Mai sharhin tamaula ya zuciya ya fice

98272163_videoass.jpg


RefreeHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Talabijin da yake taimakawa alkalin wasan tamaula yanke hukunci

Wani mai sharhi da bayanan tamaula a wani gidan talabijin a Rasha ya yi fushi saboda wani hukuncin da alkalin wasa ya yanke har ya zuciya ya tashi ya bar wurin.

Hakan ne ya sa masu kallon rukuni na daya na Gasar Rasha a talabijin suka karasa ganin fafatawa tsakanin Torpedo Vladimir da Tekstilscchik Ivanovo wadanda suka tashi 1-1 babu sharhi.

Lamarin ya faru ne bayan da aka dawo daga hutu mai tsaron ragar Ivaono, Alexei Smirnov, ya yi keta kuma maimakon alkalin wasa Pyotr Miroshnichenko ya bayar da bugun fenariti sai ya ce bugun tazara ne a wajen da’ira ta 18.

Daga nan ne mai sharhin wasan Vladimir Nikolsky ya harzuka da hukuncin da aka yanke; bayan da aka natsu ne aka yi bugun tazarar sai mai tsaron bayan Ivanovo ya sawa kwallo hannu nan ma hukuncin fenariti amma alkalin wasa ya ce a ci gaba da karawar.

Nan da nan Nikolsky ya yi minti biyu yana caccakar alkalin wasan, har ma yake cewa abin kunya ne ga kwallon kafar Rasha, kuma ya mike tsaye ya fice daga gabatar da shirin.

Haka kuma ‘yan kallon wasan suka tashi ba tare da sharhi da bayanan fafatawar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *