Zidane zai doke tarihin Guaradiola a La Liga

98272158_gettyimages-827315512.jpg


ZidaneHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Madrid tana ta biyar a kan teburin La Liga da maki 14

Bayan da aka fara kakar wasan La Liga ta 2017/18, kungiyoyin Valencia da Levante da Betis sun samu maki biyar a kan Real Madrid.

Sai da Madrid ta yi nasarar doke Deportivo da Real Sociedad da Alaves da kuma Espanyol a wasannin da ta buga a waje.

A ranar Asabar ne Real Madrid za ta ziyarci Getafe a wasan mako na takwas a gasar ta La Liga, idan har ta yi nasara ta zama ta farko da ta ci wasa 13 a jere da ta yi a waje.

Real ta ziyarci Villarreal a ranar 26 ga watan Fabrairun 2016 ta kuma doke ta 3-2, tun daga lokacin ta dunga cin wasannin La Liga da ta yi a waje.

Hakan kuma zai sa kungiyar ta doke tarihin cin wasan waje 12 da Barcelona ta kafa a karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Wannan kuma ba shi ne karon farko da Zidane ya doke tarihin da Barcelona ta kafa ba, inda Madrid ta yi wasa 40 a jere ba a doke ta ba, bayan da Barcelona ta yi 33 a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *