Yadda suturar ma'aikaciyar banki Musulma ta janyo ce-ce-ku-ce

98265636_g.jpg


Aisha Ahmad's profile photos angered conservative religious elements in Nigeria - but the online attacks also sparked a backlashHakkin mallakar hoto
AISHA AHMAD/FACEBOOK

Image caption

Hotunan Aisha Ahmad a shafukan sada zumunta sun bata wa masu tsattsaurar ra’ayin addini rai a Najeriya

Nada wata Musulma mukamin mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya ya tayar da muhawara a kasar, bayan wasu Musulmai masu tsattsauran ra’ayi daga yankinta na arewacin kasar suka zarge ta da saka tufafi mai nuna jiki – amman wasu kuma suka kareta.

Aisha Ahmad wata babbar ma’aikaciya ce a Diamond Bank, daya daga cikin manayan bankunan Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ke son nada ta domin ta maye Sarah Alade, wata mataimakiyar gwamnan babban bankin kasar wadda ta yi murabus bayan ta shafe shakara 23 a kan aiki.

Misis Ahmad mai shekara 40 ta fito ne daga jihar Neja a arewacin Najeriya, wani yankin da mata ba sa yawan samun ilimi idan aka kwatanta da kuduncin kasar, kuma wani wuri da damarmaki ga mata a kasuwanci ka iya yin kadan.

Duk da haka, rahotanni daga Najeriyar sun ce ta yi karatun digiri daban-daban, ciki har da wanda ta yi daga Cranfield School of Management da ke Birtaniya, kuma ta yi aiki a manyan bankuna daban-daban.

Duk da haka jim kadan bayan sanar da nadin da ake son yi mata, sai tattaunawar ta sauya daga zurfin karatunta zuwa ga yanayin suturarta.

Hotunan da aka dauka daga shafukanta na kafafan sada zumunta sun janyo suka daga masu ra’ayin rikau na addini daga yankinta na arewacin Najeriya.

Wasu malamai, wadanda suke da mabiya sosai a Intanet sun ja ayoyi daga Al-Qur’ani, kuma sun hakikance cewar dole mata su suturta da kyau kamar yadda addini ya tsara – inda suka soki hotunanta da ke ta yawo a shafukan sada zumunta wadanda ba ta rufe kanta ba.

Wani mai suka, Abubakar Almajiri, ya siffanta Misis Ahmed a matsayin “karuwa” a shafinsa na Facebook kuma ya ce nadinta “rashin adalci ne ga Musulmai.”

Almajiri ya yi tir da Shugaba Buhari yana mai cewa: “Muna tsammanin in har bai zabi iri mai kyau daga cikinmu ba to ya zabi Musulmi mai dan girmama addini a wannan matsayin.”

Hakkin mallakar hoto
AISHA AHMAD/FACEBOOK

Image caption

Duk da cewa Aisha Ahmad ba ta ce komai ba game da sukar da aka yi mata ba, wasu sun kare ta a shafukan sada zumunta

Da alama yawancin wadanda suka soki Misis Ahmad maza ne, kuma wasunsu sun nuna rashin jin dadinsu game da nasarar da ma’aikaciyar bankin ta samu domin ita mace ce.

Amman wasu mata masu amfanin da shafukan sada zumunta sun shiga muhawarar.

Wata daga cikinsu, Saratu G Abdul, ta yi tsokacin cewar ya kamata Misis Ahmed ta kasance abar koyi, kuma wasu ayoyin Al’kur’ani sun “hana mata bude jikinsu.”

Amman a daidai lokacin da magana a kan hotunan suka fara jan hankali a shafukan sa da zumunta, sai aka soma sukar masu tsattsauran ra’yin addini.

Gimba Kakanda, wani marubuci a Najeriya, yana daya daga cikin wadanda suka kare ma’aikaciyar bankin.

Da yake magana da BBC, ya ce masu sukar sun wuce gona da iri.

Marubucin da wasu masu irin ra’ayinsa sun bayyana cewa Najeriya, musamman ma arewacin kasar, tana da wasu matsalolin da suka fi tsanani wadanda ba su da alaka da tufafin mata.

“Abin kunya ne cewa muna muhawara kan kan jiki da kuma tufafin wata mace, yayin da sama da yara miliyan goma a Najeriya ba sa makaranta,” in ji Kakanda.

Gimba Kakanda ya kara da cewar: “Ka suranta yaya lamarin zai kasance in da mun bayar da irin himma da fusatar da muka yi wajen bakanta Misis Ahmad kan warware talaucin mai tsanani da karancin ilimi da cin hanci da rashawa a siyasa da kuma ababen more rayuwa da suka baci.”.

A halin yanzu Misis Ahmad za ta fuskanci kuri’ar tabbatarwa a majalisar dattawan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *