekarar 2016 zuwa 2017 ce ta fi muhimmanci a gare shi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Moses ya ci kofin Premier League a Chelsea bayan da ya nuna kwarewarsa a tamaula a Stamford Bridge

Bayan shekarun da ya yi wasa a matsayin aro, daga bisani ne ya koma Chelsea – inda ya zama daya daga cikin manyan ‘yan wasa da suka taka muhimmiyar rawa wajen lashe kofin firimiya.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne kocin Chelsea, Antonio Conte ya gwada sanya Moses a wasan da suka doke Arsenal da Liverpool, inda kocin ya gwada salon 3-4-3.

Wannan ne wasansa na farko a Chelsea a cikin fiye da shekara uku, amma Moses ya rika nuna kwazonsa da basirarsa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Victor Moses daya daga cikin ‘yan wasan da Najeriya take ji da su ne

Wasan da suka doke Hull City yana cikin wasanni 13 a jere da Chelsea ba ta sha kayi ba, kuma na 22 da Moses ya buga, sai dai daga bisani ya shiga jinyar raunin da ya ji a watan Afrilu.

A watan da ya gabata ne dan wasan ya kara sanya hannu a wani sabon kwantiragi da kolub din Chelsea, inda zai ci gaba da taka leda kungiyar, wadda ya fara koma a shekarar 2017.

Conte ya bukaci sabunta kwantiraginsa ne saboda yadda ya kara ganin kwarewar Moses a wannin share fagen fara kaka.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli bayani game da Victor Moses

Dan wasan mai shekara 26, ya ce yana samun nasara ta hanyar nuna kwazo da natsuwa da kuma zafin nama.

Bayan lashe gasar firimiya, Moses yana cikin ‘yan wasan Chelsea da suka zo na biyu a gasar Kofin FA, bayan Arsenal ta doke su, inda Moses ya samu jan kati.

Moses ya buga wa kasarsa wasa ne sau uku kadai a bana, amma a wasansa na farko ya ci kwallo a karawar da Najeriya ta doke Kamaru da ci 4-0, abin da ya sa Najeriya ta samu damar zuwa gasar Cin Kofin Duniya.

An fara tattaunawa kan makomar Zimbabwe


Zimbabweans awaits as soldiers took controlHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan Zimbabwe na dakon su ga matakan da sojoji za su dauka a gaba bayan sun kwace mulki a kasar

An shiga halin rashin tabbas game da makomar shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe yayin da sojin kasar ke ci gaba da yi masa daurin talala a gidansa.

Ga ‘yan Zimbabwe da dama, yiwuwar barin mulkinsa, abin marhabin ne, ko da yake, suna guna-guni, don kuwa ba su san wani shugaba sai shi tun bayan samun ‘yancin kai.

Ana gudanar da tattaunawa a kasar da kuma a Botswana mai makwabtaka kan makomar Zimbabwe.

Ana tsare da wasu ministocin gwamnati yayin da manyan makusanta suka juya baya ga matarsa Grace Mugabe wadda tashen kasaitarta ya janyo wannan matakin soja.

“Wakiliyar BBC ta ce ko da yake, Mista Mugabe ya kubuce wa takunkuman kassarawa da kasashen Yamma suka kakaba da kuma matsin lamba daga ‘yan adawa da ke da karfi a baya.

“Amma sai ga shi makusantansa sun tade shi ya fadi.”

Wani jagoran adawan kasar, Tendai Biti ya bukaci sojoji su mayar da kasar kan mulkin dimokradiyya ta hanyar kafa wata hukumar wucin gadi da za ta yi jagora zuwa zabe.

An sayar da zanen Yesu Almasihu sama da N150b


Da Vinci

Image caption

A shekarar 1958, dala sittin aka sayar da zanen yayin wani gwanjo a London

An sayar da wani zane wanda gwani, dan asalin Italiya, Leornardo da Vinci ya ƙaga a wani gwanjo cikin birnin New York, kan dala miliyan 453 kwatankwacin sama da naira biliyan 150.

Shi ne kudi mafi tsada da aka taba sayen wani zane a duniya.

A gwanjon na tsawon minti 18, jami’ai sun kasa zaune sun kasa tsaye, lokacin da suke sauraron tayi daga masu bukata ta wayar tarho.

Yayin da aka rika ninninka kudin da ake sa ran sayar da zanen.

An dakata kan tayin dala miliyan 400, masu gwanjon kuma suka daddale kan farashin da aka sallama.

Ba a da masaniya kan kowane ne ya sayi zanen.

Ana yi wa zanen wanda ke kamanta surar Yesu Kiristi lakabi da ‘Mai ceton Duniya’.

Yana daya daga cikin ayyukan fasaha guda 20 da Leonardo da Vinci wanda ya mutu a Alif Hamsin da Sha Tara ya kirkira.

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 12i


sojoji na sunturi

Image caption

Dakarun Nigeria

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai harin a wani masallaci da gidajen yan gudun hijira a yankin Muna Garage da ke wajen birnin Maiduguri a Arewa maso Gabashin Najeriya

Mutum 16 a kalla sun mutu, wasu 22 na daban sun samu raunuka .

Wannan lamari ya faru ne bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake guda 4 ,maza 2 da mata 2 suka tayar da bama-bamai.

Lamarin ya faru ne a yankin Muna Garaje da ke mashigar birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewacin Nigeria.

Maharan sun kai farmaki ne kan wani masallaci na ‘yan gudun hijira da kuma gidaje .

Boko Haram ta kashe malamai 2,295 a Borno – UNICEF

An kai harin bam wajen karbar agaji a Borno

Boko Haram: ‘Mutum fiye da 40 aka kashe a harin Borno’

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mazan daga

Akasarin wadanda abin ya ritsa da su tsoffi ne da kananan yara kusan 7 masu shekaru 5 zuwa 6.

Jagoran hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno, Alhaji Ahmed Satomi shi ya tabbatar da wadannan al’kalumma.

Wadanda suka samu raunuka na ci gaba da samun kulawa ta mussanman a assibiti.

Hukumomin jihar ta Borno da kuma kungiyar agaji ta Red-Cross ko kuma Croix -rouge su ne suka dauki nauyin yi masu magani.

Me za a kira Shugaba Robert Mugabe, gwarzo ko mai laifi?


Zimbabwean President Robert Mugabe addresses a meeting of his ruling Zanu-PF party's youth league in Harare, Zimbabwe, October 7, 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

A duk lokutan da aka shafe inda tattalin arzikin Zimbabwe ya yi ta tabarbarewa tsawon shekaru, an sha hasashen durkushewar Robert Mugabe ta fuskar siyasa da ma ta lafiya, sai dai ya tsallake wannan fata, har sai yanzu da wani abu ya faru.

Haka kuma, ana ganin kamar ya wuce gona da iri wajen ganin cewa matarsa ta gaje shi, hakan ne kuma ta sa shugabannin soji wadanda da bazarsu yake rawa a mulkin, suka daina ba shi goyon baya.

Halin lafiyarsa dai ya ci gaba da tabarbarewa cikin shekarun da suka gabata, kasancewar sa dan shekara 93, duk da cewa a hukumance ya yi aniyar sake tsayawa takara.

Kafin zaben shekarar 2008, ya ce: “Idan ka fadi zabe kuma mutane suka juya maka baya, to lokacin barin siyasa ya yi.”

Amma bayan da Morgan Tsvangirai ya yi nasara a kansa, sai Mista Mugabe ya fiddo wasu halaye da suka saba da maganar tasa, inda ya yi rantsuwa cewa ‘Allah ne kadai’ zai iya tsige shi daga ofis.

Amma don ya tabbatar da ikon nasa, sai ya dinga amfani da rikici.

Shi kuwa Mista Tsvangirai a kokarinsa na kare magoya bayansa, sai ya janye daga zagaye na biyu, amma duk da haka an tilasta Mista Mugabe ya sanya Mista Tsvangirai a matsayin mataimakinsa, shi kuma ya ci gaba da mulkin da ya fara tun shekarar 1980.

Babban abun da ya sa Mista Mugabe ya yi suna shi ne yakin da aka yi a shekarun 1970.

Tarihin rayuwar Robert Mugabe

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaba Mugabe ya bai wa matarsa Grace goyon bayan zama mataimakiyar shugaba

 • 1924: Shekarar da aka haife shi
 • An horar da shi a matsayin malami
 • 1964: Gwamnatin Rhodesia ta daure shi
 • 1980: Ya lashe zaben da aka yi bayan ‘yancin kai
 • 1996: Ya auri Grace Marufu
 • 2000: Bai yi nasara ba a zaben raba-gardamr da aka yi ba na karfin ikon shugaban kasa da kuma hana Turawa mallakar gonaki
 • 2008: Ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da suka fafata da Tsvangirai, wanda ya janye saboda harin da aka kai kan magoya bayansa
 • 2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin firai minista a lokacin da ake fuskantar durkushewar tattalin arziki a kasar
 • 2016: An gabatar da takardun lamuni a yayin da karancin takardun kudya yi tsanani
 • 2017: Ya kori mataimakinsa da ya dade suna aiki tare wato Emmerson Mnangagwa

Jigo a juyin-juya hali

Akwai lokacin da ake yi masa kallon wani jigo a juyin-juya hali, inda yake fada da tsirarun Turawa don neman ‘yancin al’ummarsa – wannan ne dalilin da ya sa shugabannin Afirka da dama suke sako-sako wajen sukar sa.

Tun bayan da Zimbabwe ta samu ‘yancin kai, an samu ci gaba a duniya, amma shi har yanzu tunaninsa na zamanin da ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Robert Mugabe (L), seen here in 1960, was greatly influenced by pan-Africanist ideals

Har yanzu jaruman yakin kwato yanci na jam’iyyar Zanu-PF na yakar munanan akidun jari hujja da mulkin mallaka.

A kan yi watsi da masu suka ana kwatanta su da maciya amana, abin da ke tunowa da yakin sari-ka-noke, lokacin da alakanta mutum da wannan kalmar tamkar hukuncin kisa ne.

Ya sha dora alhakin matsin tattalin arzikin da Zimbabwe ke fama da shi a kan kasashen yamma, karkashin jagorancin Birtaniya, don hambarar da shi saboda kwace gonakin Turawa da ya yi.

Masu sukarsa na yawan zargin sa da cewa ba ya nuna damuwa kan yadda tattalin arzikin zamani ke aiki.

Ya fi mayar da hankali kan tambayar yadda za a raba zarikin kasa, maimakon neman hanyar da za a inganta shi.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Masu zanga-zanga a shekarar 2016 sun kona kudin kasar da ba shi da daraja don nuna kin amincewa da gabatar da takardun lamuni a matsayin kudi

Mr Mugabe ya taba cewa tattalin arzikin kasar da zai taba durkushewa gaba daya ba, kasancewar kasarsa ta fuskanci matsalar tattalin arziki mafi kamari a duniya, da kuma hauhuawar farashi da ya taba kai wa kashi miliyan 231 a watan Yulin 2008, kai ka ce yana so ne ya gwada ikirarin nasa.

Farfesa Tony Hawkins na jami’ar Zimbabwe ya taba fuskantar wani abu tattare da shugaban Zimbabwe, inda ya ce: “A duk lokacin da batun tattalin arziki ya hadu da siyasa, to siyasa ce ke yin nasara.”

A shekarar 2000, ya fuskanci kakkarfar hamayya a karon farko, ya damalmala tattalin arzikin kasar don samun karfin iko a siyance.

Ya kwace gonakin Turawa wadanda su ne kashin bayan tattalin azrikin kasar, ya kuma fatattaki kungiyoyin tallafi, wato dai cikin siyasa Mista Mugabe ya yi wa makiyansa shigar-burtu – ya ci gaba da kasancew a mulki.

Ko ta halin kaka

Kuma dabarun da shi da magoya bayansa suka yi amfani da su, sun samo su ne daga yakin sari-ka-noken da aka yi a can baya.

Bayan da ya sha kaye a karon farko a zaben raba gardamar shekarar 2000, Mista Mugabe ya kaddamar da mayakan sa kai na kashin kansa, wasu tsofaffin sojoji ‘yan mazan jiya, da dakarun tsaro ke marawa baya – wadanda ke amfani da rikici da kashe-kashe a matsayin matakan zabe.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mr Mugabe says he is fighting for the rights of black Zimbabweans

Bayan shekara takwas, an sake bin irin wannan salon bayan da Mista Mugabe ya fadi a zagayen farko na zaben shugaban kasa.

A duk lokacin da aka bukata, a kan yi amfani da dakarun tsaro da kafafen yada labarai na gwamnati, wadanda mambobin jam’iyyar Zanu-PF ne, wajen yi wa jam’iyya mai mulki hidima.

Mutumin wanda ya yi gwagwarmaya kan mutum-daya, kuri’a-daya ya bullo da wani sharadi na cewa mutanen da suka cancanci zabe sai sun tabbatar sun ‘yan kasa ne ta hanyar gabatar da takardun shaida na biyan kudin lantarki ko ruwan famfo, abin da kyar ne matasa da tsantsar masu zabe marasa aikin yi ‘yan adawa, idan suna da su.

Daya daga cikin nasarorin da tsohon malamin da ya shafe tsawon shekara 33 a kan mulki, ba ko tantama ya iya cimmawa ita ce fadada ilmi.

Zimbabwe a baya-bayan nan na da alkaluman mutanen da suka iya karatu da rubutu mai yawa a Afirka da kashi 90% na al’ummarta.

Masanin kimiyyar siyasa a yanzu marigayi Masipula Sithole ya taba cewa bunkasa ilmin da shugaban kasar ke yi tamkar “hakawa kansa kabari” ne.

Matasan da suka ci gajiyar haka na iya yin tankade da rairaya kan matsalolin Zimbabwe da kansu kuma akasari suna zargin cin hanci da rashin iya gudanarwar da suka dabaibaye gwamnati a matsayin silar rashin samun ayyuka da kuma hauhawar farashi.

Mai riƙon ƙaho

Mista Mugabe na iya yin imani cewa abu ne mai sauki a mulki kasar manoma masu neman abin da za su kai cikinsu da saurin mika wuya a kan zaratan matasa masu karfi a jika da suka koshi da ilmi.

Ya yi ikirarin yana gwagwarma ne don talakawan karkara sai dai filaye da dama da ya kwace sun koma hannuwan ‘yan barandansa.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mr Mugabe has not been afraid to use violence to stay in power

Babban limamin kiristan nan, Desmond Tutu ya taba cewa dadadden shugaban na Zimbabwe ya zama kwatankwacin ‘yan kama-karyan Afirka masu riƙon ƙaho.

A lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na 2002, ya fara sanya riguna masu launukan sheki da ke dallare fuskarsa – wani salo na shugabannin Afirka masu mulkin danniya.

A cikin shekaru ashirin dinsa na farko, ana ganin dan ra’ayin riƙwan ne kawai a bainar jama’a cikin shigar jaket da lakatayel ko kuma hartin da wando.

An bar ‘yan Zimbabwe da yawa, har ma da wasu na tambayar me ya sa ba zai sawwake wa kansa ya je ya huta a ‘yan shekarun da suka rage masa da matashiyar matarsa ba.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Robert Mugabe celebrated his 93rd birthday earlier this year

Matarsa ta biyu, Grace, wadda ya ba wa ratar shekara 40, ta taba cewa yakan tashi da karfe hudun dare ya kama motsa jikin da ya saba kullum.

Mista Mugabe yana dan shekara 73 lokacin da ta haifa musu dansu na uku, Chatunga.

Yana da’awar shi riƙaƙƙen dan katolika ne, kuma lokaci-lokaci jami’an tsaro kan mamaye masu ibada a Majami’ar Katolika ta Harare duk ranar Lahadin da ya je addu’a.

Sai dai, imanin Mugabe bai hana shi samun ‘ya’ya guda biyu da Grace ba, lokacin da take sakatariyarsa, yayin da fitacciyar uwargidansa mutuniyar Ghana, Sally, ke fama da jinyar ajali sakamakon cutar kansa.

Sarki

Ko da yake, Robert Mugabe ya yi wa mutuwar da ake ta kira masa ƙwari, sai dai shekarun da suka laftu a kansa sun fara yi masa nauyi a baya-bayan nan, inda kaifin bakin da aka san shi da shi a baya, yanzu kan koma cike da gajiya idan yana jawabi.

Wani sakon diflomasiyya na Amurka a shekara ta 2011, da shafin kwarmata bayanai na Wkileaks ya fitar na nuna cewa Mugabe na fama da cutar daji.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wife Grace says Mr Mugabe wakes at 4am for his exercise

Idan ba wannan ba, a ko da yaushe Mista Mugabe ya kasance mutum mai tsananin alfahari.

Sau da dama yana cewa zai sauka daga mulki ne kawai idan kammala cika burinsa na “juyin juya hali”.

Wannan na nufin sake raba gonakin fararen fata, yana kuma so ya zabi mutumin da zai gaje shi da hannunsa, wanda tabbas zai fito daga cikin jam’iyyarsa ta Zanu-PF.

Didymus Mutasa, da ya taba zama makusantan Mista Mugabe amma yanzu sun yi hannun riga, ya taba fada wa BBC cewa a al’adar Zimbabwe, ana maye gurbin sarakuna ne kadai idan sun mutu “kuma Mugabe sarkinmu ne”.

Sai dai ga alama kamar wasu daga cikin tsoffin abokan tafiyarsa ba su shirya wa kafuwar daular ba.

Italiya ta kori kocinta Giampiero Ventura


ItalyHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Giampiero Ventura ya yi aikin wata 17 a tawagar kwallon kafar Italiya

Hukumar kwallon kafa ta Italiya ta sallami koci Giampiero Ventura, bayan da ya kasa kai ta gasar cin kofin duniya a karon farko da ta kasa zuwa tun 1958.

Italiya ta yi rashin nasara a hannun Sweden da ci daya mai ban haushi, sannan suka tashi babu ci a Milan, wanda hakan ya kawo karshen aikin Ventura mai shekara 69, wata 17 da ya ja ragamar Italiya.

Sai dai kuma Ventura ya ce tarihinsa da ya kafa a tawagar ta Italiya, daya ne daga cikin wanda ya fi fice tun bayan shekara 40.

Kocin ya ce wasa biyu kacal ya yi rashin nasara a kusan shekara biyu da ya ja ragamar Italiya a hirar da ya yi da ‘yan jarida tun kafin hukumar ta sallame shi daga aikin.

Ventura ya maye gurbin Antonio Conte a watan Yunin 2016, ya kuma samu maki daya daga shida da ya kamata a karawa da ya yi da Spaniya da canjaras da Macedonia a wasan shiga gasar cin Kofin duniya.

Klopp bai jagoranci atisayen Liverpool ba


Jurgen KloppHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Klopp ya fara jan ragamar Liverpool tun Oktoban 2015

Kungiyar Liverpool ta sanar da cewar kocinta Jurgen Kloop bai ja ragamar atisaye ba a ranar Laraba, bayan da aka kai shi asibiti sakamakon rashin lafiya.

Likitoci sun duba Kloop mai shekara 50, domin tabbatar da cewar lafiyarsa kalau a matakin riga kafi.

Liverpool ta ce a yammacin Laraba zai koma gida, idan likitocin sun tabbatar da koshin lafiyar kocin.

Sai dai kuma Klopp zai bukaci a ci gaba da duba koshin lafiyarsa lokaci-lokaci.

Liverpool tana ta biyar a kan teburin Premier za kuma ta kara da Southampton a ranar Asabar a gasar Premier a Anfield.

Atletico da Real sun hadu sau 20 tun daga 2014


La LigaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Asabar ne Atletico za ta karbi bakunci Real a gasar La Liga

A ranar Asabar za a buga wasan hamayya a gasar cin kofin La Ligar Spaniya tsakanin Atletico Madrid da Real Madrid; wannan ne kuma karo na 20 da za su fafata tun daga shekarar 2014.

Tun daga shekarar ta 2014, kungiyoyin sun fafata a Gasar Spanish Super Cup da Gasar Cin Kofin Zakarun Turai har da wanda Real ta lashe na 10 da na 11.

A karon battar da suka yi a watan Fabrairun 2014, Real ce ta yi nasara gida da waje a gasar Copa Del Rey, a kuma shekarar sun buga wasan hamayya bakwai, ciki har da wasan karshe a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai wanda Real ta ci 4-1.

Haka kuma wasan hamayya shida suka yi a 2015, ciki har da na gasar La Liga da Kofin Spaniya da na Zakarun Turai.

Real da Atletico sun yi gumurzu uku a shekarar 2016, wanda ya hada da wasan La Liga gida da waje da na Kofin Zakarun Turai da wasan karshe a Milan din Italiya, wanda Real ta lashe.

A shekarar 2017 sun kara fafatawa sau uku, biyu a La Liga da wasan daf da karshe a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai wanda ya bai wa Real damar kaiwa wasan karshe a Cardiff, bayan da ta ci 3-0.

An yi wa Shugaba Mugabe 'daurin talala' a Zimbabwe


Soldiers stand beside military vehicles just outside Harare, Zimbabwe, 14 November 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An ga motoci masu sulke a gefen hanyoyi a Harare ranar Talata

Sojojin Zimbabwe sun yi wa Shugaba Robert Mugabe daurin talala a babban birnin kasar Harare, in ji shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma.

Mista Mugabe ya shaida wa Mista Zuma ta wayar tarho cewa yana cikin koshin lafiya, in ji ofishin shugaban Afirka ta Kudun.

Sojoji sun ta yin sintiri a babban birnin kasar, Harare, bayan sun karbe iko da gidan talabijin din kasar kuma sun ce suna hakon masu laifi ne.

Wannan yunkurin ka iya kasancewa kokarin maye gurbin Mista Mugabe da mataimakinsa da aka kora, Emmerson Mnangagwa, in ji wakiliyar BBC.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda sojoji suka kwace iko a Zimbabwe

Korar Mista Mnangagwa a makon da ya wuce ya sa ana ganin matar Mista Mugabe, Grace, ce za ta gaje shi a mulki.

Mista Mugabe, mai shekara 93, ya mamaye fagen siyasar kasar tun da ta sami ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1980.

Bayan an shafe kwanaki ana zaman dar-dar da kuma yada jita-jita, sojoji sun karbe iko da kafar watsa labarai mallakar Zimbabwe, ZBC cikin daren ranar Talata.

Wani jami’in sojin Zimbabwean, Manjo Janar General Sibusiso Moyo, ya yi wani jawabi a gidan talabijin mallakar kasar cewa babu wani juyin mulki a kasar, amma ya ce sojojin suna hakon masu laifi ne da ke kewaye da Shugaba Mugabe.

Jaridar Chronicle wadda ke karkashin ikon gwamnatin Zimbabwe a birnin Bulawayo, ta wallafa labarai na musamman game da rikicin kasar.

Ta fito da kanun da ke cewa: “Sojoji sun karbe iko”, tana mai cewa sojoji sun karbe mulki domin su “kakkabe masu laifuka na jam’iyyar ZANU-PF”.

Me ya sa sojoji ba sa son amfani da kalmar juyin mulki?

Rashin ambatar kalmar juyin mulki shi ne abun da ya fito cikin jawabin da manjo janar Sibusiso Moyo ya gabatar a kafar yada labaran Zimbabwe ZBC, da safiyar Laraba.

Janar Moyo ya jaddada cewa wannan ba juyin mulki ba ne.

Saboda haka me ya sa wannan yake da muhimmanci?

Kungiyar Tarayyar Afirka AU, da kuma kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (Sadc), ba su lamunci juyin mulki ba.

An ga hakan ya faru a Burkina Faso a shekarar 2015 a lokacin da kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Burkina Faso ta kuma kakaba takunkumi kan wadanda suka yi yunkurin juyin mulki, shekara daya bayan an tumbuke Blaise Compaore wanda ya dade yana mulkar kasar.

Ba abun mamaki ba ne cewa rundunar sojin kasar tana ta kokarin nuna cewa farar hula ce take iko da kasar har yanzu.

Tuni dai, Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya fitar da wata sanarwa a madadin SADC cewa yankin ba zai lamunci juyin mulki ba.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

General Chiwenga ya yi gargadin cewa soji za ta karbe iko

‘Sojoji na dukan ‘yan sanda’

Wata mata da ke zaune a Harare, Denissa Moyannah, ta shaida wa BBC cewa ta kai ziyara tsakiyar birnin, daga gidanta da ke unguwar masu hannu da shuni ta Borrowdale da safiyar Laraba.

Ta ce motoci masu sulke sun cika ko ina a tsakiyar birnin inda suke tsayar da ababen hawa a tsakiyar hanya.

Ta ce sojoji na dukan ‘yan sanda, sannan kuma kafar talabijin din kasar tana saka wakokin neman ‘yanci.

Miss Moyannah ta kuma ce kura ta lafa a babban birnin Zimbabwe din.

An kashe wata yarinya a Nigeria don yin tsafi da sassan jikinta


Map

‘Yan sanda sun shaida wa BBC cewa an kashe wata yarinya ‘yar shekara 17 a Najeriya don a sayar da sassan jikinta wajen yin tsafin da wasu suka yi amanna yana kawo arziki.

An kama mutum uku da suka hada da wani mutum wanda ya yi ikirarin kashe ta da sayar da sassan jikinta ga wani matsafi a kan dala 25, daidai da naira 9,000.

Wani mai magana da yawun ‘yan sanda ya kuma ce bayan haka ne kuma sai mutumin ya jefa gangar jikin yarinyar a wata rijiya da ke kauyen Idosemo a jihar Ogun.

A Najeriya dai wasu mutanen sun yi amanna da al’amarin tsafi sosai.

A kan je wajen bokaye ko matsafa don neman maganin wasu cututtuka, kuma masu bin su sun yarda cewa suna da siddabarun da za su iya kawo musu sa’a a rayuwa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Abimbola Opeyemi, ya ce matsafin, wanda tuni shi ma aka kama shi, ya bayyana cewa lallai ya karbi sassan jikin mutum, amma ya ce ba shi ya bayar da umarnin kisan ba.

Ya ce an kai wa yarinyar hari ne a lokacin da take talla a kan hanya.

Mahaifinta ne ya kai rahoton batanta wajen ‘yan sandan yankinsu.

Mista Opeyemi ya ce, aikin hadin gwiwa da aka yi tsakanin ‘yan sanda da ‘yan sintiri ne ya sa aka kama matsafin, wanda ya amsa laifinsa a yayin da ‘yan sanda ke tuhumarsa.

Ya kara da cewa hakan ce ta sa har ‘yan sanda suka gano rijiyar da aka jefa yarinyar.

Har yanzu dai ba a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu ba.

Wannan kisan gilla dai shi ne na baya-baya da ya faru a kudu maso yammacin kasar, inda dama hakan na yawan faruwa.

Ya kamata a mutunta kundin tsarin mulkin Zimbabwe – Buhari


MugabeHakkin mallakar hoto
AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira da a kwantar da hankali da zama lafiya da kuma mutunta kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce shugaban ya byi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a harkar soji da ke Zimbabwe da su guji yin duk wani abu da zai jefa kasar cikin rikicin da bai dace ba wanda kuma zai yi wa kasar da ma nahiyar illa.

A cewar Shugaba Buhari, “Dole ne a yi duk wani kokari don warware matsalolin da ake fuskanta ta hanyar bin kundin tsarin mulki na Zimbabwe don ceto kasar daga rikicin siyasa.”

Wannan kira dai na shugaban Najeriyar na zuwa ne bayan da sojojin kasar Zimbabwe suka yi ikirarin cewa sun kwace mulki daga hannun farar hula, saboda yadda ake samun karuwar sa-in-sa kan sha’anin siyasa a kasar.

Sa-in-sar dai na faruwa ne bayan da Shugaba Robert Mugabe ta cire mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga mukaminsa.

Wannan a’amari ne ya jawo shugaban sojojin kasar General Constantino Chiwenga, ya yi barazanar cewa ‘sojoji za su shiga cikin al’marin’ tun da batu ne da ke da alaka da kare juyin-juya hali.

Fasto ya sa mabiyansa cin kyankyaso a Afirka Ta Kudu


End Times MinsitriesHakkin mallakar hoto
End Times Minsitries

Image caption

A shekarar 2015 ne wannan fasto ya umarci mutane su ci maciji da beraye da kuma gashi

Wani fasto a Afirka Ta Kudu Penuel Mnguni, ya sa wasu mabiyansa biyu ‘yan uwan juna sun ci kyankyasai.

Faston, wanda aka fi sani da ‘Fasto Mai Maciji,” ya yi ikirarin cewa idan suka ci to ba wai kyankyaso suka ci ba, ji za su yi kamar sun ci cukwi da kayan kamshi.

Wannan al’amari dai ya faru ne watanni biyar bayan da Mista Mnguni ya halarci cocin wani shahararren fasto a Najeriya TB Joshua, inda a can din ya yi ikirarin cewa, “bai wa mutane naman maciji su ci ba shi da halacci a addinin kirista.

Hakkin mallakar hoto
TB Joshua Twitter

Image caption

Sakon da TB Joshua ya wallafa a shafinsa na Twitter

Fasto Joshuwa ya wallafa sako a shafinsa na Twitter cewa: “Fasto mai maciji daga Afirka Ta Kudu ya yi ikirarin cewa bai wa mutane naman maciji su ci ba shi da tushe a littafin injila. Mene ne ra’ayinku kan hakan?”

Cocin Mista Mnguni ya wallafa wani sako a shafin Facebook kan batun cin kyankyason a farkon watan nan, inda sakon ya ce faston ne ya kira kyankyasai sai kuwa suka bayyana a cocin.”

Sakon ya ce: “Daga nan sai ya kira mabiyansa don su matso su ci …. Sai wasu ‘yan uwan juna biyu suka dauka suka ci, a yayin da suke ci ne sai wani abu ya bai wa daya daga cikin su, Mista Charles mamaki, inda ya ji dandanon kyankyason ya yi kama da na cukwi.

“Shi kuwa Mista Eric sai ya ji dandanon kamar na kayan kanshi da ake girki da su,” a cewar sakon.

Hakkin mallakar hoto
End Times Dicsiples Ministries

Sakon ya kara cewa: “Fasto ya ce cin kyankyason nan da suka yi zai kara musu kaifin sani kuma za su sauya su fi yadda suke a da.”

Wani sako da cocin ya sake wallafa kuma ya ce, faston ya yi addu’a kan wata fulawa mai guba, sai wani mabiyinsa ya ci, ya kuma ji dadinta ta yadda har sai da ya roki a bar shi ya cinye fulawar baki dayanta.

Sakon ya ce: “Ubangiji ya yarjewa fasto kan duk abun da ya nema.

A shekarar 2015 ne wannan fasto ya fara jawo ce-ce-ku-ce a Afirka Ta Kudu bayan da ya umarci mutane su ci naman maciji da beraye da kuma gashi.

A watan Yulin 2015 din ne kuma aka janye wata kara da Hukumar da ke kare hakkin dabbobi ta shigar kan Fasto Mnguni, saboda rashin hujjoji.

Hakkin mallakar hoto
End Times Dicsiples Ministries

Kun san Sadio Mane?


Sadio ManeHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sadio Mane da wasa ne mai zafin nama

Sadio Mane Dan wasan Senegal da Liverpool kakarsa sa yi kyau a 2017, Kuma kamar yadda aka zabi dan wasan cikin jerin tawagar zaratan ‘yan wasan PFA na bana a ingilia, yana kuma cikin ‘yan wasan Afrika biyu a cikin jerin sunayen ‘yan wasan da aka zabo domin lashe kyautar Ballon d’Or.

Ya kuma taka rawar gani wajen taimakawa Senegal shiga gasar cin kofin duniya a karo na biyu, nasarar da ba su samu ba tun shekarar 2002.

A bana Mane ya ci wa Senegal kwallaye hudu.

A farkon shekara, Mane ya dace da irin rawar da ya ke takawa, ya iya zarra, ga yanke da karfin iya cin kwallaye a raga.

Ko da yake Mane ya fuskanci kalubale a shekararsa ta bana, domin duk da ya ci wa Senagal kwallaye biyu a wasannin rukuni a gasar cin kofin Afrika, amma ya barar da fanareti a wasan dab da na kusa da na karshe, wannan ne kuma ya karfafawa kamaru guiwar zuwa ta lashe kofin gasar.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko kun san waye Sadio Mane?

A lokacin Mane, da idon duniya ya koma a kansa ya shatata kuka, domin ya barar da damar shiga sahun zaratan ‘yan wasa da suka taba lashe kofin Afrika.

Sai dai kuma hakan ya yi wa Liverpool da magoya bayanta dadi domin nasara daya ne kacal kungiyar ta samu a wasanni 7 da ta buga bayan tafiyar Mane wakiltar kasarsa a gasar cin kofin Afrika.

Da dawowarsa ne Mane ya taimakawa Liverpool samun galaba akan Tottenham da ci 2-0, daga bisani kuma ya ci wa Liverpool muhimman kwallaye a nasarar da ta samu akan abokan gaba Arsenal da Everton.

Hakkin mallakar hoto
Stu Forster

Image caption

Sadio Mane yana cikin ‘yan wasan da Liverpool take ji da shi

Mane ya nuna yana da matukar muhimmaci a Liverpool.

An kammala Kakar da ta gabata Mane na da kwallaye 13 a premier, duk da ya shafe wata biyu yana jinyar tiyata da aka yi ma sa a guiwarsa tsakanin Afrilu zuwa Mayu.

Kuma duk da haka Mane a kakarsa ta farko a Liverpool ya yi kafada da Coutinho, da yawan kwallaye a kungiyar duk kuwa da ya kauracewa wasanni da dama.

Mane ya taimakawa Liverpool shiga gasar zakarun Turai a karon farko bayan shekaru takwas.

Dan wasan na Senegal ne Liverpool ta ba kyautar gwarzon shekara.

An auna cewa Liverpool ta fi samun nasara idan Mane yana fili, sabanin idan babu shi.

To la’akari da muhimmacinsa a Liverpool, dan wasan na Senegal mai shekaru 25 na fatar lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na BBC a karon farko bayan shekaru uku yana nema.

Nigeria ta shigo da maganin maciji


A type of venomous snake found in Nigeria

Hukumomi a Najeriya sun ce sun sayo maganin dafin maciji, daga kasashen Birtaniya da Costa Rica bayan watanni ana fama da rashin maganin a asibitocin dake kula da masu fama da ciwon.

Fiye da mutum 200 sun rasa rayukansu a watan jiya daga sarar maciji saboda rashin maganin.

Yankunan da matsalar tafi kamari sun hada da Kaltungo dake jihar Gombe da Zamko dake jihar Filato, inda a kullum ake samun wadanda suka rasa rayukansu.

Jami’an kiwon lafiya sun ce an fara raba magungunan kimanin 5,000 ga cibiyoyin dake kula da wannan matsalar a cikin Najeriya.

Masana sun kiyasta cewa maciji na sarar fiye da mutum 10,000 a kowace shekara a Najeriya, kuma daruruwan mutane kan rasa rayukansu a sakamakon haka.

Saboda Najeriya bata iya samar da maganin macijin a cikin gida, ta kan aika da samfurin dafin macijin zuwa kasahen waje domin a hada maganin.

Nigeria: An kashe dalibi kan zargin luwadi a Kano


Dalibai a wata makarantaHakkin mallakar hoto
Getty Images

‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke wasu dalibai bakwai na Kwalejin Fasaha ta Ungogo, wadanda ake zargi da halaka wani abokin karatunsu da ke ajin karshe.

Daliban dai kamar yadda `yan sanda suka ce suna zargin marigayin ne da yin luwadi.

Mahaifin mamacin, Mallam Ali Sango ya nemi hukuma da ta bi masa hakkin jinin dansa Muhammad Ali Sango, dalibin Kwalejin Fasaha ta Ungogo da ke jihar Kano.

An dai samu wasu jawabai daban-daban dangane da sanadiyyar ajalin dalibin.

Amma cikin tsananin kaduwa da juyayi, Mallam Ali Sango ya mini bayanin yadda ya samu labarin rasuwar dan nasa: “Shugaban makarantar ne yayi min waya, yace in same su maza-maza a asibitin Waziri Gidado”.

Ya kara da cewa bayan ya isa asibitin, sai shugaban makarantar ya shaida masa cewa dan nasa, “ba shi da lafiya, kuma sun kawo shi asibiti amma Allah Yayi masa rasuwa. Kuma wai rashin lafiyar sakamakon ya je sayan kati masu satar waya suka lakada masa duka”.

Yace yana fatan hukuma za ta dau mataki, “ta nema mana hakkin wannan yaro da aka kashe babu gaira, babu dalili”.

Rundunar `yan sanadan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar dalibin. Amma binciken rundanar, kamar yadda kakakinta, DSP Magaji Musa Majiya ya ce ya saba da labarain da aka ba wa mahaifin marigayin:

“Bincike dai ya tabbatar mana cewa marigayi Muhammd Ali Sango, shekararsa 17, kuma dalibai a tsakaninsu suna zarginsa da neman maza”.

Ya kara da cewa, “Haka ne yasa wasu daga cikin daliban suka hada kwarya-kwaryar yadda zasu hukunta shi”.

DSP Majiya ya fada wa BBC cewa, “Yanzu akwai mutum bakwai a hannunmu, kuma a cikin mutum bakwan nan, akwai mutum hudu wadanda da su aka yi wannan dukan”.

A kwalejin Fasaha ta Ungogon, shugabannin makarantar sun ce an yi wa bakinsu sakata dangane da zargin cewa dalibai na yin gaban-kansu, suna yanke irin wannan hukunci.

Ahmad Tijjani Abdullahi shi ne sakataren Hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, kuma yace ana cigaba da bincike a kan lamarin.

“Akwai wani dan littafi wanda muke rabawa dalibai a makarantu, wanda yake rayuwar daliban gaba daya mu’amularsu a kansa ta dogara”, inji shi.

Ya ce “abin da bincike ya bayyanar shi ne zamu yi aiki a kansa”.

A watan Agustan da ya wuce ma `yan sanda a jihar Jigawa mai makwabtaka da Kano sun kama wasu dalibai 15 na makarantar sakandare ta Karkarna bisa zarginsu da kashe wani dan makarantar tasu da shi ma suke zarginsa da yin luwadi.

Buhari na zawarcin sake tsayawa takara – Dr. Kari


PMBHakkin mallakar hoto
NIGERIAN PRESIDENCY

Image caption

Mutane da dama na ganin ziyarar a matsayin wata dama ta gyara dangantakar da ke tsakanin Shugaba Buhari da al’ummar Igbo

Masharhanta harkokin siyasar Najeriya na bayyana albarkacin bakunansu kan ziyarar da Shugaba Buhari a yankin Kudu Maso Gabashin kasar, wadda suka ce tun tuni ya kamata a ce ya je.

Dr. Abubakar Kari ya ce “ina ga saboda mai yiwuwa sha’awar da yake da ita ta tsayawa takara a gaba, da alama zai rika amfani da duk damar da ta zo masa.”

Ya ce tuni shugaban ma ya fara amfani da irin wadannan damammakin, bayan dakushe kaifin masu rajin kafa Biafra.

Zuwa yanzu dai shugaban bai fito ya furta da bakinsa cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019 ba.

Ko da yake, kiraye-kirayen Buhari ya yi tazarcen a fadin kasar suna ci gaba da karuwa.

Shugaba Buhari ya fara ziyarar wuni biyu a jihohin Ebonyi da Anambra, karon farko bayan hawansa kan karagar mulkin kasar a 2015.

Wasu al’ummar yankin Igbo sun rika sukar shugaban kasar tare da zargin cewa gwamnatinsa ba ta damawa da su, sannan kuma tana nuna fifiko.

Dr. Kari ya ce bayan lafawar guguwar kafa Biafra da ta yi zafi a kwanan baya, sai shugaban “ya zagaya ta baya ya dinga zawarcin manya-manyansu.”

A cewarsa ko nuna damuwar da Shugaba Buhari ya yi game da rashin lafiyar tsohon shugaban kasa Alex Ekweme da kuma sakwannin taya murna da ya rika aika ga manyan al’ummar Igbo.

“Da kuma a duk lokacin da ya yi kalami zai nuna cewa gwamnatinna tana nan ta yi shiri don sake gina gadar nan ta Onaca, sannan kuma ya yi maganar cewa za a yi sabon asibiti a Umuahia.

Za a gyara musu hanyoyi manya-manya, to duka wadannan zawarci ne, in ji Dr. Kari”

Sojoji sun mamaye Gidan Talbijin din Zimbabwe


Zimbabwean ArmyHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An cusgunawa wasu ma’aikatan gidan talbijin din lokacin da sojoji suka mamaye tashar

An ji gagarumar karar fashe-fashen wasu abubuwa a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, inda rahotanni ke cewa sojoji sun mamaye shalkwatar kafar yada labaran kasar, ZBC.

An ga motoci masu sulke a kusa da tsakiyar birni. Tun da farko, jakadan Zimbabwe a Afirka ta Kudu, Isaac Moyo ya yi watsi da rade-radin da ake yadawa na yin juyin mulki.

A ranar Talata ce jam’iyyar Zanu-PF ta Zimbabwe ta zargi babban hafsan sojin kasar da tunzura bore bayan ya ce rundunar soja a shirye take ta shiga tsakani don kawo karshen rikicin siyasa.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar na bayyana kalaman Janar Constantino Chiwenga a matsayin wani abin mamaki da firgitarwa kuma cin amanar kasa.

Babu dai wani martani daga bakin shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe dan shekara 93 a duniya.

An samu gibin amfanin gona a Damagaram


Fadama

Image caption

Manonan rani a Niger

An samu tangarda a damunar bana ta fuskar amfanin gona a wasu yankunan jihar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin kasar ta bayyana sakamakon wucin gadi na damunar da ta gabata game da halin da jihar ke ciki.

An samun babban gibi a amfanin da aka girbe a wasu garuruwa na jihar, gibin da ya kai kashi 50 cikin 100.

Karamin minista a ma’aikatar noma da kiwo, Mohamed Busha shi ya bayyana haka bayan wani rangadi da ya kai jihar ta Damagaram.

Ya kuma ce “cikin garuruwa 3, 378 wasu 502 daga ciki ba su samu cimaka yadda ya kamata ba”.

Niger ta nemi taimakon Amurka

Niger : Ambaliyar ruwa ta yi barna a Yamai

Niger: Manoma da makiyaya na samun horo kan zaman lafiya

Image caption

Makiyaya a Niger

Kashi 15 cikin 100 na manoman kauyukan jihar ne damuna ta kayar da su saboda kamfar ruwan sama da aka samu.

Haka ma lamarin ya kasance ta bangaren abincin dabbobi.

Sai dai kuma, wutar daji na daya daga cikin barazanar da abin da aka samu na abincin dabbobin ke ci gaba da fuskanta a yanzu haka.

Bayan damuna, an samu wutar daji har sau 21 a cikin jihar, abin da ya haddasa konewar eka 4, 180 kunshe da abincin dabbobi.

Ba zan yi watsi da al'ummar Igbo ba – Buhari


Shugaba Buhari a jihar EbonyiHakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

An karrama Shugaba Buhari da kayayyakin gargajiya na Igbo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi watsi da al’ummar Igbo da ke kudu maso gabashin kasar a duk tsawon mulkinsa.

Da ya ke magana a lokacin da ziyarar da ya kai yankin, shugaban ya ce zai cika dukkan alkawuran da ya daukar wa jama’ar yankin.

“Kamar yadda na fada a baya… Ina sake jaddada wa cewa ba zan yi watsi da ku ba”. Ya kara da cewa “Najeriya kasarmu ce mu duka”.

Al’ummar yankin dai sun sha zargin gwamnatin shugaban da nuna musu banbanci, lamarin da jami’ai suka sha musanta wa.

Wannan ce ziyara ta farko da Shugaba Buhari ya kai yankin tun bayan hawansa mulki. Kuma ta zo ne duk da barazanar da kungiyar fafutikar kafa kasar Biafra ta IPOB ta yi masa na tayar da tarzoma a lokacin ziyarar.

An dai tsaurara matakan tsaro a jihohin Ebonyi da Enugu da ya ziyarta, kuma kawo yanzu babu wani labarin tashin hankali.

A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban zai ziyarci jihar Anambra inda zai halarci taron yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam’iyyarsa ta APC.

Wasu dai na cewa Shugaba Buhari ya ziyarci yankin ne domin halartar taron yakin neman zaben, amma makusantansa sun musanta.

Ra’ayoyin jamar yankin dai sun sha bambam kan wannan ziyara, inda wasu ke maraba da ita, yayin da wasu kuma cewa shugaban ya yi latti.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Presidency

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyukan ci gaban kasa a yankin

Akasarin mutanen da BBC ta zanta da su ta wayar tarho sun ce suna wa Shugaba Muhammadu Buhari maraba a wannan ziyara ta farko da zai kai yankin.

Wasu Igbo dai sun sha sukar Muhammadu Buhari kan yadda suka ce ba ya damawa da al’ummar yankin a gwamnatinsa.

Al’amarin da ya zafafa rajin ballewa daga Najeriya a tsakanin wasu matasan yanki a baya-bayan nan.

Sai dai, wani Igbo ya ce: “Za mu yi masa marhabin ta yadda zai yi wa yankinsu wani aikin ci gaban kasa. Ai Najeriya kasarmu ce.”

Za mu yi murna da zuwansa, in ji shi.

Ita ma wata ta ce “Ai babu damuwa! Ina farin ciki da haka. Ziyarar za ta sa mu ji cewa Najeriya daya ce babu batun nuna bambanci tsakanin Bahaushe ko Bayarabe ko Igbo.”

Ta ce wato dukkan al’ummar kasar daya suke. “Ina kaunar wannan ziyara da Buhari da zai kawo yankinmu”.

Haka zalika, mutanen yankin na Kudu Maso Gabas na zargin gwamnatin Buhari da rashin gudanar da ayyukan raya kasa, inda suka ce yana nuna fifiko a mulkinsa.

Shi kuma wani tsohon dan jarida a yankin, Kalu Ezee na cewa da ma ya kamata Buhari ya kai wannan ziyara.

A cewarsa tun da aka kammala zabe, Buhari bai samu damar ziyartar yankin ba, don haka zuwansa zai magance wasu abubuwa da dama.

“Ka san mutanenmu kafin ya zo, suna gani kamar bai yi musu wasu ayyukan alheri sosai ba, don haka wannan dama ce gare shi ya fada musu abubuwan da ke zuciyarsa,” in ji Mista Kalu.

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Gwamnonin yankin da dama sun hallara domin tarbar shugaban

Ya ce mutanen yankin su ma za su samu damar yi masa bayani game da matsalolin da suke ci wa al’ummar yankin tuwo a kwarya.

A cewarsa: “Za su yi masa magana a kan (mawuyacin hali da) hanyoyin gwamnatin tarayya da ke yanki. Za su yi magana a kan (aikin) gadar Neja ta biyu, wato gadar nan ta Onacha, ka san ta dade ana maganarta.”

Dan jaridar ya ce al’ummar yankin za su so su bijirowa da Shugaba Buhari batun samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tsaro.

“Za su yi magana game da rikicin nan da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, Mista Kalu ya ce.

An tambaye shi ko za a bijiro wa shugaban maganar kafa kasar Biafra sai ya ce: “Maganar Biafra ba za ta taso ba, don kuwa kungiyar Ohaneze Ndigbo ta rika ta magance al’amarin”.

Nigeria ta zura wa Argentina kwallo 4-2


Argentina NigeriaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Argentina da Nigeria za su buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta Argentina 4-2 a wasan sada zumunta da suka buga a Rasha a ranar Talata.

Ever Banega ne ya fara ci wa Argentina kwallo a bugun tazara a minti na 28 da fara tamaula, sannan Sergio Aguero ya ci ta biyu a minti na 37.

Saura minti daya a je hutu ne Super Eagles ta zare kwallo daya ta hannun Kelechi Iheanacho a bugun tazara, bayan da aka dawo ne ta farke ta hannun Alex Iwobi, sannan ta kara ta uku ta hannun Brian Idowu.

Bayan da wasa ya yi nisa kuma saura minti shida a tashi daga karawar Alex Iwobi ya kara ta hudu kuma ta biyu da ya ci a fafatawar.

Argentina ta samu tikitin zuwa buga gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 daga Kudancin Amurka, yayin da Nigeria za ta wakilci Afirka daga biyar din da za su je Rasha daga nahiyar.

Buffon ya yi ritaya bayan kunya da Italiya ta sha


BuffonHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gianluigi Buffon ya fara buga wa tawagar kwallon kafar Italiya tamaula a fafatawar da ta yi da Rasha a 1997

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafa ta Italiya, Gianluigi Buffon, yana zubar da hawaye ya nemi gafarar magoya bayan kasar, bayan da suka kasa samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Kyaftin din ya yi ritaya daga buga wa Italiya tamaula, bayan da kasar ta kasa yin nasara a kan Sweden a wasannin da suka buga gida da waje don neman tikitin shiga gasar ta duniya.

Italiya ta tashi wasa babu ci da Sweden a gida, bayan da a wasan farko ta sha kashi da 1-0, hakan ne ya sa a karo na farko tun 1958 ba za a ga kasar a gasar ba.

Buffon mai shekara 39 ya ce, ”Abin kunya ne a lokacin wasana na karshe da na buga wa Italiya na ci karo da kasa zuwa gasar cin kofin duniya”.

Shi ma Andrea Barzagli mai taka-leda a Juventus, da dan wasan Roma, Daniele de Rossi, sun yi ritaya, ana kuma sa ran Giorgio Chiellini zai bi sahunsu; ‘yan wasan uku a tsakaninsu sun yi wa Italiya wasa 461.

Buffon mai tsaron ragar Juventus ya buga wa Italiya wasanni 175 a shekara 20 da ya yi a tawagar, ya kuma lashe kofin duniya a 2006.

Ta yaya Nigeria za ta tunkari Messi, Auguero da…?


Lionel MessiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lionel Messi ya addabi Najeriya a wasan da suka kara a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014

Da yammacin ranar Talata ne tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta kara da takwararta ta Ajantina a wani wasan sa da zumunci na shirya wa gasar cin kofin duniya.

Shin Najeriya tana da karfin rike tawagar Ajantinan Messi kuwa?

A gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014, Lionel Messi ne ya ci Najeriya kwallaye biyu a kayen da ta sha a hannun Ajantina da ci 3-2 a zagaye na farkon gasar.

A wannan wasan ne kuma dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya zama dan wasan Najeriya na farko da ya fara cin kwallaye biyu a wasa daya cikin gasar cin kofin duniya.

Lionel Messi dai ya ci kwallaye sama da 600 wa kasarsa da kungoyin kwallon kafar da ya murza wa leda.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hare-haren da Messi ya kai wa Najeriya sun sa mai tsaron gidan Najeriya na wancan lokacin, Vincent Enyiama, ya tsokane shi.

Kuma a wasan Ajantina da Najeriya a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 Messi ya yi ta kai wa ‘yan Super Egales hare-hare ta yadda mai tsaron gidan Najeriya na wancan lokacin Vincent Enyeama ya yi ta tsare kwallaye.

Sai dai kuma idan aka yi la’akari da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da Najeriya ta buga da kuma adadin kwallayen da aka sha ta, za a lura cewa masu tsaron bayan Najeriya suna da ‘rowar kwallo.’

Najeriya ta buga wasanni shida kuma ta ci kwallaye 12 yayin da aka ci ta kwallaye 4, lamarin da ya sa ta kasance kasar da aka ci mafi karancin kwallaye a cikin jerin kasashen da suka nemi shiga gasar cin kofin duniya daga Afirka a teburin rukunin B.

Yaya Najeriya za ta yi da Ajantina idan babu Messi?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sai da kuma Vincent Enyeama da ya yi ta kare Najeriya daga hare-haren Messi ya dade bai buga wa Najeriya wasa ba.

Wasu rahotanni sun ce Lionel Messi ba zai buga wasan sada zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya ba. Shin wannan na nufin babu wata matsala kenan ga Najeriya?

Tarihin wasannin Najeriya da Ajantina ya nuna cewa ko a lokutan da babu Messi ma Najeriya tana shan wahala a hannun Ajantina.

A gasar cin kofin duniya ta shekarar 1994 inda Najeriya ta fara haduwa da Ajantina tawagar Super Eagles ta Najeriya ta sha kaye a hannun Ajentina da 2-1 inda Claudio Cannigia ya ci Najeriya kwallaye biyu kuma Samson Siasia ya ci Ajantina kwallo daya.

Da kasashen suka sake haduwa a shekarar 1995 a gasar zakarun nahiyoyi, sun yi canjaras ne babu ci ko daya.

Amman a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2002 Najeriya ta sha kaye ne a hannun Ajantina da 1-0 inda Gabriel Batistuta ya ci Najeriya kwallo daya.

A gasar cin kofin duniya da aka buga a shekarar 2010 kuma Ajantina ta doke Najeriya da ci daya da nema inda Gabriel Heinze ya ci Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu tsaron bayan Najeriya na yanzu suna da ‘rowar kwallo’

Sai dai Najeriya ta samu galaba a kan Ajantina wani wasan sada zumuncin da suka buga a Abuja a watan Yunin shekarar 2011 da ci 4-1.

Amman Ajantina ta dauki fansa a watan Satumbar shekarar 2011 din da ci 3-1 a wasan sada zumuncin da suka yi a Dhaka.

Nasarar da Ajantina ta samu kan Najeria a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 ne ta sa jumullar nasarorinta kan Najeriya ta kai biyar, kuma ta yi canjaras sau daya inda Najeriya ta yi nasara a kanta sau daya.

Sai dai a wasa daya ne kawai Lionel Messi ya ci Najeriya cikin wadannan wasannin.

An kera shaddar naira miliyan 36 a Amurka


An fara sayar da wata shadda mai ruwan gwal a Amurka, gabannin ranar bandaki ta duniya da za ta zo mako mai zuwa.

Wannan shadda dai kudinta ya kai dala 100,000 daidai da naira miliyan 36 kenan.

An lullube shadar ne da fatar jakankunan Louis Vuitton masu tsada har 24.

Wani mai zayyane-zayyane ne da ya shahara wajen zana hotunan Donal Trump don tsokana ya kera shaddar.

Yadda girgizar kasa ta shafe kauyuka daga doron kasa a Iran


Building damaged by earthquake in IranHakkin mallakar hoto
Khosrow

Image caption

Girgizar kasar ta lalata gine-gine da dama, inda daruruwan mutane suka mutu, da dama kuma suka jikkata

Hotunan yadda bala’in ya faru sun fara bayyana a yankin da ke kan iyakar kasar Iran da Iraki, bayan faruwar girgizar kasar mai karfin maki 7.3 a ranar Lahadi da yamma.

Ganau da suka yi magana da BBC sun yi ta bayyana yanayin da suka samu kansu a ciki sakamakon motsin kasar.

Khosrow: ‘Kanwar mahaifiyata da ‘yarta da jikokinta sun mutu

Hakkin mallakar hoto
Khosrow

Image caption

Dangin Khosrow da dama sun mutu sakamakon girgizar kasar

Khosrow na zaune ne a wani kauye kusa da Sarpol-e Zahab, daya daga cikin wuraren da abin ya fi yin ta’adi, dab da kan iyakar Iraki.

Ya ce duk danginsa sun mutu kuma kauyen ya lalace.

“Gini ya yi ta ruftowa kan mahaifina da kannena mata. Haka na yi ta janye su daga gidan.

Ya ce: “Mahaifiyata ta ji rauni. Kanwar mahaifiyata da ‘yarta da jikokinta duk sun mutu.”

“Illahirin kauyen ya ruguje.

“Kaburbura sun yi ta budewa har wasu gawarwaki suka dinga fitowa daga ciki.

“Ba ruwa. Mutane na amfani da ruwan kogi. Ba mu da abinci. Ba mu da ruwan sha da kayan sanyi.”


Amir: ‘Ina zaton yawan wadanda suka mutu zai karu

Hakkin mallakar hoto
Alireza

Image caption

Asarar da girgizar kasar ta jawo na da yawa

Amir na zaune ne a garin Sarpol-e Zahab. Ya ce kashi 30 cikin 100 na garin ya lalace.

“Kashi 30% na gine-ginen da ke garin sun rushe.

“Mutane na bukatar abinci da ruwa. Masu ceto sun zo garin amma dai ina zaton yawan wadanda suka mutu zai karu.”


Mehrdad: ‘Kauyuka sun shafe daga doron kasa

Hakkin mallakar hoto
UGC

Image caption

Girgizar kasar ta shafe dumbin gidaje daga doron kasa

‘Yan uwan Mehrdad na samun mafaka ne a yankin Kermanshah cikin sansanoni bayan da gidajensu suka lalace.

Ya ce: “Na ziyarci kauyuka a kusa da tsakiyar inda girgizar kasar ta afku a Kermanshah, don na kai wa ‘yan uwana abinci da tanti.”

“Duk kauyukan sun shafe kamar ba a yi su ba.

“Mutane ba su da isasshen abinci da ruwa da sauran kayan bukatu.”


Salah: ‘Mutane na zaune a filin Allah

Hakkin mallakar hoto
Salah

Image caption

Mutane na zaune a cikin tantuna a Kermanshah, amma dai suna cikin tsananin bukatar abubuwan amfani na yau da kullum

Salah na zaune ne a Salas-e Babajani, da ke gundumar Kermanshah.

Ya ce: “Muna kusa da tsakiyar inda al’amarin ya faru.

“Mutane na zaune ne a filin Allah.

“Babu isassun tantuna da za su fake, kuma kashi 50 zuwa 80 cikin 100 na gidajen garin sun rushe.

“Babu abinci kuma babu magani.”

Gwarzon dan kwallon BBC na 2017: Wane ne Naby Keita?


Keita NabyHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Naby Keita madugu ne a kasarsa ta Guinea

Watakila Naby Keita ya kasance dan kwallon da ba a san shi ba a Jamus a kakar wasanni ta 2016-17, to amma kuma sai ga shi sunansa ya fado cikin jerin shahararrun ‘yan wasa 11 da aka zaba a kungiyar Bundesliga na shekara.

Dan wasan na Guinea ya samu kuri’un jama’a fiye da duk wani dan wasan tsakiya da ke taka leda a Jamus.

Kungiyar Red Bull Leipzig na daya daga cikin wadanda suka yi bazata a kakar wasanni ta 2016-17 kasancewar kulob din na biyu a teburin gasar Bundesliga sannan kuma ta samu damar yin katabus a gasar zakarun Turai ta Champions League sakamakon kwazon Keita.

Minti biyar da fara wasansa na farko a gasar ta Bundesliga, Keita wanda aka saya daga kulob din kasar Austria wato Red Bull Salzburg ya ci wa Red Bull Leipzig kwallo a wasansu da Borussia Dortmund abun da ya bude ma sa kofar zama gwarzon shekara a kungiyarsa da Bundesliga.

Keita ya jefa jimullar kwallaye 8 a gasar Bundesliga, inda kuma ya taimaka aka ci kwallaye guda bakwai. Wani abu da ya kara wa dan wasan mai shekaru 22 kima shi ne kasancewar sa dan baya mai kyau.

Saboda a duk wasa irin kwallon da Keita yake bugawa ce ke kayatar da ‘yan kallo.

Kasancewar Keita dan wasan tsakiya da ke shafa leda gaba da baya, kuma ba ya wasa da zarar ya sami kwallo wanda hakan ke firgita abokan gaba har suke bayyana shi kamar daya tamkar dan wasa biyu, al’amarin da ya janyo masu horar da ‘yan wasa ke kaunar sa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Naby Keita yana taka rawar gani a kulob din Red Bull Leipzig na Jamus

Keita kwararre ne a sarrafa kwallo, yana da kuzari da basirar hangen nesa wajen yi wa abokan wasa tazara (Alkalumma sun nuna ya fi dan wasan Bayern Munich Arjen Robben yawan yanke a kakar da ta gabata), yakan ci kwallo ya kuma mika a ci.

Wani abun mamaki shi ne yadda kocinsa a Leipzig wato Ralph Hasenhuttl ya danganta shi a matsayin dan wasa mafi muhimmaci, wanda basirarsa ta taka leda ba a saba ganin irinta ba.

Keita wanda aka Haifa a birnin Conakry ya janyo hankalin kungiyar Liverpool har ta sanya makudan kudi da ba ta taba zuba wa ba domin sayen wani dan wasan Afirka, inda ta sanya £48m kan dan wasan domin taka mata leda a 2018. Sai dai kuma daga baya kungiyarsa ta Leipzig ta yi da-na-sanin sayar da shi.

Sunan Keita na daga jerin sunayen ‘yan wasan da ke fatar buga wa Guinea wasa a Russia a 2018 kuma koda dan wasan ya ci wa kasarsa kwallaye a wasannin neman cancantar shiga gasar da ta fafata da Libya da Tunisia, to za a iya cewa Guinea ba ta samu cancantar ba cikin sauki.

Keita ya ce a har kullum Yaya Toure ne gwaninsa. Saboda haka yanzu abin tambaya shi ne ko Keitan zai iya yin irin abin da Toure ya yi ta hanyar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka a jerin kyaututtukan da ya lashe?

Magani mai fasahar dijital zai shigo kasuwa


Chip

Image caption

Magunguna na da dan wani maballi da ke tura sako ga wani abu da za a mannawa maras lafiya

Hukumomin Amurka sun amince a fara sayar da wata kwayar magani ta fasahar dijital karon farko a duniya.

Kamfanin Japan mai suna Otsuka ne ya samu izinin sayar da nau’in maganin da yake sarrafawa don masu larurar kwakwalwa da ake kira Abilify dauke da wani dan kankanin maballi a kowacce kwaya.

Da zarar an hadiyi kwayar maganin, sai ta aika sako zuwa wani abu da za a manna wa jikin maras lafiya wanda shi kuma zai rika tura bayanai zuwa wata manhaja a wayoyin zamani na marasa lafiya.

Fasahar daga nan tana iya raba wadannan bayanai tsakanin jami’an lafiya da kuma ma’aikatan kula da masu irin wadannan larurori.

Wannan Fasaha na da nufin kula da masu larurorin kwakwalwa kamar birkicewar tunani wadanda ba sa shan maganinsu ko yaushe, ko kuma sun manta su yi hakan.

Ranar zaman makoki a Iran


Rugujiwar gidaje a girgizar kasa a Iran

Image caption

Girgizar kasa a Iran

Bayan girgizar kasar da ya sanadiyar mutuwar mutum sama da 400 a Iran,gwamnatin kasar ta ayyana wannan rana a matsayin ranar makoki a fadin kasar.

Masu ceto sun shafe dare baki daya su na neman masu sauren shan ruwa a gaba da suka makale a cikin tarkace.

Duban ‘yan kasar Iran da dama ne suke kwashe dare na biyu a fili allah ta’ala, wato ba cikin mahalan su ba.

Sun kwashe daren na biyu a wani yanayi na iska mai sanhi da ke ke kadawa.

Girgizar kasa ta kashe mutum 330 a Iran da Iraq

Iran na takalarmu da yaki – Saudiyya

‘Yan Shi’a ne suka hana kwace Iraqi da Syria – Iran

Image caption

Kasa ta yi motsi a Iran

A kala mutune sama da 400 ne suka mutu kuma wasu kusa 700 suka samu raunika daban -daban, sanadiyar girgizar kasar ta ranar lahadi.

Har dai cikin dari, masu cuto na ci gaba da neman mutanan da suka makkale a cikin tarkace a yankin gabashin kasar,musamman a yakin Kermanshah mai tsauni .

Gwamnati kasar ta Iran dai ta sanar da cewa wannan rana ta Talata, za ta kasance ranar makoki a cikin kasar Baki daya.

Za a ba da tukwuici ga wanda ya bayyana maboyar mabarata


Wasu daga cikin mabaratan da aka kama a babban kurkukun birninHakkin mallakar hoto
TS Sudhir

Mahukunta a birnin Hyderabad da ke kudancin Indiya suna shirin bayar da tukwuicin rupee 500 ga duk wanda ya nuna maboyar mabarata.

Wannan wata dabara ce ta raba birnin da mabarata daga 15 ga watan Disamba.

Kwamishinanan ‘yan sandan birnin ya kuma hana bara har na tsawon wata biyu.

Masu sukar lamarin sun ce wannan matakin ya biyo bayan wata ziyara da ‘yar Shugaba Trump, Ivanka za ta kai yankin, amma mahukuntan sun musanta haka.

A makon da ya gabata dai an ga jami’an ‘yan sanda na kama mabarata a wuraren ibada da tashoshin mota da na jirgin kasa.

Ana kai wadanda aka kama din zuwa wata cibiyar kula da marasa galihu da ke kusa da babban kurkukun birnin Hyderabad.

Ana sa ran Ivanka Trump za ta ziyarci Hyderabad domin ta halarci wani babban taro game da shugabanci a kasuwanci daga 28 zuwa 29 ga watan Nuwamba.

A watan Maris na 2000 ma an dauki irin wannan matakin a lokacin wata ziyara da Bill Clinton ya kai a lokacin yana shugaban Amurka.

Hakkin mallakar hoto
TS Sudhir

Image caption

Ana kai wadanda aka kaman zuwa wata cibiyar kula da marasa galihu dake kusa da babban kurkukun birnin Hyderabad

M Sampat, wanda shi ne shugaban cibiyar ya fada wa BBC cewa: “Rupee 500 din wani tukwuici ne da kurkukun birnin yake bayarwa domin raba birnin Hyderabad da mabarata.”

Ya kuma ce, “Kurkukun na fatan koya wa mabaratan sana’o’i domin su fara aiki a tasoshin sayar da mai da dama mu muke samar musu da ma’aikata.”

Gwamnatin jihar ta ce ta kama mabarata 366 kawo yanzu. Daga cikinsu, 128 sun zabi suyi zamansu a cibiyar, inda 238 kuma suka koma gida, kuma sun yi alkawarin ba za su cigaba da bara ba.

Babban shugaban kurkukun Telangana, VK Singh ya fada wa BBC cewa: “Yawancin wadanda aka kama sun musanta cewa su mabarata ne bayan da aka kawo su nan.”

“Mun rika sakin wasu daga cikin mabaratan bayan sun yi alkawarin cewa ba za su ci gaba da bara ba.

“Mu kan saka bayanansu a na’ura mai kwakwalwa domin mu iya gane su a gaba”, in ji shi.

Jami’ai sun ce wannan matakin ya sa mabarata masu yawa daga cikin kimanin guda 5,000 dake cikin birnin sun yi kaura zuwa wasu biranen dake kusa.

Jam’an sun ce kalubalen da za su fuskanta shi ne na tabbatar da cewa mabaratan ba su koma birnin ba bayan 7 ga watan Janairun 2018, lokacin da hanin yin barar zai daina aiki.

Za mu fada wa Buhari damuwarmu idan ya zo – Igbo


Igbo eldersHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Al’ummar Igbo dai na zargin Shugaba Buhari da nuna musu wariya da yin biris da su a gwamnatinsa

Wasu al’ummar Igbo a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun yi maraba ga ziyarar da shugaban kasar zai kai jihohinsu daga ranar Talata.

Akasarin mutanen da BBC ta zanta da su ta wayar tarho sun ce suna wa Shugaba Muhammadu Buhari maraba a wannan ziyara ta farko da zai kai yankin.

Wasu Igbo dai sun sha sukar Muhammadu Buhari kan yadda suka ce ba ya damawa da al’ummar yankin a gwamnatinsa.

Al’amarin da ya zafafa rajin ballewa daga Najeriya a tsakanin wasu matasan yanki a baya-bayan nan.

Sai dai, wani Igbo ya ce: “Za mu yi masa marhabin ta yadda zai yi wa yankinsu wani aikin ci gaban kasa. Ai Najeriya kasarmu ce.”

Za mu yi murna da zuwansa, in ji shi.

Ita ma wata ta ce “Ai babu damuwa! Ina farin ciki da haka. Ziyarar za ta sa mu ji cewa Najeriya daya ce babu batun nuna bambanci tsakanin Bahaushe ko Bayarabe ko Igbo.”

Ta ce wato dukkan al’ummar kasar daya suke. “Ina kaunar wannan ziyara da Buhari da zai kawo yankinmu”.

Haka zalika, mutanen yankin na Kudu Maso Gabas na zargin gwamnatin Buhari da rashin gudanar da ayyukan raya kasa, inda suka ce yana nuna fifiko a mulkinsa.

Shi kuma wani tsohon dan jarida a yankin, Kalu Ezee na cewa da ma ya kamata Buhari ya kai wannan ziyara.

A cewarsa tun da aka kammala zabe, Buhari bai samu damar ziyartar yankin ba, don haka zuwansa zai magance wasu abubuwa da dama.

“Ka san mutanenmu kafin ya zo, suna gani kamar bai yi musu wasu ayyukan alheri sosai ba, don haka wannan dama ce gare shi ya fada musu abubuwan da ke zuciyarsa,” in ji Mista Kalu.

Ya ce mutanen yankin su ma za su samu damar yi masa bayani game da matsalolin da suke ci wa al’ummar yankin tuwo a kwarya.

A cewarsa: “Za su yi masa magana a kan (mawuyacin hali da) hanyoyin gwamnatin tarayya da ke yanki. Za su yi magana a kan (aikin) gadar Neja ta biyu, wato gadar nan ta Onacha, ka san ta dade ana maganarta.”

Dan jaridar ya ce al’ummar yankin za su so su bijirowa da Shugaba Buhari batun samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tsaro.

“Za su yi magana game da rikicin nan da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, Mista Kalu ya ce.

An tambaye shi ko za a bijiro wa shugaban maganar kafa kasar Biafra sai ya ce: “Maganar Biafra ba za ta taso ba, don kuwa kungiyar Ohaneze Ndigbo ta rika ta magance al’amarin”.

Ba Italy ba zuwa Russia 2018


Italy vs SwedenHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tun farko Sweden ta ci kasar Italiya 1 – 0, sannan a wasan fitar da gwani kuma suka canjaras ba ci

Zakarun kwallon duniya karo hudu, Italiya ta gaza kai wa gasar Cin Kofin Duniya karon farko tun cikin 1958 bayan an lallasa ta a wani wasan fitar da gwani da Sweden.

Hakan na nufin kungiyar kwallon kafar Italiya ta Azzurri ba za ta halarci gasar ba a karo na biyu kenan cikin tarihi bayan ta ki taka rawa a farkon bude gasar Cin Kwallon Kafa na Duniya a 1930.

Giggs zai yi darakta a makarantar kwallon Vietnam


Ryan GiggsHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ryan Giggs ya buga wa Manchester United wasa 963 ya kuma yi wa tawagar Wales fafatawa 64

Tsohon dan kwallon Manchester United, Ryan Giggs ya karbi aikin tuntuba a matsayin daraktan makarantar koyon tamaula ta Vietnam.

Giggs mai shekara 43, zai yi aiki a cibiyar tara kudi don zakulo matasan tamaula masu fasaha ta Vietname, domin horar da ‘yan wasa da kuma koci-koci.

Tsohon dan wasan tawagar Wales, ya amince da yarjejeniyar shekara biyu, inda zai dinda zuwa Vietnam sau biyu a shekara domin gabatar da aikinsa.

Rabon da Giggs a dama da shi a fagen kwallon kafa tun bayan da Manchester United ta sallami Luis van Gaal a watan Mayun 2016.

A mako mai zuwa Giggs zai ziyarci Vietnam domin bikin kaddamar da shi, inda Paul Scholes ne zai zama babban bako a bikin.

Ronaldo ya zama uban 'ya'ya hudu


RonaldoHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ronaldo dan kwallon Real Madrid kuma kyaftin din Portugal yana da ‘ya ‘ya hudu kenan da ya haifa

A ranar Lahadi ne budurwar dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ta haifa masa ‘ya mace a birnin Madrid na Spaniya.

Georgina Rodriguez da Ronaldo sun saka wa yarinyar suna Alana Martina, kuma ita ce ta farko da ya haifa tare da wannan budurwa tasa.

A watan Yuni ne Ronaldo ya haifi tagwaye wadanda aka bai wa suna Eva da kuma Mateo, kuma da ma dai yana da Ronaldo Junior mai shekara bakwai.

Ronaldo, wanda shi ne kyaftin din Portugal, yana hutu yanzu haka, bayan da tawagar Portugal ta amince ya ziyarci budurwar tasa, yayin da ake hutu a gasar Spaniya.

Ana zaben shugaban kasa a yankin Somaliland


Zaben Somaliland

An fara zaben shugaban kasa a yankin Somaliland da ta ayyana kanata a matsayin kasa mai cin gashin kanta daga kasar Somaliya.

Zaben zai yi amfani da wata na’urar ido ta ido ta – abin da ake yi a karon farko a duniya, in ji mai magana da yawun hukumar zabe.

Masu zabe sama da 700,000 ne suka cancanci yin zaben da mutum uku ke takarar lashewa.

A kalla masu sa ido 60 ne ke cikin yankin domin zaben.

Daya daga cikinsu, Susan Mwape daga Zambia, ya shaida wa BBC cewa za su cigaba da sa ido kan harkokin zaben ciki, har da “kwarewar masu jami’an hukumar zaben.”

An yi karar ministan ilimi kan fadawar yaro shaddar gargajiya


bandaki a AfirkaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Al’ummomi da dama a Afirka na fama da rashin bandaki

Wata kafar yada labaran intanet ta Times Live a Afirka Ta Kudu ta ce, iyayen wani yaro sun shigar da karar ministan ilimi na Afirka Ta Kudu Angie Motshekga, bayan da dansu ya fada cikin shaddar gargajiya.

Kafar yada labaran News 24 ta ruwaito cewa a shekarar 2014 ne Michael Komape ya fada cikin wata shaddar gargajiya a makarantar firamare ta Mahlodumela da ke Limpopo, ya kuma nutse a cikin kashin mutane, wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Iyayensa sun ce shaddar ta lalace ne ta yadda bai kyautu a bar mutane su dinga amfani da ita ba, don haka suke bukatar dala 207,000 a matsayin diyya.

A ranar Litinin ne aka fara gudanar da shari’ar a babbar kotun da ke Polokwane.

Sashen ilimi a matakin farko na kasar ya gabatar da bayaninsa ga kotun inda yake watsi da batun cewa ministan ilimi ne ya jawo mutuwar yaron.

Ina goyon bayan el-Rufa'i kan korar malamai – Buhari


BuhariHakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai yiwu a ce malamin da ya kasa cin jarrabawar dalibinsa ya ci gaba da koyar da dalibin ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wani babban taro kan ilimi wanda aka yi a Abuja ranar Litinin.

A watan da ya gabata ne dai gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa malaman jarrabawa irin ta ‘yan aji hudu na firamare.

An dai yi wa malamai fiye da 33,000 jarrabawar, amma kamar yadda gwamnati ta ce, kaso biyu bisa uku na malaman ba su iya samun kashi 75 cikin 100 ba bayan da sakamakon jarrabawar ya fito.

Shugaba Buharin ya ba da labarin yadda ya yi karatu lokacin da yake maraya.

“Na kasance maraya lokacin da nake yaro, har yanzu na yi amannar cewa duk abin da na yi a rayuwa ya ginu ne daga rayuwata a makarntar kwana. Na yi shekara tara a makarantar kwana, shekara uku a firamare, shida a sakandare,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “A wadancan shekarun, malamai suna daukar dalibansu tamkar ‘ya’yansu. Idan ka yi daidai za su fada maka, idan ma ka yi ba daidai ba kuma za ka sha na jaki.”

Buhari ya ce bayan da ya kammala makaranta da gangan ya ki ya yi aikin gwamnati, ya shiga aiki soja.

“Na taba jin wani dan Najeriya wanda nake girmamawa, ya ce bayan ya samu horo a Najeriya da kuma Amurka. Ya koma makarantar firamaren da ya yi don ya ba da gudunmuwa. Amma sai ya kasa bambancewa tsakanin dalibai, yara da kuma malamai.

Karanta wadansu karin labarai

Maza sun fi mata kamuwa da bugun zuciya ta hanyar jima'i – BincikeCouples feet in bedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani bincike ya nuna cewa maza sun fi kamuwa da bugun zuciya ta hanyar jima’i, fiye da mata.

Ko da yake, ba kasafai aka fi samun bugun zuciya ba a wajen jima’i.

Amma binciken ya ce 34 cikin 100 ne kadai daga cikin 4,557 aka tabbatar da sun kamu da bugun zuciya cikin sa’a daya a lokacin jima’i, kuma 32 daga cikinsu maza ne.

Sumeet Chugh, na wata cibiya da ke kula da lafiyar zuciya, ya ce bincikensa ne na farko da ya gano cewa jima’i na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da bugun zuciya.

Ya gabatar da binciken ne a wani babban taron likitocin zuciya da aka gudanar a Amurka.

Ana dai samun bugun zuciya ne idan zuciya ta daina bugawa. Matsalar kuma na iya sa mutum ya fita hayyacinsa, ya daina numfashi.


Dakta Chugh da wasu abokan aikinsa sun yi nazarin matsalolin zuciya ne da suka faru a kan mutanen da suka haura shekara 18 daga 2001 zuwa 2015 a Portland, Oregun.

Binciken ya ce ana samun matsalar a jima’i kasa da kashi daya, kuma wadanda matsalar ta fi shafa maza ne.

Mutane sun ga duniyoyin Venus da Jupiter a lokaci guda


Jupiter and VenusHakkin mallakar hoto
Tim Jilani

Image caption

This photo of the planetary display was taken near Alexandra Palace in London

An ga Jupiter da Venus, duniyoyi biyu mafi haske, wadanda suka bayyana tare da juna a sararin samaniya da safe.

Ana ganin su da ido a sassan Birtaniya da wasu kasashe da ke tsakiya da arewacin duniya, da kuma wani sashe na Amurka.

Masana sun ce duniyoyin sun kasance kusa da juna, kamar wasu taurari masu haske.

An fi ganinsu a Birtaniya, minti 40 kafin fitowar rana, amma duniyoyin suna fara bayyana ne kafin fitowar Al Fijir.

A yayin da ake iya ganinsu da ido, wasu da suka yi amfani da na’urar hangen nesa na iya ganin wasu halittun duniyar Jupiter.

Mutanen Birtaniya da dama sun yada hotunan yadda duniyoyin biyu suka bayyana a shafukan sadarwa na Intanet.

Hakkin mallakar hoto
Jodrell Bank

Image caption

Duniyoyin biyu sun bayyana kamar taurari ma su haske

Hakkin mallakar hoto
Jodrell Bank

Image caption

Duniyoyin biyu sun bayyana kamar taurari ma su haske

Image caption

A shekarar 2004, an taba ganin duniyar Venus na ratsa rana kamar wani karamin digon baki

Gwarzon dan kwallon BBC na 2017: Waye Pierre-Emerick Aubameyang?


PIERRE-EMERICK AUBAMEYANGHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu na cewa Pierre-Emerick Aubameyang shi ne ran kulob din Brussia Dortmund

Ba a taba samun wani dan Afirka ba wanda ya fi kowa cin kwallaye a gasar Bundesliga har sai da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallaye 31 a kasar wasan 2016-17.

Wannan nasara ba wai kawai ta bai wa dan wasan dan asalin kasar Gabon damar dusashe tauraruwar dan wasan kasar Ghana, Tony Yeboah ba, wanda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye har karo biyu a 1990.

Pierre ne mutum na hudu a duniya da ya zarga kwallaye 30 a raga a gasar Bundesliga, irinsa na farko a tsawon shekara 40.

Wani kuma abun ban sha’awa dangane da nasarar fitaccen dan wasan na kungiyar Dortmund shi ne yadda ya ci kwallayen 31 a jerin wasanni 32, al’amarin da ya sanya kulob din nasa kasancewa na daya a gasar ta Bundesliga har karo biyu a jere sakamakon baiwar gudu da ta cin kwallaye da Allah ya huwace masa.

Kwallaye ukun da ya ci kulob din Benfica a wasa daya, a watan Maris ne suka sanya kididdigar jumullar kwallayen da dan wasan ya ci suka zama 40 a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Kwallon da ya ci a wasan da kulob dinsa ya ci Eintracht Frankfurt 2-1 wadda ta bai wa Dortmund damar daukar kofi a gasar wasan kwallon kafar Jamus na daya daga cikin kwallayen da ya ci 40.

Sakamakon kwazon Aubameyang mai shekara 28 ne ya sa aka sanya sunansa a jerin sunayen ‘yan wasan da za a zabi gwarzon dan wasan duniya na FIFA.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Aubameyang ya taimaka wa kasarsa a gasar cin kofin Afirka da ta wuce

Kuma Aubameyang ne dan wasa daya tilo daga Afirka a jerin ‘yan wasan na FIFA, ko da yake Sadio Mane da suke takara tare domin lashe kyautar gwarzon Afrika na BBC yana cikin jerin ‘yan wasan da ke takarar lashe kyautar Ballon d’Or.

Duk da tsammanin da ake da shi cewa dan wasan dan kasar Gabon wanda dan gayu ne zai bar kulob din Dortmund a karshen kaka har yanzu hakan bai kasance ba.

Manyan kungiyoyin wasa kamar Paris Saint-Germain da Manchester City sun nuna sha’awarsu kan dan wasan.

Sai dai kuma dan wasan ya dade yana burin buga wa kulob din da kakansa ya fi so wato Real Madrid, wasa, amma har yanzu burinsa bai cika ba sakamakon rashin nuna sha’awarsa, duk kuwa da irin baiwar cin kwallaye da ya nuna a Dortmund tun 2013.

Bugu da kari, a yanzu haka kwallayen da Aubameyang ya ci 135 a wasanni 204 na nufin zai iya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a kulob din Dortmund, kuma hakan na nufin zai iya zarta Michael Zorc daga nan zuwa karshen shekara.

‘Auba’ kara kwazo yake yi fiye da abun da ya yi a baya, a inda ya zura kwallaye takwas a wasanni shidan farko na gasar Champions League.

To sai dai idan an diba batun kimar kasar dan wasan ta asali wato Gabon a kwallon duniya, za a iya cewa kyaftin Aubameyang bai ji dadin yadda kasar tasa ta kasa kai bantanta a gasar zakarun kwallon kafar nahiyar Afirka ba duk kuwa da cewa shi ne mutumin da ya jefa kwallaye biyu a wasanni uku.

Abun tambaya a nan shi ne ko rawar da yake takawa a Dortmund za ta ba shi damar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka?

MTV: Davido ne gwarzon mawakin Afirka na bana


Davido ya doke takwaransa Wizkid da suke tashe a yanzu.Hakkin mallakar hoto
Davido Instagram

Image caption

Davido ya doke takwaransa Wizkid da suke tashe a yanzu

Mawakin Najeriya Davido ya lashe kyautar MTV da ake bayarwa a Turai a matsayin shahararren mawakin Afirka a gagarumin bikin da aka gudanar ranar Lahadi a London.

Davido ya doke takwaransa Wizkid da suke tashe a yanzu.

Sau biyu ke nan dai mawakan biyu ‘yan Najeriya ke takarar lashe kyautar.

Wakar Davido “IF and Fall”, ta samu karbuwa a shekarar 2017, inda a kwanan nan kuma ya saki sabuwar waka mai suna “FIA”.

Sai dai kuma Davido bai samu halartar bikin ba, saboda ya tafi wani aikinsa na waka a Luanda babban birnin Angola.

Amma mawakin ya bayyana farin-cikinsa a shafin Instagram inda ya godewa wadanda suka taimaka ya lashe kyautar da suka hada da mahaifiyarsa.

An gudanar da bikin bayar da kyautar ta MTV ne a Wembley, wanda shi ne karon farko da aka taba gudanar da bikin a London a tsawon shekaru 20.

Sauran mawakan Afirka da Davido ya doke sun hada da Nasty C, da Babes Wodumo, ‘yan Afirka ta Kudu da mawakin Kenya Nyashinski da kuma C4 Pedro na Angola.

Hakkin mallakar hoto
Davido Instagram

Image caption

Davido

'Sai an kafa Civilian JTF kan masu satar mutane'


Civilian JTFHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Matasa ‘yan sintiri dai sun ba da gagarumar gudunmawa wajen yaki da ‘yan ta-da-kayar-baya a yankin arewa maso gabashin kasar

Wani dan asalin yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna a Najeriya ya ce manoma a yankinsu kan shiga tasku lokacin jido amfanin gonakinsu saboda yawan satar mutane.

Zubairu Abdurra’uf ya ce dole sai manomi ya fanshi kansa ko kuma a yi garkuwa da shi har sai danginsa sun biya fansa.

“Idan ka taso tun daga cikin Kaduna kana wutowa daga filin jirgin sama kafin ka kai Buruku har Birnin Gwari, wannan dajin duk suna nan,” in ji shi.

Ya ce shi ya sa wannan hanya ta Kaduna zuwa Legas ta yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane.

Yankin Birnin Gwari da kan hanyar Kaduna zuwa Abuja na daga cikin sassan da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa.

Lamarin da ya sa mutanen kauyen Sabon Gayan a kan titin Abuja zuwa Kaduna suka gudanar da wata zanga-zanga ranar Lahadi don nuna damuwa kan karuwar ayyukan masu satar mutane.

A cewar Zubairu Abdurra’uf, ko kasuwa manomi ya kai hatsinsa ya sayar, to sai an bi shi gida ya ba da kudin cinikinsa.

Ya ce: “Har fulani su kansu ba a bar su ba, ana sace matansu a ce sai sun sayar da shanu sun biya fansa kafin sako su”.

Ya yi zargin cewa masu garkuwa da mutanen suna hada baki da wasu da ke tsegunta musu bayanai game da matafiya a tashoshin mota a cikin Kaduna.

“Akwai wurare guda biyu, in ba jami’an tsaro sun yi kokarin sun tada irin wadannan mutane ko sun kama su ba, to har yanzu ba a rabu da Bukar ba kenan,” a cewarsa.

Ya ce rashin ‘yan sanda a kan titunan yankunansu dare da rana na daga cikin dalilan da suka matsalar ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa.

Dan masanin Birnin Gwarin ya ce ta hanyar kafa kungiyoyin sintiri tsakanin al’ummomin wadannan yankuna da kuma samun hadin kan jami’an tsaro ne za a iya shawo kan matsalar satar mutane don neman fansa.

Amurka ta fara binciken kashe sojojinta a Nijar


Nigerien ArmyHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sojojin Nijar na samun horo da sauran tallafi daga takwarorinsu na Amurka

Masu bincike daga Amurka da kuma jamhuriyar Nijar sun kai ziyara yankin da wasu masu ikirarin jihadi suka far wa sojojin kasashen har ta kai ga kashe hudu cikin dakarun kowaccensu.

Sojojin Amurka sun ce ayarin binciken ya zanta da mutanen kauyen Tongo Tongo a yammacin Nijar a kokarin gano takamaimai abin da ya faru.

Harin ya zama wani babban al’amari cikin siyasar Amurka saboda mutuwar dakarun kasar.

Amurka ta ce ziyarar wani bangare ne na binciken hukumomin kasar masu yawa da zai shafi nahiya uku.

Maharan wadanda ake kyautata zaton sun shiga kasar daga makwabciyarta Mali sun yi wa dakarun Nijar da na Amurka kwanton-bauna a Tongo Tongo da ke arewacin jihar Tillabery, inda suka kashe sojin Amurka hudu da na Nijar hudu.

Rahotanni an yi wa dakarun hadin gwiwar kwanton bauna ne yayin wata raraka da suka yi wa ‘yan ta-da-kayar-bayan.

Sojojin Amurka na ba da horo da sauran taimako ga takwarorinsu na Nijar domin taimaka wa yaki da mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda suka hada da reshen kungiyar Al Qaeda na Arewacin Afirka.

Jagoran Shi'a a Ghana ya bukaci a saki Zakzaky


Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin Jagoran mabiya Shi’a a Ghana,

Image caption

Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin

Shugaban mabiya Shi’a a kasar Ghana, Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin, ya bukaci hukumomin Najeriya da su saki Sheikh Ibrahim el-Zakzaky wanda ke tsare.

Ya bayyana hakan ne a birnin Accra lokacin da ya jagoranci tattakin Arbaeen , wato taron tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW), Imam Hussain, ya shiga a karni na bakwai.

Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin Najeriya take tsare da Zakzaky bayan wani rikici tsakanin mambobin kungiyarsa da sojoji a garin Zariya.

Shekih Abubakar ya ce: “Zakzaky kamar sauran malaman Shi’a ana gallaza masa kan zalunci. Idan za ka tambayi duniya mene ne Zakzaky ya yi, za a ce maka babu abin da ya yi”.

Image caption

Sun faro tattakin ne daga wani masallacinsu da ke unguwar Mamobi a Kwanka Bus Stop zuwa filin Ojo a birnin Accra

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata “gwamnatin Najeriya ta saki malamin don bai yi komai ba”.

A makon jiya ne wata babbar kotu a Najeriya ta saki wadansu mabiya Shi’a 10 da aka kama kuma aka gurfanar a gaban kuliya sakamakon rikicin da ya faru tsakaninsu da sojoji a watan Disamban shekarar 2015.

Kotun ta ce ta wanke su daga laifuffuka biyar da ake tuhumarsu.

Karanta wadansu karin labarai

Abin da zai faru idan Iran ta kai wa Saudiyya hari

Nigeria na amfani da waka don yaki da cin hanci

Yadda gurgu ke koya wa masu kafa hada takalma

Girgizar kasa ta kashe fiye da mutum 100 a Iran


IraqHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani kanti kenan da girgizar kasar ta shafa a kusa da yankin Halabja inda iftila’in ya fi tsanani

Wata girgizar kasa mai karfin sama da maki bakwai ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 a yankin kan iyaka na arewaci tsakanin Iran da Iraki.

Akalla mutum 129 ne suka mutu a lardin Kermanshah na kasar Iran a cewar jami’ai ta kafar talbijin din kasar.

Haka zalika, girgizar ta haddasa mutuwar wasu mutane a makwabciyar kasar wato Iraki baya ga jikkata wasu dumbin mutanen a Iran.

An samu katsewar hasken lantarki da ruwan sha, baya ga yankewar hanyoyi a cikin birane da kauyukan da iftila’in ya shafa.

Yankewar hanyoyi sakamakon girgizar kasar kuma na kawo cikas ga ayyukan ceto.

Tsagewar da kasa ta yi ya kai har kusa da kan iyakar Iraki kusa da birnin Kurdawa na Halabja.

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum shida sakamakon girgizar kasar a Iraki.

Haka kuma, kasashe kamarsu Israila da Kuwaiti duk sun ji rugugin wannan girgizar kasa.

Buhari kansa ya san da gazawar 'yan sanda – Masani


Nigerian Police IGHakkin mallakar hoto
NIGERIA POLICE

Image caption

An sha zargin rundunar ‘yan sandan Najeriya da rashin iya aiki, sai dai a kullum tana musantawa

Wani masani kan sha’anin tsaro a Najeriya, ya yi ikirarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya amince ‘yan sandan kasar na da gazawa ta fuskar horo da kuma binciken masu laifi.

“Kasawa ta fuskar tattara shaidu wurin kama wadanda ake zargi, wanda kuma shi ne ke hana hukunta masu laifi a kasar,” in ji masanin harkokin tsaron.

Ya ce a kan haka ne Muhammadu Buhari ya yi alkawari a jawabinsa na hawa kan mulki don kawo sauyi a rundunar ‘yan sanda don karfafa mata gwiwar yaki da laifuka.

“Sai dai har yanzu ba mu ga canji ba ga wannan al’amari.”

Da yake karin haske kan wani rahoto da wata kungiya mai bincike kan harkokin aikin ‘yan sanda a duniya ta fitar a baya-bayan nan inda ta sanya ‘yan sandan Najeriya a matsayin kurar baya ta fuskar iya aiki.

Malam Kabiru Adamu ya ce bai yi mamaki ba.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Masanin ya ce duk da haka ana iya cewa an samu dan ci gaba a zamanin gwamnati mai ci ta fuskar aikin dan sanda

Kungiyar nazari da binciken kimiyyar ayyukan ‘yan sanda da hadin gwiwar wata cibiya ne suka fitar da rahoton, bayan tattaunawa da kwararru.

A mizanin kungiyar, kamata ya yi a samu dan sanda 300 da ke kula da adadin ‘yan kasa 100,000 sai dai a Najeriya dan sanda 219 ne ke kare duk mutum 100,000, “hakan kuma ya gaza,” in ji masanin.

A cewarsa batun karbuwar aikin ‘yan sandan ma a idon ‘yan kasa, al’amari ne da masanin ya ce nan akwai gibi a Najeriya.

Kabiru Adamu ya ce “batun tsarin gudanar da aikin ‘yan sanda ma a Najeriya, akwai kasawa cikinsa.”

Ya ce abin da ya fitowa fili ma a yanzu shi ne yadda dakarun sojin kasar ke gudanar da ayyukan da suka kamata a ce ‘yan sandan ne suke yi a cikin jihohi guda 28 cikin 36 na kasar.

Binciken dai kan kwazon aikin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron cikin gida a duniya ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da sukar rundunar ‘yan sandan Najeriya kan rashin iya aiki da cin hanci da rashawa.

Ko da yake, a kullum ‘yan sandan Najeriya sukan musanta irin wadannan zarge-zarge.

Masanin ya ce ko da yake, akwai dan ci gaba amma har yanzu akwai sauran rina a kaba game da ci gaban aikin ‘yan sanda a Najeriya.

An bai wa Audu Maikaba Golden Eaglets


Audu Maikaba

Image caption

Audu Maikaba shi ne kocin Akwa United, ya kuma ci kofin kalubale a shekarar nan

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta amince Audu Maikaba ya zama kocin matasa ‘yan kasa da shekara 17 da ake kira Golden Eaglets.

Kwamitin tsare-tsare da ci gaban kwallon kafar Nigeria ne ya yi bitar kwazon kocin, sannan ya bayar da shawarar da a danka wa Maikaba aikin horar da matasan na Nigeria.

Audu Maikaba tsohon kocin Kano Pillars da Enyimba, ya jagoranci Akwa United ta ci kofin kalubalen Nigeria na bana, sannan kungiyar ta yi ta hudu a gasar Firimiya da aka kammala.

Maikaba zai yi aiki da Abubakar Bala da Oluwafunsho Bunmi Haruna a matsayin mataimaka da kuma Baruwa Abiodeen a matsayin mai horar da masu tsaron ragar tawagar.

Super Eagles ta kasa kai wa gasar cin kofin duniya da aka yi a China, inda Ingila ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

'Yan Real Madrid 12 ne za su buga kofin duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid tana ta uku a kan teburin La Liga na bana

Kimanin ‘yan wasan Real Madrid 14 ne za su wakilci kasashensu a gasar kofin duniya da za a buga a Rasha a 2018.

Tun farko an tabbatar da ‘yan wasa 11 na Real Madrid da kasashensu suka samu tikitin shiga gasar da za a yi a badi, a ranar Asabar ne Morocco ta samu tikitinta, inda Achraf Hakimi ke buga wa tawagar wasa.

Sauran ‘yan wasa biyu da suka rage sune Luka Modric da Mateo ‘yan kwallon Croatia, wadanda suke buga wasan cike gurbi da Girka, a karon farko Croatia ce ta yi nasara da ci 4-1, za kuma su buga wasa na biyu a ranar Lahadi.

Ga jerin ‘yan kwallon Madrid da za su buga kofin duniya:

 • Spain: Ramos da Isco da Asensio da Carvajal da kuma Nacho
 • Brazil: Marcelo da kuma Casemiro
 • Portugal: Cristiano Ronaldo
 • Jamus: Toni Kroos
 • Faransa: Raphael Varane
 • Costa Rica: Keylor Navas
 • Morocco: Achraf Hakimi
 • Croatia: Luka Modric da kuma Mateo Kovacic

Dan Aminu ya buge Balan Kwarkwada


Dambe 112 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Daga cikin wasannin har da wanda Dan Aminun Langa-Langa daga Arewa ya buge Balan Kwarkwada daga Kudu, kuma a karon farko da ya yi nasara tun bayan da suka dade suna dambatawa.

Mohammed Abdu Mamman Skeeper ne ya hada rahoton

Wasu wasannin da aka yi kisa sun hada da Garkuwan Mutanen Karmu daga Arewa da ya buge Shagon Mai Keffi daga Kudu a turtmi na biyu.

Shi kuwa Bahagon Dan Sama’ila daga Kudu ya doke Shagon Bahagon Soja a turmin farko.

Sauran wasannin canjaras aka yi:

 • Shagon Bahagon Soja daga Arewa da Shagon Dan Sama’ila
 • Shagon Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Shagon Dogon Auta daga Kudu
 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Alaye daga Kudu
 • Usher daga Arewa da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu
 • Shagon Shagon Dan Sama’ila daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa
 • Nokia daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu
 • Sani Mai Kifi daga Arewa da Bahagon Aleka daga Kudu
 • Bahagon Aleka daga Kudu da Sani Mai Kifi daga Arewa
 • Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Bahagon Mai Maciji daga Kudu

Man United za ta dauki Asensio na Madrid


Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Asensio ya ci kwallo hudu a wasa takwas da aka fara da shi a Real Madrid

Manchester United na shirin daukar Marco Asensio, za kuma ta ba shi yarjejeniyar shekara biyar a kungiyar, in ji wani rahoto daga Spaniya.

Kocin United, Jose Mourinho na neman ‘yan wasan da za su kara masa karfin kungiyar a watan Janairu da wadanda za su buga masa tamaula a badi a Old Traford.

Jaridar Don Balon ta ce United za ta bai wa mai wasan tsakiya na Real Madrid fam miliyan 177 idan har ya amince zai koma buga gasar Premier.

Dan wasan mai shekara 21, yana da yarjejeniya da Real Madrid har zuwa kakar 2023, ya kuma ci kwallo hudu ya kuma taimaka aka zura biyu a raga a wasa takwas da aka fara da shi.

Sai dai kuma Isco na kokarin kwantar wa da Asensio hankali kan rade-radin da ake yi a kan dan kwallon.

Masu zanga-zanga sun rufe hanyar Abuja zuwa Kaduna


KadunaHakkin mallakar hoto
WhatApps

Wadansu masu zanga-zanga sun rufe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a tsakiyar Najeriya.

Wasu mazauna kauyen Sabon Gayan da ke kusa Kaduna sun rufe hanyar ce a ranar Lahadi bayan wasu da ake zargin barayi ne sun kashe wani shugaban matasan yankin.

Mutanen sun ce sun dauki matakin ne saboda yadda “saboda masu garkuwa da mutane suke cin karensu babu babbaka a yankin.”

Rahotanni sun ce dubban ababan hawa ne suka yi cirko-cirko a kan hanyar.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa masu zanga-zangar sun kwashe fiye da sa’a daya a kan hanyar.

Mai bai wa gwamnan jihar Kaduna kan harkokin siyasa Alhaji Sama’ila Yakawada ya tabbarwa da faruwar al’amarin.

Kuma ya ce akwai mutum guda da ya rasa ransa yayin da jami’an tsaro suke kokarin karbe iko da hanyar daga masu zanga-zanga.

Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya


Wasu zababbun hotunan al’amuran da suka faru a Afirka makon jiya.

Ivorians take part in the festival of Abissa in Grand-Bassam, Ivory Coast, 04 November 2017. The feast of the Abissa, a feast of rejoicing organized by the N"Zima community to symbolize the concepts of democracy and social justice. The N"Zima, a people of Ghanaian origin, finds herself around her leader and to the sounds of the tams-tams to take stock of the past year, and eventually denounce the injustices committed, or confess them publicly within the framework As part of a request for forgiveness to the people and an repentance. The festival of Abissa is celebrated each year between the end of October and the beginning of November.Hakkin mallakar hoto
EPA

An gudanar da bikin tuba da bayyana farin ciki a wurin shakatawa na Grand Bassam da ke kasar Kwaddebuwa (Ivory Coast)

Ivorians take part in the festival of Abissa in Grand-Bassam, Ivory Coast, 04 November 2017. The feast of the Abissa, a feast of rejoicing organized by the N"Zima community to symbolize the concepts of democracy and social justice. The N"Zima, a people of Ghanaian origin, finds herself around her leader and to the sounds of the tams-tams to take stock of the past year, and eventually denounce the injustices committed, or confess them publicly within the framework As part of a request for forgiveness to the people and an repentance. The festival of Abissa is celebrated each year between the end of October and the beginning of November.Hakkin mallakar hoto
EPA

Al’ummar Nzema sun halarci bikin da ake kira ‘Abissa’, ko ‘Question’. Ana kiran bikin da wannan suna ne saboda yadda mahalarta bikin suke yin tambayoyi. Ko al’ummar Nzema sun cancanci shiga sabuwar shekara kuwa?

Awoulae TANOE Amon King of Grand-Bassam is transported during the festival of Abissa in Grand-Bassam, Ivory Coast, 04 November 2017. The feast of the Abissa, a feast of rejoicing organized by the N'Zima community to symbolize the concepts of democracy and social justice. The N'Zima, a people of Ghanaian origin, finds herself around her leader and to the sounds of the tams-tams to take stock of the past year, and eventually denounce the injustices committed, or confess them publicly within the framework As part of a request for forgiveness to the people and an repentance. The festival of Abissa is celebrated each year between the end of October and the beginning of November.Hakkin mallakar hoto
EPA

An dauki basaraken gargajiyar al’ummar tare da wata yarinya ‘yar kwarai ana zagayawa da su cikin garin Bassam.

Ivorians take part in the festival of Abissa in Grand-Bassam, Ivory Coast, 04 November 2017. The feast of the Abissa, a feast of rejoicing organized by the N"Zima community to symbolize the concepts of democracy and social justice. The N"Zima, a people of Ghanaian origin, finds herself around her leader and to the sounds of the tams-tams to take stock of the past year, and eventually denounce the injustices committed, or confess them publicly within the framework As part of a request for forgiveness to the people and an repentance. The festival of Abissa is celebrated each year between the end of October and the beginning of NovemberHakkin mallakar hoto
EPA

Ana taka rawar kidan tam-tams ke tashi, wasu maza saye da kayan mata, mata kuma saye da kayan maza suna yin shagube cikin raha ga mutanen da sukia sa’ba masu a shekarar da ta gabata. Da zarar an yafe abubuwan da aka yi wa juna ba daidai ba, sai a shiga shagalin shigowar sabuwar shekara.

Nigerian Afrobeat musician Lamoj, popularly called Fela"s Ghost, sings during the Lagos International Trade Fair on November 4, 2017 in Lagos. Afrobeat musician Lamoj, also called Fela"s Ghost, is preparing to launch his album styled after late Afrobeat legend Fela Anikulakpo-Kuti.Hakkin mallakar hoto
AFP

A ranar ce kuma a Najeriya wani mawakin ‘Afrobeat’, Lamoj yake cashewa a wajen wata kasuwar baje koli ta duniya a birnin kasuwancin na Ikko (lagos). Lamoj dai yana shirin fitar da tarin wasu wakoki wadanda ya yi ta hanyar bin salo irin na shahararren mawakin nan, marigayi Fela Kuti.

Zimbabwean worshippers and congregants from various indigenous church denominations perform and dance as they wait to be addressed by Zimbabwe first lady Grace Mugabe (not in picture) at a religious gathering rally organised by Zimbabwean ruling party Zimbabwe African National Union- Patriotic Front (Zanu PF) Harare Youth Province on 5 NovemberHakkin mallakar hoto
AFP

A ranar Lahadi ne jama’ar kasar Zimbabwe suka yi ta rera waka da taka rawa a wajen wani gangamin siyasa hade da na addini da aka yi a Harare, babban birnin kasar….

Zimbabwean worshippers and congregants from various indigenous church denominations listen to Zimbabwe first lady addressing a rally on November 5, 2017 in HarareHakkin mallakar hoto
AFP

Mafi yawan mutanen da suka hallara a wajen gangamin mabiya darikokin coci ne….

Supporters of Zimbabwe"s President gather at his party headquarters to show support to Grace Mugabe becoming the party"s next Vice President after the dismissal of Emerson Mnangagwa November 8 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Reshen matasa na jam’iyyar Zanu-PF ne suka shirya gangamin, suna nuna biyayya ga matar shugaban kasar, Lady Grace Mugabe…

President Robert Mugabe listens to his wife Grace Mugabe at a rally of his ruling ZANU-PF party in Harare, Zimbabwe, November 8, 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Matar shugaban kasar ta halarci bikin tare da mijinta mai shekaru casa’in da uku, Shugaba Robert Mugabe. Matar shugaban kasar dai ta yi wani kakkausan jawabi, yayin da take haramar maye gurbin mijinta.

Moustafa, 15, carries white yarn rolls at Salama"s tannery in Cairo, Egypt, 07 November 2017. Salama started working when he was seven years old during the reign of King Farouk over Egypt because, according to him, the police used to arrest unemployed males of all ages. Now, after almost 70 years, Salama"s tannery is the only one left in the old part of Cairo. The yarn produced is used for shoe laces, mattresses upholstery, ballet dance outfits,Hakkin mallakar hoto
EPA

A ranar Talata ce kuma, wani yaro dan shekara goma sha biyar mai suna Moustafa ya ciccibi nadin farin zaren saka daga wata majema guda daya tilo da ta rage a tsohon yankin Alkahira, babban birnin kasar Masar.

Salama, 76, owner of the tannery, dyes white yarn rolls inside his tannery in Cairo, Egypt, 07 November 2017. Salama started working when he was seven years old during the reign of King Farouk over Egypt because, according to him, the police used to arrest unemployed males of all ages. Now, after almost 70 years, Salama"s tannery is the only one left in the old part of Cairo. The yarn produced is used for shoe laces, mattresses upholstery, ballet dance outfits, and suits.Hakkin mallakar hoto
EPA

A nan wani dattijo mai shekaru saba’in da shida, wanda ya mallaki majemar, yana aiki a wannan wuri tun yana dan shekara shida da haihuwa.

Libyan fishermen moor their boat at Tripoli harbour, Libya November 3, 2017.Hakkin mallakar hoto
EPA

A birnin Tripoli kuwa, babban birnin kasar Libya, masunta suna turke kwale-kwalensu a tashar jiragen ruwa…

Libyan walks at the fish market in Tripoli, Libya November 3, 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Masuntan sun baje kolin kifayen da suka kakkama, a cikin kasuwa.

An old typewriter on display at the South African Police Service"s (SAPS) Heritage Services Museum in Muizenberg, Cape Town, South Africa, 09 November 2017. South Africa has one of the highest violent crime rates in the world with a very high rate of murders, assaults, rapes and other crimes. The South African Police Service"s has released the crime statistics for 2017 showing as many as 2,129,001 serious crimes were recorded in 2017 an increase from 2015/16. The SAPS Heritage Services Museum dating back to before 1874 portrais various era"s of South African policing and documents famous crimes whilst also giving the visitor a view into a prison cell, courtroom and charge office.Hakkin mallakar hoto
EPA

Yayin da ake daukar wancan hoto a ranar Alhamis, ana nunin wata tsohon keken rubutu gidan adana kayan tarihi na ‘yan sanda a can garin Cape Town na gabar teku a kasar Afirka ta Kudu…

A 1913-1957 era charge office on exhibit at the South African Police Service"s (SAPS) Heritage Services Museum in Muizenberg, Cape Town, South Africa 09 November 2017. South Africa has one of the highest violent crime rates in the world with a very high rate of murders, assaults, rapes and other crimes.The South African Police Service"s has released the crime statistics for 2017 showing as many as 2,129,001 serious crimes were recorded in 2017 an increase from 2015/16. The SAPS Heritage Services Museum dating back to before 1874 portrais various era"s of South African policing and documents famous crimes whilst also giving the visitor a view into a prison cell, courtroom and charge officeHakkin mallakar hoto
EPA

Gidan adana kayan tarihin ya kuma baje kolin wani caji ofis wanda ya yi zamani daga shekarar 1913 zuwa 1957.

President Uhuru Kenyatta (L), Archbishop of Canterbury Justin Welby (C), and Kenyan opposition leader of the National Super Alliance (NASA) coalition Raila Odinga (R) pose for a photograph after a ceremony at the All Saints Anglican Church in Nairobi, Kenya November 5, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

A ranar Lahadi Akibishop na Canterbury, Justin Welby ya ziyarci cocin All Saints na kasar Kenya. Limamin Kiristan ya dauki hoto ne tare da wasu manyan ‘yanb siyasar kasar ta Kenya, wato Shugaba Uhuru Kenyatta da abokin adawarsa Raila Odinga. Cocin na All Saints yana bikin cika shekaru dari a wannan shekara.

Hotuna daga AFP, EPA, PA da kuma Reuters

Me zai faru idan Iran ta kai wa Saudiyya hari?


Saudi IranHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yakin Saudiyya da Iran zai jawo mummunar ta’adi

Idan kasashen Saudiyya da Iran suka fara yaki da junansu to hakan zai zama wani mummunan yaki da aka dade ba a ga irinsa, a cewar Paul Adams, wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya.

Sai dai ya ce babu wani mutum da yake ganin yaki zai iya barkewa tsakanin kasashen biyu, wadanda abokan gaba ne.

Amma ya ce kullum kasashen biyu suna nuna wa juna yatsa kuma suna yaki da juna ta bayan fage a wadansu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Me ya sa Saudiyya da Iran suke zaman doya da manja?

Takaddamar da ke tsakanin Saudiyya da Iran a ‘yan shekarun nan ta samo asali ne kimanin shekara 40 da suka wuce, daga yadda kowace take son samu gagarumin iko a yankin.

Saudiyya wadda daga nan ne addinin Musulunci ya samo asali, tana ganin ita ya fi dacewa ta kasance jagoran kasashen Musulmin duniya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ayatollah Khomeini

Sai dai a shekerar 1979 an samu juyin juya hali a kasar Iran, wanda Ayatollah Khomeini ya kafa gwamnati.

A lokacin ya samu tarbar lale marhabin daga gungun mutane wadanda ba a taba tara irin adadinsu ba a tarihin dan Adam.

Daga nan ne kasar Saudiyya ta fara kallon kasar Iran a matsayin abokiyar gaba.

Tun daga lokacin ne kuma fada jin kasar Iran ya ci gaba da wanzuwa a yankin Gabar ta Tsakiya.

Saudiyya tana ganin barazana ne kasancewar Iran wadda take daga gabashinta da kuma Lebanon wadda ke yammacinta.

Hakazalika batun addini yana taka muhimmiyar rawa wajen ruruwar zaman tankiyar da ke tsakanin Saudiyya da Iran.

Don kowannensu yana wakiltar manyan bangarori biyu ne a addinin Musulunci, wato Saudiyya tana wakiltar Sunni, Iran kuma Shi’a.

Rashin jituwar da ke tsakaninsu yana da tushe daga wannan bambance-bambancen da ke tsakaninsu a addinance.

Ta yaya kuma a ina ne suke yaki da juna?

Adams ya ce a yakin kasar Yemen Saudiyya tana goyon bayan wani bangare, yayin Iran take marawa daga gudan baya.

A kasar Syria, Iran tare da Shugaba Bashar al-Assad kuma tana tallafa mai da makamai da kuma dakaru. Saudiyya kuma tana taimakon ‘yan tawayen kasar da kudi da kuma makamai.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kifar da gwamnatin Saddam Hussein ne a shekarar 2003

Sai kuma Iraki, inda tun bayan karshen mulkin Saddam Hussein Iran take kara samun karfin fada a ji a can.

Lebanon wata kasa ce mai cike da tsarkakiya ta fuskar raba madakan ido, Iran tana mara wa kungiyar sa-kai ta ‘yan Shi’a ta Hezbollah baya ne.

Hezbollah tana cikin gwamnatin kasar kuma tana da mayaka a Syria da Iraki da kuma Yemen.

Wannan ya sa Saudiyya take ganin ikon ya yi wa Iran yawa.

Mene ne abin yi?

Yarima mai jiran gado a masarautar Saudiyya, Muhammad ibn Salman, wanda shi ne yake tafiyar da kasar, ya fara matsa wa Iran lamba yana zargin cewa za ta karbe iko da kasashen Musulmi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yarima Muhammad ibn Salman ne yake tafiyar da Saudiyya

Mutane da dama suna tunanin cewa yariman ne ya umarnin Firaministar Lebanon Sa’ad Hariri da ya yi murabus.

Firaministar ya bayyana murabus dinsa yayin da ke ziyara a Saudiyya.

“Ina so na shaida wa Iran da kawayanta cewa ba su yi nasara ba kan yadda suke shiga al’amuran kasashen Larabawa,” in ji shi.

Zargin da ake shi ne Saudiyya tana so ta fara yaki da Hezbollah ne, don ta rage mata karfin iko da kuma rage wa Iran iko.

Adams ya ce idan hakan ya tabba to babban abin tsoro ne don zai tada wani sabon yaki ne a yankin tsakanin Saudiyya da Iran.

Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassa Najeriya daban-daban a makon jiya.

 

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki yayin da sabon Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya kai masa ziyara a ofishinsa ranar Litinin
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki yayin da sabon Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya kai masa ziyara a ofishinsa ranar Litinin
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban hukumar bunkasa fasahar zamani, Sheikh Isa Pantami, yayin bikin bude wani taro kan fasahar zamani a Abuja ranar Talata
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban hukumar bunkasa fasahar zamani, Sheikh Isa Pantami, yayin bikin bude wani taro kan fasahar zamani a Abuja ranar Talata
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da za a kona jabun magunguna a harabar ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a Kano ranar Litinin.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da za a kona jabun magunguna a harabar ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a Kano ranar Litinin.
Shugaban Ma'aikatan Shugaban Najeriya, Abba Kyari, tare da Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Najeriya, Winifred Oyo-Ita, lokacin taron majalisar zartarwar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba
Shugaban Ma’aikatan Shugaban Najeriya, Abba Kyari, tare da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya, Winifred Oyo-Ita, lokacin taron majalisar zartarwar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2018 a zauren majalisar dokokin kasar ranar Talata
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2018 a zauren majalisar dokokin kasar ranar Talata
Jana'izar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, wadda aka yi wa sallah a fadar sarkin Gombe a jihar Gombe, ranar Alhamis. Marigayiyar ta rasu ne a kasar Amurka a karshen watan jiya.
Jana’izar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, wadda aka yi wa sallah a fadar sarkin Gombe a jihar Gombe, ranar Alhamis. Marigayiyar ta rasu ne a kasar Amurka a karshen watan jiya.
Uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha, yayin da ta je ta'aziyyar rasuwar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, a Gombe ranar Juma'aNIGERIA PRESIDENCY Uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha, yayin da ta je ta'aziyyar rasuwar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, a Gombe ranar Juma'a
Uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha, yayin da ta je ta’aziyyar rasuwar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, a Gombe ranar Juma’aNIGERIA PRESIDENCY
Uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha, yayin da ta je ta’aziyyar rasuwar uwargidan Sanata Danjuma Goje, Hajiya Yalwa, a Gombe ranar Juma’a
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin bikin kaddamar da wani shirin tallafawa matan jihar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ranar Alhamis
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin bikin kaddamar da wani shirin tallafawa matan jihar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano ranar Alhamis
Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf tare da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha lokacin da ta kai ziyara jihar ranar Juma'aIMO STATE GOVERNMENT Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf tare da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha lokacin da ta kai ziyara jihar ranar Juma'a
Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf tare da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha lokacin da ta kai ziyara jihar ranar Juma’aIMO STATE GOVERNMENT
Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf tare da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha lokacin da ta kai ziyara jihar ranar Juma’a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da mambobin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da mambobin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatu Bidi'a Wa'iqamati Sunna (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala-Lau, a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatu Bidi’a Wa’iqamati Sunna (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala-Lau, a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da malaman addinin Musulunci a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da malaman addinin Musulunci a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a
Wani bangare na kasuwar garin Nguru da ke jihar Yobe, inda gobara ta cinye shaguna a safiyar ranar Asabar
Wani bangare na kasuwar garin Nguru da ke jihar Yobe, inda gobara ta cinye shaguna a safiyar ranar Asabar

 

An gano diamond da ya nauyinsa ya kai karat 400 a Saliyo


Kawo yanzu dai masana basu fayyace darajar diamond din da aka gano baHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kawo yanzu dai masana basu fayyace darajar diamond din da aka gano ba

Masu hakar ma’adinai a Saliyo sun hako wani diamond wanda nauyinsa ya kai karat 476, kuma an ce shi ne diamond na 29 ma fi ya girma da aka gano.

Kawo yanzu dai kwararu basu tabbatar da darajar ko kuma kudin diamond din ba.

Lamarin dai na zuwa ne bayan da aka gano wani daimaond da nauyinsa ya fi karat 700, wanda shi ne diamon mafi girma da aka gano a Saliyo a cikin rabin karni.

A watan gobe dai zaa ayi gwajonsa a birnin Newyork na Amurka.

Shugaban hukumar ma’adinai ta kasar Saliyo, Sahar Wonday ya ce diamond din da aka gano ya nuna cewa akwai albarkatun kasa masu daraja a yankin Kono, inda a nan ne aka gano dukannin daimond din su biyu.

Kasar na son tayi amfani da cinikin watan Disemba domin ta yi kokarin kawar da abubuwan da suka faru a baya watau yakin basasa da aka shafe shekara 11 ana yi wanda kasuwanci diamond na cikin abubuwan da suka rika ruruta rikicin.

Karanta yadda gurgu ke koya wa masu kafa hada takalma


Image caption

Tukur Abubakar yana son matasa su dogara da kansu

Tukur Abubakar, wani mai nakasa ne da ke koya wa masu lafiya da nakasassu aikin hada takalma a kauyen Karmajiji da ke Abuja.

A lokacin da yake yaro, Tukur Abubakar ya yi fama da cutar Polio wadda ta nakasa kafafunshi kuma ta sa a yanzu yake tafiya da hannunsa na hagu da kuma na dama cutar ta dan taba.

Tukur ya shaida min cewa nakasarsa ba ta taba sa shi sha’awar bara ba.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda gurgu ke koya wa masu kafa sana’a a Abuja

Maimakon hakan, ya fi mayar da hankali ne kan yadda zai samu na kansa.

Da na ziyarci shagonshi na langa-langa da ke karmajiji, wadanda suke koyan aiki a wajensa sun zauna cikin inuwar gaban shagonsa suna kallon shi yana koya musu aiki.

Tukur Abubakar yana juya keken dinkinsa da hannunsa na dama wanda cutar Polio ta nakasa.

Yana dinka igiyar wani sabon takalmin da yake hadawa ne.

Image caption

Masu koyan sana’ar a wurin shi sun ce suna fatan suma za su samu damar dogaro da kansu a nan gaba

Yana dan tsayawa lokaci-lokaci domin ya bayyana wa masu koyan aiki su bakwai da ke zaune cikin inuwar gaban shagonsa, yadda yake aiki.

Sai dai a shagonsa Tukur ana fuskantar kalubale da ya dara aiki da tsohon keken tafi-da-gidanka.

Dole ya hau boris din guragu domin ya je shagon cajin waya, inda zai samu wutar lantarki ta janareto wanda zai yi amfani da shi wajen tayar da injin goge gefen takalman da ya hada.

Image caption

Tukur ya ce shi bai taba sha’awar bara ba

Me ya sa mai kafa zai koyi aiki a wurin mara kafa?

Daya daga cikin masu lafiyar da Tukur ke koya wa aiki, Aminu Adamu, ya ce suna koyar aikin ne domin su ma su samu hanyar dogara da kansu nan gaba.

Tukur ya ce shi ma yana matukar son ya ga mutane sun dogara da kansu domin a ganinsa yawan rashin aikin yi ne yake jaw

Ana fargabar barkewar cututtuka a Congo


Al'ummar Kisangani a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sun koma dibar ruwa a rafi da rijiya saboda yankewar wutar lantarki da ruwan sha kwana da kwanakiHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Al’ummar Kisangani a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sun koma dibar ruwa a rafi da rijiya saboda yankewar wutar lantarki da ruwan sha kwana da kwanaki

Ana ci gaba da nuna damuwa game da yiwuwar barkewar cututtuka sakamakon amfani da gurbatattcen ruwa a Kisangani, birni na uku mafi girma a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Tun a ranar Alhamis din data gabata ne ruwan fanfo da wutar lantarki suka yanke a birnin.

Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar ya ce, mummunan ambaliyar ruwa ce ta haddasa daukewar lantarki a babbar tashar samar da wuta.

Yanzu birnin wanda yake da mutane fiye da miliyan daya da rabi, ya dogara ne da ruwan da ba’a tace ba wanda ake debowa daga rijiyoyi da rafuka.

Rahotanni sun ce shugaban kasar Joseph Kabila, ya samar da injin din janareta wanda aka ajiye shi a babban asibitin da ke birnin, domin a samu hasken lantarki don a ci gaba da kula da marassa lafiya yadda yakamata.

Akasarin na’urori da ababan more rayuwa a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congon dai sun lalace saboda shekara da shekaru ba’a kulawa da su.

Nigeria: An fara amfani da waka wajen yaki da cin hanci


Hukumar EFCC ta ce amfani da mawaka wajen isar da sakonta, zai yi matukar tasiri a tsakanin al'ummar Najeriya, musamman mata da yaraHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Hukumar EFCC ta ce amfani da mawaka wajen isar da sakonta, zai yi matukar tasiri a tsakanin al’ummar Najeriya, musamman mata da yara

A Najeriya, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, wato EFCC, ta rungumi wata sabuwar dabara ta amfani da mawakan Kannywood don shelar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin mata da yara.

Hukumar ta yi wani gangami a Kano, inda fitattun mawaka suka nuna basirarsu wajen isar da sakon hukumar ta hanyar waka.

EFCC dai, ta bayyana cewa shigar da mata da yara a cikin yaki da cin hanci na da muhimmanci sakamakon matsayinsu a tsakanin al`uma kasancewar mata sune ginshikin tarbiyya ga yara da ake fatan su ne manyan gobe.

Dr Adamu Hamisu Danmusa, shi ne Daraktan ayyuka na hukumar EFCC mai kula da shiyyar arewa maso yamma ya ce, sun yanke shawarar fara amfani da mawaka ne domin isar da sakon da suke son isarwa ga al’umma musamman mata da yara a kan illar cin hanci.

Daraktan ya ce, mawaka ba bu inda ba sa isar da sako ta hanyar waka, don haka suke ganin amfani da mawakan zai taimaka wajen isar da sako ga al’umma, domin ba sai a rinka hada taruka don fadakar da mutane illar cin hanci ba.

Dr Adamu, ya ce dama an san mata da son waka, to ta hanyar waka za su isar da sakonni da dama.

Image caption

Mawakan Kannywood sun ce za su yi bakin kokarinsu wajen isar da sakon EFCC

A Najeriyar dai ana kukan cewa babu wani bangaren rayuwa da cin hanci bai ratsa ba.

Najeriya dai kasa ce mai arzikin man fetur tun farashi na ganiyarsa, da wasu muhimman albarkatun kasa, ga kuma yawan jama`a, amma duk da haka galibin al`ummar kasar na fama da talauci sakamakon cin hanci da rashawa.

Kodayake gwamnatin shugaba Buhari ta yi alwashin yaki da wannan annoba.

An gano manyan ramuka da ke dauke gawarwwakin mutum 400 a Iraki


Sojojin Iraki sun kaddamar da sabon farmak domin kwato garin Rawa daga mayakan ISHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sojojin Iraki sun kaddamar da sabon farmak domin kwato garin Rawa daga mayakan IS

Wani babban jami’i a Iraki ya ce an gano wasu manyan kaburbura wadanda suke dauke da gawarwwakin mutane 400 a wani wuri da ke kusa da garin Hawija, inda a nan ne aka fatattaki mayakan kungiyar IS a makon daya gabata.

Gwamnan yankin Kirkuk ya ce an gano ramukan ne a sansanin sojin sama da ke arewacin Iraki.

Ya ce wasu daga mutanen da aka kashe na sanye ne da tufafin wandanda mayakan IS suka yanke ma hukunci kisa, ya yinda sauran na sanyene da tufafi fararen hula.

Sojoji Iraki sun gano gomman kaburbura a wasu yankuna , wadanda a baya suke karkashin ikon mayakan IS.

Lamarin na zuwa ne bayan da sojojin Iraki suka kaddamar da farmaki domin sake kwato garin Rawa, wanda shi ne gari na karshe da ke karkashin ikon mayakan IS.

Garin da kuma wasu filaye sun kasance karskashin ikon IS bayan da sojoji Iraki suka kwace garin al Qaim daga hannunsu a makon daya gabata.

An samu kasashe biyar da za su Rasha a 2018


World CupHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kasashe biyar ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci

An samu kasashe biyar da za su wakilci Afirka a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Tun a ranar Juma’a Senegal ta samu tikitin zuwa Rasha, bayan da ta doke Afirka ta Kudu har gida da ci 2-0, hakan ya sa ta hada maki 11 a rukuni na hudu, Sai Afirka ta Kudu mai maki 6.

A ranar Asabar Morocco ta samu damar kai wa gasar da za a yi a Rasha bayan da ta ci Ivory Coast har gida 2-0, hakan ya sa ta hada maki 12 a rukuni na uku.

A dai ranar Asabar din Tunisia ita ma za ta wakilci Afirka a Rasha a badi, duk da tashi wasa da ta yi babu ci tsakaninta da Libya, wanda hakan ya sa ta samu maki 14, Jamhuriyar Congo ta kare da maki 13.

Tun farko Nigeria ce ta fara samun tikiti a Rasha, bayan da ta ja ragamar rukuni na biyu duk da saura wasa daya ya rage, inda ta hada maki 14, bayan da ta tashi 1-1 da Algeria a ranar Juma’a.

Ita ma Masar ta kai bantenta, bayan da ta yi ta daya a rukuni na biyar da maki 12. Kuma ita ce ta biyu a samun matakin zuwa Rasha daga Afirka.

'Yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na BBC


An bayyana ‘yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017 su biyar da suka hada da Pierre-Emerick Aubameyang da Naby Keita da Sadio Mane da Victor Moses da kuma Mohamed Salah, an kuma bude kada kuri’a domin zabo wanda zai lashe kyautar bana.

Ga tarihin ‘yan wasan da gwawarmayar da suka yi da sashen wasanni na BBC ya shirya:

PIERRE-EMERICK AUBAMEYANG –Dan wasan Gabon da Borussia Dortmund

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wannan ne karo na biyar a jere da Aubameyang ke cikin ‘yan takara

Ba a taba samun wani dan Afirka ba wanda ya fi kowa cin kwallaye a gasar Bundesliga har sai da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallaye 31 a kasar wasan 2016-17.

Wannan nasara ba wai kawai ta bai wa dan wasan dan asalin kasar Gabon damar dusashe tauraruwar dan wasan kasar Ghana, Tony Yeboah ba, wanda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye har karo biyu a 1990, Pierre ne mutum na hudu a duniya da ya zarga kwallaye 30 a raga a gasar Bundesliga, irinsa na farko a tsawon shekara 40.

Wani kuma abun ban sha’awa dangane da nasarar fitaccen dan wasan na kungiyar Dortmund shi ne yadda ya ci kwallayen 31 a jerin wasanni 32, al’amarin da ya sanya kulob din nasa kasancewa na daya a gasar ta Bundesliga har karo biyu a jere sakamakon baiwar gudu da ta cin kwallaye da Allah ya huwace masa.

Kwallaye ukun da ya ci kulob din Benfica a wasa daya, a watan Maris ne suka sanya kididdigar jumullar kwallayen da dan wasan ya ci suka zama 40 a gasar Zakarun Turai ta Champions League. Kwallon da ya ci a wasan da kulob dinsa ya ci Eintracht Frankfurt 2-1 wadda ta bai wa Dortmund damar daukar kofi a gasar wasan kwallon kafar Jamus na daya daga cikin kwallayen da ya ci 40.

Sakamakon kwazon Aubameyang mai shekara 28 ne ya sa aka sanya sunansa a jerin sunayen ‘yan wasan da za a zabi gwarzon dan wasan duniya na FIFA. kuma Aubameyang ne dan wasa daya tilo daga Afirka a jerin ‘yan wasan na FIFA, ko da yake Sadio Mane da suke takara tare domin lashe kyautar gwarzon Afrika na BBC yana cikin jerin ‘yan wasan da ke takarar lashe kyautar Ballon d’Or.

Duk da tsammanin da ake da shi cewa dan wasan dan kasar Gabon wanda dan gayu ne zai bar kulob din Dortmund a karshen kaka har yanzu hakan bai kasance ba. Manyan kungiyoyin wasa kamar Paris Saint-Germain da Manchester City sun nuna sha’awarsu kan dan wasan. Sai dai kuma dan wasan ya dade yana burin buga wa kulob din da kakansa ya fi so wato Real Madrid, wasa, amma har yanzu burinsa bai cika ba sakamakon rashin nuna sha’awarsa, duk kuwa da irin baiwar cin kwallaye da ya nuna a Dortmund tun 2013.

Bugu da kari, a yanzu haka kwallayen da Aubameyang ya ci 135 a wasanni 204 na nufin zai iya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a kulob din Dortmund, kuma hakan na nufin zai iya zarta Michael Zorc daga nan zuwa karshen shekara.

‘Auba’ kara kwazo yake yi fiye da abun da ya yi a baya, a inda ya zura kwallaye takwas a wasanni shidan farko na gasar Champions League.

To sai dai idan an diba batun kimar kasar dan wasan ta asali wato Gabon a kwallon duniya, za a iya cewa kyaftin Aubameyang bai ji dadin yadda kasar tasa ta kasa kai bantanta a gasar zakarun kwallon kafar nahiyar Afirka ba duk kuwa da cewa shi ne mutumin da ya jefa kwallaye biyu a wasanni uku. Abun tambaya a nan shi ne ko rawar da yake takawa a Dortmund za ta ba shi damar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka?

Naby Keita – Dan wasan Guinea da RB Leipzig

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Keita ya ci kwallo takwas a Bundesliga ya kuma taimaka aka ci bakwai, dalilin da ya sa shi ne fitatcen dan kwallon tsakiya a Jamus

Watakila Naby Keita ya kasance dan kwallon da ba a san shi ba a Jamus a kakar wasanni ta 2016-17, to amma kuma sai ga shi sunansa ya fado cikin jerin shahararrun ‘yan wasa 11 da aka zaba a kungiyar Bundesliga na shekara. Dan wasan na Guinea ya samu kuri’un jama’a fiye da duk wani dan wasan tsakiya da ke taka leda a Jamus.

Kungiyar Red Bull Leipzig na daya daga cikin wadanda suka yi bazata a kakar wasanni ta 2016-17 kasancewar kulob din na biyu a teburin gasar Bundesliga sannan kuma ta samu damar yin katabus a gasar zakarun Turai ta Champions League sakamakon kwazon Keita.

Minti biyar da fara wasansa na farko a gasar ta Bundesliga, Keita wanda aka saya daga kulob din kasar Austria wato Red Bull Salzburg ya ci wa Red Bull Leipzig kwallo a wasansu da Borussia Dortmund abun da ya bude ma sa kofar zama gwarzon shekara a kungiyarsa da Bundesliga.

Keita ya jefa jimullar kwallaye 8 a gasar Bundesliga, inda kuma ya taimaka aka ci kwallaye guda bakwai. Wani abu da ya kara wa dan wasan mai shekaru 22 kima shi ne kasancewar sa dan baya mai kyau.

Saboda a duk wasa irin kwallon da Keita yake bugawa ce ke kayatar da ‘yan kallo.

Kasancewar Keita dan wasan tsakiya da ke shafa leda gaba da baya, kuma ba ya wasa da zarar ya sami kwallo wanda hakan ke firgita abokan gaba har suke bayyana shi kamar daya tamkar dan wasa biyu, al’amarin da ya janyo masu horar da ‘yan wasa ke kaunar sa.

Keita kwararre ne a sarrafa kwallo, yana da kuzari da basirar hangen nesa wajen yi wa abokan wasa tazara( Alkalumma sun nuna ya fi dan wasan Bayern Munich Arjen Robben yawan yanke a kakar da ta gabata) yakan ci kwallo ya kuma mika a ci.

Wani abun mamaki shi ne yadda kocinsa a Leipzig wato Ralph Hasenhuttl ya danganta shi a matsayin dan wasa mafi muhimmaci, wanda basirarsa ta taka leda ba a saba ganin irinta ba.

Keita wanda aka Haifa a birnin Conakry ya janyo hankalin kungiyar Liverpool har ta sanya makudan kudi da ba ta taba zuba wa ba domin sayen wani dan wasan Afirka, inda ta sanya £48m kan dan wasan domin taka mata leda a 2018. Sai dai kuma daga baya kungiyarsa ta Leipzig ta yi da-na-sanin sayar da shi.

Sunan Keita na daga jerin sunayen ‘yan wasan da ke fatar buga wa Guinea wasa a Russia a 2018 kuma koda dan wasan ya ci wa kasarsa kwallaye a wasannin neman cancantar shiga gasar da ta fafata da Libya da Tunisia, to za a iya cewa Guinea ba ta samu cancantar ba cikin sauki.

Keita ya ce a har kullum Yaya Toure ne gwaninsa. Saboda haka yanzu abin tambaya shi ne ko Keitan zai iya yin irin abin da Toure ya yi ta hanyar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka a jerin kyaututtukan da ya lashe?

Sadio Mande – Dan wasan Senegal da Liverpool

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mane daya ne daga cikin ‘yan wasan Afirka biyu da suke takarar kyautar Ballon d’Or

Sadio Mane Dan wasan Senegal da Liverpool kakarsa sa yi kyau a 2017, Kuma kamar yadda aka zabi dan wasan cikin jerin tawagar zaratan ‘yan wasan PFA na bana a ingilia, yana kuma cikin ‘yan wasan Afrika biyu a cikin jerin sunayen ‘yan wasan da aka zabo domin lashe kyautar Ballon d’Or.

Ya kuma taka rawar gani wajen taimakawa Senegal shiga gasar cin kofin duniya a karo na biyu, nasarar da ba su samu ba tun shekarar 2002.

A bana Mane ya ci wa Senegal kwallaye 4.

A farkon shekara, Mane ya dace da irin rawar da ya ke takawa, ya iya zarra, ga yanke da karfin iya cin kwallaye a raga.

Ko da yake Mane ya fuskanci kalubale a shekararsa ta bana, domin duk da ya ci wa Senagal kwallaye biyu a wasannin rukuni a gasar cin kofin Afrika, amma ya barar da fanareti a wasan dab da na kusa da na karshe, wannan ne kuma ya karfafawa kamaru guiwar zuwa ta lashe kofin gasar.

A lokacin Mane, da idon duniya ya koma a kansa ya shatata kuka, domin ya barar da damar shiga sahun zaratan ‘yan wasa da suka taba lashe kofin Afrika.

Sai dai kuma hakan ya yi wa Liverpool da magoya bayanta dadi domin nasara daya ne kacal kungiyar ta samu a wasanni 7 da ta buga bayan tafiyar Mane wakiltar kasarsa a gasar cin kofin Afrika.

Da dawowarsa ne Mane ya taimakawa Liverpool samun galaba akan Tottenham da ci 2-0, daga bisani kuma ya ci wa Liverpool muhimman kwallaye a nasarar da ta samu akan abokan gaba Arsenal da Everton.

Victor Moses – Dan wasan Nigeria da Chelsea

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Moses ya ci kofin Premier League a Chelsea bayan da ya nuna kwarewarsa a tamaula a Stamford Bridge

Lokacin da Victor Moses ya waiwayi tarihin wasansa, akwai yiwuwar dan wasan Najeriyan da kuma kungiyar Chelsea, ya ce kakar shekarar 2016 zuwa 2017 ce ta fi muhimmanci a gare shi.

Bayan shekarun da ya yi wasa a matsayin aro, daga bisani ne ya koma Chelsea – inda ya zama daya daga cikin manyan ‘yan wasa da suka taka muhimmiyar rawa wajen lashe kofin firimiya.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne kocin Chelsea, Antonio Conte ya gwada sanya Moses a wasan da suka doke Arsenal da Liverpool, inda kocin ya gwada salon 3-4-3.

Wannan ne wasansa na farko a Chelsea a cikin fiye da shekara uku, amma Moses ya rika nuna kwazonsa da basirarsa.

Wasan da suka doke Hull City yana cikin wasanni 13 a jere da Chelsea ba ta sha kayi ba, kuma na 22 da Moses ya buga, sai dai daga bisani ya shiga jinyar raunin da ya ji a watan Afrilu.

A watan da ya gabata ne dan wasan ya kara sanya hannu a wani sabon kwantiragi da kolub din Chelsea, inda zai ci gaba da taka leda kungiyar, wadda ya fara koma a shekarar 2017.

Conte ya bukaci sabunta kwantiraginsa ne saboda yadda ya kara ganin kwarewar Moses a wannin share fagen fara kaka.

Dan wasan mai shekara 26, ya ce yana samun nasara ta hanyar nuna kwazo da natsuwa da kuma zafin nama.

Bayan lashe gasar firimiya, Moses yana cikin ‘yan wasan Chelsea da suka zo na biyu a gasar Kofin FA, bayan Arsenal ta doke su, inda Moses ya samu jan kati.

Moses ya buga wa kasarsa wasa ne sau uku kadai a bana, amma a wasansa na farko ya ci kwallo a karawar da Najeriya ta doke Kamaru da ci 4-0, abin da ya sa Najeriya ta samu damar zuwa gasar Cin Kofin Duniya.

Mohammad Salah Dan wasan Masar da Liverpool

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Salah ne ya ci fenaritin raba gardama da ya kai Masar gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018, bayan rabon da ta je tun 1990

Abu daya zai sa ba za a taba mantawa ba da Mohammed Salah a tarihin kwallon kafa a Masar, saboda kwallo mafi muhimmaci da ya ci wa kasarsa a ragar Congo ana dab da a hure wasan da suka kara a watan Oktoba, wanda ya ba kasar nasarar shiga gasar cin kofin duniya karon farko bayan shekaru 27.

Sau bakwai Masar na lashe kofin Afrika amma tun1990 rabon da kasar ta je gasar cin kofin duniya. Salah ne ya taimakawa kasar tsallakewa bayan ya ci fanareti a wasan da suka tashi ci 1-1 da Congo. Cin kwallon ke da wuya murna ta barke da shagali a ciki da wajen filin wasan.

Duk da cewa Salah ya dade yana cin kwallaye, amma tarihi ba zai taba mantawa da shi ba a Masar, domin ya wadatar da ‘yan kasar daga kishirwar da suka dade suna fama.

Salah ya samu yabo da girmamawa daga shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi.

Cin kwallon ne ya sa ‘yan kasar ke yi wa Salah da kirari a matsayin “Sarkin Masar mai zamani” domin ko baya ga kwallon da ya ci a ragar Congo, Salah ya jefa kwallaye biyar a raga a wasannin bakwai da suka tsallakar da Masar zuwa Rasha.

Salah ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a 2017, inda ya shiga sahun ‘yan wasa 11 da aka zabo mafi shahara a gasar, bayan ya ci kwallaye biyu tare da taimakawa aka ci hudu. Sannan ya taimakawa kasarsa zuwa matakin karshe a gasar, ko da yake Kamaru ce ta lashe kofin na Afrika.

Baya ga kasarsa, Salah sananne ne wajen cin kwallaye a kungiyoyin da ya ke taka leda musamman a Roma da Liverpool.

Tauraron Salah ya kara haskawa bayan ya dawo liverpool a watan Yuni, inda a watannin Agusta da Satumba aka bayyana shi a matsayin gwarzon dan wasan Liverpool.

Salah ya ci kwallaye 7 a wasannin Premier 11 da ya bugawa Liverpool, tare da cin kwallaye 5 a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai 6 da Liverpool ta buga.

A zamanin da yana Italiya, Salah ya taimaka wajen farfado da martabar Roma a Seria A, a kakar wasa daya da ya buga wa kungiyar inda ya ci kwallaye 15 tare d bayar wa aka ci kwallaye 11 a Lig . Kuma an kammala kakar 2016/2017 Roma na matsayi na 2 a teburin lig, tazarar maki hudu tsakaninta da Juventus.

Thierry Henry ya danganta Salah a matsayin dan wasa na musamman, amma ko dan wasan zai iya zama dan kasar Masar na farko da zai iya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na BBC bayan Mohamed Aboutrika da ya lashe kyautar a 2008.

Neymar ya yi kwana 100 a PSG


PSGHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Neymar ya ci kwallo 11 ya kuma taimaka aka zura tara a raga tun komawarsa Paris St-Germain da taka-leda

A ranar 3 ga watan Agustan 2017 ne Neymar ya koma Paris St-Germain daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Dan wasan Brazil, mai shekara 25, ya fara buga wa PSG tamaula a karawar da za ta ziyarci Guingamp a ranar Lahadi 13 ga watan Agusta a makon farko a Ligue 1, inda ya ci kwallo daya a fafatawar.

Neymar wanda ya koma Faransa da taka-leda kan fam miliyan 200, ya kuma ci biyu a karawar da PSG ta doke Toulouse 6-2 a mako na biyu a gasar Faransa a ranar 20 ga watan Agusta.

Sauran kwallayen da Neymar ya ci sun hada da guda daya da ya zura wa Metz da wadda ya ci Celtic a gasar cin kofin Zakarun Turai ya kuma ci Bayern Munich daya duk a gasar ta Zakarun.

A ranar 30 ga watan Satumba ya ci Bordeaux biyu a fafatawar da PSG ta yi nasara da ci 6-2 a gasar cin kofin Faransa.

Daga nan ne Neymar ya ci Andelecht kwallaye biyu, daya a Paris daya a Belgium a gasar Zakarun Turai sannan ya zura wa Merseille daya a gasar Faransa.

Jumulla dan wasan ya ci kwallo 11 ya kuma taimaka aka ci tara, ya kuma karbi katin gargadi mai ruwan dorawa bakwai da jan kati daya da aka yi masa a karawa da Marseille.

Kwana dari da Neymar ya yi a PSG tana ta daya a kan teburin gasar Faransa, sannan ta kai zagaye na biyu a wasannin cin kofin Zakarun Turai.

Super Eagles ta hada maki 14 a wasa shida


Hakkin mallakar hoto
The NFF

Image caption

Super Eagles ce ta fara samun tikitin kai wa Rasha a nahiyar Afirka

Tawagar kwallon kafar Nigeria ta Super Eagles ta hada maki 14 a karawa shida da ta buga a wasannin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Super Eagles wacce ita ce ta farko da ta samu tikitin zuwa buga gasar kofin duniya daga Afirka ta tashi wasa 1-1 da Algeria a ranar Asabar.

Hakan ne ya sa Nigeria take ta daya a rukuni na biyu a wasannin shiga gasar cin kofin duniya a wasa shida da ta yi jumulla, ta ci karawa hudu ta yi canjaras biyu ta kuma ci kwallo 12 an zura mata 4 a raga.

Zambia wacce take ta biyu a runin na biyun da maki bakwai za ta karbi bakuncin Kamaru mai maki shida kuma ta uku a teburin da za su kara a ranar Asabar.

Ga sakamakon wasannin da Super Eagles ta buga:

 • Zambia 1-2 Nigeria
 • Nigeria 3-1 Algeria
 • Nigeria 4-0 Kamaru
 • Kamaru 1-1 Nigeria
 • Nigeria 1-1 Zambia
 • Algeria 1-1 Nigeria

Nigeria: Gobara ta cinye shaguna a kasuwar Nguru


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Nguru

Wata mummunar gobara ta cinye shaguna da dama a babbar kasuwar garin Nguru da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda wani ganau, Sani Ballack, ya shaida wa BBC ta waya.

Ya ce “gobarar wadda ta cinye shaguna akalla 500 ta jawo mummunar asara ga ‘yan kasuwa, kodayake ba a samu asarar kai ba, sai dai jikkata”

Har ila yau ya ce gobarar wadda ba a samu an kashe ta ba har zuwa safiyar Asabar ta samu asali ne “daga tattatsin wayar wutar lantarki.”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe DSP, Jafiya Zubairu, ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Sai dai ya ce bai san girman barnar da aka tafka ba a kasuwar.

Ana sayar da atamfofi ne da kayan gine-gine da turare da dai sauransu a kasuwar.

Hakkin mallakar hoto
Sani Ballack

'Na fara shan Codeine ne bayan mutuwar aurena'


Filin ya duba yadda mata masu tu’ammali da miyagun kwayoyi suke rayuwa.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta zama ruwan dare game duniya, musamman a arewacin Najeriya.

Abin da tada hankali shi ne yadda ‘yan mata suke shiga irin wannan mummunar dabi’a. Tun daga fatauci da sayarwa da kuma kwankwadar miyagun kwayoyin.

Me yake sa su shiga harkar?

Me zai ya sa mace wadda take rayuwar kyakkyawa ta fara tu’ammali da miyagun kwayoyi, wanda hakan yake mummar cutar da rayuwa.

Na gana da wadansu ‘yan mata a birnin Kano wadanda suke tu’ammali da miyagun kwayoyi. Suna guje wa gidajensu, suna yawo daga otel zuwa otel ko kuma dakunan samari.

Har ila yau na tattauna da Mummy, daya daga cikin manyan dilolin miyagun kwayoyin mata . Ta shaida min cewa galibin masaya kwayoyin mata ne.

Kamar yadda ya ce, galibin masu sayan kayan mayen matan aure wadanda suke fama da bakin cikin zamantakewar aure.

Kuma suna shan kwayoyin ne saboda su dauke hankalinsu daga damuwar da suke ciki.

Na hadu da wata yarinya wadda ta ce min ta fara shan miyagun kwayoyi ne bayan saurarinta ta yi watsi da ita.

Wata kuma ce min ta yi ta fara ne bayan mutuwar aurenta, lokacin da damuwa da kuma bakin ciki suka yi mata dabaibayi ne ta fara kwankwadar kwalaban Codeine.

Laifin wane ne? Na iyaye ne? Ko tsohon mijinta? Ta yaya hara bin ya kai wannan matakin?

Nigeria: Buhari ba shi da dalilin tsare Zakzaky – Soyinka


 • Latsa alamar lasifika dake sama don sauraron cikakkiyar ganawar da farfesan ya yi da BBC.

Farfesa Wole Soyinka ya ce ci gaba da tsare shugaban kungiyar ‘yan Shi’a ta (IMN) Sheikh Ibrahim el-Zakzaky ya keta hakkin dan Adam.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Jimeh Saleh, Editan sashen Hausa na BBC, yayin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan.

Ya ce shi bai ga dalilin da ya sa za a ci gaba da tsare malamin ba, kuma “hakan kuskure ne.”

Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin kasar take tsare da malamin bayan rikicin mambobin kungiyarsa da sojojin kasar a Zariya.

Sai dai ya ce duk da cewa akwai fannoni da dama da gwamnatin Buhari “ta tafka kurakurai wadanda suka cancanci suka, akwai kuma fannonin da ya kamata a yaba mata”.

Ya ba da misali da yadda gwamnati ta yi aiki wajen gano kudin da aka sace wadanda aka kai kasashen ketare.

Da kuma yadda aka sa “wadansu manyan jami’an gwamnati suka amayar da kudin da suka sace”.

Hakazalika farfesan ya ce shugaban zai iya cewa ya cika aikin da aka zabe wato aikin yaki da cin hanci da rashawa da kuma shawon kan rikicin Boko Haram da kuma makamantanta.

Karanta wadansu karin labarai

Otel din kasaita ya koma gidan yarin ministocin Saudiyya


La fachada principal del hotel Ritz-Carlton en Riad, la capital saudita.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Manyan attajirai da ‘yan gidan sarautar Saudiyya suna sauka ne a otel din Ritz-Carlton

Masauki ne na kasaita da ‘yan kasuwa da hanshakan attajiran duniya ke sauka, kuma duk wanda ya taba sauka ba zai taba mantawa da masaukin ba a matsayin daya daga cikin manyan otel da ake da su a duniya.

Ritz-Carlton, Otel ce da shugabannin kasashe da Firaministoci ke sauka, domin masauki ne na hamshakan attajirai.

Amma, kafofin yada labarai a Riyadh sun ruwaito cewa, otel din yanzu ya koma wani gidan yarin kasaita.

Kasa da watanni shida da shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a Ritz-Carlton a ziyararsa ta farko a Saudiyya.

Sai ga shi yanzu masaukin na kasaita ya koma gidan yarin wasu shahararrun mutanen Saudiyya da suka saba sauka a otel din.

Wannan ya sa wasu ke danganta Otel din yanzu a matsayin wani “Babban gidan yarin kasaita a duniya”.

An kame Yarimomi ‘yan gidan sarautar Saudiyya da ministoci hudu da wasu manyan ‘yan siyasa da suka hada da tsoffin ministoci, a wani mataki da gwamnatin kasar ta kira yaki da cin hanci da rashawa a Saudiya,

Cikin wadanda ake tsare da su har da Yarima Alwaleed bin Talal, hamshakin attajiri da ke da hannun jari a kamfanin Apple da Twitter.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A makon jiya ne kafa sabon kwamitin yaki da cin hanci da rashawa wanda Yarima Mohammed bin Salman ya ke shugabanta

Ko da yake, babu tabbaci daga hukumomin Saudiyya ko ana tsare su ne a cikin ginin otel din Ritz-Carlton, amma jaridar Guardian ta Birtaniya ta ambato wani babban jami’in gwamnatin kasar na cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ba zai kargame su ba a gidan yari.

Otel din wanda aka gina shekaru shida da suka gabata, yana da yawan daki 492, kuma girmansa da harabar ginin ya kai sukwaya mita 200,000.

Katifu a wani dakin kasaita

Wani bidiyo da jaridar New York Times ta wallafa a ranar Talata ya nuna katifu kanana da aka baza a wani babban dakin taro a Ritz-Carlton.

Bidiyon ya nuna wasu mutane a kwance, lullube da bargo a cikin otel din da kafofin yada labarai da dama suka ce wani dakin taro ne da ke daukar yawan jama’a kimanin 2,000.

Wata ‘yar jaridar kafar talabijin ta Al Jazeera, Khadija Benguenna ta yada hotunan cikin ginin otel din, wasu mutanen kwance a katifu a shafinta na twitter.

Image caption

Wani bangare na otel din Ritz-Carlton

Anuj Chopra wakilin kamfanin dillacin labaran AFP a Riyadh ya ruwaito cewa tun a ranar Lahadi ‘Yan sanda ke sintiri a ciki da wajen ginin otel din, tare da rufe kofar shiga.

Sannan an wallafa wata sanarwa a shafin otel din na intanet cewa: ” saboda wasu matsaloli da suka taso, an toshe shafin da tarho har zuwa wani lokaci”.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, bakin da suka riga suka kama daki a Ritz-Carlton a ranar Asabar an bukaci su kwashe kayansu inda aka canza ma su otel a birnin Riyadh.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shekara shida ke nan da otel din ya fara karbar baki

Ko zan iya kama daki?

Shafin intanet na Ritz-Carlton ya nuna cewa babu daki da wani zai iya kamawa a watan Nuwamba, ko da yake, a tsakiyar Disamba an nuna mutum na iya kama daki biyu lokaci guda akan kudi 1,300 na riyals, kwatankacin dalar Amurka 350?

Karanta wadansu karin labarai

Saudiyya na takalar Lebanon- inji Hezbollah


Hassan Nasrallah ya ce ko shaka babu an tilasta ma Saad Hariri yin muraus ne a Saudiiyya.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hassan Nasrallah ya ce ko shaka babu an tilasta ma Saad Hariri yin muraus ne a Saudiiyya.

Shugaban kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya ce a bayanne take cewa Saudiyya ce ta tilastawa Sa’ad Hariri yin murabus.

Jagoran kungiyar ta Hezbollah da ke Lebanon ya zargi Saudiyya da ayyana yaki kan kasarsa, bayan wasu kwanaki da fira ministan Lebanon Saad al Hariri ya yi shellar ajiye mukaminsa a Riyahd babban birnin kasar Saudiyyar.

Hassan Nasrallah ya ce Saudiyya na rike da Mr Hariri ne ba tare da amincewarsa ba.

Ya kuma zargi Saudiyya da ruruta wutar rikici tsakanin Israila da Lebanon.

Kungiyar Hezbollah mai karfin fada a ji abokiyar Iran ce, wadda take zargin Saudiyya da haddassa zaman doya da manya a Lebanon da kuma yankin baki daya.

A wani jawabi da aka nuna kai tsaye a Riyadh a ranar Asabar, Mr Hariri ya ce zai ajiye mukaminsa saboda barazanar da ake yi ma rayuwarsa.

Ya kuma soki Hezbollah da Iran.

Sai dai shugaban kasar Lebanon, Michel Aoun da kuma wasu jiga jigan yan siyasa sun nemi ya dawo gida ya yin da ake zargin cewa Saudiyya ta yi masa daurin talala kuma ita ce ta tilasta masa ya bada kai domin bori ya hau.

Nigeria: 'Dole a samar da wuraren kiwo na musamman'


Dokar hana kiwo a jihar Benue ta janyo cece-kuce a NajeriyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dokar hana kiwo a jihar Benue ta janyo cece-kuce a Najeriya

A Najeriya, yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da dokar hana kiwo da ta soma aiki a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar kasar, ministan noma da raya karkara na kasar Audu Ogbeh, ya shaida wa BBC cewa saboda rikicin da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya, dole ne a kintsa makiyayan wuri guda, sannan za’a samar da wurare na musamman domin shanu inda za’a basu ciyawa da ruwa mai kyau.

Ministan ya ce, idan har aka yi hakan, to su kansu makiyayan ba za su so su yi yawo ba, kuma ko ba komai an kare su daga barazanar masu satar shanu.

Dangane da batun kafa dokar hana kiwo a jihar Benue, ministan ya ce matsin lambar mutane ne ya tilasta wa gwamnan jihar kafa wannan doka saboda tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Mr Audu Ogbeh, ya ce nan ba da jimawa ba za’a fara aiki a wuraren kiwo na musamman da aka kebe, na farko a jihar Kano, sai kuma na jihar Neja.

Ya ce da sannu a hankali mutane za su fahimci cewa lallai ana bukatar naman shanu, don haka dole a inganta yadda ake kiwon shanun.

Ministan ya ce, idan aka kori makiyaya to a ina za’a samu naman da za a ci? don haka dole ne a tanadi kebabbun wuraren kiwo na musamman, kuma za’a yi hakan ne ta hada hannu da gwamnatocin jihohin kasar.

Zakaran kwallon kafar Afirka na 2017


Zakaran kwallon Afirka na 2017

Image caption

Zakaran kwallon Afirka na 2017

Za a sanar da sunayen ‘yan wasan da aka tace don bai wa daya daga cikinsu kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2017 a wani shiri na musamman da za a gabatar kai-tsaye sashen BBC World Service mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya, da tashar talabijin ta BBC World News da shafukan BBC na intanet da kafofin sada zumunta.

Za a soma yada shirin ne daga karfe 6:05 na yamma agogon GMT, zuwa karfe 7:00 na yamma agogon GMT, a ranar 11 ga watan Nuwamban 2017.

Za a bude shafin kada kuri’a da misalin karfe 6:50 na yamma agogon GMT.

Ga kuma ka’idojin zaben a kasa.

Tsarin da aka bi wajen zabo jerin sunanyen ‘yan takarar:

Kwararru a harkar kwallon kafa a ciki da wajen Afirka ne suka zabo ‘yan takarar biyar, bayan da aka bukace su da su lissafa fitattun ‘yan wasa biyar, kuma su jera su daga 1 zuwa 5, (wanda ya fi burge su shi ke da maki biyar).

An kuma bukace su da su yi amfani da ma’aunan da ke kasa wajen zabo gwanayen nasu:

*** Bajinta wajen taka leda (wato iya sarrafa kwallo da kwazo da hadin kai da sauran ‘yan wasa, da taka rawa wajen samar da sakamako mai kyau, da lambobin yabo, da hazaka a daukacin shekarar 2017, da kuma inganta wasa).

*** Tasiri a yankin da dan wasa ya fito (wato gudunmuwar da dan wasan ya bayar ga fannin kwallon kafa da ma wasanni baki daya a yankin da ya fito, a ciki da wajen fili).

*** Muhimmancinsa a duniya (wato muhimmancin da yake da shi a fagen wasan a duniya da kuma cigaban da ya kawo).

An kuma bukaci kwararrun da su yi la’akari da shekarar bana, (daga ranar 1 ga watan Junairun 2017, zuwa yanzu).

Za sanar da jerin sunayen ‘yan wasan ne yayin wani shiri na musamman na kaddamar da gasar a ranar 11 ga watan Nuwamba, daga karfe 6:00 na yamma, zuwa karfe 7:00 na yamma agogon GMT, a tashar rediyo ta BBC World Service da tashar talabijin ta BBC World TV.

Za kuma a wallafa shirin a shafin mu na BBC Hausa.com da kuma sashen kwallon kafar Afirka na shafin wasanni na BBC. <http://www.bbc.co.uk/sport/football/african>

Idan kuma ‘yan wasa biyu suka yi kankankan, to jami’an da ke shirya Gasar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na da hakkin kara yawan ‘yan takarar zuwa adadin da bai haura shida ba.

Ta’arifin wanda ya cancanta:

Duk dan wasan da ya cancanci shiga tawagar wata kasar Afirka, ya cancanci ya lashe kyautar Zakaran Kwallon Kafar Afirka na BBC.

Kada kuri’a:

Da zarar an wallafa sunayen ‘yan wasan da suka cancanta, ma’abota shafukan BBC za su kada kuri’a don zaben wanda za a baiwa gasar.

Za a soma zabe da misalin karfe 6:50 na yamma agogon GMT a ranar 11 ga watan Nuwamban 2017, kuma a rufe ranar 27 ga watan Nuwamba 2017 da misalin karfe 6:00 daidai na yamma agogon GMT.

A ranar 11 ga watan Disamba na 2017 ne da misalin karfe 5:35 na yamma agogon GMT kuma za a sanar da sakamakon zaben kai-tsaye a tashar talabiji da ta rediyo ta BBC Focus on Africa da shafin intanet na BBC Hausa, wato bbchausa.com.

Za kuma a wallafa a sashen kwallon kafar Afirka na shafin wasanni na BBC http://www.bbc.co.uk/sport/football/african> tare da ka’idoji da sharuddan gasar.

Idan aka samu ‘yan wasan da suka yi kankankan, za su raba kyautar.

Yadda za a kada kuri’a – a intanet

A ziyarci sashen kwallon kafar Afirka na shafin wasanni na BBC <http://www.bbc.co.uk/sport/football/african> sannan a bi matakan da aka zayyana.

(Daga shafin mu na BBC Hausa ne za ka latsa:

<http://www.bbc.co.uk/sport/football/african> wanda zai kai ka shafin wasanni na BBC, inda za ka bi ka’idojin zaben.)

Kuri’a daya kawai za a iya kadawa a kan kowacce komfuta.

Kada Kuri’a: Ka’idoji da sharudda:

1. BBC ce ke kula da kada kuri’a, kuma kyautar ta dace da dokokin BBC game da gasa da kada kuri’a, wadanda za a iya karantawa a nan. <http://www.bbc.co.uk/editorialguidelines/guidelines/appendix2>

2. Wanda ya lashe gasar zai samu lambar yabo sannan za a yi masa lakabi da “Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2017”, wato “The BBC African Footballer of the Year 2017” a Turance.

3. Wani kwamitin masana harkar kwallon kafar Afirka ne ya tsara jerin sunayen ‘yan takarar da za a zabi gwarzon daga cikinsu.

4. Ma’aunan da aka yi amfani wajen zakulo wadannan ‘yan wasa su ne:

Iya sarrafa kwallo da kwazo da aiki tare da sauran ‘yan wasa, da samar da kyakkyawan sakamako, da lambobin yabo, da gudunmuwar da dan wasan ya bayar ga fannin kwallon kafa da ma wasanni baki daya a yankin da ya fito, a ciki da wajen fili, da kuma muhimmancinsa ga wasan a fadin duniya da bunkasa shi a daukacin shekarar 2017.

5. Za a bai wa jama’a damar kada kuri’a a kan jerin sunayen a sashen Kwallon Kafar Afirka na shafin Wasanni na BBC <http://www.bbc.co.uk/sport/football/african> (da ma shafin BBC Hausa, inda za ku iya shiga shafin wasani na BBC, domin kada kuri’a;

<http://www.bbc.co.uk/sport/football/african>)

6. BBC za ta yi amfani da bayanan masu kada kuri’a, bisa tanade-tanaden Manufofin Tsare Sirri da na Amfani da ‘cookies’ <http://www.bbc.co.uk/usingthebbc/privacy/privacy-policy> da kuma ka’idojin amfani da shafin <http://bbc.co.uk/usingthebbc/terms/terms-of-use>.

Misali, za mu iya amfani da bayananku wajen tattara kuri’u ko kuma gudanar da bincike a kan duk wata tangarda da ka iya aukuwa wajen yin zabe.

7. Za a rufe kada kuri’a da karfe 6:00 na yamma a gogon GMT a ranar 27 ga watan Nuwamban 2017.

8. Ba za a saurari balle a karbi wani korafi game da sakamakon zaben ba.

9. Wajibi ne a karbi kyautar da aka bayar kamar yadda aka bayyana, ba damar jinkirta ta. Ba za a bayar da kudi a maimakon kyautar ba. Kuma ba za a biya mutum don ya kada kuri’a ba.

10. Daga BBC har masu yi mata kwantiragi, da rassanta da/ko cibiyoyinta, ba wanda zai dauki alhakin ko wanne irin nakasu ko gazawa ko wata matsala game da hawa intanet, ko hanyoyin sadarwa da ka iya haddasa sarayar kuri’a, ko rashin shigarta lissafi.

11. BBC na da ikon dakatar da kuri’a idan ta samu isasshiyar hujjar da za ta kai ga zargin yin magudi ko kuma idan ta yi tunanin an yi yunkurin tafka magudi.

BBC na da ikon musanya hanyar yin zaben a duk lokacin da ta ga akwai bukatar hakan. Don samun damar gudanar da bincike a kan wasu matsaloli da aka iya samu yayin kada kuri’a a bbc.co.uk, BBC ka iya amfani da ‘cookies’ ko ajiye adireshin intanet na na’ura.

BBC ba za ta wallafa wannan bayani ba, kuma ba za ta bai wa kowa ba kan kowa ba ba tare da izini ba, sai dai kawai idan akwai bukatar yin hakan don tabbatar da aiki da wadannan ka’idoji.

12. Duk wanda ya kada kuri’a a wannan zabe ana dauka ya amince da wadannan ka’idoji da sharuddan kuma ya amince ya yi aiki da su.

A lura, dukkan ma’aikatan BBC da suk wani wanda ke da alaka da shirya wannan Gasa bai cancanci kada kuri’a ba.

13. BBC Afirka ce za ta sa ido kan zaben.

14. BBC na da ikon soke ko wanne dan takara, ko hana shi kyautar a duk lokacin da ta ga dama, idan a ganinta bayar da kyautar ga dan takarar ka iya bata sunan BBC.

15. Tanade-tanaden dokokin Ingila da Wales na da ta cewa a kan wannan zaben da wadannan ka’idoji.

Marseille ta kori Patrice Evra


Patrice EvraHakkin mallakar hoto
AFP

Kungiyar Marseille ta soke yarjejeniyarta da Patrice Evra yayin da kuma Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta dakatar da shi na tsawon wata bakwai bayan da ya harbi wani magoyin bayan kungiyarsu da kafa.

Evra mai shekaru 28 ya tokari wani dan kallon kwallon kafar ne da kafa a yayin da kungiyarsa ke shirin fafatawa da kungiyar Vitoria Guimaraes a farkon watan nan.

Yanzu an dakatar da Evra har zuwa watan Yunin 2018, tare da cin shi tarar yuro 10,000.

Dan wasan na Faransa na atisaye ne a lokacin da ya aikata laifin, matakin da ya sa aka ba shi jan kati tun kafin wasan.

Kuma Marseille ta yi rashin nasara da ci 1-0 a wasan.

Karanta wadansu karin labarai

Nigeria: Kotu ta ba da umarnin mayar da Sanata Ndume


Sanata Ali NdumeHakkin mallakar hoto
Other

Image caption

Majalisar dattawan Najeriya ce ya dakatar da Sanata Ndume a watan Maris

Wata babbar kotun a Najeriya ta ce dakatarwar da majalisar dattawan kasar ta yi wa Sanata Ali Ndume ya saba wa doka.

Kotun ta kuma ba da umarnin biyansa duka albashi da alawus-alawus din da ya kamata a biyasa na tsawon lokacin dakatarwar.

Alkalin kotun, mai shari’a Babatunde Quadri, ya ba Sanata Ndume umarnin komawa bakin aikinsa a matsayinsa na dan majalisar dattawan kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya bayyana.

Sanata Ndume ya bayyana wa BBC ta waya cewa: “Alhamdulillahi godiya nake da Allah, kuma nasara ba tawa ba ce. Nasara ce ta dimokradiyya.”

A ranar 30 watan Maris ne kwamitin da’a na Majalisar dattawan kasar ya dakatar da sanata Ndume bisa dalilin rashin cikakken bincike kafin gabatar da korafi a gabanta.

An dakatar da shi ne bayan kwamitin da’a na majalisar ya wanke shugabanta Bukola Saraki, da Sanata Dino Melaye daga zargin shigo da mota ba bisa ka’ida ba da kuma amfani da takardar shaidar digiri na bogi.

Xavi: Tsohon dan wasan Barcelona da Spaniya zai yi murabus a karshen kakar wasan bana


XaviHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Xavi ya bar Barcelona a shekarar 2015 da wasu kalamai masu ratsa zuciya kuma ya koma Al-Sadd, wadda ya taimaka wa ta lashe kofin Qatar a watan Afrilu

Tsohon dan wasan Barcelona Xavi ya shirya domin ya yi murabus a karshen kakar wasa ta bana, ya kuma fara aikin koci.

A yanzu haka dai dan shekara 37 din, wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau hudu da gasar cin kofin duniya, yana murza leda ne wa kungiyar kwallon kafa ta Qatar Al-Sadd.

Amman yana jin iya mayar da kuzarinsa bayan wasa yana raguwa.

Ya ce: “Lallai wannan zai kasance shekarata ta karshe a taka tamaula. Ina son in sami lasisina na zama koci a shekara mai zuwa.”

Xavi, wanda ya buga wa Spaniya kwallo sau 133 a shekara 14 da yayi yana murza mata leda kuma ya samu ya ci gasar kofin duniya a shekarar 2010, ya ce lokacin da ya yi a Gabas ta tsakiya ta ba shi damar hutawa.

Karanta wasu labaran:

Wanda ya fallasa dalolin da EFCC ta kama a Lagos ya 'zama miloniya'


NairaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta ce mutumin da ya fallasa kudin da aka boye a wani gida a unguwar Ikoyi da ke jihar Legas “ya zama miloniya.”

Shugaban riko na hukumar, Ibrahim Magu, ne ya tabbatar da haka a wani taro a birnin Vienna na kasar Australiya, in ji sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya fitar.

Uwujaren ya tabbatar wa BBC cewa hukumar ta bai wa wanda ya fallasa boye wadansu makudan kudade a wannan gida, amman ya ki ya bayyana nawa aka bai wa mutumin.

A shekarar da ta wuce ministar kudin Najeriya, Kemi Adeosun, ta bayyana shirin gwamnatin kasar na bayar da tukuicin kashi biyar cikin 100 ga duk wanda ya fallasa “haramtaccen kudin” da ake zargin na sata ne.

Hakkin mallakar hoto
EFCC

Image caption

Magu ya ce hukumarsa tana bai wa wanda ya samu tukuicin shawara game da yadda zai kashe kudinsa

Idan aka yi la’akari da cewa kudin da aka samu a gidan na Legas a farkon shekarar nan ya kai naira biliyan 13, za a iya cewa wanda ya kwaramata bayanin kudaden zai samu kimanin naira miliyan 650 (kashi 5 cikin 100 na kudin da aka samu a cikin wani bene a Legas).

Bayan hukumar EFCC ta yi wawan kamun ne dai aka gano cewa kudaden suna da alaka da tsohon shugaban hukumar leken asirin Najeriya ta NIA, Ayo Oke.

Wannan ya sa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sa aka dakatar da Mista Oke daga farko, kuma ya kore shi daga baya.

Gwarzon dan kwallon BBC: Za a sanar da 'yan takara


BBC African Player

Image caption

Riyad Mahrez ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon BBC na Afirka na 2016

A ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, za a bayyana ‘yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na BBC na Afirka na bana su biyar da za a zabo wanda babu kamarsa.

Za a sanar da ‘yan takarar ne a lokacin da ake gabatar da shiri kai tsaye na hadin gwiwa a BBC World News da BBC World Service da kuma ta yanar gizo da karfe 18:00 agogon GMT, daidai da karfe 7:00 na yamma agogon Nigeria da Niger.

A can baya dai zakakuren ‘yan kwallon kafar Afirka sun lashe wannan kyautar ta gwarzon dan kwallon BBC na Afirka da suka hada da Didier Drogba da Yaya Toure da Jay-Jay Okocha da kuma George Weah.

Wadanda za su tantance ‘yan takara su kuma tattauna a kan su, sun hada da Emmanuel Amuneke na Nigeria da Arnaud Djoum na Kamarau da kuma Jean Sseninde ta Uganda.

A cikin watan Disamba nan ne hukumar kwallon kafa ta Afirka Caf, za ta bayyana gwarzon dan kwallon kafa na Afirka da babu kamarsa da za a yi bikin a Ghana.

'Yadda aka tsaga gabana aka sa magani domin mallakar miji'


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wata wadda ta ce ta mallaki mijinta ta hanyar sanya magani a gabanta
 • Za ku iya latsa alamar lasifika da ke sama domin jin bayanin da ta yi.

Wata matar aure wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Fatima Zahra Umar a shirin Adikon Zamani cewa, “ba ta taba samun ikon mallakar mijinta ba sai lokacin da ta je wurin wata mai maganin mata na gyaran gida ta tsaga mata gabanta tare da sanya magani a ciki.”

Ta ce “duk matan da suke cewa kayan mata ko kuma gyaran jiki karya ne to ba su san dawan garin ba ne kawai.”

Irin wannan batu na gyaran jiki ko kuma tsare gida da mata ke yi na janyo kace-nace a tsakanin magidanta har ma da malaman addini.

Cikakkiyar hirar za ta zo muku ne a shirinmu na Adikon Zamani a ranakun Asabar da Lahadi da karfe 7:30 na safe agogon Najeriya da Niger.

Da fatan za ku kasance da mu domin jin cikakkiyar hira da wannan mata da sauran mata da ma kuma ita mai yin tsagun.

Karanta wadansu karin labarai