Southampton ta kori Mauricio Pellegrino

100390935_gettyimages-855911254.jpg


SouthamptonHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Southampton tana ta 17 a kasan teburin Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Southampton ta sallami kocinta Mauricio Pellegrino, sakamakon kasa taka rawar gani a gasar Premier.

Southampton ta ci wasa daya daga 17 da ta yi a gasar Premier, kuma Newcastle United ta doke ta 3-0 a ranar Asabar a gasar.

Kungiyar ta nada Pellegrino tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Argentina a watan Yuni, inda ya maye gurbin Claude Puel.

Southampton wadda ke kasan teburi a mataki na 17 da maki 28, za ta karbi bakuncin Wigan a ranar Lahadi a wasan daf da karshe a gasar cin Kofin Kalubale wato FA.Source link ]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *